Saturday 26 August 2017

AUREN FANSA 39

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

     
                🌹39 🌹
   
http://MaryamSBello.blogspot.com

Meenah ta dube shi tace
"My soul bai isheka ba abincin ko?"
Ya gyad'a mata kai, ta mik'o masa hannu ya sa nasa cikin nata tace
"Zo muje na had'a maka wanda yafi wannan, babu mamaki k'ila tana son cin wannan ne."
Baiyi gardama ba yabi bayanta suka nufi sashenta, tana tsaye da plate a hannunta suka fice, galala take kallonsu har suka fice, babu shakka Meenah ta yi gaba a halin yanzu ta barta baya, dole ne ma ta d'auki mataki akan haka. Ta fito daga sashen cin abinci (dinning) ta nufi sashenta.
Zaune take abin duniya ya ishe ta, ta sak'a wannan ta warware, daga k'arshe ta mik'e ta fito daga d'akin tana cizon hannu. Shiru babu motsin kowa, da alama suna cikin d'akin Faruk, haushi ya turnik'e ta kamar zata fashe.



***


Dawowarsa kenan daga gidan, rashin ganin Meenah bata tarosa ba ya tabbatar tana makaranta don tace masa yau zatayi test har biyu.
Yana shigowa yaci karo da Jidda daga bakin k'ofa sai faman washe baki takeyi.
"Sannu." Tace dashi tana taunar chewing-gum, yayi tsaki yace
"Yauwa." Ya sa kai zuwa d'akinsa yana Allah wadaran da mace marar tarbiyya.
Yana zaune bakin gado yana cire safarsa ta shigo  sai wani cika take tana batsewa. Zama tayi gefensa tace
"Ya Faruk magana nazo muyi."
Yace
"Yanzu Jidda daga dawowata sai ki tare ni da wata magana kuma, ay kya bari in huta dai ko."
Tace
"Nidai ka bari na fad'a maka."
Ya dakata yace
"Ina jinki."
Tace
"Ay dai kace kai baka tauye hakkin iyalanka ko?"
Yace
"Haka ne."
Tace
"Yauwa, to tunda baka tauye hakkin iyalanka so nake ka barni na tafi Dubai, na karanta Fashion and Design."
Ya karkato yana dubanta yace
"Da igiyar wa?"
Tace
"Da igayarka mana."
Yace
"Kinga Malama banson zancen banza, ta yaya kina matar aure kawai don rashin hankali sai ki tafi wata uwa duniya da sunan karatu, ke bari ma kiji ni ba irin mazan nan bane da mata ke juya su yadda suka ga dama ba, don haka wallahi sai na sa6a maki kika k'ara yi min zance makamancin wannan."
Cike da shagwa6e tace
"Haba don Allah ya Faruk, wai ni meyasa kake min haka ne? Saboda Allah ita Meenah ay ka barta tana karatu sai ni zaka hana ni."
Yace
"Ita Meenah ba kina ganin cikin garinnan take ba? Yau ga zancen banza zancen wofi, ke nafa gaji da rigimarki haba! Mutum kullum da abinda zaice daga wannan sai wannan to wallahi na gaji."
Kawai ya tashi ya bar mata d'akin.
Ita kuwa sai tasa kuka tana ta magana ita kad'ai.


****

Ranar wata Juma'a Luby tazo gidan, nan suka baje suna fira. Jidda ta dubi Luby tace
"Luby gaskiyar magana nayi dana sanin wannan aure, banida tantama alhakin Meenah ne ke bibiyata, ke tunda nazo gidannan ban ta6a tsintar farin ciki ba daidai da rana d'aya ba, nikam na gaji wallahi auren ma ya fita raina, mutumin nan sai shegen kulle baya bani abinda nakeso, ga abin takaici wai Meenah yanzu tayi min in mata batada tsoro ko kad'an, ke wallahi aurennan na gama shi sai ya sake ni."
Zumbur Luby ta mik'e tana salati tace
"Yanzu Jidda abubuwa nata faruwa shine bansani ba? Baki iya fad'a min? Sai da abubuwa suka jagule miki suka fi k'arfinki shine zaki sanar da ni yanzu ko?"
Jidda tace
"Kiyi hak'uri Luby wallahi na d'auka zan shawo kan abin ne."
Luby tace
"Aiko sai mun d'auki fansar abinda tayi miki, bata isa ba, wacece ita? Ke kin bani kunya kinfa girme ta, amma kin zauna tana juya ki."
Jidda tace
"A'a Luby ke kinsani sarai mu da magani mukayi aiki, ita fa? Ay ba d'aya bane ba ma."
Luby tace
"Shikenan, amma kar kiyi saurin karaya, aure kuma yanzu kika soma shi, yo mekenan idan kika tafi tun yanzu, ay ko baki warci wani abu ba ni kya wabto mani, kuma ke ina son da kike masa? Ko dama k'aryar banza ce?"
Jidda tace
"Luby don bakisan irin wahalar da nake sha ba, babu fa yadda muka iya saboda matarsa tayi mana zarra."
Luby tace
"Wallahi k'arya takeyi! Kedai ba kina amfani da kwallin da turaren ba?"
Jidda tace
"Wallahi ina yi, kedai Luby munzo inda aka kere mu."
Luby tace
"Yanzu akwai wani abu a wurinki?"
Jidda ta girgiza kai
"Babu komai sai tarin wahala da takaici."
Luby tace
"To zan san matakin da zan d'auka, zan dawo anjima ko gobe."


Washe gari da sassafe ta dawo, ta d'auki Jidda amma sai da suka shirga ma Faruk k'arya sannan ya barsu da k'yar, shima akan kar su dad'e.
Suna tafe a mota Luby tace
"Kar ki damu k'awata, zan kai ki inda za'a share miki hawaye."
Jidda tace
"Ina kenan?"
Luby tace
"Me kike ci na baka na zuba, kedai ki tsaya ki gani."

Luby ta koro ma Barmuje bayani, yayi 'yan tsubbace tsubbacensa zuwa can yace da Luby
"An 6ata aiki ay, saboda tun farko sai dana fad'a miki kar ya wuce daren farko baiyi tarayya da ita ba, amma ina bakuji ba, sannan kuma sai da ya fara yin tarayya da uwar gidanki akanki, don haka aikinki bazai ta6a yin tasiri ba! A yanzu komai ya wargaje saboda uwar gidanki tana da rik'o da addini sosai, a gaskiya kafin wani abu ya kamata da wuya. Ina tunanin kawar da ita ne kawai zai baki damar mallakar mijinki don haka sai kisan abinyi."
Suka kalli juna itada Luby tace
"To yanzu meye abinyi?"
Barmuje yace
"Akwai maganin da zan baki, zaki zuba mata a wani abun sha, kamar koko, fura da sauransu, wannan abin da kike gani guba ce data sha ita da duniyar nan sai dai a lahira."
Luby tace
"Akwai wata hoda da ka bani jiya, inaga kamar zata fi yi mata amfani."
Yace
"Tabbas! Zaifi sauk'i sai dai zan k'ara gargad'inki da kada ki kuskura ki shak'i hodar nan don idan kika shak'a.... hahaha to kema zaki bak'unci lahira, idan kuma baki mutu ba... haha! To zaki wahala a nan duniyar sai kin zamo abin tausayi."
Luby tace
"Zata kiyaye ma."
Da haka suka baro dajin da Barmuje yake, suka dawo gida.
Luby tace
"Yanzu dai ga maganin nan, kuma kinji gargad'in Barmuje wallahi kibi a sannu."
Jidda tace
"Haba kar ki damu komai zai tafi yadda akeso."
Luby tace
"In ta mutu ki sanar dani, zan had'a mana grand party."
Jidda tace
"Ay dole ne ma wannan."
Suka k'yalk'yale da dariya gami da tafawa.
Daga haka sukayi bankwana Luby tayi gida cike da murna.


****

Meenah na kwance a d'aki tana baccin rana inda Jidda ta lalla6o da hodar a hannunta, Jidda ta huro mata hodar tayo baya da sauri, sai dai mey?  Memako Meenah taji wani abu sai ma ita Jiddar ta kurma uban ihu sakamakon jikinta dake mata rad'ad'i. Meenah ta farka tana salati sannan ta fito da sauri ganin meke faruwa.
Jidda ce a tsakar parlor tana kurma ihu tana soshe soshe, Meenah tayo kanta tana tambayar lafiya? Ture ta Jidda tayi, sannan tayi d'akinta da gudu ta fad'a toilet tayi wanka da ruwa masu sanyi sosai. Sai dai babu wani sauk'i data samu. Ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuka kawai takeyi, ga sam ta hana Meenah ta ta6a ta, sai surutai takeyi marassa kan gado.
Hijabinta ta saka ta fito parlor a lokacin Meenah na sallah d'akinta, aiko da sauri ta fito ta tafi gidansu.


Mama na d'aki tana sallah ta shigo tana kuka, sai tirje tirje takeyi, bayan Mama ta sallame ta juyo tace
"Ke lafiya..."
Bata k'arasa magana ba Mama taja baya cike da tsoron ganin fuskar Jidda kamar ba tata ba, Mama ta fito da gudu tana salati tana fad'in
"Wacece ke?"
Jidda na biye da ita tana dariya tana cewa
"Ni ce, nice naje wurin boka nida Luby muka anso magani zamu kashe Meenah."
Mama tasa salati tana fad'in
"Jidda. Meya kaiki? Mekika zama? Innalillahi wa inna ilahir raj'iun! Jidda."
Jidda tasa dariya, sai ta susa kai, ta susa jiki tana zum6uro baki tace
"Wai laifina ne? Kaji man Mama, nifa kawai d'ora ni akayi akan turbar nabi kuma."
Ana haka Dada ya dawo, shima cike mamaki yake tambayar lafiya. Mama ta kwashe komai ta fad'a masa abinda Jidda ke cewa.
Dada yace
"Da alama fa kamar hauka takeyi ko?"
Mama tace
"Nima shi nagani."
Suka sa salati, Dada yace
"Duniya budurwar wawa Jidda, Allah ya shiryeki, Hajiya kamo ta ki kai ta d'aki ki rufe kafin mu san abinyi."
Tace
"To."
Ta kamo Jidda, tana tirjewa da k'yar suke tafiya, Jidda taci kwalar Mama tana dariya tace
"Ina zaki kaini? Iye?"
Mama tace
"Muje d'aki ki kwanta."
Jidda tasa dariya, can kuma tasa kuka, can tasa dariya, sai kuma tasa kuka, ta jawo hancin Mama ta matse tace
"Daman haka boka yake? Laifin duk na Luby ne saboda ita ta kaini tun farko, saboda ban ta6a zuwa ba ay ko?"
Mama tana kuka tace
"Eh muje."
Mama ta sha wahala don da k'yar ta kai ta d'aki ta rufe, sai dai taji ana bubbuga k'ofar ana ihu, can taji dariya, can taji surutai, can kuma taji ana cewa
"Boka, boka, Barmuje sunansa."
Mama tayi tsaye tana kuka, tace
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Jidda kinga halin da kika jefa kanki ko? Kinzo kiyi wa wata asiri ya dawo kanki, duniya ina zaki damu? Ka haifi d'a amma baka haifi halinsa ba. Allah ka shirya shine kawai abinda zan ce miki Jidda, Allah kuma ya yaye miki."
Dada ya kira Faruk ya sanar masa yazo yana nemansa yanzu yanzu.


Ba'a d'auki lokaci ba ya iso, Baba ya kwashe komai ya fad'a masa, Baba ya d'ora da cewa
"Ina so idan ta warke ka sallame ta, baka buk'atar cigaba da zama da ita, tunda har kamar Jidda tasan tayi kisa ay kaga zama da irinsu ba amfani.
Faruk yace
"Allah ya kyauta, Allah kuma ya bata lafiya."
Baba yace
"Amin."
Faruk yace
"Bari na dubo ta, daga nan sai na nemi asibitin da za'a kaita."
Baba yace
"To kabi a hankali, don jikin ba dad'i."

A hankali ya tura k'ofar d'akin tana zaune dirshen a k'asa tana kwa6a sabulu da toothpaste cikin wata roba, ya kalle ta duk ta shafa ma kanta, ya zauna a bakin gado yana kallonta cike da tausayi, wannan wace irin rayuwa ce? Wai Jidda tasan taje wurin boka? Ya kalli Dada dake tsaye a bakin k'ofa sannan ya maida dubansa ga Jidda da ke shafa sabulun a jikinta.
Ya gama kallonta yayi mata adduo'i sannan ya tashi ya fita.
Ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba ya je ya nemo asibitin da za'a kaita, daga nan aka kwasheta da da k'yar daga gidan. Faruk ya sanar ma sauran 'yan uwanta suma sunyi jimami sosai, daga k'arshe sukayi mata fatan shiriya da samun lafiya.


***

MSB💖

No comments: