Saturday, 1 July 2017

AUREN FANSA 10

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹



          🌹10 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com

"Mummy...! Mu.." A firgice suka farka daga bacci, da mamaki suka ce
"Waye?" Kasancewar d'akin gauraye yake da duhu fitila a kashe take, Daddy ya kai hannunsa ya kunna bedside lamp yana kallon Faruk dake tsaye, da sauri Faruk ya rungume mahaifiyar tasa yace.
"Alhamdulillah! Ashe duk lafiyarku lau, wallahi naji tsoro."
Mummy tayi murmushi don tasan ya k'ara yin mafarki. Tace
"Faruk nasha fad'a maka mafarki ba gaskiya bane ka daina d'aga hankalinka akan mafarki, nasha fad'a maka bakaji."
Faruk yace
"Nasani Mummy amma meyasa a duk lokacin da nayi mummunan mafarki sai naji gabana ya fad'i, sannan na kasa samun nutsuwa, gani nake kamar wani abu na shirin faruwa da mu!"
Daddy yace
"Haba Faruk! Ka zamo mai tawwakali mana, an fad'a maka mafarki ba gaskiya bane haba! Tashi kaje ka kwanta."
Sum sum ya tashi ya fice, Daddy ya kalli Reemah yace.
"Wai shin kuwa yaron nan na addu'a a duk lokacin da zai kwanta bacci?"
Reemah tace
"Yana yi, kullum sai na je na tabbatar da sai sunyi addu'a kafin su kwanta su duka."
Daddy ya numfasa yace
"To Allah ya kyauta amma sai ya k'ara dagewa da addu'a sosai."
Reemah tace
"Insha Allah."


***

           BAYAN WATA D'AYA

Zaune yake yana karatu wayarsa ta fara k'ara, ganin sunan Daddynsa yasa yayi saurin d'agawa.
"Hello kaine Faruk?"
Yace
"Eh nine lafiya ina mai wayar nan?"
"Sai dai kayi hak'uri mai wayar nan ya rasu dashi da matarsa!"
"What? Innalillahi wa'inna ilahir raj'un!"
"Ya Faruk!"
A firgice ya farka ganin Anisha tsaye gabansa tana kakkarwa, yasa yace
"Ke lafiya menene?"
Ta fashe da kuka.
"Mummy! Ya Faruk Daddy da Mummy babu."
Yace
"Kamar ya? Ina suke?"
Tace
"Wasu mutane na nan sun zagaye Mummy da Daddy..."
Kafin ta k'arasa ya mik'e da gudu ya fita."
Zuwansa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga masa hankali lokaci guda kuma ya gigice ya shiga rud'ani! Murza idanunsa ya fara yi don yayi tunanin wannna karon ma mafarki yakeyi, la6ewa ya shiga yi a bakin k'ofa yana sauraren mutanen da ke tsaye. Kusan su hud'u majiya k'arfi.
"Hello Hajiya Laila Sunusi! Aikin da kika samu fa an kammala abu biyu ya rage. Na farko bamuga yaransu guda biyu da kika lissafa mana ba! Na biyu takardun gidannan da sauran mahimman takardun da kika ce a baki."
"Yes Ma! Ok Ma! Insha Allah na miki alk'awarin cika miki dukkan aikin da kika
samu da ke da aminiyarki ya sunan ta ma? Haha yes Bilkisu Ringim! Ok..."
Kamo hannun Anisah yayi yana kuka d'akinsa ya fad'a ya kwashi wasu takardu nasa dashi dana Anisah na makarantarsa da abubuwan da yake buk'ata ya jefa jikka suka fito da sauri sukayi hanyar fita. Anisah na kuka shima yana kuka suka fito gate, gaba d'aya masu gadinsu basu nan, security sunfi goma amma yanzu bai ga kowa ba. Adaidaita ya samu suka wuce wata police station, yana zuwa ya fad'a masa dukkan abinda ya gani ya kuma ji sannan yace suzo su ceci iyayensa kafin su mutu.
Ba 6ata lokaci suka nufo gidan sai dai da zuwansu abin mamaki ba komai gidan asali ma gidan a rufe yake da kwad'o sai dai gawar iyayensa, nan akayi examining d'insu aka tabbatar da basuda rai, take Faruk ya rasa a wace duniyar yake, kansa yayi dip, hawaye kuwa kamar an bud'e pampo. Sambatu kawai yakeyi yana fad'in.
"Daman nasha yin mafarki an kashe mana iyaye! Nace abin kamar zai faru amma ba wanda ya kula ni..."
Duk police d'in da yayi yunk'urin tab'asa da niyyar rarrashi turesu yakeyi suna fad'uwa k'asa, gaba d'aya kamar ya zauce. Yama k'i nutsuwa asan ina danginsa suke a sanar masu de abinda ya faru. Gaba d'aya gidan ba mota ko d'aya, motocin mahaifinsa sunfi kala takwas amma yanzu ko d'aya babu.
Nan kuma kan Faruk ya fara juyawa kafin ya ankara ya fad'i k'asa tim!



MSB💖

No comments: