Saturday 1 July 2017

AUREN FANSA 12

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹



          🌹12 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com


***

Washe gari aka saka su makaranta. Yanzu abubuwan sun ma Faruk sauk'i tunda yanzu gidan da suke basuda matsala, daidai gwargwado suna samun kulawa sosai, sai dai har yau hoton gawar iyayensa ya kasa 6ace masa kai, ko rufe ido yayi sai ya gansu ya kuma ga mutanen da suka kashe su, sannan sunayen da aka ambata har yanzu ya kasa mantawa hasali ma ya samu diary nasa ya rubuta sunanayen nasu.

Ya samu shak'uwa mai k'arfi tsakaninsa da su Yazeed komai a tare sukeyi su uku abin sha'awa sun had'e kansu. Duk inda kaga d'aya to zakaga d'ayan. Haka ma Anisah da Yusra sun zama k'awaye, ita Jidda ta girmesu don haka sai dai sama sama suke shiri, daga gaisuwa sai kuma cin abinci ke had'a su. Duk da k'arancin shekarun Anisah ta fuskanci Jidda nada wuyar sha'ani sannan miskila ce ta k'arshe, sai dai akwai kuma kirki halayen nata dai gasu nan a baibai, mutum ce mai wuyar fassara, sheyasa ta lura yaran gidan basu shiga harkarta, don haka itama sai tayi baya baya kad'an.
Har yau Anisah ta kasa gane iyayensu sun mutu har abada bazasu dawo ba, don kusan kullum sai ta tambaya. Meyasa suka dawo nan da zama, ina Daddy da Mummy? Yaushe zasu dawo? Haka take tasa Faruk gaba da ire iren wad'annan tambayoyin har idan ya rasa amsa sai tasa masa kuka, dole sai dai yace sunyi tafiya mai nisa kuma zasu dad'e basu dawo ba. To tun wata rana da abin ya fara isarsa ya daka mata tsawa yace tayi hak'uri Mummy da Daddy basu dawowa, da farko ta tsorata amma da Faruk ya zauna yayi mata bayani sai kuma ta fahima, ya kuma d'ora da cewa ta dinga yi musu addu'a kullum, aikuwa tun daga ranar bata k'ara tambayarsu ba haka ma da ta motsa sai tayi musu addu'a.


***

BAYAN WANI LOKACI...

Zaune suke kan dinning suna breakfast gaba d'ayansu, Dada ne ya aje cokalin hannunsa ya soma magana.
"Wai ina Faruk ne?"
Hajiya Rukayya da suke kira da Mama tace
"Inaga yana ciki kamar wanka ya fito."

Sanye yake cikin bak'in wando wulik pencil trowser sai ya d'ora ash shirt marar hannu, tun daga k'afafuwansa ya isa ka gane cewa kyakkyawan mutum ne, don kuwa k'afar tasa fara ce tas kalar larabawa har wani gashi gashi ake gani a tsakankanin yatsanshi na k'afa.
Haka nayi ta d'aga kaina har na sauke su kan fuskarsa... tabbas duk inda ake neman namiji toh a nemi wannan mutumin, gashin kansa irin mai cikar nan ne mai yawa sannan nannad'e yake kamar na jarirai.
'Ya Faruk Dada na jiranka fa za'a ci abinci."
Kai! Wannan Anisah ce ta k'ara girma haka? Lallai idan na tsaya muku bayani bazaku gane ba, kamarta d'aya da Faruk gashinta mai kama dana larabawa an tufke shi daga can tsakiya amma duk da haka sai da ya zubo bayanta, kyakyawa ce itama.
Sanye take cikin light pink dress 'yar kanti.
Murmushi yayi mai bayyana hak'ora yace.
"Ina zuwa."
Da sauri ta fice, turare ya feshe a jikinsa sannan ya zura takalmansa ya fice.
Yana zuwa ya gaida Mama da Dada ya samu wuri ya zauna kusa da su Nabeel. Nan aka soma cin abinci.
Dada ne ya dakata ya soma magana.
"Faruk kamar kullum bazan gaji da ce maka kayi hak'uri ba, wallahi har yanzu kan aiki ake ganin an kamo wad'anda suka kashe iyayenku..."
Faruk yayi murmushi yace
"Haba Dada wallahi babu damuwa, komai lokaci ne, insha Allah Allah zai bayyana mana su."
Dada yayi murmushi, sheyasa yake son Faruk yaro ne mai kaifin tunani, da kuma nutsuwa da hangen nesa. Don haka sai yace
"Haka ne, amma insha Allah za'a cigaba da aiki Allah yasa a dace."
Suka amsa da "Amin."
Dada ya cigaba.
"Kunga yanzu kuna dab da gama makaranta, to kamar yadda nayi alk'awari mazan zan tura su Saudia don neman ilimi, to zan had'a da kai Faruk kowa ya za6i abinda zaije ya karanta. Abinda yasa kuka ga na za6i wannan k'asar saboda nayi k'wak'waran bincike ana tsaro sosai da yaran mutane, to kuma yaro ko yaso koya k'i dole ya kama kansa. Amma kamar kullum bazan gaji da jawo hankalinku ba, don Allah ku nutsu ku tsare mutuncinku, kar kuga bana kallonku to ku tuna Allah (S.W.A) yana kallonku, wallahi kuji tsoronsa abinda kuka je nema shi zakuyi, kunaji ko? Allah yayi muku albarka sai ku dage ku fito da grade mai kyau."
Suka ce
"Amin Dada, insha Allah zamu kiyaye."
A haka suka cigaba da karyawa.


***

"Mami don Allah ki barni zan sa da kaina."
Hajiya Bilki tayi tsaki
"Ke da Allah wuce can, ki bari na sa miki."
Ta zum6uro baki.
"Assalamu Alaikum..."
Bilki ta d'ago tana k'are mata kallo.
"Wa'alaikumusalam."
Daga sama har k'asa na k'are mata kallo, Meenah ce ta girma haka? Tayi tsawo ta k'ara kyau, wannan ita ake kira black beauty, ga gashin kanta duk d'ankwalin da ke kanta hakan bai hana shi fitowa ba...
"Mami na gama wanke kayan."
Bilki ta ta6e baki.
"Kin gyara min kitchen?"
Tace
"Eh na gyara."
"Kinyi shara da wanke wanke?"
Meenah tace
"Eh nayi..."
"Kin wanke toilets?"
"Eh na wanke naki..."
"Na d'akin Zarah fa? Shifa wa zai wanke?"
Ta d'an bata rai.
"Mami home work kawai zanyi sai na wanke, an bamu home work har biyar gashi ko d'aya ban ta6a ba."
Ta doka mata harara,
"Sannu 'yar boko, toh bari kiji bazakiyi ba sai kin gama min aikina tsab a gidannan sannan zaki yi wani home work."
Tayi narai narai da fararen idanunta wadda suke kamar an d'iga madara a ciki.
"Ke! Bansan iskanci ya ina miki magana kin tsaya kina wani kallon mutane zaki wuce ko sai na mauje ki!"
A zahirin gaskiya bawani assignment d'in da zatayi, don ta riga tayi shi da asuba, daman gudun aiki yayi mata yawa sheyasa data gama sallah take home work ko karatu, kawai ta gaji ne tun safe take aiki bata huta ba, daga wannan sai wannan ko kalaci batayi ba...
"Mami zan taya ta."
Bilki ta 6ata rai
"Kiyi ki gani yadda zanyi da ke a gidannan, maza kije kuma kar tayi nata home work d'in sai ta gama maki naki!"
Sum sum Zarah ta fice zuciyarta cike da tausayin Meenah...



MSB💖

No comments: