Friday, 21 July 2017

AUREN FANSA 26

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹



          🌹26 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com

Bayan an kawo amarya masu ganin gida suka gama gani tare da fatan alkhairi, sai kuma suka soma tafiya, nan kuma aka bar 'yan matan amarya wad'anda zasu kwana saboda gobe walima.
Haka kuwa akayi washe gari aka gudanar da walima, aka k'are lafiya, bayan an gama aka maido amare gidanjensu, nan kuma su Zarah suka taya ta zama har dare haka sukayi jugum babu mai cewa uffan. K'arfe takwas, tara, goma har da rabi shiru babu ango babu alamarshi. Ganin sha d'aya saura yasa Zarah cewa.
Gaskiya nikam na gaji da zaman jiran ango Meenah."
D'aya daga cikin cousins d'in su Meenah mai suna Khadija tace
"Abinda za'ayi ko idan sunzo ki kar6a mana kud'inmu zan dawo gobe in amsa har ma da sauran kazar da kuka rage ta amarci."
Wannan karon Zarah bata tanka ba don takaicin rashin zuwan ango akan lokaci, haka sukayi ta mata bankwana suka bar gidan. Tayi shiru tana tunanin abinda ya hana shi zuwa har wannan lokacin, tayi tagumi. Har kusan sha biyu saura shiru, ta gaji ta yaye lullu6in tayi zaune ta zurfafa cikin tunanin babu ango babu alamarshi.
Gyangyad'i ta fara yi tun tana yi sama sama har ta kusa 6ingirewa k'asa. A tunaninta idan ta farka zata ganshi kan gadonta sai dai wayam ta ganta ita kad'ai.
Ta mik'e ta sauya kayan bacci ta duba agogo k'arfe 1:36am. Ta koma kan gadon ta kwanta cike da fargaba, sai kuma ta mik'e tana tunanin ko lafiyarsa k'alau don abin ya fara bata tsoro.
Wayarta ta d'auko ta kirasa amma abin mamaki wayarsa a kashe! Ta dafe k'irji tare da d'ora kanta bisa pillow tayi lamo. Can bacci 6arawo ya sace ta, a tunaninta zata farka ta ganshi ya dawo amma abin mamaki babu alamarshi. Ta duba agogo 4:50am, a sanyaye ta shiga toilet ta d'auro alwala tayi sallah. Sai da gari ya d'an fara haske ta fito don ta duba ina angonnata kuma taji dalilin da ya hanashi zuwa da daddare.
Bata san kan gidan ba haka tayi ta shiga tana fita amma ba alamun mutum a gidan. Ta cika da tsoro haka ta koma d'akinta tana tunanin ko ba'a gidan ya kwana ba?
Wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin ash material doguwar riga ta d'aura d'ankwalin kayan ta hau gado ta kwanta tare da lumshe idanu tana k'ok'arin tunanin meya faru da angonta haka har ya hana shi zuwa gareta duk da kuwa yana zakwad'in zuwan wannan rana.

K'arfe sha d'aya aka soma bubbuga gidan, ta mik'e ta fito har bakin k'ofa tare bud'ewa.
"Ina kwana?" Ta fad'a gami da kawar da fuskarta gefe.
"Lafiya lau, Bismillah."
Bata tanka ba kawai tabi ta gefenta ta wuce tana k'ok'arin had'iye kishinta.
Parlor suka zauna sannan tace
"Sunana Jidda, ni k'anwar Faruk ce abinci ne aka bada a kawo muku daga gida."
Ta fad'a tana matsar mata da kwandon gabanta. Meenah tayi murmushi
"Allah sarki, mungode Allah saka da alkhairi."
Tayi yak'e tace
"Babu komai, ina yayan ko bai tashi ba?"
Ta hau inda inda.
"Eh... a'a ya tashi ya shiga wanka."
Jidda ta sunkuyar da kanta k'asa tace
"Allah sarki ni zan wuce ki gaishe shi idan ya fito."
Meenah tayi murmushi tace
"Zaiji insha Allah a gaida Mama."
"Zataji." Ta fice.
Bud'e kular ta soma yi, soyayyar doya ce da k'wai da pepper soup sai k'osai da kunu.
Kasa cin abincin tayi don rashin zuwan Faruk gareta ya mata zafi duk da kuwa har yanzu batasan dalilin rashin zuwan nasa ba. Bata buk'atar komai a halin yanzu sai son ganin Faruk da kuma son jin dalilin da ya hana shi zuwa.
Ganin tunanin bazai mata ba yasa ta jawo kular abincin ta soma ci, kasa ci ma tayi sai kawai ta zuba kunun tasha ta koma kan gado.
Wayarta ta d'auko ta k'ara kiransa wannan karon a kunne taji ta amma har ta tsinke ba'a d'auka ba. k'walla suka cika mata ido, lallai al'amarin mai girma ne.

Sai da tayi kwana biyu a na ukkun ne taji alamar shigowar mota, da sauri ta lek'a shi d'inne yana sanye da suit kalar toka da wando kalar tokar shima.
K'in fitowa tayi don tana tsananin fushi da shi. Tana zaune taji alamun bud'e k'ofa, da alama d'akinsa ya shiga. Sai da ya d'auki akalla minti talatin sannan taji alamun fitowa, da sauri ta kwanta gami da rufe idonta kamar mai bacci.  Bud'e k'ofar d'akin yayi yana tsaye yana k'are mata kallo, daurewa yayi ya tako har bakin gadon gami da zama kusa da ita.
"My baby..."
Ko motsi batayi ba bare yasa ran zata amsa. Kamo hannuwanta yayi yana murza su a hankali cikin salo na k'warewa, bugun k'irjinta ya k'aru.
"Haba my baby shirunki yana iya haifar min da matsala babba idan baki amsa ni ba, kinji my baby please ki tashi kiji abinda zan fad'a miki."
Tsananin son da take masa shi ya hana ta yi masa musu, tashi zaune tayi fuskarta kuwa kamar an mata albishir da gidan wuta.
"Nasan ban kyauta miki ba, amma kiyi hak'uri babban dalili ne yasa kika ga ban zo ba a ranar da aka kawo ki..."
Ta kalle shi idanunta cike da kwalla tace
"Wane dalili ne ya hana ka zuwa? Wane dalili ne ya hanaka zuwa gareni duk da kuwa yadda kake zakwad'in zuwan wannan rana! Wane dalili ne yasa ka mance dani har kak'i d'aukar wayata a lokacin da nake nemanka? Wane dalili ne yasa a daren da aka kawo ni ka mance dani ka maida ni dani da bola duk d'aya suke a wurinka? Wane dalili ne ya hanaka kwana a gidanka ranar dana fara takowa a gidanka? Wane dalili ne...?"
Toshe mata baki yayi da hannunsa yana girgiza mata kai, take hawayen da take rik'ewa suka yi nasarar saukowa, sannan ta bishi da kallo na ina jiran amsa.
"Don Allah ya isa haka my baby, wallahi ba laifina bane, Dada ne bashida lafiya dole tasa muka tafi wurinsa..."
Ta girgiza kanta.
"Dada bashida lafiya meyasa da jidda tazo rannan da safe ta kasa sanar dani hakan, har tambayarka tayi ko kana ciki? Ta yaya mahaifinta bashi da lafiya ta kasa sani?"
Take ya hau inda inda.
"Eh ay ko ita kanta bata sani ba saboda bata gidan, amma banyi tsammani zaki zarge ni da yin k'arya ba Meenah."
Ya k'arasa yana k'ak'alo hawaye. Hankalinta ya tashi tace
"Ko kusa ba haka bane, na yarda da kai my soul, amma ka gane duk abinda ya shafe ka nima ya shafe ni, daka sanar dani ko addu'a dana yi masa, Allah ya bashi lafiya."
Yayi murmushi
"Yawwa my baby ko kefa? To yi murmushi mana."
Ya fad'a cike da shagwa6a, hakan ya bata dariya sosai. Kamo ta yayi yana fad'in.
"Zo muje na siyo maki abin dad'i."
Tayi murmushi suka fice.


***

Da misalin k'arfe 8:35pm yayi sallama, Dada na aiki a laptop nasa ya dakata gami da amsa sallamar sannan yayi murmushi.
"Ahh Faruk kaine tafe? Shigo mana."
Faruk ya shigo bayan ya zauna yace
"Dada an wuni lafiya?"
Yace
"Lafiya lau ya iyalin naka da fatan tana lafiya?"
Yace
"Lafiya lau Dada daman wurinka nazo."
Ya dube shi kafin ya cire gilashin dake idonsa na karatu yace
"To gani lafiya dai?"
Faruk ya sunkuyar da kai tukunna yace.
"Dada daman so nake na nemi izini wurinka zan k'ara aure."
A razane Dada ya dube shi gami da gyara zama yace
"Aure fa kace Faruk? Aurenku da ko sati ba'ayi ba sai kace zaka k'ara aure? Kaima kasan hakan bazai yiwu ba. Tukunna ma wacece zaka aura?"
Ya sukuyar da kai
"Dada daman Jidda ce..."
"Ban lamunta ba! Idan ma mafarki kakeyi to ka farka!"
Mama ta fad'a tana tsaye a bakin k'ofa daga ganinta kasan tana cikin 6acin rai.


MSB💖

No comments: