Wednesday 15 September 2021

YAR AGADEZ PAGE 49 and 50

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 49&50}



To read all my books click the link below๐Ÿ‘‡๐Ÿป

Maryamsbello.blogspot.com




Yau ta kama asabar suna zaune da yamma tana kwance kan cinyarshi in banda shagwaba babu abinda Zarah ke zubawa wai ita a dole sai ya samo mata awara da wainar flour kuma ita bata son home made sai dai na saidawa, irin na bakin hanya. Da yaga abin nayi ne don dole ya tashi ya fita yaje ya samo mata don yaga alama weekend dinsa bazaiyi shi in peace ba don yanzu haka kuka take masa bil hakki sheyasa ma ya tafi jiki na rawa ya bata hakuri akan xaije ya siyo mata. Saida ya fita abin ya soma bata dariya wai dama dai yadda ake fadan cikinnan ashe dai haka yake da sai ta ringa ganin kamar abin bai kai haka ba, sai yanzu ta tabbatar ma kanta da abinda ake ji. Kallon da takeyi taji gaba daya ya gundure ta a hankali ta mike taje zata kashe tv taji an kwankwasa kofa, takawa tayi har bakin kofar tace, "Wanene?" Jin anyi shiru yasa ta bude a hankali wara idanu tayi ganin Hafsat da yayanta Yasir ay batasan lokacin datayi hugging dinsu ba tana ta ihun murna gaba daya bata iya misalta farin cikin da take ciki a yanzu, hannun Hafsat ta jawo har cikin parlor tana jan traveling bags dinsu da sukazo da ita, Yasir yana binsu a baya, zazzaunawa sukayi ita kuwa tana zaune kusa da Yasir ta kasa boye farin cikinta, "Ya Yasir shine baka kirani ba kace zaka zo ba?" Yayi dariya, "Bake kin iya bawa mutane surprise ba? Tou ya kikaji dana rama?" Tayi dariya, "Afuwan angon Hassatu, bari na kawo maku abinci ko?" Yasir yace, "Sallah zanyi amma ina mutumin?" Tace, "Ya fita amma bazai jima ba zai dawo!" Yace, "Ok naga masallaci a nan layin ku bari in tafi in dawo..." a haka ya fita ita kuma taja Hafsat guest room dinsu wanda yake a gyare tas tace ta shiga tayi alwalla tayi sallah, sai bayan tayi sallah ne tayi wanka suka ci abinci lokacin har Yasir ya dawo daga mosque. Tunda suka gano dukkansu suna dauke da jariran ciki ba karamin murna sukayi ba especially Zarah ta taya dan uwan nata murna ba kadan ba. Suna kitchen da daddare suna dafa dinner don kuwa Ashraf da Yasir sun fita zaga gari. Zarah ta kalli Hafsat cikin sigar zolaya tace, "Yanzu Inlaw wai ciki gareki ko? Na kasa yarda wai ya Yasir zai haifa mana da ko diya is so hard to believe he's going to be a father soon!" Dariya Zarah ta bata yadda take maganar kamar itama ba cikin ne gareta ba. "Kajiki yadda kike magana sai kace ke ba cikin ne dake ba? Kawai Ashraf yayi mana ajiya a cikin wannan shafaffen cikin naki." Dariya tayi daga haka ta samu ta kashe ma Zarah baki kuma bata sake tankawa ba har suka gama dafa macaroni da sauce din kaza suka jera kan dining, ta kai komai harda coconut drink dinta da basu sha da rana ba ta fiddo yayi sanyi sosai bayan sun gama suka gyara kitchen din sai suka hau kallo sunayi suna yar fira cike da nishadi. Jim kadan suka shigo hannuwansu niki niki da leda, kan dining suka aje sannan suka dawo parlor suka zazzauna suna cigaba da fira cike da nishadi. Hafsat ta kalli Zarah tace, "Ohni ko kunya mijinki na dawowa zaki fara murmushi?" Dariya tayi sosai parlon aka kwashe da dariya, Ashraf yace, "Hafsat ina ganin mutuncinki fa ki kyale man mata." Aka sake sa dariya, suna kallon Ashraf sai wani ririta Zarah yakeyi ko wurin cin abincin ma kamar ya tauna mata ita kuwa gaba daya kunya ta rufe ta, hararar wasa kawai take galla mashi akan ya daina akwai baki. Ta kasan table Yasir ya kamo hannun Hafsat, "Uhm anya Hafsat zamanmu gidannan zai yuwu? Ni gaba daya sunsa ni jin kunya!" Wani murmushin mugunta Hafsat ta sakar masa "A'a muyi zamanmu ay jibi ne fa zamu koma barsu suci karansu ba babbaka." Hararar wasa Zarah ta maka ma Hafsat, "Wallahi ki kiyayeni wannan Inlaw din tam!" Dariya akasa gaba daya, mikewa Ashraf yayi ya jawo hannun Hafsat, "Tou bari mu barku haka nan dare yayi ku cigaba da soyewa lafiya." Itadai Hafsat banda dariyar mugunta babu Abinda takeyi, dafata tayi, "Inlaw afuwan bari mu wuce mu kwanta sai da safe." Mikewa tayi zata cafko ta Hafsat ta saki yar kara ta boye bayan Yasir, "Fito nan mana kigani inba ga tsoro ba." Yasir ya saki dariya, "A'a malama ki bimin mata a hankali." Dariya suka fashe da ita sannan suka masu saida safe suka tafi daki don su kwanta. Suna tafiya ya jawota ta fado masa a hankali ya rungume ta, "Ya dai yan mata? Ba mun shirya ba ko har yanzu fadan mukeyi?" Dariya ma abin ya bata wato ma har ya saba da fadansu yanxu, dukan wasa ta kai masa tana dariya, "A'a fada man tun yanzu in bada hakuri ba sai anjima ba..." dariya tayi tana kokarin zillewa, "Don Allah ka daina." Ta fada tana binshi da hararar wasa, janta yayi cikin daki rungume da ita kamar za'a kwace masa ita. Ranar dasu Yasir zasu tafi har kuka Zarah tayi dan uwa mai dadi, da xasu tafi ta dauki atamfa guda biyu da turare ta ba Hafsat, har airport suka kaisu ko wane cike da kewarsu, a hanyarsu ta dawowa ne taga kiran Hoodah ya shigo video call da sauri ta dauka cike da farin ciki, ganin fuskar Hoodah yasa ta turbune fuska, "Ya zaki nuna man wannan fuskar taki bani babies dina ni in gansu." Hararar wasa Hoodah ta watsa mata, "Aikuwa ni zaki gani basu ba..." Zarah tace, "Don Allah kiyi hakuri in gansu." Hoodah tayi dariya sannan ta seta camera din inda suke kwance suna ta bacci peaceful, Zarah ta dafe kirji, "Awwwn so adorable MashaAllah," sun kara kyau sunyi bulbul MashaAllah kamar ta sace su, Hoodah ce ta bayyana a screen din, "Happy now? Sai ki shafa man lafiya, yanzu dai ina yayan nawa yake?" Zarah tayi dariya ta saita masa wayar ya karba, kalla yayi yana murmushi, "Lil sis how far?" Itama tana murmushi tace, "Fine fine ya kuke?" Yace "Alhamdulillah ina babies dina?" Ta nuna mashi shima cike da sha'awa yace, "Blessed them." Tace "Thank you," yace "Ina sarki?" Tace "Yanzu ya fita fada." Yace "Ki gaishe min dashi," tace "InshaAllah." Ya mika ma Zarah wayar, "Tou mai ciki naga ma kamar baku gida bari na barki." Zarah tace, "Eh wallahi su ya Yasir muka kai airport." Hoodah tace, "Haba sunzo ne?" Ta gyada kai tana murmushi, Hoodah tace "Ayyah Allah ya kaisu gida lafiya." Tace "Ameen ya Rabbi, take care." Daga haka sukayi bankwana. Wani shopping mall suka tsaya suka siya groceries da abinda take bukata harda kayan lashe lashe. Wurin snacks sukaje ta kwashi frozen ones da su frozen yogurt da ice cream. Suna isa gida ta dinga taya shi kwasar kayan saida ya nuna mata da gaske fushi zaiyi sannan ta daina saida ya gama kai kayan tas sannan ita dauko robar ice cream ta bishi cikin gida. Katuwar robar a ciki ta dauka ta rufe fridge din ta juyo tana kallonshi kanta ko dankwali babu, "Wallahi kwadayi nakeji muje muna kallo zakaga mun shanye shi." Dariya yayi yana shafa cikinta, "Kai kuwa bawan Allah ka cika kwadayi ka barmu mu dan sarara haka nan mana!" Dariya tayi tana kai mashi dukan wasa gaba tayi da robar ya bita parlon yana dariya, "Tou daga fadan gaskiya sai kiyi gaba ki barni tsaye ni kadai?" Cokalin hannunta ta dauka ta jefa mashi ya kauce yana dariya.

FEW MONTHS LATER...

Zarah na zaune kan 3 sitter tana sanye da kayan bacci tana cin goruba, cikinta ya fito yayi tulele ya rinjayeta, tana gidansu inda ta tafi can haihuwa, Khadija tana bata kulawa sosai tana kula da ita ta gyara mata dakin kasa a nan zata zauna idan ta haihu. Mummy ce ta sauko daga sama ta xauna gefenta, take Zarah aka wani shige cikin jikin Mummy, "Zarah kinaso ranki ya baci ko?" Zarah ta dago tana kallon Mummy, "Mummy menayi?" Mummy tace "Kinyi wanka yau?” Zarah tace "Meye amfanin wankan Mummy? Na zama katuwa nayi muni nayi nauyi!" Mummy mikewa tayi ta jawo hannunta da kyar take jan kafarta saboda tsananin nauyi, har dakinta ta kaita ta hada mata ruwan wanka, nan ta shiga cikin kwamin da aka cika da ruwa tayi zamanta a ciki tana wasa da bubbles, Bayan ta gama wankan ta fito daure da towel. Shiryawa tayi cikin loose cotton pink gown, turare masu dadi ta shefe jikinta dasu, gashinta ya kara tsawo ya kara zama baki wulik maybe saboda cikin ne. Wayarta ta dauka ta duba time karfe 2:10pm. Sallaya ta shiimfida ta fara sallah, tayi raka’a biyu tana na ukun ne ta ji muryar Ashraf. Dama tun tana sallar takejin bayanta na ciwo da mararta haka nan dai ta daure ta karasa sallar a haka, shiru tayi a tunaninta kawai normal pains ne saboda daman tana dan jin haka kwanan nan, sai kawai ta fita batun. Duk suna parlor suna kallo Yasir ne kawai babu don shima shekaranjiya Hafsat ta haihu baby boy ansa masa Khaleel. A hankali ta tashi ta shiga daki daidai bakin kofa kawai ta fasa wata irin kara ta zube nan dafe da cikin, a rude kowa yayi kanta, Mummy ce ta kamo ta Ashraf ya taimaka mata suka sata mota, Khadija ta dauko box din haihuwanta da sauri tayi mota. A haka suka isa aka karbesu da gaggawa. Ba Zarah ba hartta Ashraf zufa yakeyi yana kallon yadda take kokarin kawo babynsu duniya. Cikuikuye Ashraf tayi cikin kuka tace, "Bazan iya ba Allah mutuwa zanyi." Kara rungume ta yayi yace "Zaki iya princess just try!" Nurse din tace, "Naga head din just push one more time okay?" Nan suka dinga bata kalaman karfafa guwiwa ay batasan lokacin data fasa ihu ba sai jin kukan jarirai sukayi har biyu. "My princess did it! Weldon! Now look we have two babies!" Zarah ta fashe da kuka, nurse din tace "Congratulations it's girls!" Bisa kafadunta aka dora mata ko wane side take ta kara fashewa da wani kukan tana shafa kansu tana kissing dinsu Ashraf yana tayata.

Congratulations princess, we did it...!” Tayi murmushi cikin kuka.

Tace "We did it!" Yace "Thank you." yace yana hugging kanta yana mata kiss a goshi.

“Thank you..." ya sake cewa yana kokarin maida hawayen da suke shirin zubowa. Bayan an kimtsa babies din aka gyare su tas itama akayi stitching dinta aka kimtsa ta. "Ya sunansu?" Ya shafa gashinta, "You can decide princess." Tace "Your mother's name and my mother's name, sai mu dinga kirnasu Alinah da Alishah." Yayi murmushi yana kara hugging dinta, "Thank you." Zuma aka lasa masu sannan ta dora kanta bisa kafadar Ashraf tana lumshe ido kamar mai bacci, tana dauke da Alishah a cinyarta, bude ido tayi ta kalleshi, "They're so cute.." tace tana kissing kanta, dan turo baki Ashraf yayi, "Am jealous the babies have been receiving kisses but none from me." Zarah tayi dariya, "You’ll get yours idan na tashi daga bacci..." tayi hamma, don ta gaji ba kadan ba, Ashraf ya gyada kai yana tashi tsaye, "Bari naje nayi wanka, kema ki kwanta ki huta yanzu su Mummy zasu shigo wurinki..." yayi kissing dinta tare da twins din sannan ya juya yayi hanyar kofa. Har ya kai kofa ya juya yana murmushi, "I like the names you choose for them." Tayi murmushi "I like it too..."

Alishah and Alinah.

Washe gari su Hoodah suka iso nan da nan murna ta barke tsakaninsu, Su Aman sun girma sun kara kyau kai kace wasu black indians. Kowa ya gansu sai yaji sha'awar daukarsu ga su da shegiyar kyuya in ba Hoodah ba basu yarda da kowa sai Zarah shima ba ko yaushe ba. Da kyar suka saba da kawun nasu wato uncle Ashraf take ya shaku da yaran suka cigaba da makale masa. Haka aka cigaba da zaman barka mai jego da babies na samun kulawa wurin Mummy. Ranar suna anyi taron suna lafiya kuma ya kayatar mai jego tayi fes da ita tana sanye cikin wani golden lace sai kyalli takeyi kamar wata amarya. A haka aka sha pictures anci ansha an watse sai fatan Rabbi ya raya su cikin aminci.

-----

Bayan Zarah ta haihu da wata daya akayi bikin Khadija da angonta Dr Hafiz duk da mahaifiyar tashi batayi na'am da ita ba amma hakan bai hanata tayi hidimar bikin dan nata ba. Bayan an gama taron biki lafiya amarya tana dakinta suna zaman amarci lafiya, ba karamin gwargwamaya aka sha ba kafin mother Inlaw din tata tayi accepting dinta amma yanzu Alhamdulillah komai yana tafiya yadda ya kamata suna zamansu lafiya itada mijinta. Kawai matsalar ta daya rashin haihuwa duk yadda zataso walwala in ta tuna sai taji komai ya fice mata kai, Dr Hafiz ma ke bata kwarin gwiwa akan ay wannan ba abin tada hankali bane ba.

-----

Haka rayuwar ta cigaba da gudana inda Khairy yanzu haka danta ya warke har ma ta samu mijin aure wani carpenter wanda ya amince ya aure ta haka aka tattara aka aurar da ita dayake shima yana dauke da irin cutarta a haka suka cigaba da xamansu tare suke zuwa karbar magani, yanxu haka Hoodah ta bata kudi taja jari ba karamin godiya tayi ba. A bangaren Karimah kuwa abin sai wanda ya gani bayan doguwar jinyar da tasha Allah yayi mata cikawa ta rasu ranar wata alhamis da tsakar dare inda a ranar ta dinga kururuwar fitar rai take ta rasu inda aka rufe ta washe gari bayan an sanar da Abba har inda take yazo ba karamin girgiza yayi ganinta ba, nan yayi mata addu'ar rahamar Allah tare da fatan Allah yasa iyakar wahalar kenan. 

-----

Haka rayuwar ta cigaba da gudana a kowane bangare ko wace sai sam barka yanzu haka twins din Hoodah shekararsu daya harda yan watanni inda ta kara samun wani cikin, suna nan twins sai dada kyau suke suna samun kulawa don a yanzu haka ana kiransu prince and princess, duk inda kaga daya zakaga dayan, Hoodah kuwa bata fasa aikata aikin alkhairi ba sai bunkasa garin suke yanzu haka da wuya kaje kaga almajiri na bara ko daya baka gani duk a sanadiyar Hoodah, kullum soyayyarsu dada bunkasa takeyi suna kara samun cigaba a rayuwarsu..... 






             ALHAMDULLAH!


MashaAllah Alhamdulillah a nan na kawo karshen novel dina mai taken YAR AGADEZ, darasin dake ciki Allah ya bamu ikon dauka, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana ๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป, A Gaskiya naji dadin yadda kuke bani kwarin gwiwa da comments naku nagode sosai Allah ya bar zumunci love you all.๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’•❣️๐Ÿงก❤️

Friday 10 September 2021

YAR AGADEZ PAGE 48

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 48)



To read all my books click the link below๐Ÿ‘‡๐Ÿป

Maryamsbello.blogspot.com



Har ta iso dab dashi ganin yadda ya tsareta da idanu sai kawai ta sunkuyar da kanta ta juya kekenta tayi cikin gida saboda bataso ya gano yanayin da take ciki don ita gaba daya abinda takeji yafi karfinta, Dr Hafiz yabita da ido har saida ta shige, murmushi kawai yayi sannan ya cigaba da shan juice dinshi, tunani kawai yake shin wannan wace irin mutum ce? Yau zai ganta gata nan all moody wani time din kuma lafiya lau cike da nishadi. Da yamma tana fitowa daga dakinta da yake yanzu dakin kasa aka gyara mata nan ne dakinta, tana fitowa taci karo da Mummy tana waya da alama Zarah ce ke kan layi, da murmushi ta karaso kusa da Mummyn tana binta da ido har saida ta kammala wayar, Mummy ta kamo hannunta tace, "Har kin tashi? Ay tun dazu na dawo na leka dakinki naga kinata bacci abinki kina hutawa." Tayi murmushi "Mummy ina yini? Ya aiki?" Mummy tace "Alhamdulillah ya therapy din?"  Tace "Lafiya lau." Mummy tace "Tou kinyi sallah?" Ta girgiza mata kai, "Ina hutu." Mummy tace, "Ok Mama Hauwa ta kwantar dake kan gado?" Ta gyada mata kai, "Eh ay ita ke kula dani indai baki nan." Mummy tace, "MashaAllah, tou abinci fa?" Tace "Zanci anjima." Mummy tace, "Haba Khadija, kinsan akwai maganin karfe biyar kuma ana so a bada gap da abinci kafin a sha." Mummy ta mike ta nufi dining don zubo mata abinci, saida ta xubo ta dawo sannan ta fara bata abincin, sai da tayi nisa a bata sannan ta dakata tana kallon Khadija kafin tace, "Yauwa Khadija dama kuwa ina son magana dake?" Khadija tace "Ok gani Mummy." Mummy ta danyi shiru kafin tace, "Khadija ni sai inga kamar Dr Hafiz sonki yake..." da sauri ta dago tana kallon Mummy lokaci daya kuma gabanta ya fadi, da sauri ta girgiza mata kai, Mummy tayi murmushi, "Ba lallai bane ki sani duk da nasan ya kamata ki fahimta, duba da yadda yake dawainiya dake yake baki kulawa na tabbatar ba banza ba Khadija, don haka ki nutsu nidai har ga Allah Dr Hafiz ya kwanta min a rai kuma na yaba da halinsa, ki nutsu Khadija and also listen to your heart..." Khadija ta sunkuyar da kai take taji ta koshi da abincin kuma.

---

Ranar wata juma'a tana zaune parlor da safe Mama Hauwa tana tsefe mata kai Mummy ta fito da shirin fita office tana murmushi tace, "Yauwa ko kefe? Da kin zauna da kai sai kace ciyawa, anjima ki daure kije salon a wanke maki kan Khadija in kuma a gida kikeso zan dawo in wanke maki anjima." Khadija tace, "Inason inje salon din Mummy." Mummy ta ciro kudi dubu biyar ta bata, "Gashi Mama Hauwa sai ta rakaki salon din," murmushi tayi sannan ta karbi kudin, "Thank you." Mummy ta maida murmushi, "Take care." Tana fadan haka ta fita bayan ta masu bankwana. Da yamma bayan ta dawo daga salon din tana zaune garden ita kadai tana practicing zana wata gown da aka basu as assignment kamar daga sama ta hango shi yana shigowa, dagowa tayi tana kallonsa ganin irin shigar da bata taba ganinsa da ita ba wato kayan hausa kullum ciki jeans yake da riga amma yau yana sanye da dark blue shadda harta hular kansa kalar kayan jikinsa ce, a hankali ya karaso tare da turarensa wanda ya cika wurin, "Salam yan mata, zane akeyi ne?" Dan gyada mashi kai tayi a hankali tana jin kamar ta bar wurin, "Ya naganki haka kuma? Ko don nace Doctor dinki ya saki kuka rannan Khadija, fushi ake dani?" Bata san lokacin data zabga mashi harara ba, "Ohni Hafizu da harara na kisa dana dade da mutuwa, yanzu dai kiyi hakuri am sorry you hear?" Turbune fuska tayi ita sai yanzu ma ta lura bata san meya bata haushi ba, "Wai bana bada hakuri ba, yanzu dai me zanyi ki daina hararata don Allah?" Girgiza kai tayi, "Babu, ni zan tafi cikin gida."

Girgiza kai kawai yayi yace, "Nasan wani wuri a nan inda suke yin arts na fashion..." da sauri ta juyo tana kallonsa, "Really? Please mu tafi wurin mana." Yasan hakan kadai ne zaisa ta dawo daidai, da sauri ta gyara gyalenta wanda yake daure bisa kanta sannan ta turo kekenta har gaban motarsa, saida tazo shiga kuma sai ta tuna bata fada ma Mummy ba da sauri ta bude wayarta ta kirata nan ta bata izinin tafiya da kyar. Har suka isa wurin tsit kakeji a cikin motar, suna isa ta gwale idanu waje, "Wow Doctor Hafiz wurin nan ya hadu." Yayi dariya "Ashe dai ansan sunana?" Har ya karaso inda take tare da fiddo kekenta yana dariya tace, "Zaka fara ko?" Dariya yayi yana daga hannu alamun hakuri kafin ya fara janta har suka karasa ciki, baki bude take kallon wurin tun da take bata taba ganin inda ya birgeta ba irin wurin nan ba, babu abinda take sai murmushi zuciyarta fes, "Ban taba ganin murmushinki haka ba Khadija..." ya fada yana kallon yadda take snapping arts din da camerar wayarta, "Tou kawo wayar kema in maki hoton, I just love your smile today." Bata masa gardama ma ta mika masa wayar, har sai da ya dauketa kala kala kai harda ma wayarsa ya hada yana daukarta. Yana cikin daukar hoton ne wayarsa ta fara kara ganin Dr Haiydar yasa ya dauka yana fadin "Doctor yaya?" Dr Aliyu yace, "Please kuna tare da Khadija?" Yace "Eh muna tare lafiya dai?" Yace "Ah lafiya lau dan bata please minti daya." Mika mata wayar yayi yana murmushi, ta kara a kunne, "Hello ina yini Doctor?" Yace "Alhamdulillah, abinda yasa na kiraki karki zo appointment gobe sai jibi InshaAllah, abinda yasa banida number ki sheyasa na kira da wayar Dr Hafiz..." tayi murmushi "Laa bakomai Doctor Allah ya kaimu ba damuwa." Taji sautin murmushinsa "Tou godiya nake sarautar mata." Tayi dariya sannan ta mika masa wayar saida sukayi bankwana sannan ya katse kiran yace, "Yanzu Khadija sarauyinki wayata ma xai kira tsabar bai iya nemo taki number din?" Ta tintsire da dariya, "Wai saurayi! Dr Aliyu ne fa." Murmushi kawai yayi ya kyaleta daga nan wani shop taga sun nufa, tana dubawa taga shagon saida electronics ne, tsayawa tayi tana kallonsa fuskarta da alama tambaya yayi murmushi, "To make life easier for you am gonna buy you a laptop..." Girgiza kai tayi da sauri, "A'a don Allah basai ka siya ba zan cigaba da zane na a paper." Ko saurarenta baiyi ba kawai taga ya shiga shop din ya jima kadan can ya fito hannunsa dauke da tsadaddar laptop kirar apple, yana shigowa motar ya mika mata take sai yaga tana hawaye, a dan rude yake kallonta, "Khadija kuka kuma? Why are you crying please?" Share hawayenta tayi tace, "Doctor why are you doing this?" Shiru yayi ya murza key ya tada motar ya cigaba da tafiya abinsa, ta sake tambayarsa, "Please don Allah doctor ka fada man meyasa kake dawainiya dani?" Ta fada tana tsareshi da idanu, can ya numfasa, "Karki damu zan fada maki very soon Khadija..." daga haka tayi shiru har suka isa gida. ---

A hankali soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Dr Hafiz da Khadija duk da da farko tayi tunanin Dr Haiydar takeso sai daga baya ta fahimci zuciyarta tafi karkata da Dr Hafiz, duk wata kulawa daya kamata ya bata yana bata, kuma yanzu alhamdulillah ta warke tangaram ta mike kafafunta suna takawa don dai kawai dan limping din da takeyi kadan kadan amma dai ta samu lafiya. Bayan yan lokuta da basu wuce wata biyu ba aka sanya bikin Dr Hafiz da Khadija za'ayi bikin nan da wata biyar bayan Zarah ta haihu. Ranar da aka shirya akayi zataje gaida mahaifiyar Dr Hafiz Mummy ta shiryata tsaf ta taimaka ta shirya. Khadija tafi minti goma zaune a daki aka kwankwasa kofar aka shigo Mummy ce ta shigo tana murmushi Khadija ta mayar mata, "Amarya ango fa yana waje ke yace jira, ya kamata ki fito ku tafi kuje ku dawo..." gyada kai tayi tana faman sunna kai, Mummy ta mike ta jawo hannunta suka fito, tunda suka fara saukowa daga bene take murmushi, bankwana tayi wa su Mummy, Mummy ta mata sharadin kar dai suje su dade a can sannan ta kula da kanta. Tunda suka fara tafiya take jin faduwar gaba gaba daya a dare take, shima kansa baisan wace irin tarba mahaifiyar tashi zatayi mata, duba da yadda ya shawo kanta da kyar akan ta amince bayan dogon bincike da kuma ganowar ainahin wacece dan nata zai auro ba karamin gwargwarmaya akasha ba don har cewa take saidai ya zaba ko ita ko Khadija da kyar da jibin goshi ya shawo kanta ta hakura, amma koda wasa bai taba yarda ya fada ma Khadija reaction din Mamin tashi ba. Saida sisters dinshi wadanda ke aure sukayi takakkiya suka zo suka sa baki tace ba damuwa. Bayan sun isa ya sakar mata murmushi, "We are here amarya." Ta sunkuyar da kanta batace komai ba ta bude motar ta fito a tare suka jera har cikin parlon, parlon ba kowa sai karar tv sukayi sallama yace ta zauna bari yayi mata magana, a hankali ta zauna tana dan kalle kalle. Mami na zaune cikin daki tana shan fruit salad ya shiga da sallama, zama yayi kasa ya gaishe ta cike da ladabi ta amsa normal, yace, "Mami tana parlor tana jiranki." Da toh ta amsa, mikewa yayi ya fita ita kuma Mami ta sanya mayafi ta bi bayanshi. Khadija na ganinta ta fito tayi sauri ta zauna kasa Mami ta iso ta zauna kan kujera shi kuma Dr Hafiz yaje yayi ma masu aiki magana suyi arranging abinci kan dining. "Mami barka da wuni?" A wani yatsine take amsawa kamar tana tauna magani Khadija dai bata bari abin ya dameta ba ta saki murmushi, "Mun sameku lafiya?" Mami tace "Lafiya, ya mutanen gidan?" Tace "Duk suna lafiya." Tace "Tou madallah, feel at home bari na shiga ciki yanzu zan fito." Khadija ta gyada mata kai sannan Mummy ta mike ta shiga guest room ta fiddo mata hijab din sallah da carpet, sannan ta fito daga bakin kofar tace, "Zakiyi sallah?" Ta gyada mata kai Mami tace "Tou taso." A hankali ta mike sannan ta shiga ita kuma Mamin ta fito. A lokacin data gama sallar azahar ta fito babu kowa parlon amma da kamar tana dan jin maganganu na tashi sama sama daga kitchen, har tayi gaba sai kuma ta dawo fuskarta cike da shock tana sauraren maganganun da suke fadi, "Wai kana tunanin don kawai tazo na sakar mata fuska shine nayi accepting dinta as my daughter Inlaw? Tou ka bude kunnenka da kyau kajini, bazan taba accepting shegiya ba ban hanaka aurenta ba nidai babu hadina da ita, kaidai matarka ce amma ni ba surukata bace! Kawai sai kaje ka auro man saura a matsayin suruka ka kawo man ita cikin gida? Tou ban aminta ba kaidai da kaji zaka iya sai kaje kayi Allah ya taimaka..." idanunshi take suka kada sukayi ja yace, "Haba Mami da take Shegiya laifinta ne? Batada laifi ko kadan! Sannan da kike maganar saura shima ba laifinta bane, Mami idan yanzu akace yarki ce zakiso ayi mata haka?" Ta tsaida shi, "Tou nagode ma Allah ba yata bace! Don haka ka fita idona Hafizu!" Jikinta babu inda baya rawa har wani kyarmar sanyi takeyi, idanunta na neman kafewa dafa dining din tayi by mistake ta kado jug din dake kai ya fado kasa take Dr Hafiz ya zaro idanu waje yana rufe bakinsa da hannunsa, "Kinga abinda kikayi ko Mami? Nagode sosai...!" Da sauri ta juya ta fita daga parlon wanda yayi daidai da fitowar Dr Hafiz amma ina har ta fice da gudu, "Khadija please wait!" A haka yabi bayanta da sauri cike da tashin hankali! Khadija gudu kawai takeyi tana wani irin numfashi na wanda tashin hankali ya kai kololuwar tashi, "Innalillahi wa inna ilahir rajioon..." kawai take nanatawa a yayinda take kukan fitar rai, Dr Hafiz ganin bata cikin hankalinta kuma zata iya fada ma titi yasa yayi wani irin gudu yasha gabanta da gaggawa sai haki yakeyi, ita kuwa cikin kidima take wani irin kuka tana jin dama ta mutu don tasan wannan bakin cikin ta dinga haduwa dashi kenan da gori har karshen rayuwarta, karshen tashin hankali ta shiga wanda ko gabanta bata gani sai duhu take gani, "Khadija! Don Allah ki tsaya ki saurareni karki tada hankalinki a kan maganar da kika ji don't take it to heart wallahi she didn't mean it, Mami tana sonki Khadija...." ya fada yana kokarin rikota ganin nema take ta cigaba da gudun da takeyi, baisan lokacin daya fizgota ba ya rungume ta a jikinsa yana karanta "Innalillahi wa inna ilahir rajioon." A jikinshi ta saki wani irin kukan da bai taba ji ba a rayuwarshi har wanji jijjiga takeyi, ji take gaba daya komai na duniyar nan ya tsaya mata cak bata gane komai, "Don Allah ki daina kuka nan Khadija, kinsan ina sonki duk a yaya kike, I don't care what anyone else think, I love you just the way you are...." magana yake mata amma gaba daya ta rufe fuskarta da hannuwanta banda kuka babu abinda takeyi sai girgixa kanta takeyi, "Dama nasan irin ranar nan na zuwa Doctor! Wallahi dama mutuwa ce ta daukeni don nasan bakin ciki da kunci zan riska har karshen rayuwata! It will keep hunting me for the rest of my life!"  Tallabo fuskarta yayi yana share mata hawaye, "Kar ki sake wannan tunanin Khadija, am here for you no matter what, tsorona karki fasa aurena akan wannan Khadija I cannot leave without you Khadija please don't leave me..." dagowa tayi a hankali taga ya kureta da idanu yana kallonta, a hankali take share hawayenta idanun nan sun kada sunyi ja, "Tashi muje na maida ki gida." Mikewa yayi yaga sai kalle kalle takeyi shi tsoronshi daya kar ta kara ballewa sheyasa ma yaki sakin hannunta ya rike gam dan baisan ta inda zai fara tarota ba, jiki a sabule Khadija ta mike ta kalli yadda ya rike mata hannu gam, ya juyo yaga sai kallon hannun nashi daya rike takeyi sai kuma kalle kalle takeyi, "Doctor ka man alkawari bazaka taba kyamatata ba no matter what."  Kallonta yayi sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya dora dayan hannunshi saman hannunsu dake rike yana kallonta kallo na kurilla yace, "I promise you Khadija, no matter what I will never ever leave you." Sai a sannan ta dan sakar masa murmushi a haka ya cigaba da janta har mota sannan yace, "Ki tsaya a nan bari inje in dauko maki bag dinki cikin gida kinji?" Daga mashi kai kawai tayi ta bude motar ta shiga, a kan kujera ya samu Mami babu abinda takeyi sai girgiza kafa ko kallonshi batayi ba ya duka daidai kafarta ya dauki jikkar sannan ya dago yana kallonta a take ta juya fuska tana kallon wani side, jiki a sanyaye ya fito daga parlon....



Kuyi hakuri da jina shiru da kukayi kwana biyu munyi rashin wuta ne, and also kuyi hakuri da wannan ba yawa!๐Ÿ˜‚also unedited

Friday 3 September 2021

YAR AGADEZ PAGE 47

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 47}



To read all my books click the link below๐Ÿ‘‡๐Ÿป

Maryamsbello.blogspot.com





Washe gari wurin karfe goma da kusan rabi aka sallami Hoodah bayan an tabbatar da babu wani abinda yake damunta itada babies, Zarah tana nan makale da yan biyu, Abbi yayi arranging tarbar da za'ayi ma Sarauniya da ita da jariranta da irin kyauttukan da ya tanadar mata, a mota Ummi na rike da daya haka ma Zarah na rike da daya, haka suka iso gida tun kafin a bude masu gate makada suka fara buga algaita suna welcoming Hoodah da jariranta, Abbi na tsaye har suka fito daga motar inda aka karasa masa da jariransa yayi bismillah ya karbe su, wani irin farin ciki yaji ya lullube shi ya jima yana kallonsu kafin ya fara tofe su da addu'oi sannan yace, "Allah ya raya Safinah da Ahmad yayi maku albarka, Allah yasa su gaji mahaifinsu." Aka amsa da Ameen, (Ahmad sunan Abbi ne na asali) nan ya mika yaran ya kalli Hoodah yayi mata sannu ta amsa sannan Sultan ya kama ta yayi ciki da ita har dakin Ummi ya kaita, tana shiga tayi arba da Kaka xaune tsaye tayi cike da shock, batasan lokacin da fada ma kaka ba cike da murna, "Kaka yaushe kikazo?" Kaka ta kara rungume ta sosai cike da murna, "Jiya da daddare na iso, ay dama nace ni zan fara yi maki wanka bazan bari a rigani ba." Hoodah tayi dariya, nan aka miko ma Kaka yaran tace, "Kai tubarkallah ya akayi kika haife wadannan tula tulan yaya MashaAllah, lallai mamansu a koshe take." Aka sa dariya har kasa Sultan da Ashraf suka gaisheta ta amsa, sannan suka sa kai suka fita, nan Zarah ta tsugunna itama da gaida Kaka, Kaka tace "Zahara shine kika gudo kika barni ko? Ay da sai ki jirani mu taho tare ko." Zarah na murmushi tace, "Kiyi hakuri Kaka nida Ashraf muka taho, Abba ne yace mu bari zai taho dake." Tace "Nidai bawani, kawai a kawo min ruwa in gashe jikata da wadannan yan mitsa mitsan." Zarah ta mike kenan sai ga Ummi ta shigo da katuwar kula ta ruwan zafi ta dire bakin kofar bathroom tace, "Tou Kaka ga ruwan nan amma zaki iya yi mata ko inyi mata?" Kaka tace "Yi mata zanyi tas, ke sai kiyi wa jariran." Ummi ta amsa da toh sannan ta fita ba'a jima kwarai ba ta dawo da robar da za'ayi wa babies din wanka nan Zarah ta mike ta taimaka mata suka hada ruwan farko suka kai na Hoodah a guest room don sai yafi dadin wanka yafi space. Kaka ta mike taja hannun Hoodah suka fita, nan Ummi ta gyara zama Zarah ta cire ma Ahmad kaya ta mika shi nan Ummi ta sumbule shi tas Zarah ta hada masu kaya bayan ta gama aka mika Safina itama nan aka sumbule ta tas, Zarah ta shirya su sannan ta kwantar dasu, ana gamawa sai ga Sultan yasa an kawo sauran kayan babies da na Hoodah bayan an dire kayan tas sannan yace da Ummi, "Ina Hoodar?" Ummi tace "Wanka ake mata." Yace "Ok ga rago nan nasa a gasa mata sai taci sosai," Ummi tace, "Ok tou, nima gashi nan nasa ana dama mata kunu abinci ma data fito zata ci." Yace "Ok." Wurin babies din ya tafi inda Zarah ke basu kulawa ya sake dubasu sannan ya fita yana murmushi. Kafin kace me gidan ya dau harami shiga kawai ake ana fita duk da ma akwai security ba kasafai ake shiga din ba sai da umarnin sarki, yan uwa da abokan arziki ana ta zuwa ganin babies, kullum Kaka ke ma Hoodah wanka sau biyu a rana sai Ummi tayi wa babies din, ita kuwa Zarah gaba daya itace ke kula dasu ashe tanada son yara haka. Ba karamar kulawa suke samu ba daga mai jegon har jariran. Hoodah har ta fara dawowa Hoodan da muka sani yar budurwa tayi kyau ta gasu abinta, babies din kuwa tuni sun murje sun yi jajir sun fara kiba. Ana gobe suna su Yasir suka iso shida Hafsat, wani irin murna su Zarah sukayi suka basu kyakkyawa tarba nan da nan aka cika masu gabansu da kayan motsa baki da abinci da drinks. Ranar suna Abbi yayi organizing gagarumar walima, gaba daya ma harda invitation card aka buga da pass, nan masu taya murna suka fara hallara, mai jego da safe ta saka super mai kyau inda aka sha hotuna sai da yamma ta cire ta maida dankareren lace wanda yasha dinki tayi bala'in kyau tasha light makeup, gaba daya Zarah da Hafsat suna tare da mai jego suma sunsha kyau ba kadan ba. Can na hango su Hafsat da dukkan members na Yar agadez sai faman dibar abinci suke suna sawa a leda da sauri nace masu haba ku kuwa ku bari mana za'a sa maku har sai kun ture๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜๐Ÿ˜œ. Su angon jego dasu Ashraf da Yasir suma suna tare a cikin fada tare da Abbi a can suka ci abinci kafin a fara daukar pictures, sai gab da magrib taro ya watse sai fatan Allah ya raya mana Ahmad da Safina inda Sultan ya bukaci a saya sunan saboda yace bazai iya ringa kiran sunan mahaifiyarta kai tsaye ba, shine aka sa mata Afreen inda Ahmad za'a dinga kiransa da Aman. Bayan sallar magrib su Hoodah da Zarah suna zaune palor suna cin snacks da peppered chicken inda su kaka suna dakin Ummi suna faman hutawa don ba karamin gajiya sukayi ba, su Sultan kuwa Ashraf ya hada masu wata yar get together ta maza kadai suna can sunayi, knocking kofa akayi jakadiya da wasu maids da ke ta faman gyara parlon inda ya baci ta fita wajen kofar ta bude, wani dogari ne a tsaye yace da ita, "Jakadiya, Sarauniya tayi bakuwa a waje, amma ban ce ta shigo ba tukunna sai naji idan tana da appointment?" Jakadiya tace "Tou bari a sanar mata dan jira a nan." Nan taje gefen Hoodah ta tsugunna har kasa tace, "Allah ya karawa Sarauniya lafiya kinada bakuwa a waje." Tace "Wacece?" Jakadiya tace "Nima bansani ba bari in tambaya." Tana fadan haka ta mike, nan Ummi ta bukaci Zarah ta kawo su Afreen ayi masu wanka, Zarah dama tana goye da Aman Hafsat kuma na goye da Afreen, nan Zarah ta fara mikewa ta shiga ciki. Jakadiya ce ta dawo ta tsugunna, "Allah ya kara maki lafiya wai maman Khairy ce." Nan gaban Hoodah ya dan fadi tadai dake tace, "Ba damuwa a shigo da ita, ta sameni gazebo." Daga haka ta mike ta yafa gyalenta tayi hanyar kofa, maids dinta guda biyu suka rufa mata baya. A cikin gazebo din ta zauna bisa kujerun wurin alamun na hutawa ne, tana zaman jiranta sai gata ta karaso dogari na gaba ita tana baya, saida yazo gaban Hoodah ya sunkuya, "Ranki shi dade gata nan." Godiya ta masa godiya inda ta sallame shi nan ta kalli maman Khairy tana murmushi tace, "Bismillah shigo Mama." Da sauri ta shigo zata bada gaisuwa Hoodah ta tsaida ta tace, "Don Allah karki gaishe ni Mama." Mama tayi murmushi ta zauna kujerar dake gefen ta Hoodah, Hoodah tace, "Ina yini Mama?" Tace "Lafiya lau Alhamdulillah, ashe an samu karuwa?" Hoodah tayi murmushi, Mama tace "Tou Allah ubangiji ya raya mana ya masu albarka." Hoodah tace "Ameen."

Mama ta numfasa sannan tace, "Kiyi hakuri da wannan zuwan ba zatan da nayi maki, da naso sai hidima ta lafa amma kuma sai naga ya cacanci inxo maki barka sheyasa nace bari inzo gaba daya, wata alfarma ke tafe dani idan bazaki damu ba?" Hoodah ta numfasa, "Allah sarki ay babu damuwa anytime kike son xuwa xaki iya zuwa Mama wannan ay ba wani abu bane, komai fa ya wuce tsakaninmu wallahi babu komai." Mama tace, "Hakane." Hoodah tace, "Wace alfarma ce wannan Mama?" Mama tace, Akan Khairy ne taimakonki muke nema..." Hoodah tace, "Ina jinki?" Mama tace, "A lokacin da Khairy zata haihu na farko bayan ta haihu ta kamu da matsalar yoyon fitsari wannan lalura munyi magani har mun gaji abu yaci tura, tana nan yanzu in ba mu da muka zame mata dole ba wallahi babu mai son ta matso kusa dashi duk ta zama kazamar karfi da yaji ranki shi dade, sai abu na biyu bayan ta haihu sai dan ya fito da matsala irin jariran ne da ake haifan su da katon kai wallahi akan yaronnan munyi karkaf nida mahaifinta yanzu abun ya kai har motarsa saida ya saida, kullum muna zarya hanyar asibiti yan uwanmu sunyi iya nasu wallahi basuda karfin taimaka mana, yanzu tana nan a gida ga jikinta yadda kikasan an yaba mata gawayi wasu kattan kuraje takeyi a fuska da kuma wasu wurare na jikinta, wallhi ko asibiti sun kasa karbarta fuskarta ma kanta sai ta baki tsoro, shine nazo wurinki ki taimake mu kamar yadda Allah ya taimake ki, ki cece wannan yara da kudin magani ko yaya ne abinda Allah ya hore..." ta karasa tana goge hawaye, matukar tausayi ta bata, Hoodah tace, "Innalillahi wa inna ilahir rajioon, Allah ya basu lafiya yasa kaffara ne, yanzu zan fara baki wani abu ki rike, don  sarki baya gida idan ya dawo zan same shi in mashi bayani nasan bazata gagara ba InshaAllah." Mama ta sake share hawayenta da hannu tace "Mungode Allah ya saka maki da alkhairi ya kara girma da arziki, mungode sosai da sosai, sheyasa akace dan adam kowa da baiwarsa kuma babu kyau wulakanta mutum saboda shi wannan da kake wulakantawa a gaba zai iya taimaka maka..." Hoodah tayi murmushi ta mike tana kallon Mama, "Mama ina zuwa." Daga haka ta fara tafiya maids dinta na biye da ita, da tagumi Mama ke binta da kallo abun duniya duk ya ishe ta, Hoodah ta kai kusan mintina sha biyar can sai gata ta dawo fuskarta dauke da murmushi har tazo ta zauna hannunta rike da envelope, ta kalli Mama tace "Mama ga wannan ku fara amfani dasu zuwa gobe InshaAllah zamu zo sai muga abinda zamuyi a kai." Mama hannunta na rawa ta karbi envelope din tana ta jero godiya tana kuka sosai Hoodah na nuna mata ay babu damuwa ta daina kuka, "Dole ne in maki godiya ranki shi dade, kin mana abinda ko dan uwanmu bai mana ba, duk da abinda Ummalkhairy tayi maki amma gashi kece silar taimakonta, dole ne mu kara jin tsoron Allah wallahi rayuwar nan ba komai bace." Hoodah tayi murmushi, "Babu komai Mama dama ita duniya makaranta ce a cikinta muke daukar darasi, kuma a cikinta ne muke banbance fari da baki, don haka kedai kije ki kai yarki da jikanki asibiti Allah ya kara lafiya." Mama na murmushi tace, "Tou nagode kwarai da gaske ni zan koma." Hoodah tace, "Bazaki shiga kiga babies ba? Sannan zaki tafi ko ruwa baki sha ba ki shigo ciki." Bata musa ba suka mike inda suka taka har ciki ta shiga tayi barka sai yaba kyan babies din takeyi kamar ta sace daya takeji, sannan basu barta ta tafi ba saida aka kawo mata abinci dasu snacks da drinks ga kaji da salad saida taci sannan Hoodah tasa daya daga drivers dinta ya dauketa ya kaita har gida aikuwa tana zuwa ta basu labari jikin Khairy duk yayi sanyi, ji take dama za'a iya komawa baya da zata gyara rayuwarta sannan ta gyara barnar da tayi. Ganin kudin yasa suka razana Baba ya kirga yaga million daya ne harda wani abu a kai, tagumi yayi yana bin Khairy dake kwance kan tabarma da kallo  yace, "Kinga rayuwa ko Ummalkhairy? Kinga abinda na dade ina fada maki ko? Amma duk kikayi watsi da maganata kika dinga aikata abinda ranki yakeso, Khairy duk da na yafe maki amma na kasa mancewa da abinda kika aikata Khairy, kin kai kanki kin baro Khairy wallahi sheyasa annabi yayi gaskiya da yace mai hakuri yana tare da nasara yanzu da kinyi hakuri da duk abinnan bai faru da ke ba abu goma da ashirin duk ke kadai?" Khairy kuka Mama kuka, ya numfasa, "Yanzu ay bamuga ta zama ba tashi zakuyi muje mu fara biyan kudin aikin yaron nan ko ya samu saukin rayuwa, wannan ruwan dake fito masa babu dadin gani, ke kuma idan Sarki sukazo suka kara taimaka mana sai a diba ciki a fara naki treatment din..." ta gyada kai wasu hawayen masu dumi na gangaro mata daga haka Baba ya mike yana fadin, "Bari in dan fita nan waje kafin ku kimtsa ba jimawa xanyi ba." Mama ta masa a dawo lafiya sannan tace "Sai ki tashi ki shirya mu tafi, sannan inaso mu siya maki wannan robar da akesa wa masu yoyon fitsari wannan zaurin da kike yi babu dadi Khairy, sannan shima yaron nan kina daukar shi a jikinki kina sa masa zauri, yanzu ki tashi kije kiyi wanka ki chanza wadannan kayan masu zauri, shima yaron ki chanza masa." da toh ta amsa hawaye masu matukar zafi suna zubo mata, ta yunkura ta mike tana dunkuna zani yadda fitsarin bazai zubo kasa ba ta wuce bandaki, ita kuma Mama ta dauki yaron a hankali ta shiga daki dashi don ta kimtsa shi.

---------

Ranar wata laraba Ashraf ya dawo daga aiki da yamma lis misalin biyar da da rabi, a gajiye ya shigo, daga bakin kofa Zarah ta tare sa sukayi hugging juna kiss ya mata a kumatu kamar yadda ya saba duk sanda ya shigo gidan, hannunsa ta kama ta taimaka masa ya zauna kan kujera, manne masa tayi tare da kwantar da kanta bisa kafadarsa tana mai lumshe idanu tace, "Yanzu wanka zakayi ko abinci zaka fara ci?" yayi murmushi yana jin sonta na kara ruruwa a cikin ransa, yace

"Duk abinda kika ce princess shi zan fara yi?" Tayi dariya tace

"A gaskiya wanka ya kamata ka fara yi saboda zakaji saukin gajiyar da ka kwaso daga nan sai kaci abinci ko?" Yace "Yess! princess hakan za'ayi." A tare suka mike hannunsu sakale cikin na juna. Ta hada masa ruwan wanka sannan ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa, ko wane motsi nata akan idonsa ji yake kamar ya hadiye ta don so, ya sauke ajiyar zuciya yace

"Princess a gaskiya ki daina shagwaba ni da yawa, kinsan irin wannan duk ranar da bakida lafiya ko nayi tafiya zan sha wahala fa..."

Tayi dariiya bayan ta cire masa 

riga tace, "Wannan kuma ay daban ne, kuma ni ka daina cewa ranar da baka nan tou ina zaka je ma?" Yayi murmushi yana kamo hannunta duka biyun, "Kinsan tafiya na iya kamawa ko kuma mutuwa..." Da sauri ta toshe masa baki tace "Ka daina fadan haka, in ma mutuwa ce bana fatan ta riga daukar min kai na fiso ta fara daukata ta." Yayi murmushi

"Ba wanda yasan gawan fari princess, mudai yi addu'a Allah yasa mu cika da imani"

A sanyaye tace "Amin"

A haka ya shiga wanka, ita kuma ta fiddo masa kayan da zai sanya marassa nauyi saboda yanayi ne na zafi. Bayan ya fito ta taimaka masa ya shirya ta fesa masa turare sannan ta kamo hannunsa suka fito parlor. Kan dinning ta zaunar dashi bayan ta zuba masa jollof d'in taliyar data ji kifi da kayan lambu sai lemo mai sanyi. Sai da yaci yayi nat sannan suka koma parlor suna kallo suna fira har aka soma kiran sallar magriba.

----

Ranar wata litinin tafiya ta kama Ashraf zuwa Nigeria Kaduna duk da dai tafiyar daga office d'insu ne bama shi kad'ai zaije ba harda abokan aikinsa su kusan biyar, tun da yake wayar Zarah dake kwance gefensa ke masa wani irin kallo har ta kai ya tsargu, sai da ya gama wayar ne ya juyo yana kallonta yace "Yada kallo haka princess?"

Ta bata rai hade da zumburo pink lips nata masu kara mata kyau tace cikin shagwa6a "Ina zakaje?" Yayi murmushi yace "Wallahi tafiya ce ta kama mu yau d'in nan amma kar ki damu kwana biyar kawai zamuyi mu dawo." Ta juyar da kanta gefe alamun fushi, yayi murmushi tare da kamo ta ya maido bisa jikinsa yace

"Fushi kuma princess? Meyafaru?"

Idanunta suka kawo ruwa tace

"Naji kana zancen tafiya ka barni, kuma kai kanka kasan tunda mukayi aure baka taba tafiya daidai da rana daya ba, sannan kasan ban iya bacci idan baka kusa dani" Take yaji babu dadi saboda shima din ba iyawan zaiyi ba sai dai yazama dole ya tafi saboda aiki ne zai kaishi don haka sai ya rungume ta tare da fara aika mata da sakkonin kisses ta ko ina, itama ta biye masa sun d'auki tsawon lokaci a haka kafin Ashraf ya sauke ajiyar zuciya yace

"Princess wallahi inda kinsan dauriyar da zanyi muje mu dawo da bakiyi magana ba, wallahi zanyi missing dinki sosai, kiyi hakuri kar kice zakiyi kuka don bazan iya jure jin kukanki ba, i love you so much kwana biyar kawai zamuyi mu dawo insha Allah kinji my princess?" Ta kankame shi tace

"I love you more, inshaAllah zan daure har ka dawo amma kasani zanyi kewarka sosai." Yace

"Yes i know princess nima haka."

Daga nan Zarah ta tashi ta hada masa hadaden breakfast, ta shirya masa kayansa kafin ya fito wanka hade da fiddo masa kayan da zai sanya. Tana gamawa itama tayi wanka tasa wata bakar loose top marar hannu da pink dogon skin tight sai ta daura red dan kwali, ta kimtsa ta fito. Dakin Ashraf ta leka a lokacin yana shafa mai, ganinta yasa ya saki murmushi ta mayar masa, karasawa tayi ta taimaka masa ya shirya suka nufi dinning suka karya. Tunda suka fara cin abincin Zarah ke kallonsa kamar zata cinyesa, ya kalleta yace

"Princess?" Ta sadda kanta kasa tana murmushi tace "Na'am?" Yace "Na gama fa sai tafiya yanzu kuma..." Sai kuma ta 6ata rai duniya ba abinda ta tsana taji zatayi nisa da Ashraf dinta, yana ta lura da yanayinta amma sai yayi sauri yace, "Ga wannan." Ya mika mata kudi dubu hamsin yace "Ki rike wannan abinda kike 6ukata kiyi yi amfani dasu har Allah yayi mana dawowa, kuma duk sadda kikaji kadaici ki tafi wurin su Kaka kuma kinga gidan akwa maids ko ina so bakida kadaici." Tana dai ta daurewa bataso tayi kuka amma abu yaci tura sai kawai tasa kuka, take hankalin Ashraf ya tashi ya rude, hugging dinta yayi yana ta aikin lallashi tare da assuring nata cewa kwana biyar dinnan zaiyi ya dawo kuma duk abinda take bukata ya aje mata, sai da ya tabbatar ta bar kukan sannan ya tafi. Bayan tafiyar Ashraf duk gidan gaba d'aya ya mata fadi ba dadi sam, yau batasan ya zatayi bacci ba babu Ashraf a kusa da ita.

Haka ta wuni daga kallo sai chatting, idan ta gaji ta buga game a wayarta ko kuma ta kira Hoodah a nuna mata twins dinta.

Tunda ya isa ya kira ta ya sanar mata sun isa lfy...

------

Mikewa yayi yana kallonta da yar dariya yana kallon kofa, "Tou Khadija tunda nidai yanzu ba'son ganina sai Dr Haiydar sai yayi maki shi." Ko kadan baiji haushi sai ma dadi tinda da taimakon shi akan iya ceto rayuwarta, sunkuyar da kanta tayi tana murmushi irin am sorry dinnan ta kusa minti ashirin a office din Dr Hafiz amma duk maganar da zai mata bata ce masa kala kuma taki sakin jiki dashi yayi mata therapy din yadda suka saba karshe yace mata ko a kira mata Dr Haiydar sai a lokacin ta daga mashi kai alamar eh, sai kuma tayi murmushin jin kunya tana dan girgiza kanta. "Allah ba haka nake nufi ba." A hankali ta furta shi kuwa Dr Hafiz sai yayi dariya yana faman tattara wasu files ya mike ya nufi hanyar kofa, tun ranar da suka yi therapy da Dr Haiydar tou kullum sai ya kira mata shi, "Kila dai daga yanzu zan dinga maki kwatancen office dinsa ba sai kin dinga tashina daga office dina ba..." daga haka ya fita yana murmushi, can Dr Aliyu ya shigo yana kulle office din a hankali saida ya karaso kusa da ita yace, "Khadija kina lafiya?" abinda ya tambaya kenan a hankali ta dago tana kallonsa tana murmushi a hankali, "Alhamdulillah, ina kwana?" Kallonta yake sosai yana murmushi shidai baisan dalili ba amma Khadija tana burge shi kuma sosai ba kadan ba, duk da cewar duk wanda ya kalleta yasan tana tare da tarin damuwa kuma sai kaji kana son taimaka mata da dukkan wani iko da Allah zai baka. Murmushi yayi a hankali yace, "Ina kwana kuma? Ay saidai ina yini don ba dadewa xakiga har sha biyu ta buga," gyada kai tayi alamun ta tuna, "Tou ina jinki Khadija yaya dinki? Ana class din ko kuwa?" Ya tambaya yana kureta da idanu, dagowa tayi da fara'arta alamar zatayi maganar abinda takeso. "Sosai ina jin dadin class din, na manta wayata a gida dana nuna maka wasu pictures." Murmushi yayi inda ya mike yajata zuwa therapy room din daga nan ya fara aiwatar da aikinsa cikin gwaninta da kwarewa, yaji dadi yadda ake samun improvement kuma da alama bazata dade kwarai ba zata samu sauki sosai. Yana cikin aikin ne yace, "Yanzu yaya batun karatu kuma Khadija?" Tace, "Final year nake na kusa gamawa InshaAllah." Yace "Kina zuwa?" Ta gyada masa kai alamun eh, yayi murmushi, "Yanzu da ace Allah xai baki dama ki goge wani abu daga cikin rayuwarki gaba daya Khadija me xaki goge?" Gabanta ya fadi kafin tace, "Abubuwa da yawa Dr, da ina da iko da na goge wani abu da nayi wa yar uwata wanda bazan iya fada maka ba, sannan da ina da iko zan goge ta hanyar da aka bi aka sameni da kuma kaddarar data afka man kwanakin baya, zanso inga mahaifiyata in rayu da ita ta bani mother's love duk da dai ban rasa wannan ba amma dai I still wish zan ga mahaifiyata koda sau daya ne..." zuwa yanzu kuka take kamar ranta zai fita tunda akayi mata fyade takejin rayuwarta ta kare sannan takejin duk wani pain dake ranta ya darsu da abubuwan da suka faru da ita, saida ya barta ta gama kukan kafin ya mika mata hanky, "Sannu ko in baki ruwa?" Ya tambaya yana yin hanyar fridge da sauri ta daga mashi kai disposable cup ya aje mata saida tasha ruwan hankalinta ya dan kwanta kafin shima ya koma ya zauna. "Allah ya jikanta Khadija, sannan komai da kikaga ya faru mukaddari ne daga Allah nima nan da kike gani banida mahaifiya a hannun kishiyar uwa na tashi." Da sauri ta dago tana kallonshi, "Da gaske?" Yayi mata murmushi "kwarai kuwa, tun ina dan shekara biyar ta rasu ta barni hannun matan babana..." take taji ba dadi, "Allah sarki Allah yayi mata rahama." Yace "Ameen." Mikewa yayi bayan ya kammala therapy din yana yar dariya yana kallon wrist watch din hannunshi ganin har lokaci ya kure, "Ya kamata mu tashi haka nan mun bar Mummy tana jiranki a waje..." ta kalleshi, "Da driver muke ita tana wurin aiki." Kamo wheelchair din tata yayi ya fara janta zuwa wajen asibitin, a haka suke tafiya yana bata labarin rayuwarshi, babu abinda ke ciki sai tsantsan tausayi rike kukanta takeyi har sukayi bakwana yasata a mota, tana shiga mota ta saki kukan sosai kuka take kamar an aiko mata da sakon mutuwa, driver din babu abinda yake sai faman bata hakuri yana mata sannu shi ya dauka ma ko ciwo takeji a jikinta. Shiga tayi cikin gida bayan Mama Hauwa ta dora ta saman wheelchair dinta suna tafe tana goge hawaye, kamar daga sama taji ance, "Wai nikam dadin kuka kikeji ne?" A razane ta juyo taga Dr Hafiz zaune bisa daya daga kujerun garden gefensa drink ne da snacks hannunsa da waya yana latsawa, da sauri ta goge hawayenta tana mamakin ganinsa, "Ina yini?" Yayi murmushi "Ina yininki? Tou ya exercise din akwai wahala? Shi wancan likitan haka ake therapy ki dawo gida kina kuka?" Yar dariya ta subuce mata. "Ba ruwansa..." da murmushi saman fuskarshi yace, "Aww haka zakice? Wato karesa ma kikeyi ko a gabana?" Yar kunya ta kamata hakan yasa ta kama keken nata ta karasa kusa da shi fuskarta a sunkuye...

Monday 30 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 46

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 46}



To read all my books click the link below๐Ÿ‘‡๐Ÿป

Maryamsbello.blogspot.com





Da asuba Ashraf  ya farka a hankali ya zare jikinsa daga nata sannan yaje bathroom ya dauro alwalla ya wuce masallaci, dama Zarah taji motsinsa don haka itama sai ta mike ta tafi don yin tata alwallar. Tana gamawa tare da azkhar dinta da addu'ointa ta haye gado ta koma bacci. Sai wurin karfe tara ta farka mamaki tayi yadda ta ganta kwance bisa kirjin Ashraf, saida tayi dubara sannan ta samu ta zare jikinta ta wuce dakinta, brush tayi ta wanke fuskarta sannan ta hau gyaran gida tas ta tsabtacce ko ina ta kunna turaren wuta ta fesa freshner ta kunna ac kafin kace me gidan ya fara bada wani scent mai dadin gaske. Tana gamawa tayi wanka ta shirya cikin wani dinkinta na atamfa doguwar riga tasha stone work sai kamshi ke tashi daga ko wane bangare na jikinta. Tana gamawa ta fada kitchen dama already kafin ta shiga wanka duk ta fera dankali ta yanka albasa da sauransu tana xuwa kawai ta dora wuta kan gas ta cigaba da aikinta a natse. Tana tsakar hada breakfast din tana rera waka in a low tone amma ana jin sautin kadan. "Yaya xanyi in misalta soyayya? Yaya zanyi in fisalta soyayya?.....Itace ba'a siye da kudi duk dukiya... itace mai gida na mulki shine zuciya... ta sanya mai karfi ya sunkuya..... ya zubda hawayen idaniyaaa....." ta dora mai a bisa pan da yayi zafi sai ta saka sausages din suna soyuwa sannan ta cigaba da wakarta.... "idanuna suka jani kafafu sukka ka kaini zuciya tana dauki.... nasan xan kece raini zai zamto ba kamar ni kin kirani angonki... ko nawa aka ce gareni indai har za'a bani xan biya sadakinki.... da zan zamo miji gunki... zan kare dukka hakkinki... in zamo adali a mulkinki.... mai martaba a fadarki..." Ba zato kawai taji an rungumeta ta baya, "Ashe dai idan na biya sadaki zaki kira angonki? Dont mind yanzu ay na riga na biya sadakin tuni har ma kin shigo fadata kuma zan zama adali a mulkinki..." yar dariya yayi ganin yadda ta dan xama shocked alamar batayi expecting dinsa ba. Juyowa tayi tana faman turo baki, "Ni gaskiya ka bani tsoro sannan kuma ban shiga fadarka ba."

Murmushi yayi ya lakuci hancinta, can kuma sai ya bata rai, "Ni ay fushi ma nake dake ko kice ma ya jiki ko?" Da yake kwana biyu yayi fama da ciwon kai marar dadi, ya hade rai gamida bata baya, saurin rungumo shi tayi ta baya ta rike shi gam gam, "Am sorry wallahi I didn't forget, ya jikinka? Kaji sauki ko?" Ta tambaya fuskarta cike da tausayi karara, Ashraf yayi murmushin mugunta ya juyo a hankali tare da tallabo fuskarta yana fadin, "My cry cry baby, kar dai kiyi min kuka kinji? In kina so nayi hakuri sai kin bani hot kiss wanda baki taba yi min irinsa ba a nan..." ya karasa yana nuna bakinsa wanda yake light pink naturally haka yake duk cikin fuskarsa babu abinda ke kara masa kyau kamar bakin nan nasa, Zarah ta zaro idanu waje tare da juya fuskarta cike da kunya, dama ta kwashe komai da sauri ta hada cikin warmers ba tare data sake kallonsa ba ta wuce da sauri dining tana jera kayan, tana ajiye flask din zata juya taje da dauko masu plates da cups kawai tana juyawa sai ganinsa tayi tsaye ya dauko plates din da cups yana faman yi mata murmushi ita kuwa da sauri ta sadda kanta kasa, bama taso ko da hada idanu suyi, kanta kasa ta zo zata wuce ta gabansa kenan taji ya riko mata hannu da sauri ta dago kanta tana kallonsa take yayi mata wink, janye hannun nata tayi da sauri ta wuce kan kujera ta zauna kanta kasa ta fara masu serving abincin, saida ta kammala zuba masu sannan suka fara karyawa a natse. Shi kuwa Ashraf babu abinda yake mata sai magana ita kuwa taki koda kallonsa bare yasa ran zata amsa masa. Kallonta yayi yace, "Tou Zarah nidai zan tafi office mata nacan suna jiran the most handsome man..." ya fada yana dariya kasa kasa ganin yadda take mood dinta ya chanza ta hade fuska kishi bayyane saman fuskarta kafin tace, "Wai wama ya dauke ka wannan aikin? Ni kwatakwata banso Mummy ta samo maka aikin bankin nan ba, yawancin duk mata ne ke sa matsatsun kaya ko kuma ka gansu da dogon wando, ga Christians nan duk sun sha dagaggun skirt duk kafafunsu a waje...." Dariya yayi sannan ya fara bata amsa, "Zarah kenan, ah sosai fa zan rika ganin mata kala kala har sai na darje, gara ki rike Ashraf dinnan fa kar ki bari ya fita yanzu..." Dariya tayi sosai sannan ta dan bigi kafadarsa tana cigaba da dariya. Har ya fita ya dawo yana fadin, "Am joking princess, besides yau ba aiki sai gobe inshaAllah it's a public holiday today remember?" Tayi murmushi tana gyada kai, key din gidan ya bata don yana so ya kulle ta gaba duniyar yanzu ta zama abinda ta zama, "Ga key dinnan karki sake ki bude ma wanda baki sani ba har sai na dawo." Tace "InshaAllah." Har bakin kofa ta raka shi sannan ya bata spare key din ta rufe gidan, tana dawowa ciki ta saka wayarta charge sannan ta gyare dakinsa ta wanke bathroom sai ta dora abincin rana. Saida ta kammala tas  ta zauna parlor ta kunna kallo har bacci yayi gaba da ita.

******

2 WEEKS LATER... 

Yau satin Zarah  biyu da taje ganin gida da kuma duba jikin yar uwarta Khadija, Ashraf ji yake tafi shekara biyu bata tare dashi gaba daya gidan ya masa girma saukinsa ma yana zuwa aiki kuma kullum suna waya da chatting. Ranar da tayi shirin dawowa tayi niyyar bashi surprise kasancewar yau Tuesday ta kama tasan definitely yana office, saida ta wuce gida ta sauke boxes dinta tas sannan ta kullo gidan ta dauki hanyar bankinsu Ashraf, koda ta shigo sai ta iske wayam office dinsa babu kowa nan suke sanar mata ay sun fita shida manager din bankin sun tafi wani branch din, xama tayi kan kujera tana bin office din da kallo yadda ya kawatu duk da ba yau bane ta fara zuwa amma sai taga duk ya chanza mata lallai central bank ta hadu, bisa table din hotonsu ne na biki ansa cikin frame ya aje shi a tsakiyar table din, gefe kuma wasu files ne wanda basu kai ashirin ba, sai laptop dinsa dake ajiye a gefe kwatakwata dai office din very simple yet classy, ac duk ta cika wurin ga kamshi na musamman na tashi, murmushi tayi a cikin ranta ta kagara ya dawo, tana cikin wannan tunanin ne kawai taji alamun shigowarsa, tana juyawa ta ganshi tsaye idanunsa waje bakinsa bude yana kallonta itama cike da murna ta daka wani uban tsalle wane karamar yarinya taje ta rungume shi, shi farin ciki ma ya hana shi magana, fuskarsa cike da murna hade da mamaki, kara rungumota yayi yana rufe kofar office din nasa da kafa, "Oh my princess is back, ya Allah am so happy I really miss you princess." Ya fada yana juyi da ita tsakiyar office din ita kuwa sai dariya takeyi tana kara makalkale shi, "Meyasa baki fada man yau zaki dawo ba princess? Ko duk missing din nawa ne yasa bazaki iya kirana ba? Da ba sai inje airport in dauko ki ba?" Tayi dariya, "I wanted to surprise you ne fa,  kuma ni na kosa na ganka bazan iya jira har sai kazo ba, mu tafi gida ko baka tashi ba?" Dariya yayi ya aje file din da ya dawo dashi saman table sannan ya dauko key din motarsa, hannayensu rike cikin na juna ko wanenensu fuskarsa dauke da farin ciki sai binsu ake kallo cike da sha'awa, "Kasan yadda nakeji kuwa da na tafi? Ji nake kamar zuciyata zata fashe tsabar yadda nayi kewarka." Yayi dariya tare da rungumota ta gefe, yace "Wai ya naga kin kara kyau da haske ne? Kodai wayau kikayi man kika tafi can Mummy ta dinga baki kayan dadi kina ci ke kadai a can?" Shi ya fara bude mata motar ta shiga sannan ya zaga ta side dinsa ya shiga shima tana ta dariya tana girgiza kai kafin a hankali taji saukar lips dinsa a goshinta, kunna motar yayi ya fita da reverse, saida ya hau titi ya juyo yaga ta langa6e kan kujera idanunta na rufewa sama sama ga gajiya nan bayyane saman fuskarta da kasala. "Anya Zarah? Dama na lura tun kafin ki tafi kike wannan yawan kasalar, yanzu kuma jirgi fa kika hau balle ace gajiyar hanya ce." Idanu ta bude waje da sauri ta mike tana auna maganganusa, ganin yanayinta yasa ya kyalkale da dariya yace, "Wasa nakeyi koma kiyi baccinki rankishi dade." Daga haka ya cigaba da driving dinsa can taga ya tsaya pharmacy bai jima ba ya dawo wanda batasan meya siyo ba, daga nan kuma taga ya tsaya kfc ta dago tana kallonsa, "Na dauka gida xamuje inyi wanka in chanza kaya?" Yayi murmushi "Bari na siya mana abinci tunda nasan bazaki iya mana girki ba ganin yanayinki a halin yanzu..." yana gama fadan haka ya fita daga motar yana dariya itama ta fito, family size ya siya masu da chips sai katuwar coke. A haka suka dawo gida yana driving da hannu daya dayan kuma ya rike ma Zarah hannu dashi. Bayan sun fito a mota ta tayashi daukar kayan suka shiga ciki, tayi mamakin ganin gidan tsab don ita dazu ma ko lura batayi ba ajiye kayanta kawai tayi ta fito, gidan babu datti ko guda daya kitchen dinnma haka ba karamin mamaki tayi ba, batayi zaton haka zata iske gidan ba. Tana zaune kan gado daga ita sai karamin towel tana kokarin warware kanta, rabon data data gyara kan tun kafin tayi tafiya duk ya curkude wurin daya, shigowa yayi ya aje ledar kan side drawer kafin ya zauna gefenta yana kama gashin nata yana tayata kwance inda ta kitse shi, "Wai meyasa bakyason yin kitso ne Fatima? Gashi kullum sai ya wahalar dake, dama ance duk masu gashi basu san ta6a gashinsu tou gashi nan na tabbatar dai a kanki." Dariya tayi tana tayashi warware kan nata, "Ni banma san yadda xanyi ba tunda na tafi ko ta6ashi banyi ba, Ashraf kasan yau sai nayi ciwon kai tsabar wahalar da zansha." Lumshe idanu yayi a hankali kafin ya bude, "Tou ko a wanke kan yau? Dama kin dada baki wanke shi ba nasan bazaiyi zafi ba idan har na wanke maki da kaina?" Dariya tayi tana kwantawa saman gadon tana kallon kyakkyawar fuskarsa tana murmushi. "A'a kabari sai gobe don nagaji sosai, kaji yadda nakejin bacci kuwa? Yanzu ma wanka nakeso in shiga sai in kwanta..." ledar daya aje ya jawo ya rike a hannunsa kamar za'a kwace masa ita, "Wai meye a cikin ledar nan kake ta faman rike shi kamar ranka?" Ita da wasa ta fada amma shi har ransa yaji, gyara zama yayi yana faman dagata saura kadan towel din ya fadi tayi saurin riko shi gam, "Ashraf!" Yanda ta rude sai abun ya bashi dariya, mika mata ledar yayi, ta bude nan taga PT strip ne da sauri ta dago tana kallonshi, "Wannan fa? Ba shi bane ka siyo kafin inyi tafiya muka gwada mukaga negative? So kake yanzu ma in sake gwadawa in kara ganin wata negative din ko? Kuma ranar duk ka nuna damuwarka da ya nuna negative har kwalla nayi ranar da daddare..." jawota yayi ya rungume ta a jikinsa yana kissing gashinta daya baje bisa bayanta, "I know princess, kawai mu sake gwadawa, I promised you in babu bazan sake gwadawa ba har sai ya fito da kansa cikin," gyada kayi tayi alamun eh sannan ta tashi ta shiga bathroom sai da abun yayi reading sannan ta fito ta dora shi bisa drawer ta bar wurin da sauri she don't want be disappointed again kuma. Tashi yayi bayan minti biyar ya leka abin ya dago mata shi, nan ya jawota ta fasa ihu hade da runtse idanu gabanta na faduwa, "Menene?" Da wani irin murmushi yake kallonta yana kara rungumeta, kissing fuskarta ya fara yi cike da farin ciki kafin yace, "Thank you so much Zarah! It's positive Alhamdulillah!" Rumgume shi tayi tana hawaye she can't believe wai zata haifi gudan jinin Ashraf Allah mai iko. Kara rungumeta yayi yace "I love you so much Zarah, kin biya ni yau am so happy, so so happy! Am the happiest man right now Zarah, zaki haifa man jinina! Ina sonki Zarah kinji?" Hawaye suka kara shatata daga idanunta ta rungume shi gam gam tana jin yadda farin ciki ke sauka saman zuciyarta...

--------

FEW WEEKS LATER!

Sintiri kawai yake yi a bakin kofar labour room din, Ashraf da Zarah ma ko wane cike da damuwa ji take kamar ta shiga taga meke faruwa a ciki, Ashraf kuwa damuwar data bayyana a fuskarsa yama kasa koda magana ne, sarki Sultan kasa shiga dakin labour room din yayi ba yadda ba'ayi dashi ba akan ya shiga amma fir yaki don gani yake yana shiga za'a ce mashi ta mutu amma shi kansa ya tabbatar da cewar Hoodah na mutuwa tou shima babu abinda zai hanasa ya bita. An fi minti talatin can wata Doctor ta fito duk ta hada xufa fuskarka dauke da damuwa, "Your wife's life is in danger your highness, don a halin yanzu ta kasa haihuwa da kanta kuma babu abinda takeyi sai kuka tace ka shigo ka tsaya gefenta, sannan maybe we have to save one of them ko uwar ko dan." Da wani irin expression yake kallon likitan, "What are you saying to me Doctor?" Ya fada yana goge idanunsa da hawaye ke zubo masu, suma kansu su Ashraf ko wane ya zama speechless hankalinsu tashe, gasu Ummi da isowarsu kenan suka tsaya cike da shock suna kallon doctorn, Doctor din ta sauke ajiyar zuciya, "Bance ko bazata haihu lafiya ba amma dai  ina nufin rayuwarta na cikin hadari kudai tayata addu'a." Tana fadan haka ta kalli Sultan, "Wa kake da bukatar muyi saving the mother or the baby?" Kasa tsayuwa Sultan yayi nan ya fada kan kujerun da ke ajiye a nan Ashraf yayi saurin rike sa, sai ya fashe da kuka kamar karamin yaro, "Ya zakiyi min wannan tambayar doctor? You know I love my wife more than life itself, I also love my child wanda ban riga na gansa ba, but If I am to choose I will have to choose my wife over and over again, so yes Doctor save my wife first!" Ya fada cike da karfin hali kafin ya rungume Ummi yana cigaba da kuka, Zarah kasa daurewa tayi ta fita da sauri ta nufi bathroom ta dauro alwalla, ta tafi masallacin asibitin ta fara sallah tana rokon Allah yayi saving dukansu gaba daya. Nan Doctor din ta wuce ciki ta barsu cikin wani irin mawuyacin hali. Ummi ta dafa Sultan, "You did the right thing son Allah zai baku wani InshaAllah." Ya gyada kai cikin karfin hali yana goge hawaye. A hankali suke jiyo kukan jarirai har guda biyu a tare gaba dayansu suka sauke ajiyar zuciya cike da mamaki, Sultan zubewa kasa yayi yana ma Allah godiya daidai nan Zarah ta shigo da saurin jin sautin kukan babies na tashi, batasan sadda ta rungume Ummi ba tana hamdala. Bayan mintina kadan sai ga Doctor din ta sake fitowa fuskarta dauke da murmushi, "Congratulations your highness, it's twins! Matarka da yaranka suna nan cikin koshin lafiya!" Ay bata karasa magana ba Sultan ya mike da hanzari yayi hanyar dakin. Ita kuwa Ummi da Zarah kara rungume juna suke yi suna dariya kamar wasu kananan yara. Iyakar wahala tasha ta, hannunta ne taji a cikin nashi basai ta bude ido ba ta tabbatar da Sultan ne, nan ta bude idonta a hankali tana saukewa bisa fuskarsa wacce ta sauya kala tayi jajir sannan ga farin ciki nan saman fuskarsa, zama yayi gefenta yana kara kamo hannunta yana sauke mata kiss a hankali, Hoodah ta goge hawayen farin ciki ta mike zaune da kyar tana kallonsa, "Congratulations my king a boy and a girl..." ya kalleta yana juya kansa don neman babies din tayi murmushi, "An tafi dasu for general checkup." Ya gyada kai sannan yace, "Kin tuna alkawarinmu?" Ta gyada kai "And we both won!" Bata karasa magana ba ya hade lips dinsu wuri daya sun dade a haka kafin ya janye a hankali ta sadda kanta kasa, shigowa nurse din tayi hannunta dauke da jariran biyu ko wane an kimtsa shi tsab sai dan motsi sukeyi sunata baccinsu a natse, a hankali ya mike ya isa inda suke ya tsaya yana kallonsu kamar wani statue ya tsura masu idanu sosai idanunsa na kawo ruwa. Amsar su yayi take ya lumshe idanu yana jin son yaran na fizgarsa, kisses yake aika masu ko ta ina a fuska kafin ya taka inda Hoodah ke kwance ya zauna gefenta, duka su biyun ya daura mata bisa cinya sai a lokacin ta saki hawayen da take rikewa, shafa fuskarta yayi yana goge mata hawayen, yace "Banida bakin da zan gode maki kin bani kyauta ta musamman, Alhamdulillah na gode ma Allah da ya bani wannan gagarumar kyauta wanda ba kowa yake bamawa ba, yau da ace na rasa ki Hoodah de sai dai na biki nasan take zuciyata zata buga nima in mutu..." da sauri ta toshe masa baki da hannunta, rike hannun yayi ya rungume sannan ya mike ya fita ya kaiwa su Ummi yaran. Bai jima kwarai ba ya dawo ya zauna gefenta tare da rungume  ta a jikinsa, "Ina fatan banyi katsalandan ba don inaso ki bani izini na maida sunan mahaifiyarki a macen..." da sauri ta kalle shi speechless toshe bakinta tayi kawai sai ji yayi ta makalkale shi tare da fashewa da wani irin kuka, "Thank you so much for this Sultan, Allah ya biya maka bukatunka na alkhairi." Wani irin kiss ya kai mata a goshi, "No need my queen you deserve the best..." a haka ta dora kanta bisa kirjinsa har bacci yayi awon gaba da ita, Sultan hannunsa ya dora bisa kan nata yana shafa gashinta a hankali yana lumshe idanu...

Saturday 28 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 45

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 45)


To read all my books click the link below๐Ÿ‘‡๐Ÿป

Maryamsbello.blogspot.com




Bayan Mummy ta kammala bata abinci kamar kullum sai ta mike ta nufi kitchen kafin Mama Hauwa tazo ta tattara kitchen din, ita dai Khadija tabita da kallo har ta dawo hannunta dauke da cup da ledar maganinta, dawowarsu kenan daga therapy har yau Mummy bata sake mata kuma hakan ba karamin damun Khadija yake ba gaba daya ta rasa meke mata dadi, zama Mummy tayi kan kujera ta ballo mata duka magungunan nata ta zo bata kenan Khadija tasa hannunta mai Lafiyar ta rike ma Mummy hannu idanunta na kawo ruwa, girgiza kai Khadija keyi sannan ta fashe da kuka sosai kuka take kamar ranta zai fita, saida kukan ya tsaigata sannan ta dubi Mummy da itama idanunta cike da hawaye tace, "Nasan banida isassun kalmomin da suka dace inyi amfani dasu wajen baki hakuri Mummy, fushin nan da kikeyi sam banga laifinki ba saboda ya dace ma kiyi fiye da haka, na butulce ki upon irin kaunar da kika nuna min da soyayyar ki a gareni sai gashi abinda na saka maki dashi kenan..." hawayen ta share kafin ta cije lebe wasu na kuma taruwa a idanunta, "Kamar yadda nace fushin da kikeyi ya dace dani amma kuma bazan iya jurewa ba Mummy, sam bana jin dadin yadda kike treating dina saboda na saba da care dinki na saba da kulawarki, na saba da kaunarki wallahi zuciyata bazata iya dauka ba Mummy don Allah ba don halina ba kiyi hakuri ki yafe man koda na samu nutsuwa a cikin raina..." ta karasa cikin tsananin kuka, Mummy ta share hawayen fusakarta ta mika mata maganin bayan ta sha sai kawai ta mike ta kai cup din kitchen tazo tabi ta gaban Khadija zata wuce kawai sai Khadija tayi sauri ta damko mata hannu gam, Mummy ta juyo tana faman goge hawaye kafin ta janye hannun nata a hankali tayi hanyar sama, dama Khadija ta dauko wata yar karamar wuka, Mummy har ta kusa hayewa sai Khadija ta saita wukar daidai wuyanta tana kuka tace, "Fine! Tunda bazaki yafe mun ban banga sauran amfanina ba a duniya, Mummy you're my whole world, don haka barina duniya shine yafi alkhairi...." Cak Mummy ta tsaya gamida juyowa da sauri idanu ta zaro waje kafin ta juyo Khadija ta fara kokarin caka maka kanta wukar nan, aiko Mummy tana isowa ta warce wukar a tsorace tana kallon Khadija cike da shock, durkusawa Mummy tayi har wata kyarma takeyi tace "Khadija meye haka? Are you mad? Mekike shirin aikatawa?" Khadija tayi murmushi, "Dama nasan har yanzu kina sona Munmy, why are you pretending?" Mummy ta juya fuskarta gefe kafin tace, "Saboda kin aikata babban laifi a gareni! Na saki a inuwa sai kika tunkuda ni rana Khadija you betrayed me, meye namiji? Da har zaki cuci yar uwarki akansa? Haba Khadija!" Khadija Ta girgiza kai cike da karfin hali tace, "Nasani, amma yanzu na gane kuskurena, don Allah don annabi ki yafe mun, ni mai laifi ce na kuma amsa laifina, ki yafe man Mummy." Mummy ta rungumeta a hankali, "It's okay Khadija na yafe maki, ya wuce kinji? Koda wasa kar ki sake aikata makamancin haka kina jina?" Da sauri ta girgiza kai cikin kuka tace, "Never Mummy InshaAllah." 

---------

2 WEEKS LATER...

A hankali Mummy ke tura ta a bisa wheelchair har sai da suka tsaya daidai office din Dr Hafiz, Mummy ta gyara mata wheelchair din yadda zata iya tura kanta don wani botton ne kawai zata danna keken ya fara tafiya, sannan ta dan sunkuyo tana murmushi, "As always ki shiga zan jiraki a inda na saba jiranki kinji ko?" Ta gyada kai sannan Mummy ta juya ta fara tafiya, ita kuma tasa hannu ta fara knocking kofar a hankali, ji tayi ance mata "come in." tasa hannu ta bude kofar ta fara tura kanta a ciki, saida ta isa daidai table din office din sannan ta tago tana kare masa kallo, a dan tsorace ta fara kokarin tura keken nata zata fita dan ita a tunaninta ma ba office dinsa ta shigo ba saidai kuma data sake bin office din kallo tsab sai taga lallai office din nasa ne komai yana nan a yadda ta saba gani, daidaita kanta tayi sannan tace "Salam? Good morning?" Ta furta a hankali tana kallon bakuwar fuskar data tsareta da idanu, "Wslm, morning too, Khadija ko? don ya sanar dani ke kadai ce yakeda appointment dake yau ko?" A hankali ta gyada masa kai tana kallon kasa, "Ina yake?" Ta tambaya tana kara kallon kofa koda zataga Dr Hafiz din ya shigo, "Wani emergency yake attending to so bazai samu damar ganinki ba a halin yanzu, sunana Dr Aliyu yau ni ne zan maki therapy." Kafin ya mata bayani har tanada niyyar juyawa ta fita sai kuma ta dakata tana saurarensa, tana tunanin yau Allah ya hadata da mai surutu, a hankali ya mike yana murmushi ya kamo keken nata sannan ya shiga janta zuwa wata yar kofa inda zata sadaka da therapy room din. Duk wani abu da ya kamata Dr Hafiz yayi mata Dr Aliyu yayi har ma fiye, har ma cikin aikin nasa ya kan tsaya yana mata yar hira ko tambayoyi don ma ya dauke mata hankali daga pain din da takeji a jikinta, hannun nata yake massaging a hankali cikin kwarewa, ganin tana dan cije lips dinta sai ya dakata yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi yace, "Khadija yanzu what do want to do with your life? Kinga kamar ni kullum karatun likitanci baya kare min, kullum cikin research nake amma still ina samun lokaci inyi karance karancen novels da poems, and also ina da babban shop a nan garin ina siyar da kayan maza kamar su shadda, jallabiya, shoes, hula everything da kika sani na maza ina dasu, ke me kikeso kiyi?" Ya tambaya yana cigaba da mata therapy din, dan murmushi tayi mai cike da hawaye sai tace, "Koda ina so amma a halin yanzu bazan iya yi ba saboda condition dina..." Shiru yayi yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya, yace, "No Khadija don't say that, you can do it kar ki sake bari lalurarki ta hanaki purchasing dreams dinki," tun tana yarinya babu abinda takeso kamar fashion and design especially idan ya zamana tana designing kayan da kanta tana zanawa, saidai tunda wannan abin ya faru da ita taji komai ya fice mata a kai, murmushi tayi ya taimaka mata ta tashi zaune a hankali tana sunna kai, "Ina son fashion and design especially a harkar designing kaya bawai a dinka min ba a'a na dinga dinkawa da kaina kuma ina designing, I so much love it." Murmushi yayi ganin ya samu hanyar da zai taimaka mata yace, "Tou yanzu Khadija idan aka baki paper da pen zaki iya farawa? Kuma kin iya ko kuwa kina bukatar training?" Da murmushi mai gaggawa ta daga mashi kai, a hankali yayi lifting rigarta zuwa cinyarta ya tsugunna daidai kafar ya fara mata massaging kafar, sannan ya jawo wani machine mai kamar bicycle ya dora mata kafar ta fara exercise din kafin tace, "Zanyi sosai, akwai abubuwa da yawa wanda bayan fashion and design zan iya mantawa dashi, nidai for me wannan ne kadai ke sani farin ciki I think it's the best gift, my opinion though." Mamakin kanta ma take yaushe rabon da tayi magana har haka? Balle ma ta tsaya dogon bayani, cike da salo da dubara ya cigaba da mata massage dinnan har saida ya kasance sam bataji wani wahala ba kamar yadda take ji a wurin Dr Hafiz sai taji yau salon nasa na daban ne, nan ya gama lura da ita akan cewar fa da gaske take har kasan ranta tana son fashion and design, bayan ya gama sai ta daga waya ta kira Mummy, Mummyn tace, "Ina kika yadar wayarki ina ta faman kiranki baki dauka ba?" Khadija ta duba wayar cike da mamaki tace "Wallahi Mummy ban ji ba kiyi hakuri." Mummy tace "Bakomai, dama ince maki wallahi wani emergency meeting ne manager din company dinmu ya kirani wai yana son ganina da gaggawa, tou ga Audu driver nan na kirashi yace min zaizo ya dauke ki, nace wa Mama Hauwa ta bashi key din dayar motar tawa zaizo ya dauke ki kinji? Ki samu nurses sai su taimaka maki ki shiga mota, am truly sorry daughter." Khadija ta marairace tace, "Ok Mummy bari in kira Audun yanzu." Mummy "Ok tou, sai na dawo take care kinji?" Khadija tace "Thank you." Sannan ta katse wayar ta shiga kiran number din Audu kamar da wasa taki shiga, ta dago kamar zatayi kuka tace "Number driver dinmu taki shiga, kuma Mummy ta tafi wani meeting." Dr Aliyu yace, "Tou yanzu ya za'ayi kenan Khadija?" Tace "Ko in dan kara jira nasan zaizo tunda Mummy tace tayi magana dashi." Yayi ajiyar zuciya, "It's ok, am sorry Khadija na shafa'a ko ruwa ban kawo miki ba." Tayi murmushi "Ba damuwa ay bana jin kishirwa." Zama yayi a gabanta yana binta da kallo kafin yace, "Tou malama Khadija baki fada man sunanki ba?" Da wani yanayi take kallonsa irin ba yanzu ka gama kiran sunana ba? Amma sai ta dake tayi murmushi tace, "Sunana Khadija." Ya girgiza kai, "Ni kinga sunana Aliyu Haiydar Mahmud, ke meye sunanki?"da kyar ta kakalo murmushi kafin tace "Sunana Khadija Hamza." Bata jira cewarshi ba ta juya kan wheelchair dinta ta fita daga office din, dan fadan sunanta ya taso mata da dukkanin damuwar da take kokarin dannewa. Saidai kuma idan ta tuno da abinda takeso a rayuwa wato fashion and design sai taji sanyi a ranta, tana hango kanta a matsayin fashionista sai ta saki dan karamin murmushi har ta isa harabar asibitin bisa yar verandar a waje a nan ta tsaya, bata kai minti biyar a zaune ba sai kawai taga mutum tsaye a kanta ta dago tana kallonsa amma da alama baisan abinda zai fada mata ba, can yayi yar dariya cike da zolaya kamar yadda ya saba yi mata yace, "Kece?" Ya tambaya kamar wani sakarai yana kokarin danne dariyarsa, hade fuska tayi tamau "Nice wa?" Ya hade hannu waje daya, "Sorry malama Mummy ta kirani akan nazo na dauke ki, so dana zo naga kin tasani a gaba da kallo so I thought bake bace bama." Ta kara hade rai, "Am sorry Doctor but ni ba inda xan bika saboda Mummy tace man driver ta aiko ba kai ba." Yayi yar dariya gamida zaro wayarsa aljihu yana adjusting glass dinsa, ya dadanna wayar kafin ya sa a speaker, Mummy ce ta daga, "Hello Mummy ina wuni?" Mummy tace "Lafiya lau Dr Hafiz, har ka ganta?" Yace "Eh naganta Mummy gamu nan tare gida zan kaita ko?" Tace "Eh, amma don Allah kayi hakuri doctor na taso ka aiki nace ka maidata, wallahi babu yadda zanyi ne na kasa samun driver dina don na kirashi yace man zaije har dai na gaji da jira ashe shi baima je gidan ba, sheyasa na kiraka am sorry to disturb your work." Yayi murmushi yana tsareta da idanu, "Mummy bakomai ay yanxu mun zama daya karki damu.... yauwa thank you." Daga haka ya katse wayar yana kallon Khadija wacce tunda ya fara wayar take binshi da kallo cike da mamaki, wai me yake nufi? Shi zai kaini gida kenan? Da guntun murmushi a fuskarsa ya kamo wheelchair din tata ya fara janta a hankali, "Tou malama Khadija yanzu kin yarda xaki bini kenan?" Gyada kai tayi kawai har suka isa inda ya paka motarsa ya bude gaba ya taimaka mata ya sata motar sannan ya nade kaken ya sashi booth ya zaga side dinshi ya rufe motar har yanzu fuskarshi murmushi yakeyi, bayan ya harba titi saida tafiyar tayi nisa sannan yayi magana amma can kasan makoshi, "Are you hungry? Zan tsaya restaurant na karbi abinci." Juyowa tayi taga yana magana sannan ta girgiza kai a hankali, "A'a thank you." Daga haka suka cigaba da tafiya, can sai kuma taga sun shiga gidan mai, suna nan tsaye ana zuba masu man sai ya juyo yaga idanun Khadija sunyi rau rau, da mamaki yace "Khadija lafiya?" Da sauri ta share hawayenta batasan lokacin da tace "Don Allah ka ara man kudin in ba matar can." Bata taba tambayar namiji abu ba yau ta tsinci kanta da hakan, don ko bakada imani matar sai ta baka tausayi, ta window ya dan leke ya kalli matar yaga tana kallonsu take ta bashi mugun tausayi, yasa hannu aljihu ko tsayawa kirgawa baiyi ba ya mika ma Khadija, bude motar tayi tana shafar fuskar yaron sannan ta mika ma matar kudin, "Gashi nasan ba lallai bane suyi maki maganin matsalarki amma ina rokon Allah yayi maki maganin duk wata damuwar da kike ciki ya yaye maki alfarmar annabi (SAW)." Matar babu abinda takeyi sai godiya ta sa6i yaronta wanda daga gani baida lafiya ta goya shi tana goge hawaye, bata tsammaci samun kudi koda rabin haka bane a yau, tayi masu sallama gamida godiya marar adadi sannan ta juya ta cigaba da tafiya, kofar motar ta rufe tana bin matar da kallo cike da tausayawa, daga nan Dr Hafiz yayi payment sannan suka cigaba da tafiya. Saida yayi yar tafiya kadan sannan ta juyo tana murmushi, "Nagode sosai, idan muka je gida zan mayar maka." Murmushi yayi mata ganin yadda take kokarin maida hawayenta ita ta rasa yaushe ta zama mai tausayi haka sosai? "tou ay ni kaina bansan ko nawa bane saidai ki maida man da wani abin amma ba kudi ba." Kallonsa tayi tana auna maganarshi kafin tace "Ay ba kudi zaka bani ba, amma dai me kakeso?" Lokacin ne yayi daidai da zubar hawayenta, dan jim yayi yana kallonta kafin yace, "Yanzu a bar maganar bashin nan Khadija, first of all ki goge hawayenki." Batayi masa musu ba tasa hannunta mai lafiyar tana ta faman goge hawayen amma kamar ana kara tunkudo su. Har suka isa bakin restaurant din Khadija na kuka saida ya kashe motar kafin ya juyo yana dubanta gaba daya jikinta rawa yakeyi, hanky ya ciro daga aljihunsa ya mika mata, saida tayi kamar bazata karba ba sai kuma ta amsa ta fara share hawayenta, gaba daya tausayi take bashi ko ba'a fada ba yasan tana cikin kunci da bakin ciki, yasan ba ganin almajirar nan kadai yasa ta kuka ba, dama dai akwai abubuwa cunkushe a cikin zuciyarta, tabbas kukan nan nata yanada nasaba da mummunar kaddarar data afka maka kwanakin baya amma bawai don an mata fyaden kadai take kuka ba akwai connection gameda fyaden. Saida ta gama share hawayen sannan ta mika masa maimakon ya amsa sai ya dauko bottle water dake ajiye gefensa ya mika mata, "Wash your face Khadija, kar mu shiga cikin mutane suyi tunanin sato ki nayi ko kuma cutar dake zanyi." Khadija batasan lokacin data maka masa wata uwar harara ba, (ashe ma satowa) ta fada cikin ranta, dariya ya fashe da ita, "Ashe dama kin iya masifa? Irin wannan harara haka ay sai kisa tari ya sarke ni!" Bata tanka sa ba ta karbi ruwan ta bude kofar motar ta wanke fuskarka yana zuba mata har tagama, juyowa tayi bayan ta mika masa murfin kwalbar tace, "Thank you." Haka kawai sai ta fara dana sanin kukan da tayi a gabansa ta fara tunanin kar ya fara raina mata wayau ko kuma makamancin haka. Amma duk da haka bayan tayi kukan sai takejin ranta yayi sanyi zuciyarta tayi mata wasai, tana Kallonsa ya bude motar ya fita ya zagayo ya dauko wheelchair dinta sannan ya gurgurota a gabanta, "Muje ko? Bari na taimaka maki." Da sauri ta girgiza kai, "Ay da ka barni a nan ka tafi ka karbo ni zan zauna a mota." Ta mirror take kallon kanta yadda kwayar idanunta ta kada tayi jajir, sannan ita sam bataso a ganta akan wheelchair tazo restaurant, "A'a baza'ayi haka ba Khadija, ya kamata kizo muje tare nasan bakici komai ba, kuma nasan halinki sarai yadda Mummy ke fama dake akan abinci kullum, yanzu kuma ga kukan da kika sha in ba so kike abu biyu ya hade maki ba ga damuwa ga yunwa su karasa rayuwarki gaba daya." Da kamar bazata je ba can kuma ta gyada kai da haka yayi mata murmushi sannan ya taimaka mata ta hau kan wheelchair din kafin ya rufe motar, a hankali yake janta as if idan ya tura ta da karfi zataji zafi, wuri ya sama masu kusada window suka zauna kafin ya bada order abinda zasuci dan yasan ko ya tambeyeta ba lallai bane ta fada masa abinda takeso, shiru duk sukayi alamu sun nuna Khadija ta koma duniyar tunani, dan snapping finger dinsa yayi yana daga mata kai, "Hello what happened?" Da sauri ta girgiza kai tana kakalo murmushi, "Bakomai am fine." Ya tsareta da idanu, "Are you sure?" Ta sake girgiza kai da sauri, "Am sure." Suna nan aka kawo masu order dinsu, jollof din shinkafa da half chicken sai salad, saida suka gama cin abincin ya biya sannan yajata suka tafi mota, bayan sun shiga Dr Hafiz ya juyo yana kallonta, "Dr Haiydar yace man kina son fashion and design, kina son na siya maki keken dinki?" Bata san lokacin data daga kai ba tace eh, sai can kuma ta tuna me tayi, ya za'ayi ta bari Dr Hafiz ya siya mata keken dinki? After all bada paper ake siya ba, da sauri tace, "What i mean is inaso, amma bawai aje a siya ba...." dariya kawai Dr Hafiz ya fara yi, "Karki damu zan siya maki, I will make sure nayi maki dukkanin abinda na san zai saki farin ciki Khadija..."  da sauri Khadija ta girgiza kai, "A'a don Allah kar ka siya, kai kasan bazan iya dinki ba and I also need proper training." Yayi murmushi "Tunda na hadu dake Khadija ban taba ganin farin cikinki ba sai da Dr Haiydar yayi man expressing how happy you are, and I promise myself am going to make you happy no matter what Khadija, you don't need to start using it now if you don't want to, xaki iya aje shi har sadda kikeso kinji ko?" Ya karasa yana mata murmushi sosai, gyada kai tayi cike da farin ciki marar iyaka, kafin su wuce inda zai siyo mata keken kamar yadda yayi mata alkawari, aikuwa haka akayi keke ya siya mata har guda biyu yayi making payment da komai ba tare da ya tsaya jin tsadar su ba bai ma damu da wata tsada ba shidai burinshi kawai yasa Khadija farin ciki wanda yasan cewar her happiness lies in his happiness, he don't know how it happened but all abunda ya sani shine ya kamu da kaunar Khadija kuma kauna bata wasa ba, sai daya ya gama ya biya motar da zata daukar masu har gida suma ya biyasu kudin dauka, sannan yaja ta mota babu abinda Khadija keyi sai share hawayen farin ciki, daidai harabar gidansu yayi parking yana kallonta, "Zan maki registration inda zakiyi training dinki na cikar burinki." Tayi murmushi, "Dr banida bakin da zan gode maka akan abinda kayi nagode sosai sosai, registration dinma na gode." Hanky dinsa wanda ke hannunta da ya bata dazu ta share hawayenta ta dalilin kuka da tayi ta mika masa, kin karbar hanky din yayi yace, "Shi hanky din kyauta na baki, duk sadda kikayi kuka zaki shiga mutane sai ki goge hawayenki dashi, amma da bashina na dazu da kudin registration wata rana zance ki biyani." Ya karasa yana sakar mata wani irin kayattacen murmushi, itama murmushin ta mayar masa kafin ya zagayo ya bude mata ya taimaka mata ta hau kekent, Mama Hauwa ce ta fito ta jata ciki, nan kuma yasa mai gadi ya shigar mata kekenta duka biyun cikin gida, bakin motar ya tsaya yana kallonta har saida suka shiga ciki kafin a hankali ya juya ya shiga motarsa ya tada ya bar gidan....

-------

Kusan rabin jikinta a nashi yake wai kuma a haka kallo take, robar ice cream ce a hannunsa yana bata a hankali duk da ya hanata shan abu mai sanyi amma akan ice cream sai su tada gari ta dinga mishi kuka kenan indai bata sha ba, wani lokaci da gangan zai ki bata ice cream din sai ta juyo ta kalleshi sai ya dan sunkuyo yayi mata peck a kumatu kafin ya sake bata tasha. Zuwa yanzu soyayyar da Gimbiya Hoodah ke wa Sultan ta kara linkuwa kan wacce take masa a da har ma ji take duk soyayyar da tayi masa ba komai bace compared to yanzu da take jinsa har can kasan ranta, daga karshe ma ta kwantar da kanta saman kafafunsa tana kallon fuskarsa dauke da kyakkyawan murmushi tace, "Ka gaji ko?" Aje ice cream din yayi kan center table din parlon yana kallonta, "Abba fa yazo na fada maki kuwa?" Da sauri ta kalleshi, "Abbana? Shine ko ka fada man inje in gaishe shi?" Yayi yar dariya, "Bai iso da wuri bane shine ma yayi min umarni akan kar na fada maki sai gobe da safe, amma yace da kinji sakonsa da safe ki garzaya wurinsa don yayi kewarki da yawa." Wani irin dadin murna ta fara yi wane an mata albishir da gidan aljanna shi kuwa Sultan kallonta ya tsaya yi fuskarsa cike da annuri. Sai kuma ya bata fuska, "Nifa gaskiya Hoodah ina da complain, an jima rabon da kice man I love you..." ya kara tsuke fuska, tayi dariya, "La abinda ka tsiro dashi yau kuma kenan? Tou shikenan kayi hakuri kaji?" Ya kara bata rai, "Aww tsurowa ma nayi kenan? Wato kin daina sona ma kenan ko?" Ta fashe da dariya sosai, kara tsuke fuska yayi yana kokarin dagata daga jikinsa ta makalkale shi, "Tou wai bana baka hakuri ba?" Turbune fuska tayi shima ya bata rai, "Ay ban hakura ba tunda har yanzu kin kasa furta kalaman da nake son ji a bakinki." Gani tayi dai da gaske yayi fuska  sai abin ya burgeta ba kasafai take ganin fushinsa ba da wuya kafin tagani. Akwai ranar data bashi haushi sosai yace mata, "Hoodah sonki da nake yasa bana iya fushi da ke, amma duk ranar da nace zanyi fushin da ke abin bazaiyi kyau sheyasa ban taba yarda har ma in yarda inyi fushin dake." Kara makalkale shi tayi tsam, "Tou wai fushin na menene? Ina sonka Sultan, I love you so much! Shikenan happy?" Da sauri ya kalleta amma can kasan makoshi ta furta, "Ay banji ki ba, maimaita." Dariya sukayi dukkansu ta jawo kansa ta saita bakinta daidai kunnensa ta fada cikin wani irin tsawa, "Ina sonka mijina!" Wani irin toshe kunnensa yayi ita kuwa ta kyalkyale da dariya, ji tayi ya rungumeta tsam a jikinsa, bata ankara ba taji ya dagata duk da katon cikinta kuwa bai ji nauyinta ba, idonta a rufe sai data ji karar kashe tv tayi sauri ta bude idanunta tace, "Ina zamuje?" Dariya ya danyi yana kissing kumatunta sosai, sannan ya duko daidai kunnenta yayi maganar kamar rada rada, "Bacci zamuyi mana naga yau soyayyar da gaske kike yinta." Dariya kawai tayi ta kulle idanunta hade da kara makalkale shi wani irin farin ciki yana sauka cikin zuciyarta....





Na gode da addu'oinku Allah ya bar zumunci๐Ÿค❤️

Thursday 12 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 44

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 44}



To read all my books click the link below๐Ÿ‘‡๐Ÿป

Maryamsbello.blogspot.com




Kura ma ceiling idanu tayi dakin bakajin karar komai sai karar machines alamun ICU, jikinta in banda ciwo babu abinda yake mata hawaye kuwa sunkasa tsaya mata, kanta nade yake da katon bandage, fuskarta manne da oxygen mask, drip kuwa ansa mata kala biyu daya na ruwa daya na jini duk suna shiga a kowane hannu, zagaye kwayar idanunta takeyi sannan ta tabbatar a asibiti take, "Alhamdulillah kin tashi?" Taji muryar wata ta fada a gefenta, matar ta share mata hawayen da suka kasa tsaya mata, hannu Khadija tasa ta zare oxygen din a hankali bakinta na kyarma ta furta, "Where's my Mummy?" Dafa ta tayi ta mata murmushi, "Bari na kira Doctor, yanzu zaizo ya duba ki, you're a brave girl everything will soon be alright sannu ko?" Ta fita ba jimawa ba sai ga Mummy ta shigo kamar an tunkudo ta, dah da farko tsaye tayi saboda itama har yanzu ba karamin kuka take ba, tsaye tayi bakin kofa tana ta goge hawaye saida ta tabbatar kukan ya dan tsagaita sannan tayi ajiyar zuciya ta karasa ciki, a hankali ta tsaya gefen gadon tana kare mata kallo, Khadija ta juyo da fuskarta suka hada idanu sai ta fara kokarin tashi zaune, Mummy tasa hannu ta dafata tana ce mata, "No don't get up, an maki surgery a kasanki doctor yace mana karki yi moving Khadija, wait sai wurin yayi sauki tukunna." Ko sauraren Mummy batayi ba tana sheshekar kuka tana kokari tashi zaune, Mummy ta riketa gam tana girgiza kai hawaye na faman zubowa daga idanunta, "Why am I still alive?? Why do you save my life? Ay da bari kukayi na mutu meyasa kuka ceto rayuwata? Meye sauran amfani na kuma? Rayuwata batada wani amfani kuma." Ta fashe da wani irin kukan fitan hankali, da sauri Mummy tayi hugging dinta, "Karki ce haka Khadija, ba kanki aka fara fyade ba, kuma kaddara ce bata wuce kan kowa so please ki daina fadan haka Khadija rayuwarki nada sauran amfani a garemu we all love you so much...." ture Mummy ta shiga yi tana shesheka, "No! Mine is different Mummy! My own father raped me! He molested me over and over again, mahaifina! How do you expect me to continue living my life? Just how?!" Mummy ta kara rungume ta zuwa yanzu ta kasa controlling kanta kuka takeyi kamar ranta zai fita, a hankali aka turo kofar dakin Doctor ne ya shigo nurse na biye dashi a baya, Mummy ta janye jikinta daga na Khadija tana share hawaye tana kakalo murmushin dole, "My patient how are you feeling today? And why are you crying?" Ya furta yana kokarin zama gefenta, bata bashi amsa ba sai ma kukanta da ya karu, umarni ya ba Mummy da nurse din akan su bashi wuri ya ga patient din tasa zai kirasu back, fita sukayi shi kuma ya maida dubansa ga Khadija wacce ke shar6ar kuka kamar wacce ake yanka ma naman jiki. Dr Hafiz bai ce mata komai ba yabita da idanu har sai data tsaigaita da kukan da takeyi sannan yace mata, "Feel better?" Ta gyada kai tana share hawaye, murmushi yayi sannan ya dauko ruwan dake cikin bottle kan side table din dake gadon da cup ya tsiyaya mata half cup ya mika mata, "Drink thisvwater you'll feel much better." Ta karba a hankali tasha ta mika masa, gyara zamansa yayi sannan yace mata, "Komai da kikaga ya faru da mutum kaddara ce, Allah yana san bawa ya dauki kaddara mai kyau ko marar kyau, duk abinda ya hukunto maki ki karba hannu bibiyu sai kiga komai yazo maki da sauki...." girgiza kai ta shiga yi wasu sabbin hawayen na wanke mata fuska, "Doctor mahaifina.... he....he...." kasa karasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta, don dole ya mike ya kira nurse taje ta siyo allurar bacci akayi mata, itama tana fizge fizge da surutai babu abinda take fadi sai, "Mahaifina ne.... mahaifina ne... shine ya cuceni.." abu daya take ta nanatawa babu abinda Mummy keyi sai kuka wane an aiko ta, sai can bacci yayi gaba da Khadija sai sannan Mummy ta samu yar natsuwa cikin ranta, ta jima a nan zaune tana bin Khadija da kallo kafin Doctor din yace, "Meet me in my office Hajiya I want to speak to you privately." Gabanta ya dan fadi can dai ta dake tace "Ok Doctor."  Daga haka yayi gaba nurse din ta sake gyara Khadija ta chanza mata drip sannan ta fita. A corridor ta iske Zarah, Hoodah da Hafsat zaune jugum jugum ko wane ya rafka tagumi, Mummy ta dafa Hoodah, "Hoodah ya kamata ki koma gida kije ki huta sai Zarah ta tafi dake ta bude miki dakina, you need rest my dear you see your condition bai kamata kina stressing kanki ba...." Hoodah tayi murmushi "An not stressed I am okay Mummy." Mummy zata sake magana Zarah tace "Don't worry Mummy she's fine." Mummy ta kakalo murmushi "Okay, em... Zarah ga Khadija nan please look after her zanje in dawo." Ta gyada kai Mummy ta wuce inda ta tadda Ashraf, Yasir da Sultan suma suna zaune ko wane da tunanin da yake, tace masu "The Doctor wants to see me, I think you should come with please," suka gyada kai suka mike a sanyaye. Da sallama suka shiga dakin Dr Hafiz da alama su yake jira yana ganinsu yayi murmushi yace "Please come in." Suka shigo a sanyaye, bayan sun zauna ya sauke ajiyar zuciya, "Kamar yadda kukasani Khadija was molested and abused, lokacin da aka kawo mana ita munyi mata duk wani gwajin da ya dace muyi mata thankfully she's okay, hiv negative etc. Mutumin ya halbeta ba a ciki ba iyaka which badly affected her womb, I really don't want to say this to you amma dole ku sani..." Ya numfasa gaba daya gabansu faduwa yakeyi, "Na farko shine Khadija bazata taba haihuwa ba her womb was damaged completely, sai buguwar da tayi da ya wurga ta kasa ta bugu a bayanta whiich badly affected her spinal code, zaiyi wuya ta sake takawa I thought we can fix it but sadly we couldn't, she has to be on wheelchair for the rest of her life, am so sorry for this news ba yadda zanyi dole in fada maku.... and lastly, she broke her hand ya taba mata jijiyar hannu which caused the side to be paralyzed in zaki kula dazu tana ta kokarin tashi zaune ta kasa sannan zaki lura hannun hagunta kadai take dagawa dayan bata daga sa, inshaAllahu with time zamu dinga mata physiotherapy zata dawo da hannunta, sai kun dinga daurewa shima maganarta ya danyi affecting amma kadan thankfully ba da yawa bane in no time zata dawo da hannun and her speech will be clear. Sai kun bata kyakyawar kulawa sannan you have to support her through this journey har Allah ya iyakance mata, maganar karshe you don't have to tell her now zaku barta har sai taji sauki in ba haka ba it will worsen her condition, keep any bad news apart just try and make her happy..." zuwa yanzu Mummy bata iya kwakwaren motsi, a sanyaye Ashraf da Sultan suka mike suma kansu sun saka magana suka fice daga office din,  a hankali Yasir ya kamo Mummy wacce ta kura ma Doctor din idanu tun dazu, ta mike tsaye Yasir yace "Mungode Dr." daga haka yaja mahaifiyarsa wacce ke behaving kamar marar lakka, bakin kofar dakin ICU din ya zaunar da ita sannan ya zauna gefenta hannunshi cikin nata, yana zama ta jinginar da kanta bisa shoulders dinsa ta runtse idanu wasu hawaye masu shegen dumi suka gangaro mata, suma su Zarah hankali tashe suke tambayar lafiya babu wanda yake da energy din magana saidai Yasir ya bisu da idanu kafin yace, "Please don't stress Mummy with questions for now, yanzu Mummy tana bukatar hutu in ba haka ba she will also fall sick, please ku kula da ita da kyau." Ya fada yana mikewa tsaye, da sauri su Zarah suka zauna gefenta sai faman magana suke mata kamar ma bata san sunayi ba, karshe ma da suka isheta sai ta mike tsam batace dasu komai ba tayi dakin ICU din ta shiga a hankali, jingina tayi da kofar tana kallon Khadija wacce ke bacci da alama tayi nisa a baccin nata, a hankali take tafiya har ta isa bakin gadon har yanzu bata dauke idonta a kanta ba, zama tayi tare da kamo hannuwanta ta damke tare da dora kanta bisa hannun ta lumshe idanu, dagowa tayi tana kallonta hawaye na gangaro mata tace "Khadija ko kinyi ma wani ko wata laifi ne? Ko kuwa Allah kikayi ma laifi?" Mummy ta tambayeta tana tsareta da idanu kamar tana jinta, tafi minti goma tana kallonta kafin ta goge hawayenta da sauri ganin ta fara motsi...

2 DAYS LATER...

A hankali ta bude idonta ganin Mummy gefenta ya sanya ta fara kokarin tashi, Mummy tace "No Khadija don't move please, na fada maki da aiki a kasanki ba'a son yawan motsi." Daina motsin tayi ta koma ta kwanta tana bin Mummy da kallo, can tace "Can I ask you a question?" Mummy ta gyada mata mata kai "Sure darling what is it?" Khadija tace, "Bayan na suma what happened after that? I can't recall anything abinda kawai na iya tunawa kawai shine ina jin ana tafiya dani bisa emergency bed but daga nan bansan meyafaru ba after that." Mummy tayi murmushi gamida kamo hannunta, "Nothing much sweetheart, meyasa kikeso kisani yanzu?  Ki bari idan kinji sauki I will tell you everything, but for now you rest and rest, that's all you need to do for me okay?" Khadija tayi murmushi, "Okay but please one last question Mummy?" Mummy tayi ajiyar zuciya tace "Okay ya akayi?" Tace "Where's my dad?" Shiru Mummy tayi na yan seconds kafin tace "He's where he deserves to be right now, he is in police custody Khadija, kuma InshaAllah za'ayi masa hukuncin daya dace dashi so please don't worry okay?" Khadija tace "I know, can I see him amma?" Mummy ta bata rai, "Me xakiyi masa after what he did to you he doesn't deserve to be called a man or a father!" Mummy ta fada a fusace, Khadija tace "I know Mummy, I just wanted to tell him some things he should know, sannan to tell him how much hate I have for him in my heart!" Mummy ta shafa kanta, "Don't stress yourself because of that monster, that's exactly how he did to my sister, he dated her for 5 months thinking he was the right guy for her, but then he showed his true colors, he did exactly what he did to you." Ta fada wane cikin bacin rai, Khadija feeling hurt tace "Then why did you let him get away with it back then?" Mummy ta share guntun hawayenta tace "We tried our possible best Khadija, but that man left this country, kinsan dai tunda ya riga ya gudu wata kasa we don't have any right to do something har sai dawo." Khadija tace "He's wicked and heartless," Mummy ta kakalo murmushi "Hakane, saidai babanki ne no matter what ba'a chanza ma tuwo suna, addu'a kadai zaki taya shi Allah ya shiryeshi kinji??" Ta gyada kai, Mummy tace "That's my brave girl, now what do you want to eat?" Ta girgiza kai, "Nothing bana jin yunwa." Mummy tace "A'ah, you have to eat koda liquid ne don kisha magungunan ki." Tana fadan haka ta mike ta nufi waje don samo mata wani abu har Mummy ta kai kofa Khadija ta tsaida ta, Mummy ta juyo da murmushi saman fuskarta tace, "Do you need something?" Khadija tace "Can I speak to Zarah and you Mummy?" Mummy ta dawo kusa da ita tace, "Meyafaru haka? Me kikeso kice mana?" Khadija tace "I will say it if Zarah is here." Mummy tace "Alright let me get her," Mummy ta tafi ba'a juma ba sai gata itada Zarah sun shigo, Khadija tace so take ta jingina a gadon Mummy ta taimaka mata, bayan ta gyara zaman nata ne ta kallesu sannan ta fara magana, "A wannan zamanin baza'a taba samun butulu ba kamar ni...!" Cike da mamaki Mummy ta matso kusa da ita ta zauna harda rike mata hannu tace, "Subhnallah Khadija! Ki daina furta kalmomi makamantan haka! Kar ki sake kiran kanki butulu a ina kika yi butulci? Kuma wa kikai mawa? Please keep that word out of your mind!" Girgiza kai Khadija ta shiga yi, "It's true Mummy! Nayi maku butulci, ban kyauta ba I am ashamed of myself now I don't deserve your love Mummy Instead I deserve your hatred!" Mummy ta kalle ta cikin shock idanunta a waje tace, "Why are you talking in riddles? Explain yourself!!" Zarah tace "Khadija maganar nan ya wuce basai kinyi wani bayani ba please a manta da abinda ya riga ya wuce..." Mummy ta juyo tana kallon Zarah sannan ta mike tsaye ta isa dab da ita tace "What are you hiding from me Zarah? Me Khadija tayi miki da ni banida labari?" Zarah ta hadiye kukanta amma still saida stubborn one ya zilalo mata, Mummy ta girgiza ta tace, "Talk to me Zarah! What happened between you two?" Zarah dai batace komai ba sai kukan da takeyi, Mummy ta juyo tana kallon Khadija, Khadija ta fara magana cikin karfin hali kanta na kasa, "Bayan na dawo hutu sai naga Ashraf a gidanmu at first I was pissed off sai daga baya na kamu da sonsa! I started becoming jealous of Zarah ina neman hanyar da zan raba su, I even drugged him, na kwanta dashi saboda Zarah taji haushi ta rabu dashi, but none happen! I keep plotting against Zarah even after I find out we are not related, ban tsaya a nan ba na rubuta mummunar letter lokacin bikinta bayan ta tare kafin na dawo gida, a letter din na rubuta abu mafi muni inda na sa suka fara fada tsakaninsu bayan nan naje nayi photoshop fuskar Ashraf da wata kafira tsirara na aje a wardrobe din Ashraf, I guess sun gano ni sheyasa suka shirya, despite what I have done Zarah bata taba fada maki ba ta rufa man asiri cuz tasan idan kika sani zata bata relationship dinmu dake! I know sheyasa abinnan ya faru dani my father raped me meyafi wannan bakin ciki? Ina girbar abinda na shuka gradually! Da haka nake cewa Mummy ki yafe man nasan I don't deserve your forgiveness. But you are a good person kin rike ni fiye da yadda kika rike yayan cikinki amma ga abinda na saka maki dashi, please forgive me Mummy na tuba...!" Tunda Khadija ta fara magana Mummy ta zama shocked tsaye tayi har ta gama saurarenta kafin ta fara ja baya a hankali, "Khadija...! Dama ashe haka kike?" Khadija ta fara girgiza kai ga ba halin tasowa, "Mummy don Allah kiyi hakuri ki yafe man wallahi na gane kuskurena! And I love you please don't punish me by not forgiving me I cannot bear it..." Zarah ce ta taro ta ganin har ta kai kofa amma ina kafin ta karasa har Mummy ta fita da sauri daga dakin, Zarah ta kwala mata kira sannan ta bita a guje, Khadija kuwa kokarin moving takeyi har sai da ta kai karshe gado ta zube akan gadon saboda bata iyawa, wani kuka na fitan hankali tasa tana fadin, "I made a huge mistake please forgive me Mummy!" Kuka take kamar ranta zai fita ji take gaba daya duniyar ta isheta kuka ta dinga rigza tana kiran Mummy har baccin wahala ya dauketa.

Tun daga ranar Mummy ta fita harkar Khadija, gaba daya ta janye daga jinyarta da takeyi ko tazo saidai tazo ta duba ta amma bata wani bata kulawa kamar da, amma komai tanayi duk wani payment da medication dinta bata fasa ba, saidai ta chanza mata sosai, Zarah da Hafsat kadai ke faman jinya Hoodah kuma sun koma itada Sultan cikinta ya cika wata takwas cip sheyasa ma Mummy tace su tattara su koma haka nan. Abinnan ba karamin damun Khadija yakeyi ba har sunyi sati uku yau babu abinda ya chanza itama Mummy taji babu dadi amma ta dake she's just so angry at her. Satinta hudu chip aka sallameta sun siya wheelchair sannan za'a dinga dawowa physiotherapy sau biyu a sati. Khadija ba karamin shiga senses dinta tayi ba duk ta chanza ta zama shiru shiru da ita. Zarah ma sun tattara sun koma Agadez itada angonta Ashraf.

--------

A hankali ta bude idonta a daidai lokacin ne duk abubuwan da suka faru a daren jiya suka dawo mata, wani irin faduwar gaba taji at the same time kuma zuciyarta fal take da farin ciki marar adadi ji take kamar a mafarki. A hankali ya turo kofar dakin ya shigo da wani irin kayataccen murmushi a fuskarsa, saurin kauda kai tayi tare da lumshe idanunta sabuwar kunya taji ta ziyarce ta, wata irin kunya taji wacce bata taba zato zataji ba. Zama yayi gefenta har lokacin ta kasa bude idanunta, "Princess ba gaisuwa? Ko yan masifar ne suka taso?" Batasan lokacin data bude idanunta ba harda murguda baki, "Wai suka taso sai kace wata mai aljannu!" shiru yayi kawai yana binta da kallo yana jin sonta na kara shigarsa yana ratsa ko wace jijiya da kuma ga6o6insa. Saida ta bari ta mike tayi hanyar kofa sannan tace "Ina kwana?" Tana fadan haka sai ta fita daga dakin gaba daya. Yar dariya yayi kafin ya mike ya shiga bathroom don yin wanka. Side dinta ta tafi ta wanke bakinta tayi wanka, har ta karasa wankan nan murmushi bai bar lips dinta ba kaunar mijinta na sake linkuwa a cikin ranta da ruhinta. Tana fitowa ta shafa creams wanda Mummy tasa akayi mata hadin kamshi ta shafa ta fesa sprays kala kala a jiki, wata red gown ta atamfa ta saka ta daura dankwalinta tasa costumes, kwalli kawai ta shafa sai lipstick kadan tayi kyau ba kadan ba, wayarta ta dauka ta fito tana ta kamshi dama gidan baiyi wani datti ba dan kara kimtsa shi kawai tayi sannan ta tafi kitchen tana faman tunanin abinda zata dafa da rana. Cak ta tsaya tana bin dining din da kallo yadda ya cika shi da abinci yayi setting dinshi gwanin ban shaawa. Yadda kuka san shine matar gidan, wani irin dadi taji a ranta, zuciyarta fal haka ma fuskarta ta kasa daina murmushi haka ta juya da niyyar tafiya side dinsa sai gashi ya shigo waya kara a kunnensa, babu abinda ke tashi parlon sai kamshin turarensa, binshi tayi da kallo sai ma taga bai taba mata kyau ba irin na yau sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda blue color hular kansa ta shiga da kayan da ya sanya, yanata waya fuskarsa cike da annuri sai murmushi yakeyi, take sai taji tukukin kishi ya taso mata wai dawa yake waya haka sai wani murmushi yakeyi? "Ah haba na isa in manta dake?... haha kin fiya abin dariya wallahi... yanzu dai kinsan tsada garemu ki biya in kinaso a bata." Jin alamar da mace yake waya sai kawai tasha kunu ta zauna kan dining gamida zuba abincin tana wasa dashi gaba daya sauraren conversation din nasa takeyi. Tun yana tsaye yana wayar har yaja kujerar dining ya zauna yana fuskantarta yafi minti sha biyu sannan taga ya katse wayar, kallonta yayi yadda take ta juya abincin fuskar nan a tamke wane tana jiran dambe, yar dariya yayi sannan ya matso gefenta ya zagayo da hannayensa saman wuyanta yana kissing gefen fuskarta, "Sana'ar ta taso kenan?" Wata irin harara ta watsa masa ta gefen ido tana ture hannayen nasa dake sargafe saman wuyanta. "idan ka gama wayar sai kazo kaci abinci, ko wayar ta kosar da kai ne?" Wata dariyar ta su6uce masa ba shiri yana jin nishadi a cikin ransa, plate ya janyo ya tura gabanta, "Ayi hakuri ranki ya dade bata kosar dani ba yet, zanci abincin." Zuba masa tayi cikin masifa ta hankada masa plate din gabansa, murmushi yayi ya girgiza kai sannan ya fara cin abincinsa a natse, a hankali ko wanensu ya fara cin abincinsa gaba daya zuciyar Zarah cike take da tunanin dawa yake waya haka? Kodai Khadija ce ta kirashi da salon kara yaudara? Nan take taji zuciyarta har tafasa takeyi, "Zarah kodai in tafi wurin aiki ne?" Da sauri ta dago da wani irin expression a kan fuskarta tace, "Bangane ka tafi aiki ba, dama bazakaje aikin ba?" Danne dariyar shi yayi yana shan tea a hankali kafin yace, "Kin manta na dauki hutu wurin aikina? Amma naga kullum fada muke Zarah ba gara in tattara inawa inawa ba in koma wurin aiki ba? Idan baki ganina kila kin fi jin dadi," kallonsa takeyi kafin tace, "Tou ay kwana biyu bamuyi fada ba."  Batasan lokacin da maganar ta fito daga bakinta ba, murmushin data ga yanayi ne yasa tayi saurin cewa, "Idan wurin wacce kuke waya zakaje tou ka gayyace ta tazo gidannan kaga sai ku huce takaicin rashin ganin juna da bakuyi ba." Tana gama fadan haka ta mike da sauri ta tattara kwanukan tayi kitchen dasu don wankewa, gaba daya kishi duk yabi ya addabeta gashi yaki gaya mata dawa yake waya. Wanke kwanukan ta farayi duk ranta babu dadi, ba zato kawai taji ya rungumeta ta baya nan ta fara mutsu mutsu akan ya saketa, "Wai bakaga aiki nake ba?" Ya kara matse ta, "Tou kawo in tayaki wai princess fushin na menene? Kefa da bakinki kike cewa mun daina fada why can't we continue living that way happily?" Taji ya fara kissing bayanta da kanta lightly, tace "Ba kace aiki zaka koma ba halan tayi missing dinka tace ka dawo ta ganka?" Gimtsa dariyarsa yayi sosai kafin yace "Wai wacece wannan ake ta fushi akanta?" Ta kara hade rai "Wacce kuke waya dazu da ita mana! Sai wani narke murya kake kana kashe mata murya, indai haka ne gaskiya na fasa soyayyar da kai sai ka tafi wurinta tunda ita kakeso yanzu bani ba!" Ta karasa gamida murguda baki, a hankali Ashraf ya juyo ta, "Zarah da Hoodah fa nake waya, wannan kasa da murya da kika inayi nace mata ay bacci kike kar na tashe ki, Zarah a tunaninki zanyi waya da wata a gabanki nasan daga ni har ita bazamu tsira ba wurinki? Besides ni matata kuma princess dina kawai nakeso, ita kadai ta samu damar mallakar zuciyata." Harara ta watsa masa duk da cewa fuskarta dauke take da murmushi alamar taji kunyar abinda ya faru, "Ni ka daina man haka kunya nakeji, sai kayita man rashin mutunci sai kuma a dawo ana cewa ana sona ehe!" Dan peck yayi mata a goshi zuciyarsa cike da farin ciki sannan yasa hannayensa ya zagayo dasu saman waist dinta ta sunkuyar da kanta fuskarta dauke da murmushi, Ashraf yace "Niii Ashraf yaushe nayi rashin mutunci? Ya zaayi in wa matata rashin mutunci duk yadda nake kaunarta?" Yar hararar wasa ta masa, "Da wannan maganar dama kawai hakuri ka bani da yafi," hancinta yaja yana dariya, "Kiyi hakuri kinji princess? My love, my chicken peri peri, my curry, my onion..." wata irin dariya takeyi har dukewa takeyi shima yana tayata hugging dinsa tayi tana kyalkyatar dariya shima yana dariyar yakeyi sai da tayi mai isarta sannan ta tura shi waje ta rufe kitchen din, "Go and watch football or news ka barni nayi aikina in peace abeg!" Tana juyo dariyarshi yana fadin "Your wish is my command your highness!" Aikinta ta cigaba da yi cike da nishadi kafin wayarta ta fara ringing, AirPod dinta ta dauko ta jona a kunne tana dariya tace "Hello..." ta furta farin ciki mamaye a zuciyarta.. Can bangaren tace, "My Inlaw how far ya kike?" Zarah tace "Wallahi lafiya lau mai girma Sarauniya! Ko kin haihu ne mu taho?" Hoodah tayi dariya sosai tace, "Kaji ki da zolaya Fatima, ay kafin in haihu zan kiraki ki garzayo kece zakiyi raino!" Zarah ta kyalkyale da dariya, "Ba dole ba ay shima babyn bai isa ya fito ba sai uwarsa tazo!" Hoodah cikin dariya tace, "Gaskiya bai isa ba, yanzu dai ina wuni? Ya kuke? Ya amarci? Ya ango? Ina fatan ana kula min da yayan nawa yadda ya kamata?" Zarah tayi dariya cike da nishadi tace, "Wannan tambayoyi haka Sarauniyar mu? Hehe Tou komai kalau kalau wallahi ya gajiyanku?" Hoodah tace, "MashaAllah, ah gajiya tabi jiki ay ya me jiki kuma?" Zarah tace, "Haka akeso ay, me jiki dasauki alhamdulillah mungode fa da dawainiya Allah ya kara girma da arziki." Hoodah tayi dariya "Ah meye na godiya kuma? What are family for? Aa ni kam ki daina mun godiya." Zarah tayi murmushi kurum, Hoodah tace "Gaskiya Zarah you're a great person, dan zaman da mukayi asibiti na shaku dake we became good friends, tunda na dawo nakejin ba dadi I really miss you all." Zarah tace "Same here my dear, am glad we met, yanzu ay mun zama yan uwa." Hoodah tace, "InshaAllah... tou bari naje dama na kiraki mu gaisa naga kin wani manta dani kina ta amarci ko?" Zarah ta kyalkyale da dariya,  "Wallahi ba haka bane, nagode sosai Sarauniya, take care regards to sarki..." Hoodah tace "You too InshaAllah." Suka katse wayar zukatansu fes a haka ta karasa aikin ta kimtsa kitchen din sannan ta fito parlor.  Tana fitowa parlor taji an fizgo ta, a tsorace ta saki kara Ashraf ya saki dariya yace, "Lallai yarinyar nan kin cika tsoro, daga na jawoki sai ki kama tsorata? Wai dama raki gareki a haka zaki haihu?" Ta saki dariya, "Haihuwa kuma? A ina zan iya haihuwa yar yarinya dani?" Dariya ya kyalkyale da ita harda dukewa, ta saki baki galala tana kallonsa, can yace "Yarinya kuma? Kodai rowa zakiyi man? Nida nake sa ran by next year muna nan rike da babynmu?" Ta wangale idanu cikin wasa tace, "Ni Ashraf? Rufa man asiri in haihu ay nayi yarinya da haihuwa, banma iyawa gaskiya." Ya daga mata gira daya sama "Haka kikace? Tou ko nazo na gwada ne?" Kauda fuskarta tayi gefe tana wata irin dariya, "Kuut Ashraf ko kunya wani wai ka gwada, kuma mutum yana kusanto ni zan fasa ihu mai gadi ya shigo ehe!" Dariya yayi sosai yana hugging dinta ta waist a hankali ya fara matsowa saida ya zo gab da fuskarta tuni ta fara zille zille tana neman guduwa, "A'a ki tsaya mu gwada mana mugani, kinga kenan nan da wata tara cip lokacin mun gama soyayyar mu har mun gaji." Tayi dariya cikin jin kunya tace, "La la wai dama idan akayi aure rashin kunya akeyi wallahi da ba haka kake ba, ni ka kyaleni tafiya xanyi in kwanta in danyi bacci." Kara rungume ta yayi, "Me nayi nakawai inyi iskancin da hujja." Wara idanu tayi sannan tasa hannunta ta toshe bakinta alamun mamaki, "Na shiga uku nidai ba ruwana kar kaja man sharri." Dariya yayi yana faman kissing din kanta yana kara matseta sosai hade da lumshe idanu, "Ina sonki Zara'u sosai fa ba kadan ba." Dagowa tayi tana kallonshi wani irin kallo as in kallo na masoya wani soft look mai kwantar da hankali, hannu tasa saman zuciyarsa hade da lumshe idanu, "Ay ga zuciyarka nan na bugawa tana dim dim dim!" Shiru yayi yana kallonta, pecking lips dinta yayi lightly sannan yace "Tunda da gaske bacci kikeji muje mu kwanta tou." Kokarin zillewa takeyi tana dariya ya riketa gam; "Kaida wa?" Yace "Da matata mana." Murmushi yayi ya jawo hannunta suka tafi daki duk son zillewarta haka ta hakura suka kwanta hannunshi rike da nata kamar wanda akace za'a sace masa ita a haka bacci yayi awon gaba dasu....




Tou yan team Zarah sai ku shirya zuwa suna nan da wata tara nikuma yar team Khadija (zuba ido hade da tagumi)๐Ÿ˜”