Saturday 5 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 03

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 03}



"An koya mana a kullum mu girmama hukuncin iyayenmu, tun zuwana duniya tunda nake ban ta6a sa6a umarnin iyayena ba I always respect their decisions and honors, zan iya cigaba da rayuwa ba tare da Khairy ba? Abbi yana so ya jefa rayuwata cikin bakin ciki na hana ni abinda nake so..." yana tunanin nan yake tafiya cikin dakinsa daga wannan corner din zuwa wata... t-shirt dinsa ya dauko ya saka ya fito harabar mahaifinsa ya nufa nan ya iske sa shida mutanensa, Abbi na ganinsa ya umarci da mutanen su basu waje nan suka fita Abbi yace "Da fatan kanada labari nan da wata daya za'a daura maku aure kaida Hoodah...? Ya kalleshi da sauri yace "Why are you doing this Abbi? Kasan meke tsakani na da Khairy ta yaya kawai rana daya ace na rabu da ita haka kawai?" Abbi yace "Look, na riga na yanke hukunci am not going back on my word! Who's Khairy? Sai kace idan ka rabu da ita rayuwarka ta kare?! Maganar nan na riga na gamata jibi zakaje kaga yarinya ku tattauna a tsakaninku I mean ku daidaita kanku!" Sultan ya girgiza kansa yace "No! Bazan iya ba! Banda auren dolen da kace zakayi mun har sai an tursasa ni naje wurin wacce nakejin tsanarta cikin raina!kun rusa mun farin ciki Abbi!" Abbi ya hassala yace "Nine mahaifinka! A gidana kake kuma a karkashin ikona kake, kuma dole ayi mun biyayya don haka I said you're going to meet Hoodah whether you like it or not!" Shiru yayi ya kasa cewa komai wannan wane irin turn ne yayi taking a rayuwanshi lokaci daya? Zaiso ace wannan abun da yake faruwa mafarki ne ya tashi yaga komai bai faru ba. "Do you have anything else to say? If not u may leave..." Shiru yayi still ya kasa furta koda kalma daya "Haba mai martaba! Meya faru da kai lokaci daya kabi ka chanza akan wata wadda bamuda alaka da ita? Kodai sun asirce ka ne har kake neman jefa dan da ka haife a cikinka cikin kunci da bakin ciki? Kasani fa shi aure ba abun wasa bane, abu ne da ake fata ayi na har abada! Taya zaka aura masa wacce baya so sannan kace su zauna a inuwa daya a matsayin ma'aurata....!" Ummi ta karaso tana huci Abbi yace "Ke lokacin da za'a aura mun ke sonki nakeyi? Bama gwanda shi ba na bashi izini yaje yaga yarinya su daidaita ba? Kefa? Sai ranar da aka daura mana aure kika shigo cikin gidana a lokacin na fara ganin fuskarki...." tace "Toh naji amma ay a wancan zamanin akayi haka bare yanzu zamani ya riga ya chanza yaron nan yana maka biyaya daidai gwargwadon ikonsa toh don me kawai yanzu zaka ce zaka masa wannan danyan hukuncin?" Abbi yace "Wai meyasa kuke nema ku bijire ma umarni na ne? Toh ko me zakuce auren nan kamar anyi an gama ne babu fashi sai idan na mutu ne sai kuyi yadda kukaga dama!" Daga haka yasa kai ya fice Ummi da Sultan sunyi cirko cirko suna mamaki yadda tashi daya ya rikice haka!

*********

Ta idar da sallar magriba kenan aka shigo babu ko sallama, dagowa tayi taga Sarauniya Karima ce tsaye saida Hoodah ta dan razana da farko kafin a hankali ta mike tsaye tace "Barka da dare Umma?"  Karima tace "Barka bakiji sakona bane nace ki sameni harabata shine kikayi watsi dashi saboda kin raina ni ko don ban isa da ke ba?" Tace "Ko kusa ba hakane Umma, inaso na idar da sallah ne sannan saboda lokacin da sakonki ya iso gareni ana kiraye kirayen sallah...." ta daga mata hannu "Toh sannu uwar musulunci sai akace ke kadai kikeyin sallah a fadin duniya!? Well anyway bari dai kar na bata lokacina a nan na fada maki kai tsaye abinda ya kawo ni...." Hoodah tace "Ok..." hannunta ta harde wuri daya sannan tace "Jibi Yarima zaizo ku fuskanci juna kuma kinsan Allah na samu labarin kin masa wulakanci sai naci ubanki cikin gidannan no matter what ki karbesa hannu biyu kar ki wulakanta sa...." Hoodah ta dago da sauri gabanta ya bada wani ras ras, tace "Na'am?" Karima ta daka mata wata uwar tsawa "Kinga kar ki nemi ki raina man hankali meye kuma wani na'am? Sarai kinji abinda nace don haka sai ki fara shiri daga yanzu na barki lafiya....!" Har ta tafi sai kuma tadawo tana wani murmushin mugunta "Aww na manta abu daya ban fada maki ba, nan da wata daya za'a daura maku aure da Yarima, daga yau ki fita harkar Ashraf in ba haka ba ke kinsan wacece ni sarai zan iya saba maku daga ke har shi a bi umarni na a zauna lafiya..." daga haka ta fice daga dakin tana wani yanga da cika da batsewa, zubewa Hoodah tayi kasa wannan karon kukan ma yaki zuwa a halin da take ciki gwara ace kukan takeyi da abinda takeji a yanzu. Tafi minti talatin zaune a nan har aka fara kiran isha da kyar ta yunkura ta tada sallah tana gamawa ta fashe dawani irin kukan bakin ciki.

Saida ta gaji don kanta tayi shiru sannan kuma ta fara jero addu'oi na neman za6in Allah akan wannan al'amari. Tana nan har bacci barawo yayi awon gaba da ita...

2days later ******

Tun safe haka ta tashi batada walwala ko kadan, taga Karima sai  wani shirye shirye takeyi. Ita kuwa duk fushin da takeyi bai sa Abbanta ya chanza mind dinshi ba, Sarauniya Karima tace "Sai ki tafi ki shirya don suna hanya yanzu haka nasan neman Ashraf kikeyi toh kar ki damu bazaki ganshi ba har sai bakinmu sun tafi!"

Ba da dadin rai ake kimtsa ta ba bayinta guda biyu ne keta faman shirya ta bayan sun kammala suka yafa maka gyalenta mai kama dana indiyawa suka daura mata har bisa kai ba karamin kyau yayi mata ba, daya daga bayin Umma ce tayi sallama ta durkusa kasa tana fadin "Ranki shi dade kizo bakinki sun iso sunce ayi maki iso..." gabanta ya buga, kallon yarinyan Hoodah ta tsaya yi can ta numfasa tace "Ina zuwa..." a hankali take tafe kamar mai tsoron taka kasa ta nufi harabar saukar baki inda ta tabbatar can suka sauka, tsaye tayi bakin kofa ta kasa shiga har sai da Karima ta fito ta watsa mata wani irin kallo sannan ta shiga ciki da sallama, Abbanta ta gani zaune suna tattaunawa saida suka kammala sannan Abba yace "Shigo mana...." a hankali ta karaso kanta kasa sannan ta samu wuri ta zauna can Abba ya mike "Bari na baku waje ku tattauna ko?" Daga haka ya mike dogarawansa suka rufa masa baya... Su Biyu ne tagani zaune saidai bata tantance wanene yariman ba a cikinsu, ganin an cika masu gabansu da kayan alatu yasa tace "Bazaku sha koda ruwa ba?" Daya daga cikinsu ne yace "No we're ok." Ta kakalo murmushin dole tace "Hospitality dina zai zama abin tambaya idan har baku amsa tayina ba..." tana gaman fadan haka ta fara tsiyaya masu juice cikin cups din da aka ajiye masu, ba masu suka karba daga hannunta ita kuma ta mike ta koma kan kujera yadda suka tsareta da idanu yasa gaba daya ta zama uncomfortable, amma duk da haka sai ta daure tasan dai ba dadewa zasuyi ba. Daya daga cikinsu ne yace "Sultan kace ma future wife dinka wani abu mana tunda mukazo bakayi magana ba ko da sau daya ba..."  wanda yayi maganar ne kasa kasa amma duk da haka taji me yake cewa, ta dago a hankali tana kallon wanda akayi ma magana, "Me zance mata? Ay kai ya kamata kayi magana bani ba Usman..." Hoodah ta kalleshi a kule tace a ranta "As if ina son magana dakai kaima..." ta hadiye abu da kyar wanda aka kira da Sultan mai kama da larabawa shine ya dago yana kare mata kallo sannan yace "Kina son auren nan ko bakiso?" Tayi shiru na yan dakikai sannan tace a hankali "Aure abu ne mai kyau amma idan har ma'auratan suna son junansu..." ya karkata kansa kadan sannan ya yace "Bakiso kenan? I mean wannan auren da ake shirin yi tsakani na da ke?" Ta ciji lips dinta kadan na wannan tambayar daya jefo mata sannan tace "Hakane, amma kuma bazan iya bijire wa iyayena ba..." yace "Kin riga kinyi, kamar yadda bakison auren nan haka nima bana son auren nan dukkanmu muna bin umarnin iyayenmu..." tayi murmushi kadan "Toh kai me kake ganin mafita a nan tunda dukanmu bamu son auren nan?" Ya dora kafa daya kan daya "Sai ki bani lokaci nayi tunani a kai..."  tace "Amma kuma idan baka ce wani abu ba kenan haduwarmu ta xama in complete kenan if you don't decide..." yayi sipping juice cikin nuna isa yace "As I said before ki bani lokacin in har kikaji shiru toh kisa aranki auren zai tabbata kenan, sai dai kuma kinsan me zaki tarar kika bari aka daura auren nan don bana sonki dole akayi mun..." ta hadiye kululun bakin cikin ganin irin kalar mutumin da xa'a hada ta rayuwa dashi wanda bai iya adana kalamansa da kyau ba don haka sai tace a kule "Kamar yadda na tsane ka ba? Ay inajin an fi yin mun dole akanka don haka anyi equal dukkanmu bama son juna....!" Yayi wata yar dariya "Very well then Hoodah, is your saying not mine..." yana gama fadan haka ya mike da niyyar tafiya. Nan sukayi bankwana dasu Abba sukayi gaba. 

"Nasan me kikayi..." Hoodah ta fada tana shiga cikin harabar Karima. Sarauniya Karima ta mike tace "Kamar yaya?" Hoodah tace "Da girmanki kike mana labe don kiji abinda zamu ce?" Sarauniya tace "Eh...ehh, nayi laben is a good thing Abbanki xai maki aure whether you like ot not, duk magaganun da kuka fada na cewar bakusan juna duk a banza ne, kuma naji ko wace kalma da kuka fada..." tayi wani shu'umin murmushi tace "So it doesn't matter aure babu fashi..." tana gama fadan haka tace "Zaki iya tafiya..." tace tana nuna mata kofa. Tunda suka tafi ta shiga tunani kala kala ita kam mutumin bai mata ba ko kadan kyan dan maciji kenan zuciyarsa bakikirin kamar hadarin kaji, "Ya Allah! Meyasa za'a zabi a aura mun wannan mutumin duk mazan dake duniya? I deserve the best meyasa mahaifina ya zaba man rayuwar bakin ciki meyakon farin ciki? Anya Abba shine ya haife ni kuwa? Duk wani uba zaiso yaga yarsa cikin farin ciki a kullum amma banda nawa mahaifin, Abba meyasa why? Why?" Ta fada tana buga karfen gadonta da karfi hawaye na shatata daga idanunta duk tayi squeezing gashinta kamar wata sabuwar mahaukaciya data fara hauka a titi. Bayinta ne suka shigo da sauri jin ihu suka ce "Ranki shi dade lafiya?" Ihu ta daka masu "Ku fita ku bani wuri!" Da sauri suka fita ita kuma ta cigaba da kuka....

*******

Tunda suka zauna yanzu za'a kai kimanin minti sha biyar amma bai ce da ita komai ba idanunsa na kan table din dake tsakiiyarsu, kafafunsa kuwa yana dan bubbuga kasa dasu duk Hoodah taji ba dadi amma karshe daya dago yana dubanta sai ta gwammace dama cigaba da kallon kasan yayi, idanunsa sun koma abun tsoro kamar ba Abban data sani ba yadda yake tsareta da mugun kallo sai ka rantse da makiyarsa yake bada yar cikinsa yake ba, wani ajiyar zuciya ta sauke tasan cewar Sarauniya Karima ce ta kawo masa wata magana wanda ta tabbatar ba abinda ya faru kadai ta fada ba ta kara karya da gaskiya ta zuge shi don ya bata mata rai. An jima rabon data ga fushinsa har haka koba komai duk abinsa da fadansa idan ya tashi ya iya controlling kansa amma duk ranar daya kasa controlling kansa toh sai mutum ya rantse tashin duniya ne yazo.

"Cin mutunci!" Abinda ya furta kawai kenan tunda ya kirata harabarsa ita dai kanta na kasa batace komai ba, "Kinci mutuncina da kimata kin kuma ci mutuncin masarautata.....!" Ta runtse idanunta gam cikin jin zafin kalamansa da duk abinda zai fito bakinsa, ya juya yana kallon tagar harabar. Can sai kuma ya mike ya fara zagaye harabar hannuwansa sarke ta baya "Na hadaki da mutumin kirki, mutumin arziki mai kirki da sanin ya kamata......" ya bata baya sai ya dan karkato kadan yana kallonta "Amma kin bata hakan! Kamar yadda kike bata komai na rayuwarki gaba daya!" Ya cigaba da tafiya yana huci "Duk kinyi wannan abun ne saboda bakisan darajata ba da kuma kimata a matsayina na mahaifinki! Toh kisani basu kika ci mutuncinsu ba nine kika ci ma mutunci!" Ta dago idanunta cike da kwalla tace "Kayi hakuri Abba banci mutuncinsu ba....!" Wani irin mugun kallo ya watso mata kamar zai fashe yadda ya cika yayi fam "Toh kina nufin matata karya tayi maki kenan?" Ta girgiza kanta da sauri hawaye na zuba daga idanunta, iska ya furzar na haushi sannan ya dora "Kina sane maganar auren nan ba inda bata zaga ba cikin garin Agadez amma kina nema ki watsa man kasa a ido! Duk kinyi wannan abun ne saboda ki nuna man cewa kin iya soyayya ko? Toh kanki aka fara ne ko kuwa akanki za'a kare?" Ta dago tana dubanshi tana share hawayenta "Na dauka na isa dake ashe ban isa ba, kinyi rejecting wanda na kawo koba komai bazakiyi considering nina kawo shi ba kiyi man biyayya a'a sai kika je kika ci mutunci na ko? Me za'a daukeni? So kike a fara man kallon mutumin banza ko?" Hoodah ta kai kololuwa wurin gajiya da abinda makirar matar nan keyi mata! Ita kullum burinta ta hadata da Abbanta, wai shin kishi haukane? Ita wadda take kishin akan ta riga ta tafi! Haba! Kuka ta fashe dashi mai kara harda shesheka ya juyo yana kallonta "Dama ki bar kuka ke kika jawo ma kanki!" Sai kuma ya dawo dab da ita yana nuna ta "Zan sake gayyatarsu ki basu hakuri sannan ki gyara barnar da kikayi!" Cikin kuka tace "Toh!" Ya nuna mata kofa "Tashi ki fita!" Ta sauri ta mike   gudu gudu ta fita tana wani irin kuka bata xame ko ina ba sai dakin Kaka, tana azkhar taji an shigo da kuka Hoodah na zuwa ta fada bisa Kaka ta kara fashewa da wani irin matsananci kuka! Kaka tayi hugging dinta tana dan bubbuga bayanta tace "Menene? Jalal ko Karima?" Cikin kuka tace "Su duka! Ni meye laifina? Kaka matar nan anya tanaso ta gama da duniya lafiya? Taje ta hadani da Abbana yayi mun wulakanci da magaganu marassa dadi sai kace ba yarsa ba? Ko makiyarsa bazaiyi mata abinda yayi man ba Kaka..." ta kara sa kuka sosai Kaka tace "Kiyi hakuri Hoodah! Komai na duniya mai wucewa ne wata rana sai labari, duk abinda ka shuka shi zaka girba don haka kiyi hakuri ki kai kukanki ga Allah shi zai share maki hawayenki...". A hankali tayi shiru tana share hawaye tace "Kaka ina Ashraf?" Kaka tace "Ya bar gari yau da safe Karima ta koreshi wai ya dawo gobe, shima ay nasan bazai so ya ganki tare da wani ba gwanda da akayi haka idan ya dawo kinga bai gani ba yafiye masa a'ala..." tace "Uhm..." kaka tace "Ki tafi ki huta sannan koda Karima ta fada maki maganar banza kar ki tsaya ki saurare ta kar ki bari maganganunta suyi maki tasiri a cikin rai." 

Washe gari Abba ya sake inviting dinsu a gabanshi da Karima yasa ta durkusa ta basu hakuri ta kuma assuring dinsu bazata sake ba...  Sultan ne yace "Babu abinda tayi mana meyasa xakace ta bamu hakuri?" Abba yace "Karka damu kaidai tunda nace haka kawai ka amsa, ba yadda ya iya haka yace ya hakura shidai bai san wani laifi tayi ba, kodan dan maganganun da sukayi amma ay bai kai ace har sai an sake taso suba saboda a basu hakuri!  Yayi ajiyar zuciya ya saki murmushi yace "Karki damu komai ya wuce bakiyi mun komai ba...." Abba yace "Toh MashaAllah, ya kamata kuci abinci kafin ku juya ko?" Suka amsa ta toh nan aka kaisu inda ake sauke baki aka shiga kawo masu abinci kala kala, Hoodah ta fara tunanin he didn't seem like a bad person saidai babu abinda zai chanza daga kiyayyar da take masa.....

Bayan sun tafi Sarauniya Karima ta kirata harabarta da isarta sai ta kyalkyale da wata irin muguwar dariya tace "Da fatan zaki kiyayeni Gimbiya, kinga dai kadan daga cikin sharrrina, ba'a ja da sarauniya! Dama sai dana ja maki kunne nace kar ki sake ki wulakanta su amma kika ji, ay ga irinta nan..." ta sake kyalkyalewa da dariya sannan ta daure fuska tamau kamar wata aljana. Hoodah tace "Bakomai duk abinda kikeyi Allah nagani kuma ki saurari sakamonki tun a nan duniya kafin ki iske na lahira, kinyi mun abubuwa na shanye saboda ina baki girma a matsayinki na matar mahaifina amma kibi a hankali kada wata rana na zubar da girman nan naki da nake gani...." Sarauniya Karima ta ce "Har kin isa? Na riga nayi maki zarra babu wanda ya isa ya ja da Sarauniya shi kanshi ubanki shakkata yake ballantana kuma ke....." tace "Naji amma ay ba'aja da ubangiji ko? Duk takamarka shine kadai zai iya dakai kije zan hada ki dashi..." ta daga mata hannu "Tafi ki bani wuri kuma kar ki manta dokata na cewar kar na sake ganin kin tsaya da Ashraf!" Hoodah tace "Ko babu soyyaya kar ki manta Ashraf dan uwa na ne bazaki iya karya bond din dake tsakaninmu mu ba!" Tana gama fadan haka tayi wucewarta zuciyarta na harbawa.

No comments: