Friday 3 September 2021

YAR AGADEZ PAGE 47

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 47}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com





Washe gari wurin karfe goma da kusan rabi aka sallami Hoodah bayan an tabbatar da babu wani abinda yake damunta itada babies, Zarah tana nan makale da yan biyu, Abbi yayi arranging tarbar da za'ayi ma Sarauniya da ita da jariranta da irin kyauttukan da ya tanadar mata, a mota Ummi na rike da daya haka ma Zarah na rike da daya, haka suka iso gida tun kafin a bude masu gate makada suka fara buga algaita suna welcoming Hoodah da jariranta, Abbi na tsaye har suka fito daga motar inda aka karasa masa da jariransa yayi bismillah ya karbe su, wani irin farin ciki yaji ya lullube shi ya jima yana kallonsu kafin ya fara tofe su da addu'oi sannan yace, "Allah ya raya Safinah da Ahmad yayi maku albarka, Allah yasa su gaji mahaifinsu." Aka amsa da Ameen, (Ahmad sunan Abbi ne na asali) nan ya mika yaran ya kalli Hoodah yayi mata sannu ta amsa sannan Sultan ya kama ta yayi ciki da ita har dakin Ummi ya kaita, tana shiga tayi arba da Kaka xaune tsaye tayi cike da shock, batasan lokacin da fada ma kaka ba cike da murna, "Kaka yaushe kikazo?" Kaka ta kara rungume ta sosai cike da murna, "Jiya da daddare na iso, ay dama nace ni zan fara yi maki wanka bazan bari a rigani ba." Hoodah tayi dariya, nan aka miko ma Kaka yaran tace, "Kai tubarkallah ya akayi kika haife wadannan tula tulan yaya MashaAllah, lallai mamansu a koshe take." Aka sa dariya har kasa Sultan da Ashraf suka gaisheta ta amsa, sannan suka sa kai suka fita, nan Zarah ta tsugunna itama da gaida Kaka, Kaka tace "Zahara shine kika gudo kika barni ko? Ay da sai ki jirani mu taho tare ko." Zarah na murmushi tace, "Kiyi hakuri Kaka nida Ashraf muka taho, Abba ne yace mu bari zai taho dake." Tace "Nidai bawani, kawai a kawo min ruwa in gashe jikata da wadannan yan mitsa mitsan." Zarah ta mike kenan sai ga Ummi ta shigo da katuwar kula ta ruwan zafi ta dire bakin kofar bathroom tace, "Tou Kaka ga ruwan nan amma zaki iya yi mata ko inyi mata?" Kaka tace "Yi mata zanyi tas, ke sai kiyi wa jariran." Ummi ta amsa da toh sannan ta fita ba'a jima kwarai ba ta dawo da robar da za'ayi wa babies din wanka nan Zarah ta mike ta taimaka mata suka hada ruwan farko suka kai na Hoodah a guest room don sai yafi dadin wanka yafi space. Kaka ta mike taja hannun Hoodah suka fita, nan Ummi ta gyara zama Zarah ta cire ma Ahmad kaya ta mika shi nan Ummi ta sumbule shi tas Zarah ta hada masu kaya bayan ta gama aka mika Safina itama nan aka sumbule ta tas, Zarah ta shirya su sannan ta kwantar dasu, ana gamawa sai ga Sultan yasa an kawo sauran kayan babies da na Hoodah bayan an dire kayan tas sannan yace da Ummi, "Ina Hoodar?" Ummi tace "Wanka ake mata." Yace "Ok ga rago nan nasa a gasa mata sai taci sosai," Ummi tace, "Ok tou, nima gashi nan nasa ana dama mata kunu abinci ma data fito zata ci." Yace "Ok." Wurin babies din ya tafi inda Zarah ke basu kulawa ya sake dubasu sannan ya fita yana murmushi. Kafin kace me gidan ya dau harami shiga kawai ake ana fita duk da ma akwai security ba kasafai ake shiga din ba sai da umarnin sarki, yan uwa da abokan arziki ana ta zuwa ganin babies, kullum Kaka ke ma Hoodah wanka sau biyu a rana sai Ummi tayi wa babies din, ita kuwa Zarah gaba daya itace ke kula dasu ashe tanada son yara haka. Ba karamar kulawa suke samu ba daga mai jegon har jariran. Hoodah har ta fara dawowa Hoodan da muka sani yar budurwa tayi kyau ta gasu abinta, babies din kuwa tuni sun murje sun yi jajir sun fara kiba. Ana gobe suna su Yasir suka iso shida Hafsat, wani irin murna su Zarah sukayi suka basu kyakkyawa tarba nan da nan aka cika masu gabansu da kayan motsa baki da abinci da drinks. Ranar suna Abbi yayi organizing gagarumar walima, gaba daya ma harda invitation card aka buga da pass, nan masu taya murna suka fara hallara, mai jego da safe ta saka super mai kyau inda aka sha hotuna sai da yamma ta cire ta maida dankareren lace wanda yasha dinki tayi bala'in kyau tasha light makeup, gaba daya Zarah da Hafsat suna tare da mai jego suma sunsha kyau ba kadan ba. Can na hango su Hafsat da dukkan members na Yar agadez sai faman dibar abinci suke suna sawa a leda da sauri nace masu haba ku kuwa ku bari mana za'a sa maku har sai kun ture😂😂😝😜. Su angon jego dasu Ashraf da Yasir suma suna tare a cikin fada tare da Abbi a can suka ci abinci kafin a fara daukar pictures, sai gab da magrib taro ya watse sai fatan Allah ya raya mana Ahmad da Safina inda Sultan ya bukaci a saya sunan saboda yace bazai iya ringa kiran sunan mahaifiyarta kai tsaye ba, shine aka sa mata Afreen inda Ahmad za'a dinga kiransa da Aman. Bayan sallar magrib su Hoodah da Zarah suna zaune palor suna cin snacks da peppered chicken inda su kaka suna dakin Ummi suna faman hutawa don ba karamin gajiya sukayi ba, su Sultan kuwa Ashraf ya hada masu wata yar get together ta maza kadai suna can sunayi, knocking kofa akayi jakadiya da wasu maids da ke ta faman gyara parlon inda ya baci ta fita wajen kofar ta bude, wani dogari ne a tsaye yace da ita, "Jakadiya, Sarauniya tayi bakuwa a waje, amma ban ce ta shigo ba tukunna sai naji idan tana da appointment?" Jakadiya tace "Tou bari a sanar mata dan jira a nan." Nan taje gefen Hoodah ta tsugunna har kasa tace, "Allah ya karawa Sarauniya lafiya kinada bakuwa a waje." Tace "Wacece?" Jakadiya tace "Nima bansani ba bari in tambaya." Tana fadan haka ta mike, nan Ummi ta bukaci Zarah ta kawo su Afreen ayi masu wanka, Zarah dama tana goye da Aman Hafsat kuma na goye da Afreen, nan Zarah ta fara mikewa ta shiga ciki. Jakadiya ce ta dawo ta tsugunna, "Allah ya kara maki lafiya wai maman Khairy ce." Nan gaban Hoodah ya dan fadi tadai dake tace, "Ba damuwa a shigo da ita, ta sameni gazebo." Daga haka ta mike ta yafa gyalenta tayi hanyar kofa, maids dinta guda biyu suka rufa mata baya. A cikin gazebo din ta zauna bisa kujerun wurin alamun na hutawa ne, tana zaman jiranta sai gata ta karaso dogari na gaba ita tana baya, saida yazo gaban Hoodah ya sunkuya, "Ranki shi dade gata nan." Godiya ta masa godiya inda ta sallame shi nan ta kalli maman Khairy tana murmushi tace, "Bismillah shigo Mama." Da sauri ta shigo zata bada gaisuwa Hoodah ta tsaida ta tace, "Don Allah karki gaishe ni Mama." Mama tayi murmushi ta zauna kujerar dake gefen ta Hoodah, Hoodah tace, "Ina yini Mama?" Tace "Lafiya lau Alhamdulillah, ashe an samu karuwa?" Hoodah tayi murmushi, Mama tace "Tou Allah ubangiji ya raya mana ya masu albarka." Hoodah tace "Ameen."

Mama ta numfasa sannan tace, "Kiyi hakuri da wannan zuwan ba zatan da nayi maki, da naso sai hidima ta lafa amma kuma sai naga ya cacanci inxo maki barka sheyasa nace bari inzo gaba daya, wata alfarma ke tafe dani idan bazaki damu ba?" Hoodah ta numfasa, "Allah sarki ay babu damuwa anytime kike son xuwa xaki iya zuwa Mama wannan ay ba wani abu bane, komai fa ya wuce tsakaninmu wallahi babu komai." Mama tace, "Hakane." Hoodah tace, "Wace alfarma ce wannan Mama?" Mama tace, Akan Khairy ne taimakonki muke nema..." Hoodah tace, "Ina jinki?" Mama tace, "A lokacin da Khairy zata haihu na farko bayan ta haihu ta kamu da matsalar yoyon fitsari wannan lalura munyi magani har mun gaji abu yaci tura, tana nan yanzu in ba mu da muka zame mata dole ba wallahi babu mai son ta matso kusa dashi duk ta zama kazamar karfi da yaji ranki shi dade, sai abu na biyu bayan ta haihu sai dan ya fito da matsala irin jariran ne da ake haifan su da katon kai wallahi akan yaronnan munyi karkaf nida mahaifinta yanzu abun ya kai har motarsa saida ya saida, kullum muna zarya hanyar asibiti yan uwanmu sunyi iya nasu wallahi basuda karfin taimaka mana, yanzu tana nan a gida ga jikinta yadda kikasan an yaba mata gawayi wasu kattan kuraje takeyi a fuska da kuma wasu wurare na jikinta, wallhi ko asibiti sun kasa karbarta fuskarta ma kanta sai ta baki tsoro, shine nazo wurinki ki taimake mu kamar yadda Allah ya taimake ki, ki cece wannan yara da kudin magani ko yaya ne abinda Allah ya hore..." ta karasa tana goge hawaye, matukar tausayi ta bata, Hoodah tace, "Innalillahi wa inna ilahir rajioon, Allah ya basu lafiya yasa kaffara ne, yanzu zan fara baki wani abu ki rike, don  sarki baya gida idan ya dawo zan same shi in mashi bayani nasan bazata gagara ba InshaAllah." Mama ta sake share hawayenta da hannu tace "Mungode Allah ya saka maki da alkhairi ya kara girma da arziki, mungode sosai da sosai, sheyasa akace dan adam kowa da baiwarsa kuma babu kyau wulakanta mutum saboda shi wannan da kake wulakantawa a gaba zai iya taimaka maka..." Hoodah tayi murmushi ta mike tana kallon Mama, "Mama ina zuwa." Daga haka ta fara tafiya maids dinta na biye da ita, da tagumi Mama ke binta da kallo abun duniya duk ya ishe ta, Hoodah ta kai kusan mintina sha biyar can sai gata ta dawo fuskarta dauke da murmushi har tazo ta zauna hannunta rike da envelope, ta kalli Mama tace "Mama ga wannan ku fara amfani dasu zuwa gobe InshaAllah zamu zo sai muga abinda zamuyi a kai." Mama hannunta na rawa ta karbi envelope din tana ta jero godiya tana kuka sosai Hoodah na nuna mata ay babu damuwa ta daina kuka, "Dole ne in maki godiya ranki shi dade, kin mana abinda ko dan uwanmu bai mana ba, duk da abinda Ummalkhairy tayi maki amma gashi kece silar taimakonta, dole ne mu kara jin tsoron Allah wallahi rayuwar nan ba komai bace." Hoodah tayi murmushi, "Babu komai Mama dama ita duniya makaranta ce a cikinta muke daukar darasi, kuma a cikinta ne muke banbance fari da baki, don haka kedai kije ki kai yarki da jikanki asibiti Allah ya kara lafiya." Mama na murmushi tace, "Tou nagode kwarai da gaske ni zan koma." Hoodah tace, "Bazaki shiga kiga babies ba? Sannan zaki tafi ko ruwa baki sha ba ki shigo ciki." Bata musa ba suka mike inda suka taka har ciki ta shiga tayi barka sai yaba kyan babies din takeyi kamar ta sace daya takeji, sannan basu barta ta tafi ba saida aka kawo mata abinci dasu snacks da drinks ga kaji da salad saida taci sannan Hoodah tasa daya daga drivers dinta ya dauketa ya kaita har gida aikuwa tana zuwa ta basu labari jikin Khairy duk yayi sanyi, ji take dama za'a iya komawa baya da zata gyara rayuwarta sannan ta gyara barnar da tayi. Ganin kudin yasa suka razana Baba ya kirga yaga million daya ne harda wani abu a kai, tagumi yayi yana bin Khairy dake kwance kan tabarma da kallo  yace, "Kinga rayuwa ko Ummalkhairy? Kinga abinda na dade ina fada maki ko? Amma duk kikayi watsi da maganata kika dinga aikata abinda ranki yakeso, Khairy duk da na yafe maki amma na kasa mancewa da abinda kika aikata Khairy, kin kai kanki kin baro Khairy wallahi sheyasa annabi yayi gaskiya da yace mai hakuri yana tare da nasara yanzu da kinyi hakuri da duk abinnan bai faru da ke ba abu goma da ashirin duk ke kadai?" Khairy kuka Mama kuka, ya numfasa, "Yanzu ay bamuga ta zama ba tashi zakuyi muje mu fara biyan kudin aikin yaron nan ko ya samu saukin rayuwa, wannan ruwan dake fito masa babu dadin gani, ke kuma idan Sarki sukazo suka kara taimaka mana sai a diba ciki a fara naki treatment din..." ta gyada kai wasu hawayen masu dumi na gangaro mata daga haka Baba ya mike yana fadin, "Bari in dan fita nan waje kafin ku kimtsa ba jimawa xanyi ba." Mama ta masa a dawo lafiya sannan tace "Sai ki tashi ki shirya mu tafi, sannan inaso mu siya maki wannan robar da akesa wa masu yoyon fitsari wannan zaurin da kike yi babu dadi Khairy, sannan shima yaron nan kina daukar shi a jikinki kina sa masa zauri, yanzu ki tashi kije kiyi wanka ki chanza wadannan kayan masu zauri, shima yaron ki chanza masa." da toh ta amsa hawaye masu matukar zafi suna zubo mata, ta yunkura ta mike tana dunkuna zani yadda fitsarin bazai zubo kasa ba ta wuce bandaki, ita kuma Mama ta dauki yaron a hankali ta shiga daki dashi don ta kimtsa shi.

---------

Ranar wata laraba Ashraf ya dawo daga aiki da yamma lis misalin biyar da da rabi, a gajiye ya shigo, daga bakin kofa Zarah ta tare sa sukayi hugging juna kiss ya mata a kumatu kamar yadda ya saba duk sanda ya shigo gidan, hannunsa ta kama ta taimaka masa ya zauna kan kujera, manne masa tayi tare da kwantar da kanta bisa kafadarsa tana mai lumshe idanu tace, "Yanzu wanka zakayi ko abinci zaka fara ci?" yayi murmushi yana jin sonta na kara ruruwa a cikin ransa, yace

"Duk abinda kika ce princess shi zan fara yi?" Tayi dariya tace

"A gaskiya wanka ya kamata ka fara yi saboda zakaji saukin gajiyar da ka kwaso daga nan sai kaci abinci ko?" Yace "Yess! princess hakan za'ayi." A tare suka mike hannunsu sakale cikin na juna. Ta hada masa ruwan wanka sannan ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa, ko wane motsi nata akan idonsa ji yake kamar ya hadiye ta don so, ya sauke ajiyar zuciya yace

"Princess a gaskiya ki daina shagwaba ni da yawa, kinsan irin wannan duk ranar da bakida lafiya ko nayi tafiya zan sha wahala fa..."

Tayi dariiya bayan ta cire masa 

riga tace, "Wannan kuma ay daban ne, kuma ni ka daina cewa ranar da baka nan tou ina zaka je ma?" Yayi murmushi yana kamo hannunta duka biyun, "Kinsan tafiya na iya kamawa ko kuma mutuwa..." Da sauri ta toshe masa baki tace "Ka daina fadan haka, in ma mutuwa ce bana fatan ta riga daukar min kai na fiso ta fara daukata ta." Yayi murmushi

"Ba wanda yasan gawan fari princess, mudai yi addu'a Allah yasa mu cika da imani"

A sanyaye tace "Amin"

A haka ya shiga wanka, ita kuma ta fiddo masa kayan da zai sanya marassa nauyi saboda yanayi ne na zafi. Bayan ya fito ta taimaka masa ya shirya ta fesa masa turare sannan ta kamo hannunsa suka fito parlor. Kan dinning ta zaunar dashi bayan ta zuba masa jollof d'in taliyar data ji kifi da kayan lambu sai lemo mai sanyi. Sai da yaci yayi nat sannan suka koma parlor suna kallo suna fira har aka soma kiran sallar magriba.

----

Ranar wata litinin tafiya ta kama Ashraf zuwa Nigeria Kaduna duk da dai tafiyar daga office d'insu ne bama shi kad'ai zaije ba harda abokan aikinsa su kusan biyar, tun da yake wayar Zarah dake kwance gefensa ke masa wani irin kallo har ta kai ya tsargu, sai da ya gama wayar ne ya juyo yana kallonta yace "Yada kallo haka princess?"

Ta bata rai hade da zumburo pink lips nata masu kara mata kyau tace cikin shagwa6a "Ina zakaje?" Yayi murmushi yace "Wallahi tafiya ce ta kama mu yau d'in nan amma kar ki damu kwana biyar kawai zamuyi mu dawo." Ta juyar da kanta gefe alamun fushi, yayi murmushi tare da kamo ta ya maido bisa jikinsa yace

"Fushi kuma princess? Meyafaru?"

Idanunta suka kawo ruwa tace

"Naji kana zancen tafiya ka barni, kuma kai kanka kasan tunda mukayi aure baka taba tafiya daidai da rana daya ba, sannan kasan ban iya bacci idan baka kusa dani" Take yaji babu dadi saboda shima din ba iyawan zaiyi ba sai dai yazama dole ya tafi saboda aiki ne zai kaishi don haka sai ya rungume ta tare da fara aika mata da sakkonin kisses ta ko ina, itama ta biye masa sun d'auki tsawon lokaci a haka kafin Ashraf ya sauke ajiyar zuciya yace

"Princess wallahi inda kinsan dauriyar da zanyi muje mu dawo da bakiyi magana ba, wallahi zanyi missing dinki sosai, kiyi hakuri kar kice zakiyi kuka don bazan iya jure jin kukanki ba, i love you so much kwana biyar kawai zamuyi mu dawo insha Allah kinji my princess?" Ta kankame shi tace

"I love you more, inshaAllah zan daure har ka dawo amma kasani zanyi kewarka sosai." Yace

"Yes i know princess nima haka."

Daga nan Zarah ta tashi ta hada masa hadaden breakfast, ta shirya masa kayansa kafin ya fito wanka hade da fiddo masa kayan da zai sanya. Tana gamawa itama tayi wanka tasa wata bakar loose top marar hannu da pink dogon skin tight sai ta daura red dan kwali, ta kimtsa ta fito. Dakin Ashraf ta leka a lokacin yana shafa mai, ganinta yasa ya saki murmushi ta mayar masa, karasawa tayi ta taimaka masa ya shirya suka nufi dinning suka karya. Tunda suka fara cin abincin Zarah ke kallonsa kamar zata cinyesa, ya kalleta yace

"Princess?" Ta sadda kanta kasa tana murmushi tace "Na'am?" Yace "Na gama fa sai tafiya yanzu kuma..." Sai kuma ta 6ata rai duniya ba abinda ta tsana taji zatayi nisa da Ashraf dinta, yana ta lura da yanayinta amma sai yayi sauri yace, "Ga wannan." Ya mika mata kudi dubu hamsin yace "Ki rike wannan abinda kike 6ukata kiyi yi amfani dasu har Allah yayi mana dawowa, kuma duk sadda kikaji kadaici ki tafi wurin su Kaka kuma kinga gidan akwa maids ko ina so bakida kadaici." Tana dai ta daurewa bataso tayi kuka amma abu yaci tura sai kawai tasa kuka, take hankalin Ashraf ya tashi ya rude, hugging dinta yayi yana ta aikin lallashi tare da assuring nata cewa kwana biyar dinnan zaiyi ya dawo kuma duk abinda take bukata ya aje mata, sai da ya tabbatar ta bar kukan sannan ya tafi. Bayan tafiyar Ashraf duk gidan gaba d'aya ya mata fadi ba dadi sam, yau batasan ya zatayi bacci ba babu Ashraf a kusa da ita.

Haka ta wuni daga kallo sai chatting, idan ta gaji ta buga game a wayarta ko kuma ta kira Hoodah a nuna mata twins dinta.

Tunda ya isa ya kira ta ya sanar mata sun isa lfy...

------

Mikewa yayi yana kallonta da yar dariya yana kallon kofa, "Tou Khadija tunda nidai yanzu ba'son ganina sai Dr Haiydar sai yayi maki shi." Ko kadan baiji haushi sai ma dadi tinda da taimakon shi akan iya ceto rayuwarta, sunkuyar da kanta tayi tana murmushi irin am sorry dinnan ta kusa minti ashirin a office din Dr Hafiz amma duk maganar da zai mata bata ce masa kala kuma taki sakin jiki dashi yayi mata therapy din yadda suka saba karshe yace mata ko a kira mata Dr Haiydar sai a lokacin ta daga mashi kai alamar eh, sai kuma tayi murmushin jin kunya tana dan girgiza kanta. "Allah ba haka nake nufi ba." A hankali ta furta shi kuwa Dr Hafiz sai yayi dariya yana faman tattara wasu files ya mike ya nufi hanyar kofa, tun ranar da suka yi therapy da Dr Haiydar tou kullum sai ya kira mata shi, "Kila dai daga yanzu zan dinga maki kwatancen office dinsa ba sai kin dinga tashina daga office dina ba..." daga haka ya fita yana murmushi, can Dr Aliyu ya shigo yana kulle office din a hankali saida ya karaso kusa da ita yace, "Khadija kina lafiya?" abinda ya tambaya kenan a hankali ta dago tana kallonsa tana murmushi a hankali, "Alhamdulillah, ina kwana?" Kallonta yake sosai yana murmushi shidai baisan dalili ba amma Khadija tana burge shi kuma sosai ba kadan ba, duk da cewar duk wanda ya kalleta yasan tana tare da tarin damuwa kuma sai kaji kana son taimaka mata da dukkan wani iko da Allah zai baka. Murmushi yayi a hankali yace, "Ina kwana kuma? Ay saidai ina yini don ba dadewa xakiga har sha biyu ta buga," gyada kai tayi alamun ta tuna, "Tou ina jinki Khadija yaya dinki? Ana class din ko kuwa?" Ya tambaya yana kureta da idanu, dagowa tayi da fara'arta alamar zatayi maganar abinda takeso. "Sosai ina jin dadin class din, na manta wayata a gida dana nuna maka wasu pictures." Murmushi yayi inda ya mike yajata zuwa therapy room din daga nan ya fara aiwatar da aikinsa cikin gwaninta da kwarewa, yaji dadi yadda ake samun improvement kuma da alama bazata dade kwarai ba zata samu sauki sosai. Yana cikin aikin ne yace, "Yanzu yaya batun karatu kuma Khadija?" Tace, "Final year nake na kusa gamawa InshaAllah." Yace "Kina zuwa?" Ta gyada masa kai alamun eh, yayi murmushi, "Yanzu da ace Allah xai baki dama ki goge wani abu daga cikin rayuwarki gaba daya Khadija me xaki goge?" Gabanta ya fadi kafin tace, "Abubuwa da yawa Dr, da ina da iko da na goge wani abu da nayi wa yar uwata wanda bazan iya fada maka ba, sannan da ina da iko zan goge ta hanyar da aka bi aka sameni da kuma kaddarar data afka man kwanakin baya, zanso inga mahaifiyata in rayu da ita ta bani mother's love duk da dai ban rasa wannan ba amma dai I still wish zan ga mahaifiyata koda sau daya ne..." zuwa yanzu kuka take kamar ranta zai fita tunda akayi mata fyade takejin rayuwarta ta kare sannan takejin duk wani pain dake ranta ya darsu da abubuwan da suka faru da ita, saida ya barta ta gama kukan kafin ya mika mata hanky, "Sannu ko in baki ruwa?" Ya tambaya yana yin hanyar fridge da sauri ta daga mashi kai disposable cup ya aje mata saida tasha ruwan hankalinta ya dan kwanta kafin shima ya koma ya zauna. "Allah ya jikanta Khadija, sannan komai da kikaga ya faru mukaddari ne daga Allah nima nan da kike gani banida mahaifiya a hannun kishiyar uwa na tashi." Da sauri ta dago tana kallonshi, "Da gaske?" Yayi mata murmushi "kwarai kuwa, tun ina dan shekara biyar ta rasu ta barni hannun matan babana..." take taji ba dadi, "Allah sarki Allah yayi mata rahama." Yace "Ameen." Mikewa yayi bayan ya kammala therapy din yana yar dariya yana kallon wrist watch din hannunshi ganin har lokaci ya kure, "Ya kamata mu tashi haka nan mun bar Mummy tana jiranki a waje..." ta kalleshi, "Da driver muke ita tana wurin aiki." Kamo wheelchair din tata yayi ya fara janta zuwa wajen asibitin, a haka suke tafiya yana bata labarin rayuwarshi, babu abinda ke ciki sai tsantsan tausayi rike kukanta takeyi har sukayi bakwana yasata a mota, tana shiga mota ta saki kukan sosai kuka take kamar an aiko mata da sakon mutuwa, driver din babu abinda yake sai faman bata hakuri yana mata sannu shi ya dauka ma ko ciwo takeji a jikinta. Shiga tayi cikin gida bayan Mama Hauwa ta dora ta saman wheelchair dinta suna tafe tana goge hawaye, kamar daga sama taji ance, "Wai nikam dadin kuka kikeji ne?" A razane ta juyo taga Dr Hafiz zaune bisa daya daga kujerun garden gefensa drink ne da snacks hannunsa da waya yana latsawa, da sauri ta goge hawayenta tana mamakin ganinsa, "Ina yini?" Yayi murmushi "Ina yininki? Tou ya exercise din akwai wahala? Shi wancan likitan haka ake therapy ki dawo gida kina kuka?" Yar dariya ta subuce mata. "Ba ruwansa..." da murmushi saman fuskarshi yace, "Aww haka zakice? Wato karesa ma kikeyi ko a gabana?" Yar kunya ta kamata hakan yasa ta kama keken nata ta karasa kusa da shi fuskarta a sunkuye...

No comments: