Tuesday 12 September 2017

AUREN FANSA 44

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

http://MaryamSBello.blogspot.com
     

                🌹44🌹


A bakin gado Zarah tayi arba da ita ta kifa kanta tana kuka kamar wacce aka aiko ma da labarin mutuwa, a hankali ta k'arasa gami da zama gefenta ta d'an dafata sannan ta kira sunanta cikin sigar rarrashi.
"Meenah..."
A hankali ta d'ago da jajayen idanunta tana kallon Zarah a yayinda hawayenta suka cigaba da zuba ba k'akk'autawa, Zarah ta sa hannunta ta share mata hawayen tace
"Haba Meenah, meye haka? Meye abin kuka a nan? So kike sai wani ciwon yaje ya kama ki a banza? Don Allah kiyi shiru ku fahimci juna keda mijinki."
Meenah tayi murmushin da ya fi kuka ciwo tace
"Zarah, a halin yanzu ba zaki gane halin da nake ciki ba saboda bake bace aka yaudara ni ce aka yaudara, ke kina can zaune lafiya da mijinki kina sonsa yana sonki, ni kuwa fa? Ashe wanda nake matuk'ar so kamar raina ashe yaudara ta yakeyi? Mutumin da zan iya sadaukar wa rayuwata domin farin cikinsa, mutumin da nake da burin samun zuri'ah ta gari da shi, mutumin da nake kallo a matsayin masoyina na hak'k'ika ashe shi ba haka yake kallona ba, ya cuce ni! Ya cuci rayuwata, yayi min wasa da feelings ba kad'an ba, wallahi Zarah namiji mugu ne, namiji bashida tabbas! Allah wadaran namiji!"
Zarah tace
"Haba Meenah! Ki saurari kanki ki daidaita tunaninki, yes na yarda Faruk bai kyauta miki ba, kuma baiyi amfani da hanyar da ya dace ya d'auki fansa ba, amma tunda yayi admitting a gabana dake da Baba kinsan yayi namijin k'ok'ari, ina so ki sani ba ko wane mutum bane zai iya haka ba, ya kamata ko nan kiyi respecting decision d'insa, kuma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba ya na matuk'ar sonki a yanzu, kuma ya gane kuskurensa."
Ta mik'e tsaye tana huci
"Sonsa na banza, bana so ya rik'e kayansa, kuma nidai na gama zama da mayaudarin mutum kamar Faruk, bazan koma gidansa ba!"
Zarah ta mik'e tana kallonta galala kafin tace
"Are you kidding me? In ma wasa kike ki daina tun wuri, Meenah kamar yadda na fad'a miki da farko zan kuma maimaitawa, Faruk yana sonki ko ki yarda ko kar ki yarda, koda can baya sonki to yanzu Allah ya d'ora masa. Don haka kiyi tunani."


Baba ne ya aiko kiransu, suka mik'e jiki a sanyaye suka fice, a parlor suka iske Faruk kallo d'aya zakayi masa ka tabbar da hankalinsa a tashe yake, tunda suka shigo ya kafa mata ido ita kuwa ko kallon inda yake batayi ba, suka samu wuri suka zauna k'asa, Baba ya fara magana.
"Da farko dai ina so nayi muku nasiha akan zaman duniya, gaba d'ayanku nan musulmai ne, kuma shi musulmi a duk inda yake ana so ya zamto mai hak'uri da kuma juriya da kuma imani, tabbas Faruk baka kyauta ba a wani 6angaren, amma kuma ina so ke Aminatu kiyi hak'uri na tabbata yanzu Faruku yana sonki bada wasa ba, kuma tunda ya fito fili ya fad'a miki bai kamata kuma ki juya masa baya ba. Don haka ina so kiyi hak'uri ki d'auki k'addara, kuma komai na duniya mai wucewa ne, ki rik'e mijinki kiyi masa biyayya don shine gatanki duniya da lahira."
Meenah tace
"Nagode Baba, amma ni gaskiya bazan koma gidansa ba, ya sauwak'e mini kawai."
Ba Faruk kad'ai ba hartta Baba sai da ya razana da jin kalaman Meenah, Faruk sunkuyar da kansa kawai yayi yana jin tashin hankalin da bai ta6a ji ba.
Baba yana kallon Meenah yace
"Aminatu, kalamanki basuyi min dad'i ba, don banyi zaton kamar ki mai ilimi da aiki da shi zai furtawa mijinki haka ba, amma ina so ki sani saboda gaba duk wani 6acin rai in zaizo miki to kisan irin kalaman da zaki furta. Mijinki dai mijinki ne. Sannan zancen ya sake ki ma bai taso ba, idan ma ya taso sai kiyi tunani wa kuma zaki aura? Maza majoritin mu halinmu a rufe yake, kafin kuma ki gane halin sai kin zauna da mutum.
Aminatu duk rintsi kiyi hak'uri ki zaunawa aurenki, kedai ki cigaba da add'ua, duk wani hargirsi idan ya taso a tsakaninku kok'ari zakiyi wajen ganin kun zauna kun warware matsalarku."
Ya gyara zamansa ya d'an yo gaba daga jinginar da yayi, yayi ajiyar zuciya ya cigaba
"Kin bani kunya Meenah, ban ta6a tsammanin haka daga gareki ba, ni kome Faruk yayi na yafe masa, don haka kiyi k'ok'ari ki yafe masa kema. Ki tashi ki fara shirin komawa d'akinki, Allah yayi maku albarka ya kwa6e muku duk wata fitina."
Ya kai dubansa ga Faruk yace
"Allah ya jik'an iyayenka ya gafarta masu, ga matarka nan sai a kiyaye gaba, ka kula da ita da kuma kanka, kasan dai matsayinta yanzu, don haka ka rik'e ta amana Allah yayi maku albarka."
Yace
"Amin Baba, na gane kuskure na kuma insha Allah hakan bazata sake faruwa ba, nagode sosai insha Allah zan kula da Meenah, zan kuma rik'e ta bisa amana da gaskiya."
Cike da farin ciki Baba yace
"Amin, zan shiga daga ciki na d'an kwanta."
Sukayi sallama ya fice.



Zarah ita da mijinta su sukayi mata rakiya har gidanta da misalin k'arfe biyar da rabi na yamma, suna nan har akayi sallar isha'i bayan sunci abinci suka fara shirin tafiya, Zarah ta k'ara yi mata fad'a sannan ta bita da nasiha, sukayi sallama dasu suka shige gida suma.
Bayan ta shigo ta maida k'ofar ta rufe, yana nan tsaye bakin k'ofa yana faman murmushi, ta kauda fuskarta tace
"Ya dai?"
Yace
"Bacci nakeji my baby, amma inaso na fara yin wanka kuma ke nakeso kiyi min da kanki, kinsan na gaji da yawa rabona da bacci mai dad'i har na manta."
Ta so ce masa bazatayi ba amma tuno da nasihar Baba ya sanya bata musa ba ta bishi da "To."

Ta kunna masa ruwan zafi da taimakonta ya watsa, ta taimaka masa ya shafa cream mai k'amshi shi kuwa duk wani motsinta akan idonsa yake. Ta kammala ta tafi tayi wanka ta fito sanye da kayan baccinta masu kyau da kuma firgita tunani, sai zuba k'amshi take ya cije lips d'insa na k'asa yace
"My baby, kullum k'ara chanza min kikeyi, yanzun ma sai naga kinfi ko yaushe yin kyau."
Duk da taji dad'in kalaman nasa haka bai hanata turbune fuska ba tana cigaba da linke kayansa da ya cire yanzu.
Yayi murmushi ya mik'e ya jawo ta ta fad'o bisa k'irjinsa yana kallonta cike da so da k'auna marar misaltuwa, ita kuwa k'ok'arin k'wace kanta ta shiga yi wanda ta kasa saboda irin rik'on da yayi mata....




MSB💖

No comments: