Sunday 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 46

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤
    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ
        πŸ’šπŸ’™
            πŸ’™


MSBπŸ’–


maryamsbellowo.wordpress.com



*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*



46


A kwana biyu da suka gabata komai ya lafa ma su Khadija wanda yanzu Adnan ya dena nuna mata qyama ko makamancin haka. Yau ma kamar kullum tana zaune tana karanta wani novel mai suna "Weird in love" tayi nisa don kuwa bata ji shigowarsa ba sai dai taji an fizge littafin hannunta, ta dago suka hada ido ya sakar mata murmushi, ita kanta sai dai taji ta mayar masa da martani. Sai dai zuciyarta cike da fargabar abinda zai biyo baya idan ta kusance shi hakan yasa ko bata yarda ta matsa kusa da shi, shi kansa ya lura da hakan tsananin tausayin matarsa yakeji, hakan yasa takanas ya je ya siyo mata gifts don yana so ya gusar da damuwar da suka shiga a kwana biyun da suka gabata. Sai dai ance addu'a itace tagobin mumini, cikin hukuncin Allah komai ya lafa.
Hannunta ya kamo ya miqar da ita tsaye, ya sumbaci kuncinta tukunna ya soma magana.
"Khadija a zahirin gaskiya banida bakin da zan baki haquri, tabbas haqurinki ma riba ne kuma dama ance Mahakurci Mawadaci tabbas haka maganar take, amma har ila yau bazan gaji da baki haquri ba don Allah kiyi haquri..."
Da sauri ta katse shi
"Don Allah ka daina bani haquri, wallahi ban riqe ka a zuciyata ba hasalima na yafe maka duniya wa lahira"
Yayi qayataccen murmushi ya bude wata yar leda mai kyau ya fiddo wani dan akwatin zobe dan qarami ya bude shi yana fuskantarta. Zoben silver mai shape in heart sai shinning yakeyi.
Dan murmushi tayi ta rufe idonta da hannuwanta, hannunsa yasa ya sauke mata hannun sannan ya jawo hannun damanta yana kallonta yace.
"Wannan zoben da zan sa miki shine alqawarin da zan daukar miki na qaunar ki tare da kulawa da ke har abada, sannan ina so duk sadda kika kalli zoben ki dinga tunawa dani"
Ya ciro zoben daga cikin dan akwatin ya zura mata a dan siririn yatsanta cif! yayi mata kyau yayi mata daidai kamar don hannunta aka yi zoben. Yayi kissing hannun sannan ya zaro wani akwatin zoben ya miqa mata yana murmushi.
Ga nawa ki saka min a hannuna duk sadda na kalle shi zan tuna da ke"
ta sadda kanta tana murmushi, sannan ta zura mishi zoben. Kamo ta yayi ya rungume abarsa yana jin sonta na ratsa ko wane saqo na jikinsa da jijoyinsa. Sai kuma ya sake yana kallonta cike zolaya yace.
"Ashe jinina yana nan yana yawo cikin jinin matata, kinga hakan ma yana nuni da ni dake duk daya ne, a lokacin da kike neman taimakon jini aka rasa wanda zai baki ashe ni mijinki ni zan baki" ya qarasa yana murmushi hade da daga mata gira.
Ita farin cikin da take ciki baya misaltuwa, ta yi godiya ga Allah da ya dawo mata da mijinta ya dena jin warinta sannan zata cigaba da addu'a Allah ya qara daidaita tsakaninsu.
Hannunsa ya kalla yana fadin.
"Bari naje masallaci don sallar azahar yanzu zan dawo"
Tana shirin shiga dakinta don yin sallah wayarta ta fara ruri. Ganin Umma ya sanya ta dauka gami da yin sallama.
Umma tayi murmushi
"Khadija ya kuke ya mijinki?"
Ta danyi murmushi
"Lafiya lau Umma ya qarfin jiki?"
Tace "Alhamdulillah na samu sauqi sosai jibi idan Allah ya kaimu zamu dawo"
Cike da farin ciki tace
"Alhamdulillah Umma! Kin fara tafiya?"
Umma tayi murmushi
"Ina takawa Khadija, ga Ummi zaku gaisa"
Bayan sun gaisa sukayi sallama daga haka ta shige bayi don yin sallar azahar.

* * *

Washe gari tun qarfe tara na safe Zee ta sanar ma Badiya zasu tafi qauyen Dan ja don bokanya ta tabbatar mata dole sai Badiyar taje aikin zaiyi yadda ya kamata.
Qarya tayi tace zataje gidan gaisuwa baban qawarta ya mutu.
Sun hau titi Badiya na kur6ar lemo a yayinda zee ke tuqi suna ta hirar yadda bokanya ke aiki kamar yankan wuqa.
Har sun kusa kaiwa ba tare da Zee ta kula ba wata daf tayo kanta sai dai ihun Zee Badiya taji.
Kafin wani lokaci mutane an taru kansu da qyar aka zaro su, ita Zee ma sam ba'a gane ta duk ta qone ita kuwa Badiya jina jina haka aka fiddo ko wacensu batasan inda kanta yake ba.
Cikin ikon Allah aka samu aka zaro wayar Badiya duk ta fashe da qyar aka lalubo number farko aka kira.
A lokacin Adnan ya dawo daga masallaci suna zaune kan dinning suna cin abinci wayarsa ta fara ruri, ganin mai kiran ya sa ya saki guntun tsaki yaqi dagawa. Haka aka kuma kira a karo na biyu cike da jin haushi ya katse.
Khadija zata kai loma ta tsaya tana kallonshi. Can kuma ta numfasa
"Ka dauka mana"
Yayi tsaki "Badiya fa ce"
Tayi murmushi
"Kayi haquri ka dauka dan Allah qila akwai babban dalilin..."
Kafin ta qarasa wani kiran ya shigo, ba da son ransa ya daga ba.
"Hello" yace daqile, jin muryar namiji ya sashi saurin cewa
"Waye kai ina mai wayar?"
Adnan ya miqe tsaye yana salati, jin haka yasa yan hanjin Khadija suka hautsine ta miqe tana jiran ya gama taji ko lafiya?
"Ok gamu nan zuwa yanzu"
Cike da tashin hankali Khadija tace
"Don Allah meyafaru"
A sanyaye yace "Badiya ce da qawarta sukayi hadari a hanyar Dan ja, gashi nan za'a juyo da su nace zamu iske su asibiti"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"
Daki ta ruga ta dauko hijabinta jikinta sai rawa yakeyi, Adnan na tsaye yana sanar da su Abba halin da ake ciki. Bayan ya kammala suka fice da sauri ko wane cike da tashin hankali ba kamar Khadija da gaba daya hankalinta ya tashi addu'a take Allah yasa da ransu.

Sun isa asibitin inda suma yanzu aka shigo da su cikin Ambulance, nan aka fiffido su, Khadija ta fashe da kuka tana karanto innalillahi, haka aka shiga da su don ceto ransu. Suna nan sai gasu Abba dasu Isma'il suma sun iso, tuni Khadija ta sanar da Mami da kuma Heenad halin da ake ciki.
Sai da aka kwashi akalla awa biyar ana tsaye wanda da qyar aka samu Badiya ta farfado, sai dai damejin da qafarta tayi ba kadan ba. Dakin hutu aka kaita, ita Zee har yanzu ba'a san babin da take ciki ba.

Kwance take kan gadon asibiti hawaye kawai ke bin kuncinta, ko magana ba ta iya yi ita kadai tasan azabar da take ji, likita ne ya shigo bayan ya dubata ya kalli su Abba da Adnan da ke tsaye yace yana son ganinsu. A sanyaye suka bi bayansa a yayinda da Khadija ta shiga don zama da ita.
Bayan sunje ofis din likitan bai 6oye musu komai ba ya soma magana cike da damuwa.
"Mun yi iya bakin qoqarin mu don ceto qawarta, da qyar muka samu ta dawo daidai sai dai kanta ya bagu ma'ana dai ta kamu da ta6in hankali"
Wurin ya kaurade da salati, likitan ya cigaba da magana.
"Ita kuma dayar babu wani dogon bayani illa qafarta daya za'a yanke wanda tilas sai anyi aikin kafin gobe idan ba haka ba akwai matsala"
Salati kawai su Abba keyi wanda tsananin tashin hankalin ya hana su magana.



Maryam S belloπŸ’–

No comments: