✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹30🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Mairo Gafai Allah ya baki lafiya yasa anyi a sa'a😍
Daga d'an nesa yakejin kamar ana k'wala masa kira, hakan ya dakatar dashi daga bud'e motarsa da yakeyi. Hango Najeeb yayi yana k'arasowa cikin d'an gudu gudu, tun daga nesa yake hango sa kamar yana cikin damuwa. Sai da ya k'araso dab da shi sannan Najeeb yace
"Wai tafiya zakayi da wuri haka? Wurinka nazo fa."
Faruk yace
"To, kuma gashi har na rufe office zan wuce gida, amma idan maganar batada tsawo mu shiga daga ciki."
Najeeb yace
"No batada wani tsawo sosai, no need ma mu shiga daga ciki muna iya tsayawa a nan."
Faruk yace
"Ok kafin nan ya gida ya k'anwata da fatan ana kula min da ita sosai?"
Najeeb yace
"Haba mana kai kason yadda nakeson Anisah ay, dole ma na kula da ita. Yawwa wata magana nake ji daga gida cewar zaka k'ara aure, shin gaskiya ne ko ba gaskiya bane ba?"
Faruk yace
"Wannan magana gaskiya ne, haka take."
Najeeb yace
"Amma ka bani mamaki Faruk, ta yaya zaka k'ara aure yanzu? Daga yin aurenku, baka bari nan gaba kad'an idan ma zaka k'ara sai ka k'ara. Haba Faruk..."
Faruk yayi murmushi yace
"Najeeb kenan, gani nayi fa ba haramun bane k'ara aurennan, sannan ba wata bare bace zan aura 'yar gida ce."
Najeeb yace
"Nasani mana, amma baka ganin Jidda bata dace da kai ba?"
Faruk sai ya kama dariya yace
"Ta yaya?"
Najeeb yace
"Haba Faruk, yarinyar nan kasani sarai batajin magana, kullum cikin yawo take, gata ta tara k'awaye a gida, baka ganin yadda su Dada ke fama da ita? Kai baka tunanin ta zame maka matsala a gidanka da kai da iyalinka nan gaba? Kuna zaman lafiya kaje ka jajibo ma kanka masifa har gida...?"
"Wa'iyazubillahi! Haba Najeeb ka daina kira min masifa a gida, insha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi. Kuma da kake batun Jidda bataji zan gyara ta, kai kanka zakayi mamaki."
Najeeb ya kad'a kafad'a alamun oho yace
"Well it's your choice not mine, don't say I didn't warn you to."
Faruk yace
"Yawwa kuma nagode da shawara, zamu iya tafiya?"
Najeeb yace
"Of course, ni zan tafi sai anjima a gaida gida."
***
A gajiye ya shigo gidan, tana zaune kan kujera ta zaman mutum uku, hannunta rik'e da remote tana chanza channel d'in da take muradin kallo.
Tunda ya shigo yake binta da ido, a tsawon rayuwarsa bai ta6a ganin Meenah cikin irin wannan ado haka ba.
Wani dark blue leshi ne a jikinta mai yarfin golding, ga wasu duwatsu dake rauraya daga gaban rigar, d'inkin an mata wanda ake cema da peplum sai skirt da ya kamata, d'aurin d'ankwalin kuwa kamar don ita akayi shi, tana sanye da 'yan kunne da sark'a kalar kayanta, yadda kasan wata matar shugaban k'asa ko wani gwamna saboda yanayin shigarta ya nuna hakan. K'amshin gidan ya had'u ya gauraye dana sanyin ac, hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba.
Bata ankara ba sai ganin mutum tayi tsaye a gabanta, murmushi ta sakar masa mai saurin fizge zuciya a yayinda ya mayar mata ba 6ata lokaci, sannan kuma ta tashi a hankali ta k'araso inda yake tana mai tafiya cike da nutsuwa. Shi dai yana tsaye yana binta da idanu, ta amshi briefcase d'insa tare da kama hannunsa tace
"My soul lafiya ka dawo da wuri haka?"
Ya dube ta cikin kulawa yace
"Wallahi kuwa na gaji ne, sannan yau bawani aiki sosai."
Tace
"Ok muje kayi wanka ko abinci zaka fara ci?"
Ya girgiza kansa alamun a'a yace
"Bari inyi wankan dai zai fi, sai inci abincin daga baya."
Hannunsa take ja yana biye da ita har d'akinsa sannan ta shiga ta had'a masa ruwan wanka kamar kullum, bayan ta fito ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa, sannan ta fice ta bashi wuri ya kimtsa.
Bayan sun gama cin abinci ne suna zaune a parlor suna hutawa Meenah ta soma magana.
"My soul don Allah na tambaye ka?"
Ya gyara zamansa yana fuskantarta yace
"Eh Allah yasa nasani."
Tayi murmushi tace
"Daman... nace ina kake ganin za'a samu 'yar aiki?"
Yace
" 'Yar aiki kuma? Me za'ayi da ita?"
Tace
"Mami daman keso, ni bansan inda ake samu ba shine nace bari na tambaye ka."
Hajir ta fad'o masa a rai, take kuma ya fara murmushi ganin wata dama ta samu da zaiyi amfani da ita kuma bazai bari ta wuce shi ba. Sai yayi saurin cewa.
"Haba indan wannan ne kar ki damu, Mama na da masu aiki, so samowa bazaiyi wahala ba, zan mata magana."
Cike da jin dad'i tace
"Kai nagode sosai my soul."
Ya d'an tsunkuli gefen kumatunta yace
"Anything for my baby."
****
Washe gari a office yasa aka kira masa Hajir, tana zuwa yace ta zauna, bayan ta zauna ya soma magana.
"Kamar yadda nayi miki bayani jiya zamuyi magana, to shine yanzu zan miki bayani. Da farko wani aiki zakiyi min, sannan don Allah ina buka'atar had'in kanki Hajir."
Hajir tayi dariya
"Insha Allah sir."
Yaji dad'i yace
"Da farko ina so ki chanza identity d'inki gaba d'aya."
Cikin rashin fahimta tace
"Bangane ba?"
Yayi ajiyar zuciya yace
"Ma'ana ina so ki tashi daga Hajir, 'yar gayu, mai ilimi, mai kud'i ki koma Atika bak'auya, marar ilimi, marar kud'i sannan kuma 'yar k'auye sannan Atika 'yar aiki, amma kar ki damu aikin naki bazai dad'e ba, sannan zansa a linka miki albashinki fiye da yadda ake baki."
Da mamaki tace
"Naji bayaninka, amma zan iya sanin dalili?"
Yace
"Yawwa, dalili kuwa shine, information nake buk'ata daga wurinki dangane da labarin dana baki jiya, dangane da mutuwar iyaye na. Abinda nake so dake zakije a matsayin 'yar aiki. So aikinki yana buk'atar hak'uri, dauriya, jajircewa, da fatan kin fahimta?"
Tace
"Na fahimta sir, kuma insha Allah baza'a samu matsala ba. Na farko taimako zanyi, duk da ban ta6a cin karo da aiki irin haka ba, amma na maka alk'awarin zaka same ni mai cika alk'awari. Sannan insha Allah zaka same ni mai hak'uri da kuma dauriya."
Yaji dad'i sosai ya cigaba
"Alhamdulillah, da farko zan d'an baki wasu kud'i kije kasuwa ki siyo 'yan atamfofi ki kai ayi miki d'inkin 'yan k'auye, sai ayi ta wanke su har su k'ok'e, daman ba masu tsada bane hakan bazaiyi wahala ba. Na biyu idan kin zama ready sai ki sanar dani sai nasa a kaiki inda zaki fara aikin. Na uku duk wani abu da kikaji ya zamanto kin rubuta shi inda hali ma ki mani vnote, ko kiyi duka biyun. Sannan zan siya miki k'aramar waya marar tsada ki saka sabon sim card yadda bawanda ya sanki da layin don kar a samu matsala. Aikinnan Hajir yana buk'atar lura da sa ido, ko wane motsi nata akanki, duk abinda kikaji ki rubuta ki kuma yi recording. Da munsamu muka had'a duk wani information da zamu buk'ata shikenan, sai na fad'a miki yadda za'ayi. Kar kiyi wani abu da zata gane ke ba 'yar k'auye bace, kar ki kuskura ki nuna kin iya turanci, kuma ki mata biyayya duk abinda ta saki kiyi. Shine kawai abinda nake buk'ata a wurinki."
Ta saki ajiyar zuciya tace
"Tabbas bazan baka kunya ba sir, insha Allah na maka alk'awarin taimaka maka wurin gano abinda kakeson ganowa, yanzu dana tashi daga nan zan wuce kasuwa sai na siyo abubuwan da nake buk'ata, ka bani nan da kwana biyu, zan zo sai ka kaini wurin aikin."
Yayi murmushi mai bayyana hak'ora yace
"Kai naji dad'i sosai wallahi, Allah ya bada sa'a, zan rik'a turo maki da kati lokaci zuwa lokaci, duk sadda kike buk'atar wani abu sai ki kirani. Ki tafi da babbar wayarki saboda recording d'in sai ya zamana kin 6oye ta yadda baza'a gane ta ba. Sai ki rik'a fiddo k'aramar kina amfani da ita. To make it more successful zaki iya rik'ayin wayar k'arya kamar kina kiran iyayenki kuna gaisawa a can k'auye."
Tace
"Babu matsala insha Allah."
Yace
"Yawwa."
Nan ya fiddo cheque ya rubuta mata kud'i masu tsoka sannan yayi mata godiya ta tafi.
MSB💖
No comments:
Post a Comment