Wednesday, 5 July 2017

AUREN FANSA 17

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹


Dedicated to Kiddies friends 4ever, thanks for the support you are special to me! Love you guys❤️


          🌹17 🌹


http://MaryamSBello.blogspot.com

D'aya bayan d'aya yake duba hotunan dake baje a gabansa, sai daya d'auki lokaci kad'an yana analyzing ko wanensu duk Usman yana kallonsa. Sai da ya gama sannan ya d'ago yana kallon Usman yace.
"Nagode, sai kayi min bayaninsu."
Usman ya gyara zama yace
"Yalla6ai ka duba wannan takardar na rubuta komai amma duk da haka zan maka bayani da baki.
"Da farko hotunan nan sai da nayi k'wak'waran bincike akansu kafin nazo nan."
Hoto d'aya ya d'auko ya mik'a masa.
"Wannan sunansa Alhaji Hamza Umar, haifaffan d'an garin Katsina ne kafin ayi masa transfer zuwa nan Abuja. Wannan kuma matarsa ce Hajiya Bilkisu, yaransu biyu kacal duka mata. Babbar itace Amina wadda suke kira da Meenah ga hotonta nan, sai k'aramar wadda babu wani tazara a tsakaninsu mai suna Fatima Zarah. Duk wad'annan hotunan sai da nayi bincike na gano account name d'in d'iyarsa mai suna Zarah duk a nan na kwaso hotunansu, ita Meenah a nata account d'in babu hoto ko k'wara d'aya, hartta handle d'insu yana nan a rubuce a jikin takardar.
Sai ita d'ayar mai suna Hajiya Layla ita tana Kaduna da zama da mijinta mai suna Alhaji Sambo, sai d'iyarta k'wara d'aya mai suna Yasmeen."
Gwauron numfashi Faruk ya sauke a lokaci guda kuma ya d'auko hotunan yaran nasu da akayi masa nuni dasu yana ta kallonsu yana juya hotunan. Aje hotunan kuma yayi yana kallon Usman tare da d'ora hannayensa saman table d'in yace.
"Good job, so anything else?"
Usman ya cigaba
"Yes, makaranta d'aya suke zuwa mai suna Turkish, ita babbar tana k'ok'arin kammala karatun nata ne while ita k'aramar wato Zarah tana SS2 a yanzu. Duk weekend suna zuwa Katsina wurin  mahaifiyar Hamzan mai suna Hajiya Fatima.
Idan suka je kamar misali ranar Juma'a zasu dawo ranar Lahadi, amma yanzu bincike ya nuna mani cewar sunyi akalla sati biyu basuje ba, sakamakon jarabawa da d'iyar Alhaji Hamza take shirin zanawa ta fita daga secondary.
Alhaji Hamza yakan d'auki yaranshi su fita yawon shak'awatawa duk ranar Alhamis da daddare."
Ajiyar zuciyar ya sauke yana kallon Usman ya kuma cewa
"Anything else?
"Yawwa, ka tambaya ina da ina suke zuwa, to a zahirin gaskiya yaran Alhaji Hamza basa fita yawo, daga makaranta sai islamiyya, amma daga nan basu cika zuwa ko ina ba. Amma kayi hak'uri a 6angaren Hajiya Layla sai na k'ara bincike don bansamu wani information sosai ba, na dai gano cewar tana yawan fita Dubai saro kaya."
Faruk yace
"Nagode, ka manta ka sanar dani aikin da sukeyi fa."
Usman yace
"Sorry sir, Alhaji Hamza ma'aikacin banki ne, amma matarsa bata aiki tana harkar kasuwanci, wanda naji ance tana da gidajen mai, shaguna, mall, tana da k'aton shagon saida saide, da sauransu.
Haka zalika Alhaji Sambo shi d'an kasuwa ne kuma yana aikin gwamnati."
Ya saki ajiyar zuciya yace
"Nagode da taimakon da kayi min duk da akan aikinka ne amma ni ka taimake ni ba kad'an ba, so nagode Allah saka da alkhairi."
Usman yayi dariya
"Haba yalla6ai menene na godiya? Ni keda godiya ay."
Faruk yace
"Bakomai Usman zaka iya tafiya."
Daga haka ya amsa da "To." Sannan yayi masa sallama ya fita.
Yana fita ya saki murmushin da shi kad'ai yasan mana'arsa.
Murd'a k'ofar akayi aka shigo, Najeeb ne, da murmushi Faruk yace
"Ka shigo mana."
Bayan ya zauna ne Najeeb ya soma magana
"Ka bani mamaki Faruk, ban ta6a tunanin haka daga gareka ba..."
Gaban Faruk yayi mummunan fad'uwa, yace
"Me akayi?"
Najeeb yace
"Yanzu daman abinda kake shiryawa kenan baka sanar dani ba? Inda banji me kuke cewa ba da bazaka ta6a fad'a min ba ko?"
Faruk yace
"Ko kad'an ba haka bane, naso ace sai na gama duk abinda ya kamata sai na sanar maka..."
Najeeb yace
"To tunda yanzu naji sai ka fad'a min komai."
Faruk yayi dariya yace
"Akan dai maganar nan ce ta kwanakin baya."
Najeeb yace
"Maganar iyayenka ko?"
Faruk yace
"Eh ita, so wani d'an bincike nasa aka yo mani akan mutanen kuma an kawo."
Ya k'arasa yana mik'a masa hotunan.
Najeeb ya duba bayan ya gama yace.
"Ok to menene next move naka?"
Faruk yayi murmushin nasa da ya saba yi masu ma'ana daban daban yace
"Zan sanar da kai komai, yanzu muje muyi sallah mu dawo."
Najeeb yace
"Ok muje."
A tare suka mik'e suka fice daga office d'in.


***

Yana shiga d'akin nasa ya jiyo k'amshin turaren wuta mai dad'i, ga sanyin ac gaurewa da d'akin. Yasan baya wuce aikin Jidda, don ya lura tunda suka dawo take faman d'wainiya dashi, bakin gado ya zauna ya shiga cire takalminsa da safa, bai kai ga gamawa ba ta shigo d'akin nasa, hannunta d'auke da tray d'in ruwa da lemon kwali 5alive, a d'an k'aramin table ta ajiye ta d'ago tana kallonsa cike da kunya, tace
"Sannu da zuwa yaya."
Yace
"Yawwa sannu da aiki."
Tace
"Yawwa, kana buk'atar wani abu?"
Ya d'an karkato gami da kallonta yace
"A'a nagode."
Daga haka ta fice daga d'akin a yayinda shi kuma ya fad'a toilet don watsa ruwa.


MSB💖

No comments: