Friday 21 July 2017

AUREN FANSA 24

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹



          🌹24 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com


Baba na zaune a parlonshi ya kira Bilki yace ta turo masa Meenah.
Tana d'akin Zarah a bakin gado tayi tagumi, Zarah kuma na jera kayanta cikin wardrobe da aka kawo daga wurin wanki da guga da safe.
Bilki ta shigo d'akin, da sauri Meenah ta d'ago fararen idanunta ta kalle ta, kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da tana cikin damuwa mai tsanani, take Bilki ta 6alla mata harara tace
"Taso muje."
Ta mik'e a sanyaye tabi bayan Bilkin har parlon Baba, jikinta yayi matuk'ar yin sanyi.
Baba na duba newspaper da idanunsa mak'ale cikin farin gilashi a lokacin da suka shigo.
Ya ajiye takardun gefe ya kuma cire gilashin yabi Meenah da kallo a lokacin da take zama kan carpet, sai ya saki murmushi yace
"Aminatu jiya wannan yaron Faruk yake sanar dani cewar yana sonki, kuma yana so in bashi izini don ya turo da magabatansa, k'warai na yaba da hankalin yaron da kuma nutsuwarsa, amma kinsan bazanyi saurin yanke hukunci kai tsaye ba, ina so inji ta bakinki tukunna. Shin Amina kin amince Faruk ya turo da iyayensa ayi magana, ko kuma baki amince ba?"
Farin ciki marar misaltuwa taji ya lullu6e ta har ta gaza 6oye hakan, take kuma ta sadda kanta k'asa fuskarta d'auke da k'ayataccen murmushi. Ta kai dubanta ga Bilki taga yadda ta had'e rai tayi murtuk.
"Amina." Ta d'ago ta kalli Baban tace
"Na'am Baba."
Yace
"Ke nake sauraro, shin kin amince Faruk ya turo magabatansa ko baki amince ba?"
Da k'yar ta bud'e baki saboda matsananciyar kunyar da takeji tace
"Haka ne Baba, kuma na amince."
Yayi murmushin jin dad'i yace.
"Alhamdulillah, idan yazo kice ya turo magabatansa, Allah yayi muku albarka."
Kanta na k'asa tace
"Amin Baba."
Yace
"Tashi ki tafi."
Tashi tayi ta  fita. Tana fita Bilki tace
"Alhaji!"
Ya dube ta yaga tayi kicin kicin da fuska yace
"Lafiya dai Bilkisu?"
Dama kamar jira take tace
"Haba Alhaji don me zaka biye wa yarinya daga tace tana son mutum sai ka d'auke ta ka bashi, sannan baka ganin yarinyar nan k'aramar yarinya ce duka duka nawa take da zakayi mata aure yanzu? Ko university fa bata shiga ba, gaskiya ni ban amince ba sam." Sai ya kalle ta yayi murmushi yace
"A lokuta da dama ku mata kuna bani mamaki, kina k'in auren Meenah ne saboda k'aramar yarinya ce? To ni banga k'ank'anta a tattare da ita ba, shekaru goma sha bakwai gareta idan baki manta ba wata mai zuwa shekararta goma sha takwas, a hakan ne kike ganin yarinya ce?"
Tayi shiru tana ciccin magani. Ya cigaba
"Babu wani abu da iyaye zasuyi alfahari dashi face suga sun aurar da 'ya'yansu, shine kad'ai kwanciyar hankalinsu saboda idan zaki auna karatu baifi aure ba, haka zalika zata iya cigaba da karatunta d'akin mijinta. Saboda haka nake gargad'inki da kiyi gaggawar kawar da wannan gur6ataccen tunaninki ki koma hanya madaidaiciya." Jiki a sanyaye tace
"Kayi hak'uri Alhaji, a had'o shayin ne ko sai anjima?"
Yace
"Bari sai anjima."

A ranar duk wanda ya kalli Meenah yasan tana cikin matanancin farin ciki.
Cike da farin ciki ta lalubo wayarta ta kira Faruk, bugu biyu ya d'auka.
"My baby." Ya fad'a yana murmushi. Tayi murmushin jin dad'i. Tace
"My soul." Sunan ta dake kiransa kenan.
"Albishirinka!"
Yace
"Goro."
"Fari ko ja?"
Yayi dariya
"In banda abinki ya ina ganin farin goro zan d'auki ja? Ay farin zan d'auka."
Tayi murmushi
"Haka ne, to Baba ya baka izini ka turo iyayenka my soul."
Yace
"Wow alhamdulillah! Gaskya nayi farin ciki insha Allah zan sanar da Dada, i love you so much my baby Allah ya nuna mana ranar auren mu lafiya."
Tayi murmushin jin dad'i tace
"Amin my soul love you too, bari naje Mami tana kirana sai anjima."
Yace
"Awwn kamar kar ki tafi, amma zan kiraki anjima, take care."
Sukayi sallama ta kashe wayan, yana cire wayan a kunnensa ya hango Najeeb tsaye a bakin k'ofa yana kallonsa. Ya hau susan kai yace
"Najeeb me kakeyi a nan? Ka k'araso ciki mana."
Najeeb yayi ajiyar zuciya ya k'araso ciki ya zauna gefen Faruk kan gado tare da dafa sa. Yace
"Faruk a gaskiya banga dalilin da zaisa ka yaudari yarinya ba alhalin ba itace tayi maka laifi ba."
Faruk yayi murmushi yana kallon Najeeb yace
"Don na yaudare ta shine me? Wannan shine first step da zan d'auka shine auren d'iyarsu!"
Najeeb yace
"Faruk da zaka ji shawarata da ka k'yale yarinyar nan akwai hanyoyi da dama da zaka d'auki Fansa ba dole sai ta wannan hanyar ba, she's too innocent wallahi dana ganta ta bani tausayi."
Nan take Faruk ya fara huci, bak'in ciki had'e da 6acin rai suka taru suka masa dirar mak'iya! Ya mik'e a lokacin ne kuma idanunsa suka sauya kala daga fari zuwa ja tsabar 6acin rai, shi kanshi Najeeb ya tsorata da ganin yanayinsa. Faruk ya soma magana cikin 6acin rai.
"Najeeb! Kar ka manta alk'awarin da na d'auka a baya, na k'watar mana 'yancinmu, auren Meenah shine abu na farko da zanyi, don gudanar da duk wani bincike na da zanyi. Idan har ban auri d'iyarsu ba ta yaya zan cimma burina na gano musabbabin yadda aka kashe mana iyaye? Dole sai na kusance su, sun yarda dani sun kuma amince dani, ta haka kad'ai zan sa ido sosai akansu. Bayan haka! Sai nasa sun raina kansu, sai sunyi dana sanin abinda suka aikata, ita kanta Meenah lokacin kad'an nake jira dana aure ta zan kuma wulak'anta ta, dole idan nayi haka abin zaiyi wa iyayenta zafi, to wannan kad'an ne daga cikin abubuwan dana tanada!"
Najeeb ya mik'e tsaye da sauri zuwa inda Faruk ke tsaye.
"Dan girman Allah ka sauke k'udurinka na wulak'anta d'iyarsu, bata ji ba bata gani ba, haba ya laifin iyayenta zai shafe ta?"
"Ya shafe ta! Kai harta karensu ko magensu laifin ya shafe su, na tsane su, na tsane su! Na tsane su! Wallahi duk sadda na kalli Meenah ko wani nata sai na ji kamar yanzu nake kallon gawar iyayena kwance cikin jini."
Ya runtse idanunsa gam gami da dunk'ule hannu, take jijjiyoyin kansa suka mik'e tar!
"Ka barni na cigaba da abinda na sa gaba, abinda kawai nake buk'ata daga gareka shine fatan alkhairi, amma idan ba wannan ba to bana buk'atar shawararka." Ya fad'a cike da 6acin rai
"Haba Faruk! Meyayi zafi haka? Kayi hak'uri don Allah ka kwantar da hankalinka, mubi komai a sannu, insha Allah zaka cimma burinka."
Take yayi murmushi. Rungume Najeeb yayi yana fad'in.
"Yawwa ko kaifa, haka ya kamata ka fad'a."
Najeeb ya k'ak'alo murmushi kurum.


*

Da daddare bayan Dada yaci abinci sai ya aika a kira masa Faruk, bayan ya shigo parlon Dada yana kallon tashar BBC, rage volume yayi yana kallon Faruk sadda yake zama kan carpet, bayan ya gaishe shi kamar kullum Dada ya soma magana.
"Faruk dalilin da yasa na kiraka shine, naji labarin daga wurin Hajiya cewar ka samu matar da kake so haka ne?"
Yace
"Haka ne Dada."
Dada yace
"To alhamdulillahi, daman abinda nake jira kenan Allah yasa albarka 'yar gidan waye?"
Faruk yace
"Sunan mahaifinta Alhaji Hamza, 'yan garin Katsina ne amma nan garin yake aiki baban nata."
Dada yace
"To yayi kyau, da fatan kayi k'wak'waran bincike kafin ka fara soyayya da ita?"
Yace
"Eh Dada, mahaifinta ma'aikacin banki ne, shine manager na First bank yanzu haka, kuma mutumin kirki ne, to yama ce na fad'a maka na tura magabatana a yi magana."
Dada yace
"To alhamdulillah, indai wannan ne babu matsala kar ka damu zamu je insha Allah, ni na d'auki nauyin komai kai da k'anwarka, zan shirya nida Alhaji Musa da Alhaji Sufyan (k'aninsa da yayansa) sai muje insha Allah. Jeka kira min Nabeel da Najeeb."
Yace
"To Dada."
Ya mik'e ya fita, ba'a juma ba suka shigo tare gaba d'aya, bayan sun zauna Dada ya fara magana.
"Kamar yadda nayi muku alk'awarin gina muku gidaje, to an kammala, ga ma makullen nan, kai Nabeel bazan baka ba sai ka samo wacce zaka aura, amma da Faruk da Najeeb su tunda suna da wad'anda suke so, sheyasa zan damk'a masu takardun gidajen da kuma mukallen. Sai kuma anyi maku order d'in motoci guda uku, zasu iso nan da sati d'aya insha Allah. Sai abu na k'arshe maganar lefenku Hajara (k'anwarsa) na damk'a mata ragamar yin lefe na kowanenku, abinda zakuyi list sai ku rubuta duk abinda kuke buk'ata, Allah yasa alkhairi yasa ayi damu."
Suka amsa da "Amin." Sannan kuma suka shiga jero masa godiya marar adadi tare da fatan alkhairi.
Sai yanzu Faruk ke tunanin anya zai iya cin amanar Meenah kuwa? Ko don albarkacin Dada wannan kaya da ya masa haka? Sai dai ya k'udiri a ransa ya zama dole ya d'auki Fansa kota wani hali ne! Jikinsa yayi matuk'ar sanyi a yayinda dayake fita daga  parlon.



MSB💖

No comments: