Monday 3 July 2017

AUREN FANSA 15

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹



          🌹15 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com

Ba'a fi minti biyar ba suka kunno kai, ko wanensu yana tura trolley nasa, tunda suka fito Jidda ke kallonsa ya za'ayi ta mance da wannan fuskar?
Ya chanza gaba d'aya ya zama wani babba, k'irar jikinsa kansa abin kallo ce irin giant
 d'innan, abinka ga fari sai ya k'ara murjewa ya zama bature sak! Ta kalleshi yana murmushi.
"Sannu da zuwa yaya!" Anisah ta ruga tare da mak'alk'ale shi, a yayinda Yusra ke mak'ale da nata ya'yyen, sai a lokacin Jidda ta dawo duniyar tunani.
Da k'yar ta daidai nutsuwarta tace
"Sannunku da zuwa!" Ko alama bai gane ta ba.
"Yauwa sannu... Jidda ko?"
"Wow haka muryarsa take?" Ta fad'a tana k'ara kallonsa cike da mamaki. Tace
"Eh nice yaya."
"Wow duk kun girma..."
Suka taya su jan kayan nasu har bakin mota. Tafiya suke amma idonta na kansa. Abu d'aya take maimaitawa a zuci...
"What kind of change is this?"
Haka aka loda kattunan jakunansu a boot.
Koda suka shiga mota shi ya zauna gaba, daga baya babu abinda Jidda keyi sai aikin kallonsa.
"Ya Faruk? Ya Faruk? Ya Faruk?" Wannan abu shi take ta fad'i a ranta. Ta d'an k'ara kallonsa ta baya, gashin kansa kad'ai abin kallo ne, ya k'ara kyau akan wanda yake dashi da, sai shinning yake kamar taurari a sama...
"Anya bayada iri da larabawa?"
"Wa kenan?"
Ta kai dubanta tana kallon Najeeb daya tsareta da kallon tuhuma, tace
"Uhm uhm bangane ba."
Nabeel yace
"Rabu da ita tun d'azu na lura da yadda ta chanza."
Tace
"Na chanza kamar ya?"
Najeeb yasa dariya.
"Kamar yadda kika fahimta."
Daga nan ba wanda ya tanka har suka iso gida.

Mama harda d'an gudunta tana fad'in
"Welcome home."
Suka shiga parlor Najeeb ya kalli matan yace
"Ku kai mana kayanmu d'aki."
Sannan ya maida kallonsa da Mama.
"Bari mu d'an watsa ruwa muyi sallah."
Mama tayi murmushi
"Eh hakane lokacin sallar azahar yayi ya kamata ayi sallah sai aci abinci, sannunku da hanya."
Nabeel yace
"Yauwa Mama, ina Dada?"
Tace
"Yana Ireland yau satinsa d'aya da tafiya, amma insha Allah ya kusa dawowa."
Najeeb yace
"Ok... hakane munyi waya yake fad'a min batun tafiyar tasa Allah ya dawo dashi lafiya."
Aka amsa da "Amin"
Daga haka kowa yayi hanyar d'akinsa.

Faruk d'akinsa ya burgeshi yadda yayi tsab sai k'amshi da sanyin ac ke ratsa dukkanin illahirin jikinsa, bai tsaya wata wata ba ya fad'a toilet.
Yana gamawa ya saka k'aramar riga da dogon wando.
A dinning aka hallara kowa yayi serving kansa jollof d'in shinkafa, da pepper soup, sai kaza gasassa sai salad.
Sun fara cin abincin ne Mama tace.
"Alhamdulillah, Allah na gode maka daka nuna man wannan ranar, ranar da 'ya'yana suka kammala karatunsu lafiya, fatana Allah ya albarkaci karatunku, Allah ubangiji ya baku sa'a."
Gaba d'aya sukace "Amin amin."
Ta cigaba
"Yanzu dai ga Likita Najeeb, ga Detective Faruk, ga kuma Banker Nabeel, kai masha Allah! Allah yayi albarka."
Suka ce "Amin Mama mun gode Allah ya saka da alkhairi."
Tace
"Amin, yanzu dai ya kamata kuyi settling kowane ya nemi mata yayi aure, shine kad'ai abinda ya rage."
Duk kansu k'asa basu ce komai ba, itama Mama murmushi tayi a haka suka cigaba da cin abinsu.


***


Bayan Wata D'aya...!


Zaune yake kan kujerar office d'insa yana faman dube dube a computer d'insa, aka shigo da sallama, a hankali ya d'aga ido ya kalli k'ofa yayi murmushi.
"Ah Usman! Shigo mana ya zaka tsaya a bakin k'ofa?"
Ya k'araso yana gaishe shi
"Ina wuni sir?"
"Lafiya lau zauna magana zamuyi."
Bayan ya zauna, Faruk ya soma magana.
"Wani aiki zan saka, don Allah ina so duk abinda nake nema ka yi k'ok'ari wajen ganin ka samo min duk wani abu zan buk'ata."
Usman yace
"Insha Allah, ay ba yau ka fara sani aiki ba, kuma duk lokacin da kake sani abu ina k'ok'ari waje ganin na gano maka koma me kake nema."
Faruk yace
"Haka ne, to yau ma ina tafe da wani aikin mai matuk'ar mahimmanci a wurina."
Ya fad'a yana fiddo wani abu a cikin drawer d'in table d'insa.
"Karanta kaga."
Da ladabi ya kar6a ya soma karantawa. Bayan ya gama yace
"Yalla6ai amma suna ne kawai nake gani."
Faruk yayi wani d'an guntun murmushi yana juya kujerar da yake zaune akai. Sai da ya d'auki tsawon mintina biyu zuwa uku sannan ya soma magana.
"Eh sunaye ne na mutum biyu, bincike nake buk'ata akansu."
"Toh yalla6ai."
"Yawwa, i want every bit of information regarding them. Ina buk'atar komai idan nace komai i mean everything. Wane gari suke? Wace unguwa? Sunada 'ya'ya? Guda nawa ne? Suna da miji? Meye sunansa? Wane aiki yake? Ina da ina suka fi zuwa? Wace makaranta yaransu suke? Don't left out anything, including their photos."
Usman ya gyara zamansa yana fuskantarsa.
"Angama amma yalla6ai meyasa kake neman information d'innan haka? Sannan ta ina zan samo hotunan su?"
Faruk ya mik'e tsaye tare da dawowa gaban Usman gami da zama saman table a kusa da shi yace
"Usman bana son shishigi, aiki na saka shi zakayi min, kawai kaje ka kawo min abinda na saka please banda wasa, sannan hotunansu wannan kai zaka nemo."
Usman yace
"Hakane insha Allah zanyi k'ok'ari."
"Yauwa kana iya tafiya."
Daga haka ya fice, inda Faruk yayi murmushi yace.
"This is my first step towards my goal, waiting for the next step."
Yayi murmushi yana kad'a kai.



MSB💖

No comments: