Wednesday, 26 July 2017

AUREN FANSA 29

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹

Dedicated to Anty Zee and AishatFareeda❤️ nagode da k'auna😍

          🌹29 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com

Bayan ya gama shirinsa yayi breakfast sai ya fara k'ok'arin fita, ba yadda Meenah batayi dashi ba akan ya hak'ura a gama ruwannan yak'iya yace aikin da zaiyi yana da mahimmanci sosai. Haka nan ya d'auki umbrella ya fice cikin ruwannan.
Bayan ya fita kuma ta hau aikin gida kamar kullum, ta kimtsa ko ina ta turara gidan da tuararen wuta ta bi da freshener ta fesa ko ina. Tayi kalacinta bayan ta gama tayi wanka ta shirya cikin wani simple lace kalar sararin samaniya (sky blue) da pink. Tana shirin d'aura d'ankwali wayarta ta fara ringing, ganin Zarah yasa tayi murmushi ta kara a kunne.
"Assalamu Alaikum..."
Zarah tayi murmushi
"Wa'alaikumusalam, ya kike?"
Meenah tace
"Uhm bansani ba bayan kin manta dani ma."
Zarah ta d'anyi dariya tace
"Haba sis, ni na isa ne? Gani nayi bai kamata na takura miki ba nasan kina can kina cin amarci yadda ya kamata, ba kya buk'atar takura..."
"To aku sarkin magana ya isa haka, ya garin ya su Mami?"
Tace
"Suna nan lafiya, daman kiranki nayi naji idan kina gida zan biyo, daga school nake ance admission ya fito shine naje na dubo mana..."
Cike da murna Meenah tace
"Haba don Allah? Munci?"
Zarah tayi dariya tace
"Oho sai nazo dai, amma ina fatan ango baya gida don wallahi idan yana nan zan wuce gida kawai."
"Haba mana Zarah wallahi baya nan kizo ina kewarki da yawa."
Zarah tayi murmushi
"Nima haka sai nazo."
Da haka sukayi sallama.


Minti sha biyar tsakani Zarah ta iso, rungume juna sukayi suna murna, Meenah ba k'aramin dad'in ganin Zarah tayi ba. Can ta shiga kawo mata kayan motsa baki su lemo da cake, su dambun nama da sauransu. Meenah tayi murmushi tace
"La Zarah kinga yadda kika jik'e kuwa? Meyasa kika fito cikin ruwa? Ki shiga d'akina ki cire wad'annan kayan ki saka nawa."
Tace "Tab kayanki sun mani kad'an ay."
Meenah tace
"Inji waye? Akwai wanda sukayi min yawa ay."
Zarah tace
"To."
Tunda Zarah tazo take bin Meenah da kallo, har dai Meenar ta tsargu a lokacin da take tsiyaya mata lemo a cikin glass cup, bayan ta gama ta koma ta zauna tana kallon Zarah tace
"Wai lafiya kike min wannan irin kallon haka?"
Zarah ta zuba mata idanu, kafin kuma ta saki ajiyar zuciya tace
"Meenah gani nayi kin rame sosai, akwai abinda ke damunki ne?"
Meenah tayi murmushin da bai kai zuci ba tace
"Babu komai me kika gani?"
Zarah tace
"Haba Meenah, tsawon shekarun da muka d'auka tare da ke nasanki, nasan idan kina cikin matsala ko akasin haka, kuma a matsayina na k'anwarki bai kamata ki 6oye min abinda ke ranki ba Meenah."
Meenah taja ajiyar zuciya tace
"Hakane, bawai na 6oye miki abinda ke raina bane, kawai abinda zan fad'a ne nasan zai rud'a ki had'e da mamaki marar misaltuwa."
Da mamaki Zarah tace
"Niko zanso inji menene wannan da zai rud'a ni haka zai kuma bani mamaki."
Meenah tace
"Uhm bari kedai, to ki nutsu kar ki rud'e dan Allah Zarah, to ba komai bane ba illa wai Faruk zai k'ara aure..."
Lemon da ta kai bakinta shi yayi sanadiyyar k'warewar da tayi hakan yasa ta dinga tari, da k'yar Meenah ta dinga bata ruwa har tarin ya tsaya tana ta faman yi mata sannu.
Sai da ta nutsu Zarah tace
"Wai wane Faruk d'in tukunna Meenah?"
Meenah ta d'anyi dariya tace
"Akwai wani Faruk da kika sani bayan mijina ne? Shi dai nake nufi Faruk da na aura a matsayin mijina to shine zai k'ara aure."
Salati Zarah ta shiga yi cikin tashin hankali sannan tace
"Faruk dai your soul Meenah? Wai aura fa kika ce? To kuma shine kika zauna kamar baki damu ba?"
Meenah tayi murmushi
"To ya kikeso inyi? Kashe kaina zanyi ne? Abinda Allah ya kaddara waya isa ya hana? Nidai na rungumi kaddara kuma ina fatan wadda zai aura mutuniyar kirki ce, sannan ina fatan bada tashin hankali zata shigo min ba, amma nidai idan mijina na sona banida matsala."
Zarah nata kallonta tana magana cike da mamaki, sai data gama Zarah tace
"Lallai an gaishe ki Meenah, kinyi k'ok'ari sosai, ba kowace mace bace zatayi abinda kikayi ba, ni gaskiya inda nice bazan yarda ba, sai anyi tashin hankali ba kad'an ba, tab kishiya fa lallai!"
Meenah tayi dariya.
"To Allah ya kyauta dai, kedai kiyi ta addu'a Allah ya baki miji na gari shine kawai.
Wai shin ina Nabeel kuna ta shan soyayya ko? Kuma yana zuwa zance ko kuwa?"
Zarah tayi dariya
"Han! Kin cika ni da tambaya wane zan fara amsawa?"
Suka d'ara su duka, Meenah tace
"Duka zaki amsa mana."
Zarah tayi murmushi mai bayyan hak'ora tace
"To Nabeel yana nan lafiya lau, yana ta zuwa wurina and kuma Baba yace ya turo iyayensa."
Cike da murna Meenah tace
"Masha Allah! Allah ya tabbatar da alkhairi Zarah."
Tace
"Amin... yauwa Meenah ina za'a samu mai aiki?"
Meenah tace
"Mai aiki kuma? Me za'ayi da ita?"
Zarah tace
"Mami mana, ta matsa ita 'yar aiki takeso, wai gwara ta samo don idan nayi aure nima babu kowa gidan."
Meenah tace
"To kin ta6a ganin na samo masu aiki ne? Amma zan tambayi Faruk ko yasan inda ake samu."
Zarah tace
"Yauwa nagode, batun result naga sunayenmu sun baki Business admin ni kuma Biology."
Cike da murna Meenah tace
"Alhamdulillah, kin anso admission letter?"
Zarah tace
"No sunce sai next week, so zamuje sai muyi registration."
Nan sukayi ta murna marar misaltuwa.
Kafin Zarah ta tafi sai da ta taya Meenah tayi abincin rana, shinkafa da miya sukayi da salad. Bayan sun kammala Zarah ta fara shirin tafiya. Nan sukayi bankwana akan Meenah zatazo gida ta gaida su Baba, Zarah kuma ta tuna mata batun mai aiki.


***

Tarin takardu ne da laptop a gabansa ya tasa gaba yana kallo, amma a zahiri hankalinsa baya wurin idonsa ne kawai ke kan takardun, tunanin Meenah yasa shi a gaba ya hana shi sak'at har ma ya rasa inda zai sa kansa. B'angare d'aya na zuciyarsa yana tunani akan yadda zai cimma burinsa, d'ayan 6angaren kuwa, Meenah ce tayi masa tsaye a rai duk yadda yaso yakice ta daga ransa abin yaci tura. Sai ma dad'a gaba abin yakeyi.
K'wank'wasa k'ofar akayi, ya bada izini aka shigo, matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru ashirin da biyar (25) a duniya, suna kiranta da young detective, saboda sabuwar shiga ce sannan gata yarinya.
"Sir wai kana nema na ko?"
Yace
"Yes ina nemanki, bismillah."
Tace
"Ok sir."
Bayan ta zauna ne yace
"Wani taimako zakiyi min Hajir, amma kafin nan bari na baki labarin komai tukunna."
Nan ya shiga bata labari tun daga farko har k'arshe sannan yace
"To yanzu kinji inda nakeson focusing, ina so kije kiyi tunani nima zanyi tunanin hanyar da zamu dinga samun information daga gidan, da naso muyi magana sosai but gaskiya na gaji kuma bana d'an jin dad'in jikina, so zan tafi."
Ya duba tima k'arfe 3:47pm. Yace
"La'asar ta kusa, zan je masallaci idan na tashi daga nan, sai na wuce gida, zuwa gobe idan nazo zamuyi magana."
Tace
"Insha Allah."
Yace
"Ya batun case d'innan da akayi assigning d'inki kin gama shi kuwa?"
Tace
"Na gama amma case d'in ya bamu wahala sosai, sai dai cikin ikon Allah munyi succeeding."
Yace
"Haka ake so ay, nima akwai cases masu bani wahala amma da mutum ya sa confidence a ransa da kuma jajircewa akan aikin sai kiga komai ya tafi yadda ake so."
Tace
"Haka ne."
Ya mik'e ya soma tattara komatsansa cikin briefcase yace
"Hajir zaki iya tafiya, sai goben insha Allah."
Tace
"To sir Allah ya kaimu."
Yace
"Amin."
Daga haka ta fice a yayinda ya kammala kimtsa kayansa sannan ya fice daga office d'in....


MSB💖

No comments: