Sunday 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 1 to 5

TAGWAYE NE? Na Maryam s bello {1 to 5}
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤           πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

                πŸ’šπŸ’™

                    πŸ’™
         MSBπŸ’–
Dedicate to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)* πŸ’˜

*(Xarah)*


Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zimunci amin.
 *πŸ’•Tagwaye ne?πŸ’•*
Bismillahir rahmannir rahim


01
Dattijuwar macece da bata haura shekaru talatin ba ke ta faman kai kawo daga kitchen wanda aka katange shi da 'yar rumfa, daga gani ansan bamasu hali bane, wani bokiti take 'dauke dashi fari wanda ke 'dauke da robobi, da yawa a cikinshi, daidai sa'adda ta zaune kan kujerar tsakar gida tana ta faman mita sai a sannan na 'kare mata kallo, tabbas fara ce tas wanda farinta har ya so yayi yawa, mai matsaikaicin jiki tana sanye da wata ko'da'diyar shadda kalar kunun kanwa ta kape 'daurin 'dankwalinta irin na talakawa amma duk da haka jelar kitsonta sai da ta le'ko, mitar da takeyi ya dawo da duba na gareta.
"Oh ni Bilkisu shin mey ke damun Khadija ne? Sai ka aiki mutum amma ya tsaya wasa, Allah ya shirye ta"
Ba'a cika minti goma ba aka doka sallama, hijabinta ta 'dauka daga kan igiyar shanya tare da amsar sallamar, gabanta sai da ya fa'di.

"Dama na sani ta ayyana a ranta"

"Hajiya barka da kwana?"

Cikin murmushin ya'ke tace.

"Barkanmu Anas an tashi lafiya?"

"Lafiya" kawai yace ya fara koro mata bayani kamar yanda ta zata.
"Hajiya dama Baba yace a fa'di maku yana dai 'kara tuna muku ku'din haya yana ta 'daga muku amma har yanzu baku bayar ba"
Tayi jim kamar mai nazari, can kuma tayi 'karfin halin cewa.

"Dan Allah ina mai 'kara bashi ha'kuri wallahi yanzu 'kokarin da nakeyi kenan in ha'da masa kudinsa gaba 'daya kayi masa bayani don Allah"

To kawai yace sannan ya juya tana jin sadda yace.

"Kullum ku kenan kawo kabli da ba'adi haba sai kace ku ka'dai ke fama da talaucin? "



Ta girgiza kai cikin takaici tare da juyawa ciki, daidai nan Khadija ta shigo 'dauke ta bokiti da alama marka'de taje, a gajiye ta 'karaso tare da sallama.

"Umma kinga na dade ko? Wurin ne layi sosai sannan ga k'u'din sunyin ka'dan damma Hamza ne akwai sanayya a tsakaninmu da bazaiyi mana ba"

Umma cikin jin tausayin kansu tace.

"Bakomai Dije Allah yayi miki albarka"

Khadija ta turo baki

Sarai Umma tasan ta tsani sunan dama zolayarta take.
Nan da nan Umma da Khadija suka ha'da kunun ayansu sai 'kamshin da'di yakeyi"
Bayan sun gama Umma ta dubi Khadija tace.

"Maza Khadija 'dauka Allah ya bada sa'a kinji"

Tace "to Umma amin bari nayi sauri na siyar sai na dawo"
* * *
Sanye take cikin wata 'yar ficiciyar riga pink ta mugun matse ta da wando three quarter kalar purple, ko dankwali bata sa ba sai wani gyale shara shara pink tare da pink jaka, tana shirin 'daukar mukullin motarta wayarta 'kirar iPhone 6s ta fara ruri.

 Ta kalli wayar tare da sakin tsaki sannan ta 'daga.

"Hello Heenad?"

Daga nan 'bangaren tana yamutsa fuska tace.

"Wai Abida meye haka ne? what's wrong with you? Bana ce miki gani nan zuwa ba haba"

Abide ta tuntsure da dariya tace.

"Me yayi zafi 'kawata? Allah ya baki ha'kuri sai kinzo"

Amin kawai tace ta katse kiran, ta suri key 'din motarta ta sauko downstairs.
Ba'a abinda akeji sai 'karar takalmanta tana wani yanga kai kace batason taka 'kasa.
Tana saukowa tayi kicibus da daddynta shima da alama office ya nufa, yana ganinta ya washe baki yace.

"My girl sai ina?"

Itama murmushin tayi da ya 'kara bayyanar da ainahin kyawunta har sai da kumatunta suka lotsa.

"Morning dad, fita zanyi"

"Ok my girl a dawo lafiya"

"Amin daddy dama yau da motarka nakeson fita please"

Without any hesitation daddy ya mi'ka mata key 'din motarsa yana mata a dawo lafiya"
Mami dake kitchen tana ha'da ruwan tea tayi tsaye cike da takaicin halin Alhaji.

"Shikenan komi yarinya takeso haka za'ayi kuma kayi magana yace batason 'yarsa, Allah dai ya kyauta"
"Morning mom nina fita"

Muryar Heenad ta tsinkaya daga bakin 'kofa.

Da sauri Mami ta fito tana fa'din.

"Haba Alhaji nasha fa'da maka ka rage 6ata yarinyar nan, abinda kakeyi yayi yawa, duk tabi ta raina mutane batasan datajar mutum ba ko ka'dan, ya kamata..."
"Kinga Safiyya banason zancen wofi to in banyi wa 'yata ba wa zanyi wa? Ita ka'dai fa Allah ya bani"

"Nasani ba'a ce kar kayi mata ba amma ka rage yanzu ji shigar..."

Kinga Safiyya ni na tafi office"

"Uhm Allah dai ya kyauta, to ka tsaya ka karya mana..."

"Na 'koshi" ya fa'di tare da yin gaba abinsa.
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™
MSBπŸ’–
Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*
Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.
*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*
02
Heenad na fitowa waje... tsarin gidan ka'dai ya isa ya tabbatar wa da mutum cewar akwai daula dan'kare a gidan, straight wurin motocin daddynta ta nufa, tazo bu'de motar da daddy ya bata kenan taja ta tsaya tare da saurin cire dan'kareren glass 'din da ke ma'kale a 'yar fuskar tata.
"What?!" Ta fa'da tana huci.

"Auwal"!!! Ta 'kwala wa mai wankin mota kira.
Da gudu ya rugo har yana neman fa'duwa, ya iso gareta cikin girmamawa ya isar da gaisuwarsa gareta.
Kallon arzi'ki bai ishe ta bare yasa ran zata amsa kamar kullum, dama bata cika amsa gaisuwa ba.
"Meyasa baka wanke motar daddy ba?" Ta tambaya cikin 'daure fuska.

"Wallahi Madam taki na fara wankewa shiyasa ban wanke wannan ba..."

"Mtswww! Zancen banza ma kakeyi to wallahi na baka minti biyu ka wanke motar nan in ba haka ba, sai dai kayi bankwana da aikin ka gaba 'daya stupid kawai, ina jiranka"
Ta wuce cikin gida cike da jin haushin Auwal.
Daidai bakin 'kofa tayi kici'bus daddy zai wuce office.

Ya kalle ta da mamaki.

"Ah 'yar baba ashe baki tafi ba, waya ta6a man ke?"

"Auwal ne mana bai wanke mota ba" ta fa'da tana zum'buro baki.

"Yi ha'kuri my girl nasha fa'da miki ki dena bata ranki a kan masu aiki, fa'da mun mey kikeso?"

"Ku'di" ta bashi amsa kai tsaye.

Nan da nan ya ciro bandir din 'yan 'dari biyar sabbi fil ya mi'ka mata"

Ta yamutsa fuska.

"Daddy nawa ka bani?"

"Dubu goma ne, ki saki ranki kinji? "

Ta zum'buro baki.

"Ni gaskiya daddy sun mani ka'dan"

Yayi murmushi

'Heenad rigima, to ga ten nan ki 'kara sama shikenan?"

Ta daka tsalle.

"Thank you daddy!"

Daga haka ta shigo gida shi kuma ya wuce office.
Mami dake tsaye bakin 'kofar kitchen tana sauraronsu ta daka mata tsawa.

"Ke! Zo nan"

Ta 'karaso tana 'kun'kuni.

"Bani ku'din nan"

Heenad ta kalle ta da mamaki tace.

"What? Haba Mami ni gaskiya baki kyauta mani haba!

Bakisan mey zanyi da ku'dinnan bane"

"Koma mey zakiyi dasu nace ki bani ko?'' Ta fa'da fuska 'daure.

Haka nan ba don taso ba ta mi'ka mata ku'din.

 Tana wani buga 'kafa a 'kasa alamun shagwa'ba.
Cike da takaici Mami tace.

"Sakaryar banza wadda batason ciwon kanta ba, ke bakisan kin girma bako? Kalle ki WAEC fa zakiyi very soon amma kina behaving kamar 'yar shekara biyar"
"Kar6i nan" ta cire dubu biyar ta mi'ka mata.

"Nasan dai wannan ya isheki"
Heenad ta'ki 'kar6a sai ma juya mata baya da tayi.

"Ke kika sani gasu nan kan table zan ajiye miki sauran duk lokacin da kike bu'kata a hankali sai a baki, amma ina amfani a dinga 6ata ki da ku'di?"
Daidai nan Auwal ya le'ko da sallama.

"Madam na gama" daga haka ya juya ya fice don yasan ba amsawa zatayi ba.
Tana ta ba'kin rai kamar ta mari Mamin ta kwashi ku'din ta fice da sauri daga gidan gaba 'daya ta suri motar daddy ta hau gudu kamar zata tashi sama.
Bata zame ko ina ba sai gidan su Abida (her best friend ) tana shiga ta fa'da 'dakinta tana huci, Abida ta 'dago daga karatun da ke tace.

"Ke kuma lafiyanki? Nayi zaton ma bazaki zo ba har na fitar da rai"

Tayi banza da ita kamar ba da ita take ba.

Sanin ba'kin halin 'kawar tata yasa daga haka taja bakinta tayi shiru bata 'kara cewa komai ba.
* * *
Gidan General Usman Buhari babban gida ne mai sassa daban daban, 'dakin uwar gidansa Hajiya Hasiya tana da manyan 'ya'ya maza da mata guda takwas maza uku mata biyar duk ta aurar da matanta kap sai mazan suka rage wanda biyu ke kan karatu wato Isma'il da Abba sai babban cikinsu Adnan wanda shi ya kammala karatunsa a Uk ya karanta likita a fannin hi'da (surgeon).
Sai matarsa ta biyu wato Zainab ana kiranta da Hajiya Abu, fitanniyar mata wadda ta 'dauki son abun duniya ta 'dora wa kanta, ita kuma yaranta hu'du ta farkon Bilkisu sai Fa'iza sai Ummi sai autanta wato Faruk. Daga haka Alhaji Umar bai sake aure ba.

Wannan kenan...
* * *
Da sallama ta shigo gidan ga gajiya ta kwaso ji take kamar ta fa'di 'kasa don yunwa, Umma na sallar la'asar, ta lalla6a ta ajiye bokitin ta fa'da ban'daki, wanka tayi sannan ta fito tayi alwalla ta gabatar da sallar la'asar.
Umma ta bu'de bokitin tayi dariyar jin da'di.

"Kaga 'yar albarka ta saido kuwa"

Khadija ta fito daga 'daki tana gyara 'daurin 'dankwalinta tace.

"Umma ga ku'din yau"

Umma ta kar6a dubu biyu da 'dari takwas ne cip.

Ta jinjina, "lallai Allah da iko yake, dama gidan basuda ko hatsi, ta cire dubu 'daya da 'dari biyar da ha'da cikin ku'din hayarsu sannan ta mi'ka ma Khadija sauran canjin tace mata.
"Khadija gasu maza jeki shagon Abdullahi ki anso mana garin kwaki na 'dari biyu sugan 'dari sai 'gya'dar hamsin daga nan ki siyo mana ruwa, maza ki dawo"

Ta 'karbi ku'din tace "to Umma" tare da ficewa da sauri don ta dawo da wuri.

❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

03

* * *

Nnamdi Azikiwe International Airport ABUJA
Misalin 'karfe bakwai da kwata na dare a hankali jirgi ke saukowa daga sararin samaniya an rubuta "British airways" ba tare da 6ata lokaci ba ya diro 'kasa. Sai da ya 'dauki tsawon minti goma sannan aka hangame 'kofar jirgin, shima a nan sai da aka 6ata minti biyu sannan naga mutane 'daya bayan 'daya suna fitowa...
Wata yarinya nagani da gudu 'yar kimani shekara sha biyu ta taho da gudu tana.

"Yayah...! Ga Yayah...!!!"

Daga nan sai wasu 'yan matan suka rufa mata baya da sauri suna kiran sunansa cike da jin dadi.

Can na hangi 'yan matan nan suna ta sauri burinsu su isa inda yayansu yake.
Tafe yake yana jan trolley mai 'dauke da akwatunansa gudu biyu manya manya, sanye yake cikin blue 'din shadda mai ma'tukar taushi ga she'ki tana yi, sai a sannan na 'kare mishi kallo.

Fari ne amma ba tas ba, yana da tsawo masha Allah sai cikar jiki, sanye yake da farin gilashi 'dan siriri wanda ya fito da fuskar tasa ya zauna das bisa hancinsa 'dan siriri, daga nesa ma kana hangen sajen fuskarsa wanda ya fito da ainahin kyan nasa, Adnan kenan, namiji mai cikar zati, gwarzon namiji, ha'kika duk wacce ta sameshi ta dace. Kuma kamar su 'daya da mahaifiyarsa sak hasken ne ka'dai ta fishi.
Hayaniya ce ta dawo dani daga duniyar tunani, wurin ma'kil yake da jama'a maza da mata yara da manya zagaye da Adnan, daka kalli kowa cikin farin ciki da raha yake. Bayan angama gaggaisawa da yaushe gamo, sai suka 'dunguma gaba 'dayansu suka shiga mota sai Maitama District.

'Dan'kareren gida naga sun dosa, koda aka wangame gate 'din sojoji ne burjit ke gadin gadin.
Babban parlour 'din gidan suka baje bayan sun kammala sallar isha'i sun ci abinci.

Adnan ya bu'kaci yin wanka saboda ya kwaso gajiya, bayan ya tashi sai naga kowa ma ya tashi ya nufi 'dakinsa, musamman yaran da naji Miminsu na cewa suje suyi home work saboda gobe akwai school. Don haka duk suka mi'ke.
Falon ya rage daga Hajiya Abu da wata yarinya 'yar kimani shekara ashirin da 'daya masu matu'kar kama da ita.
 Hajiya Abu tace.

"Badiya ki saki ranki ni nasan damuwarki, Adnan ko? To ba gashi nan ya dawo ba?"

"Uhm Yaya kenan, ke kike ganin ya dawo amma wannan mutumin wula'kancin tsiya ke gareshi, baki ga yadda yake wula'kanta ni ba..."

Da sauri Hajiya Abu ta rufe mata baki tare da jawo hannunta suka shige 'daki.
Hajiya Abu tace bayan ta kullo 'kofar.

"Wai ke sakarai ce kamar ba mace ba, ay dabara zakiyi irin taku ta mata ki samu ki janyo hankalinsa gare ki, kingane ay?"

Ta 'karasar maganar tana kashe mata gira.

"Uhm Yaya kenan ay kinsan yadda nake 'kaunarsa Kuma nagode da shawarki gareni zan kuma yi amfani da ita"

Hajiya Abu tace

"Yauwa tawan"

Daga haka suka 'kyal'kyale da dariya tare da kashewa kai kace 'kawaye.
* * *
Tara da minti hamsin tayi pakin motarta a ma'adanin motoci ta fito a gajiye li'kis.

Ko sallama batayi ba ta fa'da falo.
 Mami na zaune kan capet tana yanka kankana tana sha kawai taga mutum daga sama.

"Wash! Wallahi na gaji, Mami akwai abinci, ko a dafa mani indomie..."
Mami ta kalleta cike da takaici tace.

"Wakika ajiye da zai dafa miki indomie, 'yar rainin wayau kawai, ki gama gantalinki amma saboda tsabar raini ki dawo kina tambayata abinci shashasha wadda batasan inda ke mata ciwo ba, Wallahi kibi duniya a sannu, ki dena 'daukar duniya da zafi"

"Kuut! Ai fa ke matsalarki kenan Mami da zarar anyi magana sai ki fara wa'azi, wai me nayi ba daidai ba? Gidan su Abida fa naje..."

"Da Allah ni rufe mani baki sakarai kawai, wai shin ma kinyi sallah?"

"Nayi mana..."

"Kar kiyi mani 'karya, ki tashi kije kiyi sallah"

Ta'ki tashi.

"Zaki tashi ko sai na mauje ki...!"

Da sauri ta mi'ke tana fa'din

"Sai na fa'da ma Daddy bari ya dawo haka kawai an takurawa mutum.
Maryam S belloπŸ’–
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

04
Tana zuwa 'daki sai ta fa'da kan gado ta cigaba da chatting 'dinta hankalinta a kwance.
Mami ce zaune a falo amma tunda Heenad ta shige 'daki hankalinta yake bata wani abu, ita tasan da 'kyar ne idan Heenad sallar nan takeyi.

Ta jinjina.

Duk abubuwan da takeyi 'daurin gindin Alhaji ta samu.

Cikin 'kwarin gwiwar son tabbatar da zarginta ta haura sama.
Banko 'kofar da akayi ya sa Heenad razana tare da mi'kewa da sauri har wayar na 'fadowa daga hannunta.

Mami ta doka salati tare da kai ma Heenad bugu.
Lalala! Mami dukana fa kikayi?"

"An dake ki 'din ko kinfi 'karfin dukan ne? Sha sha sha kawai, wai ke bakisan kiyi sallah ba? Kamar ba musulma ba, balagaggiyar mace Kamar ki amma sai ance tayi sallah?"
"Ai fa wa'azin ne ya taso kuma"
Mami ta mauje mata baki.
"Bana son 'kara jin komai daga bakinki ki tashi kije kiyi sallah"
Mami ta 'dauke wayarta.
"Kuma daga yau ke da 'kara ganin wayar nan sai kin gyara halinki da sallar ki"
Daga haka Mami ta fice cike da takaici da jin haushin Alhaji.
Heenad tana kuka wiwi ta fa'da toilet ta 'dauro alwalla, haka ma tana kuka kamar ranta zai fita ta gabatar da sallah.

Ba dukan da Mami tayi mata ba take ma kuka ba, illar wayarta da aka raba ta da ita, saboda ji take kamar ranta ne aka 'kwace.
'Karfe sha 'daya daidai Abba ya dawo.

Mami na sanya kayan bacci ya shigo 'dakin da sallama, amsar sallamar kawai tayi ta cigaba da abinda take. Saboda wani irin haushin sa takeji kamar ta sha'ke shi.
"Safiyya me kuma ya faru naga kina wani share ni?" Abba ya fa'da yana kallonta.

"Me ka gani?" Ta fa'da tare da hawa kan gado ta juya masa baya.
"Safiyya ya haka? Ina magana kin juya mani baya" ya fa'da yana kallonta da mamaki.
"Bansani ba sai kaje ka tambayi 'yarka"

Ta fa'da with I don't care attitude.
"Safiyya badai wani abin kika yi mata ba ko, don nasan muguntarki kullum abun da'da gaba yake, ni na rasa meyasa kika tsani yarinyar nan" ya fa'da tare da fita daga 'dakin.
Shiga 'dakin Heenad yayi, iske ta yayi kwance 'kasan 'dakin tana kuka kamar ranta zai fita, tana ganin Abba ya shigo sai ma ta 'kara sautin kukan.
"Subhanalillah! Fatima me yasame ki haka? Hala mamanki ce ta ta6a ki?" Ya fa'da yana tallabo kanta.
Ta girgiza kai tare da 'kara fashewa da wani kukan.
"Yi shiru mamana, fa'da min abinda ya faru" ya fa'da cike da tausayinta yana goge mata hawaye.
Nan da nan ta fa'da masa 'karya da gaskiya tanayi tana sheshekar kuka.
"Zo muje mu sameta sai ta fa'da man dalilin 'kwace miki waya da tayi, ita ta siya miki ne?" ya fa'da yana jawo hannun Heenad.
Suna shiga ya shiga 'kwala wa Mami kira, firgit ta tashi saboda 'dan baccin da ya fara kwasar ta.

"Lafiya wai Alhaji wannan irin kira haka?"
"Lafiyar ce ta kawo haka, bani wayar Fatima" ya fa'da yana hararar ta.
"Wace waya?" Ta fa'da kamar ba tasan me yake nufi ba.
"Wayar Fatima da kika 'kwace zaki bada"
"Bazan bada wayar ba nace sai tayi hankali"
"Kinsan Allah Safiyya ki bani wayar nan tun kafin ranki ya 6aci, ki tashi nace"
Ba don taso ba ta 'dauko wayar ta mi'ka mai.
"Kasan Allah Alhaji ka cigaba da biye wa yarinyar nan wata rana zakayi nadama"
"Kar6i nan mama na, je ki cigaba da chatting 'dinki" ya fa'da yana murmushi.
"Allah ya kyauta amma ya kamata Alhaji kasani Heenad fa ba kamar yarinya bace ba..."

Bata gama magana ba ya shige toilet ya barta nan tsaye kamar wata sakarai.
* * *
Washe gari tun da sassafe ta tashi, saboda tana so ta kai marka'den kunun aya da wuri saboda kawarta Larai zata biyo mata suje kitso.

Bayan ta dawo, sai ta iske Umma na shiri da alama unguwa zataje.
Khadija ta kalli Umma tace, "Umma ya naga kina ha'da kaya wani wurin zamuje?"
Umma ta kalleta tana hawaye.

Nan da nan hankali Khadija ya tashi itama ta soma hawayen.
Umma ta kalli Khadija fuska duk hawaye tace.
"Khadija yanzu ina zamu dosa? Mai gidan ya tada mu yace wasu zai saka wasu 'yan hayan wai ya gaji da jiran babu"
Hankalin Khadija ya 'kara tashi itama kukan take wiwi saboda tasan muddin suka bar nan gidan to tabbas ba inda zasu je, don ita tun tasowarta batasan ko wa ba a dangin mamanta da babanta in ta tambayi Umma sai tace bata da kowa wai duk sun mutu. Wani lokacin ta yarda wani lokacin ta 'ki yarda, data gaji da tambaya dole daga 'karshe ta ha'kura ta yarda da cewar basuda kowa 'din.
"To Umma baki ce masa kin kusa ha'da ku'din gaba 'daya ba?"
Umma tayi dariyar da tafi kuka ciwo tace.
"Ba abinda ban gaya masa ba amma mutumin nan ya'ki saurare na, 'karshe ma cewa yayi ya bamu daga yau zuwa gobe mu bar masa gidansa"
Maryam S belloπŸ’–
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

05
Khadija tace.

"Umma yanzu ya zamu yi?"

Umman ta numfasa, tace.

"Ya fa zamuyi Khadija dole ne mu bar masa gidansa, mu doshi wani wajen"
In banda "innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ba abinda Khadija keyi.

 A yanzu ma hawayen sun kafe, tunanin makomar rayuwarsu kawai takeyi, sai dai tayi imani da cewar Allah zai taimake su, kuma zai karesu a duk inda suke, cikin sanyin jiki ta mi'ke ta fara tattara duk wani abin amfanin su wanda suke so, ta killace su wuri 'daya.
Da daddare suna zaune tsakar gida, Khadija ta dubi Umma tace.

"Umma wai bazaki bar tunani ba? Kar kuma wani ciwon ya same ki, barmu muji da wannan tukunna"
Umma ta sauke tagumin da tayi ta dubi Khadija tace.

"Ai dole ne in shiga damuwa Khadija, ina tunanin rayuwarki, kina 'yar yarinyar ki amma zaki shiga gararin rayuwa ina matu'kar tausaya maki"
Khadija tayi murmushin ya'ke.

"La Umma indan wannan ne kar ya ma dame ki, kowa da yadda Allah ke tsara masa rayuwarsa, kuma komai na duniya mukaddari ne ko kuwa?"
Itama Umma murmushin tayi tace.

"Tabbas hake ne Khadija Allah kasa mu dace duniya wa lahira.

Tace "Amin"
Washe gari ko wayewa gari bai ida yi ba suka ji ana bubbuga musu 'kofa, dama 'kyauran irin na 'karfen nan ne, don haka har cikin kansu suke ji, gabansu ya yanke ya fa'di, Umma ta mi'ke daga lazumin da take yi da nufin fita, Khadija tayi saurin ri'ko mata hannu tare da girgiza mata kai. Umma ta dube ta tace.

"Khadija menene?"

Khadija tace.

"Umma kikasan ko su waye da zaki je"

Umma tace.

"Nasan bai wuce Alhaji Hamisu bari naje na gani"
'Karar buga 'kofar ya sa Umma ficewa da sauri, gaban Khadija ya cigaba da fa'duwa tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta.
Hannunta na kyarma tare da bismillah ta bu'de 'kofar, shi 'dinne kuwa, mutum ne mai matu'kar 'kiba da fa'din jiki, yana sanye da brown shadda 'ko'ka'kiya tsabar 'ko'kewa daga brown ya komawa fari fari, ya 'dora babbar riga, kansa hula ce amma a karkace, saboda tsabar mugunta daga ganinsa anga masifaffe. Aswaki ne hannunsa yana ta faman goge baki.
Umma ta gaishe shi cikin ladabi, amma maimakon ya amsa sai cewa yayi.

"Da ban kwana ba da kinganni? Da fatan dai kun harha'da kongwamman ku, saboda 'karfe takwas masu gidan zasu 'ka6i mukulli"
Umma ta kalle shi a razane tace.

"Takwas kuma Alhaji? Dan Allah kayi ha'kuri mu gama kwashe kayanmu zuwa yamma sai ka kar6a"
Ya 'kyal'kyale da wata irin muguwar dariya yace.

"Kina nufin su kuma ba'kin nawa inyi yaya dasu kenan? Bazai fa yiwu ba gara tun muna shiri da ku ku tattara komatsan ku in ba haka ba zan sa ayi waje da kayayyakin ku, kuyi ku shirya ku fito, sau nawa ina 'daga muku haba abin ya isa"

daga haka ya baza rigar sa yayi gaba yana fa'din "sai na dawo 'kar6ar mukulli"
* * *
Tafe take tana shantaka gudu kamar zata tashi sama, tana jin wa'kar "The hearts wants what it wants" Ta Selene Gomez, a tsorace Abida ta kalle ta tace.

"Gaskiya Heenad kibi mu a hankali haba wai saurin me kikeyi ne?"

Ta kalli Abida ta saki tsaki tace.

"Haba Abida ke kin cika mita ina gudun da nakeyi a nan?"

"Ai ba dole, sai in fita daga motar haka kawai kije ki kashe mu bamu shirya ba"
Burki taja da 'karfi ji kake 'kiiiiiiiii!

 Abida ta saki 'kara tare da juyowa a tsorace, tace "Heenad"!

Ita kanta Heenad ta tsorata don sai zare ido take. Wata ba'kar jeep ce tsaye gabansu ashe karo suka kusan yi wanda ya jawo Heenad ta taka wannan burkin ba shiri.
Da 'karfi Heenad ta fito daga motan da niyyar masifa, sai dai tana fitowa taga wurin duk jama'a, kowa na tofa albarkacin bakinsa, duk yawanci Heenad suke zagi ganinta 'karamar yarinya tana wannan gudun yasa suke zagin nata, a zuciye tayi gaban jeep 'dinnan daidai nan ya fito cikin 'kananan kaya sanye da ba'kin jeans da ba'kar top an rubuta "touch me" a jiki, ba tare da ta kula ba kawai ta watsa mishi wani irin lafiyayyen mari a fuska, bata daddara ba ta cigaba da yarfa mishi masifa ha'de zagi sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru, sai a sannan ta 'kare mishi kallo, sai kuma taji ta kasa cigaba da magana, shi kuma kallonta yake irin ke mahaukaciyar ina ce ke, still baiyi magana ba, sai daga baya ya bu'de motar zai shiga ya juyo da manyan idanunsa da suka ka'da sukayi ja tsabar bacin rai, yana kallonta alamun zaki gane kurenki, ya dake yayi ta maza yace mata "thanks for the slap" ya juya ya shiga mota ya tafi ya barta tsaye kamar gunki.

Tayi tsaye tana ayyana kamanninsa a ranta.
Maryam S belloπŸ’–

No comments: