✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹23 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Baba yayi murmushi yana dubansa yace.
"Faruk ka saki jikinka dani mana, ka d'auke ni a matsayin mahaifinka, ka bani amsar tambayar da nayi maka."
Ya daure yace
"Da...dama Baba, dama... dama... ina so mu lokaci ne, sannan na gabatar maka da kaina a cikin manaiman auren Meenah, duk da dai tace min batada wanda ta tsada, to amma... amma mun daidaita kanmu."
Baba yayi murmushi gami da lumshe idanu na 'yan mintina, sannan ya bud'e su a hankali kan Faruk.
"Haka ne, Meenah batada wanda ta tsaida, hasali ma kai ne mutum na farko da ta ta6a yin soyayya da shi, sai dai wani hanzari ba gudu ba, kafin na amince maka da auren Meenah, ina so kayi min alk'awarin rik'e ta bisa amana da gaskiya, kar ka ci amanarta kar ka yaudare ta, shine kawai abinda nake buk'ata daga gare ka. Duk da nasan dai mahaifinka mutumin kirki ne kuma ina da tabbacin tarbiyarsa gareku, kuma ina masa addu'a Allah ya jik'ansu da gafara."
Yace
"Amin Baba, indai wannan ne kar kayi haufi a kaina insha Allah babu matsala."
Baba yayi murmushin jin dad'i yace
"Alhamdulillah, amma kuma ina so ka bari in tuntu6i yarinyar tukunna inji ta bakinta, nafiso na tabbatar sai a sanar da kai don ka turo magabatan naka." Faruk yayi murmushi.
Yace
"To Baba babu damuwa insha Allah."
Baba yayi murmushi gami da mik'ewa tsaye.
Yace
"Kana iya tafiya Allah yayi muku albarka. Ya amsa da "Amin."
Baba ya yi gaba, Faruk yabi bayansa yana jinjina al'amarin.
***
Abu k'arami na neman zama babba, tun tana ganin abin kamar wasa ta fara ganinshi babba. Cikin k'ank'anin lokaci Jidda ta fahimci Faruk soyayya yake, kuma wacce yake so d'in ta kame masa zuciya farat d'aya, duk wani observation nata akan Faruk ta gama gane komai, tausayin kanta ya kama ta. Anisah ce ta shigo d'akin tana tsaye a bakin k'ofa ta k'ura ma Jidda idanu, hannunta d'aya d'auke da cup d'in tea d'ayan kuma yana rik'e da wayarta k'irar Samsung galaxy S6, a hankali ta k'araso ciki tana murmushi. Zama tayi kan gadon da Jiddar ke zaune a kai ta dafa ta.
"Yaya Jidda..."
Firgit! Ta dawo daga duniyar tunani tana kallon Anisah, sai kawai ta k'ak'alo murmushin dole. Anisah tayi murmushi.
Meyake damunki?"
Tayi tsai kamar mai tunani kafin tace
"Babu komai."
Anisah ta girgiza kanta.
"Sam ban yarda ba yaya Jidda, na dad'e da ganin chanzawarki, gaba d'aya kin bi kin sussuce kin zama wata iri? Har Mama ta soma tambayarmu abinda akayi miki,a gaskiya yaya Jidda koma meyake damunki ki fito fili ki fad'a mana, k'ila da akwai taimakon da zamuyi miki..."
Har yanzu bata d'ago ba kanta na k'asa dai tana kallon wayarta. Yusra ce ta lek'o tace
"Anisah ya Najeeb na kira, kuma yace kiyi sauri kiran nada mahimmanci."
Sai a sannan Jidda ta d'ago tana dariya tace.
"Kice dai za'a je a soye, wai yanzu Anisah har ta girma ta iya soyayya ko?"
Anisah ta sunkuyar da kanta k'asa tana murmushi kafin kuma ta fice da gudu ganin zasu sakata gaba da zolaya.
Yana zaune a garden bisa kujera yana sanye da jar riga da ash wando (jeans). Kayan sun haska fatarsa da take kalar fatarsa chocolate mai haske, ta k'araso tana murmushi, tun daga nesa yake kallonta har ta iso inda yake. Yayi nisa a kallonta har bai san lokacin data zauna ba, sai data kira sunansa yayi firgit ya dawo duniyar tunani.
"Ya Najeeb."
Yayi sassanyar murmushi yace.
"Anisah kina lafiya?"
Tace
"Lafiya lau, ya naganka nan kai kad'ai?"
Yace
"Ke nake jira ki taya ni fira, ko baza'a ta ya ni ba?"
Tace
"Uhm, daman Yusra tace kana nema na, sheyasa na fito."
Yayi murmushi yace
"Hakane, ni nace ta kira ki, daman inji batun karatunku ina kukayi applying?"
Tace
"Nayi applying first choice d'ina a Base nida Yusra, sai second choice mukasa Turkish Nile. Sai last mukasa BUK."
Yace
"Ok yayi Allah ya taimaka."
Tace
"Amin."
Yace
"To ya batun maganarmu ina aka tsaya? Har yanzu fa baki bani amsa na ba, kullum dana miki maganar baki bani gamsashiyar amsa, amma yau ba inda zaki sai kin fad'a min."
Cike da kunya tace
"Wace magana ya Najeeb?"
Yace
"Kin fini sani."
Ta sunkuyar da kanta tana kallon k'asa, yace
"Ke nake saurare fa."
Tace
"Ya Najeeb, wai yanzu kake nufi za'ayi auren?"
Yayi dariya
"Eh mana idan har kin amince me ake jira? Bakiji me Baba yace ba? Yace mu dukkanmu zai had'a ya aura damu, yace mazan su fad'i matan da suke so, matan kuma su gabatar masa da wanda suke so, yace so yake yayi gaba d'aya ya huta. Kinga ni da ke sai ayi 'yar gida tuwo na maina. Ko ba haka ba?"
Tayi shiru bugun zuciyarta ya k'aru, tabbas tana son Najeeb kuma shima d'in yana sonta sosai. Tace
"To ya Najeeb Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Yaji dad'in kalamantanta sosai yace
"To Amin ya Rabbi, daman haka nake so naji daga bakinki."
Tayi murmushi.
Sai da suka kammala firar tasu ne kafin kuma su tashi su shige ciki.
MSB💖
No comments:
Post a Comment