Sunday, 9 July 2017

AUREN FANSA 20

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹

Dedicated to each and every reader, you always support me, and i am grateful for that! Thanks alot!❤️

          🌹20 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com

Awa biyu tsakani ya diro cikin garin katsina, yana isa airport ya ciro wayarsa ya buga ma Meenah waya ya sanar da ita isowar tasa. Zarah bata gama shan mamaki ba sai da Meenah ta shiga kitchen don girka masa lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Coconut rice da miyar kaji, gefe kuma Russian salad ne, sai drinks kala kala. Banda su snacks da aka tanada. Goggo da k'amshi ya cika mata hanci ta fito daga d'aki ta lek'o tana fad'in.
"Kai lafiya me kuke dafawa?"
Zarah tayi dariya tace
"Ay Goggo surukinki ne zaizo, shine fa su Meenah ake ta shiri haka."
Meenah ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Goggo tayi dariya tace
"Ahh lallai kice munada babban bak'o, ay gara dai yayi yazo ko zamu huta hakan nan."
Bata gama komai ba sai da k'arfe bakwai harda rabi. Kasacewar yace mata da anyi sallar isha'i zaizo.

Tana gama wannan aikin ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin wani lace ruwan zuma (coffee brown) da light pink a jikinshi, d'inkin riga da skirt. Da taimakon Zarah ta d'aure d'ankwalin kayan irin na zamin da ake kira mai steps. Ga d'ankunne an sa kalar kayan. Tana gama fesa turare wayarta ta hau ruri da alama Faruk ya iso. A karo na farko taji ta gigice, kasancewar a yau zata ta6a fuskantar wani d'a namiji a rayuwarta da idanun soyayya. Bayan ta d'auka ya sanar da ita isowar tasa cewar yana bakin k'ofa. Ba yadda batayi da Zarah ba akan ta shigo dashi tak'i, harda zolayarta wai ay ba saurayinta bane ita. Hakan yasa ta d'auki waya ta tura masa da message akan yasa a shigo da shi bakin k'ofa (main entrance).

Tana bud'e mishi k'ofa suka bi juna da kallo mai kwantar da zuciya, kafin kuma dukkansu su saki murmushi mai d'auke da wani 6oyayyen sirri. Mamaki takeyi akan yadda yafi kyau a fili akan a hoto...
Ta kauce ta bashi hanya ya shigo, yanan sanye da shadda marar nauyi kalar sky blue sun kama jikinshi, idonshi mak'ale cikin farin glass wanda ya k'ara fito da cikar kamalarshi na cikakken namiji, wanda boko ya zauna masa sannan kud'i ma suka zauna  masa had'e da hutu, ga kuma uwa uba kyau, ba abinda ke tashi a wurin kamar k'amshin turarensa mai sanyaya zuciya.
Meenah fa tayi nisa a kallonsa yayi murmushi ya soma karkad'a mata key d'in motarsa, taji kunya sosai ta wuce ciki kanta k'asa, yabi bayanta. Suka zauna kan kujeru parlon Goggo, da k'yar ta ce
"Ya hanya? Ya kuma gajiya?"
Yayi k'awataccen murmushin dake fizge zuciya yace
"Alhamdulillah, ya gida ya hutu?"
Tayi murmushi still bata d'ago kanta ba tace
"Komai alhmdulillah, yasu Anisah?"
Yace
"Suna can lafiya lau, ina Goggo da Zarah?"
Kafin tayi magana Zarah ta fito da k'aton tray mai d'auke da lemo kala kala da cups d'in glass guda biyu. Sai data dire bisa center table d'in dake parlor sannan ta zauna suka gaisa a mutunce, yace
"Ga Zarah nan kenan? Itace sweet sister d'inki. Sannu Zarah ya kike? I've heard so much about you, gaskiya sister nan taki tana ji take."
Zarah tayi dariya
"Haka ne, nima ina ji da ita ay."
Tana gama fad'an haka ta mik'e tsaye ta fice. Ba'a juma ba kuma ta dawo d'auke da wani tray d'in mai d'auke da kuloli guda biyu, plate biyu sai kuma bowl na snacks da salad. Bayan ta dire sum sum ta fice saboda yadda taga sun kasa 6oye soyayyar da ke zuciyoyinsu a gabanta.

Ta lek'o don zuwa kitchen had'o tea, daman ita Zarah al'adarta ce duk dare sai tasha ruwan lipton (green tea) kafin ta kwanta, nan ta hango su suna cin abinci a plate d'aya, sai kuma sukayi mata kyau, kuma sun mugun dacewa da juna, abinda Faruk zai nuna ma Meenah shine haske fata don shi fari ne nesa ba kusa ba, Meenah kuwa bak'a ce (chocolate color). Suna cin abincin suna kallon juna, fatar bakinsu kuwa kad'an take motsi daga lokaci zuwa lokaci. Ta koma d'aki tana mamaki sai kace ba Meenah ba, gaba d'aya ta fad'a tarkon so.
Kafin ya tafi ya d'auko kyauta gift d'in turare da agogo ya bata, amma sam tak'i kar6a, sai da yayi da gaske har yana neman yin fushi sannan ta kar6a tana godiya sosai.

Soyayya tsakanin Meenah da Faruk kullum abin dad'a gaba yake cike da salo na ban mamaki, basu iya yini d'aya basuyi waya ba, haka ma kullum yana kan hanyar zuwa wurinta.
Tabbas zuwa yanzu soyayyar da Meenah ke ma Faruk bata misaltuwa, abin mamaki Faruk ya iya tafiyar da soyayya yadda ya kamata ya kuma son hanyoyi daban daban na yadda zai jawo hankalinta gare shi, ga yaci sa'a wannan shine karo na farko data fara sanin yadda ake soyayya, sheyasa a halin yanzu duk wanda zata so zata soshi ne da dukkan zuciya da kuma ruhinta. Faruk ya riga da ya saye zuciyarta farat d'aya, ko irin kalaman da yake furta mata kad'ai ya isa ya saye zuciyar Meenah, don haka sheysa bai sha wahalar yiwa zuciyar Meenah kamun kazar kuku ba!
Batada wani tunani sai na Faruk, batada wani ra'ayi sai nasa, sannan batada wani buri sai na mallakarsa a matsayin mijinta na abokin rayuwa na har k'arshen rayuwarta ba.



MSB💖

No comments: