Thursday 3 June 2021

YAR AGADEZ PAGE O1

 YAR AGADEZ

 

Na MSB 

              {Page 01}



Bismillahi Rahmannir Raheem! Am back y'all!😆🥰



Lumshe idanuwanta tayi tare da shakan dadad'an kamshin iskan dake kadawa, bayinta guda biyu dake gefenta ta kalla bayan ta bude idanunta a hankali ta kalli daya ta saki murmushi, daka kalli wurin yadda ya kawatu kadai abin kallo ne ga ruwa malale yayi blue sharr gwanin ban kyau, banda itacen da suka kewayen wurin ga grasses hade da kasa data kara ma wurin kyau duk fadin garin agadez babu inda takeso tazo fiye da nan ko damuwa ta shiga data tazo wurin nan take samun sauki. A hankali ta juya ta fara tafiya a hankali kafafuwanta na nitsewa cikin kasa tana tafe suna binta a baya duk inda tasa kafa kamar rakumi da akala. Daga nesa take hango shi yana nufarta fuskarsa dauke da annashuwa da murmushi itama haka, saida sukazo dab da juna sannan suka tsaya inci biyu zuwa uku tsakaninsu, da murmushi a fuskarsa yace "Gimbiya yar sarki jikar sarki, da ay wurinki zanje don nasan a ina zan same ki, saidai kuma na hango ki kina dawowa da alama zaki koma gida ko?" Cikin muryarta mai dadin sauraro tace "Na jira zuwanka Yaya Ashraf amma baka zo ba kamar yadda ka saba, toh nikuma na gaji da jira sheyasa na dawo..." yace "Kema kinsan duk rintsi zanzo mai martaba ne ya tsaida ni sheyasa kika jini shiru..." tace "Toh tunda mun a hadu a nan sai mu koma gida ko?" Yayi murmushi "Har kin gaji da ganina ne da kike cewa mu koma gida?" Tayi yar siririyar dariya "Ko kadan ba haka bane yaya Ashraf kaima kasan bana gajiya tare da kai, ko ba komai kai dan uwa na ne na jini sannan mun shaku tun muna yara kaine abokin shawarata kaine abokin wasa ne, kai kadai ne na tashi na gani a kusa dani banda iyayena..." yace "Hakane Gimbiyata..." tayi murmushi tace "To muje ko..." yace "Your wish is my command your highness." Tayi dariya suka soma takawa cikin masauratar agadez kasancewarsu jinin sarauta, tun daga nesa dogarawan dake baje a waje suka hango su take suka fara kirari "Yar sarki jikar sarki, Gimbiya jinin sarauta, muna maku barka da dawowa Ashraf da Gimbiya Hoodah...  Allah ya karawa sarki lafiya ya kara maki lafiya...." murmushi kawai sukayi suka shige ciki kanta tsaye bata zame ko ina ba sai harabar mahaifinta wato Sarki Jalal. Tana shiga dogawaran sarki suka mike suka fara mata sannu da zuwa hade da kirarin da suka saba yi mata, tana shiga ta isa inda Abbanta ke zaune yana ganinta ya fadada murmushinsa ya gyara zamansa tace "Barka da hutawa Abba..." yace "Yawwa Gimbiya Hoodah da fatan kina lafiya?" Tace "Lafiya lau Abba." Ashraf ya gaishe da sarki ya amsa da sakin fuska sannan yace "Duk inda kaga zara zakaga wata..." sukayi murmushi a take Abba ya kuma cewa "Dazu naji kaka tana ta nemanki kina da labari ko baki dashi?" Tayi Murmushi "A'a Abba banida labari yanzu na dawo gidan..." yace "Toh maza kije wurin ta kiji kiran me take miki..." ta mike tare da bayinta suka taka mata baya har dakin kaka wanda yake bangarensa na daban, da sallama ta shiga kaka na kishingide saman katon carpet din da ke baje a harabar parlon ta kishingida bisa tuntunaye ana yanka mata Apple, tana ganin Hoodah ta dan gyara zamanta kadan tana mai murmushi, zubewa tayi har kasa tana gaida kaka, kaka ta amsa da fara'a itama tace "Halan kina wajen da kike so duk fadin garin nan ko?" Hoodah tace "Kwarai kuwa kaka tun dazu nake a can, saboda can ya fiye man zama cikin gidannan sau million..." take fuskarta ta sauya hawaye suka taru cikin idanunta zucuyarta na tafasa, kaka ta dafata itama fuskarta ta sauya tace "Sai hakuri Hoodah kina ganin dai kowa hakuri yakeyi ba yadda muka iya" Hoodah tace "Toh wai meyasa Abba bazai iya daukar mataki ba a kanta? Taya zatazo ta takura mana ta hana mu sakat sannan ta gagari kowa ba wanda zai iya daukar mataki a kanta..." Kaka ta gyara zama tace "Toh wai kina tunanin haka nan ta barshi ne? Kina ganin ko ni dana haife shi ban isa nayi magana ba, gaba daya ta shanye shi sai yadda tayi dashi bai tankwaruwa...." Hoodah tace "Tunda na rasa mahaifiyata a gidannan nayi bankwana da farin ciki gaba daya rayuwata ta sauya..." Kaka tace "Ay bake kadai ba tunda Safinah ta rasu shekaru kusan goma kenan kowa yayi bankwana da zaman lafiya, gaskiya munyi rashin Safinah gidannan mutuniyar kirki mai halin dattako Allah jadadda rahama a gareta." Hoodah tace "Ameen kaka ke kadai ce nake zuwa wurinta naji dadi yanzu haka ma Abba ne yace nazo kina nemana..." kaka tace "Eh babu komai dama naga baki shigo ba nan da safe shine nake cigiyarki..." Hoodah tace "Ina nan lfylau kaka... bari na shiga ciki." Kaka tace "Sai kin fito." Daga haka ta mike ta fito bayinta na binta har bangarensu tana shiga tayi sallama hakimar na kan kujerar mulkinta ga bayinta nan sun kai bakwai suna mata fifita, Hoodah ta isa gareta ta zauna kan sauran kujarun da suka zagaye makeken parlon tace "Barka da hutawa Umma..." wani mugun kallo ta watsa mata sannan tace "Lafiya... daga ina kike?" Tace "Daga Darwish Mahal nake..." Ta karkada kafa "Da izinin wa kika fita?" Hoodah is beginning to lose her patience, wani ajiyar zuciya ta sauke tace "Da izinin Abbana..."  Sarauniya Karima tace "Daga yau na sake ganin kin fita baki sanar dani ba zanga uban da zai tsaya maki a gidannan, tashi ki bani wuri..." ta mike zuciyarta na kuna tayi dakinta, bayinta ta kalla idanu duk kwalla tace "Privacy..." take suka fita daga waje ita kuma ta kulle kofarta ta jingina tana mai lumshe idanu. Tafi minti sha biyar a haka ita batason wannan rayuwar tanaso tayi rayuwa as normal mutum she hates being royal, tanaso tayi rayuwar privacy ba tare da an takura mata ba, tanaso taganta tana rayuwa normal ba irin wannan rayuwar ba... gathering courage nata tayi ta wuce bathroom tayi wanka ta fito bayan ta kimtsa aka kirasu cin abinci gaba dayansu wato dinner. Bayan kowa ya hallara aka masu serving abincinsa Ashraf ne da Hoodah suka kalli juna sannan sukayi murmushi a haka suka kare cin abinci. Can wurin karfe takwas daya daga bayi ce ta shigo da sallama bayan Hoodah ta amsa tace "Ranki shi dade kizo Ashraf na son ganinki acan harabar shan iska..." dan murmushi tayi tace "Ki ce masa ina zuwa." Daga haka ta dan russuna kadan sannan ta dau mayafinta ta fita inda yace mata yana nan, bayinta basuyin gigin binta ba saboda dama inda Ashraf yayi mata kiran nan na musamman basu cika binta ba. Zaune yake bisa daya daga kujerun shakatawa da center table mai dauke da Apple da aka yayyanka sai glass cup guda biyu wanda aka cika da madara yana cin Apple din a hankali yaga ta shigo da sallama, ya karkato kansa yana dubanta duba na musamman sannan ya amsa da fara'a yace "Ya zaki tsaya a nan? Ki karaso mana..." tayi murmushi ta karaso ta zauna tana fuskantarsa sannan yace "Da fatan gimbiyar tawa tana nan lafiya lau? Ko dayake banga alamun haka a tattare da ita ba... meyake damunki?" Tayi yake tace "Babu komai Yaya Ashraf meyasa kake zaune a nan kai kadai?" Yayi murmushi "Ba ni kadai nake zaune a nan ba daman ke nake jira sheyasa kika ganni a nan... amma still ina so ki fada man me Umma tayi miki nasan dai itace..." ta hadiye abu da kyar tace "A gaskiya yaya Ashraf abinda Umma takeyi bata kyautawa gaba daya tabi ta tsaneni bansan menayi mata ba, abu kadan zata hauni da fada da zagi na cin mutunci nida gidan mahaifina amma bana tare da farin ciki..." yace "Haba Gimbiya ay kema kinsan bake kadai takeyi wa haka ba in kin kula haka halinta yake batada imani ko kadan sannan batada kirki, don Allah daga yau kar ki sake bari maganganunta suyi tasiri a cikin zuciyarki..." ya numfasa ya cigaba "wato akwai wata mahimmiyyar maganar da nake so muyi dake Gimbiya in har bazaki damu ba..." tayi murmushi "Nagode yaya Ashraf kai kadai ne kake sanyaya raina kaida kaka idan an bata mun rai, sannan kwarai zaka iya yin magana dani ina jinka..." ya sauke ajiyar zuciya yace "Mun dauki tsawon lokaci muna soyayya a boye baki ganin lokaci yayi da ya kamata mu fito fili asan irin kaunar dake tsakanina dake? Ya kamata manya su shiga cikin maganar nan...." ta dago da sauri tana dubansa tace "Nasani yaya Ashraf kamar yadda kake sona nima haka nake sonka saidai kana ganin hakan mai yuwuwa ne kuwa?  Ina tsoron Umma karta hanani aurenka idan na rasaka bansan a wane hali zan shiga ba..." yace "Haba Gimbiya meyasa kike irin wannan maganar? Ita Umma keda iko da ke da zata hanamu aure? Ay indai Abba ya bada goyon ay sai inga ba wata matsala..." tayi ajiyar zuciya tace "Shikenan..." nan suka cigaba da fira cikin so da kaunar junansu...



      Washe gari


Gimbiya Hoodah tanason zane like real drawings tana dakinta karfe kusan 9 na safe tana making outline na gown da black pencil, tana cikin sanya colors din akayi knocking kofa daya daga cikin bayin Umma ce tsaye ta gaida Hoodah, Hoodah tace "Yadai?" Ruqayyah tace "Afuwan ranki shi dade Umma tana son ganinki yanzu yanzu..." Hoodah ta dan zaro ido kadan tace "lafiya?" Ruqayyah tace "Banida masaniya ranki shi dade ta dai ce ki sameta harabar mai martaba yanzu..." tayi tsaye kamar gunki sannan ta gyara zaman gyalenta tace "Ina zuwa..." 

tafe take tana maganar zuci "Wai meye matsalar matar nan ne? Me take bukata daga gareni tunda uwar safiyar nan, tausa takeso nayi mata ko wanka?" Tana tafe tana kara zama frustrated. Sallama tayi mahaifinta ne zaune cikin kujerarsa ta musamman yar mulkin na gefensa, saiga kaka da yayar shi Aunty Rahanatu. Duk suka amsa sallamanta ta samu gu ta zauna yadda ta tabbatar Umma zata sha wahalar ganin fuskarta. 

"Ke Hoodah!" Ta daka mata tsawa mai razanarwa tace "Dawo gabana ki zauna..." ta nuna wurin da yatsanta, zama tayi kanta kasa sannan Umma ta fara magana cikin nuna isa "Kamar yadda kuka sani nice na hada wannan taron don mu tattauna gameda auren Gimbiya da Yarima...." a razane kowa na parlorn ya dago yana kallo Umma cike da firgici da rudu, Abba ne yace "A'a Umma maganar nan mun riga munyi ta dake ba wata maganar aure da za'ayi wa Gimbiya ina tunanin mun gama maganar nan tuni?" Nuna shi tayi da yatsa cikin daga murya "Jalal wannan maganar ba wanda ya isa ya chanza ta a gidannan a matsayina na uwar yarinya ay ko ban haifeta ba ni ce na rike ta don haka inada hakki a kanta kuma yanzu nace zan hada aurenta da yarima ba wanda ya isa ya chanza ta." Shima nuna ta yayi da yatsa "Amma nine ubanta! Inada hakki a kanta nima kuma na fada bazata auri yarima ba, ke sanin kanki ne bamu shiri da masauratarsu don me zaki so ki hada yata aure dasu? Baki isa ki yanke hukunci ina raye ba saidai bayan na mutu!" 

 Umma ta mike tsaye tace "kaga Jalal bana son wani dogon bayani ko surutu a nan ko uwarta daka aura ay kaima hadaku akayi inace ba ganinka kayi kace kanaso ba? Don haka kamar yadda akayi wa uwarta itama haka za'ayi mata!" 

Hawaye suka fara wanke ma Hoodah fuska zuciyarta kamar ta bar kirjinta, kallon Ashraf da yayi tsaye bakin kofa kamar an dasa shi a wurin, Kaka cikin rawar murya ta mike tace "Saboda kece uwarta? Toh ko mahaifiyarta bazan yarda tayi mata dole ba bare kuma ke..." Jalal ya kalli kaka yace "Kiyi shiru kaka ki barni inyi magana kar ki bata mata rai..." kaka tasa salati tana tafe hannu "Wato kafi gudun bacin ranta akan ka na yarka? Kai kadai ne zaka iya mata fada amma mu bamu isa ba kenan? Wannan ay zancen banza ne zancen wofi ba itace uwar yarinya ba don haka bata isa ba!" Cikin nuna halin ko in kula tace "Well, mun riga mun gama yanke hukunce shima kanshi mai martaba ranar da mukayi maganar bai musa man ba dan haka za'a daura auren ko kuna so ko baku so..." kowa yayi shiru parlon an rasa me bakin magana 

"Excuse me!" Hoodah tayi magana karon farko tun zuwanta "Meyasa kike treating dina kamar wata dutsi? Ina da damar yin abinda nakeso da abinda naga dama dan haka bazan auri wani yarima ba..." ta fada muryarta na sama  "Zancen banza kikeyi!" Umma ta fada tana buga sandarta a kasa  "Dama wayace sai kin yarda sannan mu cigaba da shiri ? Duk nan manyanki ne kar ki sake saka man baki ba tare da an baki izinin magana ba!" Hawaye wasu suka sake wanke mata fuska, kakkausar muryarsa sukaji yana fada "Kinyi tunanin feelings dinta ko bakiyi ba?  Da abinda takeso da wanda bataso? Kinyi tunani? Ko ke uwarta ce da zaki zo ki nuna isa a nan?" Tasss! Abba ya dauke shi da wani irin wawan mari yace yana nuna shi da yatsa "Dayake bakada kunya  agabana kake fadawa matata magana!?" Wata irin razananiyar kara Hoodah ta fasa tace "Nace baxan aure shi ba! Stop!" Ta fada cikin razana ihu! Aunty Rahanatu ta taso ta kamata take Hoodah ta tura ta gefe "Ba inda zanje inada damar da zanyi magana na fada bazan auri yarima ba, baza'ayi manipulating dina ba a cuce ni da wani auren dole!" Ta fada cikin daga murya hawaye na wanke mata fuska.....

No comments: