Thursday 14 September 2017

AUREN FANSA 45

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# *http://maryamsbello.blogspot.com

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_❣️
     
                🌹45 🌹


Ya d'an yi tsai yana dubanta, ta kawar da fuskarta gefe, yace
"My baby, ki tausaya min ki kula ni, idan har kika za6i ki guje ni to wallahi rayuwata tana cikin matsala, nayi laifi tabbas kuma na gane kuskure na har ma na bada hak'uri, to meyasa bazaki yafe min ba? Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare mu mutane? Wallahi ina k'aunar ki, da zaki bani dama da na nuna maki hakan Meenah..."
Shirun dai ta kuma yi, yace
"To in bazaki yi magana ba, kiyi hak'uri ki saki ranki, kin hak'ura?"
Ya shafi fuskarta yana mai juyo da ita, take tayi k'asa da k'wayar idonta.
"Kinji ni baby? Ki tuna matsayina a gareki, na baki hak'uri kiji tausayina don Allah Meenah. Da me zanji? Kina fushi dani kink'i hak'ura, ke kad'ai fa guda nakeda a halin yanzu, ina zansa kaina Meenah? Please please! Tuba nake, na tuba bazan k'ara ba, kar6i wannan takardar ki gani abin farin cikin da ya same mu."
Ya zura mata takardun cikin hannunta, ta kalla shek'ek'e ba tare da ta karanta ba ta mik'a masa yace
"Yanzu har kin duba baby?"
Ta gyad'a masa kai, yace
"To me kika gani?"
Tace
"Oho!" Kalmar data ambata a ciki kenan ashe ta fito fili, yayi murmushi yace
"Daman wannan takardar k'arin ilimi ne aka tura ni na tsawon shekara biyu wanda zanyi shi a k'asar ingila, shine nake neman shawararki saboda karatunki."
Har ranta taji dad'in alherin da ya same shi wanda ta tabbata yaga hakan a fuskarta
Sai kawai ta ce masa
"Na taya ka murna, sai dai duk yadda ka tsara yayi min."
Yayi murmushi yace
"Alhamdulillah naji dad'i, sai dai inaga kamar zamanki a nan don ki k'arasa karatun naki yafi, amma zan rink'a waiwayanki, bawai natafi har sai na kammal ba ne, a'a zan rink'a ziyartarki, donma in banda ina son kiyi karatun da k'afata k'afarki, yanzun ma idan kinfson mu tafi taren sai mu ajiye shi gaba kya yi shi."
Ba tare da ta kalleshi ba tace
"Babu damuwa, kaje zan zauna."
Yayi murmushi yace
Ay da yake yanzu level 3 zaki shiga kinga dana dawo kin kammala insha Allah, kinga dana dawo sai mu baje soyayyarmu yadda ya kamata."
Tace
"Allah ya taimaka."
Haka yayi ta lalla6a ta kamar k'wai, sai wani riritata yakeyi yana yi mata kalamai masu tausasa zuciya har ya samu ta d'an sauko daga dokin data hau har ma tana d'an kula sa.


Washe gari ne yayi shirin aikinsa, bayan ya kimtsa ta raka shi bakin motarshi yace mata yau da wuri zai dawo yaci abincin rana ta masa amala da miyan ku6ewa d'anya, ta bishi da "To." Da fatan dawowa lafiya.
Yana tafiya ta tashi tayi wanka ta kimtsa gidan sannan ta hau mota tare da kud'in da ya bata ta nufi kasuwa, ta siyo garin amala da k'ashin rago da ku6ewa, tana dawowa ta fad'a kitchen ta fara kacaniyar dafa abinci, k'arfe d'aya da rabi daidai ta gama 1:30 pm, tana gamawa ta fad'a wanka ta fito ta shirya cikin wata atamfa dark blue d'inkin riga da skirt d'inkin ya zauna dabas a jikinta.
Amma shiru ba alamunshi har wajen uku, ta d'auko wayarta ta shiga neman layinsa nan ma bai d'auka ba. "Oh God!" Ta fad'a tare da jefar da wayar ta mik'e bisa doguwar kujera, sama sama bacci ya ringa fisgarta tana k'in yi don bata son baccin yazo.
Can wayarta ta fara ruri ta mik'e zumbur ta d'auka yace
"Baby zan aiko a d'aukar min abincin nan don meeting zamu shiga yanzun nan, idan nace sai na dawo kafin na koma zan makara."
Tace
"Sai ka turo bakomai."
Ta mik'e ta had'a shi cikin basket, ta kira d'an almajirinta Yusha'u tace
"Koda bacci zai d'auke ni idan wani yazo ka d'auko basket bisa dinning ka mik'a masa."
Yace
"To Anty."
Ta koma tayi kwanciyarta. Itace bata tashi ba sai k'arfe hud'u har da 'yan mintina, tashinta yayi daidai da k'wank'wasa k'ofa, ta mik'e zaune daga kwanciyar tana gyara d'aurin d'ankwalinta, sannan ta mik'e tayi tattaki izuwa bakin k'ofa gami da bud'ewa.
Wata budurwa ce sai dai ko ba'a fad'a mata ba tasan yarinyar tana cikin matsala babba.
Ta bata izinin shigowa, ta koma kitchen ta had'o mata kayan lashe lashe da tand'e tand'e, ta koma ta zauna suka soma gaisawa a mutunce, Meenah tace
"Baiwar Allah sai dai ban gane ki ba, sannan meya faru da ke haka naga jikinki duk ciwo haka?"
Maimakon budurwar tayi magana sai kawai ta durk'usa har k'asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsanani.
Meenah ta razana tana tambayar lafiya? Da k'yar budurwar ta tsagaita daga kukan da takeyi sannan ta fara magana cikin sanyin jiki.
"Mu talakawa ne tu6us, wanda har cin yau yakan gagare mu, Allah yayi ma mahafina rasuwa da jimawa, sai mahaifiyata, mahaifiyata ita take fafutukar nema mana abinci da kuma kud'in makaranta, ba irin aikin da batayi ba, haka muka cigaba da rayuwa mahaifiyata itace komai na, sai dai a kwana a tashi na had'u da hatsabiban k'awaye wanda suke hure min kunne har na biye musu na kai kaina a halaka!"
Ta share hawayenta ta cigaba.
"Nazo na fara fita lokacin dana ga dama na dawo lokacin dana ga gama, tun mahaifiyata na fad'an tana duka na har ta gaji ta bini da addu'a, gashi bana jin maganarta, nabi na raina ta ban d'auke ta a bakin komai ba, tasha yi min kuka akan abubuwan da nake mata amma ni ko a jikina, na had'u da samari 'yan k'arya suna min wayau suna kaini hotel su bani kud'i, daga nan idanuna suka ida bud'ewa gaba d'aya, bana ji bana gani, sutura kuwa sai wadda na cire duk akan idon mahaifiyata, har ta kai ta kowa mahaifiyata bata iya fita unguwa, data fita za'a fara nuna ta ana gulmarta.
Kwatsam wata rana sai na had'u da Jidda..."



MSB💖

No comments: