✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Dedicated to Miss Hafsy and Aisha Ali Garkuwa❤️
🌹25 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Da gudu ta fad'a jikin Mama tana kuka sosai, Mama dake had'a kayan wankinta a cikin kwando ta dakata tana kallonta cike da mamaki, sannan kuma tace
"Jidda lafiyarki haka zaki shigo kina kuka? Wani abin ne ya faru?"
Ta k'ara fashewa da wani kukan har tana shasheka. Hankalin Mama ya tashi matuk'a har ta fara tunanin ko batada lafiya ne ma.
"Wai bazakiyi magana ba, ni sa'ar ki ce ina miki magana kin min shiru?"
Cikin kuka tace
"Mama ki taimake ni! Mama idan na rasa shi kamar na rasa raina ne, bazan iya rayuwa bashi ba Mama ki taimake ni Mama!"
Taci gaba da kukanta. Da mamaki Mama tace
"Waye kuma idan kika rasa shi zaki rasa ranki? Ke bakida hankali ne? Akan namiji ki zauna kina wannan kukan, ni kin ma bani haushi. Wai waye ana miki magana kin ma mutane shiru?"
"Ya Faruk ne Ma..."
Ture ta Mama tayi daga jikinta tana kallonta galala sannan tace
"Wa kika ce? Wane Faruk d'in?"
Cikin kuka tace
"Na nan gidan, naji ance aure zaiyi, ni na yarda ya had'a mu ya auremu tare da wadda yake so..."
Buge mata baki Mama tayi hakan yayi sanadiyar katsewar maganar tata, ta dafa wurin tana cigaba da kuka.
"Lallai yarinyar nan ashe bakida mutunci? Kawai sai a shiga hak'kin yaro babu dalili? Shi baice yana sonki ba haka kawai sai a takura masa, to wallahi ahir d'inki! Kar na kuma jin magana makamanciyar wannan a nan gidan, tun wuri ki fitar da Faruk daga ranki kinji na gaya miki, ashe bakida wayau bansani ba? Tashi ni ki bani wuri."
Da gudu ta fice tana kuka, tsakanin d'a da mahaifi kuma sai Allah, take tausayin Jidda ya kamata don haka sai tabi bayanta.
Rarrashinta ta shiga yi da nasiha, har ta samu tayi shiru, nan dai tayi ta kwantar mata da hankali cikin hikima da dabara.
***
Ranar Juma'a magabatan Faruk suka gabatar da komai na auren d'annasu. Duk wata dukiya da ake buk'ata ta aure da kuma al'ada sun gabatar tare da sadakinsu. Bayan kammala komai aka saka bikin wata d'aya saboda Baba ya buk'aci hakan, don yace yafi so ta fara karatu a d'akin mijinta.
Bayan Sati biyu da hakan kuma suka kawo lefe saitin akwati/jaka takwas da kit. Akwatinan sunyi kyau kalar purple.
Yanzu bikin ya rage saura sati biyu kenan.
To daga nan kuma aka cigaba da shirye shiryen biki, tun daga kan su dilka, gyaran gashi Baba ne yasa aka d'auko ta daga maiduguri mai suna Salima. Matar ta k'ware a gyaren jiki da gyaran amarya. Kwanan ta d'aya amma Meenah ta fara murjewa, ko wucewa tayi sai k'amshin jikinta ya bugo mutum.
Kayan d'aki kuwa Baba daga dubai yasa akayi mata order, gado set biyu masu matuk'ar tsada da kyau, sai set d'in kujeru suma biyu, kayan dining da kitchen ma duka a can akayi order komai da komai. Don Baba a shirye yake don nuna ma Meenah gata.
Hartta katin d'aurin aure daga dubai d'in aka bugo su, sheyasa ya fita daban ko kallon shi kayi kasan ya had'u!
Tun ana saura sati d'aya bikin Baba ya tafi Katsina ya d'auko Goggo. Nan itama aka fara hidimar biki da ita.
A 6angaren ango shima shiri sukeyi sosai, don su mutum hud'u ake ma biki, da Faruk da Najeeb da Yusra, sai Anisah, Nabeel da Jidda suka rage kasancewar basu fiddo wad'anda suke so ba. Don haka gidan ya kacame da hidima ba kad'an ba.
Events d'in da Meenah zatayi kamu ne kawai tasa sai yinin biki, sai d'aurin aure sai walima sai kai amarya sai ango zasuyi dinner shikenan.
Tun ana saura sati d'aya aka fara jere a unguwar Aso Villa, manyan gidaje ne jere guda uku amma kowa da katangarsa haka ma kowa da gate d'insa, babban gida ne ba laifi don yana da wadatar fili, gidan dai yaji shuka banda carpet grass dake shimfid'e a k'asa, ginin zamani mai d'auke da parlor biyu, d'akuna uku, kitchen da dinning. Gidan yayi sai dai fatan Allah basu zaman lafiya!
Ranar laraba ta kama ranar da ake ma Meenah k'unshi, nan fa aka zauna daga can garden aka shiga yaryara mata k'unshi. Sai wata kuma daban tana ma 'yan matan amarya da sauransu.
Ranar alhamis ranar da ake kamu k'arfe hud'u za'a fara a gama k'arfe shidda.
Amarya tayi shiri cikin ja da silver bridal gown wanda ya amshe ta ya kuma yi mata kyau! A yayinda da Zarah suke sanye cikin ashobi pink da black.
Bayan an gama shiri aka rufe mata fuska suka tafi wurin kamu.
Nan kuma aka shiga gabatar da kamun yadda ya kamata, tun a wurin kuma Nabeel yake ma Zarah wani irin kallon da har sai da ta tsargu, shikam tunda ya ganta yaji ta masa. Anyi taro lafiya, ansha hotuna. K'arfe shidda daidai aka kammala aka watse.
Bilki anata fama da jama'a, 'yan uwa, mak'ota, abokan arzik'i, 'yan cin arzik'i, da kuma k'awayenta don haka ko tana cikin 6acin rai ma bazaka gane ba. Hidima tasha kanta, gidanta a cike yake taf ba matsaka tsinke. Hartta dai Hajiya Laila da d'iyarta sunzo tun ana saura kwana biyu bikin.
Nabeel dai ya kasa hak'uri ya sanar da Najeeb yana son k'anwar Meenah, aiko yaji dad'in haka. Don haka ya sanar da Faruk, Faruk ya sanar da Meenah ita kuma Meenah ta tuntu6i 'yar uwarta taji ta bakinta. Batayi saurin amincewa ba sai daga baya, take kuwa suka kar6i number juna yanzu har sun fara gaisawa ta waya!
Ranar juma'a cikin garin Abuja dubban mutane suka shaida auren FARUK ADAM DA AMINATU HAMZA, NAJEEB DA ANISAH, YUSRA DA SADIQ.
Daga nan angwaye suka zarce walima a guest house d'in Dada dake can Asokoro.
Washe gari akayi wunin biki, tun safe jikin Meenah ya fara yin sanyi kuma, ko abinci tak'i ci, jinta take kamar wata marar lafiya. Gashi Bilki bata damu ba bare kuma ta tilasta mata taci. Zarah keta lalla6a ta har dai ta samu tasha ruwan tea.
Haka aka cigaba da gudanar da wunin biki cike da kwanciyar hankali.
K'arfe takwas na dare motocin d'aukar amarya suka iso.
Tun a sannan Meenah ta fara kuka, tun tana ganin zata rabu da 'yar uwarta sai kuma hankalinta ya tashi sosai. Take suka rungume juna suna ta kuka mai ban tausayi.
Da k'yar wata daga dangin Faruk ta janyota, bayan an kaita parlon Baba take kuma ta fara sabon kuka, shi kansa Baban idanunsa sunyi ja, su Goggo da Bilkin duk suna zaune a wurin, nan aka shiga mata nasiha mai ratsa jini da jijiyoyi, kuka kawai take, suka sassaka mata albarka da fatan zaman lafiya, sannan aka jawo ta wajen mota ana ta rangad'a mata gud'a. A kan hanyarsu ta zuwa hankalin Meenah yayi matuk'ar tashi, tunda zataje inda bata sani ba, bata ta6a rayuwa a ciki ba, zuwa cikin rukunin sabuwar rayuwa mai cike da garari, dad'i ko akasin haka....
MSB💖
No comments:
Post a Comment