Sunday 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 49

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤
    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ
        πŸ’šπŸ’™
            πŸ’™


MSBπŸ’–


Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM
*(zeebee)*
*(Xarah)*


Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.


*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*


49

Qarfe sha daya da rabi suka isa saboda sammakon da sukayi, da kwatancen da Khadija keyi suka isa, unguwar tana nan yadda Khadija ta santa sauyin da aka samu kadan ne, daga nesa ya faka motar kasancewar mota bata shiga lungun gidan, sun soma tafiya a yayinda da Khadija ke kallon wurin cike da alja'abi kamar bata yi rayuwa a nan ba, tana tafe tana tunanin rayuwar da tayi dasu Inna, sun isa daidai qofar gidan Khadija gabanta ya fadi, Heenad ta lura da hakan ta kamo hannun yar uwarta bayan tayi mata murmushi tace.
"Ki kwantar da hankali don Allah babu abinda zasuyi miki"
Daga haka suka shige gidan. Sallama suka shiga dokawa wanda babu kowa a tsakar gidan, suka kuma yin sallama a karo a biyu Inna ce ta fito daga bandaki da alama daga wanka ta fito. Tayi murmushi tana kallon baqin da ke tsaye bakin zaure ta qaraso tana fadin
"Lale ashe baqi mukayi ku qaraso mana"
Suka shigo gaba daya cikin yar doguwar baranda (veranda) ta shimfida musu tabarma ta kalle su tace.
"Ina zuwa bari in sanya kaya"
Suka ce to daga haka ta shiga zuciyarta cike da tunanin baqin nan don ita sam bata sansu ba. Cikin minti uku ta kammala ta fito, suna kallo ta bude randa ta kwalho musu ruwa sannan ta rufe da marfi ta dawo ta zauna sannan ta aje gabansu.
 Suka gaisa a mutunce sannan Inna ta kalle su tace
"Ban fa shaida ku ba"
Adnan ya gyara zama yana kallonta yace
"Inna ki kalli wannan kiga baki santa ba?" Ya qarasa yana nuna Khadija
Ta girgiza kai "gaskiya ban gane ta ba"
Khadija tayi murmushi
"Nice Inna, nice Khadija da kuka riqe a kwanakin baya wadda kuka nema kuka rasa a dalilin guduwa da nayi"
Inna ta kara kallon Khadija a razane tana salati
"Hadiza kece? Hadizar da na sani fa?"
Khadija ta girgiza kanta
"Eh nice dai Khadija da kika sani"
Inna ta hau salati tana tafa hannu, can kuma sai hawaye ta hau kuka sosai harda shasheka, su Adnan ke bata haquri. Bayan tayi shiru ne take cewa.
"Wato Khadija na jima ina nemanki in nemi gafararki, nasan abinda nayi miki a baya ban kyauta ba, wato ban fara nadama ba sai da muka fara shiga jarabawar Allah kala kala, tun tuni malam ke min wa'azi amma ina ban sauraronsa, sai da mukayi ma Nabila da Jamila aure, Nabila watanta daya kacal mijin ya koro ta, bayan sati daya Jamila ta biyo ta"
Tayi shiru a dalilin kukan da ya zo mata.
Ta numfasa ta cigaba
"Da kyar da sudin goshi muka maida Jamila don ita saki daya yayi mata ita kuwa Nabila saki uku ya danqara mata, babban tashin hankalin ashe da ciki ya koro mana ita, bayan nan Hassan ya kone da ruwan zafi ga wani irin talauci da Allah ya jarabe mu dashi, sai mu wuni mu kwana bamuci komai ba, ga rainon cikin Nabila dake mugun wahalar da ita karshe ma dole sai da muka kaita asibiti ga ba kudi, su kansu malaman asibitin sallamota sukayi a dalilin rashin kudi muka dawo muka cigaba da fama"
Tayi shiru tana share hawaye.
"Bayan sati biyu Nabila ta samu sauqi shi kuma Malam bamu san yadda akayi ba sai dai aka shigo mana da shi a sume, munyi magani munyi magani har mun gaji, ashe ajali ne ke kiransa, ranar da zai rasu yayi min nasiha akan abinda nayi miki ya dora da cewar tilas na nemi gafararki musamamn Nabila saboda duk abinda takeyi miki yana sane"
Khadija batasan sadda ta fashe da kuka ba
"Innalillahi wa inna ilahir raji'un ashe Baba ya rasu? Allah ya jikansa da rahama"
Suka amsa da amin. Inna ta cigaba
"Ki yafe mana Khadija don Allah ki yafe mana abinda mukayi miki kinji?"
Khadija tayi saurin cewa
"Don Allah inna ki dena durqusa min kina bani haquri, wallahi na dade da yafe miki, Allah ya yafe mana gaba daya dama ban riqe ki a zuciyata ba"
Inna tace
"Kayya Khadija kin dai fada ne, amma tilas abinda mukayi miki bazaki manta ba"
Khadija ta girgiza kanta tana murmushi kurum.
Inna ta kalli Heenad wadda sai yanzu ma ta lura da ita tace
"Wacece kuma wannan mai kama da ke?"
Khadija tayi murmushi
"Yar uwata ce" nan ta bata labari tun daga farko har karshe, bayan ta kare Inna ta kalle su cike da sha'awa
"Ikon Allah kenan, ashe ba Ummanki ta haife ki ba? Lallai Allah da iko yake" ta kuma kallon su Adnan
"Wadannan kuma fa?"
Wannan karon Khadija batayi magana ba tadai sadda kanta kasa tana murmushi.
Inna ta gane tayi murmushi
"Ah masha Allah Hadiza iko sai Allah ashe kinyi aure Allah ya bada zaman lafiya"
Ta karasa tana miqewa, kicin ta nufa can sai gata ta fito da dammammiyar furar da taji nono ta aje gabansu.
"ku sha hura kafin na girka muku abinci"
Khadija tace
"La Inna da kin barshi dama tafiya zamuyi"
Inna tace "a'a baza'ayi haka ba dole sai kunci abinci kafin ku tafi" ta fada a yayinda da take kokarin shiga kicin.

Sun sha furar sosai bama kamar Adnan gwanin shan fura yana sonta sosai yafi kowa sha.
Taliya Inna ta dafa da taji kifi ta kawo musu, nan ma sun saki jiki sunci sosai, sai da suka kammala a  lokacin sallar azahar ya kusa saboda haka sai da suka jira suyi sallah sannan su kama hanya.

Bayan sunyi sallah Adnan ya bude but ya fiddo tsarabar Inna wadda ya siyo a 6oye, Khadija tasha mamaki don kuwa buhun shinkafa ne, da na gero, sai galan din man gyada, sai katan din taliya guda biyu, da kuma  buhun masara. Inna harda kuka tayi, tasa musu albarka sosai. Khadija tayi ta satar kallon Adnan a yayinda shi kuma yake kashe mata ido, hakan da yayi ya bata dariya.
Suna shirin tafiya yaran gidan suka shigo, nan ma sai da Inna ta fada musu ko wacece suka hau murna, Khadija taji dadin ganinsu sosai don kuwa tayi kewarsu ba kadan ba.
Nabila ta fito daga daki tana hamma da alama bacci ta tashi hannunta rike da yarinya yar kimanin wata bakwai.
Tsai tayi tana kallonsu Khadija a yayinda Inna ke mata fada.
"Ke Nabila sai yanzu kika damar tashi ko? Tun yaushe na tashe ki nace kizo ku gaisa da su Hadiza ashe ke komawa kawai kikayi kika kwanta ko?"
Ta zaro ido waje
"Inna wace Hadizar?"
"Wadda kika sani mana"
Da sauri ta karaso tana kuka tana kare mata kallo sannan tace
"Khadija dan Allah abinda nayi miki a baya ki yafe min"
Khadija tace "don Allah ku dena bani haquri ni tuni na yafe muku wallahi"
Inna tace "kinga yar uwarta nan ashe TAGWAYE NE? Ga kuma mazajensu nan"
Nan ma zaro ido tayi waje riqe da baki alamun mamaki ta kuma kasa cewa uffan, sai dai kallonsu take daya bayan daya.
Nan suka hau bankwana, Kafin su tafi Adnan ya fiddo kudin da baisan ko nawa bane ya damqa ma Inna, ya kara kirgo dubu goma yaba Nabila. Nan suka hau kuka suna kara neman gafara, har dai su Khadija suka shiga mota suna mamakin yadda ta koma.
Suna takawa ciki Inna ta kalli Nabila
"Nabila kinga rayuwa ko? Sheyasa ba'ason wulaqanta mutum saboda bakasan ya gaba zata kasance ba, saboda wanda ka wulakanta  shine zai  taimake ka, yanzu dai kingani, mu kiyayi duniya wallahi"
Nabila da jikinta yayi mugun sanyi "uhm" kawai tace har suka shige ciki.



Maryam S belloπŸ’–

No comments: