Friday 10 September 2021

YAR AGADEZ PAGE 48

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 48)



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Har ta iso dab dashi ganin yadda ya tsareta da idanu sai kawai ta sunkuyar da kanta ta juya kekenta tayi cikin gida saboda bataso ya gano yanayin da take ciki don ita gaba daya abinda takeji yafi karfinta, Dr Hafiz yabita da ido har saida ta shige, murmushi kawai yayi sannan ya cigaba da shan juice dinshi, tunani kawai yake shin wannan wace irin mutum ce? Yau zai ganta gata nan all moody wani time din kuma lafiya lau cike da nishadi. Da yamma tana fitowa daga dakinta da yake yanzu dakin kasa aka gyara mata nan ne dakinta, tana fitowa taci karo da Mummy tana waya da alama Zarah ce ke kan layi, da murmushi ta karaso kusa da Mummyn tana binta da ido har saida ta kammala wayar, Mummy ta kamo hannunta tace, "Har kin tashi? Ay tun dazu na dawo na leka dakinki naga kinata bacci abinki kina hutawa." Tayi murmushi "Mummy ina yini? Ya aiki?" Mummy tace "Alhamdulillah ya therapy din?"  Tace "Lafiya lau." Mummy tace "Tou kinyi sallah?" Ta girgiza mata kai, "Ina hutu." Mummy tace, "Ok Mama Hauwa ta kwantar dake kan gado?" Ta gyada mata kai, "Eh ay ita ke kula dani indai baki nan." Mummy tace, "MashaAllah, tou abinci fa?" Tace "Zanci anjima." Mummy tace, "Haba Khadija, kinsan akwai maganin karfe biyar kuma ana so a bada gap da abinci kafin a sha." Mummy ta mike ta nufi dining don zubo mata abinci, saida ta xubo ta dawo sannan ta fara bata abincin, sai da tayi nisa a bata sannan ta dakata tana kallon Khadija kafin tace, "Yauwa Khadija dama kuwa ina son magana dake?" Khadija tace "Ok gani Mummy." Mummy ta danyi shiru kafin tace, "Khadija ni sai inga kamar Dr Hafiz sonki yake..." da sauri ta dago tana kallon Mummy lokaci daya kuma gabanta ya fadi, da sauri ta girgiza mata kai, Mummy tayi murmushi, "Ba lallai bane ki sani duk da nasan ya kamata ki fahimta, duba da yadda yake dawainiya dake yake baki kulawa na tabbatar ba banza ba Khadija, don haka ki nutsu nidai har ga Allah Dr Hafiz ya kwanta min a rai kuma na yaba da halinsa, ki nutsu Khadija and also listen to your heart..." Khadija ta sunkuyar da kai take taji ta koshi da abincin kuma.

---

Ranar wata juma'a tana zaune parlor da safe Mama Hauwa tana tsefe mata kai Mummy ta fito da shirin fita office tana murmushi tace, "Yauwa ko kefe? Da kin zauna da kai sai kace ciyawa, anjima ki daure kije salon a wanke maki kan Khadija in kuma a gida kikeso zan dawo in wanke maki anjima." Khadija tace, "Inason inje salon din Mummy." Mummy ta ciro kudi dubu biyar ta bata, "Gashi Mama Hauwa sai ta rakaki salon din," murmushi tayi sannan ta karbi kudin, "Thank you." Mummy ta maida murmushi, "Take care." Tana fadan haka ta fita bayan ta masu bankwana. Da yamma bayan ta dawo daga salon din tana zaune garden ita kadai tana practicing zana wata gown da aka basu as assignment kamar daga sama ta hango shi yana shigowa, dagowa tayi tana kallonsa ganin irin shigar da bata taba ganinsa da ita ba wato kayan hausa kullum ciki jeans yake da riga amma yau yana sanye da dark blue shadda harta hular kansa kalar kayan jikinsa ce, a hankali ya karaso tare da turarensa wanda ya cika wurin, "Salam yan mata, zane akeyi ne?" Dan gyada mashi kai tayi a hankali tana jin kamar ta bar wurin, "Ya naganki haka kuma? Ko don nace Doctor dinki ya saki kuka rannan Khadija, fushi ake dani?" Bata san lokacin data zabga mashi harara ba, "Ohni Hafizu da harara na kisa dana dade da mutuwa, yanzu dai kiyi hakuri am sorry you hear?" Turbune fuska tayi ita sai yanzu ma ta lura bata san meya bata haushi ba, "Wai bana bada hakuri ba, yanzu dai me zanyi ki daina hararata don Allah?" Girgiza kai tayi, "Babu, ni zan tafi cikin gida."

Girgiza kai kawai yayi yace, "Nasan wani wuri a nan inda suke yin arts na fashion..." da sauri ta juyo tana kallonsa, "Really? Please mu tafi wurin mana." Yasan hakan kadai ne zaisa ta dawo daidai, da sauri ta gyara gyalenta wanda yake daure bisa kanta sannan ta turo kekenta har gaban motarsa, saida tazo shiga kuma sai ta tuna bata fada ma Mummy ba da sauri ta bude wayarta ta kirata nan ta bata izinin tafiya da kyar. Har suka isa wurin tsit kakeji a cikin motar, suna isa ta gwale idanu waje, "Wow Doctor Hafiz wurin nan ya hadu." Yayi dariya "Ashe dai ansan sunana?" Har ya karaso inda take tare da fiddo kekenta yana dariya tace, "Zaka fara ko?" Dariya yayi yana daga hannu alamun hakuri kafin ya fara janta har suka karasa ciki, baki bude take kallon wurin tun da take bata taba ganin inda ya birgeta ba irin wurin nan ba, babu abinda take sai murmushi zuciyarta fes, "Ban taba ganin murmushinki haka ba Khadija..." ya fada yana kallon yadda take snapping arts din da camerar wayarta, "Tou kawo wayar kema in maki hoton, I just love your smile today." Bata masa gardama ma ta mika masa wayar, har sai da ya dauketa kala kala kai harda ma wayarsa ya hada yana daukarta. Yana cikin daukar hoton ne wayarsa ta fara kara ganin Dr Haiydar yasa ya dauka yana fadin "Doctor yaya?" Dr Aliyu yace, "Please kuna tare da Khadija?" Yace "Eh muna tare lafiya dai?" Yace "Ah lafiya lau dan bata please minti daya." Mika mata wayar yayi yana murmushi, ta kara a kunne, "Hello ina yini Doctor?" Yace "Alhamdulillah, abinda yasa na kiraki karki zo appointment gobe sai jibi InshaAllah, abinda yasa banida number ki sheyasa na kira da wayar Dr Hafiz..." tayi murmushi "Laa bakomai Doctor Allah ya kaimu ba damuwa." Taji sautin murmushinsa "Tou godiya nake sarautar mata." Tayi dariya sannan ta mika masa wayar saida sukayi bankwana sannan ya katse kiran yace, "Yanzu Khadija sarauyinki wayata ma xai kira tsabar bai iya nemo taki number din?" Ta tintsire da dariya, "Wai saurayi! Dr Aliyu ne fa." Murmushi kawai yayi ya kyaleta daga nan wani shop taga sun nufa, tana dubawa taga shagon saida electronics ne, tsayawa tayi tana kallonsa fuskarta da alama tambaya yayi murmushi, "To make life easier for you am gonna buy you a laptop..." Girgiza kai tayi da sauri, "A'a don Allah basai ka siya ba zan cigaba da zane na a paper." Ko saurarenta baiyi ba kawai taga ya shiga shop din ya jima kadan can ya fito hannunsa dauke da tsadaddar laptop kirar apple, yana shigowa motar ya mika mata take sai yaga tana hawaye, a dan rude yake kallonta, "Khadija kuka kuma? Why are you crying please?" Share hawayenta tayi tace, "Doctor why are you doing this?" Shiru yayi ya murza key ya tada motar ya cigaba da tafiya abinsa, ta sake tambayarsa, "Please don Allah doctor ka fada man meyasa kake dawainiya dani?" Ta fada tana tsareshi da idanu, can ya numfasa, "Karki damu zan fada maki very soon Khadija..." daga haka tayi shiru har suka isa gida. ---

A hankali soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Dr Hafiz da Khadija duk da da farko tayi tunanin Dr Haiydar takeso sai daga baya ta fahimci zuciyarta tafi karkata da Dr Hafiz, duk wata kulawa daya kamata ya bata yana bata, kuma yanzu alhamdulillah ta warke tangaram ta mike kafafunta suna takawa don dai kawai dan limping din da takeyi kadan kadan amma dai ta samu lafiya. Bayan yan lokuta da basu wuce wata biyu ba aka sanya bikin Dr Hafiz da Khadija za'ayi bikin nan da wata biyar bayan Zarah ta haihu. Ranar da aka shirya akayi zataje gaida mahaifiyar Dr Hafiz Mummy ta shiryata tsaf ta taimaka ta shirya. Khadija tafi minti goma zaune a daki aka kwankwasa kofar aka shigo Mummy ce ta shigo tana murmushi Khadija ta mayar mata, "Amarya ango fa yana waje ke yace jira, ya kamata ki fito ku tafi kuje ku dawo..." gyada kai tayi tana faman sunna kai, Mummy ta mike ta jawo hannunta suka fito, tunda suka fara saukowa daga bene take murmushi, bankwana tayi wa su Mummy, Mummy ta mata sharadin kar dai suje su dade a can sannan ta kula da kanta. Tunda suka fara tafiya take jin faduwar gaba gaba daya a dare take, shima kansa baisan wace irin tarba mahaifiyar tashi zatayi mata, duba da yadda ya shawo kanta da kyar akan ta amince bayan dogon bincike da kuma ganowar ainahin wacece dan nata zai auro ba karamin gwargwarmaya akasha ba don har cewa take saidai ya zaba ko ita ko Khadija da kyar da jibin goshi ya shawo kanta ta hakura, amma koda wasa bai taba yarda ya fada ma Khadija reaction din Mamin tashi ba. Saida sisters dinshi wadanda ke aure sukayi takakkiya suka zo suka sa baki tace ba damuwa. Bayan sun isa ya sakar mata murmushi, "We are here amarya." Ta sunkuyar da kanta batace komai ba ta bude motar ta fito a tare suka jera har cikin parlon, parlon ba kowa sai karar tv sukayi sallama yace ta zauna bari yayi mata magana, a hankali ta zauna tana dan kalle kalle. Mami na zaune cikin daki tana shan fruit salad ya shiga da sallama, zama yayi kasa ya gaishe ta cike da ladabi ta amsa normal, yace, "Mami tana parlor tana jiranki." Da toh ta amsa, mikewa yayi ya fita ita kuma Mami ta sanya mayafi ta bi bayanshi. Khadija na ganinta ta fito tayi sauri ta zauna kasa Mami ta iso ta zauna kan kujera shi kuma Dr Hafiz yaje yayi ma masu aiki magana suyi arranging abinci kan dining. "Mami barka da wuni?" A wani yatsine take amsawa kamar tana tauna magani Khadija dai bata bari abin ya dameta ba ta saki murmushi, "Mun sameku lafiya?" Mami tace "Lafiya, ya mutanen gidan?" Tace "Duk suna lafiya." Tace "Tou madallah, feel at home bari na shiga ciki yanzu zan fito." Khadija ta gyada mata kai sannan Mummy ta mike ta shiga guest room ta fiddo mata hijab din sallah da carpet, sannan ta fito daga bakin kofar tace, "Zakiyi sallah?" Ta gyada mata kai Mami tace "Tou taso." A hankali ta mike sannan ta shiga ita kuma Mamin ta fito. A lokacin data gama sallar azahar ta fito babu kowa parlon amma da kamar tana dan jin maganganu na tashi sama sama daga kitchen, har tayi gaba sai kuma ta dawo fuskarta cike da shock tana sauraren maganganun da suke fadi, "Wai kana tunanin don kawai tazo na sakar mata fuska shine nayi accepting dinta as my daughter Inlaw? Tou ka bude kunnenka da kyau kajini, bazan taba accepting shegiya ba ban hanaka aurenta ba nidai babu hadina da ita, kaidai matarka ce amma ni ba surukata bace! Kawai sai kaje ka auro man saura a matsayin suruka ka kawo man ita cikin gida? Tou ban aminta ba kaidai da kaji zaka iya sai kaje kayi Allah ya taimaka..." idanunshi take suka kada sukayi ja yace, "Haba Mami da take Shegiya laifinta ne? Batada laifi ko kadan! Sannan da kike maganar saura shima ba laifinta bane, Mami idan yanzu akace yarki ce zakiso ayi mata haka?" Ta tsaida shi, "Tou nagode ma Allah ba yata bace! Don haka ka fita idona Hafizu!" Jikinta babu inda baya rawa har wani kyarmar sanyi takeyi, idanunta na neman kafewa dafa dining din tayi by mistake ta kado jug din dake kai ya fado kasa take Dr Hafiz ya zaro idanu waje yana rufe bakinsa da hannunsa, "Kinga abinda kikayi ko Mami? Nagode sosai...!" Da sauri ta juya ta fita daga parlon wanda yayi daidai da fitowar Dr Hafiz amma ina har ta fice da gudu, "Khadija please wait!" A haka yabi bayanta da sauri cike da tashin hankali! Khadija gudu kawai takeyi tana wani irin numfashi na wanda tashin hankali ya kai kololuwar tashi, "Innalillahi wa inna ilahir rajioon..." kawai take nanatawa a yayinda take kukan fitar rai, Dr Hafiz ganin bata cikin hankalinta kuma zata iya fada ma titi yasa yayi wani irin gudu yasha gabanta da gaggawa sai haki yakeyi, ita kuwa cikin kidima take wani irin kuka tana jin dama ta mutu don tasan wannan bakin cikin ta dinga haduwa dashi kenan da gori har karshen rayuwarta, karshen tashin hankali ta shiga wanda ko gabanta bata gani sai duhu take gani, "Khadija! Don Allah ki tsaya ki saurareni karki tada hankalinki a kan maganar da kika ji don't take it to heart wallahi she didn't mean it, Mami tana sonki Khadija...." ya fada yana kokarin rikota ganin nema take ta cigaba da gudun da takeyi, baisan lokacin daya fizgota ba ya rungume ta a jikinsa yana karanta "Innalillahi wa inna ilahir rajioon." A jikinshi ta saki wani irin kukan da bai taba ji ba a rayuwarshi har wanji jijjiga takeyi, ji take gaba daya komai na duniyar nan ya tsaya mata cak bata gane komai, "Don Allah ki daina kuka nan Khadija, kinsan ina sonki duk a yaya kike, I don't care what anyone else think, I love you just the way you are...." magana yake mata amma gaba daya ta rufe fuskarta da hannuwanta banda kuka babu abinda takeyi sai girgixa kanta takeyi, "Dama nasan irin ranar nan na zuwa Doctor! Wallahi dama mutuwa ce ta daukeni don nasan bakin ciki da kunci zan riska har karshen rayuwata! It will keep hunting me for the rest of my life!"  Tallabo fuskarta yayi yana share mata hawaye, "Kar ki sake wannan tunanin Khadija, am here for you no matter what, tsorona karki fasa aurena akan wannan Khadija I cannot leave without you Khadija please don't leave me..." dagowa tayi a hankali taga ya kureta da idanu yana kallonta, a hankali take share hawayenta idanun nan sun kada sunyi ja, "Tashi muje na maida ki gida." Mikewa yayi yaga sai kalle kalle takeyi shi tsoronshi daya kar ta kara ballewa sheyasa ma yaki sakin hannunta ya rike gam dan baisan ta inda zai fara tarota ba, jiki a sabule Khadija ta mike ta kalli yadda ya rike mata hannu gam, ya juyo yaga sai kallon hannun nashi daya rike takeyi sai kuma kalle kalle takeyi, "Doctor ka man alkawari bazaka taba kyamatata ba no matter what."  Kallonta yayi sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya dora dayan hannunshi saman hannunsu dake rike yana kallonta kallo na kurilla yace, "I promise you Khadija, no matter what I will never ever leave you." Sai a sannan ta dan sakar masa murmushi a haka ya cigaba da janta har mota sannan yace, "Ki tsaya a nan bari inje in dauko maki bag dinki cikin gida kinji?" Daga mashi kai kawai tayi ta bude motar ta shiga, a kan kujera ya samu Mami babu abinda takeyi sai girgiza kafa ko kallonshi batayi ba ya duka daidai kafarta ya dauki jikkar sannan ya dago yana kallonta a take ta juya fuska tana kallon wani side, jiki a sanyaye ya fito daga parlon....



Kuyi hakuri da jina shiru da kukayi kwana biyu munyi rashin wuta ne, and also kuyi hakuri da wannan ba yawa!😂also unedited

No comments: