Thursday 14 September 2017

AUREN FANSA 46

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_
     
                🌹46🌹


Da mamaki Meenah tace
"Jidda kuma? Meye mahad'inki da ita?"
Budurwar tace
"Nasan zakiyi mamakin idan na sanar da ke ni ba kowa bace face Lubabatu wacce aka fi sanin da Luby..."
Meenah ta mik'e tsaye a razane tace
"Luby? Kece haka?"
Luby da kanta ke k'asa tace
"Eh nice! Nice Luby aminiyar Jidda, ki zauna Zan k'arasa bayani na."
Ta k'i zama still tana kallonta da mamaki, Luby ta sake d'agowa tace
"Ki zauna don Allah ba don ni ba."
A hankali ta koma ta zauna tace
"Ina jinki." Luby ta cigaba
"Kamar yadda na fad'a miki a baya cewar na had'u da Jidda a wurin bikin wata 'yar makarantar mu da akayi, duk da ba ajinmu d'aya da Jidda ba amma a ranar muka k'ulle muka zama best friends. Nice sanadin lalalacewar Jidda, ni na d'ora ta bisa gur6attaciyar hanyar ita kuma ta bi, a tare muka cigaba da harkar mu ta bin maza da sauransu. Nidai yanzu ba komai ya kawo ni ba illa nazo neman gafararki, ba don ni ba don Allah ki yafe min, nayi kuskure amma yanzu na gane kuskure na, ki gafarce ni..."
Meenah tace
"No kar ki damu ni banida rik'o, kuma na yafe maku, Allah ya tsare gaba, sai dai garin yaya kika ji wannan ciwon haka a hannu?"
Ta kai dubanta ga hannun dake nad'e da bandage gaba d'aya tace
"Wannan a ranar muka samu sa'insa da mahafiyata akan ina so na fita da misalin k'arfe takwas na dare, a lokacin mahaifiyata ta tashi tace ita sam bazan fita ba, niko na dage akan sai na fita sai dai ayi wacce za'ayi, na fad'a mata maganganun sannan nayo hanyar waje, sai dai daidai bakin k'ofa mahaifiyata ta tako da sassarfa tana fad'in, Lubabatu idan kika sa k'afa kika fita ban yafe maki ba, daga haka kawai ta juya ta koma gida, ni kuma kawai naja tsuka na fice abina ba tare da na damu ba. A ranar hotel muka kwana bayan mun gama abinda mukeyi muka zarce club, muna can har asuba, sai da gari ya fara haske sannan muka fito don komawa gida. Sai dai me? Muna kan hanya nida saurayin nan nawa muna jin kid'a muna rawa a mota ba tare da mun ankare ba muka yi had'ari, shi saurayin nawa take ya cika ni kuwa asibiti aka wuce dani rai a hannun Allah, sai dana kwana bakwai ban farfad'o ba, bayan na farfad'o naji likita na cewa sai an yanke min hannu, nayi kuka nayi kuka, nayi bak'in ciki, nayi nadama ba kad'an ba. A ranar nayi Allah wadarai da son abin duniya gami da bijire wa iyaye, nidai cewa nayi ban yarda ba, daga nan akayi wa hannuwa na hotuna (Scan) kusan kala uku, gashi banida kowa dole ni likitan yake tunkara da maganar. Yace min k'ashin hannun ya lalace da yawa, ya ratattake k'ashin, wato sai an yanke su, ido waje na zaro nace
"Duka hannuwa na?"
Yace
"Eh to, zai iya yiwuwa dukansu amma gaskiya hannu d'aya yafi samun dameji wanda idan aka d'auki lokaci zai iya ru6ewa, zamuyi iya k'ok'arinmu muyi miki 'yan dabaru a shi d'ayan hannun, idan Allah ya taimaka sai ya zauna. Sannan abu na biyu wurin yin 'yan bincikenmu mun gano kina d'auke da wannan cutar wato cutar H.I.V AIDS."
Luby ta d'an dakata saboda kukan da yaci k'arfinta, haka itama Meenah sai da tayi hawayen, Luby ta cigaba.
"Wani abu naji ya sokeni a k'irji kamar an sara mani mashi, kuka nakeyi tamkar raina zai fita, gaba d'aya duniyar da abinda ke cikinta sun fitan min a rai, likita ya zayyano min kud'in aiki wato gaba d'aya miliyan biyu harda rabi, kaina ya d'auki chaji sosai, nace su sallameni na tafi na samo kud'in aikin sai na dawo. Suka sallame ni nayi gidanmu, na tarar da mahaifiyata tana ganina ta razana tana tambayar meyasame ni, na koro mata bayani, tayi ta min fad'a tace ita ba ruwanta dani don haka na tafi na nemo kud'in da kaina daman na saba neman kud'i, ta koro ni na fito ina kuka. Babu wadda ta fad'o min rai kamar Jidda, nasan ko bata bani kud'i ba zata taimakeni da shawara, sheyasa na taho nan."
Meenah ta kalli Luby kallo na k'urilla sannan itama ta koro mata nata bayanin.
"A gaskiya Luby idan har kud'in aiki kike nema sai dai kije ki nemi taimako kamar su gidan radio, wurin manyan k'asa, sannan Jidda da kika zo nema bazaki same ta ba, saboda Jidda dai ta haukace."
A razane tace
"Ta haukace kuma?"
Meenah tace
"Eh ta haukace, a ranar da kuka je wurin boka amso maganin da zaku sa min ta saka min ya koma mata, tun daga wannan ranar ta fara hauka tana tona muku asiri, yanzun ma zancen da nake miki ana can ana hadaniyar fidda ta can k'asar waje neman magani. Luby wato ita daman duniya haka take, duk yadda ka d'auke ta haka zata zo maka, tabbas kin tafka babban kuskure a rayuwarki, waya ce miki iyaye abin wasa ne? Musamman uwa, kin wulak'anta uwarki ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kin bi boka ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kinyi zina ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki?  Shekara da shekaru kina shayar da mahaifiyarki gubar 6acin rai, ke ba yarinya ba ak'alla zaki kai shekaru ashirin da shidda yanzu a yadda nake kallonki, yaci ace yanzu kina gidan mijinki kina bautar Allah amma kin tsaya shashanci, shekarunki sun kai ace kinyi hankali ki gane halin da duniya ke ciki, abinda yafi miki kije ki rungumi mahaifiyarki ki nemi gafara, ki mata biyyaya sannan ki gyara rayuwarki tun kafin ki koma ga mahaliccinmu. Ina so ki maida komai kamar tafiyar ruwa ki kuma tari gaba, ki yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau, wallahi Allah gafurur Raheem ne, kuma insha Allah  nima zan taimaka miki da wani abin, cikin gadon mahaifina zan baki wani abu sai ki k'ara cikin kud'in aikin da za'ayi miki."
Ta bud'e baki cike da mamaki sai kuma hawaye suka fara wanke mata fuska.
"Meenah, nagode! Nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya k'ara bud'i, Allah ya jik'an iyaye yayi mana gafara, bani da bakin da zan gode maki, na bibiyeki da sharri ke kuma kin saka min da alkhairi, haka rayuwa take daman ko wannan ya ishemu ishara."
Meenah tayi murmushi
"Kar ki damu, bakomai wallahi ai yiwa kai ne, wannan ba wani abu bane."
Tana kallo Meenah ta mik'e ta shiga d'aki, ba'a jima ba ta dawo hannunta d'auke da paper, ta zauna tana mik'a mata.
"Gashi."
Tasa hannunta mai d'an lafiyar ta kar6a tana kuka, Meenah tace
"Yanzu shiga ta na kira Faruk, na masa bayani shine yace na k'ara miki shima ya bayar." Luby ta duba tace
"Har dubu d'ari uku? Kai nagode Allah ya k'ara bud'i."
Meenah tace
"Wannan ba abu bane ba babu damuwa, Allah ya k'ara tsare mana imaninmu, ya tsare mu daga fad'awa halaka, Allah ka shirye mu ya ganar da mu."
Luby tace "Amin ya Rabbi."
Luby bata tafi ba sai da Meenah ta bata abincin rana tana mai k'ara mata fad'an ta nemi yafiyar mahaifiyarta, a haka ta bar gidan tana mai jinjina al'amarin.

BAYAN SATI BIYU

****

Ranar wata talata, tana zaune taji horn d'in motarsa, ta mik'e cike da mamakin ganin ya dawo da wuri, ta lalla6o ta fito don tun jiya bata jin dad'i. Ta k'arasa wajensa sai fara'a yakeyi yana mata murmushi itama tana tayasa duk da batasan dalilin farin cikin nasa ba. Ta kar6o jakarsa suka jero har parlor ta dire jakar ta d'auko masa ruwan sanyi a fridge ta tsiyaya masa ta bashi.
Bayan ta zauna tace
"Lafiya ka dawo da wuri yau?"
Ya kuma dubanta yace
"Lafiya lau, tafiyar nan ce ta taso wai jibi jibin nan zamu tafi, kin tuna maganar da mukayi a baya ko?"
Tace
"Eh na tuna."
Yace
"To itace yau abin ya ida tabbata."
Tace
"Masha Allah, yanzu jibi zaka tafi?"
Yace
"Insha Allah."
Tace
"Zaku dad'e kenan?"
Yace
"Da shekara biyu zamuyi amma yanzu insha Allah bazai wuce shekara d'aya ba mun juyo, kuma in mun dawo zamu iya samun chanjin aiki da kuma k'arin girma. Yanzu ma so nake naje na shaida masu Dada maganar kuma ke nakeso ki raka ni."
Ta d'an yamutsa fuska tace
"To amma fa ni bana ma jin dad'i."
Ya zaro idanu yana k'are mata kallo, yace
"Kodai abin arzik'in ne ya samu?"
Tace
"Me kenan?"
Yaja hancinta yace
"Kinfini sani, amma banga ta zama ba tashi zakiyi mu tafi asibiti a auna ki don a tabbatar."
Kafin ma tayi magana ya zura mata hijabinta pink color tare da jawo hannunta suka nufi mota.
Ba k'aramar murna Faruk yayi ba da yaji daga bakin likita cewar ciki ne da ita har na kusan wata biyu, tun da suka shiga mota yake washe hak'ora kamar gonar auduga.



MSB💖

No comments: