Monday 21 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 22

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 22}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Kamar wata marar lakka haka ta dauki madaidaicin akwati ta fara hada kayanta, tasan yadda yace zaiyi kwana goman nan ita sai ta wuce haka a agadez, zuwa yanzu ma hawayen sun daina zuba ta koma kukan zuci, bayan ta gama hada kayanta tsab, zuciyarta kamar ana zuba mata garwashi haka takeji, hijab ta saka maroon color ta dauko hand bag ta saka wayarta da sauran abubuwan da zata bukata kafin ta fita. Booth ta gani a hangame ta saka kayanta a ciki ta zagayo ta shiga driver ya jasu ya kaisu airport. A cikin jirgi ne ya juyo ya kalleta yaga tayi wani fayau ta rame kamar wacce babu jini a jikinta, sam jikinta babu karfi kamar wacce ta shekara tana jinya. 

Har suka kusa isa Agadez babu wanda ya ce uffan a cikinsu, sai can ta juyo ta kalle shi tace "Ka taimakeni ka sakeni Sultan, idan munje agadez ka bani takardata in yaso sai ka dawo kai." Wani irin juyowa yayi har yana neman sarkewa, "Me kikace? Saki? Ay tsakani na dake babu maganar saki." Ta fashe da kuka "Toh meyasa kake azabtar dani Sultan? Babu abinda nayi maka fa baka tunanin kana daukar alhakina?" Wani mugun kallo ya watso mata take ta kara karfin kukanta ta duke bisa cinyarta ta dinga sheshekar kuka wane ana zare mata rai, har suka isa Hoodah bata daina wannan kukan datake ba, ko kallonta baiyi ba yace "Idan kin gama kukan zaki iya fitowa." Uber yayi masu suna tsaye suna jiran motar ya dauko mata robar ruwa ya bata ta wanke fuskanta, har motar ta iso sannan suka shiga har kofar gidan su Hoodah aka tsaya, sai ganin Sultan tayi baida niyyar fita ya wani hade rai kai kace bai taba dariya a duniya ba, "Ki fita daga cikin motar nan, ko gidan naku ne baki gane ba? Ko akwai inda za'a ki?" Mamakin rashin tausayinsa takeyi sai kace ba Sultan din da tasani ba shagwa6a6e ba, yana fadin haka ya janyo wayarsa ya fara latsawa ba tare da ya sake koda kallon inda take ba, tafi minti biyar tana kallonshi kafin ta hadiye kukanta mai cike da bakin ciki da takaici, "Sakina kayi?" Dan ita bataga dalilin maido ta gida da yayi ba, ko kallonta baiyi ba yace "In sakinki nayi ay xan fada maki!" Share hawayenta tayi tace "Akwai ranar da zakayi dana sani Sultan, amma still kasani zan yafe maka kuma zan fahimce ka, sannan duk ina alkwarin I have you in my life? I will always be by your side? Ko dayake it's fine I totally understand Just know that zaka dawo da kanka kana rokona gafara good bye." Tana gama fadin haka ta fita daga motar ta bude booth ta kwashi kayanta ko kallon inda yake bata kara yi ba ta shige gida. Ya kusa kai minti goma yana kallon gate din gidansu kafin yace da driver din su tafi inda zai sauka. Hoodah ba karamin mamakin irin tarbar da Umma tayi mata tayi ba dan sosai ta tarbeta hannu biyu biyu harda taimaka mata ta sauke kayanta daki, Abbanta ma yaji dadin ganinta sosai yayi kewarta, kamar yadda Sultan ya fada mata cewar ten days zaiyi itama haka tace masu ay kwana goma zasuyi....

*******

Wani irin wahalallen amai takeyi kamar xata amayo yan cikinta, "Innalillahi Khairy me nake gani haka? Lahaula fi shi'atillah! Aman me kikeyi Khairy?" Mama ce ke rafka wannan salatin yadda kasan ance mata yau ka gawar Khairy nan a kwance, wani irin mugun numfashi taja ita kam yau ta shiga uku ta ga rayuwa, yau babu mai kwatarta hannun Mama "Ke dan ubanki kinaji ina maki magana kin man shiru, ana tambayarki abu amma kin zura ma mutane na mujiya!" Ta furta da karfi tana janyo hannun Khairy daga cikin bathroom din tana kare mata kallo, ita kuwa Khairy kuka ta fara yi a hankali cike da tsoro da kuma fargaba, yadda taga Mamar na janta har parlor yasa tace "Mama dan Allah ki tsaya sai jana kike kamar ance maki an kamani ina sata!" Ta fadi haka tana neman kwace hannunta daga hannun Mama, nan Mama ta kureta da idanu tana mata wani irin kallo "Nace ki fada man aman me kikeyi? Tun jiya na kula dake daga amai sai kwanciya uban me ke damunki? Wallahi ko kiyi magana ko inci ubanki cikin gidannan yanzun nan shegiya mai mugun hali!" Nufar inda Khairy ke tsaye bakin kofa tayi kamar wata zakanya don son tabbatar da zarginta Khairy ta kurma wani uban ihu, "Dan Allah ki tsaya Mama! Zan fada wallahi zan fada!" Mama ta kama kugu tana jijiiga "Toh ina jinki!" Nan ta fara karkarwa "Dama.... dama.... ya kamata ace na ga al'adata tun sati daya ya wuce ban gani ba, shine na sa6e naje akayi man test.... aka...aka...ga ciki...na wata daya...." ko karasa maganar bata yi  ba take Mama ta wanke da wani irin wawan mari! Ihu ta kurma nan Mama ta damko ta "Dama nasani yawan karuwanci kike zuwa! Dan ubanki wa yayi maki ciki? Iyye wani dan iskan ne yayi maki cikin shege!? Ciki? Na shiga uku na lalace Khairy kin cuceni kin gama dani! Dan ubanki abun naki har ya kai haka? Aikau zaki ga ciki don wallahi badai a nan gidan ba, na rantse da Allah na cikin kabari sai yafi ki jin dadi dan ubanki! Gara ma tun wuri kisan nayi cikin gidannan!" Ihu ta zabga ta fashe da kuka "Na shiga uku Mama ki hakuri ki rufa man asiri!" Ranar Khairy ta daku mutuwa kadai ya rage mata tayi, da kyar da sudin goshi Baba ya ceceta daga hannun Mama.

Tana kwance dakinta bisa gado tana kukan fitar rai, babu abinda takeji sai karar tsuntsaye cikin daren nan tayi mugun buguwa wurin Mama, amma abun mamaki duk da jikinta na ciwo amma zuciyarta tafi komai ciwo, gaba daya ta rasa meke mata dadi a duniya wai yau itace da cikin shege? Kukan ne yakeson yaci karfinta toshe bakinta tayi da hannunta ta dinga razgar kuka...

Da safe kamar daga sama taji saukar bulala, ko ba'a fada mata ba tasan Mama ce ta fara gana mata daya daga cikin azabobinta, wani kukan zuci tayi kafin idanunta su bude tabbas kuwa Mama ce tana ta faman huci, kallon window Khairy tayi nan taga rana fayau, ruwa Mama ta sharara mata mai sanyin bala'i ihu ta fasa ihu take ta fara karkarwa "Dan Allah Mama kiyi hakuri wallahi da kin magana zan tashi..." kukan ma ta kasa yinshi "Dan ubanki inzo inta faman tadaki kiyi sallar asuba amma kik'i tashi saboda ni kin maidani sakara shashasha ko? Wato sai kika kwanta kika cigaba da baccinki ko? Tou na rantse da Allah zaki gane kurenki, wannan kafircin ba'a nan gidan zakiyi man shi ba, ga karuwanci da rashin yin sallah ga cikin shege dan ubanki! Munafuka algunguma!" Mama ce keta faman masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba. Mikewa Khairy tayi da kyar ta nufi hanyar bathroom "Kuma wallahi na baki minti goma ki fito, sharar gidannan kaf hade da tsakar gida zakiyi shi ko inci ubanki yanzun nan, ga wanke wanke da wanke band'aki! Ina jiranki!" Hawayenta ta share "Bazan iya shara ba Mama bayana  ke ciwo kamar zai balle..." ta fada tana nufar hanyar bathroom "Toh dan ubanki sai kinyi! Wallahi gara ma kiyi cikin arziki, ki gama zagaye zagayenan sai kinyi shi! Kuma cikin gidannan sai na lahira yafi ki jin dadi badai ciki kika yo ba na shege? Tou zaki ci ubanki kuwa! Ke karewa ma daga yau awara zaki dinga toyawa kofar gidannan kuma inga uban da xai hanaki ko shi uban naki yayi kadan!" Share hawayenta tayi, tayi tsaye bakin bathroom din zuciyarta na tafarfasa, da sauri ta share hawayenta jin wani zagin da Mama ta kunduma mata daga parlor, da sauri ta shige bathroom din da sauri. Bayan ta kammala ta fito a hankali ta fara sharar tsakar gida tana yi tana jin kamar zuciyarta zata bar kirjinta, duk ta rasa sukuni ta rasa abinda yake mata dadi. Tun kafin ta gama sharar nan Mama ta fito tsakar gida ta dinga yarfa masifa da bala'i ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, dole ta dinga sauri ta karasa aikin gidannan tas ta gama wanke wanke, ita ko abinci bata tunanin xata iya ci, a nan inda ta gama wanke wanken ta zauna sai kuka ya kufce mata a daidai nan Baba ya fito daga daki don zuwa wurin aiki. Yana ganinta a haka yaji tausayinta matuka saidai kuma ko menene ita ta jawo ma kanta ko jiya baisan meke faruwa ba sai yau da safe Mama ke fada masa abinda tayi, yace ko kusa kar wanda ya sake ya zubda cikinnan don ita Mamar tace zubarwa za'ayi yace ahir laifi kan laifi kenan? Yace kar a sake a zubda shi. Tsugunnawa yayi daidai saitinta ya miko mata abinci yace "Kar6a kici Ummalkhairy, kiyi hakuri da duk wata rayuwa da zatazo maki, kuskure ne kin riga kin tafka, saidai fatan Allah ya yafe maki kurakurenki ya zamo wannan shine sanadin shiriyarki, zuciya a koda yaushe ko ta kasance cikin farin ciki ko kuma kunci, kuma na hana zubar da cikinnan don nace koda bayan idona kika zubda shi toh ki sani ban yafe maki ba, don ke kanki zaki aikata laifi akan laifi ga laifin aikata zina ga kuma na kisan kai!" Nan ya aje mata abinci ya tashi ya fita, ganin yadda Khairy ke kuka ya sanya Mama ta danji wani iri a ranta "yau xaki zakici ubanki wallahi, saboda ke ay ya fita bai bada ko sisi ba toh wallahi sai na fanshe ta a wurinki, maza tashi ki gama wanke wankenan kije ki tashi ki fara wanke wake suya, badani za'ayi wannan iskancin ba don wallahi in kika bata man rai ko haihuwa kika tashi yi kallon arziki ma bazanyi maki ba sai ki nemi wata uwar, shegiyar yarinya kawai haka nan kin kwaso mana abin kunya. Kai innalillahi wa inna ilahir rajioon." Sai kuma ta fashe da kuka harda fyace majina, cikin kuka Khairy tace "Mama suyar awara a kofar gida zanyi?" Wata uwar harara ta watsa mata wane zata cire idonta "Toh kinfi karfin kiyi ne dan ubanki shashasha yarinya! Zakici ki tashi ko sai na iso nan? Ubanwa yace kiyo cikin shegen?" Ta daka mata tsawa wadda batasan lokacin data hadiye kukan nata ba ta fara tura dumamen tuwo da miyar kuka tana hadewa da kyar.

Fad'in yadda rayuwa ta sauya ma Khairy ma bata baki ne gaba daya duniya ta juya mata baya, kawayenta sun guje ta yanzu iyayenta ko nan da kofar gida basu isa su leka ba yanzu za'a fara nunasu ana cewa yarsu tayi cikin shege. Zagin yau daban na gobe daban... Ranar tana xaune tsakar gida ta zabga tagumi abun duniya duk ya isheta ji take kamar ta kashe kanta ta huta "Dan ubanki taso kizo ki amsa ki sha bazaki kashe kanki ba tunda dai cikin ya riga ya shiga mazinaciya! Allah kadai yasan irin mugun abun da kika shuka Allah ya jarabe ki ta wannan sigar!" Yadda tayi tsaye kememe a bakin kofar ya tabbatar ma da Khairy jiranta take taxo ta amsa, a hankali kamar wacca kwai ya fashe mawa a jiki ta mike dab da kofar dakin Khairy tayi mika daidai da dagawar rigarta sama cikinta yadda ya bullo shi ya tsorata Mama wani wawan ihu ta kurma hade da dora hannu bisa kai, da sauri Khairy ta karasa wajenta tana tambayar lafiya? Ita tsoro ma ta bata. "ubanki lafiya lau Shegiya yar iska! Ashe dai maganar cikin nan da gaske ne wallahi Allah na dauka wasa ne, gashi nan ya bullo wallahi ya bullo!" Khairy don dole tayi baya cikin tashin hankali ta fara magana "Na shiga uku don Allah don annabi kiyi hakuri wallahi sharrin shaida ne!"  Finciko ta Mama tayi hade da shaketa "Kar kiyiwa shaidan karya dan ubanki!"

No comments: