Tuesday 22 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 23

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 23}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



2 WEEKS LATER

Tun ranar da Sultan ya sauke Hoodah gida bai sake waiwayarta ba, bai kira ba baiyi text ba, gashi Abba yayi wata tafiya baya kasar ma, nan ita kuma Umma ashe babu abinda ya chanza, a wurin Kaka ne kawai take samun kulawa da nutsuwa, gashi Kaka ta dada tsufa ciwon yau daban na gobe daban batada lafiya, aikuwa Umma ta baje ganin Abba bai nan gashi Kaka batada lfy ta dinga gana ma Hoodah azaba. Wata rana tana zaune cikin dakinta tana danne danne a wayarta kawai sai ga Umma kamar an hankado ta, Hoodah ta mike a tsorace tana kallonta, Umma tace "Wai ke ina mijinki da zai zo ya aje ma mutane ke yayi tafiyarsa?" Inda inda ta fara "Zai zo ya daukeni yana wani aiki ne..." dungurinta Umma tayi ta juya ta rufe dakin gam yadda ko wani yazo kwatarta bazai iya shigowa ba, dan so take yau taji uban meye ya hada su da Sultan dan bata yarda da abinda Hoodah ta fada mata ba, so take taji abinda takeso taji wato ya wulakanta ta ya koro ta! Baya baya Hoodah ta fara yi ganin Umma ta nufo ta kamar wata yunwattaccen zaki "Don Allah Umma ki tsaya, karki dakeni! Wallahi abinda na fada maki iyakar gaskiya ta ce, don Allah karki dakeni." Kuka ta fara yi har ta kai bango ta runtse idanunta gam duk a tsorace take, wani irin mari ta dauke ta dashi har guda biyu a jere take ta kara rikicewa ta fashe da kuka har kyarma takeyi duk ta fita hayyacinta, "Wai ke mahaukaciyar ina ce? Dan uwarki nace ki fada man meya hadaku amma kike man karya ko? Ko ce maki akayi ni karamar yarinya ce?" Cikin kuka tace "Gaskiya na fada maki babu abinda ya hadamu, yana wani aiki ne sai ya gama zaizo ya daukeni!" Tace "Toh naji amma meya hanashi zuwa ko sau daya tunda ya ajeki!" Ta fara kyarma "Aiki ne ya masa yawa sheyasa...." shako ta tayi "Karya kike dan uwarki! Nace ki fada man uwar me kikayi masa? Ko iskanci kikayi masa ya koroki?" Tace "Ni ba yar iska bace ba!" Wayarta ta warce cikin sa'a taga ba password nan ta lalubo number Sultan ta fara kiranshi, tun yana rejecting, daga karshe ma sai ya barta tanata ringing. "dan uwarki nasan karya kikayi man yanzu gashi nan yaki dauka! Ki fada man nace me kikayi mashi ya koro ki?" Hoodah tace "Maybe he's busy ki gwada kira kigani ko zai dauka." Tsaki tayi ta sake dialing number din, cikin sa'a kuwa bugu biyu ya dauka Umma tasa ma Hoodah a kunne tana kyarma tace "Sul....tan!" Muryarta har wani daukewa tayi, jin muryarta yayi tun daga saman kanshi har tafin kafarshi, dama yana cikin hotel din daya sauka zaune shi kadai abun duniya duk ya ishe shi, ji yake kamar ya ganta gabanshi ya rungume ta amma ya dake, har zai danna ya kashe kawai yaji ta fara kuka "Sultan don Allah yaushe zakazo? Kazo kafin Umma ta kasheni don Allah ba don ni ba!" Bata ida magana ba kit ya kashe wayar, bata san lokacin da ta ture Umma ba ta bude kofar ta fita a guje, haka Umma ta bita da gudun itama har kofar gida nan Umma ta umarci bayinta da su bi bayanta su kamo mata Hoodah, sunkai tsawon minti ashirin suna zagaye cikin gidanan har daga karshe sukayi nasarar kamata mutum biyu ke rike da ita, suna tsaye bakin gate dinsu suna kokowa da Hoodah kawai taganshi tayi tsaye jikin mota ya juya yana magana da wani yaro alamun kiranta zai sa ayi, wasu hawaye suka gangaro mata kafin kace mey ta fara kukan fitar hankali kamar ance mata gawar Sultan ce aka kawo, yaron ne yace ay gata nan ma tafito a hankali ya juyo suna hada ido yawani sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, wani karfi yazo mata ta bankade su ta ruga a guje tayi hugging dinshi, kuka ta fashe dashi mai ratsa zuciya, take yaji zuciyarshi ta tsinke yayi hugging dinta back, saidai ta gaji dan kanta amma fa ko uffan bai ce mata ba, tausayi ta bashi ganin yadda ta koma kamar wacce ta shekara a kwance tana jinya, a hankali ta janye daga jikinshi tana faman share hawaye, a hankali yasa hannu yana share mata hawaye "Tou kukan ya isa haka, ba gani nazo ba? Menene ya faru waya taba mun ke?" A hankali yake maganar yana jin sonta na kara fizgarshi kamar ma sonta ne zaiyi ajalinshi, hannunta ta daga tana nuna mashi Umma da bayinta dake tsaye hannunta har kyarma yakeyi, Umma ta wani hade rai tace "Dan uwarki ba ciki kikayo ba ya koroki?" Da wani shock take kallon Sultan tana girgiza kai "Banida ciki, Umma haka take bata son ganin farin cikina ka yarda dani," ta fada a rude ganin yadda yake bin Umma da kallo baki bude can ya juyo yace "Ciki? No no I cannot accept this pregnancy! Am sorry I can't." Wani irin heartbreaking step tayi taking back tana kallonshi hawayenta ma sun kafe, "Karka hukuntani akan abunda baka da tabbas a kanshi, I know she's lying, abinda kayi man kadai ya isa na horu, ka yarda dani don't listen to her she's a witch!" Shiru yayi can ya furta "Anything can happen, ko a cikin gidan nawa ne." Ya fada cike da kokonta part of him ya yarda da ita wani part din  kuma  bai ma sani ba, wani kukan kura Umma tayi ta fizgo Hoodah bata tsaya wata wata ba ta fara dukanta, Hoodah tana ihu tana rokonta akan ta kyaleta, shi kuwa Sultan tsaye yayi kamar gunki kamar wanda aka dasa ya kasa motsi, wata irin tsawa Umma ta daka mata "Ni kike kira witch?" Take ta daga kafarta ta kai mata wani irin harbi a kirjinta da cikinta, wani irin gigitaccen ihu ta saki take ta silale a gurin, ta zube kasa idanunta na wani kakkafewa "You're going to loose me forever Sultan, I know you love me amma yau na tabbatar a yau that your love is weak tunda ka kasa cetona." A hankali take fada amma baiyi missing ko word daya ba a hankali idanunta suka dinga rufewa, idanunta kyam a kansa Umma na cigaba da jibgarta bata ma yi wani motsi ba ta barta ta cigaba da dukan nata, take jikinta ya saki, wani irin ihu Sultan ya fasa "Hoodaaaah!" ay baisan lokacin da ya rugo a guje ba yayo kanta ya zube kasa ya dinga jijjigata da karfi hawaye na zubo mashi babu abinda yake furtawa sai "I am sorry." Mikewa yayi yana kallon Umma dake ja baya ya wani damko ta a fusace, yana shake da ita ya ciro wayarshi ya sa aka kira mashi DPO yayi magana dashi ya kashe wayar. Ko cikkakken minti biyar ba'ayi ba sukaji jiniya da kugin yan sanda, yan sandan suka dinga durowa daga cikin motocin suka yo kan Umma yace suyi arresting din Umma da tayi mutuwar tsaye. Juyowa yayi ya kalli ogansu yace "Ku tafi da ita, zanyi magana da manyanku." Sultan a hankali kamar wanda kwai ya fashe mawa a jiki ya tako inda take kwance kamar marar rai ya sureta. Har ya turata mota ya rufe ya juyo kenan zai zagaya ya shiga shima kawai sai ganin Abba yayi kamar daga sama yana huci, "Maza ka kirasu su sakar man mata!" Ya juyo yana kallon Sultan cike da tsana, dan sunkuyawa yayi alamar girmanawa yace "Abba barka da wuni?" Yana fadan haka ya mike da sauri zai shiga motar don shidai tunaninshi bai wuce halin da Hoodah ke ciki ba, "Da ban wuni ba da ka ganni a nan? Sultan kake ko wa? Wallahi tallahi ka gaggauta fito man da matata a sako man ita tun muna shaida juna dakai! Dan ta d'an daki wannan yarinyar shikenan? itama ba kamar yar cikinta ta dauke ta ba? Kasani ko wani rashin kunyar tayi mata ta daketa? Ba uwarta bace? Ba ance nan ka barta wata da watanni ko waiwayarta bakayi ba ko ace maka bansani ba? Ohh sai yanzu ka damu da ita, ka sakar man mata na fada maka kasan ko ni wanene a garinnan zanfa sa a daure man kai! Ko kasheta tayi ina ruwanka? Yarka ce?" Baki sake Sultan ke kallon Abba in shock, so this is the what Hoodah has been telling him all along akan Abba da Umma? Ashe makircinta ya kai haka? What a life? Sai yaji ta kara bashi tausayi ya juya yaganta unconscious, "Amma Abba baka tunanin yanzu the most important thing to us shine rayuwar Hoodah? Zata iya rasa ranta fa kuma duk a sanadiyar your so called wife!" Bai taba tunanin akwai ranar xai wa Abba rashin kunya ba sai gashi ranar tazo. Ko kara kallon inda Abba baiyi ba ya bude mota ya shige, kofar motar Abba ya rike gam yace "Ina fada maka ka sakar man mata kana wani maganar marar lafiya! Yarinyar nan raki ne da ita baka santa bane, abinda ya fiye maka alkhairi shine ka sakar man mata!" Shiru yayi cike da mamaki "Abba kayi hakuri amma nidai xan wuce da ita asibiti, dama ni na kawota toh na dawo daukarta daga asibiti ma idan an sallameta bazan dawo da ita nan ba in ma kayanta ne idan tana bukata zan aiko a karbar mata." Yana gama fadan haka bai kara koda second biyar ba ya cire hannun Abba daga jikin motar ya rufe ya bar unguwar gaba daya, yana kallo ta mirror yadda Abba ke zazzaga masifa har dai kaka ta fito tana faman janshi su koma ciki abun kunya ne aga sarki a haka kofar gida yana masifa, shidai kawai girgiza kai yakeyii. Agadez Hospital ya nufa suna isa nurses sukayi gaggawar tafiya da ita emergency, zaune yayi a reception ya rasa wa zai kira ko yaji sassauci, sai a lokacin yaji hawaye ya kawo idonsa suka sauko mashi, mai ya aikata haka ya cutan da yar mutane? What has gotten into his dull brain? Wani irin haushin kansa ya dinga ji, sai can wajen la'asar kafin Doctor din ya fito yanata masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, ko gane fadan baiyi shidai kawai burinshi bai wuce yaje yaga halin da Hoodah take ciki ba, mikewa yayi tsaye dayaga doctor din baida niyyar yin shiru yace "Yanzu a ina zan ganta?" Don dama ya riga ya biya kudin baki daya "Room 12." Abinda ya fada kenan Sultan ya juya ya fita da sauri, duk taku daya dayake kusantar dakin da Hoodah take wani irin bugu zuciyarsa keyi kamar ta bulo kirjinsa, daidai dakin ya tsaya yana maida numfashi kafin a hankali ya murda handle din ya kutsa kai ciki, kwance ya isketa tana bacci fuskar nan tayi wani fau hannunta drip ne yana shiga cikin veins dinta, ganin yadda take numfashi ba karamin tsorata shi yayi ba kamar she's struggling to breathe duk da kuwa oxygen din da aka saka mata, wani pain yakeji a kirjinsa yanzu fa duk a sanadinsa hakan ya faru da ita ko babu wanda yaja mata in ba shi ba he's responsible for all that has happened to her, har bakin gadon ya taka yana kare ma fuskarta kallo, shidai abun ya masa yawa ga Hoodah ga iyayensa da wane zaiji? Zama yayi kan kujerar dake gefen gadon a hankali har yanzu bai daina kallon fuskarta ba, hannunta ya riko mai drip din very carefully yana dan murzawa. Bata farka ba sai can bayan sallar isha'i, ko bude ido batayi ba ta fara neman ruwa, shaf ya manta ana siyo abubuwa a aje, kamar zai tashi sama ya fita daga dakin yaje shop din cikin asibitin ya siyo ruwa da drinks da sauran abubuwan da za'a bukata ya dawo. Lokacin da yashiga ya sameta ta bude ido tangaram ga Doctor da nurses dake kanta suna examining dinta, yana shigowa ta daga ido ta kalleshi bata sake kallon wurin ba, kallo ne mai cike ma'anoni, kallo ne irin wanda ya maka babban laifi kake masa irinshi, saida suka gama dubata sannan suka fita, a hankali ya taka inda take ya bude ruwan ya mika mata kin karba tayi ta juya mashi baya, soyake yayi mata magana ko da hakuri ne ya bata yasan ya aikata babban laifi a gareta, rufe kwalbar ruwan yayi jiki a sa6ule ya haye gadon yayi hugging dinta, tana jin haka sai ta fashe da kuka baisan yadda akayi ba shima sai jin hawaye yayi suna sauko mashi, kuka sukeyi mai cike ma'anoni daban daban, "Habibty me ma zance miki? I just want to apologize please habibty ki saurareni." A hankali ta ture shi daga jikinta hannunta har wani rawa yakeyi "Don't ever call me that! Sultan din dana sani da bashi bane wannan Sultan din marar tausayi marar imani, ba kai bane mijina Sultan wannan mugu ne wanda baya tausayi na...." ta fada tare da juya fuskarta gefe tana cigaba da zubar hawaye....

No comments: