Thursday, 17 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 17

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 17}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



"Kayi hakuri Sultan attackers ne da alama dai makiya ne suka diro, kafin muyi wani yunkurin kama su har sun gudu, kayi hakuri amma duk sunada rai babu wanda ya rasa ransa a cikinsu, munyi making duk wani arrangement a fita dasu waje yanzu nan da awa uku za'a tafi, sannan likitoci sun tabbatar mana cewar indai aka barsu a nan zasu iya rasa ransu..." A hankali ya dago kansa yace "Kawu? Yaushe kazo?" Kawu Murtala yace cikin damuwa "Saukar dare nayi jiya sanda na iso kayi bacci, da niyyar in kawo ziyara na taho ashe abinda zan tarar kenan?" Ya fada yana fashewa da kuka. Wata ajiyar zuciya suka sauke shida Hoodah jin ance ay basu rasu ba, kafin Hoodah ta rike Sultan tana sheshekar kuka, tabbas tayi bonding dasu sun zama tamkar iyayenta. Kafin nan da minti 30 sai ga ambulance din asibiti ta iso nan da nan aka fara basu taimakon gaggawa, Sai da aka jojjonasu da machines sannan sukayi masu bankwana nan aka samu kannen Ummi su biyu mace da namiji zasu tafi dasu, kamar ransu xai fita haka suka dinga yi masu Abbi sallama kamar suna jinsu, bayan sun tafi nan Sultan yayi tsaye yana bin motar da kallo har ta bace bat bai daina kallon wurin ba, ji yayi an riko hannunsa ya juyo da kyar yaga Hoodah ce tsaye idanu sun kumbure, janshi ta shiga yi da kyar yake daga kafarsa kafin ya iya takowa zuwa babban parlor, memories suka dinga dawo masa kala kala idan ya yakalli parlorn, zama yayi dirshen a kasa hannunsa cikin na Hoodah itama a hankali ta silale a gun ji yake kamar wanda aka zare ma lakka, kuka yake so yayi amma jin yadda Hoodah tayi squeezing hannunsa ya sanya ya fasa kukan, yafi minti sha biyar a haka kafin a hankali ya fara magana "Ummi da Abbi nasan ko bakuji abinda kowa yake fada ba nasan zakuji nawa, ko ban fada ba nasan kunji Sultan, your one and only son, sai cewa sukeyi ba lallai bane ku dawo da rai daga can zaku iya tafiya ku barni shikenan bazan sake ganinku ba? Sai dai nasan ba gaskiya bane, how can they leave their life and go elsewhere? Am their life bazaku iya tafiya ku barni ba ko Abbi? Ko Ummi? Kuma ko su waye suke da sa hannu a wannan muguntar na gano su wallahi sai na dau fansa!" Sai ya fashe da kuka dama Sultan ya lafiyar kura bare kuma tayi hauka? Ay indai kuka na baya masa wahala. Hugging dinshi Hoodah tayi tana share hawaye, breaking hug din yayi "Mamata tafi ta kowa she can sacrifice the world for you just to be happy, nasha fada mata  I love her so much, kar tayi losing hope and keep fighting, fight for me and for us, Ummi batada makiyi ko daya toh waye yake son ganin bayanta? Also Abbi, you are everything a son would have ask for, you will make it inshaAllahu I know you will I have faith in Allah, InshaAllah zai dawo daku lafiya..." Hoodah ta share hawayenta ta fara magana "Tunda nazoo nan sun nuna man kauna, sun yarda dani they also trust me, i look up to them as my biological parents, banida mahaifiya bansan dadinta ba, amma danazo ta fara maye man gurbin Ammina, dan Allah Ummi be strong for us, I need you more than i have ever needed anyone in my life, idan babu ke our lives will have no meaning, dan Allah for our sake be well again." Ta girgiza hawaye na cigaba da shatata "Abbi, he was like a father to me, ya kaunace ni, dan Allah ka warke ka samu lafiya..." ta karasa muryarta na rawa, kan cinyarta Sultan ya kwanta "Nayi missing su Abbi kina ganin zasu dawo?" Sai yanzu hawayen nashi suka samu damar zuwa yadda ya kamata fiye da da, wani irin tausayinsa ke ratsa ko wane lungu da sako na jikinta, tasan zafin rashin mahaifi ko mahaifiya ta rasa daya bataji da dadi ba inaga Sultan da yake neman rasa duka nashi a take? Wa yasani ko zasu dawo ko bazasu dawo ba? Hannu tasa cikin sumar kanshi a hankali tana murzawa "I can't say zasu dawo ko bazasu dawo ba Allah kadai yasan gaibu, Sultan abinda zamu sa ma ranmu shine Abbi da Ummi suna sonmu bazasu yarda su tafi su barmu ba zasu dawo InshaAllah, nasan kana sansu more than anything else amma ka yarda dani they're part of me too, I lost my mother at a very tender age, Ummi is now the only mother figure I have in my life..." sai kuma tayi shiru ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, a hankali Sultan ya dago yadda take kukan tamkar za'a zare mata rai, take tausayinta ya kama shi, a hankali ya mike zaune ya matso daf da ita ya rungume ta a kirjinsa yana shafa kanta, "Duk yadda rayuwa ta kasance maki zaki iya zuwa ki sameni Hoodah, don naga alamar banda abinda ya faru akwai wani abu dake damunki, ban dade da saninki ba amma ki yarda dani nasan kina cikin damuwa, bansan meke damunki ba amma zan iya baki hakuri idan zaki iya hakura, kiyi murmushi kinada wadanda suke sonki a rayuwa wadanda ko duniya zata juya maki baya suna tare da ke Hoodah, nasan Abbi da Ummi suna ciki sannan nima ina so ki sani cikin jerin mutanen nan a cikin rayuwarki." Shidai yasan bazai iya cewa yana sonta ba dan yasan babu digon sonta a cikin ransa, amma kuma he respect her, cares for her and also adores her, yana jin dadin zama da ita yasan shi dai ba soyayya bace tou menene? Shiru Hoodah tayi kafin a hankali ta dago da idonta tana kallonsa, ido cikin ido suke kallon juna "Are you sure duk sadda nake cikin damuwa zan iya fada maka? I am safe with you right?" Gyada mata kai yayi ba tare da yace uffan ba, ajiyar zuciya ta sauke, a nan suka cigaba da zama kowane na addua'ar samun lafiyar su Abbi. Murtala ne ya shigo da tun dazu yake tsaye bakin kofa ya karaso ciki zama yayi kan kujera ya dafa shi "Ka dangana addua'ar ka ita kadai suke bukata ba kuka ba, bacin haka ma kai ne zaka jagoranci mahaifinka har Allah ya basu lafiya, kai zaka karbi mulkinsa kai zaka cigaba da yi har ya dawo cikin koshin lafiya." Girgiza kai yayi "Bazan iya ba kawu, mulki dawani sarauta ni ba damuna sukayi ba sheyasa ma kaga ban fiya xama nan ba saboda bana son wani abu daya shafi hakkin mutane a kaina, dan haka wallahi bazan iya ba kawu." Murtala yace "Hakuri zakayi wa yake dashi da zai iya karba in ba kai ba? Dolenka zakayi ay ba wai don kana so ba..." yace "Kaifa? Ba dole sai ni ba, badai rikon kwarya bane don Allah ka karbar masa kafin Allah ya basu lafiya..." yar razana yayi "A'a Sultan kabar ma wannan maganar ma hakan bazai taba yuwuwa ba, kaine ya cancanta ka karba bani ba kaima kasani..." Sultan yace "Bakomai kawu, ni da bakina nace na bar maka tou meye a ciki? Kaima fa yayan Abbi ne uwa daya kuma uba daya Menene don ka karbar masa mulki?" Kawu Murtala yace "Jayayya bashida wani amfani Sultan, amma tunda ka kafe ka nace zan karba din nagode." Sultan yayi murmushi "Bakomai." D'aga Hoodah yayi data fara bacci bisa kafafarsa yace "Tashi mu tafi bangarenmu, an kusa kiran asuba..." mikewa tayi ya kama hannunta suka tafi sashensu. Saida da suka yi nisa kawu ya saki murmushi da shi kadai yasan ma'anarsa sannan ya dauki wayarsa ya kara a kunne....

****

Da daddare Sadiya d'aya daya cikin bayi ce ta kawo masu dinner wurin karfe taran dare, gaishe su tayi ta aje masu kan dining kawai ta juya ta fita, tuwon shinkafa ne da miyar gyada, shi kuma Sultan ko miyar miye bazai ci ba yadda ya tsani tuwo, indai kaga yana cin tuwo toh Ummi ca ta girka duk bala'in mutum bazai ci indai ba ita tayi ba.

Hoodah ta mike ta zuba masu a plate daya dan tasan baci zaiyi ba sosai, hannunsa ta kamo har sai ya zauna k'asa kusa da ita, "Kaci abinci please." Abinda tace kenan da disashiyar muryarta, girgiza kai yayi a shagwa6e ya tabe baki, nan taga zallar shagwa6a a fuskarshi tayi murmushi, koda Ummi ce tasan bazai ci tuwon nan ba yau saidai in ma zaici saidai ta bashi a baki. "Ko na baka a baki nima?" Ya girgiza kai alamun a'a "Dan Allah haba Sultan ka daure kaci please." Tayi rai rai da idanu kamar zatayi kuka, duk yinin yau ba wanda yaci wani abun arziki, "Kici kema toh." Ya fada wane karamin yaron daya yi kuka, "A'a sai kaci sannan zanci nima." Abinda tace kenan tare da kai hannunta wurin bakinsa amma ya juyar fa fuska "A'a kinga Hoodah kici abincin nan yanzu idan su Abbi suka dawo sukaga kin rame zasu ce mugunta nake maki, bana baki abinci ko bazasu ce haka ba?"  Ya fada idanunsa na ciccikowa da kwalla, dan murmushi yayi yace "Abbi will be like "Sultan bana son muguntarka fa yanzu dan kaga bana nan shine ko abinci baka bata? So kinga please kici." Girgiza kai tayi tana sharbar hawaye "Zasu dawo, kuma Abbi bazai ce maka haka ba, zanci abincin amma kaima sai kaci." Ta fada tana tallabo fuskarshi kafin a hankali ta dinga feeding dinsu tare. 

Washe gari Sultan yayi shawara take kuma waziri da sauran manyan manyan mutane bayan jayayya na wani lokaci daga karshe aka yanke baza'a nada shi ba amma zai zamana shine zai dinga tafiyar da harkokin garin, da kuma duk wasu ayyuka da ya kamata yayi. 

Wayarsa ce ta fara ringing sai da ya ke6e ya dauka "Da fatan kayi completing abinda na saka?" Yayi kasa kasa da murya "Nayi saidai duk basu mutu ba kamar yadda muka tsara amma dai rai a hannun Allah, saidai fa ina jin tsoro don garin gaba daya an baza yan sanda ana gudnar da bincike..." ta sheke da dariya "Kai da Allah! Nace maka babu ubanda ya isa ya gane mu dan haka kar ka damu kaidai ka cigaba da yin duk abinda na saka..." yace "Toh shikenan ranki ya dade angama," tace "Bissalam." Kit ta kashe wayarta tana wani dariya.

*****

Satika sun tafi tun su Hoodah nasa ran dawowar su Abbi har suka hakura, ya zama busy tare suke gudanar da harkokin gari shida kawu Murtala, kawu murtalan shine yake jawo shi a jiki yana nuna masa aiyyukan tun baya yarda har ya hakura yana binsa..... 

2 days duk Sultan ya zama wani iri dashi kullum cikin damuwa zaka ganshi gaba daya ya chanza, gashi baya bacci sosai cikin dare wani lokaci sai Hoodah ta farka taga hawaye na sauka bisa kuncinsa, haka zatayi ta lallashinsa wani lokacin sai ta fara kuka sannan yake shiru gaba daya Sultan yazama wani sabon Sultan ba wanda tasani ba a da. Wannan Sultan din baya son magana, ya wani da  rashin son mutane Sultan din yanzu sai tayi magana yafi sau biyar bai bata amsa ba. Gashi kullum yayi video call da yan asibiti basu yarda su bashi yayita roko a nuna masa fuskokinsa, kullum idan yace zaije India sai a hana shi ace ya zauna ya kula da harkokin Abbi. Kwana biyu da suka wuce Hoodah ta fara lura da yanayinsa ya fara canzawa, ga wani irin mugun bacci daya koya Idan ya shigo gida sometimes a parlor zai zube. Toh yau kam abin yafi na kullum har sha biyun dare bai dawo ba ta kalli window yafi a kirga shiru kakeji, bataso tasa ma ranta tunanin da takeyi a kansa ya zama Gaskiya, tasan alamu tasan signs tasan how they act, babu abinda bata gani ba tana yarinya Umma babu abinda batayi, salo salo na iskanci kala kala, don har mamaki takeyi wai mace da wannan dabi'un? "Ya Allah ya Allah kasa ba haka bane!" Abinda ta fada kenan tana faman zagaye parlornsu, ta zauna ta tashi, ta shiga daki ta fito har daya ta gota bai dawo ba, zama tayi kan kujera ta dafe kai kamar daga sama taji an banko kofa, tangadi yakeyi kamar zai fadi ga robar coke yana rike da ita a hannu daya, a razane ta mike ta karasa inda yake tsaye kafin ma yayi wani yunkure har ta fizge robar ta bude ta da sauri takai hanci kawai saita saki robar duk abin ya malale a kasa, tana furta "Innalillah wa inna ilahir rajioon! No not you Sultan not you!" Kafin kace me hawaye ya wanke mata idanu, wani irin kuka ta saki tana girgiza kai, baya baya takeyi tana faman girgiza kai, tasan kamshin abin don tun batada wayau take ganin kwalbar a dakin Umma tasha boyewa, har dauka take tana sinsina don haka tasan wannan ko menene har ta mutu bazata taba manta warinsa ba. "Sultan me ka jefa kanki a ciki? What have you gotten yourself into? Meka rasa Sultan? Dama baka dauki kaddara ba? Wannan wace irin rayuwa ce ka jefa kanka a ciki?"  Kuka takeyi bil hakki kamar ta fiddo Zuciyarta ko zataji sanyi, yanzu Sultan mijinta shine ya koma dan shaye shaye? Tangal tangal yazo inda take sai tayi sauri taja baya "Waya jefa ka wannan harkar Sultan? Innalillahi wa inna ilahir rajioon! Nasan dai ko kayi magana yanzu duk karya ce." Ta ma rasa abinda ya kamata tayi, tasan dai da kyar idan ba wani bane ya jefa shi wannan hanyan.... toh who? Umma? But how? Umma dake can Agadez ina taga Sultan? Haka ta jera ma kanta tambaya amma ba amsa. Zai fada kan kujera tayi saurin damko masa riga "Let's go to bed...." kallonta yakeyi kamar wani sakarai, toh wai kukan me takeyi? Shi ya ya kamata yayi kuka ta zubda mashi drink, drink din da kawunsa ya basa yace idan yasha zai rage damuwa, yasha kwalba tafi uku a yau, sanda ya fara bashi da da farko ya nuna bazai sha ba sai yace masa ay coke ne kuma mai sanyi, nan ya kafa kai ya shanye, toh tun daga wannan ranar kullum sai yaje ta bashi yasha, Hannunshi ta kamo ga hawaye gawani tukar bakin ciki dake cizon ranta, fizge hannunsa yayi yawani tunkudeta ta fadi tim bisa kujera!

Wednesday, 16 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 16

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 16}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



A hankali yake rocking dinsu yana dan jijjigasu kafin yaji chanji daga yanayin saukar numfashinta wanda hakan yana nuni da cewar tayi bacci. Daukarta yayi ya kaita kan gadonsa har ya juya zai tafi sai yaga alamun hijab dinta kamar ta takura mata, cire mata hijab din yayi sannan ya sunkuyo yayi mata dan karamin peck a goshinta karasa kashe fitilun yayi zuciyarsa cike da tausayinta.

A hankali ta bude idanunta nan ta fara juye juye, tana ganinshi ya taho gunta sai ta dan tsorata ita tabata yayi jya dafa hannunta "Calm down a Hoodah, babu abinda zan maki kinji?" A hankali ta sauke ajiyar zuciya ya xauna kusa da ita yana sanye da towel yana kallon face dinta da hawaye har ya taru "Hoodah kukan me kikeyi?"  Ya fada cikin sauti mai taushi mai kuma kwantar da hankali, ji yake kamar ya bude kirjinsa ya sata a ciki yakeji, shiru tayi ta kasa magana, matsowa yayi dab da ita ya zauna yana goge mata hawayen fuskarta "Do you still trust me? Komai zai faru a gaba zaka yi trusting dina?" Bai bari ta karasa ba yayi hugging dinta hade da shafa gashinta, "Look at me Hoodah..." ya fada yana scooping fuskarta da hannuwansa biyu a hankali ta sauke idanuwanta cikin nashi "I trust you dear, I will never let anything happen to our relationship again, and I promise you Hoodah zan gano ko wacece take neman tarwatsa farin cikinmu, it's fine kinji?" Kuka ta fashe dashi "Thank you Sultan, nagode I feel relieved now..." dan Murmushi yayi mata "Tou kukan na menene kuma? Sai kace ance maki na mutu?" Ya fada yana hugging dinta, shi kanshi mamaki yake ya kasa tsaida kansa daga faruwar hakan, "How can I not trust my wife? Na maki alkawari daga yanzu I will always be by your side, kuma bazan sake bari a hada mu ba." Ta yi murmushi ita tama kasa magana mamaki kawai yake bata yadda Sultan ya chanza gaba daya kamar bashi ba, "Tashi ki shiga bathroom kije kiyi wanka, zan dauko maki duk abinda kike bata a dakinki, and forget about cooking na mana breakfast..." ba zato ba tsammani kawai sai jin hannunsa tayi ya daga ta cak har suka sauka kasa, tsaye tayi kamar an dasata ita gaba daya ji yake jiyoyin jikinta basu aiki tayi tsaye kamar wata dogari sai kawai ta tsaya tana kallonshi, "Hoodah kafin nayi counting 3 ki tafi ki wuce bathroom kiyi wankan nan, 1,2..." bai ida rufe baki ba ta zunduma da gudu bata tsaya ko ina ba sai bathroom dinsa, saida tasa key ta rufe ta tsaya tana maida numfashi, amma meyakon ta fara wankan sai kawai ta durkusa ta rizgi kukanta a nan bata taba tunani ba ko a mafarki Sultan zai zama caring haka ba, ashe dama haka yake bata sani ba? Abinda ya mata yau ya ta6a mata zuciya. Tana shiga shi kuma ya gama gyara dakin tsab baka taba cewa namiji ne ya gyara shi haka tas, yana gamawa ya sa kaya sai ya wuce dakinta ya dauko mata duk abinda yayi tunanin zata bukata da kayan da zata sanya. Koda Hoodah ta fito ta gama shirinta tsab bata ganshi ba, tana fitowa ta ganshi yana jera plates bisa dining yana ganinta ya saki murmushi itama ta mayar masa, hannunta yazo yaja ya zaunar da ita ya shiga serving dinta abinda ya girka masu wato doya da minced meat sauce sai hot coffee, ba karamin enjoying abincin nan tayi ba, ya mata dadi sosai, suna gamawa ta sauko hijab dinta yaja hannunta suka tafi gaida  su Abbi. Bata taba tsintar kanta cikin farin ciki ba irin yau ba, he's a blessing to her.

Throughout ranar yau data yi spending da Sultan he's the sweetest man ever, riritata yake kamar kwai, dan wani lokaci saidai ta tsaya tayita kallonshi har sai ya mata snapping hannu sannan ta daina kallon nashi, idan ya tambayeta kallon me take mashi saidai tayi dariya tace "So nake na tabbatar idan da kai nake zaune anya Sultan kaine kuwa?" Bai iya yace mata komai saidai yayi dariya don shima kansa mamaki yakeyi. Tun daga ranar suke zaune lafiya kalau cikin kulawa da juna saidai fa ba wanda ya fahimci me zuciyoyinsu ke ciki. Shi da mai martaba gaba daya babu abinda sukeyi sai bincike sosai don gano waye ke haddasa masu fitina a tsakaninsu waye ke masu wadannan abubuwan.

******

An shude watanni, cikin watannin nan Ashraf yanata healing a hankali duk da dai ba gaba daya ba amma ya ragu sosai all thanks to Yasir, saidai fa ko fita baya yi sai Yasir yayi da gaske kafin ya fita. 

Yana kwance cikin dakinsa kullum saidai kawai yaje ya gaida Hajiya mahafiiyar Yasir da safe shikenan, kannen Yasir kuwa su biyu suke kawo masa abinci kulllum, suna matukar tausaya masa gidan gaba daya dan haka suna kokarin ganin sun tsamo shi daga dilemma da ya afka ciki, ya danyi adjusting to environment din, wani lokaci haka zai kura ma bango ido abubuwa da yawa suna rushing back cikin kwalwarsa yana tunanin abubuwa da yawa da suka faru a baya, baya tunanin zaya gushe daga cikin ransa har abada har bayan ransa, wani lokaci haka zaka tsince shi yanata murmushi ko kuma yana goge hawaye, yasan dai tunda ya rasa Hoodah toh bazai taba samun wata rayuwar da yayi ta farin ciki a baya ba, saidai kunci da bakin ciki, a hankali yaji knocking kafin ma yayi magana yaji an murda kofar an shigo a hankali, Zarah ce tsaye bakin kofa rike da tray din abinci, stool ta jawo ta aje mashi kusa dashi, sannan ta tsugunna tana kallonshi cike da tausayawa "Yaya Ashraf barka da dare? Ga abincinka nan inji Hajiyah tace don Allah ka daure kaci abinda kake so ne tayi maka da kanta, don Allah kaci tace na dawo anjima na kwashe na kai mata taga ko kaci..." tunda ta fara magana yake kallonta bai ce uffan ba ya kai akalla second kamar ashirin sannan ya kalleta "Nagode Zarah." Yayi murmushi har cikin ransa, "Basai kayi godiya ba yaya Ashraf, ka riga ka zama dan gida yanzu." Ta fada tana murmushi, ta kuma ce masa "Try and be strong duk da is not going to be easy, nasan da ciwo kuma duk naji labari daga gurin yaya Yasir yadda kuke da Hoodah da duk abubuwan da suka faru abu baiyi ba dadi ba, amma kasani kowa da tasa kaddarar wannan itace taku kaddarar yaya Ashraf..." shiru yayi na yan dakikai "It's not going to be easy amma kasani kaifa namiji ne, ita kanta Hoodah baza taso ta ga yayanta cikin wannan halin ba, wata kila ita ta dauki kaddara ta cigaba da rayuwarta, kai me zai hana ka yin hakan?" Wani kwalla ya goge "I will be fine, it will surely take time, but gradually ko?" Tasaki murmushi "Yes sure, kadai ci abincin nan please ko in zuba maka?" Ya girgiza kai "A'a Zarah karki damu, thank you." Ta mike tana murmushi "You are welcome kaci fa zan dawo na duba." Yayi murmushin shima "Zanci." Daga haka ta sa kai ta fita daga dakin. 

Yasir ya shigo parlon Hajiya tana zaune kan kujera ya zauna kasa kusa da ita "Ina wuni Hajiya?" Tace "Lafiya lau Yasir." Yace "Gani Hajiya naji ance kina nemana?" Tace "Eh hakane, abinda yasa na kiraka shine inason muyi shawara da kai." Yace "Toh Hajiya." Ta gyara zama "Wannan yaro Ashraf wato abokinka dinnan, a gaskiya ina matukar jin tausayinsa, kuma ni gani nake wannan zaman kadaicin da yake yana kara contributing to kara damuwa a gareshi, sheyasa na zauna nayi tunani naga me zai hana mu hada shi aure da Zarah?" Yasir yayi murmushi "Hakika Hajiya ba ke kadai ba nima abin ya dameni sosai da sosai, nayi iya yina na ganin na tsamo shi daga cikin wannan halin da yake ciki amma abun yaci tura, gaskiya naji dadin shawarar nan taki Hajiya, kuma bana tunanin za'a samu matsala daga ko wane bangare, Allah ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi, hakan ma karamin rage masa damuwa zaiyi ba." Tace "Sosai ma dan haka kaje kayi shawara dashi." Yace "InshaAllah zanyi." Tace "Shikenan tashi kaje." Daga haka ya mike ya shige ciki.

*********

2 days later....

A gigice ya bude idanu, ba inda jikinshi baya kadawa zufa kuwa gaba daya ta wanke masa jiki, ya saba mummunan mafarkai amma na yau yasha bam bam, bazai iya cewa ya kalar mafarkin yake ba amma dai ya tsorata matuka, Hoodah ta bude idanu itama a tsorace ta kunna bed side lamp tace "Sultan lafiya? Meyafaru? Ko mafarki ka sakeyi marar kyau?" Ta tambaya tana dan taba fuskarsa data jike jagab da zufa, duba time Hoodah tayi taga karfe biyun dare, addu'a ya shiga jerawa jikinshi na cigaba da kadawa Hoodah na tayasa addu'ar duk da tazo bakinta. itama zuwa yanzu ta fara tsorata, "Sultan menene?" Ta sake tambaya a tsorace, saida ya dan dawo daidai ya furta yana maida numfashi "Wani mummunan mafarki nayi marar kyau." Tace "Wane iri?" Yace "I can't say, bansan ya zan fassara sa ba," ta dora kanta bisa kirjinsa "It's okay InshaAllah, everything will be ok." Yayi mata murmushi, nan ta tashi taje ta debo masa ruwa ta kawo masa ya fara sha, yana cikin sha dinne sukaji kururuwar mutane da hayaniya, da sauri Hoodah ta kalleshi jin ana jijjiga kofarsu kamar za'a ballata, Hoodah batasan lokacin data bude ba, dogawara sun kai bakwai tsaitsaye sai zufa ke keto masu, "Ranki yadade, Sarki da Sarauniya...!" Cup din Sultan ya saki take ya tarwatse kasa, Hoodah ta juyo sai yanzu ma kwalwarta tayi registering abinda suka fada masu, kallo daya tayi masa ta lura kamar hankali baya jikinsa, "Meyafaru dasu?" Ta tambayesu, "Sai dai kuzo ku gane ma idonku." Suna fadan haka suka juya da sauri suka bar wurin, a hankali ta taka kusa da shi wani irin bala'in shock ne kwance kan fuskarshi, kofar ya kura ma ido bako kyaftawa gaba daya kwalwarsa ta chunkushe, Hoodah itama kanta batasan yadda zata misalta abinda takeji ba, glass din da ya tarwatse kasa Hoodah ta tattara gudun kar a ji ciwo don dukkansu bamai takalmi a kafa, dispenser taje ta debo masa ruwa ta sa masa a baki gaba daya ya zuke ruwan nan kafin ya saki wata ajiyar zuciya, sulalewa yayi kasa gani yake kamar abinda suka fada mashi karya ne gani yane wasa ake masa, dan marin kansa yayi yaji ko shin har yanzu mafarki yakeyi bai farka ba? Hoodah itama sulalewa tayi bisa gwiwoyinta kusa dashi ta kura mashi ido, tunda ya sulale a gurin da kyar ko numfashin kirki bai iya yi, sai da yaji muryar Hoodah tana fadin "Sultan kazo mu tafi..." ta fada tana dragging dinshi wai ya tashi, sai yanzu Sultan ya dawo hayyacinsa tunani yake meyafaru? Meyafaru da iyayensa? Mutuwa sukayi? How? When? Where? Ya za'ayi su tafi su barshi a take? Shin basu san rayuwarshi is incomplete bane without his parents? The people he love beyond everything and everyone, they're his entire life, saukar hawaye daidai kumatunsa yayi daidai da furtawarsa "I need to go and see... nasan ko me nake tunanin ya faru dasu ba haka bane, they're ok, they can't do this to me ko Hoodah?" Take yaji wani tausayin kanshi ya dirar masa, wani gunjin kuka ya saki wanda ya razana Hoodah itama take ta fashe da kuka, sun kai minti hudu a haka kafin Hoodah tayi karfin halin mikewa tsaye kamar yar maye tana tangadi, cikin karfin hali ta soma jan hannun Sultan "Tashi muje Sultan, let's go and see for ourselves." Gyada kansa yayi ya mike tsaye da kyar kafin ta kamo hannunsa suka fita daga gidan. Tun daga wajen sashen zuciyarsu na wani irin harbawa ba kamar Sultan da yake jin kamar zata huda kirjinsa ta fito, hannunsu rike cikin na juna suka kutsa kai ciki, wani irin sakin hannun Hoodah yayi ya karasa cikin parlon da sauri hawayenshi suka tsaya cak, Abbi da Ummi suka gani kwance kasa tsakiyar parlor dogarawa sun zagaye su da wasu wanda baya gane ko su waye, steps uku ya kara baya baya ganin jini na fita ta goshinsu da cikinsu, Hoodah na karasowa kusada su a gigice ta rufe bakinta da hannuwanta biyu, wata irin kara ta saki ta zube nan jikinta na kyarma....!

Tuesday, 15 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 15

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 15}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Haka ta kwanta tana ta faman tunanin little Affan, yayi karami ace yana experiencing wannan abubuwan, subhnallah kuma mahaifinsa wanda shi ya cancanta ya zamana yana gefensa yana share masa hawaye wannan wane irin uba ne? Anya shine ma ya haife shi kuwa? Abinda matar nan ta fada mata gakiya ne ko kuwa? Kodai wani 6oyayyen al'amari ne tattare da abin? Indai har gaskiya ne bai dace ma ace ya ta6a haihuwa ba, astagfirullah ita wacece da zatayi judging abinda Allah ya hukunta? Da kyar bacci 6arawo ya sace ta.  Washe gari ta kai kimanin minti 30 tana wanka, gaba daya ta rasa mafita ta rasa meye abinda ya kamata tayi, tana son ta taimaka mata amma wani bangare na zuciyarta baya so. Kamar kullum sai ta fada ma Sultan zataje yawan shakatawa, har fa fita sai ya kirata "Wai bakya gajiya da zuwa wurin nan ne? Kullum sai kinje?" Dariya ta kakalo "I promise wannan ne zuwan da zanyi na karshe zan dauki time banje ba..." yace "It's fine, but do you need someone to take you?" Tace "No, I will be ok thank you." Gyada mata kai yayi "Alright be safe..." daga haka tasa kai ta fita zuciyarta na harbawa, inda suka saba haduwa yau ma a nan ta iske matar na zaune tana zaman jiran Hoodah ta karaso, idanunta jawur alamun taci kuka murmushi ta kakalo ganin Hoodah, sallama Hoodah tayi mata ta amsa "Ya jikin Affan? Wurin wa kika barshi?" Tace "He's better Alhamdulillah, na barshi da nannynshi." Hoodah tace "zamu iya tafiya? Amma gaskiya bazan shiga hotel ba, sai dai ki masa magana ya fito waje..." matar tayi yak'e ta tashi suka fito parking lot, mota suka shiga ta jasu, tafe suke babu wanda ya tanka cikin motar amma ji take kamar abinda take ba daidai bane, tana ji kamar bata kyauta ba, gani take wannan shine worst mistake da zata aikata,  parking sukayi gaban makekiyar hotel din matar tace "Muje?" Hoodah tayi shiru gabanta na faduwa, "Muje ina? I thought I said am meeting him outside? No kije ki kirashi I can't go inside..." matar ta numfasa sai ga hawaye shar shar tace cikin shesheka "Taya xan fara ce masa ya fito? Bakisan halin Aliyu bane wallahi bazai fito ba, amma indai har kina ganin kamar cutar dake xanyi kawai mu hakura mu koma, am seriously telling you and ke da kanki kikayi niyyar taimaka man I want my baby to survive..." Hoodah tayi shiru gabanta na harbawa tana sauraren sheshekar matar "Don Allah ki daina kuka, bawai ban yarda dake ban, kawai dai zuciyata ce bata amince man da in shiga ciki ba I don't know why!" Matar sai ta kifa kanta a steering wheel ta dinga sheshekar kuka "Babu komai, a haka ma nagode da niyyar taimaka man da kikayi, I don't mean to make you feel uncomfortable, bari naje na gwada kiran nasa nagani... amma alfarma daya xakiyi mun, muje bakin receptionist sai na masa magana a nan ya sauko..." tace toh ta fito daga motar suka cigaba da tafiya a natse duk Hoodah is uncomfortable sai kalle kalle take, can tace "Kar kice na cika complain amma gani nake kamar ana kallonmu..." matar ta juyo ta dafata "Toh ko dai ki tsaya a waje? Idan baki iya shiga." Hoodah tayi smiling back "A'a it's fine muje kawai." Nan ta shiga ciki ta bar Hoodah tsaye. Tun Hoodah nasa rai zata fito har ta fara gajiya da jira, toh dama akwai steps a wurin sauka nan tana cikin tafiya kawai sai tayi taga taga zata fadi, wani dake gefenta yayi saurin tarota.....

Shi kuma a bangaren Sultan tunda Hoodah ta bar gida ya kasa samun nutsuwa, a hankali ya fito ya dinga binsu ga mamakinsa sai yaga sun tsaya a hotel, nan ya fara tunanin meya kawo Hoodah hotel wacece wanann da suka zo tare? Kawai yana fitowa daga mota sai ga Khairy kamar an korota, "Sultan!" Cak ya tsaya ya juyo yana ganin Khairy yace "Khairy me kikayi a nan?" Ta matso daf dashi "Mama ce ta aikeni nan kawai ina fitowa sai naga matarka da wata mata sun shiga cikin hotel, toh a hankali na dinga binta ina zuwa sai naga asha da wani ne suka hadu..." yace "Mey? Me kikace? Yoh must be joking." Tace "I am sorry Sultan but that's the truth, believe it or not gaskiya matarka tana bin maza... karka ce kishi nake ko wani abun, ni da idona na ganta..." ya runtse idonsa gam gam yana girgiza kai "No! Karya kike Khairy kishi ke damunki amma Hoodah bata bin maza..." Khairy tace "Oh really, why don't you go inside and see it for yourself!" Kasa tsayuwa yayi nan yaji kamar zai fadi, rigarshi Khairy ta damko ta dinga jansa kamar wani gunki haka suka shiga cikin reception din, yana fara hawa steps daidai lokacin da Hoodah ta kusa faduwa wani ya tarota, tsayawa yayi yana kallonta take ya fara wani girgiza kai ya fasa kara "Hoodah!!!!" Yayi gigitaccen kara kamar wani zaki, ita kuma lokacin ta kusan fadowa tana kokarin rike stairs kar ta fada masa amma ina ta kasa controlling hakan, wata irin zabura tayi ta jiyo a gigice, kafin ta ankare sai ganin Sultan tayi ya nufo ta gadan gadan wane kura ta ga nama, wata irin damka ya kai ma kugunta ya dinga janta suka fita hotel din don mutane nata kallonsu, cikin motarsa ta tullata har sai da kanta ya bige da karfen motar ta rike kan hawaye na taruwa cikin idonta, gefe ya shigo ya kunna motar ya tada ta da karfin balai yaja su wane zai kifar dasu, "Na yarda da maganar da ake fada a kanki yau na tabbatar!" Muryarta na rawa tace "Me kake nufi?" Ko amsata baiyi ba ya kara wutar motar kamar zaiyi accident, a tsorace take kallon shi jikinta babu inda baya rawa, yana isa gida ya finciko ta ko tsayawa baiyi ba sauraron kowa ya nufi sashensu, yana zuwa ya wullata kasa yasa ma kofar key, "Sultan wai lafiyanka?" Ta fada tana kokarin mikewa tsaye tuni hawaye sun wanke mata idanu, finciko hannunta yayi ya matse gam gam yana kallon cikin idanunta "Tambayata ma kikeyi?" Ya fada kamar zai fasa mata dodon kunne Hoodah tace itama a tsawace "Dole na tambayeka! Naga alamar kamar kwalwarka ta samu matsala!" Kara matse karfin rikon da yayi ma hannunta yayi "Naganki dawani kato a cikin hotel sannan kizo kina tambayata meye faru da kwalwata?" Hannu tasa tana kokarin cire rikon da yayi mata cikin kuka tace "This is the second time Sultan zargina kake? Baka yi trusting dina ba? Sultan what the hell is wrong with you? Subhnallah don kawai kaganni da wani bai ci ace ka zargeni da aikata abinda ba daidai ba, trust me da wata naje taje ciki ta dawo kawai nazo faduwa...." daga mata hannu yayi "Bana son jin komai daga bakinki Hoodah! Akace maki ni wawa ne bansan me nakeyi ba?" Hoodah tace "Oh haba? Now I get it! Dama dai kiris kake jira ka fara mun abinda ba daidai ba! In banda haka meyasa bazaka tsaya kayi bincike ba? Ka gano idan na aikata hakan?" Idanunshi jajir jijiyoyinsa a waje yace "Ni mamakin da kike bani sai wani cewa kike bakiyi komai ba, bayan sau biyu ina kama ki dumu dumu amma still you're denying the fact!" Hannu tasa take karfi yazo mata ta fincike masa hannu daga jikinta tace "Toh bari kaji Sultan! Nagaji! You know what? I don't care anymore am tired of all this!" Ta fada tana nufar hanyar dakinta "And where do you think you are going?!" Saida ta kai dakinta ta juyo tace "My room, kuma babu abinda ka isa kayi!" Tana fadan haka ta shige daki nan yaji anata knocking "Sultan ka bude mana kofar nan!" Da sauri yaje ya bude nan sarki suka tsaya suna kallonsa "Lafiya? Me kuma ya faru? Ina Hoodar?" Ummi ta fada tana sa kai ciki, knocking dakin Hoodah tayi ta kai minti biyu sannan tazo ta bude, Hoodah na ganin Ummi kawai taje ta rungumeta gam ta saki kuka mai ban tausayi "Ummi I think someone else is setting me up! Inaga akwai wanda baya son zamana cikin gidannan ..." Ummi ta dago ta tana share mata hawaye "Meya faru?" Ta fada tana kamo hannunta ta zaunar kan kujera mai martaba ma ya shigo ya zauna shima yace "Meya hadaku fada tun farko?" Sultan yace "A hotel na kamata dawani kato..." daga masa hannu yayi "Ba kai na tambaya ba yata na tambaya ita nakeso tayi man bayani dalla dalla..." kwafa yayi ya fice daga gidan wane zai tashi sama, share hawayenta tayi ta dago daga kan cinyar Ummi sannan ta basu labari daga farko har karshe, mai martaba ya numfasa "Tabbas wannan set up ne daga ji ma, amma kema Hoodah kinyi ganganci meyasa kika bita kuma meya hana ki fada ma Sultan gaskiya tun farko?" Tace "Wallahi nima bansani ba! Kawai na tsinci kaina da son taimaka mata shine fa, amma bayan nan babu wani abu wallahi." Ummi tace "Toh wai wacece wannan da take son hanaku zaman lafiya? Sau biyu fa kenan! Amma karki damu zamu gano ko waye kuma wallahi idan na gano I won't spare her! Share hawayenki inshaAllah Allah zai bayyana mana gaskiya." Ta share hawayenta sai yanzu ta soma fahimtar komai dalla dalla. 

Bayan mai martaba sun fita nan Hoodah ta dinga safa da marwa a dakinta tana tunani "Waye wannan yake nemana da sharri? Meye hadina da shi? Me na masu? Waye?" Nan ta dinga tafiya tana tunani zama tayi gefen gado "Tunda yanzu na fahimci komai, I won't rest sai na gano ko waye wanann yake tarnishing image dina yake kuma hadani da Sultan, mark my word sai na gano ko ke wacece no matter what it takes I won't spare you!"

Tana nan zaune a haka har aka kira sallar magrib jiki a sa6ule ta tashi ta shiga bathroom ta watsa ruwa hade da alwala tana fitowa ta saka loose gown. Can bayan isha'i taji shigowar Sultan garam haka aka buga kofar dakin aka shige kamar zata balle, a hankali ta fara tunanin yadda rayuwarsu ta sauya cikin kankanin lokaci da irin kulawar da suka ba junansu amma yanzu lokaci daya ansamu wata shegiya ta tarwatsa masu farin ciki, tafi minti talatin sannan ta mike a sanyaye ta nufi dakin nasa, jikinta babu inda baya rawa, tana shiga ta tsaya kofar dakinsa tana kalle ganin babu kowa, nan tayi tsaye lost in her thoughts kamar daga sama taji takun tafiyarsa kusa da ita, wani irin mugun firgita tayi da tilas tari ya sarketa, bai ce komai ya juya ya fita ashe ruwa ya debo mata ya mika mata ta sha da sauri amma fa fuskar nan kamar an aiko mashi da sakon mutuwa, ta kula yayi wanka ya chanza kaya "Meya kawo ki dakina?!" Ya fada cikin daga murya, muryar nan babu taushi ko kadan. Ta dago da rinannun idanunta tana kallonshi, kafin ya ankara sai hawaye ya runtse idanunsa ya zauna kan kujera, ganin haka yasa Hoodah ta zame ta zauna kusa dashi tana tunanin maybe zata samu sassauci, kallonta yake babu ko kyaftawa ita kuwa kuka take tamkar ranta zai fita, kasa ta sauko don tayi alkawarin bazata taba barin gurin ba sai ya daina fushin nan da yakeyi, tayi missing kulawar da yake bata kwana biyu da suka wuce, ya dandana mata zuma mai saurin kama zuciya. Dan kwanciya tayi bisa cinyarsa ta lumshe idanu "Sultan ya kamata ka fahimceni kai kasan wannan ba halina bane is a set up don a rabamu, nasan bamu zaman lafiya bama son junanmu da farko, amma wallahi ban taba aikata abinda kake tunani ba please..." tausayi ta bashi matuka kamar ya durkusa ya rungume ta amma ego bazai barshi ba "Tashi ki fitan man daga daki!" Rufe idanunsa yayi da san ya manta abubuwan da suka faru 2days ago, it's a beautiful moment a happy one, "No bazan tafi ba har sai kace kayi trusting dina, sannan sai kayi hakuri nasan nima inada laifi da na tafi ban fada maka ba, kayi hakuri wallahi ba laifina bane matukar tausayina ne yaja mun amma nayi learning lesson, I was just trying to help her she told me to talk to her husband, yaronta yanada cancer batasamun kulawa daga garesa, I even offer to help her nace ta fada mun nawa ne kudin aikin yaronta tace indai inaso na taimaka kuma nayi niyya sai dai nayi magana da mijinta da ke zaune a hotel, kayi hakuri don Allah, nidai kawai so nake kace kayi trusting dina that's all that matters to me, ko da zaka dakeni ko kace ka tsaneni as long as zaka yi trusting dina I don't care, please Sultan don Allah..." ganin ko kallonta baiyi ba yasa ta zagayo da hannayenta duka biyun a waist dinsa ta makalkale wani irin shock sukaji su duka, juyowa yayi ya kalleta kafin yabi hannunta da kallo dake zagaye dashi!" Shiru yayi kafin yace "I hate you! Nace ki tashi ki fitar man daga daki! Abinci ma karki sake bani zan dinga fita inaci! And lastly koda wasa karki kara taba jikina!" Ya fada yana ture hannunta daga jikinshi ko second daya bai kara a dakin ba ya tashi ya fita ya buga kofar da karfin bala'i. Wani abu Hoodah taji kamar madaci ya tsaya mata a makoshi, sai yanzu ta tabbatar da duk kukan da take a baya ba kuka bane takaicin data kunsa dazu ba komai bane ba compared to na yanzu, duk wata kafa dake zuciyarta saida ta toshe sannan ya bude mata kofofin bakin ciki da damuwa mai tarin yawa. Kuka ta saki mai cin rai a nan, nan ta kwanta a kasa tayita kuka kamar ranta zai fita, tun tanayin kukan har bacci ya fara fizgarta, sannu a hankali bacci ya sureta a nan inda take.

Ashe Sultan yana parlor kwance shima a nan bisa kujera bacci yayi awon gaba dashi, can cikin dare fitsari ya ishe shi, ko lura da ita baiyi ba kasa sai da yafito daga bathroom ya hango ta can kamar xata shige cikin kujera ta kudundune da hijab dinta sai faman ajiyar zuciya takeyi, samun kansa yayi da rage mata sanyin ac sannan ya rage mata fitila, karasowa yayi a hankali inda take ya dafata a firgece ta farka "Kayi hakuri kace ka yar...."  sai a yanzu ya lura da kuka takeyi cikin bacci, tana bude idonta ta ganshi kawai sai tayi hugging dinshi ta fashe da wani irin kuka, "Kace kayi trusting Sultan, azzalumai ne suke so su rabamu, zaka nemo su? Ka hukunta su?" Kuka take har can kasan ranta, wani irin tausayinta yaji yana shigarsa, a hankali yayi hugging dinta back yace "Kiyi shiru ki daina kuka kinji? Zan sa a nemo su bazan bari su kara hadamu fada ba ki koma baccinki yi shiru."

Monday, 14 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 14

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 14}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



******

"Malama Khairy lafiya kika kirani tunda sassafe haka?" Ya fada yana son jin dalilin kiran nata, ta numfasa "Naji dadin aikin da kayi man kwanaki but I have another plan, this is going to be my second success, na farko mun aiwatar dashi nayi bincike komai ya tafi yadda na zata! Am really happy about what I heard!" Yayi wata arniyar dariya "Ay ni kinsanni sarai indai da yayan banki babu abinda zai gagara!" Tace "Good! our second full proof plan is going to be a little different amma dai duk tafiyar tasu daya ce!" Yace "Ba matsala kawai ki man bayani me zan aikata maki amma fa kinsanni sarai you have to pay, in ba haka ba bazan amsa aikinki ba..." tace "Karka damu ay zan biyaka! Nidai bukatata ta biya, kagane...." nan ta zayyana masa aikin da takeso yayi mata, ya gyada kai can ya kece da dariya "Babu matsala ko kadan, zan maki amma ki tabbatar kin biya da tsoka don wannan aikin ba irin wancan bane...." tace "Babu matsala."

********

A hankali ya zare jikinshi daga nata yaje yayi sallah yana dawowa ya isketa yadda ya barta haka ya dawo ya sameta, yana kwanciya kamar tana jira ta makale shi ta kwanta bisa kirjinsa a haka ya kura mata ido ganin yadda take bacci so innocently kamar idan aka sa mata yatsa bazata ciza ba, haka ya samu kansa da cigaba da kallonta cike da sha'awa baima san yana smiling ba, gashi dan kwalinta ya zame ya cire gashi duk wani ya dawo gaban fuskarta ya dan rufe mata goshi, lips dinta ya kalla ashe haka lips dinta suke da kyau? Gasu wasu light pink sai sukaje da skin color dinta, daga gani bacci take mai nauyi, samun kansa yayi da sa hannu yana cire mata gashin fuskarta a hankali take ya kura ma lashes dinta idanu sunyi zara zara gasu masu cika wasu bakiirin dasu, gashinta yake shafawa wani irin santsi yaji da taushi marar misali, a hankali ya fara ta6a bayanta yana bubbugawa, bude idanunta tayi a hankali sai ta sauke su bisa fuskar Sultan, ta saki wani kayattacen murmushi ta danyi mika kadan "Good morning." Har yanzu bata daina murmushi ba, babu wanda ya dauka nan da minti biyar Hoodah zata iya yin fada amma dai let's wait and see no one trust her. "Morning to you too, yunwa..." sai kawai ya tsinci kansa da mata magana haka cikin kwanciyar hankali, dan tashi tayi zaune take Sultan ya fara kallonta da wata kayatacciyar night gown mai matukar kyau shi sai yanzu ma ya lura, kamar an kwance mashi noti haka yakeji, Sultan har dawani alamun shagwaba ita kuma yadda yayi haka sai kawai taga ya mata kyau, yau gaba daya sai taji yau ta tashi bata jin haushin shi, "Toh yanzu meye abinyi? Nidai kasan banida lafiya ko ya jiki ma bakace man ba..." ta fada cike da shagwa6a ba karamin burge Sultan tayi ba, "Am so sorry ya kike? Hope you slept well in my room? Ya ciwon cikin ya daina?" Idanunsu a makale cikin na juna yake mata maganar nan gaba dayansu yau mamakin kansu sukeyi, "Alhamdulillah, dasauki and yes I slept like a queen in your room thank you.. well Abincinka ko muje muyi tare?" Murmurshi Sultan yayi ya gyada kai wane karamin yaro a haka ya mike ita kuma ta tafi dakinta don yin wanka shima bathroom dinshi ya shiga don yin wanka. Haka tayi wanka har ta gama bata bar murmushi ba tana gama sa kaya taji ana knocking a hankali, kafin ma tayi magana har an shigo tana kokarin sanya sarka, galala yayi bakin kofa yana kallonta tana sanye da wata gown red color dinkin material mai taushi red and brown ne color dinta, karasowa yayi ta gaban mirror yana kallonta ta ciki, face dinta ba makeup dama ita ba makeup takeyi ba iyakarta da makeup powder da kawalli idan an kure lipstick shima bata sawa da yawa kadan kadan take shafawa, idanunta ya kalla ta mirror farare kal dasu gashi sunsha kwalli dama gasu dara dara  manya dasu MashaAllah, "Should I help ma'am?" Ya tambaya yana kallon sarkar tata golden color da ganinta kasan ta gold ce marar hayaniya, fuskarshi dauke da murmushi, dukkansu sunsan cewar abinnan da suke da kyar zai kai daren yau amma kawai duk sun tsinci kansu haka yau, a hankali ya kama sarkar dake hannunta bisa neck dinta ta lumshe idanu yana kallon fuskarta yasa mata a hankali yana jin wani bakon al'amari cikin zuciyarsa, "You look stunning." Ya furta a lokacin ne ita kuma ta bude idanunta ta taji wani yanayi na daban, wani tari ne ya dan sarke ta tayi saurin fita daga dakin "Muje rana tanayi..." yana shiga cikin Kitchen to make it less boring sai Hoodah tace "Ka taba girki kuwa? Sultan karfa muzo ka kona mana abinci.." dariya tayi ya tayata. "Wai ke bakyajin dan kunyar fadin sunana? Ko Yaushe Sultan wannan Sultan wancan..." dariya ta kyalkyale dashi "Toh idan ban kira sunanka ba Sultan sunan wa zan kira? Wa nake gani a cikin gidannan kullum in ba kai ba? Ni sunan ne ma yake burgeni gashi sunan yayi kama da sunan sarauta ne wai sultan, gashi na yan gayu, sunan ajebo kuma dan mamanshi, sunan fa ya dace da kai..." tahowa yayi gadan gadan zai damkota ta fita da gudu dan tasan babu abinda ya tsana ace mashi ajebo.. ta bayan kitchen ta nufa ashe suna da wani babban lambu bata taba sani ba nan ta tsaya galala tana kallon wurin cike da sha'awa, fruits dai ba irin wanda babu ga wurin gwanin kyau MashaAllah..." tana jin tafiyarshi ya karaso tace "Sultan dama kunada lambu a nan bansani ba? Gaskiya wurin yayi bala'in kyau kasan me za'ayi mu manta da wani breakfast kaga mango din can da basu nuna ba zamu sha... katso mana guda biyu ya isa kaga manya ne sosai." Baki bude yake kallonta "Hoodah ta ina kika ta6a ganin anyi breakfast da danyan mango? Ga wadanda suka nuna nan birjit sai ki rasa wanda zamu sha sai danye?" Ta kyalkyale da dariya "A'a da dadi fa bakasani ba? Kaidai katso mana kagani." Har wani dukawa tayi wai ita nan tana rokonshi. "Wallahi baki isa ba don bazan hau iccen nan ba, saidai na kira maki gardener yazo ya katso miki..." Wani shiru tayi tana kallonshi can yace "Umar wai mangwaro take so guda biyu danyu ka katso mana idan ka katsa ka sameni backyard kitchen," yana gama fadan haka yaja hannunta suka koma ciki, a hankali ya saki hannunta babu wanda yace komai acikinsu har Umar ya kawo masu mangoes luka luka guda biyu "Yanzu kazo ka tayani mu yanka su duk abinda kaga nayi haka zakayi, kabi a hankali fa kar kaje ka yanke hannu kaja na amsa query wurin Ummi." Dan harararta yayi kafin ya wanke mangoes din sannan suka yanka shi kanana. "Bari nazo." Tafada tana nufar cabinet, wani bowl taje ta dauko mai kyau fari kal, tana kawowa ta koma fridge ta dauko kwalin milk tasan idan Sultan yaci abinnan sai yayi karamin hauka, shi dai kallonta yakeyi ta gama kwad'on mangoes dinnan ta tuttula masu madara cikin glass cup, ta dauko ma kowa spoon daya daya sannan ta debo tayi loma daya nan da nan ta lumshe idanu tana hmmm hmmm kamar wacca take cin shawarma ko kuma pizza "Kasan Allah Sultan ka dandana kaji dadi kuwa? Just give it a try....Wallahi dadi sosai." Yayi kuri yana kallonta baki bude ganin yadda take ci kamar ta samu nama, da kyar ya dauko spoon ya debo shima ya kai baki, ji yayi tsami, maggi, albasa, yaji kai komai ma, runtse ido yayi yana taunawa da kyar har ya samu ya hade, aje spoon din yayi yana girgiza kai, danne dariyarta tayi ta kara dauko spoon ta tura mashi a baki haka nan ya daure ya dinga ci gudun kar ya bata mata rai suyi fada. Idan yaji azabar yajin yayi masa yawa sai yasha madara, ruwa taje ta dauko masu tana dawowa ta lura da yanayinshi "Ya salam Sultan yaji kakeji?" Ta tambaya innocently tare da dora hannu bisa kafadarshi cike da damuwa, daga kai yayi yama kasa magana, zuba mashi madara tayi a cup ta mika masa yasha amma a banza "Ko na dauko maka yoghurt? Maybe zai daina..." Girgiza mata kai yayi, ta kara cewa "Toh me kakeso?" Ya dinga nuna ta da hannu "Nikuma? Me zan maka ko wani abin zan dauko maka?" Kafin ta kare maganar ya hade lips dinsu wuri daya take ya fara kissing dinta itama kamar tana tsoronshi ta fara responding, sai can ta farga take jikinta ya fara rawa ta fara kacaniyar kwace kanta ina ya mata wata irin damka ta kasa ture shi, take ta tuna da irin zaman da sukeyi tasan Sultan tsab xai iya juyewa ya rikice ya koma mugu ba karamin aikinsa bane, da kyar ta kwace kanta sai ta tsinci kanta da sa kanta bisa kafadarsa ta fashe da wani irin kuka, bai hanata kukan ba sai ma hugging dinta da yayi yana rarrashinta, sai can tayi shiru dan kanta kafin ya zare jikinshi ya fita daga gidan. 

********

      2 days later

A kwana biyun da suka gabata ya kasance Hoodah na yawan fita yawan shakatawa da yamma, a hankali sai ta fara enjoying kanta takanje park ta zauna a gurin tana ta kallon yara suna wasansu, a hankali sai ta dinga lura da wata mata sai ta rakube gefe tayi shiru, an kwana biyu ana haka ita dai Hoodah tace bari taje ta sameta taji ko lafiya? dan ta6ata Hoodah tayi hawayen da take rikewa suka gangaro mata tayi sauri ta goge, Hoodah tace "Can I sit please?" Matar ta gyada mata kai tana cigaba da share hawayenta a hankali, Hoodah ta zauna "Thank you, karki ce na maki shishigi amma na lura a yan kwanakin nan kullum nazo sai na ganki a same position, same spot, always crying, nasan ba hurumina bane but please can you tell me what's bothering you?" Matar tayi shiru na yan dakikai can tace "Ni matar aure ce na kasance ina da yaro dan shekara biyar, and that boy yanada matsalan zuciya my husband doesn't have my time he's always busy, gashi Affan ya saba da baban nan nasa toh yanzu sai ya zama baya bashi enough time, ko dawowa yayi gida baya kula shi baya ko kalllonsa...." ta karasa muryarta na rawa "Nayi iya kokarina na ganin na jawo hankalinsa especially for my sick baby, amma abu yaci tura shine boss kuma shi ya ke kula da gida gashi sisinsa bana ci baya bani, so ba lallai bane ko nayi complain ya saurareni...." Hoodah ta numfasa "Baki taba samun aiki ba? Ko bakida ra'ayi?" Ta share hawaye "Na samu aiki mai kyau amma ba'a  dade ba kwarai aka koreni daga aiki..." Hoodah ta numfasa tana matukar jin tausayin matar yana ratsa ruhinta "Yanzu haka sai an masa aiki wanda muna bukatar kudi masu yawa banida halin da zan biya amma wallahi kinji rantsuwar musulmi ko? Toh Aliyu yana da kudin aikin nan, kawai dai bazai bayar ba." Hoodah cikin jin tausayin matar tace "Wannan wane irin uba ne haka? Nawa ne kudin aikin yanzu?" Matar tace "Ki yarda danii bazaki so jin kudin ba don gaskiya sunada yawa." Hoodah tace "No karki damu, zan iya taimaka maki inada halin da zan taimaka..." matar tace "Nasani ke matar dan sarkin garinnan ce, amma wannan ba huruminki bane it's not your place to help me..." Hoodah tace "Nace karki damu meye amfanina toh in bazan iya taimaka maki ba? Trust me zan taimaka maki just tell me the amount." Matar tace "Naji amma ki man alfarma daya kafin nan." Hoodah tace "Ok Menene?" Matar tace "Inaso ki taimaka man ki magana da mijina?" Dan zabura tayi tace "Na'am? Me kikace? Meyasa?" Matar tace "Bai cika zama gari ba, hotel ya cika zama meyakon gidanmu..." wani irin kuka matar ta fashe dashi "Don Allah ki cece baby na, indai kinyi niyyar taimaka man wannan nakeso kiyi man, don Allah ki taimakeni zan iya rasa dana..." Shiru Hoodah tayi tana kallonta na rashin sanin abin cewa....

Daga can nesa bakin wata bishiya wata mata ce cikin niqab kawai daga niqab din tayi tana murmushi tana juya wayarta, "Kawai kiyi accepting wannan kudirin namu, and surely you will meet your doom, just say yess Hoodah.!"

Sunday, 13 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 13

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 13}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Wani irin mugun tsaki yaja har saida ya kada ma Hoodah yan hanji, "Wallahi tallahi in baki daina mani wannan kukan munafuncin ba sai na lahira yafiki jin dadi, in banda munafunci kinsan abinda kika aikata amma ki kasa bada hakuri and accept your damn mistake, amma da yake taurin kai ya maki yawa, sannan I don't know wani mistake din ya kawo ki gidana, what do you want from me? Nasan dai ba dukiya ba! Ba kuma sarauta ba! Are you after my life? Do you want to kill me? Talk to me!" Ya fada yana wani irin girgiza ta da karfi fuskarsa jawur wanda hakan ba karamin kidimar da Hoodah yayi ba, bare ma aje ga maganganun da ya fada mata ba karamin girgiza ta sukayi ba, "Ki fada man nace what do you want from me? Ko ance maki bansan halin stepmom dinki ba ko wani asirin tayi man aka kawo ki gidana?" Ko rufe baki baiyi ba hannayenshi dake saman kafadunta suka fado kasa kallonta ya tsaya yi, nan yaga wani irin zallar bacin rai da tsantsar tsanarshi a idanunta, take yaga Hoodar da yasani ta bace bat wata sabuwa ta bayyana with no sign of respect, "Kayi kadan! Ko kadan baka kai matsayin da za'a mallake ka da asiri ba, kai waye kai da za'a aikata shirka a kanka? Kai nan har tunani kake kana da wani matsayi a duniya da za'a soka a bika har a sabawa mahallicinmu? Me kake takama dashi? Mulki? Sarauta? Kudi? I am far more better than that! Abinda kawai yasa nake maka shiru kana taka ni yadda kaga dama shine na farko kai mijina ne ko ba komai ance nayi maka biyayya dukda ba sonka nake ba! Na biyu ina respecting kakata wadda itace ta rokeni akan nazo na zauna dakai kar na sa6a maka! Kai wallahi ba sarauta ba ko ni almajira ce babu wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yafi tsoronsa! Duka duka nawa kake? Who the hell do you think you are? Bana living life donni wata tsiya ce in fact I hate being royal! Yadda kake mutum nima haka nake yadda kake da kafafuwa da hannuwa da baki da ido da kunne nima duk haka neke dasu! Zuciyar da ke bugawa a kirjina daya ce kaima taka ce daya ce tak! Idan ka isa kana kuma tunanin kanada wani matsayi a idon duniya da kuma Allah, don Allah ka chanza halitta ingani ya kasance kai kadai ka fita daban ka fita unique a duniya that is idan har ka isa! Kuma da kake maganar munafunci I am all acting naga dai we are married ko? Kai ko kunya bakaji ba ace kana kiran matarka mazinaciya yaushe ka kamani da idonka inayi? Kai baka mayi tunanin ya akayi ma har aka dauki videon ba? Daga gani kasan shiri ne! Kuma da kake maganar stepmom dina tana bin bokaye da malamai wallahi ta fiye man a kanka sau dubu! Duk wani isarka da mulkinka are nothing compared to her in my life! Indai wannan wahalallen auren ne  agabana da bamu kai haka ba! Ni nan ba zaman ka nake ba zaman kakata nakeyi da Abbana! Kai bari kaji fa wallahi tallahi inda naso tun ranar da aka kawoni cikin gidannan sai nasa ka duka kasan gwiwowinka kana rokona sai nasa ka zama bawana na dinga juya ka son raina! Nima fa inada matsayin da zan dinga juyaka amma banyi ba saboda baka gabana, kallon banza ma baka isheni ba, sannan bari kaji wallahi babu boka babu malam sai na hargitsa duk wani tunaninka saina kwance duk wani notin da ke kanka." Hawayen ma kwata kwata sun daina tsiyaya, bakin cikin data kwasa tun ranar data shigo gidan ta sauke mashi san ranta kafin tayi hanyar bathroom din. "Idan ka gama tsayuwar ka fitan man daga daki ka rufe man kofa... kuma ka aje man wayata bisa gado, kuma idan naga dama sai na fada mata duk abinda kake man kaga idan zaka kwana lafiya gobe da sai na nuna maka matsayina nima!" Tana gama magana ta shige bathroom tasa key, tana shiga ta zube kasan bathroom din ta dinga rizgar kuka bata ma damu dayana cikin dakin ba itadai bakin cikin dake cikin ranta take fiddawa. 

Sultan yafi minti araba'in tsaye inda ta barshi yana jin sautin fitar kukanta, yadda kukan ke fita daga ji na bakin ciki ne da kunci dake cikin zuciyarta. Gaba daya Sultan sai ya rasa meke mashi dadi wani irin guiltiness da dana sani ne ya fara dirar masa cikin ruhinsa, zai iya cewa yafi kowa sanin dadin uwa amma yau ya bude baki ya kira wacce ta dauka a matsayin uwa mai bin bokaye da malamai, meya aikata haka? Jiki a sabule ya fita daga part dinta ga kuma magaganun Ummi wanda take fada mashi rikon maraya yadda yake take wani guiltiness ya sake rufe shi barin garin yayi gaba daya, sai da yayi kusan awa biyu sannan ya dawo cikin garin Niamey, haka yayita yawo yama rasa ina zaije, sai can ya dawo gida. Direct dakin shi ya shiga yayi wanka. 

Ita kuwa Hoodah tafi awa daya cikin bathroom tana shar6ar kuka saida ta gaji dan kanta ta watsa ruwa ta fito, tana fitowa ta chanza kayan bacci ta haye gado, a hankali bacci barawo ya sace ta haka tayi bacci tana sauke ajiyar zuciyar kuka.

********

Da safe Sultan yana tashi sai ya tsinci kansa da son zuwa dakin Hoodah, yau dai yasan ba lallai bane ya samu breakfast amma to his surprise yana fita yaga abinci jere saman dining, gidan sai kyalli yake ko ina fes fes ga wani irin kamshi na musamman na fita daga gidan yaji turaren wuta ga freshener yana tashi, sai yaji ta bashi tausayi, zama yayi kan dining din sai yaji yanaso tayi serving dinsa, gashi ya tuna yace kar ta kara bari su hadu idan yana nan. Yana gama cin abinci ya tashi ya fita daga gidan, rasa inda zaije yayi gaba daya abin duniya ya ishe shi ya dame shi.

********. 1 MONTH LATERAL 

Tun abinnan da ya faru tsakaninsu babu abinda ya chanza masifar yau da daban ta gobe daban abu kadan zaiyi ta hau shi da masifa kamar wata uwarshi, amma duk da haka tana dan shakkarsa, gaba daya dawo wani solo6iyo ya daina ta6uka komai. 

Da daddare ranar wata litinin ne tayi masu indomie mai shegen yaji, haka suka ci abincin nan har tari ya dinga yi na yajin abincin gashi ba damar yayi magana yanzu ta hau shi da fada. Yanzu ya daina hanata kallo kunnawa takeyi ko yana so ko baya so tayi kallonta son ranta, bayan sun gama cin abincin ne ta tatttara ta tafi dakinta ta kwanta. Can da daddare wurin karfe biyu na dare ciwon ciki ya tasheta tun kwana biyu da suka wuce take jin alamun shi, azabar kadan kadan kamar wasa, can kamar a mafarki ta farka tana ta uwar zufa ko ta ina, nan ta fara juye juye tana mirgina, can dai ta mike tsaye ta kwanta ta kife, ta tsugunna kasa, duk abinda zatayi a banza kamar ana karo shi, ganin numfashinta na bazaranar daukewa sai yasa ta rarrafa ta nufi wurin kofar Sultan a galabaice ta isa kofar ta fara bubbugata da karfin bala'i. Shi kuma Sultan dama yajin da yaci ya ishe shi da kyar ya samu bacci ya dauke shi, wannan uban knocking ya tashe shi ya bude kofar da sauri yana budewa sai ya ga Hoodah durkushe kasa dirshen dafe da cikinta, siririn tsaki yaja "Ka lafiya me kike man a kofar daki?" Ya tambaya a hankali ba cikin masifa ba, wata uwar harara ta watsa mashi "Aww tambayata ma kakeyi? To marata ke ciwo... komin banza dai ba wanda zan fadi mawa sai kai ay ko?" Ta fada cike da tsiwa, wani azaba taji ya turnuke ta batasan lokacin data saki kara ba ta cakumo wandon shi ta makalkale mashi kafa dan dole ya durkushe kasa ya rungume ta shi tsoro ma ta bashi, wani tight hug ya bata hakanan yaji yana bukatar wanda zai rungume yama manta shaf ciwon ciki takeyi, wani ciwon ya sake turnike ta ta saki kara tare da sakin wani wahalallan nishi tace "Na shiga uku wayyo Abba zan mutu!" Ta fada wane za'a zare mata rai, a hankali ya zare jikinshi daga nata yana kallon fuskarta yadda ta jike da zufa tsabar azaba ta cije le6e ta dafe cikinta ta rike shi gam gam, "Yanzu me kikeso na maki? Kinga dai am not a doctor Hoodah..." cikin sanyin murya yake maganar yana kallonta ita kam idanunta a rufe suke ita dai burinta baifi ya lafa mata ba. "Ohh wai tambaya ma kakeyi? Kai ka taba jin ance menstrual pain nada magani? Ko don ba jikinka ciwon yake ba, ka wani tsaya kana kallona ko pain reliever ay ka bani ko?" Kallonta yayi baki sake "Oh wai dama menstrual pain ne? I thought ulcer ce due to yajin da kika ci jiya Allah ya baki hakuri uwar masifa, ke bakisan rana ba bare kuma dare..." yana gama fadan haka ya mike ya koma dakinshi ya rufe kofarsa. Kwanciya tayi a nan ta gama juyinta bakin kofa kafin ta bude kofar dakinsa ta shiga, dan tsabar iskanci na Sultan ulcer ce zata sa man ciwon mara? "Amma wallahi kai dan rainin hankali ne, yanzu yaji ne zai sa man ciwon mara? Kuma da kaji ba ciwon ulcer din bane meya hana ka tashi ka bani magani? Kai dama ba tausayi gareka ba kama san meye ciwon mara kuwa? Toh wallahi ko ka nema man maganin rage pain ko kaji sammaci daga wurin Ummi, na lura don kaga ina rufa maka asiri kafi wulakanci..." tana fadin haka ta durkusa kasa rike da ciki yau ita kam ta bani ciwon yau yafi na kullum. Jin an ambaci Ummi yasa Sultan sakin wani dan guntun tsaki kafin ya tashi tsaye, closet dinsa ya nufa ya dauko first aid box, pain killer ya ballo mata guda biyu ya mika mata, "Gashi nan kije kisha kuma ki fitar man daga daki, na lura munafuncinki yana nema ya wuce gona da iri..." ya fadi haka yaga taki karbar maganin, wani tsaki yaja ya koma kan gado ya juya mata baya ya rufe idonsa "Toh wai haka ake shan magani babu ruwa ba komai?! Ko na maka kama da yar kwara da zan banki magani ba ruwa? Wallahi ka kiyayeni Sultan..." saida taji wani d'ar data fadi mashi haka don ita bawai ta daina tsoronshi bane gaba daya. Guntun tsaki ya kara ja shidai burinshi ta bar mashi daki, mikewa yayi a fusace ya fita parlor ya dauko cup ya debo mata ruwa yana dawowa ya wani mika mata shekeke, "Ansa ki karba ki sha dan Allah dan Allah kar ki sake takura man bacci zanyi, out." Ya nuna mata kofa, batayi musu ba ta karba tasha maganin, ga mamakinsa sai yaga tana gama sha ta aje cup din ta kwanta kasan carpet din dakin, ba irin maganar ba baiyi mata ba amma fir taki tashi ta fita, da ya isheta ma sai ta rarrafa ta isa bakin gadonsa ta hau taja bargo ta kwanta. "karka cika ni da surutu nasamu yayi sauki, ka kashe fitila don ni bacci zanyi." Idan kaji yadda take maganar sai ka rantse da Allah dakinta ne, galala yake kallonta baki bude "Ke wai bakida hankali ne? Hoodah a dakina kike fa bazaki tashi ki koma naki dakin ba zakizo nan ki dinga mun iko a nawa dakin? Tashi da Allah ki tafi." Ya fada yana jawo mata bargon, rikewa tayi gam tana harararshi, "Saida safe Sultan, at least be nice koda sau daya ne, kaga banason kana tabani kuma ni ba iya tashi zanyi da kaina ba, idan har kaga bakason kwana nan din kana iya komawa parlor, bye." Kallonta ya tsaya yi anya yarinyar nan batada ta6in kwalwa kuwa? Shi dariya ma ta bashi, ashema bataso ya ta6a ta shine ta kwaso jiki tazo masa daki? Yanzu kuma gata a kan gadonshi inda yake kwanciya? Fitila ya kashe ya koma dayan side din ya ja bargo ya lullu6e ya kwanta. Ko kwakkwaran motsi ya kasayi saboda tsoron kar ya ta6a mata jiki. Can cikin dare Hoodah ta gangaro gefenshi ta rungume shi ta kwantar da kanta bisa kirjinsa a haka ta cigaba da baccinta, da sauri ya bude ido yana zare su kamar munafuki sabon kamu, wani irin zabura yayi kamar ya kurma ihu, karshe dai a haka ya hakura ya rufe idonshi har bacci yayi gaba dashi...

Saturday, 12 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 12

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 12


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




A bangaren Sultan kuwa sashen Ummi ya nufa, tana kwace daki ta mike kafa bayinta na mata tausa, gefenta bowl din guava ce tana yanka tana ci a hankali tana kallon series a Zee world, "Ummi baku gajiya ko? Salamu Alaikum..." ya furta yana nufar inda take zaune..." amsa sallamar tayi ta juyo ta amsa masa sannan ta juya ta cigaba da kallonta, wannan yana daya daga cikin abinda yasa ya tsani Zee world, shidai Umminsa tana son kallon channel din zata iya bata minti 20 ta kalla abinta batako kula shi ba. Dama episode din ya kusa karewa sadda ya shigo sai da aka kare ta juyo tana kallonshi da murmushi a fuskarta tace "Afuwan Sultan I was carried away that's why.... kasan Jodha ta..." katse ta yayi da sauri jin zata fara bashi labari yace "Su Akhbar da Jodha ko? Ummi naji labarinsu har nagaji tun anayi a zee tv na kalla ta bakinki yanzu dai ina kwana?" Yayi tambayar yana kwantar da kansa kan cinyarta don dama ta sauko da kafafunta kasa daya shigo. Tayi murmushi "Lafiya lau an tashi lafiya? Dazu ay mun shiga sashen naku hala baka tashi daga bacci ba?......" Suna cikin firar ne sai ga mai martaba ya shigo a natse yana ganin Sultan ya ware idanu waje "Wai kai bazaka girma bane? Ke kuma kina kallonshi kika barshi ya wane haye kan cinyarki god'e god'e dashi wanda ya isa ya aje yara amma jishi dan Allah, kai da Allah tashi ni kar na sake ganin ka a haka, ita diyar mutane da ka aje gidanka batada uwar zata hau kan cinyarta sai kai katoto dakai ka wani dale bisa cinya, kasan Allah Sultan ka fita daga idona...." nan Abbi ya rufe ido ya dinga bala'i ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba Ummi tace "Komai girmansa ay nice uwarsa yaro baya girma da mamansa ay..." yace "Nadai gaya maku yaron nan lalaci gareshi ni banga ta inda zai iya rike masauratar nan ba duk sadda akace babu ni, tunda ya dawo ban taba ganin ya kama man komai ba sai shiririta, kai daga yau ka dinga zuwa ina dora ka bisa hanya ka dinga ganin me akeyi ina ma amfani? Kuma yawon zuwa da kake nan bangaren yayi yawa kar na sake ganinka nan sai weekend har sai aurenku yayi wata biyu ka zauna can wurin matarka kana ji na?" Shi yanzu ina zai rika zuwa? Dama ba fita yake idan anga ya fita toh ya tafi farauta shida dogarawansa sai kuwa yawon shakatawa da yake zuwa da yamma, gashi an hana shi zuwa gida wai sai weekend, lallai Hoodah zata dandana gudarta badai ance sai ya xauna da ita ba 24/7 toh wallahi sai ta kirasu tana kuka akan su barshi ya dinga zuwa wajen Ummi tsabar azabar da zai mata sai ya gasa mata aya a hannu. Haka ya mike ya bar Abbi yana ta faman mita yau Ummi ta bani dama ya sabayi mata.

Sashensu ya koma yana isa ya jiyo sautin muryarta saman dining tana gurza carrots ko lura dashi batayi ba, cikin muryarta mai sanyi da dadin sauraro da alamar cikin damuwa take karanta Qurani mai girma cikin suratul Maryam, kan doguwar kujera ya kwanta tun Sultan na jiyo sautin muryarta har bacci yayi awon gaba dashi dama bacci sama sama yayi jiya. Saida Hoodah ta gama hada lunch dinta tsab baiji abinda takeyi ba, kawai tazo wucewa daki zatayi wanka da alwala kawai sai ta hango shi kwance da farko tsoro ya bata saida ta leka sai ta ganshi yana ta sharar baccinsa hankali kwance, cike da fargaba ta taka inda yake saboda ita har ga Allah tana jin tsoro ta shiga wanka ta barshi parlor yana iya shigo mata, da wannan tunanin yasa tayi hanzarin karasawa inda yake din tana dan bubbuga kafadarsa a hankali, ashe shikuma wani mummunan mafarki yakeyi Hoodah bata sani ba, aiko tana dafa shi yayi wani irin kukan kura ya finciko ta tilas ta fado bisa shi take yawani makalkaleta ya saki ajiyar zuciya ya koma baccinsa, toh shi dama koda yana yaro idan yayi mafarki mai ban tsoro haka zai kankame Ummi a haka zasuyi bacci har asuba, take jikin Hoodah ya fara 6ari ta fara kacaniyar kwace kanta sai ga hawaye shar shar zuciyarta na harbawa, aikuwa ashe hawayenta bisa kirjin Sultan suke sauka, cikin sheshekar kuka tace "Don Allah Sultan kayi hakuri, wallahi tunda ka fita ban kunna tv ba dan girman Allah ka rabu dani Wallahi sallah zanyi..."  tama rasa dame zata rokeshi ya kyaleta ita dai burinta ya rabu da ita. Cikin bacci ya bude idanunsa wanda yayi sanadiyyar saukarsu cikin idanun Hoodah wanda har yanzu hannunshi na nade a kugunta, wani sabon tsoro ya shigeta da sauri ta kulle idanunta gam gam "Babu abinda xan maki kinji? Ummi haka take min idan nayi mafarki marar kyau hold on for a moment please." Ya fada bakinshi na rawa dan har yanzu jinshi yake tsundum cikin mafarkin.. "A'a Amma...." ta fara rokonsa yayi sauri yace "Please Hoodah, koda minti biyar ne, kawai calming zanyi in ba haka ba zan iya suma..." ya fadi maganar a hankali tare da rufe idanunshi, ba yadda Hoodah ta iya illa tayi hakuri ta dora kanta bisa kirjinsa comfortably itama ta rufe idanunta itama kanta so take ta samu nutsuwa don har yanzu jikinta bai bar kyarma ba. 

********

Zaune suke a garden Sarauniya Karimah na hakimce kan kujera an cika mata gabanta da kayan makulashe bayinta na ta aikin fita, da alama dai wani take jira tana nan har kusan minti goma sha uku sai gashi ya iso cikin shiga ta alfarma, da sauri tasa akayi masa iso ya shigo nan ta sallami bayinta suka fita da sauri, zama sukayi kan kukera a take nan Karimah tace "Barka da isowa? Da fatan dai ban takura ka ba?" Yace "Ko kusa it's a pleasure to be here..." tayi murmushi "MashaAllah, Da fatan dai kasan dalilin da yasa na kiraka a nan?" Yace "Nasani ay zuwan nawa nan din nasan zai amfane ni sheyasa kikaga na zo..." tace "Alhamdulillah, ay dai kana da alaka da sarkin Niamey ko?" Ya gyada kai "Kwarai ma kuwa, cousin dina ne na jini da mahaifinsa da mahafiyata uwarsu daya ubansu daya..." tace "MashaAllah, dama musabbabin kiran kenan, don mu cigaba da tattaunawa kan maganar mu ta rannan? Are you still interested ko kuwa?" Yace "Inaso sosai indai har zan samu mai zai hana?" Ta numfasa "A rayuwata banaso inga Hoodah cikin farin ciki ko kadan! Nafiso ta kasance cikin kunci da bakin ciki sheyasa tun farko na tsiro da wannan aure saboda cimma wata manufata, inata tunanin hanyar da Zan bullo nan na fara aiwatar da bincike akan Sarkin Niamey aka gano man cewar ay baida kowa sai kai, iyayensa shi kadai suka haifa..." yace "hakane..." tace "Kaga kenan idan ya mutu dansa ne zai gaji sarautar ko ba haka bane?" Yace "Hakane..."  tace "Toh nikuma bazan zira ido inga Hoodah na samun cigaba ba, inaso mu hada karfe da karfe mu tarwatsa farin cikinta..." ya gyara zama "meyasa? Kuma ta yaya zamuyi hakan?" Tace "Inada shawara! Idan har plan din namu yayi working successfully tou ina tabbatar maka da kaine zaka gaji sarautar sannan idan ka hau kan mulkin sai yadda kakeso zakayi, amma kafin nan sai nasa an kawar da sarki shida matarsa, sannan mu samu yadda mukeso ta karfi zakayi a matsayinka na kawun Sultan, zaka rikide ka zama mugu, nikuma daga nan zan rika baka order abunda xakayi, kasani riba gareka ga ta hayewa kan karagar mulki by force, nima daga gareni kana da kasonka mai tsoka nidai burina shina ka yarda ka kuma bani hadin kai..." ya numfasa gamida gyara zama "Na dade ina kwadayin kujerar nan saidai nasawa kaina dangana nasan bazan samu ba, amma naji dadin maganar nan da kika kawo man saidai wani hanzari ba gudu ba, kina ganin asirinmu bazai tonu ayi saurin gano ba?" Ta kyalkale da dariya "Ba ubanda ya isa ya gano mu na dade ina shirya wannan plan din nawa, kai kana ganin a banza na hada auren Yarima da Hoodah ne? Ay ina sane da abunda nakeyi, don haka kar ka samu damuwa yanzu haka ma sarki baya nan sheyasa kaga na kiraka ban bar wata kofar da za'a zarge mu ba, yanzu zan fada maka yadda zamu fara aiwatar da wannan shiri namu...." yace "Toh Alhamdulillah, nagode kwarai da gaske kuma naji dadin wannan daukaka da kika zo man da ita na maki alkawari ko mey kika sani zan maki shi without any hesitation..." ta saki dariya "Good, zan neme ka ta waya yanzu ka tashi ka tafi kafin sarki ya dawo bana so plan dinmu ya ruguje, zan maka bayanin komai ta cikin waya..."  wani briefcase ta dora masa bisa cinyarsa, bude masa tayi sai ga kudi dollars makil ciki ya saki salati yana ta6a kudin not believing his eyes ya dago yana kallon Karimah "Duk naka ne wannan, wannan ay somun ta6i ne muddin xaka bani hadin kai..." yana kyarmar jiki yace "Kisa a ranki anyi an gama kawai..." ta saki dariya "Very good, ka tashi ka tafi din zan neme ka..." mikewa yayi da sauri yana faman washe baki "anytime kike da bukatar magana dani just call me babu wata matsala!" Tace "Tou shikenan malam Murtala nagode." Daga haka sukayi sallama yayi gaba cike da farin ciki. 

***********

Kamar yadda Sultan yayi alkawarin minti biyar din nayi yayi kokarin mikewa tana ganin haka tayi zumbur ta mike cikin rudu ko kallonshi batayi ba ta wuce dakinta direct ta rufe kofar da key tayi hanzarin fadawa bathroom don yin wanka, koda ta fito saida ta bata lokaci sosai sannan ta shafa mai tasa kaya, gabatar da sallah tayi tana idarwa tayi azkhar dinta da kartun quran dinta ta dade tana adduar Allah ya kareta daga sharrin masu sharri sannan ta tattara kayan ta adanasu inda suke, zama tayi gefen gado yunwa na cinta amma tsoron fita takeyi, can dai taga zaman bayi mata zaiyi ba ta mike ta fita daga dakin aikuwa sai gashi ya shigo da alama daga masallaci yake, komawa tayi da gudu dama bai lura da ita ba zama yayi gamida kunna tv ya fara kallon sports, ta kara akalla minti 30 can dai tayi shahada ta fito daga dakin yanajin motsinta yayi sauri ya kashe tvn, nan ta saki baki tana mamaki toh shi meyake nufi kenan ita bazata yi kallo ba sai shi? Wata irin uwar tsawa ya daka mata bakasan lokacin data zabura ba gabanta yayi wani mumunan faduwa. "da kikayi tsaye a nan kina kallona cikin cikinki xaki maidani ki sake haifeta? Malama zaki daina kallona ko kuwa?" Kasa daga idanunta tayi tana jin tsoro ita dai abubuwanshi sun fara bata tsoro, yanzu he's kind and caring anjima yafi wuta zafi... Mikewa yayi ya nufi dining fuskarshi kamar saukar mutuwa, shi ba komai ke bashi haushi ba sai yadda ya dinga rokonta tayi huggin dinsa ashe dai shi sakari ne baisani ba? Har Yaushe zai tsaya rokon wannan hug? Yayi mey da banzan jikinta? Shi ma idan ma ba wawanci ba da ban haushi irin nashi wannan har nawa take fisabillahi da zata dauke mashi hankali? Wani mugun tsaki yaja cikin jin haushin kanshi ya daga kai ya hango ta tsaye inda ya barta hawaye sun taru a cikin idanunta amma basu sauko ba, "Zakizo ki zuba man abinci ko kuwa? Ko so kike ni in zuba da kaina ne?" Wata tsawar ya daka mata wanda batasan lokacin data karaso kan dining din ba dan har tuntu6e ta kusan yi da kasan rigarta, idanunta na kan warmers ta tambayeshi mai zai ci? Don tana gudun kar ta kalleshi kuma cibi ya zama kari, bai amsata ba sai kawai ya bude laptop dinsa ya fara danne danne, jollof rice da coleslaw sai peppered chicken ta zuba masa hade da zobo mai sanyi, plate ta kara daukowa zata zuba ma kanta yayi wani irin uban tsaki, hakan ya dakatar da ita daga zuba abincin, "Ke daga yau duk inda kika ganni kar ki kara wuce minti biyar a gurin, karki kara cin abinci tare dani ni ba sa'anki bane ba don Wallahi 6alla ki zanyi kika take dokata a gidannan kinji ni?" Ta gyada kai a hankali don ita bazata ma iya amsa masa ta rasa meyake takama dashi duka abinda yake takama dashi itama tana takama dashi, koko don ya ganta yar yarinya yake mata wannan abubuwa yana ganinshi wani babba, wata tsawa ya daka mata mai gigitarwa batasan sadda tace toh ba har razana tayi jikinta na rawa ta juya da sauri ta shiga daki. Tana shiga ta aje plate din bisa dress mirror ta fashe da wani irin kuka. Kuka takeyi har cikin ranta bamai rarrashinta, itafa batace dole sai sunyi rayuwar aure da Sultan ba, ya kamata dai yayi treating dinta kamar mutum, wulakanci da yake mata ya fara isarta, gashi batajin zata iya fighting dinsa back tsoronshi take har cikin ranta. 

Sai can lokacin la'asar taji karar fitarshi daga gidan da sauri ta fito ta kwashe kayan ta tattara komai ta gyara wurin tas, da gudu ta ruga dakinta tayi sallah, tana gama azkhar sai ta fara tunanin tayi masa dinner tun yanzu kafin ya dawo, haka kuwa akayi, tana hada miyar egusi ta jiyo sautin tafiyarshi, da sauri ta maida kofar Kitchen din ta rufe don bataso ya ganta abin ya zama wani bala'in.. zafi ne ya isheta amma tasan ko zata mutu bazata bude ba sai ta jira ya bar parlorn. Hawayenta ta goge tana cigaba da aikinta, har ta gama tsab amma tilas ta zauna a kitchen saida ya tafi sallar magrib sannan ta fito ta jera saman dining sannan ta tafi dakinta.

Can wajen karfe tara tana kwance kan gado tana waya da kaka kamar daga sama taga mutum a kanta wata irin zabura tayi har sai da kashin bayanta ya bada wata yar kara, hannunsa yake miko mata alamun tasa masa wayar tata, mika masa tayi jikinta na rawa ya amsa fuskar daure kamar tashin duniya ya kara a kunne yaji ance "toh amma kin tabbatar da babu abinda kikayi masa?" Bude baki yayi yana kallonta, Hoodah a rikice ta mike da gudu tayi hanyar bathroom, har ta kai kofa taji an finciko ta da karfin bala'i a rikice ta fasa wani uban ihu, bayanta ya hada da bango ya damki kumatunta da hannunsa biyu "Ashe ke munafuka ce? Uban ne kikaje kikace nayi maki? Ke baki fada masu abinda kika aikata bane? Why are you after my life?! Ko so kike ace wani abu nayi maki ki kira man mazinata yan uwanki su kasheni?" Yayi maganar cikin tsantsar tsanar da yakeyi mata, har shaking kafadunta yakeyi idanunsa sunyi jawur yana mata wani irin mugun kallo kamar zai kasheta! Jijiyoyin wuyanta babu wacca bata fito waje ba hawaye kuwa kamar an koro su, wani irin karfi yazo mata ta shako masa wuyan riga "Ni ba mazinaciya ba! Daga yau karka sake kira na da mazinaciya na gaji na gaji!" Ta fada cikin sheshekar kuka. Wani irin mari taji a kumatunta mai rikitarwa ta fasa wani irin ihu bata san lokacin da tace "Kayi hakuri Dan Allah dan annabi ka kyaleni!" Ta fada kamar ana kara yawan hawayen idanunta, wani irin kallo yake binta dashi idanunshi kadai abin tsoro ne can yace "Hakuri my foot!"

Friday, 11 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 11

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 11}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Yafi minti biyar yana kallon saukar numfashinta yana kuma kare ma fuskarta kallo, wani irin yawu ya hade ji kake k'utt ya juyar da fuskarsa gefe yana tunanin mafita, don shidai baisan mey zaiyi ba yanzu cire mata zaiyi ko kuwa? Tunani ya tsaya yi cikin sanyin jiki ya nufi wardrobe dinta, yana budewa yaga kayanta tsaf tsaf dasu, wata pink nighty ya hango bangaren kayan bacci cotton mai zanen katuwar teddy tayi hugging heart hannunta dan siriri, tsawon rigar iya gwiwa, sai ya samu kansa da daga rigar yana kallo... karasawa yayi bakin gadon yanayin daya ga Hoodah ya tabbatar masa da bacci ya dade da daukar ruhinta, irin baccin nan ne da mutum keyi idan yana zazzabi, shawara ya yanke a kan ya fara zare mara skirt din jikinta hakan kuwa akayi ya gyara mata kwanciya rigingine ya hade kafafunta ya shiga jan skirt din, prefect skin color dinta yake kallo chocolate color mai haske sosai, sai gashi yala yala da take dashi na jiki ya kwanta lub lub, ya dade a haka kafin ya runtse idanunsa yana sauke numfashi "For Ummi's sake..." yafada cikin sa ma kansa kwarin gwiwa, zaiyi ne bawai don she mean something to him ba sai don tana cikin wannan halin, baisan mai zai fara yi ba hannun zai cire ko hook din zai fara zarewa? Wayyo Allah! Ji yake kamar ya daura hannu saman kai yayita ihu, gashi bayinta basu nan ballantana su taimaka masa wayyo yau yaga ta kansa shikam, tsaye yayi kamar zai fashe da kuka, ganin tsayuwar bazata yi masa ba yana 6ata ma kanshi lokaci a banza, siririn tsaki ya saki wani irin weakness yakeji yana dirar ma ruhinsa baiki ace yaje ya kwanta yanzu ba, zama yayi gefenta yana sauke numfashi ya tallabo kanta da bayanta yaji skin dinta wani irin bala'in taushi kamar jariri sabuwar haihuwa, wannan anya ta san wahalar rayuwa kuwa? Komai na jikinta lugub, da kyar ya samu ya cire hook din bra din, ya zagayo hannunshi a hankali ya zare mata hannun bra din so ya ke ya gama ya wuce wurin. Ashe baisani ba wannan shine babban kuskuren da zai tafka! Yana janyo bra din komai na jikin Hoodah ya bayyana, gabanshi ne yayi wani mummunan faduwa ya dan saki kara yana runtse idanunsa "Innalillah....!" Ita kuma Hoodah wani relief taji yana cire mata ta saki wata irin nannauyar ajiyar zuciya har salon numfashinta ya chanza take ta sake masa jikinta gaba daya ya sake sakin kara gwanin ban dariya yana runtse idanunsa, yau shidai yaga rayuwa! Da sauri ya dauko rigar baccin ya sanya mata yana gamawa ya saketa da sauri ya mike tsaye yana wani shesheka kamar wanda yayi gudun fanfalaki, ko tsayawa gyara mata kwanciya baiyi ba yayi wurgi da bra din saman gado ya fita a guje daga dakin kamar wanda aka biyo za'a kashe, direct dakinshi ya shiga wanda yake gefen dakin Hoodah yana shiga ya nufi bathroom da gudu ya sakar ma kanshi shower ya dade tsaye a nan yana zare ido kamar munafuki, a hankali yaji hankalinshi ya fara dawowa jikinshi, saidai fa har yanzu taushin jikin Hoodah bai daina ji a hannunsa ba. Yana fitowa ya zauna gefen gado kwalwarsa ta daina ja ya kai kimanin kusan minti arba'in yana zaune da tagumi, can dai ya mike a kasalance gaban mirror ya shafa mai ya fesa turare ya dauko kayan baccinsa ya sanya yama manta ko isha'i baiyi ba gashi ta wuce dama yayi alwalla kawai ya tada sallah yana gama azkhar ya hau gado yana kalle kalle, a haka ya kwanta yau yama manta ko saida safe baiyiwa su Abbi ba, kwana yayi yana juyi ba abinda yakeji sai taushin jikin Hoodah bai ta6a tsamannin haka take ba, her figure, her structure astagafirullah kamar ita ta kera abunta, da tunanin Hoodah yau ya kwanta wanda hakan ba karamin haushi yake bashi ba, why yake tunaninta? Ya saki tsaki, har Hoodah ta isa ta rikita masa lissafi har nawa take? A haka ma bacci takeyi inaga idonta biyu? Ya salam yau shidai yaga ta kansa....

********

Khairy cike da bacin rai tace "Wai me Sultan ke nufi? Ya naji shiru har yanzu bai korata ba? Kuma har yanzu banji wani mummunan labari ba ya fito daga gidan sarki, by now yaci ace sunga videon duk wannan shirin da nayi indai har bai korota ba ya tashi a banza kenan? No impossible! Bazai yuwu ba! Khairy never fails! Don haka a shirye nake da sake zage damtse da shirya wani makircin da tuggu! Idan har wannan aikin baiyi tasiri akan yarima ba toh ya zama dole na sake daukar wani mataki akan wannan tsinanniyar matar tasa! Zan kara bada kwana biyu idan naji shiru zanyi tattaki koda na 6adda  kama ne sai naje, idan naga komai lafiya lau toh ina mai tabbar ma kaina da cewa zan sake wani shirin, Ni Khairy Usman na dauki alkawarin cewa, sai na tarwatsa Hoodah, sai nayi destroying dinta, sai na keta mata haddi! Sai na kuma daukar fansar abinda tayi man, bana asara duk abinda nakeso sai na samu...." ta kece da wata irin muguwar dariya tace tana shafa hoton Sultan dake hannunta "Welcome to hell Hoodah, kin kawo kanki da kanki babu mai cetanki sai Allah! Let the game begin!" Ta sake kecewa da dariyar mugunta sai kace wata witch.

*********

Sanyin safiya ne ya tada Hoodah, ko da asuba bata farka ba sai yanzu Allah ma ya taimake ta hutun sallah take, jiki a sanyaye ta mike kamar wacce akayiwa duka ta wuce bathroom tayi brush, ta wanke fuskarta, ta fito tana tafiya kamar marar lakka ta zauna shakaf kan gado, jikinta ta kalla a razane taji ko bra bata dashi, batasan lokacin data mike zumbur ba! Tana kare ma kanta kallo ta mirror kuka ta fashe dashi kamar an aiko ta, "Na shiga uku! Kar dai Sultan ne ya cire mani bra?!" Ta furta a rude tana dudduba jikinta, Shikenan taga ta kanta yanzu Sultan yaga jikinta kenan? Haka tayi tsaye ta kasa ta6uka komai, can dai a sanyaye ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta kimtsa kanta da dakinta sai kamshi ke fita daga jikinta kamar koda yaushe, yadda ta bar parlon jiya haka ta tarar dashi... gyara ko ina tayi yayi fes ta kunna burner ta sa turaren wuta, ta kunna ac, ta rufe curtains, tana kitchen tana hada tea aka yi knocking da sauri ta fito ta leka ta whole din kofar sai ganin Sarki da Sarauniya tayi tsaye, ware fararen idanunta tayi da sauri taje daki ta dauko mayafinta ta fito da bude kofar da sauri kanta kasa,  sukayi sallama suka shigo suka zauna ita ma ta zauna kasa ta gaishe su da ladabi suka amsa, Sarki yace "Yaya jikin naki? Da fatan kin samu sauki?" Ta gyada kai "Alhamdulillah." Sarauniya tace "Toh MashaAllah, daman munzo ganin jikin naki sanann abunda ya faru rannan inaso ki manta dashi kamar ba'ayi ba sannan kiyi hakuri da yadda mukayi treating dinki..." ta dago da sauri tace "Basai kun bani hakuri ba Ummi, nagode da kulawa..." Abbi yace "Madallah da y'a ta gari Allah yayi maki albarka..." tayi murmushi "Ameen, bari na kawo ruwa." Ta fara kokarin mikewa tsaye Batul ta tsaida ta "Karki damu sai kace wasu baki? Bari mu tafi Allah ya kara lafiya." Suka mike a tare ta rakasu har waje ta masu sallama sannan ta juyo ciki. Daki ta tafi ta maida mayafinta ta nufi kitchen ta karasa hada tea dinta ta fito ta kunna tv, series dinta na jiya taga anayi, cike da jin dadi ta fara kallo tana sipping tea dinta a hankali, tana cikin kallon taji sautin bude kofa, kafin ma ta juya sai ta gansa har ya karaso cikin parlon, kai tsaye wurin tvn ya nufa ya kasheta gaba daya, bata tsaya tambayarsa dalili ba kuma haka ma batace dashi komai ba, sai ma tace "Ina kwana?" Ta dan russuna alamar girmamawa, muryarta har wani rawa rawa takeyi, tama ki yarda su hada idanu, wani siririn tsaki yaja "Daga yau ban yarda ki sake kunna koda socket ba sai da izini na, is my house sai abinda nace za'ayi do you understand?" Wani kallon banza yake binta dashi yasa tayi saurin kai kanta kasa tana wasa da cup din hannunta "Naji..." tana fadin haka ta mike tana maganar zuci "Ji man mutum kai sai kace kayan kallon ba nawa bane yake wa mutane wani iko da su mtsw." Kitchen ta wuce ta sauke dankalin dake kan wuta ya soyu, ta kwashe egg sauce a warmer dankali ma ta xuba ta wuce kan dining ta jera komai ta kai plates da kayan tea, bata ma jira abinda zai fada mata ba ta fara serving dinshi yana zaune hakimce yana latsa waya, tura masa tayi gabansa ta debi nata ta koma can tsakiyar parlor inda bazai hangeta ba saboda kejeru, kujerun ma dakakkun royal chairs ne, tana zama kawai sai ta fara kuka amma fa ko kadan bamai sauti bane ba, baima jita ba har ya gama ya mike zai shiga dakinsa ya hango ta tana goge hawaye wani tsaki yaja wai don ya hanata kallo shine take masa kukan munafunci? Har ya wuce kuma sai ya tuna magaganun Ummi ajiyar zuciya ya sauke yazo daidai inda take zaune ya durkusa ya kureta da ido da sauri ta dago kai tana dagowa suka kalli juna ido cikin ido haka kuma yayi da zubowar hawaye bisa kumatunta, wani abu yaji ya tokare masa kirjinshi yayi masa wani irin sukar da harda saida ya runtse idanunsa yace "Ya Rabbi!" ita kuwa Hoodah yadda kasan an bude tap haka ta cigaba da rizgar kuka wane an aikota kuka takeyi bill hakki har can cikin ranta, karshe ma data ga abin nayi ne kawai sai ta kifa kanta bisa kujera ta cigaba da rera kuka, shi kuma Sultan zugui yayi yana kallonta don shi sam baiga abun kuka a nan ba. Da ya gaji da tsugguni dan kansa sai ya zauna dirshen ya cigaba da kallonta kamar ya samu tv baice kala ba, amma dai sai yau ya lura kamar tana tare da damuwa kala kala, ko da yake irin haka is better mutum yayi kuka kar hawan jini ya kama shi yasan dai Hoodah bata tare da depression. Ganin ta rage kukan nata yasa ya gyara xama yace "Feeling better?" Gyada kai tayi kamar wata yarinya tana faman share hawaye, ita kanta mamakin Sultan takeyi sai kace ba dazu ya gama yi mata masifa ba? Amma yanzu jishi yana wani kwantar da murya kamar bashi ba, ba tare da yayi koda murmushi ba don ma kar tayi tunanin yawani sauko, a hankali ya mike yana zura hannu cikin aljihunsa both hands, "Good, dama na kyaleki ki ne ki gama kukanki don nasan bai dace ba mutum yana pouring heart dinsa out a tsaida sa ba, amma hakan ba yana nufin na chanza abunda na fada ba yana nan daram no tv kina jina?" Yadda yawani daure fuska sai ka rantse bashi bane yayi mata magana dazun nan ba, ta dukar da kanta tana gyada kai zuciyarta na harbawa har mugun da tasani a fuskar shi ya dawo sabo, tace "Naji..." juyawa yayi ya sa kai ya fita ita kuma ta bi da kallo har ya fice, ajiyar zuciya ta sauke yadda kaddara ta fada mata lokaci daya, take kuma ta tuna Ashraf nan nan hawayenta suka dawo sababbi wanda suka fi nada zafi da kunci da bakin ciki... sake dukar da kanta tayi kan kujera ta fashe da wani irin matsaanancin kuka mai ban tausayi....

Thursday, 10 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 10

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 10}




To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Daya daga cikin kuskuren daya tafka shine daya bari Hoodah ta kufce ba, da kuma ya tafi ya bar family dinsa, ya bar yan uwansa da masauratarsa, tushensa, asalinsa da kuma zuciyarsa!

(Emotions, loads and deep emotions)...shine kawai abinda Ashraf ke ayyanawa a ransa, ya tsaya tsayin daka tare da family dinsa duk rintsi duk wahala duk abinda yafaru ya dinga dawo masa crushing his weak heart gaba daya yayi breaking down, dalla dalla, guilt, bakin ciki, fargaba ya dinga bin ko wane lungu da sako na jikinsa, bai taba tunani ko a mafarki cewar zai taba rasa Hoodah ba duba da yadda suka taso cike da hope na mallakar junansu amma rana daya tak komai ya ruguje kamar glass din da ya tarwatse kasa yayi breaking into pieces haka relationship dinsu ya tarwatse wanda baya tunanin zai gyaru, heart dinsa tana tare da ciwo kuma warkewarsa ba nan kusa ba, ba abinda ya zama sai prisoner din kansa da kansa tunda ya baro Agadez! Akwai shakuwa! Akwai farin ciki! Akwai kwanciyar hankali! Da kuma soyayya! Kwalla ya taru cikin idanunsa a yayin da yake tuna wasu abubuwa da dama, abinda yakeji yafi karfin rubutu... Wani abu ya tuna shekarun baya da suka shude...

"Yaya Ashraf...!" Yar kimanin shekara bakwai ce ta fito tana tafiya hannunta dauke da lollipop guda biyu, a hankali ya juya yana ganinta ya saki murmushi yace "Na'am Hoodah habibty...!" Ya durkusa daidai ita yana kallon cute fuskarta da dimple dinta wanda ke kara mata kyau idan tayi smiling, tace "me kakayi a nan??" Baiyi replying dinta ba sai ya tsaya yana kallon fuskarta yadda take tsotsar lollipop dinta... miko mashi lollipop din tayi dake dayan hannun nata wanda bata fasa ba tana murmushi sosai wanda ya kara bayyanar da cute dimple din nata, yayi murmushi "Wannan fa? Nawa ne?" Ta gyada kai "Nawa ne Abba ya bani shine na aje maka daya....." yayi murmushi "Wow habibty, amma fa gaskiya ni daya ya min kadan saidai ki hada dana hannunki wanda kika fara sha kibani..." shiru tayi jin abinda yace tana kallon lollipop din nata ta kasa cewa komai, gimtse dariyarsa yayi ganin yadda ta boye lollipop din nata bayan hannunta ta mika masa dayan "Wannan ne naka, wannan nawa ne..." ta fada tana turo dan karamin pink bakinta, sai yayi alamun fushi ya mike tsaye yace "Shikenan na gane rowa zakiyi man toh bazan ma sha ba gaba daya jeki shanye kayanki...." wai shi nan harda tafiya kamar gaske da sauri tayi wuff ta kamo masa hannunsa harda dan kwallanta ta hade lollipop din da nata da nashi ta mika masa "Toh na koshi gashi ka shanye duka..." baisan sadda ya saki dariya ba ya duka tare da dagule mata hanci "Wasa nakeyi habibty, da inada wani ma dana kara miki, amma ki bari zan siyo maki da yawa ki dinga tafiya school dashi..." ta wani daka tsalle tace "Thank you yaya Ashraf you are the best best best ever!" Yayi dariya "And you are also the best Habibty..." haka ya dawo daga duniyar daya lula lokaci zuwa lokaci yake goge kwallan dake gangaro masa, this feeling really hurts damn! Knocking yaji a kofa ashe an kai minti kusan ashiri ana knocking mikewa yayi yana kara goge hawayen idanunsa ya nufi kofar tare da budewa, Abokinsa ne Yasir wanda yake zaune a gidansa tare sukayi university abokinsa ne na kut da kut. Turus Yasir yayi bakin kofa da mamaki yace "What's wrong with you? Are you okay?" Ashraf yace "Yasir!" Ya daka masa tsawa yana mai rike hannuwansa duka biyun hawayen na cigaba da zuba daga idanunsa, da sauri Yasir yayi hugging dinshi take ya fashe da kuka kamar wani karamin yaro, "Yasir..." yace cikin muryar kuka "Ashraf please tell me what's wrong?" Runtse idanunsa yayi har ga Allah so yake ya manta da ita yasan ita yanzu matar wani ce bai kamata yana tunaninta ba amma ya rasa ta wace hanya zaiyi hakan, "I...i....ba....zan iyaba....!" Yasir yace "Menene?" Jikinsa na wani kadawa yana wata irin zufa yace "Ka taimaka man Yasir! Please help me!."

*********

Yadda yake rufe mata baki da hannunshi ba karamin razana tayi ba gashi ya matse hannayenta duka ya harde su wuri daya, girgiza kai tayi tana wani irin zillewa tanata kokarin maida hawayen idanunta hakan bai hana Sultan kara mata karfin rikon da yayi mata ba, ba karamin cikin tashin hankali ta shiga ba ita gaba daya yanzu tsoronsa takeyi. Daga karshe data kasa rike hawayen kawai saita hakura ta sake su suka cigaba da zuba freely kamar da bakin kwarya, janta yayi ya xaunar da ita kan kujera, wani irin tsoro ne marar misaltuwa yake shigarta har yafi wanda taji ranar da mutanen nan suka durar mata! Suna tafe inda zai zaunar da ita sai yaga numfashinta na sama sama tana wani irin gunjin kuka hade da shesheka irin kukan nan inka zuciya kake sakinsa, shifa kukan munafuncin nan ke baya so in har tana masa wannan kukan wahalar shi zata sha a banza. Wurgar da ita yayi saman kujera sannan ya taka daf da ita, girgiza mashi kai kawai takeyi hawaye kuwa kamar ana tunkudo su, ganin ya nufota gadan gadan sai tsoro ya dirar mata ko dai shima irin abun nan zaiyi mata da aka shigo mata, kodai shima irinsu ne? Sai ta fara kyarma take ta fasa wata irin razananniyar kara "Wayyo Abbana! Na shiga uku Abba ka cece ni! Dan Allah dan annabi kayi hakuri! Dan girman Allah! Wayyo Abbana na shiga uku!" Turus yayi cike da mamaki yana kare mata kallo "Meye haka? Bakida hankali ne? Wani abun kikaji nace zan maki? Me zanyi da kazamin jikinki?! So disgusting!" Ya fada yana mai juyar da fuska feeling hurt, wata irin tsawa ya daka mata mai razarnawa jin bata daina masa ihu ba duk ta cika masa kunne, take ta hade kukan nata sai dai yaga tayi shiru bata kara motsi ba idanunta na kallon sama, a tunaninshi duk cikin iskancin nata ne data tsiro dashi kwana biyu, tsaki yaja ya wuce dining ya zuba abinci bai kara bi ta kanta ba, can dai yace "In kina son zaman lafiya dani better confess ki bani hakuri a wuce wurin, amma na lura shegen taurin kai ne dake!" Saida ya gama cin abincinsa to his surprise yaji abincin yayi mugun dadi ashe ta iya? Yana gamawa yabi da pineapple and mango juice sannan yayi wani balancing ya fiddo wayarsa yayita chatting dinsa yana latse latse hankalinsa a kwance. Can ya saki guntun tsaki "Ina zaman zamana aka kakaba man wannan mugun aure, auren nan ko auren kaddara auren wahala! Mts!" Tsaki ya kuma ja cikin takaici ya mike zai shiga daki yaga tana nan yadda ya barta, yaga dai alamun ko kafarta bata motsa ba har ya kai cikin daki sai kuma ya dawo yana fadin "Wannan wane irin sabon iskanci ne haka Hoodah?" A kanta ya tsaya hannayensa harde yana kallon fuskarta wanda hawaye duk ya bubbushe mata, "Ke tashi kije kiyi clearing kan dining... wane irin sabon salon iskanci ne kika tsiro dashi haka?" A tsawace yake maganar amma ga mamakinsa sai yaga ko motsi batayi ba, "Lallai yanzu kuma raini kika tsiro dashi kenan?" Ya fada yana kada key din hannunshi "Zaki tashi ko kuwa one last chance! Wallahi karki bari raina ya kara baci!" Still dai shiru ko motsin kirki batayi ba, sai a sannan ya lura da yadda numfashinta ke tsaye cak kirjinta baya motsi, take hankalinshi yayi matukar tashi! Dukawa yayi ya kamo hannunta sai yaji shakaf hannun ya koma ya fadi, innalillahi wa inna ilahir rajioon! Zuciyarsa ta buga, cikn rudu ya kai hannunsa saitin hancinta yaji numfashinta bai fita, yar da key din hannunsa yayi a guje yayi fridge ya dauko katuwar kwalbar swan tsabar rudu baima san a bude ya bar fridge din ba, yana zuwa ya bude ya fara yayyafa mata a fuska, sam baiyi tunanin suma tay ba don shidai bai ta6a ganin anyi suma a haka ba, daya ga yayyafawan bazaiyi ba kawai sai ya juye mata shi gaba daya amma ina shiru kakeji Hoodah bata dawo ba, cikin rudu ya fara neman wayarsa a cikin gidannan yama manta shaf tana cikin aljihunsa, haka yayi ta watsi da pillows din parlorn ya daga wannan ya maida, ya bude can ya rufe, wata irin zufa ce ke keto masa can ya laluba wayarsa sai gashi ya ganta a take ya kira family doctor dinsu, nan Sultan yayi masa bayani abinda ke faruwa nan ya fadi mashi me zaiyi kafin ya karaso. Abinda Doctor din yace mashi shi ya fara yi mata, nade hannun rigarsa yayi with both hands ya fara daddana kirjinta amma duk a banza, can dai ya dage iya karfin yayi mata wani irin danna take tari ya sarke ta, baisan lokacin daya furta "Alhamdulillah." ba, ya wani saki ajiyar zuciya ya zauna dirshen kasa yana maida numfashi feeling relieved, tana ganin shi gefenta sai ta nemi ta kara birkicewa saboda gabanta ne ke cigaba da faduwa ba kakkautawa, Sultan ya lura tabbas tsoro takeji matuka, yasan idan mutum ya suma ba'a motsa shi in ba haka ba attack din zai dawo. Mikewa tayi da kyar tana dudduba jikinta taga me yayi mata? Ajiyar zuciya ta saki sai ga hawaye shar shar ta fara kokarin tashi tsaye ta kasa ga wani weakness dake kwasarta, ji take kamar zata kara suma. To her surprise sai ganin Sultan tayi ya koma da sauri kusa da ita, zatayi magana kenan kawai taji an janyo ta a hankali anyi hugging dinta yana saitata "Listen, karki tsorata nothing will happen to you, ki natsu Doctor yana hanya..." yadda yayi maganar cikin kwantar da hankali yaba Hoodah mamaki, sai tayi lamo ta samu kanta da kasa motsin kirki don ita bawai zata iya motsawa daga wajen ba she's weak, a kirjinsa ya kwantar da ita sun kai kimanin minti goma sai ga doctor ya iso sallama doctor yayi kawai Sultan sai ya tsinci kansa da zuwa daki dauko mata hijab, yana sa mata hijab din sai yaje ya bude ma Doctor din kofa ya karaso ciki, nan yayi yan duba dubensa ya fada ma Sultan cewa idan mutum ya suma ba'a jijjiga shi ko a zuba masa ruwa mutum ya farka hakan yana kara guddumuwa akan suman, "She had a panic attack! Ya kamata ka zauna ka tambayeta meke damunta, she should avoid it at all cost." nan ya bata wasu magungunan yace "Wanann zasu rage mata panic din don haka kar tayi wasa dashi ta dage tasha na kwana bakwai ne..." nan Sultan yayi masa godiya ya tafi, koda ya dawo isketa yayi ta bingire kan kujera tana ta bacci, tsaye yayi yana kallonta ya jima a haka yana shi kanshi baisan dalilin kallon ba, sai can yasaki ajiyar zuciya ya daga ta ya jinginar da ita bisa kafardarsa ya kaita daki, kwantar da ita yayi yace "Hoodah..." wani yar yaji daya kira suna nata,  ta dan bude ido kadan tace "Uhmm?" Ta amsa da kyar, hijab din ya cire mata ya lura sai zufa takeyi, sannan ya dinga ta6ata alamun ta tashi "tashi ki canza kayannan jike suke kar kiyi mura... ko so kike ki mutu ne?" A kasalance ta mike dankwalin kanta ta zame take gashinta ya warware ya baje bisa bayanta, hannu ta daga kamar wata yarinya ita sam ta manta da wa take ita bama muryar maza takeji ba ita duk a tunaninta Kaka ce. "kaka cire mun rigar please wallahi bazan iya ba na gaji..." cike da shagwaba Hoodah ke maganar tawani turo baki tsabar baccin da takeji... kallonta kawai ya tsaya yanayi innocently take maganar, sai kayi tunanin wata yarinya yar shekara goma ce, ganin dai da gaske bacci takeyi a haka dole yasa ya matso dab da ita, ajiyar zuciya ya sauke yanzu ya zai cire mata rigar nan? Kuma bazaiso ya barta haka ba sanyi yana iya kamata, daure fuska yayi yace "For the sake of Ummi," kafin ya fara cire mata rigar harda runtse idanu, Hoodah na jin an cire mata riga tayi wani luuuu ta fada kan gado ta cigaba da baccinta, tace "Thank you..." daga nan ko motsi bata kara yi ba sai numfashinta ya fara fita a hankali mai nauyi alamun bacci takeyi mai dadi. Sukuku Sultan yayi baki sake yake kallonta yau shikam yaga ta kanshi ya jawo wa kansa, gashi Doctor yace kar a bari komai ya takura mata har yanzu numfashinta bai dawo daidai ba, yanzu ya zaiyi ya cire mata bra fisabilillahi?!

YAR AGADEZ PAGE 09

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 09}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Washe gari koda Hoodah ta farka ta kimtsa tayi wanka ta shirya tsaf, saidai fa kusan zaman minti 20 tayi cikin dakinta tana jero addu'oi tana fatan kar ya sake shigowa inda take don ita ko kaunar ganinsa batason yi, a hankali jiki a sanyaye tayi shahada ta dan leko kadan taga ba kowa don ta cewa bayinta su bata wuri ita kadai zata kwana gidan yau, don haka parlon babu kowa sai masu aiki daya na jera abinci kan dining daya kuma na goge tv stand, duk suka dago suka gaisheta da sauri ganinta tsaye tsakar parlor ta amsa a mutunce, bata ga alamar Sultan ba ko ta tambayi inda yake? Bayan sun kammala aikinsu suka tattara suka fita, dining din ta karasa don wata irin wahalalliyar yunwa takeji kamar tayi hauka. Ta zauna kenan tana tsakar serving ma kanta abinci taji an bude kofa, da sauri ta juya ganinshi tsaye bakin kofa directly idanunsa cikin na juna, yayi bal'ain yi mata kwarjini sanye yake cikin white shadda mai kyalyali marar nauyi ta amshi jikinshi tayi masa kyau ainun. Take tasha jinin jikinta yadda taga ya wani murtuke fuska dole ya sakar mata da wani irin tsoro da fargaba sai kace taga dodo. Wani siririn tsaki ya saki na jin haushin iyayenshi don su suka tursasa masa yazo duba ta, tabbas suna fushi suma saidai fa bazasu fasa duty dinsu na amanar da aka basu ba na kula da yar mutane, tunda sassafe Ummi ta hankado keyarsa don tasan d'an nata bai iya fushi ba ko kadan idan yayi fushi yakan kasa controlling emotions dinsa, don haka da lalla6a da nasiha ta samu ya yarda zaizo din, abinda tace dashi yana kai kawo cikin ranshi "Sultan bazamu taru mu zama marassa tunani ba, tabbas Hoodah bata kyauta ba amma kuma wani abu da ya bani mamaki bayan daka jata kun tafi sashenku sai kawai naji ba dadi, naji gaba daya jikina bai bani Hoodah zata aikata hakan ba, bansan dalili ba amma nidai haka nakeji, toh yau da safe sai na wayi gari na nemi fushin da nakeyi da ita na rasa, Yanzu abinda nakeso dakai shine ka daure ka tashi ka tafi wajen yar mutane, please go and check on har nasan ba sashen ka kwana ba, amana ce a wurin mu, bazanso ayiwa tawa yar abin da akayi mata ba...." ya dago yana kallon Ummi "Haba Ummi, bakiga me ta aikata bane da zaki ce haka? To nidai gaskiya bazan iya danne zuciyata ba na cutu she tarnished our reputation! It really hurts!" Ummi tace "I know, kayi hakuri komai mai wucewa ne, nidai just go to her do it for Ummi..." gyada kai yayi ya mike ba don yaso ba ya nufi sashen nasu...

Da sauri ta dauke idonta daga kanshi ta dukar da kanta kasa feeling hurt kwalla cike idanunta, a hankali ya tako inda take da kyar kamar ya koma yakeji, wani mugun kallo yake watsa mata ita kuwa idonta na kan plate din dake gabanta wanda ko spoon daya ta kasa ci sai wasa take dashi. Ji yake kamar ya shake ta ya huta amma dai albarkacin Umminsa ya sa yazo ma inda take. "Ba'a koya miki gaisuwa bane? Ko har yanzu rashin kunyar taki bata sake ki ba!?" Yafada cike da masifa, murya na rawa Hoodah ta furta "Kayi haku...ri, ina kwana?" Meyakon ya amsa gaisuwar tata sai kawai yaja tsaki sannan yaja kujera daya ya zauna yana karkada kafa, ita dai sai binshi take da ido, sunfi minti goma a haka babu wanda yayi magana a cikinsu can Hoodah ta mike tana share hawayenta tana kokarin kar hawayen ya zubo mata amma dai ta daka ganta  kasan daurewa kawai takeyi abu kadan za'ayi mata ta fara kuka. Juyawa tayi ta bashi baya tana faman goge hawayenta, sai data maida kukan da kyar sannan cikin karfin hali ta juyo tace "Me zan zuba maka?" Jikinta har wani rawa yakeyi, ko dagowa daga kallon wayarshi da yakeyi yana latse latse balle ma tasa ran zai amsa mata baiyi ba, hade hawayen nata tayi, kawai ta bude warmers ta shiga zuba masa casserole din da yasha kayan lambu da sausage, bayan ta gama zuba mashi ta tura mashi gabanshi ta hada masa tea ta mike masa, sai da ya dankara mata harara sannan ya karba, tana kyarmar jiki ta mika masa ashe bata lura ba bai kama cup din da kyau ba sai ji kawai tayi cup din ya sa6ule daga hannunta ya fadi kasa duk tea din ya fantsalar masa a farin kaya, wani irin shock ya kama shi yana dudduba jikinshi baki bude, a fusace ya mike yana huci, Hoodah ta fasa wani irin razanannen ihu tayi baya tama dauka dukanta zaiyi yadda ta ganshi, "Ke dakikiyar ina ce? Ke yarinya ce da zaki sakar man cup a kasa ya bata mun jiki? Kuma kukan me kikeyi haka? Kin cika man kunne kamar wadda aiko ma da mutuwa! Zakiyi man shiru ko sai na sa6a miki yanzun nan? Stupid kawai!" Wata irin tsawa ya kuma daka mata wadda tasa don dole Hoodah ta hadiye kukan da takeyi amma jikinta babu inda baya rawa, hannuwanta duka biyun tasa ta rufe lips dinta gam gam tana shesheka a hankali "Am sorry please...."  ita dai burinta kawai taga ya fita bata son ganinshi wani irin shakkarshi takeyi yanzu... 

"hold your sorry to your filthy self, banason munafunci Meyasa jiya kika kasa bani hakuri sai yanzu xaki wani kama bani hakurin karya, toh kisani wani kalar tausayi da wani kukan karyar da kikeyi man bazai sa na sauko ba har sai kinyi admitting laifinki kin kuma bani hakuri sannan mu dawo normal rayuwa! Kisa wannan a ranki na tsani abinda kika aikata yadda nakejin tsanarki a yanzu bana tunanin akwai irinta a duniya, daga yanzu babu wata baiwa da zata sake yi maki aiki a cikin gidan I dont care about your status ke zaki cigaba da aikin da sukeyi that's your punishment! Ki tabbatar kar na dawo na tarar da wannan cup din daya fashe kasa baki tattara ba sai na lahira yafi ki jin dadi, sakarya kawai idiot dakikiya!" Yana kaiwa nan kawai yayi gaba abinshi ya shige daki ji kake garam! Tanaji yasa ma kofar key ya rufe ta gam gam da karfin bala'i.

Durkushewa tayi kasan tiles din parlon ta saki wani irin kukan da tunda tazo duniya bata ta6a yin irinshi ba, kalamansa ba karamin impact sukayi mata ba sun ta6ata sosai, wai idan bazai iya zama da ita ba ya saketa mana, ko ta ta6a cewa tana sonshi? Toh dole ne? Ashe dama baida tausayi haka? Ashe duk wannan sanyin muryar dawani kirkin da yake mata ashe duk na munafunci ne? Kuka takeyi bil hakki ta dade a haka kafin a hankali taja jiki taje kitchen ta dauko broom da packer tazo tana dafe kai saboda yana sara mata, a hankali ta tattara gurin tana fama share hawaye saida ta gyara shi tsab sannan ta maida kitchen din. Shi kuma Sultan koda ya shiga daki bathroom ya nufa ya cire kaya ya watsa ruwa fuskar nan a murtuke kamar tashin duniya, yana gamawa ya sa kai ya fita yaje ya sallami bayinta yace Hoodah tace kar su kara zuwa aiki for a while har sai ta neme su da kanta. Side din Abbinshi ya nufa yana haraba da mutanenshi kota su bai bi ba kawai ya samu Abbi take Abbi yace su basu wuri na minti kadan, yana isa kamar wani karamin yaro sai ya fashe da kuka mai cin rai, "Abbi yanzu ka rasa wacce zaka aura man sai mazinaciya? Abbi so nake ka bani dama na rabu da ita inaso na sallameta bazan iya cigaba da zama da ita ba bazan jure ba Abbi, am tired Abbi..." Abbi ya dafa shi  "Sultan bansanka da rashin hakuri ba da tausayi ba, dan me zaka rabu da ita? Yanzu idan kanwarka ce haka ta faru da ita xakaso mijinta ya koro maka ita? Bazaka so ayita mata uzuri ba? Sannan gaskiya kabani kunya a matsayinka na namiji namijin ma jarumi wanda nake sa ran zaka gajeni wata rana ka rika zubar da hawayenka a banza ba..." da sauri ya goge hawayen nasa yace "Ba haka bane Abbi, raina ne ya baci fa, kuma ni Abbi meyasa aka man aure da ita kasani fa Khairy nakeso na aura kaje ka hadani da ita, dole saini?" Abbi ya numfasa "Komai kaga ya faru da mutum mukkadari ne daga Allah, I know you like Hoodah koda kadan ne, and kunyi bonding a yan kwanakin da suka gabata kafin wannan abun ya sameta..." ya zaro idanu waje "So kuma Abbi? Me zanso a jikin wancan yarinyar? Allah ya kyauta nikam..." dariya Abbi ya kyalkyale dashi "Sultan kenan, karfa kazo kayi dana sanin abinda kake fada mun nan gaba kazo kana mana kuka saboda kaunar Hoodah... kuma don Allah ka daina cewa ka tsaneta especially a gabanta babu dadi, nima kaina abubuwan dana fada mata jiya nayi regretting kasan idan mutum yayi fushi babu abinda bazai iya fadi ba, zamuje nida Batul mu bata hakuri har sashenta, inaso mubi komai a sannu, nasan gaskiya zata fito inma ta aikata inma bata aikata ba duk Allah zai bayyana mana inshaAllah, don haka ka danne zuciyarka ka daina mata mugunta saboda abinda ya faru..." numfasawa yayi "Wallahi I hata her I hate everything about her now amma saboda kai zan daina InshaAllah..." godiya Abbi yayi mashi da bashi baki da kuma tunatar dashi akan zamantekawar aure, shidai jinshi kawai yake amma baiyi niyyar aikata abinda yace mashi ba, "kuma naji labarin ka korar mata bayi meyasa Sultan? Bafa daga gidan banza ta fito ba yadda kake dan sarki itama haka yar sarki ce, kuma tunda ka koresu na tabbatar wata rana da kanka zaka nemo su, amma Bakomai bazan tirsasa maka sai ka dawo dasu ba, tashi kaje Allah yayi maku albarka..." tur6une fuska yayi ya amsa da Amin sannan ya mike tsaye, daga nan wajen Ummi ya shiga don yana so ya fita ne, itama dai shigen irin abubuwan da Abbi ya fada masa kusan itama shi ta fada masa, har mamaki yayi yadda akayi suka sauko lokaci daya a take jiya kamar zasu kashe Hoodah amma wai yau har sune suke cewa ya daina hantararta?

Sultan dai bai dawo gida ba sai can bayan sallar magrib, yana shiga ya iske Hoodah cikin shigar da bai taba ganin tayi ba wato riga wando na jeans sai tasa wata farar top ta shan iska, ta sa pillow gaban tv tayi rub da ciki ta dan daga kafafuwanta sama kafar nan tasha jan lalle yayi maroon gwanin ban sha'awa, gaba daya hankalinta naga tv tana kallon wani series daga gani tana jin dadin kallon da takeyi har wani smiling takeyi tana kallon, har ya taka yaje daidai inda remote yake batasani ba saida remote din ya kubce masa a hannu ya fadi ne ya tsoratar da ita ta saki wata irin kara tana juyowa sukayi ido biyu dashi, hawayen daya gani a idanunta ne ya kular dashi, abun haushin bai yi mata komai ba kawai zata fara mishi kuka daga yada remote ikon Allah! Hannunta duka biyun ya matse wuri daya sannan yasa dayan hannun nasa ya hade lips dinta na kasa da sama ya rufe su hakan ya dakakar da ita daga ihun da takeyi na tsoronshi, "Wallahi kika kuskura hawayen nan ya zubo sai kinyi regretting kuma ki zubar dasu in gani..." ya fada yana tsareta da idanu. Kallonshi takeyi cike da tsoro da kuma fargabar da bata ta6a tunanin zata ji ba a tsawon rayuwarta ba....!