Tuesday 28 November 2017

JAKAR MATA PAGE 06

🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀
     *JAKAR MATA*
🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    we don't just educate and entertain but we also touches the hearts of the readers.



Na

*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA(Sweery)*
*JANNART LAMEE'DO*
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO (MSB)*

*THE UNTOUCHABLES ARE BACK KEEP FOLLOWING US FOR BETTER STORIES*πŸ‘ŒπŸΌ

# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_




_friends muna masu baku hak'uri da jinmu shiru da kukayi,wannan ya farube sbd wasu dalilai amma yanzu insha allah zaku riga ganin posting dinmu,zamuyi anfani da wannan damana wajen nuna farin cikinmu da jinjina ga masu tambayar lapiyarmu ganin kwanan biyu shiru,wannan nuna mana kuna kaunar untouchables mungode sosai muma muna jinku muna jidaku aduk inda kuke_



Page 6







Botsewa Barrister yayi yace baisan yaci da kanshi ba,sai dai ta bashi a baki harda 'yar shagwab'an shi.


Abin nashi ba k'aramin birgeta yayi ba,nan take taji ya k'ara shiga ranta sosai.


Haka ta dinga bashi sai da ya k'oshi,itama nata borin ta tayar akan saiya bata,tsayawa kawai yayi yana kallan sabon salon shagwab'a dan gani yayi nashi nafila ne domin yarinya ta koma masa ,harda biga k'afa takeyi,da k'yar ya shawo kanta ya bata taci ta k'oshi.



Sun d'an tab'a hira kad'an kafin suka haura sama.



Ganin sun tashi yasa Sadiya komawa d'aki da sauri daga inda take lab'e,dan duk abinda sukayi tana kallansu,kuma ba k'aramin birgeta sukayi ba, taso ace itace a wannan matsayi.




Soyayya sosai suka watsa bayan wani lokaci Jalilah tayi wanka,wasu english wears ta saka wanda sukai matuk'ar karb'an jikinta,Barrister ya yaba wannan shiga tata sosai dan har kyauta saida yayi mata.cikin salon soyyaya tace bari in lek'a wajen friends d'in nawa karsu jini shiru. Yace "Ok ba damuwa amma karkije a haka kisa mayafi ko doguwar riga." kanta ta kalla tace "dear bafa gun namiji zaniba,wajen friends d'inane sannan matane dukanmu."




"Nasani amma kisa ba komai."
Wata after dress tasa tayi
rolling da gyalanta ta tafi.


Tsayawa tayi cak akan step tana tunanin ta ina zata fara cema friends d'inta su tafi a gidanta,kai gaskiya abin da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa,ai zasu d'aukeni da wani manufa maybe ma k'awancenmu yayi rawa koma mu b'ata gaba d'aya ni kuma bazanso hakan ba,nasan friends d'ina ba sauk'i,kumafa koni akaima haka bazanji dad'iba.



Toh ke miye naki inma kun b'ata,dama yanzu ke ba class d'insu bane you're now a married woman,ki barsu ki rik'e mijinki, duk a zuci taketa faman sak'awa da kwancewa.



K'arar bud'e toilet d'in da Barrister yayi shiya dawo da ita daga tunanin da takeyi,da sauri tayi hanyan d'akin friends dinta.




Shigarta keda wuya suka dau ihu kamar had'in baki suka taho a tare suka rungumeta,Barrister na jiyo ihunsu yayi tsaki yace "zaku bar gidan ai, sai abi wani sarkin kuma."


"Dear kinga yadda kikayi kyau kuwa? Sai kace wata hasken farin wata a daren sha biyu, gaskiya da alamun aure ya karb'eki kwana biyu kacal amma kiga lots of changes a tare dake gaskiya Barrister yana shanawa danya tsinci dami a kale." cewar Zee-Zee.


Murmushi Jalilah tayi sannan tace "friends bakwa rabo da zaulaya wallahi,ina wani canji anan?" ta fad'a tare da kallan jikinta.


"Dama ke ai ba lallai ki ganiba"

Sai yanzu Jalilah ta kula da kayansu da suka gama shiryawa tsaf,wani dad'i taji a zuciyarta tace Allah yasa tafiya zakuyi,cike da damuwa akan fuskarta tace "friends ya naga akwatuna a tsaye kamar wasu masu tafiya,ko wani sabon decoration ne haka?"



Zee-Zee ne ta matso kusa da ita sannan tace tafiya zamuyi Jalilah,saboda wani uziri daya taso mana amm......" katseta Jalilah tayi da cewa "Amma ai ba haka mukayi dakuba,one week fa kukace zakuyi,amma daga kwana d'aya sai kuce zaku tafi? ko dai wani abu nayi muku dan Allah ku fad'a min." harda kukanta na munafurci dan bataso su fahimci tana son tafiyar nasu.



"Karki damu dear wallahi ba abinda kikayi mana akwai abinda zamu aiwatar ne amma da zarar mun gama zamu dawo,ai bamu gama cin amarciba cewar sadiya."

Dariya suka kwashe dashi dukansu, Jalilah ko na fad'in Allah sa karku dawo cikin ranta, ahaka sukai sallama suka tafi.












*Untouchables*πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀

Wednesday 27 September 2017

WANDA YAYI NISA PAGE 33 to 34

πŸ’—                         πŸ’—                   πŸ’— πŸ’—                  πŸ’—  πŸ’—
*WANDA YAYI NISA*...... _baya jin kira_
πŸ’—                         πŸ’—                   πŸ’— πŸ’—                  πŸ’—  πŸ’—
                       _BY_
      *MARYAM    Y  ZANGO*

*_PURE MOMENT OF LIFE_*
          *_WRITERS_*


_we dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readers_❤


_domin samun littattafan wanan k'unya mai nishad'an tar daku da fad'akarwa shiga wad'annan links d'in_πŸ‘‡

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035



Ina kike

*zainab shukra zakasai*

Wanan shafin nakine Allah ya bar zumunci nagode da addu'an ki gareni nida swt mommah na *aunty sis*πŸ’   Allah k'ara dank'on zumunci.


Gaisuwa mai tarin yawa gareku

*Maryam Ahmad kt*
*Meryerm Abdoul*
*Fatima momyn jiddo*
*Sadnas and momyn sultan*
_iyayen love😍_




3⃣3⃣to3⃣4⃣

Da kuka ta farka da asuba, zuciyarta na k'una, oh ni Juhaifa mai na aikata wa kaina haka?

Shiko gogan bakinshi har kunne da ya d'ibi gara b'asa sosai, shi ya taimaka mata ya kaita toilet ya gasa mata jikinta ya fito ya barta tayi wankan tsarki, sannan shima ya shiga yayi sukayi sallah.

Juhaifa dai tayi shiru tana tinani, lura da hakan da kamal yayi yasa yake ta janta da hira,  yaci gba da ci kata da kalaman soyayya na k'arya dan ya gama fahimtar tana sonshi fiye da tinanin mutum.


Juhaifa taso nuna masa rashin jin dad'inta akan abinda ya faru, amma da yake Kamal cikakken d'an duniya ne haka ya waskar da maganan ya wuce,


Sai da Juhaifa tayi sati tana jinya.

Batare da Kamal ya nuna buk'atar wani abu a gurinta ba, tattali kuwa tana ganinshi sosai, dan ba hali tayi kod motsi ne zai tambayeta me take so,


A ranar kwana na takwas d'inne ya nuna buk'atarsa gare ta,


"Gaskiya nikam a'a wallahi da wahala, sannan ai kasan hakan babu kyau wananma tsautsayine"


"Haba Baby nace miki fa wanan karon baza kiji zafiba, kuma da kike maganan babu kyau bani zan aureki ba, ai dai nasan ni na rabaki da budurcinki, saboda haka karki damu,"


Haka yayi ta kashe ta da dad'in baki har ya samu biyan buk'atarshi,

Washe gari ma haka abun ya faru, sai dai ana gamawa Juhaifa tasa kuka, jawota jikinshi yayi yana rarrashinta daga nan suka k'ara komawa ruwa, a rannan sai da sukayi haka sau uku,

Tun daga nan Kamal ya daina nuna buk'atar shi gareta,

Taji dad'in hakan sosai, amma sai dai me, kwanannan dakyar dake iya bacci in dare yayi saboda azababben ciwon maran da ke damunta, wata rana harda kuka,


Duk abun da takeyi Kamal na lura da ita, dan da gangan ya shareta kwana biyun dan ya gama fahimtar ta tana da tsananin sha'awa dan haka yasan da kanta zata kawo kanta,

Yauma kamar kullum kwance take idonta yayi jajajir ta rasa me zatayima taji dad'i,

Kamal dake kwance ya juya mata baya dariyace fal zuciyar shi,


Jin bazata iya jure abin da take ji bane  ya sata mik'ewa a hankali ta lek'a idon Kamal dan ganin ko yayi bacci, shikuma da gangan yayi likimo,

Ganin bacci ya keyi yasa ta shiga jikin shi ta kwanta a hankali,

Wani nunfashi mai nauyi ta sauk'e jin jikinsu ya had'u a hankali ta k'ara shigewa jikinshi,

Shafa k'irjinshi ta farayi, jin abunnata yayi yawane ya sa shi bud'e idon shi,


Ture ta yayi

"meye haka kike yi ne Baby"


"please Baby kaji tausayina"

"me zan miki ni kuma, kefa kika ce babu kyau yanzu kuma kinzo zaki hanani bacci"

"naji ni dai please ka taimaka min"


"in taimka miki ni kuma ko oho ko?"

"a'a kaima in kana buk'ata bazan hanaka ba please"


"Ok naji amma sai kin min alk'awarin nima duk lokacin da  nake da buk'ata bazaki hanani ba"


"cikin sauri ta amince dan ji takeyi kamar tayi hauka"


Wani lalataccen murmushi Kamal yayi kafin ya shiga sarrafata, a ranan sun gurji juna kamar ba gobe har mamaki yakeyi yaushe Juhaifa tazama haka.



Tun daga nan suka koma rayuwa kamar mata da miji aduk sanda suke buk'atar junansu za su biyawa jina buk'ata ba tare da shayin komaiba.





****************************



"Tinanin me kikeyi ne haka ya Aysha?"


"Hafiz yanzu ka ga fa watan ya Juhaifa tara rabonta da gida, tun ina ganin kamar wata rana zata dawo har na hak'ura, Mama ma ina ganinta wata rana tana kuka kuma nasan duk akan rashin ya Juhaifa ne"


"hmmm wallahi nima abun na damuna amma addu'a shi zamu ci gaba da mata Allah ya dawo mana da ita gida lafiya ya kareta"



"kaga fa ya Haroun kwata kwata ya daina walwala kamar da, "


"Allah dai ya karkato mana da hankalinta gida"

"ameeen ya Allah"



Kwana na tafiya sati wata yanzu shekaran Juhaifa daya da wata bakwai rabonta da iyayenta, tun suna kukan a b'oye har sun dangana sai dai basu fasa addu'an Allah ya kareta ya karkato da hankalinta gida ba aduk inda take



*KADUNA*



πŸ’ž *ummu khady ce*πŸ’ž

JAKAR MATA Page 05

🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀
     *JAKAR MATA*
🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    we don't just educate and entertain but we also touches the hearts of the readers.



Na

*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA(Sweery)*
*JANNART LAMEE'DO*
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO (MSB)*

*THE UNTOUCHABLES ARE BACK KEEP FOLLOWING US FOR BETTER STORIES*πŸ‘ŒπŸΌ

# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_

Page 5


       Kai tsaye bedroom d'in ta ta wuce tayi brush tayi wanka  sannan ta fito wajen friends d'inta


       Suna Ganinta suka saki wani ihu Wanda ya firgita Barrister da ke cikin d'aki,rungume juna suka yi Sadiya tana zagaye Jalila tana k'are mata kallo,cewa take "wow k'awata kar ki so kiga yanda kika yi masifar kyau wlh,Gaskiya amarcin nan ya karb'e ki"



        Dai-dai nan kuma Barrister ya fito daga bedroom d'in shi a sukwane don ihun da ya jin ya zata wani abun ne ya faru Wanda ya sa suka yi ihu haka


        Ganin su a tsaye suna ta nishad'i ya sa shi tsayawa turus yana musu kallon mamaki Wanda su Sam basu ma san yana wajen ba



        Wani takaici ne  ya kama shi ya dube su ya ce "wanne irin rubbish ne kuke min a cikin gida haka? Ya za'ayi Ku dinga mana shouting Kuna d'aga wa mutane hankali? are you all in your right senses?"


       Wani shek'ek'e suka kalle shi,har xee zata yi magana sai kuma  ta fasa ta ja hannun sadiya suka bar palour d'in gaba d'aya, banda jalila wadda ranta ya gama b'aci da abinda Barrister yayi


      Kallon shi tayi had'e da k'ank'ance ido alamar ba mutunci tace masa
"Wai Barrister meke damunka ne haka? Daga yin aure Kwana d'aya duk kabi ka uzzura min da masifa?ka duba time fa 9:30am amma har kayi masifa sau biyu kamar Wanda  ya Kwaba da yunwa, haba ni Gaskiya ba zan yi tolarating wannan abun ba ka dinga min ihu kamar wani Wanda ya haife ni,kai irin Yanda Angwaye suke tattalin Amare ma Sam baka iya ba, kuma Ai da ba haka kake ba"


        Kallon talaici ya Bita da shi ya ce "Ke tunda kike a ina kika tab'a jin k'awayen Amarya suje tare da ita su kwana? Ai su Amaren da ake tattalin nasu ba haka suka yi ba, atleast ya kamata a ce by now we are still asleep,be with each other for some time sai in sami chance d'in tattalin ki amma ki Tara min k'artin mata a gida suna shashanci and u expect me in sa Miki ido? Impossible!!! Better think Right,
Ya wuce ya barta a tsaye da baki a shanye kamar k'ofar gari


       Su kuwa Sadiya da xee-xee suna lab'e suna jin komai don haka da azamar su suka wuce d'akin da suka Kwana suka fara had'a kayan su don niyya suka yi su yi 1 week amma Gaskiya ba zasu iya bala'in wannan Barrister d'in ba



          Jalila na tsaye a palour ta kasa gaba ta kasa baya sai Ganin shi tayi cikin shirin shi tsaf na fita,ya sha ash colour suit yayi kyau sosai


          Zuwa yayi sai wuce ta yace mata "kuma wlh kafin na dawo ki tabbata wancan sakarun friends d'in naki  sun tafi"


       Ganin ya d'au abun da zafi yasa ta fara sassautowa don tana bala'in son shi ta ce "haba dear,yanzu fita zaka yi? Jiya fa Muka tare a gidan nan amma kuma yau zaka fita this early? Haba dear auren soyayya fa Muka yi ba arrange marriage ba amma kuma daga Kwana d'aya mun fara samun misunderstanding"


        Yanda ta langab'e take maganar ya sa shi jin jikin shi yayi sanyi,tabbas abun da ta fad'a gaskiya ne love marriage suka yi amma kuma every couple Wanda sauke newly married suna bukatar privacy amma ba daga tashi ya ga wasu mata haka a gidan shi ba


       Hannun shi ya saka kan waist d'in ta ya goga hancin shi jikin nata wanda hakan ya saukar mata da wani kasala, ya ce "Sweery I dint mean to be so harsh on u,kawai dai its not proper ace daga auren mu wasu su zo su tare mana a gida su hana mu sakewa ba ,ki duba irin ihun da suka yi wallahi I was scared na zata wani abu ne ya faru na tashin hankali amma sai na zo na ga Ku babu abinda ya dame Ku nishadin Ku ma kuke yi"


      "To dear I am sorry kaga childhood freinds d'ina ne, ba zai yiwu in ce musu su tafi kai tsaye ba,amma Ai na san ba Dad'ewa zasu yi ba,kawai dai al'ada ne k'awaye ake turawa da tsohuwa su yi one week a gidan Amarya amma tunda banka so zasu tafi,kaji I am sorry" ta fad'a hadi da kama kunnen ta guda d'aya ta langab'e kanta



        Light kiss ya mata a lips d'inta ya ce "is Ok love"


        Itama kiss d'in ta mishi tace  "tnx so much yanzu mine muyi breakfast and please ka FaSa fita yanzu  kaji"



       Ya ce "ni kan ba zan iya cin jagolgolonsu ba"



      "To ni Gaskiyar kanaso ka bani wahala ba zan iya yin wani sabon girki ba yanzu"

    "Kwantar da hankalinki  ki zo muje zan had'a mana breakfast d'in da kaina kinga na hutar da ke"


      Tsalle ta daka ta d'afe jikin shi tana fad'in  "Yeeee zan ci cooking d'in huby na"


      A haka suka shiga kitchen d'in yana had'a breakfast ita kuma tana taya shi hira har suka gama suka kai dining














*Untouchables*πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀

JAKAR MATA page 04

🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀
     *JAKAR MATA*
🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    we don't just educate and entertain but we also touches the hearts of the readers.



Na

*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA(Sweery)*
*JANNART LAMEE'DO*
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO (MSB)*

*THE UNTOUCHABLES ARE BACK KEEP FOLLOWING US FOR BETTER STORIES*πŸ‘ŒπŸΌ

# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_


*AS ALULLAHUL AZEEM RABBUL ARSHIL KAREEM AYYASHFIKI MY CWT JANNART*😭😭😭

.

Page 4



Hamdala barister Suraj yayi yau Allah ya mallaka mashi farin cikin zuciyarshi,abinda ya dad'e yana mafarki gashi yau mafarkinshi ya zama gaskiya.


Gaisawa yai tayi da mutane ana masa Allah sanya alkhairi bayan nan suka dunguma wajen da zasuyi reception,bayan anci ansha kowa ya watse.



Suma gidansu amarya baa barsu a bayaba wajen hidima,amarya ta sha kyau harta gaji,8:00pm aka kaita gidanta.



Turk'ashi! Yan kai amarya sun sha kallo da mamakin yadda gidan ya had'u.


Gidane madai daici white and black,ma'ana fentin gidan fari sai gate bak'i,k'atan falunane guda biyu ko wanne yasha kujeru na alfarma,d'aya komai na ciki lemon green da bak'i, d'ayan kuma purple da ratsin pinck,sai dining area da kitchen,inka haura sama kuma anan bedrooms suke da toilet,sai kuma wani waje da alamun gun hutawane.



Haka wasu daga cikin yan kawo amarya suka rink'a kwad'ayin dama sune a gidan,k'awayen sadiya kuwa sumane kawai basuyiba dan bak'aramin tafiya dasu tsarin gidan yayi ba.



Tuni suka haura sama suka bud'e d'aki d'aya suka b'ararraje,aka sami side d'aya aka jere akwatina dama ko wacce da akwati tazo da alamunfa sunga wurin zama.



Haka akasha shagali lafiya k'awayen Jaleela d'aki guda suka ware.


Bayan an rako ango komai ya kankama na rufe musu k'ofa na barsu dan suji dad'in aiwatar da ibada lafiya.


Washe gari tunda safe su Zee-Zee suka fito suka d'aura breakfast dafa wancan soya wannan gaba d'aya gidan ya kauraye da k'amshi, Barrister Suraj dake kwance rungume da Jaleela jin hayaniya a falo ne ya tayar dashi daga bacci da sauri ya bud'e ido wani k'amshi yaji wanda ya sashi duban jalila ganinta kwance ne yasashi mamaki da sauri ya tashi ya zura jallabiya ya fita falo.


Daga nesa ya hangosu a zazzaune sunyi rashe-rashe kaman gidan ubansu ko suturan kirki babu a jikinsu, da sauri ya koma d'akin ya fara tashin Jaleela, cikin gigin bacci ta tashi tana cije baki " lafiya irin wannan kiran haka Dear?" .
Cikin had'a fuska yace mata "su waye a gidannan ?" Murmushi tayi tana k'ok'arin komawa baccinta tace "k'awaye nane" tana fad'a taja bargo ta rufu, daskarewa yayi a wajen yana al ajabin abinda tace.


"Jaleela ki tashi muyi magana dan Allah kinsan zaman wayannan a gidannan bai dace ba" tashi tayi cikin fusata tace "Haba Barister nifa banson k'ananun magana dan Allah ka barni bacci nakeji, jiya ka hanani bacci yau ma still kace zaka dameni da zancen banza" sake baki yayi yana kallonta danjin yanda take zuba magana ba ko alamar respect, "ya zama dole ki tashi muyi magana ba tayanda zaayi ace daga auren mu munfara samun matsala" tashi tayi tace "kaga tafiyta inka gama banbamin naka saika fad'a mun" binta yayi da kallonta harta fita daga d'akin zuciyarsa cike da mamaki, wannan wani irin zaman aure zasuyi kenan.

.


Tirk'ashi keeeep following us a kwai chakwakiya agaba.




*Untouchable*πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀

Saturday 23 September 2017

JAKAR MATA Page 03

. 🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀
     *JAKAR MATA*
🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    we don't just educate and entertain but we also touches the hearts of the readers.



Na

*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA(Sweery)*
*JANNART LAMEE'DO*
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO (MSB)*

*THE UNTOUCHABLES ARE BACK KEEP FOLLOWING US FOR BETTER STORIES*πŸ‘ŒπŸΌ

# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_




.

Page 3


Hakance ta kasance da Zuhra da Jalila ko wacce lallab'awa tayi ta shige d'aki,Allah ya taimakesu ba Wanda ya jisu.


Itama zee-zee hakan tayi,tana shiga d'aki ta cire kaya tasa na bacci ta dau waya ta fara sana'a(night call)gwanace wajen iya wayan dare dan bata biyan bashi,kirarin da ake mata kenan tun suna school


Washe gari tun safe suka tashi suka nufi gidansu amarya dan yauce ranar *YAUMUS-SAMARAT*ranar kayan itatuwa kenan,tun safe masu aiki suka fara aikinsu dansu basa aiki sai dai su dauko masuyi su biyasu,ba laifi kayan itatuwa aka tara musu ba abun da babu,sai dai muce babun ce kawai babu,haka aka yankasu in a nice shape aka saka a wani irin glass cup mai murfi designer  tare da spoon aka jere ko wanne a farantinshi.sai da suka tabbatar komai ya dai-dai ta kafin suka bar wajen dan lokacin 3:00pm




Ko wacce wanka tayi me makeup ta shiga aikinta,ba kyarya kowa acikinsu ta fito dan makeup din ba k'aramin kyau ya musuba dayake experfect suka dakko,Sadiya amarya kuwa kamar karka dena kallanta.




Dogayen riguna suka saka different colours dayake haka tsarin yaumus- samat d'in yake,sun fito kamar larabawa,kowacce shigar ta mata kyau,abinfa baa magana sunfito ba kyarya, amarya Sadiya sai d'aukar ido take mu kanmu mun kasa dena kallanta.






Babban hall ne cike yake da mutane kowa ya zauna yana shan kayan itatuwansa,abin ya birge ba laifi,amarya da tawaganta suna shigowa kallo ya koma gurinsu,nan aka saki wata wak'a ta larabci mai sanyin sauti.High table suka hau,wak'ok'in larabawa ake ta sakawa, masu pic da coverage sunata aikinsu.



Bayan dan wani lokaci aka dakata da mokai,zee-zee ta fara bayani"tayiwa kowa barka da zuwa da kuma farin cikin da sukaji dan ganin mutane da dama sun amsa gayyatarsu, tacigaba da cewa,dayake ranace ta kayan itatuwa dan haka zanba amarya shawarwari kad'an dangane da yadda zatayi anfani dasu ta fannoni da dama a gidanta.nan fa ta fara zayyano bayani ke kyace malamar islamiyya ce,ta d'auki lokaci tana bayani kafin ta kammala da yiwa amarya fatan alkhairi ta koma ta zauna,nan fa guri ya kaure da kabbara abu yayi nice.



Ba'a d'auki lokaciba taro ya tashi amarya da  tawagarta sukayi gida.




Dayake gobene d'aurin aure,Baffa Ali kanin mahaifin Sadiya ya kirata yayi mata fad'a,da gani maganganunshi sun tsumata,gaban hijabinta haka ya jike da hawaye da majina,bayan ya gama Anty Karima ta d'aura nata yayar mahaifiyarta kenan,haka Sadiya ta zama so silent cikin daren gaba d'aya sun kashe mata jiki.




Bayan ta dawo d'akinta su Zuhra suka bata baki harta dan saki jiki suka cigaba da shirye shirye da yake duk kansu anan zasu kwana.






A b'angaren ango barister Suraj kuwa suma shirye-shirye suketa fama ba kama hannun yaro,sunyi events  kala-kala wasuma besan dasuba,friends dinshine kawai suka had'a masa,farin ciki kam yana cikinshi,bakin nan ya kasa rufuwa,haka suka raba dare suna shiri.



Asubar fari suka tashi aka d'aura shiri daga inda aka tsaya,dayake d'aurin auren 11:00am ne kafin lokacin suka saita komai.


Lallai yau ranar barister Suraj ce ba laifi ya dau ado,farar shadda yasa mai dinkin babban riga anyi mata aiki da bakin zare, ya d'ora bakar hula da wani bak'in takalmi sau ciki,kayan sunyi matuk'ar masa kyau ,abinka da farin mutum,kana daga nesa zaka jiyo kamshin turarenshi.


Yana shiga gida nan fa abokan wasa suka mai caa kowa da abinda yake fad'a,shidai ba abinda yakeyi sai murmushi,sallama ya yiwa Ummanshi sannan ya fito suka tafi.


Babu b'ata lokaci aka daura auren barister Suraj da Sadiya wanda ake musu lak'abida *SADRAJ*

*Untouchables*πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀

Friday 15 September 2017

JAKAR MATA page 02

🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀
     *JAKAR MATA*
🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    we don't just educate and entertain but we also touches the hearts of the readers.



Na

*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA(Sweery)*
*JANNART LAMEE'DO*
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO (MSB)*

*THE UNTOUCHABLES ARE BACK KEEP FOLLOWING US FOR BETTER STORIES*πŸ‘ŒπŸΌ

# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_

Page 2



   Suna shiga motar khaleed ya rufe glasses d'in Wanda suka kasance tincted ne,ya sakar musu sauti


       Su zuhura sai bin wak'ar suke yi suna rawa inda ita kuma Jalila suke D'an hira sama-sama da khaleed d'inta


     Kai tsaye wani katafaren hotel suka shiga Wanda kyau da tsaruwar sa sai Wanda ya gani,haka suka fito kowacce ta sake shafa powder aka bad'a zafafan perfumes sannan suka fito cikin yauk'i da isa irin na had'ad'd'un chicks


       Khaleed ko hannun shi ya sak'ala a k'unkurun Jalila ya sak'alo ta tana Rungume jikin shi har suka shiga cikin wani hall Wanda tun daga nesa kid'a ke faman tashi



        Suna shiga kallo ya dawo Kansu domin kuwa sun yi kyau sun burge jama'ar da ke wajen Wanda yawancin su 'yan school d'in su


       Daga can kan high table suka hango Amarya da Ango sun yi kyau har sun gaji, straight high table d'in suka nufa domin yin pix da kuma musu Allah sanya Alkhairi


         Sadiya ja'afar Amarya wadda ta kasance itama class d'in su d'aya ta fara washe hak'ora ganin yanda k'awayen nata suka d'au Wanda,Wanda hakan ne ya sa take afahari da su don suna kankaro mata mutunci da wannan wanka nasu




       Da hannu ta ya fito camera man ya zo ya shiga basu pix,sannan daga k'arshe suka koma seat d'in da aka tanadar musu Wanda daga table d'in Amarya sai nasu



       D.j ya saka kid'a mutanen  amu suka taso jiki na rawa suka fara zubar da gallons na rawa suna kwanar shoki





       Ita ko Jalila da yake bata da kankanba kamar su komawa tayi wajen khaleed tace ya bata kud'in lik'i



      Babu musu ya zaro mints na 100naira notes ya bata taje tayi lik'in da shi,hakan kuwa ba k'aramin faranta ran Sadiya yayi ba




      Haka dai aka dinga shan rawa har aka yi sallahr maghriba sannan aka tashi daga wajen luncheon d'in



     Kai tsaye gidan khaleed suka wuce inda zasu shirya domin zuwa wajen dinner d'in Sadiya



Khaleed bai ji kunyar idon su zuhura ba ya fara ya tab'e-tab'en shi a jikin Jalila itama kuma bata damu ta biye masa suka D'an yi charge sannan suka shirya suka wuce wajen dinner around 9:30 pm



      Wani had'ad'd'en material ne black mai kyalli a jiki sai suka saka golden d'in head da golden d'in costume sun yi kyau sosai



        Wajen dinner d'in ya had'u k'arshe don shi ba rawa sai dai an saka cool music



       Ga abinci kala-kala sai Wanda ka zab'a zaka ci,ga drinks komai dai zam-zan

   

       Ba a tashi daga wajen dinner d'innan ba sai 12:00am don Amarya da Ango ma sai past 10:00 suka zo wajen



         Sai da aka fara sauke zuhura sannan aka sauke zee-zee daga can kuma suka wuce gidan su Jalila




          Sun Dad'e a mota suna Dayn tsotse-tsotsen su kafin daga bisani suka hak'ura don Kansu



      Cikin sand'a Jalila ta shige cikin gidan nasu don bata son tayi motsin da za a ji ta a ga time d'in da ta dawo

           Key ta Ciro a jakar ta bud'e gate d'in sannan ta shige part dinta da sauri takalmanta a hannu, zuciyar ta sai lugude take yi don ta san ita da ka ta bata kyauta ba



        Sai da ta shiga cikin bedroom d'inta sannan ta samu nutsuwar zuciya



.       kanta ta d'aga ta dubi agogo inda ya nuna k'arfe d'aya dai-dai,tace "alhamdulillah Allah na gode maka da baka sa an kama ni ba"



     Wullar da jakar ta tayi ta shiga wanka ta fito ta rama sallar la'asar,maghriba da isha'i,bayan ta idar ta kwanta ta fara baccin gajiya


.













*Untouchables*πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀

JAKAR MATA page 01

🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀
     *JAKAR MATA*
🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀🀷🏼‍♀


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    we don't just educate and entertain but we also touches the hearts of the readers.



Na

*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA(Sweery)*
*JANNART LAMEE'DO*
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO (MSB)*

*THE UNTOUCHABLES ARE BACK KEEP FOLLOWING US FOR BETTER STORIES*πŸ‘ŒπŸΌ

# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_

Page 1 by *Faridat sweeeery*




Bissmillahirrahmanurrahim

Gargad'i

Wannan littafi mai suna Jakar mata k'irk'ira mukayi bamuyishi dan wani ko wata ba,sannan bamu yarda wani ko wata ya juya mana littafi ta wani siga ba duk wanda yayi haka bamu yafe ba,
Fatanmu Allah yasa sak'on da muke k'ok'arin aikawa ya isa ga al'umma musamman masu hali irin na Jakar mata.


Wannan shafin naki ne sukutum d'insa *FATIMA MAMYN JIDDAH* natayaki murnan bupday d'inki Allah ya k'aro shekaru masu albarka.



Zaune take a gaban dressing mirrow tana chab'a kwalliya kaman wata amarya da alama dai wani waje zataje mai matuk'ar muhimmanci daga ganin kwalliyar da takeyi, ta shafe nan ta fente nan sai datayi kusan 1 hour tana abu d'aya nidai sake baki nayi ina kallon kwalliya, bayanta kammala ne ta dawo wedrobe neman kayan sawa ta gwada wannan ta canja wannan ita da kanta ta rasa wanda zata d'auka.

Sai data gama ruwan idonta sannan ta d'auko wata atamfa mai ruwan shud'i wanda akaci mutuncin sa da wani lalataccen d'inki duk wanda ya kalli kayan zaiyi zaton bazai shigeta ba tsabar k'ank'antar d'inki.


Da k'yar rigar ta shigeta ballantana skirt d'in sai data had'a zufa kafin tasa Jannart dake gefe sai dariya take Mrs Fawwaz ta toshe mata baki dan karta tona mana asiri aga lab'e mukeyi, sake baki nayi ina kallonta saboda tsabar had'uwar da tayi jaka da takalmi ta d'auko ta mak'ala gyale a kafad'arta sannan ta fito tana chewing gum,batare da tunanin sanar da Mahaifiyarta yanda zataje ba tayi waje a dai-dai gate sukaci karo da Maman kallonta tayi daga sama har zuwa k'asa sannan ta girgiza kai tace "Yanzu fisabilillahi Jalilah haka zaki fita kaman ba 'yar musulmai ba ki duba kiga irin shigan da kikayi?".
Zunburo baki tayi sannan tace "Haba Mama wai meyasa kullum sai kin fad'a mun magana ne in zan fita?, yaci ashe kin gane da banbanci tsakanin zamanin da dana yanzu, da kanku a duhu yake amma yanzu an waye" tsayawa tayi kawai tana kallonta dan ta rasa me mazata ce mata lamarinJalilah sai ita, "Ni na wuce kawai mama" tana fad'a tasa kanta tayi gaba tana karkad'a jiki kaman macijiya,
"Allah ya shirya munke Jalilah ki gane Annabi ya faku".
🀷


Tana fita ta hango wanda yake jiranta a bakin titi yayi parking k'arasawa tayi ta bud'e motar ta shiga peck ya manna mata a kumatu sannan yaja motar suka hau hanya "Bebe ina zamuje ne?" .

Wani fari tayi da ido sannan tace gidansu "Zee-Zee mana kasan sai mun d'aukota kafin mu wuce Vanillah" "ok ba yawa" kid'a ya sake musu kaman zasu tashi sama , chaiii wa'yannan basu san annabi ya faku ba.


A daidai k'ofar gidansu Zee-Zee sukayi parking Jalilah ta fito ta nufi gidan cikin takunta na isa da k'asaita, direct d'akin Zee tayi batare da ta tankawa mutanen data gani a tsakar gidan ba.


A gaban mirrow ta sameta tana rolling gyale a kanta da alama ta gama shiryawa dubanta tayi sannan tace "Ai da nad'auka baki shirya bane wallahi da mun tafi mun barki ina Zuhura take?" Hmmmm ajiyar zuciya ta sake sannan tace "Ai kinsan Zuhura da African time ba tasamu k'arasowa ba" "ai kuwa tafiya zamuyi ba abunda ya shallen…" . kafinta k'arasa maganan Zuhura ta katseta "To marar mutunci basai ku tafin ba".

"Allah yayi saving d'inki 'Yan mata " ha ka suka ringa tad'i harta gama shiryawanta sannan suka fito itama ko kallon arziki batayiwa 'Yan gidansu ba balle su samu jin furucin bankinta Allah ya shirya.













*Untouchables*πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀

Thursday 14 September 2017

AUREN FANSA 47/END

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     πŸŒΉMARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_

     

                🌹47 πŸŒΉπŸ”š


A ranar sukaje wajen Dada, ya dad'e yana sa masa albarka tare da fatan dacewa, sannan ya ce lallai lallai sai ya bashi takardar Jidda don data warke ya mik'a mata, yasan dole zata koyi hankali. Haka Faruk ya rubuta ya mik'a ma Dada, haka ma Mama tayi masa fatan dacewa da sanya albarka. Daga nan suka wuce gidansu Meenah ya shaida ma Baba, Baba ya bishi da doguwar addu'a ya sanya masa albarka.

Sai dai tun ana gobe zai tafi hankalinsa ya tashi bai ta6a tunanin daidai da kwana d'aya zaiyi nesa da Meenah ba gashi har za'a shafe watanni bai ganta ba, yana shigowa d'aki a lokacin tana kwance kan gado ya zauna gefenta yace
"A gaskiya Meenah bazan iya tafiya na barki ba, kawai kiyi hak'uri ki shirya mu tafi tare." Ta juyo tana dubansa tace
"Nidai jeka ka barni, ina nan gida Nigeria bazan iya binka ba a yadda nake jina d'innan."
Ya tur6une fuska ya shiga zayyano mata matsalar da zai shiga idan bata bishi ba, har da cewa tayi differing semester d'in mana idan suka dawo sai ta gyara. Da k'yar ta lalla6a sa yayi hak'uri ya barta, amma idanunshi sun kad'a sunyi ja, haka itama ta wuni tana kuka har bacci yayi awon gaba da ita. A daren ranar Meenah taga tarairaiya kamar wata k'wai, ya dad'e yana shayar da ita zuma kafin kuma suyi bacci mai dad'i.
Washe gari ya fara shirin tafiya, kafin ya tafi sai da ya nemo mata wata mata dattijuwa da zata zauna da ita har ya dawo, haka suna ji suna gani sukayi bankwana har airport ta kaishi, sai data ga tashin jirginsu sannan ta dawo zuciyarta na k'una ta rasa meke mata dad'i.
Haka ta kwana tunaninsa har ciwon kai ya sauko mata wanda kafin safe zazza6i mai zafi ya rufe ta, sai da tayi ta shan magaunguna sannan ta samu taji sauk'i.
Shi kuwa gogan naka yana sauka masaukinsa dama ya siya sabon sim, yana sawa ya kirata, bugu biyu ta d'auka.
"Hello."
"Baby ya nake jin muryarki can k'asa ko jikin ne?"
Ta lumshe idanu tace
"Eh to zazza6i ne yake d'an damuna amma da sauk'i."
Ya rude ya shiga mata tambayoyi.
"Kinsha magani? Yanzu meke miki ciwo? Ya kike ji yanzu?"
Tayi murmushi
"Wallahi yanzu kam bana jin komai sai kasala, so ya hanya? Ya kuma gajiya?"
Yace
"Alhamdulillah, gani nan na sauka masaukina yanzu zanyi wanka sai na kwanta na huta."
Tace
"Ai gara kayi bacci kam, sannu."
Yace
"Yauwa baby, kema sannu."
Sun dad'e suna fira kafin suyi sallama, kowane yana jin kewar d'an uwansa.
Meenah ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali, kullum cikin missing Faruk takeyi sai dai kullum suna mak'ale a waya suna fira basa gajiya da junansu.
Sun cigaba da zumuncinsu itada Zarah kusan kullum suna ziyartar juna, haka ma Anisah wacce ke fama da tsohon ciki itama tana k'ok'ari wajen ganin tana zumunci dasu Meenah.


****

BAYAN WATA BAKWAI

Meenah na zaune a parlor tana cin guava kamar a mafarki taji horn, ta yunk'ura da k'yar ta lek'a ta window ganin motar haya ya sanya ta fara mamakin ko waye?
Bata gama mamaki ba sai data ga ana fiffido da akwatina daga boot, gabanta ya fad'i batayi tsammanin ganinsa yanzu ba, yayi wani kyau yayi k'iba sai k'yallin hutu yakeyi. Ga k'asumbar nan tasha gyara sai walk'iya takeyi.
Ta lalla6a ta fito bakin k'ofa daidai nan ya k'araso yana murmushi, take ya ware hannuwansa duka biyun alamun ta iso  gareshi. Ta dafe cikinta daya turo gaba tare da sunkuyar da kanta k'asa, yayi murmushi tare da takowa daf da ita sannan ya rungume abarsa tsam tsam kamar za'a k'wace masa ita don ma tulelen cikinta ya hana shi ya rik'e ta sosai.
Ya sumbace ta a goshi yana dubanta yace
"Wow! Baby cikinnan fa yayi miki kyau sosai."
Ya k'arasa yana kashe mata ido d'aya, tayi murmushi, ta zum6uro baki cikin shagwa6a tace
"Shine zaka taho ban sani ba?"
Yayi dariya
"I'm sorry baby, just wanted to surprise you daman."
Hannunta ya rik'o suka k'arasa ciki, ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa yana ta zolayarta wai yanzu ta zama k'atuwa ko tafiya da k'yar takeyi, ita dai sai dariya takeyi. Bayan ya huta kuma ya shiga bubbud'e akwatina yana fiddo mata tsarabarta, kaya ne mak'il akwati guda na kayan baby wanda babu abinda babu a ciki, kaya masu kyau da tsada, sai akwati guda nata wanda ya k'unshi leshi, atamfa da su kayan bacci da kayan kwalliya da sauransu, tayi murna tayi ta masa godiya ba adadi.
A ranar dukkansu sunyi kwanan farin ciki da kuma kewar juna.
Washe gari sai ga Jidda itama ta warke ras, tazo neman gafara kuma duk sun yafe mata, tace ta samu mijin aure, sun taya ta murna da fatan alkhairi inda har Faruk yayi mata alk'awarin bata tasa gudumuwar.

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah yau Allah ya sauki Meenah da misalin k'arfe biyu na dare, Faruk yana tare da ita har ta haifi santalelen d'anta k'ato mai k'oshin lafiya, bayan an gyare shi tas aka mik'a ma Faruk shi sai kallonsa yakeyi cike da sha'awa, ya sumbati kumatun Meenah yace
"Wane suna zamu sa masa?"
Tayi murmushi tace
"Duk sunan da kaga ya dace dashi ka sa masa."
Yayi masa hud'uba da sunan mahaifinsa wato Adam amma za'a ringa kiransa da Khalifa.
Ranar suna anyi taron suna lafiya kuma ya k'ayatar mai jego tayi fes da ita tana sanye cikin wani golden lace sai k'yalli takeyi kamar wata amarya.
Mai jego da d'anta sun cigaba da samu kulawa sosai a wurin Faruk, ga yalwatar arzik'i musamman da akayi masa k'arin girma kud'i sun zauna masa sosai, hakan yasa Meenah ta bashi shawarar ya gina masallaci ya kuma ringa bada tallafi a gidan marayu, ba k'aramin dad'i shawarar nan tayi masa ba, yayi tasa mata albarka yana jin dad'i.
A haka har sukayi arba'in inda ta cigaba da karatunta a lokacin ne kuma ita Zarah ta haifi d'iyarta mace sun sha suna babyn taci sunan mahaifiyar Nabeel wato Sadiya, za'a ringa ce mata Nasreen.
A yanzu su Meenah har sun kammala karatunsu suna jiran result.


****

Zaune take tana shayar da Khalifah Faruk ya fito daga d'aki da alama bacci ya tashi, yana zuwa ya rank'wafo yana sumbatar kanta, yace
"Zo muje na baki wani abu."
Ta mak'ale kafad'a alamun a'a tace
"Nak'i wayon, nasan dalilin da yasa ka kirani."
Yayi murmushi yace
"A'a fa result d'inki zan nuna miki."
Da sauri ta aje Khalifah ta mik'e tsaye tana murmushi tace
"Da gaske? Mu je nagani."
Ya wuce tabi bayansa suna shiga yasa ma k'ofar key yana dariya k'asa k'asa, tace
"La daman wayau zakayi min ko? Ni gaskiya ka bud'e min na fita."
Yace
"Nak'i, ga key d'in zoki k'wata."
Ta nufo sa ta fara k'ok'arin k'wace key d'in aikuwa ya damk'e ta yace
"Wana kama?"
Ta fara kukan shagwa6a tana fad'in.
"Wayyo my soul, mun bar Khalifah shi kada'ai a parlor fa kar yayi kuka."
Yace
"To tsaya mu nema masa k'anwa sai ki tafi."
Tace
"Nidai a'a."
Yace
"Aiko baki isa ba."
Ya fara k'ok'arin zage mata zip da k'yar tayi nasarar k'wace kanta tana ta faman dariya sosai sannan ta d'auki pillow ta jefe shi da shi har yanzu bata bar dariya ba. Nufo ta yayi ya chafke ta yace
"Zan baki punishment, kina jifan mijinki."
Kafin tayi magana ya had'a bakinsa na nata....



            ALHAMDULILLAH!!!



Alhamdulillah da Allah ya nuna min farkon book d'innan da k'arshensa lafiya! Darasin dake ciki Allah ya bamu ikon d'auka, kuskuren da ke ciki Allah ya ka yafe mana.

Godiya ta musamman ga dukkanin masoya na da wanda na sani da wanda bansani ba kusani a duk inda kuke ina k'aunarku.
Fatan alkhairi ga duk wani mai karanta novel d'ina, Allah ya bar zumunci Amin.
Daga k'arshe ina mai bak'in 😭😭cikin sanar da masoya na cewar zan dakatar da rubuta 😭😭😭novel zuwa wani lokaci bisa wasu dalilai wanda basai na fad'e su ba da fatan masoya na zasuyi min uzuri zasu kuma fahimce ni, nagode da k'aunar da kuke nuna mun nima kusani ina k'aunar ku a duk inda kuke.😘



MSBπŸ’–

AUREN FANSA 46

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     πŸŒΉMARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_
     
                🌹46🌹


Da mamaki Meenah tace
"Jidda kuma? Meye mahad'inki da ita?"
Budurwar tace
"Nasan zakiyi mamakin idan na sanar da ke ni ba kowa bace face Lubabatu wacce aka fi sanin da Luby..."
Meenah ta mik'e tsaye a razane tace
"Luby? Kece haka?"
Luby da kanta ke k'asa tace
"Eh nice! Nice Luby aminiyar Jidda, ki zauna Zan k'arasa bayani na."
Ta k'i zama still tana kallonta da mamaki, Luby ta sake d'agowa tace
"Ki zauna don Allah ba don ni ba."
A hankali ta koma ta zauna tace
"Ina jinki." Luby ta cigaba
"Kamar yadda na fad'a miki a baya cewar na had'u da Jidda a wurin bikin wata 'yar makarantar mu da akayi, duk da ba ajinmu d'aya da Jidda ba amma a ranar muka k'ulle muka zama best friends. Nice sanadin lalalacewar Jidda, ni na d'ora ta bisa gur6attaciyar hanyar ita kuma ta bi, a tare muka cigaba da harkar mu ta bin maza da sauransu. Nidai yanzu ba komai ya kawo ni ba illa nazo neman gafararki, ba don ni ba don Allah ki yafe min, nayi kuskure amma yanzu na gane kuskure na, ki gafarce ni..."
Meenah tace
"No kar ki damu ni banida rik'o, kuma na yafe maku, Allah ya tsare gaba, sai dai garin yaya kika ji wannan ciwon haka a hannu?"
Ta kai dubanta ga hannun dake nad'e da bandage gaba d'aya tace
"Wannan a ranar muka samu sa'insa da mahafiyata akan ina so na fita da misalin k'arfe takwas na dare, a lokacin mahaifiyata ta tashi tace ita sam bazan fita ba, niko na dage akan sai na fita sai dai ayi wacce za'ayi, na fad'a mata maganganun sannan nayo hanyar waje, sai dai daidai bakin k'ofa mahaifiyata ta tako da sassarfa tana fad'in, Lubabatu idan kika sa k'afa kika fita ban yafe maki ba, daga haka kawai ta juya ta koma gida, ni kuma kawai naja tsuka na fice abina ba tare da na damu ba. A ranar hotel muka kwana bayan mun gama abinda mukeyi muka zarce club, muna can har asuba, sai da gari ya fara haske sannan muka fito don komawa gida. Sai dai me? Muna kan hanya nida saurayin nan nawa muna jin kid'a muna rawa a mota ba tare da mun ankare ba muka yi had'ari, shi saurayin nawa take ya cika ni kuwa asibiti aka wuce dani rai a hannun Allah, sai dana kwana bakwai ban farfad'o ba, bayan na farfad'o naji likita na cewa sai an yanke min hannu, nayi kuka nayi kuka, nayi bak'in ciki, nayi nadama ba kad'an ba. A ranar nayi Allah wadarai da son abin duniya gami da bijire wa iyaye, nidai cewa nayi ban yarda ba, daga nan akayi wa hannuwa na hotuna (Scan) kusan kala uku, gashi banida kowa dole ni likitan yake tunkara da maganar. Yace min k'ashin hannun ya lalace da yawa, ya ratattake k'ashin, wato sai an yanke su, ido waje na zaro nace
"Duka hannuwa na?"
Yace
"Eh to, zai iya yiwuwa dukansu amma gaskiya hannu d'aya yafi samun dameji wanda idan aka d'auki lokaci zai iya ru6ewa, zamuyi iya k'ok'arinmu muyi miki 'yan dabaru a shi d'ayan hannun, idan Allah ya taimaka sai ya zauna. Sannan abu na biyu wurin yin 'yan bincikenmu mun gano kina d'auke da wannan cutar wato cutar H.I.V AIDS."
Luby ta d'an dakata saboda kukan da yaci k'arfinta, haka itama Meenah sai da tayi hawayen, Luby ta cigaba.
"Wani abu naji ya sokeni a k'irji kamar an sara mani mashi, kuka nakeyi tamkar raina zai fita, gaba d'aya duniyar da abinda ke cikinta sun fitan min a rai, likita ya zayyano min kud'in aiki wato gaba d'aya miliyan biyu harda rabi, kaina ya d'auki chaji sosai, nace su sallameni na tafi na samo kud'in aikin sai na dawo. Suka sallame ni nayi gidanmu, na tarar da mahaifiyata tana ganina ta razana tana tambayar meyasame ni, na koro mata bayani, tayi ta min fad'a tace ita ba ruwanta dani don haka na tafi na nemo kud'in da kaina daman na saba neman kud'i, ta koro ni na fito ina kuka. Babu wadda ta fad'o min rai kamar Jidda, nasan ko bata bani kud'i ba zata taimakeni da shawara, sheyasa na taho nan."
Meenah ta kalli Luby kallo na k'urilla sannan itama ta koro mata nata bayanin.
"A gaskiya Luby idan har kud'in aiki kike nema sai dai kije ki nemi taimako kamar su gidan radio, wurin manyan k'asa, sannan Jidda da kika zo nema bazaki same ta ba, saboda Jidda dai ta haukace."
A razane tace
"Ta haukace kuma?"
Meenah tace
"Eh ta haukace, a ranar da kuka je wurin boka amso maganin da zaku sa min ta saka min ya koma mata, tun daga wannan ranar ta fara hauka tana tona muku asiri, yanzun ma zancen da nake miki ana can ana hadaniyar fidda ta can k'asar waje neman magani. Luby wato ita daman duniya haka take, duk yadda ka d'auke ta haka zata zo maka, tabbas kin tafka babban kuskure a rayuwarki, waya ce miki iyaye abin wasa ne? Musamman uwa, kin wulak'anta uwarki ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kin bi boka ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kinyi zina ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki?  Shekara da shekaru kina shayar da mahaifiyarki gubar 6acin rai, ke ba yarinya ba ak'alla zaki kai shekaru ashirin da shidda yanzu a yadda nake kallonki, yaci ace yanzu kina gidan mijinki kina bautar Allah amma kin tsaya shashanci, shekarunki sun kai ace kinyi hankali ki gane halin da duniya ke ciki, abinda yafi miki kije ki rungumi mahaifiyarki ki nemi gafara, ki mata biyyaya sannan ki gyara rayuwarki tun kafin ki koma ga mahaliccinmu. Ina so ki maida komai kamar tafiyar ruwa ki kuma tari gaba, ki yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau, wallahi Allah gafurur Raheem ne, kuma insha Allah  nima zan taimaka miki da wani abin, cikin gadon mahaifina zan baki wani abu sai ki k'ara cikin kud'in aikin da za'ayi miki."
Ta bud'e baki cike da mamaki sai kuma hawaye suka fara wanke mata fuska.
"Meenah, nagode! Nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya k'ara bud'i, Allah ya jik'an iyaye yayi mana gafara, bani da bakin da zan gode maki, na bibiyeki da sharri ke kuma kin saka min da alkhairi, haka rayuwa take daman ko wannan ya ishemu ishara."
Meenah tayi murmushi
"Kar ki damu, bakomai wallahi ai yiwa kai ne, wannan ba wani abu bane."
Tana kallo Meenah ta mik'e ta shiga d'aki, ba'a jima ba ta dawo hannunta d'auke da paper, ta zauna tana mik'a mata.
"Gashi."
Tasa hannunta mai d'an lafiyar ta kar6a tana kuka, Meenah tace
"Yanzu shiga ta na kira Faruk, na masa bayani shine yace na k'ara miki shima ya bayar." Luby ta duba tace
"Har dubu d'ari uku? Kai nagode Allah ya k'ara bud'i."
Meenah tace
"Wannan ba abu bane ba babu damuwa, Allah ya k'ara tsare mana imaninmu, ya tsare mu daga fad'awa halaka, Allah ka shirye mu ya ganar da mu."
Luby tace "Amin ya Rabbi."
Luby bata tafi ba sai da Meenah ta bata abincin rana tana mai k'ara mata fad'an ta nemi yafiyar mahaifiyarta, a haka ta bar gidan tana mai jinjina al'amarin.

BAYAN SATI BIYU

****

Ranar wata talata, tana zaune taji horn d'in motarsa, ta mik'e cike da mamakin ganin ya dawo da wuri, ta lalla6o ta fito don tun jiya bata jin dad'i. Ta k'arasa wajensa sai fara'a yakeyi yana mata murmushi itama tana tayasa duk da batasan dalilin farin cikin nasa ba. Ta kar6o jakarsa suka jero har parlor ta dire jakar ta d'auko masa ruwan sanyi a fridge ta tsiyaya masa ta bashi.
Bayan ta zauna tace
"Lafiya ka dawo da wuri yau?"
Ya kuma dubanta yace
"Lafiya lau, tafiyar nan ce ta taso wai jibi jibin nan zamu tafi, kin tuna maganar da mukayi a baya ko?"
Tace
"Eh na tuna."
Yace
"To itace yau abin ya ida tabbata."
Tace
"Masha Allah, yanzu jibi zaka tafi?"
Yace
"Insha Allah."
Tace
"Zaku dad'e kenan?"
Yace
"Da shekara biyu zamuyi amma yanzu insha Allah bazai wuce shekara d'aya ba mun juyo, kuma in mun dawo zamu iya samun chanjin aiki da kuma k'arin girma. Yanzu ma so nake naje na shaida masu Dada maganar kuma ke nakeso ki raka ni."
Ta d'an yamutsa fuska tace
"To amma fa ni bana ma jin dad'i."
Ya zaro idanu yana k'are mata kallo, yace
"Kodai abin arzik'in ne ya samu?"
Tace
"Me kenan?"
Yaja hancinta yace
"Kinfini sani, amma banga ta zama ba tashi zakiyi mu tafi asibiti a auna ki don a tabbatar."
Kafin ma tayi magana ya zura mata hijabinta pink color tare da jawo hannunta suka nufi mota.
Ba k'aramar murna Faruk yayi ba da yaji daga bakin likita cewar ciki ne da ita har na kusan wata biyu, tun da suka shiga mota yake washe hak'ora kamar gonar auduga.



MSBπŸ’–

AUREN FANSA 45

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     πŸŒΉMARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# *http://maryamsbello.blogspot.com

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_❣️
     
                🌹45 🌹


Ya d'an yi tsai yana dubanta, ta kawar da fuskarta gefe, yace
"My baby, ki tausaya min ki kula ni, idan har kika za6i ki guje ni to wallahi rayuwata tana cikin matsala, nayi laifi tabbas kuma na gane kuskure na har ma na bada hak'uri, to meyasa bazaki yafe min ba? Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare mu mutane? Wallahi ina k'aunar ki, da zaki bani dama da na nuna maki hakan Meenah..."
Shirun dai ta kuma yi, yace
"To in bazaki yi magana ba, kiyi hak'uri ki saki ranki, kin hak'ura?"
Ya shafi fuskarta yana mai juyo da ita, take tayi k'asa da k'wayar idonta.
"Kinji ni baby? Ki tuna matsayina a gareki, na baki hak'uri kiji tausayina don Allah Meenah. Da me zanji? Kina fushi dani kink'i hak'ura, ke kad'ai fa guda nakeda a halin yanzu, ina zansa kaina Meenah? Please please! Tuba nake, na tuba bazan k'ara ba, kar6i wannan takardar ki gani abin farin cikin da ya same mu."
Ya zura mata takardun cikin hannunta, ta kalla shek'ek'e ba tare da ta karanta ba ta mik'a masa yace
"Yanzu har kin duba baby?"
Ta gyad'a masa kai, yace
"To me kika gani?"
Tace
"Oho!" Kalmar data ambata a ciki kenan ashe ta fito fili, yayi murmushi yace
"Daman wannan takardar k'arin ilimi ne aka tura ni na tsawon shekara biyu wanda zanyi shi a k'asar ingila, shine nake neman shawararki saboda karatunki."
Har ranta taji dad'in alherin da ya same shi wanda ta tabbata yaga hakan a fuskarta
Sai kawai ta ce masa
"Na taya ka murna, sai dai duk yadda ka tsara yayi min."
Yayi murmushi yace
"Alhamdulillah naji dad'i, sai dai inaga kamar zamanki a nan don ki k'arasa karatun naki yafi, amma zan rink'a waiwayanki, bawai natafi har sai na kammal ba ne, a'a zan rink'a ziyartarki, donma in banda ina son kiyi karatun da k'afata k'afarki, yanzun ma idan kinfson mu tafi taren sai mu ajiye shi gaba kya yi shi."
Ba tare da ta kalleshi ba tace
"Babu damuwa, kaje zan zauna."
Yayi murmushi yace
Ay da yake yanzu level 3 zaki shiga kinga dana dawo kin kammala insha Allah, kinga dana dawo sai mu baje soyayyarmu yadda ya kamata."
Tace
"Allah ya taimaka."
Haka yayi ta lalla6a ta kamar k'wai, sai wani riritata yakeyi yana yi mata kalamai masu tausasa zuciya har ya samu ta d'an sauko daga dokin data hau har ma tana d'an kula sa.


Washe gari ne yayi shirin aikinsa, bayan ya kimtsa ta raka shi bakin motarshi yace mata yau da wuri zai dawo yaci abincin rana ta masa amala da miyan ku6ewa d'anya, ta bishi da "To." Da fatan dawowa lafiya.
Yana tafiya ta tashi tayi wanka ta kimtsa gidan sannan ta hau mota tare da kud'in da ya bata ta nufi kasuwa, ta siyo garin amala da k'ashin rago da ku6ewa, tana dawowa ta fad'a kitchen ta fara kacaniyar dafa abinci, k'arfe d'aya da rabi daidai ta gama 1:30 pm, tana gamawa ta fad'a wanka ta fito ta shirya cikin wata atamfa dark blue d'inkin riga da skirt d'inkin ya zauna dabas a jikinta.
Amma shiru ba alamunshi har wajen uku, ta d'auko wayarta ta shiga neman layinsa nan ma bai d'auka ba. "Oh God!" Ta fad'a tare da jefar da wayar ta mik'e bisa doguwar kujera, sama sama bacci ya ringa fisgarta tana k'in yi don bata son baccin yazo.
Can wayarta ta fara ruri ta mik'e zumbur ta d'auka yace
"Baby zan aiko a d'aukar min abincin nan don meeting zamu shiga yanzun nan, idan nace sai na dawo kafin na koma zan makara."
Tace
"Sai ka turo bakomai."
Ta mik'e ta had'a shi cikin basket, ta kira d'an almajirinta Yusha'u tace
"Koda bacci zai d'auke ni idan wani yazo ka d'auko basket bisa dinning ka mik'a masa."
Yace
"To Anty."
Ta koma tayi kwanciyarta. Itace bata tashi ba sai k'arfe hud'u har da 'yan mintina, tashinta yayi daidai da k'wank'wasa k'ofa, ta mik'e zaune daga kwanciyar tana gyara d'aurin d'ankwalinta, sannan ta mik'e tayi tattaki izuwa bakin k'ofa gami da bud'ewa.
Wata budurwa ce sai dai ko ba'a fad'a mata ba tasan yarinyar tana cikin matsala babba.
Ta bata izinin shigowa, ta koma kitchen ta had'o mata kayan lashe lashe da tand'e tand'e, ta koma ta zauna suka soma gaisawa a mutunce, Meenah tace
"Baiwar Allah sai dai ban gane ki ba, sannan meya faru da ke haka naga jikinki duk ciwo haka?"
Maimakon budurwar tayi magana sai kawai ta durk'usa har k'asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsanani.
Meenah ta razana tana tambayar lafiya? Da k'yar budurwar ta tsagaita daga kukan da takeyi sannan ta fara magana cikin sanyin jiki.
"Mu talakawa ne tu6us, wanda har cin yau yakan gagare mu, Allah yayi ma mahafina rasuwa da jimawa, sai mahaifiyata, mahaifiyata ita take fafutukar nema mana abinci da kuma kud'in makaranta, ba irin aikin da batayi ba, haka muka cigaba da rayuwa mahaifiyata itace komai na, sai dai a kwana a tashi na had'u da hatsabiban k'awaye wanda suke hure min kunne har na biye musu na kai kaina a halaka!"
Ta share hawayenta ta cigaba.
"Nazo na fara fita lokacin dana ga dama na dawo lokacin dana ga gama, tun mahaifiyata na fad'an tana duka na har ta gaji ta bini da addu'a, gashi bana jin maganarta, nabi na raina ta ban d'auke ta a bakin komai ba, tasha yi min kuka akan abubuwan da nake mata amma ni ko a jikina, na had'u da samari 'yan k'arya suna min wayau suna kaini hotel su bani kud'i, daga nan idanuna suka ida bud'ewa gaba d'aya, bana ji bana gani, sutura kuwa sai wadda na cire duk akan idon mahaifiyata, har ta kai ta kowa mahaifiyata bata iya fita unguwa, data fita za'a fara nuna ta ana gulmarta.
Kwatsam wata rana sai na had'u da Jidda..."



MSBπŸ’–

Tuesday 12 September 2017

AUREN FANSA 44

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     πŸŒΉMARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

http://MaryamSBello.blogspot.com
     

                🌹44🌹


A bakin gado Zarah tayi arba da ita ta kifa kanta tana kuka kamar wacce aka aiko ma da labarin mutuwa, a hankali ta k'arasa gami da zama gefenta ta d'an dafata sannan ta kira sunanta cikin sigar rarrashi.
"Meenah..."
A hankali ta d'ago da jajayen idanunta tana kallon Zarah a yayinda hawayenta suka cigaba da zuba ba k'akk'autawa, Zarah ta sa hannunta ta share mata hawayen tace
"Haba Meenah, meye haka? Meye abin kuka a nan? So kike sai wani ciwon yaje ya kama ki a banza? Don Allah kiyi shiru ku fahimci juna keda mijinki."
Meenah tayi murmushin da ya fi kuka ciwo tace
"Zarah, a halin yanzu ba zaki gane halin da nake ciki ba saboda bake bace aka yaudara ni ce aka yaudara, ke kina can zaune lafiya da mijinki kina sonsa yana sonki, ni kuwa fa? Ashe wanda nake matuk'ar so kamar raina ashe yaudara ta yakeyi? Mutumin da zan iya sadaukar wa rayuwata domin farin cikinsa, mutumin da nake da burin samun zuri'ah ta gari da shi, mutumin da nake kallo a matsayin masoyina na hak'k'ika ashe shi ba haka yake kallona ba, ya cuce ni! Ya cuci rayuwata, yayi min wasa da feelings ba kad'an ba, wallahi Zarah namiji mugu ne, namiji bashida tabbas! Allah wadaran namiji!"
Zarah tace
"Haba Meenah! Ki saurari kanki ki daidaita tunaninki, yes na yarda Faruk bai kyauta miki ba, kuma baiyi amfani da hanyar da ya dace ya d'auki fansa ba, amma tunda yayi admitting a gabana dake da Baba kinsan yayi namijin k'ok'ari, ina so ki sani ba ko wane mutum bane zai iya haka ba, ya kamata ko nan kiyi respecting decision d'insa, kuma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba ya na matuk'ar sonki a yanzu, kuma ya gane kuskurensa."
Ta mik'e tsaye tana huci
"Sonsa na banza, bana so ya rik'e kayansa, kuma nidai na gama zama da mayaudarin mutum kamar Faruk, bazan koma gidansa ba!"
Zarah ta mik'e tana kallonta galala kafin tace
"Are you kidding me? In ma wasa kike ki daina tun wuri, Meenah kamar yadda na fad'a miki da farko zan kuma maimaitawa, Faruk yana sonki ko ki yarda ko kar ki yarda, koda can baya sonki to yanzu Allah ya d'ora masa. Don haka kiyi tunani."


Baba ne ya aiko kiransu, suka mik'e jiki a sanyaye suka fice, a parlor suka iske Faruk kallo d'aya zakayi masa ka tabbar da hankalinsa a tashe yake, tunda suka shigo ya kafa mata ido ita kuwa ko kallon inda yake batayi ba, suka samu wuri suka zauna k'asa, Baba ya fara magana.
"Da farko dai ina so nayi muku nasiha akan zaman duniya, gaba d'ayanku nan musulmai ne, kuma shi musulmi a duk inda yake ana so ya zamto mai hak'uri da kuma juriya da kuma imani, tabbas Faruk baka kyauta ba a wani 6angaren, amma kuma ina so ke Aminatu kiyi hak'uri na tabbata yanzu Faruku yana sonki bada wasa ba, kuma tunda ya fito fili ya fad'a miki bai kamata kuma ki juya masa baya ba. Don haka ina so kiyi hak'uri ki d'auki k'addara, kuma komai na duniya mai wucewa ne, ki rik'e mijinki kiyi masa biyayya don shine gatanki duniya da lahira."
Meenah tace
"Nagode Baba, amma ni gaskiya bazan koma gidansa ba, ya sauwak'e mini kawai."
Ba Faruk kad'ai ba hartta Baba sai da ya razana da jin kalaman Meenah, Faruk sunkuyar da kansa kawai yayi yana jin tashin hankalin da bai ta6a ji ba.
Baba yana kallon Meenah yace
"Aminatu, kalamanki basuyi min dad'i ba, don banyi zaton kamar ki mai ilimi da aiki da shi zai furtawa mijinki haka ba, amma ina so ki sani saboda gaba duk wani 6acin rai in zaizo miki to kisan irin kalaman da zaki furta. Mijinki dai mijinki ne. Sannan zancen ya sake ki ma bai taso ba, idan ma ya taso sai kiyi tunani wa kuma zaki aura? Maza majoritin mu halinmu a rufe yake, kafin kuma ki gane halin sai kin zauna da mutum.
Aminatu duk rintsi kiyi hak'uri ki zaunawa aurenki, kedai ki cigaba da add'ua, duk wani hargirsi idan ya taso a tsakaninku kok'ari zakiyi wajen ganin kun zauna kun warware matsalarku."
Ya gyara zamansa ya d'an yo gaba daga jinginar da yayi, yayi ajiyar zuciya ya cigaba
"Kin bani kunya Meenah, ban ta6a tsammanin haka daga gareki ba, ni kome Faruk yayi na yafe masa, don haka kiyi k'ok'ari ki yafe masa kema. Ki tashi ki fara shirin komawa d'akinki, Allah yayi maku albarka ya kwa6e muku duk wata fitina."
Ya kai dubansa ga Faruk yace
"Allah ya jik'an iyayenka ya gafarta masu, ga matarka nan sai a kiyaye gaba, ka kula da ita da kuma kanka, kasan dai matsayinta yanzu, don haka ka rik'e ta amana Allah yayi maku albarka."
Yace
"Amin Baba, na gane kuskure na kuma insha Allah hakan bazata sake faruwa ba, nagode sosai insha Allah zan kula da Meenah, zan kuma rik'e ta bisa amana da gaskiya."
Cike da farin ciki Baba yace
"Amin, zan shiga daga ciki na d'an kwanta."
Sukayi sallama ya fice.



Zarah ita da mijinta su sukayi mata rakiya har gidanta da misalin k'arfe biyar da rabi na yamma, suna nan har akayi sallar isha'i bayan sunci abinci suka fara shirin tafiya, Zarah ta k'ara yi mata fad'a sannan ta bita da nasiha, sukayi sallama dasu suka shige gida suma.
Bayan ta shigo ta maida k'ofar ta rufe, yana nan tsaye bakin k'ofa yana faman murmushi, ta kauda fuskarta tace
"Ya dai?"
Yace
"Bacci nakeji my baby, amma inaso na fara yin wanka kuma ke nakeso kiyi min da kanki, kinsan na gaji da yawa rabona da bacci mai dad'i har na manta."
Ta so ce masa bazatayi ba amma tuno da nasihar Baba ya sanya bata musa ba ta bishi da "To."

Ta kunna masa ruwan zafi da taimakonta ya watsa, ta taimaka masa ya shafa cream mai k'amshi shi kuwa duk wani motsinta akan idonsa yake. Ta kammala ta tafi tayi wanka ta fito sanye da kayan baccinta masu kyau da kuma firgita tunani, sai zuba k'amshi take ya cije lips d'insa na k'asa yace
"My baby, kullum k'ara chanza min kikeyi, yanzun ma sai naga kinfi ko yaushe yin kyau."
Duk da taji dad'in kalaman nasa haka bai hanata turbune fuska ba tana cigaba da linke kayansa da ya cire yanzu.
Yayi murmushi ya mik'e ya jawo ta ta fad'o bisa k'irjinsa yana kallonta cike da so da k'auna marar misaltuwa, ita kuwa k'ok'arin k'wace kanta ta shiga yi wanda ta kasa saboda irin rik'on da yayi mata....




MSBπŸ’–

Sunday 10 September 2017

AUREN FANSA 43

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     πŸŒΉMARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L


Dedicated to First Lady 😍

PML You are the best Allah ya bar mu tareπŸ‘ŒπŸΌπŸ˜‰πŸ˜Œ

     
                🌹43🌹

Cikin wani irin yanayi yace "What?"
Bilki kuwa k'ara d'aga murya takeyi tana fad'in
"Ke Amina ba mu muka haife ki ba."
Laila tana ta d'an zunguranta akan ta bari ina bata ma saurareta ba. Baba ya sunkuyar da kansa yana mai tsananin jin haushin Bilki, ko kusa bai so Meenah tasan matsayin ta ba, a ganinsa hakan zai iya haifar mata da damuwa sosai, da yawan tunani, duk da yasan sanin matsayintan ba wani abin bane don kuwa cikakiyyar 'yar sunnah ce, hakan yasa ya tattaro nutsuwarsa yana kallon Meenah data tsareshi da ido kamar yau ta fara ganinshi, yace
"Kar ki damu zan sanar da ke komai, Faruk kammala aikinka sai mu tattauna."
Da k'yar Faruk ya tattara nutsuwarsa amma gaba d'aya hankalinsa naga Meenah da kuma son jin in da gaske ne zancen Bilki.
Police guda biyu ke tsaye a waje Faruk ya kirasu suka shigo, da hannu kawai ya basu order wanda su kad'ai suka san me yake nufi, sara masa sukayi sukace
"Yes sir..."
Fita sukayi ba'a jima ba sai gasu sun dawo da matasan maza majiya k'arfi su kusan biyar masu k'iran 'yan daba, ko su Zarah sai da suka tsorata da ganinsu, sai wani huran hanci sukeyi suna zare idanun kamar kura taga nama. Take jikin Laila ya fara 6ari don kaf d'insu ta ganesu, haka zalika ita kanta Bilki sai ta fara salati tana bada hak'uri da neman gafara.
Faruk yace
"Wad'annan sune wad'anda kukayi assigning suka aikata kisan da hannunsu, suka kashe min iyayena..."
Take tsikar jikinsa ta tashi idanunsa suka kawo ruwa, ya kai dubansa ga Anisah yaga tana kuka itama, duk sai ta basa tausayi a ransa yace
"Ke kenan da bakida wayau a lokacin bare kuma ni."
Bilki tace
"Ni dai bansansu ba. Billahi bansan ko su waye ba."
Baba ya daka mata tsawa
"Yi mana shiru a nan! Ko so kike sai na sa an harbe ki ne da bindiga? Ga laifi an kamaki dumu dumu amma kina k'aryatawa?"
D'aya daga cikin 'yan daban suka ce
"Tabbas nine wanda Hajiya Laila ta kira take sanar dani irin aikin da za'ayi musu, sannan sukayi min alk'awarin mak'udan kud'i idan na aikata abinda suka sani, ita kuma Hajiya Bilki ita bani umarnin kisan tace idan ban aikata ba to tabbas ni zatasa a kasheni, haka sukayi min ko wanensu zai bani dubu d'ari biyar biyar idan aikin ya kammala. Don haka na samu abokanan aikina na sanar musu yadda zamuyi aikin. Ko bayan faruwan haka sai da suka mallaka min gida da mota wai a cewarsu farin cikin abinda nayi musu ne."
'Yan sandan suka matso kusa da su Hajiya Laila sukace
"You're under arrest for the murder of Hajiya Reemah and Alhaji Adam, you have the right to remain silent, because anything you said will be used against you in a court of law."
"Don Allah ka gafarce ni, ku yafe min abinda nayi."
Ta matso kusa da Meenah tace
"Ki yafe min irin cin zalin da nayi miki a baya, nasan kin sha wahala a wurina ki yafe min."
Baba yace
"Kamar yaya?"
Zarah ta matso tana share hawaye tace
 "Baba, tunda na taso nake ganin yadda Meenah ke fuskantar wulak'anci, mugunta da kuma zalunci a wurin Mami, bugun yau daban na gobe daban, ga sata aiki kamar jaka, abinci kuwa data gama wannan sai a sata wani, wanke wanke, wanki, wankin toilets, shara, goge goge, duk Meenah ce keyi. Sannan bata cin abinci sai ka kusa dawowa, haka zata wuni da yunwa ga uban aiki, da ka kusa dawowa zata korata tayi wanka taci abinci yadda bazaka gane ba. Ko nayi yunk'ura fad'a maka sai Mami ta hana, ko tace zata zane ni muddin na sanar da kai..."
Baba yace
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Bilki ashe yadda na d'auke ki ke ba haka kika d'auke ni ba? Tun farko dana san haka kike da ban d'auki amanar maraininiyar Allah na baki ba, amma kisani akwai ranar hisabi kuma Allah sai ya mata sakayya..."
"Na tuba Alhaji, ka yafe min..."
"Bilki kije na sake ki saki d'aya..."
Kowa sai da ya zabura jin sakin da Baba ya yiwa Bilki, sannan ya bita da nasiha da fatan zata gane kuskurenta, haka aka saka musu ankwa itada Laila aka jasu suna tirjewa da maganganu suka fice.
Faruk gaba d'aya jikinsa yayi sanyin abinda yaji, wai Meenah marainiya ce?
"Me nayi? Na d'auki alhakin baiwar Allah." Ya fad'i a cikin ransa.
Duk da daurewarsa sai da k'walla suka zubo masa, ya share sannan ya bi bayansu Bilki inda Anisah ma tabi bayansa, suka bar gidan. Suna fita Meenah ta kifa kanta a hannun kujera tayi ta kuka kamar ranta zai fita, Zarah na ta aikin rarrashinta inda itama kukan takeyi, Baba yaja su suka shiga cikin d'aki yana ta faman rarrashinsu.


*****

Daddare kowa ya nutsu a parlor amma daka kalli kowa kasan ba a cikin nutsuwa suke ba.
Baba ya maida dubansa ga Meenah yace
"Dalilin da yasa ban ta6a fad'a miki ba shine, na farko baniso kiyi kukan maraici, na biyu baniso ki shiga damuwar rashin iyaye, don kinsan yawan damuwa ga yaro ba abu bane mai kyau, amma ina mai baki hak'urin 6oye miki da nayi duk da nasan you have the right kisani."
Nan ya kwashe labarin komai ya fad'a mata, su waye iyayenta da kuma yadda akayi ta dawo hannunsu da zama. Sannan ya d'ora da cewa
"Duk da nasan banyi niyyar fad'a miki ba amma wallahi ji nake kamar an sauke min wani nauyi da ke bisa kaina,  Meenah bana fad'a miki maganar nan ba don ki shiga damuwa ba, a'a na fad'a miki ne bisa tirsasawa da akayi min, sai dai ina rok'onki da kada ki d'ora damuwa a ranki don Allah, sannan ki cigaba da yiwa iyayenka addu'ar samu rahama daga Allah, inda suka tafi muma zamu iske su wata rana."
Ya fad'a da guntun k'walla a idanunsa. Meenah ta share hawayenta tace
"Wallahi Baba ban ta6a sanin cewar bakai ka haifeni ba saboda babu alama, duk wani gata ka min shi, sai dai nace Allah ya saka da alkhairi, amma kasani har yanzu bazan daina ganinka a matsayin mahaifina ba saboda kaima mahaifina ne saboda yaya kake ga mahaifiyata don haka duk d'aya ne, kuma insha Allah na maka alk'awarin cire damuwa a raina."
Yace
"Alhamdulillah, ke kuma Fatima kema kar ki shiga damuwar ganin mahafiyarki da aka kama, ki cigaba da yi mata addu'a."
Tace
"Insha Allah Baba."
Faruk da ke zaune jikinsa sanyi k'alau yace
"Baba inada magana idan an bani dama."
Baba yace
"Bismillah mana."
Faruk ya sunkuyar da kansa saboda nauyin maganar amma kuma dole ne ya fad'i, don ya samu su yafe masa.
Yace
"Baba, ka gafarce ni, nayi kuskure babba."
Sai kuma yayi shiru, Baba yace
"Kuskure kuma Faruku? Na me?"
Ya kalli Meenah yaga shi d'in take kallo, sannan ya maida kansa k'asa yana wasa da zoben azurfar da ke hannunsa yace
"Wallahi Baba da zan auri Meenah ba sonta nakeyi ba... daman don na d'auki fansar abinda akayi wa iyayena ne sheyasa na aureta..."
Ras! Ras! Gaban Meenah ya yanke ya fad'i,  ya d'ago ya kalleta yaga idanunta sun kad'a sunyi jawur! Tana masa kallon mamaki had'e da tsana...
"Meenah nasan nayi kuskure a nan amma wallahi..."
Da gudu tayi ciki tana kuka mai sauti...!
Zarah ta bi bayanta da gudun itama tana k'wala mata kira...




MSBπŸ’–

Friday 8 September 2017

AUREN FANSA 42

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     πŸŒΉMARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

Ina yi ma d'aukacin musulmai barka da sallah, da fatan munyi sallah lafiya? Allah ubangiji ya maimaita mana Amin thumma Amin! ❤️

Wannan page d'in nakune Faty Ladan, Hauwee Bash, Asma'u Ammani, Hafsat Kabeer, Farida Bature, Feedn, Machika, and Aisha Basheer dama sauran wad'anda ban ambata ba, nagode da k'aunar book d'innan da kukeyi.😘

Fatan alkhairi ga Auren Fansa Fans😍Allah ya bar zumunci.❤️

       
                🌹42 🌹

Cikin girmamawa Faruk ya isa inda Baba ke tsaye ya gaishe shi ya amsa masa yace
"Meyake faruwa ne haka a nan?"
Faruk yayi murmushi yace 
"Yanzu zaka fahimci komai Baba."
Faruk ya koma inda Hajir ke tsaye yace
"Hajir ina so ki bani wayar nan dana baki zan duba wani abu."
Hand bag d'inta ta bud'e ta fiddo ta mik'a masa, ya maida dubansa ga Bilki yace 
"Ina so ki nutsu ki kalla."
Tace
"Bangane abinda ke faruwa a nan ba, don Allah ayi mana bayani mana."
Faruk yace
"Abinda nake k'ok'arin yi kenan ay."
Wayarsa ya zaro daga aljihu ya kira bugu d'aya aka d'auka yace
"Usman bud'e motata ka d'auko min system d'ina tana nan daga bayan seat, sai wasu wayoyi amma ba'a jiki suke ba suna nan a gefe sai ka d'auko mun su duka."
Bansan me Usman yace ba naji dai Faruk yace
"A'a motar a bud'e na barta kawai ka bud'e, yanzu yanzu muna jira don Allah."
Baba yace
"Wai lafiya haka Faruk? Har yanzu ban fahimci inda ka sa gaba ba."
Faruk yace yana k'ok'arin maida wayarsa aljihu
"Yanzu zaka fahimta Baba."
Bilki kuwa kamar ruwa ya cita haka kurum gabanta ya tsananta bugu, don har wata kyarma take duk da batsan abinda ke faruwa ba.
Usman ne yayi sallama hannunsa d'auke da laptop da wayoyi, Faruk ya kar6a inda ya aje ta a saman center table d'in dake ajiye a parlor d'in, yayi ta had'e had'ensa ya jona nan ya had'a can, cikin minti kad'an wani video ya bayyana a saman screen d'in laptop nasa. Ya juya ta setin da kowa ke tsaye ya danna play.
Hoton farko video Bilki inda take waya da Laila a gameda makircin da suka had'a, maganar yadda take kwasar dukiya da shawarwarin da Laila ke bata akan yadda zata dage wajen cigaba da juya dukiyar.
Next scene kuwa hoton Laila ne da Bilki suna zaune cikin d'aki suna maganar yadda suka kashe Hajiya Reema da Alhaji Adam, take Bilki ta fara zufa itada Laila, wannan abu ya basu mamaki ya akayi aka d'aukesu hoto haka? 
"Waye ya d'auki wannan videon?" Ta fad'a jikinta na kyarma, Baba kuwa kallonta kawai yana salati, inda Zarah da Meenah ke tsaye suna kuka suna mamaki.
Scene na gaba kuwa yana d'auke da video d'in Laila da Bilki inda Laila ke narrating yadda akayi kisan da kuma shawarar su cigaba da 6oye sirrinnan, har Bilki ke nuna mata tsoronta kar wata rana asirinsu ya tonu. Laila tana nuna mata asirinsu a rufe yake babu mai ji.
"Wallahi bani na kashe su ba, wallahi Laila ce ta kawo wannan shawarar."
Bilki ta fad'a tana kyarma, Laila tace
"Dana baki shawarar wa yace ki d'auka don haka kina da laifi kema."
Bilki tace
"Nidai wallahi kin cuce ni Allah ya isa wallahi."
Laila ta buga tsoki tace
"Aikin banza, yo Allah ya isarki me zatayi min?"
Faruk ya cigaba da displaying duk wani abu da aka d'auka na Bilki da Laila, tare da voice notes, Baba da zufa ta jik'e shi jagab, ya kalli Meenah da Zarah yaga yadda suke kuka, sannan ya juya ga Bilki da take borin kunya suna chachar baki itada Laila suna ta k'ara bankad'e asirinsu da kansu.
"Tun farko ina zaman zamana kika kawo wannan shawarar kika ce mu kashe su..."
"Dana kawo shawarar nace dole kibi ne? Kema a lokacin kina jin haushin Alhaji Adam, akan ya samu kujarar da kikeso mijinki ya mallaka ko nayi k'arya?"
Bilki tace
"K'arya kike munafuka algunguma, abin naki harda sharri kuma? To wallahi..."
Maganarta ta katse ne sakamakon wani zafafan mari da Baba ya d'auke ta dashi, har sai data ga gilmawan wuta sannan ta nemi ji da ganinta ta rasa na wuchin gadin.
Dafe kuncinka tayi cike da azaba kafin kuma ta ankara ya k'ara d'auke ta da wani wanda yafi na farko zafi, kyarma ta fara yi inda hawaye ke ambaliya a saman fuskarta, ya d'aga hannu zai k'ara wanke ta da wani marin cikin azama Meenah ta rik'e masa hannu gam gam tana kuka, tace
"Kar ka k'ara mata wani Baba, ka rabu da ita don Allah."
Baba ya fara k'ok'arin k'wace hannunsa yana nuna Bilki yace
"Ashe ke mutuniyar banza ce bansani ba? Shashasha marar mutunci! Ashe ke muguwa ce? Makira! Anya kinada imani kuwa? Kin bani mamaki ban ta6a zaton haka daga gareki ba..."
Sai ta fara borin kunya tana fad'in
"Yo har abin kunya ya wuce daga gareka? Kai fa kana zaune da mutum ka kasa gaya mata iyayenta na asali tsabar rufa rufa!"
Baba yace
"Ki min shiru a nan, anya kina da hankali kuwa?"
Tace
"Ras nake, yo tunda aka tona min asiri na wa zan iya rufewa kuma? Ai wallahi sai na fasa k'wan! Ke Amina! Kalleni nan Alhaji bashi ya haife ki ba! Haka nima ba nice na haife ki ba! Kije ki tambaye shi inda iyayenki suke."
Gaban Meenah yayi mummunar fad'uwa, dafe k'irjinta tayi a yayinda hawaye suke kwarara a fuskarta, Baba take kallo tace
"Ni 'yar tsintuwa ce ko?"
Faruk kuwa tsaye yayi cike da mamaki a yayinda k'walwarsa ta tsaya cak da aiki....



MSBπŸ’–

Tuesday 29 August 2017

AUREN FANSA 41

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     πŸŒΉMARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

     
                🌹41 🌹

   
http://MaryamSBello.blogspot.com


A hankali ta bud'e idonta juyi d'aya tayi ta hango shi bakin wardrobe da alama wanka ya fito yana shirin fita, duba agogo tayi k'arfe 8:30am, zumbur ta mik'e tana mamakin abinda ya haddasa masa makara yau, zaune ta mik'e tana kallonsa yana k'ok'arin d'aura agogo a hannunsa, ta sauko daga gadon ta kamo hannunsa tana cigaba da sa masa.
"Yau ka makara my soul."
Jin yayi shiru ya sanya ta d'ago tana dubansa da mamaki, damuwa ta gani k'arara bayyane a fuskarsa wanda idanuwansa ma sun nuna hakan.
"Meyake damunka my soul?"
Yace
"Babu komai, kije kiyi wanka yau tare zamu fita, sannan ki sanar da Zarah ta tamabayi mijinta ya bata izini zamu fita tare da ita."
Tayi shiru tana tunani can kuma tace
"Lafiya?"
Yace
"Koma me kenan zaki gani nan da lokaci kad'an, kedai kawai ki kirata ki sanar da ita."
Tace "To." Sannan ta wuce tana tunanin dalilinsa nace mata haka.

Tayi wanka ta sanya bak'ar after dress, tea kawai suka sha inda a waje sukayi kaci6us da Zarah inda take shaida musu da mijinta zasu tafi yace zai kaita, haka ma Anisah tazo a daidai sadda zasu shiga mota, itama ta shaida musu mijinta zai kaita, nan kuma kowa ya fara shirin tafiya.
A mota babu wanda yayi magana ko wane da tunanin da yakeyi, ta kai dubanta ga Faruk da alama ya zurfafa cikin tunanin, ta ta6o sa tace
"My soul wai meke faruwa haka ne? Sannan duk ina zamuje da su Anisah?"
Ya karkato kad'an ya kalle ta sannan ya maida kansa ga titi yace
"Ki gafarce ni my baby."
Tace
"Akan me fa?"
Yace
"Kawai ki yafe min akan abinda zai faru yau."
Cikin rashin fahimta tace
"Me zai faru yau?"
Bai kai ga bata amsa ba wayarsa tayi ringing, ya d'auka yace
"Hello Usman."
Usman yace
"Muna hanya ka turo mana address d'in."
Yace
"Muma muna hanya, zan turo maka sai mun had'u d'in."
Ya kashe kiran ya tura masa address d'in.
Meenah da zuciyarta fal damuwa tace
"Kaji my soul, wai meke faruwa?"
Yace
"Kiyi hak'uri zaki ga koma menene."
Ganin ya d'auki hanyar unguwarsu ya sanya tace
"Daman gida zamu shine kak'i sanar dani?"
Ya d'anyi murmushin k'arfin hali a zuciyarsa yace
"Nasan yau zanyi breaking heart d'inki my baby, amma abinda zanyi ya zama dole in ba haka ba hankali na bazai ta6a kwanciya ba."
Ya kalle ta yaga ta zurfafa cikin tuanani, yayi ajiyar zuciya a lokacin da ya karya kwanar layinsu Meenah.
Ganin motoci a k'ofar gidansu ya sanya ta d'an razana kad'an gami da zaro idanu waje, ya kalleta ya kawar da fuskarsa gefe, yasan kota masa tambaya baisan abinda zai ce mata ba.
Yayi parking ya fito daga mota, yana d'an kalle kalle, ganin ba motar Usman ya sanya yasan bai iso ba, amma motoci hud'u sun iso na abokanan aikinsa, su Zarah duk sun iso inda take ta tambayar abinda ke faruwa. Amsa d'aya take samu wato,
"Nima bansani ba."
Su Najeeb ne kad'ai suka san abinda ke faruwa saboda ya sanar musu daman.
Ya d'auki waya ya kira Hajir ya sanar mata yana k'ofar gida. Tace she's ready tun d'azu. Nan suka cigaba da tsara plan d'in nasu.
Ita dai Meenah bata k'ara magana ba illa dai gabanta da ya tsananta bugu.

A 6angaren Bilki kuwa tunda ta tashi da safe k'awarta ta iso akan yau zasu walimar bikin d'iyar wani sanata da za'ayi a cikin garin Abuja, Baba kuwa yana d'akinsa yana wanka zai fita, shiryawa tayi cikin wani dank'areren leshi mai matuk'ar tsada sai k'yalli takeyi, wayoyin da ke hannunta sun kai kala uku kuma manyan wayoyi masu tsadar gaske, ta fito parlor sai zuba k'amshi take kamar shagon saida turare, kaci6us tayi da Hajir sanye cikin bak'ar after dress tayi tsaye a bakin k'ofa idanunta manne cikin bak'in glass wato no respect.
Suka ja suka tsaya Bilki ta kalle ta daga sama har k'asa tace
"Ke Atika meye haka? Ina aikin dana saki zaki zo kiyi wa mutane tsaye a ka haka! Matsalar d'an k'auye kenan ka wayar da shi sai daga baya ya nuna yafika wayewa. Mts."
Laila tace
"Gaskiya kam da alama don wannan yarinyar 'yar rainin hankali ce, ke Malama ki bamu wuri zamu wuce."
Hajir ta kalle su da chewing-gum a bakinta sai hannunta dake hard'e tace
"Wacece Atika don Allah?"
Bilki tace
"Ahh! Kiji min neman magana fa, yo wacece Atika 'yar aiki in ba ke ba? Kaji min yarinya zata nemi ta maida ni k'aramar yarinya."
Laila tace
"Gaskiya wannan ta samu wuri da yawa. Da nice ke da tuni na sallame ta don bazan iya ba, zan iya farfasa mata jiki."
Bilki tace
"Eh gaskiya ne, ke Atika! Ki wuce kije ki d'ora girkin rana kafin mu dawo."
Hajir ta kallesu a wulak'ance tace
"I'm sorry to say Hajiya, amma bazanyi ba, sai dai idan kece zaki je ki d'ora."
Suka fara salallami suna tafa hannu, Laila tace
"Wai bazaki gaura mata mari ba, ni wallahi sheyasa kikaga bani d'aukar 'yan aiki saboda bansan wadda zan kwaso ba, ya za'ayi ki zauna kina fad'a tana fad'a? Ki d'auki mummunan mataki akanta mana."
Bilki tace
"Lallai kin k'oshi da sadda aka kawo ki kamar zakiyi min sujjuda amma yanzu kin k'oshi kin mik'e k'afa ko? Lallai sannu Atika, to wallahi kizo ki kwashi kayanta ki bar min gida munafuka kawai."
Hajir tayi murmushin mugunta tace
"Daman yau zan bar miki gida Hajiya kar ki damu."
Bilki tayi tsaye ta rasa ma me zatace sai tafa hannu kawai takeyi.

Minti goma tsakani Faruk ya doka sallama, Bilki ta washe baki tace
"Ah kinga surukinmu ne yazo, sannu da zuwa Faruk."
Ya shigo yana k'are ma gidan kallo, yana d'aga kwalar rigarsa yace
"Ki gyara kalamanki Hajiya ba Faruk zakice ba, Inspector Faruk Adam Ishaq zaki ce."
Suka kalli juna itada Laila, Laila ta rad'a ma Bilki a kunne
"Adam Ishaq fa yace, me hakan ke nufi kenan?"
Hajir tayi murmushi ta cire after dress d'inta     ta dawo kusa da Faruk tace
"Sunana Inspector Hajir ba Atika ba."
Bilki tace
"Ke kamar ya keba Atika bace, to wacece ke?"
Meenah da Zarah da Anisah suka shigo ganin Ikon Allah a daidai nan Baba ya sauko yana gyara hular kansa ganin mutane da hayaniya ya sanya yaja tsaya yana tambayar lafiya?



MSBπŸ’–

Sunday 27 August 2017

AUREN FANSA 40

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     πŸŒΉMARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

     
                🌹40🌹
   
http://MaryamSBello.blogspot.com


Ya shigo gidan a lokacin da ya tarar da Meenah a bakin k'ofa, tana sanye da brown and cream atamfa d'inkin riga skirt, tayi kyau sosai, da sauri ta taro sa ya k'ura mata idanu yace
"My baby ya akayi ne?"
Yaushe rabon da taji sunan nan a bakinsa har ma ta manta, tayi murmushi tace
"Jidda ce tun d'azu banganta ba, ko da saninka ta fita?"
Ya kwashe labarin komai ya fad'a mata, tace
"Ikon Allah kenan, amma Jidda bata yi wa kanta adalci ba, amma sai inga duk bai kai na saki ba my soul."
Ya kamo ta suka dawo parlor suka zauna yana kallonta sosai yace
"Rabuwa da Jidda shine mafi alkhairi a garemu my baby, saboda a gaskiya bazan iya cigaba da zama da ita a matsayin matata ba, besides ba'a son raina na aure ta ba."
Ta dube shi cike da mamaki tace
"Bangane ba my soul."
Yace
"Wato akwai wata rana na fito zan tafi aiki sai naji Jidda na magana da mahaifiyarta tana ce mata ita ba wanda takeso sai ni, a nan naji Mama na ta rarrashinta akan tayi hak'uri tunda ni ba sonta nakeyi ba, tun daga wannan lokacin sai na karaya nake ganin kamar ban kyauta ba, abin yana ta damuna sosai, a ganina abinda kawai zanyi na faranta ransu shine na bijiro da maganar auren Jidda, a tunanina sun mani komai a rayuwa bai kamata d'iyarsu tana sona nak'i ta ba."
Meenah ta kamo hannunsa tana murmushi tace
"A gaskiya kayi tunani mai kyau kuma ka kyauta, sai dai daman tun farko kayi min bayani da sai nafi fahimtarka my soul."
Yace
"Naso yin hakan my baby, amma a lokacin sai na rasa dalilin da yasa na kasa fad'a miki gaskiya, kuma wallahi bansan yadda akayi ba sai dai naji ance wai matata ce, abin zai baki mamaki is like bansan abinda nakeyi ba, kuma a lokacin Jidda tayi amfani da magani wajen jawo hankalina gareta, nidai kawai idan ta warke zan sallame ta, taje can ta nemi wani daidai da ita."
Tace
"Bazan iya saka yin abinda baka so ba, duk abinda kaga yafi dacewa kayi ni kuma zan baka goyon baya d'ari bisa d'ari my soul."
Ya kamota ya rungume a k'irjinsa gami da lumshe idanu yace
"Sheyasa nake sonki my baby."
Tace
"Nima haka, yanzu muje kayi wanka kaci abinci ko, na dafa maka abinda kafi so."
Cike da jin dad'i yace
"Allah my baby?"
Tace
"Wallahi kuwa."
Yace
"Shikenan muje, don yau ma kece zakiyi min wanka da kanki."
Ta tashi tana fari da ido tace
"Muje."
Ta wuce yabi bayanta.



****


Yana zaune a office d'insa aiki yasha gabansa wayarsa ta fara ringing, ganin Hajir ya sanya ya dakata ya d'auka.
"Hello Hajir."
Tace
"Hello Sir ina wuni?"
Yace
"Lafiya lau, ya dai?"
Tace
"Aikinka na kammala komai Sir, yanzu ya za'ayi?"
Cike da jin dad'i yace
"Da gaske kin had'a komai da komai?"
Tace
"Yes Sir komai ya kammala."
Yace
"Wow Weldon Hajir, a gaskiya nayi matuk'ar farin cikin jin haka, yanzu abinda za'ayi, ki shirya zuwa gobe zan shigo gidan, dana kiraki sai ki fita daga shigar Atika ki koma Inspector Hajir d'inki. Sauran bayanin zan kiraki. Yanzu wani d'an bincike nakeyi akan wad'anda suka turo domin kashe iyayena, nama kammala don har na tura a kamo yaran, don muna buk'atarsu."
Tace
"Yayi haka sir, sai Allah ya kaimu goben."
Yace
"Amin, thank you."
Daga haka sukayi sallama, Faruk yayi murmushin jin dad'i sosai.


****

Kiran farko na sallar asuba a kunnensa akayi, domin ba bacci yake ba, saboda tsabar farin cikin kalar matar da Allah ya bashi, shi kwata kwata bai k'ara tabbatarwa ba sai yau, tambayar kansa yakeyi anya kuwa akwai wanda ya kai shi sa'a?
Ya lalubi bed side lamp sannan ya dube ta tana bacci, numfashinta yana fita a natse.
Kyakkyawar fuskarta nata annuri, yayi ta kallonta baya ko kyaftawa har sai da idanunsa suka kawo ruwa sannan ya dawo hankalinsa, ya sunkuyo a hankali ya manna mata light kiss a goshinta, ya numfasa, Allah kad'ai yasan tarin son da yake mata. Da k'yar ya lalla6a ya sauka daga gadon ya shiga toilet yayi wanka ya fito da alwalarsa, ya shimfid'a sallaya yayi nafilfili har alfijir ya fito, sannan ya nufi masallaci.


Yanda ya barta haka ya dawo ya same ta, yayi tsaye a gaban gadon rungume da hannayensa yana kallonta.
"Wai lallai baby an gaji."
Ya zauna gefenta ya tallabo kanta sannan yace
"Meenah... Meenah..."
Ta bud'e ido a hankali tabi shi da kallo har idon ya washe gaba d'aya. Yace
"Ki tashi kiyi sallah, ko gajiyar ce ta hana ki tashi?"
Ta runtse ido tana k'ok'arin tashi, yayi murmushi kawai ya d'aga ta cak sai toilet, ya tarba ruwa masu d'umi ya saka ta ciki, ita kuwa idonta har yanzu a lumshe yake, yana tsaye yace
"Haba ragguwa sai kace first time dai."
Tayi murmushi kurum, daga haka ya fita ya bata wuri don ta kimtsa.
Tsawon minti 20 tafito, ya matso yana dariya.
"Ragguwa kawai ni tuni naje masallaci na dawo."
Ta wuce shi tayi shirin sallarta tana jin wani irin nishad'i marar misaltuwa. Kwanciyarsa yayi, ta gama sallarta tayi adduo'inta gami da mik'a godiyarta ga Allah da ya karkato mata da hankalin mijinta gareta tana fatan su dauwwama haka har k'arshen rayuwarsu. Sai kuma ta tuna Jidda ko a wane hali take yanzu? Ta dad'e tana mata addu'ar samu sauk'i, tana gamawa sai kawai ta maida kanta bisa sallayar tana lazumi. Ya d'ago yana dubanta yace
"Ya zaki kwanta a nan?"
Tace
"Haka nan."
Yace
"To kodai?"
Ta k'udundune fuskarta da hijabi ta k'yale shi, cicci6o kanta yayi ya d'ora bisa jikinsa yace
"Tashi mu koma kan gado."
Tayi shiru tana kallon kyakkyawar fuskarsa, yace
"Allah yayi miki albarka my baby."
Taji dad'i sosai ta amsa da
"Amin my soul."
Ya cigaba da fad'a mata dad'd'an kalamai masu rikita lissafi, ganin haka yasa na tashi na baro d'akin, sai dai fatan Allah ya kawo k'azantar d'aki.



MSBπŸ’–

Saturday 26 August 2017

AUREN FANSA 39

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     πŸŒΉMARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

     
                🌹39 🌹
   
http://MaryamSBello.blogspot.com

Meenah ta dube shi tace
"My soul bai isheka ba abincin ko?"
Ya gyad'a mata kai, ta mik'o masa hannu ya sa nasa cikin nata tace
"Zo muje na had'a maka wanda yafi wannan, babu mamaki k'ila tana son cin wannan ne."
Baiyi gardama ba yabi bayanta suka nufi sashenta, tana tsaye da plate a hannunta suka fice, galala take kallonsu har suka fice, babu shakka Meenah ta yi gaba a halin yanzu ta barta baya, dole ne ma ta d'auki mataki akan haka. Ta fito daga sashen cin abinci (dinning) ta nufi sashenta.
Zaune take abin duniya ya ishe ta, ta sak'a wannan ta warware, daga k'arshe ta mik'e ta fito daga d'akin tana cizon hannu. Shiru babu motsin kowa, da alama suna cikin d'akin Faruk, haushi ya turnik'e ta kamar zata fashe.



***


Dawowarsa kenan daga gidan, rashin ganin Meenah bata tarosa ba ya tabbatar tana makaranta don tace masa yau zatayi test har biyu.
Yana shigowa yaci karo da Jidda daga bakin k'ofa sai faman washe baki takeyi.
"Sannu." Tace dashi tana taunar chewing-gum, yayi tsaki yace
"Yauwa." Ya sa kai zuwa d'akinsa yana Allah wadaran da mace marar tarbiyya.
Yana zaune bakin gado yana cire safarsa ta shigo  sai wani cika take tana batsewa. Zama tayi gefensa tace
"Ya Faruk magana nazo muyi."
Yace
"Yanzu Jidda daga dawowata sai ki tare ni da wata magana kuma, ay kya bari in huta dai ko."
Tace
"Nidai ka bari na fad'a maka."
Ya dakata yace
"Ina jinki."
Tace
"Ay dai kace kai baka tauye hakkin iyalanka ko?"
Yace
"Haka ne."
Tace
"Yauwa, to tunda baka tauye hakkin iyalanka so nake ka barni na tafi Dubai, na karanta Fashion and Design."
Ya karkato yana dubanta yace
"Da igiyar wa?"
Tace
"Da igayarka mana."
Yace
"Kinga Malama banson zancen banza, ta yaya kina matar aure kawai don rashin hankali sai ki tafi wata uwa duniya da sunan karatu, ke bari ma kiji ni ba irin mazan nan bane da mata ke juya su yadda suka ga dama ba, don haka wallahi sai na sa6a maki kika k'ara yi min zance makamancin wannan."
Cike da shagwa6e tace
"Haba don Allah ya Faruk, wai ni meyasa kake min haka ne? Saboda Allah ita Meenah ay ka barta tana karatu sai ni zaka hana ni."
Yace
"Ita Meenah ba kina ganin cikin garinnan take ba? Yau ga zancen banza zancen wofi, ke nafa gaji da rigimarki haba! Mutum kullum da abinda zaice daga wannan sai wannan to wallahi na gaji."
Kawai ya tashi ya bar mata d'akin.
Ita kuwa sai tasa kuka tana ta magana ita kad'ai.


****

Ranar wata Juma'a Luby tazo gidan, nan suka baje suna fira. Jidda ta dubi Luby tace
"Luby gaskiyar magana nayi dana sanin wannan aure, banida tantama alhakin Meenah ne ke bibiyata, ke tunda nazo gidannan ban ta6a tsintar farin ciki ba daidai da rana d'aya ba, nikam na gaji wallahi auren ma ya fita raina, mutumin nan sai shegen kulle baya bani abinda nakeso, ga abin takaici wai Meenah yanzu tayi min in mata batada tsoro ko kad'an, ke wallahi aurennan na gama shi sai ya sake ni."
Zumbur Luby ta mik'e tana salati tace
"Yanzu Jidda abubuwa nata faruwa shine bansani ba? Baki iya fad'a min? Sai da abubuwa suka jagule miki suka fi k'arfinki shine zaki sanar da ni yanzu ko?"
Jidda tace
"Kiyi hak'uri Luby wallahi na d'auka zan shawo kan abin ne."
Luby tace
"Aiko sai mun d'auki fansar abinda tayi miki, bata isa ba, wacece ita? Ke kin bani kunya kinfa girme ta, amma kin zauna tana juya ki."
Jidda tace
"A'a Luby ke kinsani sarai mu da magani mukayi aiki, ita fa? Ay ba d'aya bane ba ma."
Luby tace
"Shikenan, amma kar kiyi saurin karaya, aure kuma yanzu kika soma shi, yo mekenan idan kika tafi tun yanzu, ay ko baki warci wani abu ba ni kya wabto mani, kuma ke ina son da kike masa? Ko dama k'aryar banza ce?"
Jidda tace
"Luby don bakisan irin wahalar da nake sha ba, babu fa yadda muka iya saboda matarsa tayi mana zarra."
Luby tace
"Wallahi k'arya takeyi! Kedai ba kina amfani da kwallin da turaren ba?"
Jidda tace
"Wallahi ina yi, kedai Luby munzo inda aka kere mu."
Luby tace
"Yanzu akwai wani abu a wurinki?"
Jidda ta girgiza kai
"Babu komai sai tarin wahala da takaici."
Luby tace
"To zan san matakin da zan d'auka, zan dawo anjima ko gobe."


Washe gari da sassafe ta dawo, ta d'auki Jidda amma sai da suka shirga ma Faruk k'arya sannan ya barsu da k'yar, shima akan kar su dad'e.
Suna tafe a mota Luby tace
"Kar ki damu k'awata, zan kai ki inda za'a share miki hawaye."
Jidda tace
"Ina kenan?"
Luby tace
"Me kike ci na baka na zuba, kedai ki tsaya ki gani."

Luby ta koro ma Barmuje bayani, yayi 'yan tsubbace tsubbacensa zuwa can yace da Luby
"An 6ata aiki ay, saboda tun farko sai dana fad'a miki kar ya wuce daren farko baiyi tarayya da ita ba, amma ina bakuji ba, sannan kuma sai da ya fara yin tarayya da uwar gidanki akanki, don haka aikinki bazai ta6a yin tasiri ba! A yanzu komai ya wargaje saboda uwar gidanki tana da rik'o da addini sosai, a gaskiya kafin wani abu ya kamata da wuya. Ina tunanin kawar da ita ne kawai zai baki damar mallakar mijinki don haka sai kisan abinyi."
Suka kalli juna itada Luby tace
"To yanzu meye abinyi?"
Barmuje yace
"Akwai maganin da zan baki, zaki zuba mata a wani abun sha, kamar koko, fura da sauransu, wannan abin da kike gani guba ce data sha ita da duniyar nan sai dai a lahira."
Luby tace
"Akwai wata hoda da ka bani jiya, inaga kamar zata fi yi mata amfani."
Yace
"Tabbas! Zaifi sauk'i sai dai zan k'ara gargad'inki da kada ki kuskura ki shak'i hodar nan don idan kika shak'a.... hahaha to kema zaki bak'unci lahira, idan kuma baki mutu ba... haha! To zaki wahala a nan duniyar sai kin zamo abin tausayi."
Luby tace
"Zata kiyaye ma."
Da haka suka baro dajin da Barmuje yake, suka dawo gida.
Luby tace
"Yanzu dai ga maganin nan, kuma kinji gargad'in Barmuje wallahi kibi a sannu."
Jidda tace
"Haba kar ki damu komai zai tafi yadda akeso."
Luby tace
"In ta mutu ki sanar dani, zan had'a mana grand party."
Jidda tace
"Ay dole ne ma wannan."
Suka k'yalk'yale da dariya gami da tafawa.
Daga haka sukayi bankwana Luby tayi gida cike da murna.


****

Meenah na kwance a d'aki tana baccin rana inda Jidda ta lalla6o da hodar a hannunta, Jidda ta huro mata hodar tayo baya da sauri, sai dai mey?  Memako Meenah taji wani abu sai ma ita Jiddar ta kurma uban ihu sakamakon jikinta dake mata rad'ad'i. Meenah ta farka tana salati sannan ta fito da sauri ganin meke faruwa.
Jidda ce a tsakar parlor tana kurma ihu tana soshe soshe, Meenah tayo kanta tana tambayar lafiya? Ture ta Jidda tayi, sannan tayi d'akinta da gudu ta fad'a toilet tayi wanka da ruwa masu sanyi sosai. Sai dai babu wani sauk'i data samu. Ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuka kawai takeyi, ga sam ta hana Meenah ta ta6a ta, sai surutai takeyi marassa kan gado.
Hijabinta ta saka ta fito parlor a lokacin Meenah na sallah d'akinta, aiko da sauri ta fito ta tafi gidansu.


Mama na d'aki tana sallah ta shigo tana kuka, sai tirje tirje takeyi, bayan Mama ta sallame ta juyo tace
"Ke lafiya..."
Bata k'arasa magana ba Mama taja baya cike da tsoron ganin fuskar Jidda kamar ba tata ba, Mama ta fito da gudu tana salati tana fad'in
"Wacece ke?"
Jidda na biye da ita tana dariya tana cewa
"Ni ce, nice naje wurin boka nida Luby muka anso magani zamu kashe Meenah."
Mama tasa salati tana fad'in
"Jidda. Meya kaiki? Mekika zama? Innalillahi wa inna ilahir raj'iun! Jidda."
Jidda tasa dariya, sai ta susa kai, ta susa jiki tana zum6uro baki tace
"Wai laifina ne? Kaji man Mama, nifa kawai d'ora ni akayi akan turbar nabi kuma."
Ana haka Dada ya dawo, shima cike mamaki yake tambayar lafiya. Mama ta kwashe komai ta fad'a masa abinda Jidda ke cewa.
Dada yace
"Da alama fa kamar hauka takeyi ko?"
Mama tace
"Nima shi nagani."
Suka sa salati, Dada yace
"Duniya budurwar wawa Jidda, Allah ya shiryeki, Hajiya kamo ta ki kai ta d'aki ki rufe kafin mu san abinyi."
Tace
"To."
Ta kamo Jidda, tana tirjewa da k'yar suke tafiya, Jidda taci kwalar Mama tana dariya tace
"Ina zaki kaini? Iye?"
Mama tace
"Muje d'aki ki kwanta."
Jidda tasa dariya, can kuma tasa kuka, can tasa dariya, sai kuma tasa kuka, ta jawo hancin Mama ta matse tace
"Daman haka boka yake? Laifin duk na Luby ne saboda ita ta kaini tun farko, saboda ban ta6a zuwa ba ay ko?"
Mama tana kuka tace
"Eh muje."
Mama ta sha wahala don da k'yar ta kai ta d'aki ta rufe, sai dai taji ana bubbuga k'ofar ana ihu, can taji dariya, can taji surutai, can kuma taji ana cewa
"Boka, boka, Barmuje sunansa."
Mama tayi tsaye tana kuka, tace
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Jidda kinga halin da kika jefa kanki ko? Kinzo kiyi wa wata asiri ya dawo kanki, duniya ina zaki damu? Ka haifi d'a amma baka haifi halinsa ba. Allah ka shirya shine kawai abinda zan ce miki Jidda, Allah kuma ya yaye miki."
Dada ya kira Faruk ya sanar masa yazo yana nemansa yanzu yanzu.


Ba'a d'auki lokaci ba ya iso, Baba ya kwashe komai ya fad'a masa, Baba ya d'ora da cewa
"Ina so idan ta warke ka sallame ta, baka buk'atar cigaba da zama da ita, tunda har kamar Jidda tasan tayi kisa ay kaga zama da irinsu ba amfani.
Faruk yace
"Allah ya kyauta, Allah kuma ya bata lafiya."
Baba yace
"Amin."
Faruk yace
"Bari na dubo ta, daga nan sai na nemi asibitin da za'a kaita."
Baba yace
"To kabi a hankali, don jikin ba dad'i."

A hankali ya tura k'ofar d'akin tana zaune dirshen a k'asa tana kwa6a sabulu da toothpaste cikin wata roba, ya kalle ta duk ta shafa ma kanta, ya zauna a bakin gado yana kallonta cike da tausayi, wannan wace irin rayuwa ce? Wai Jidda tasan taje wurin boka? Ya kalli Dada dake tsaye a bakin k'ofa sannan ya maida dubansa ga Jidda da ke shafa sabulun a jikinta.
Ya gama kallonta yayi mata adduo'i sannan ya tashi ya fita.
Ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba ya je ya nemo asibitin da za'a kaita, daga nan aka kwasheta da da k'yar daga gidan. Faruk ya sanar ma sauran 'yan uwanta suma sunyi jimami sosai, daga k'arshe sukayi mata fatan shiriya da samun lafiya.


***

MSBπŸ’–