✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹11 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
A hankali ya bud'e idanunsa bakinsa d'auke da salati, sai kuma ya fara kiran
"Mummy! Daddy! Wai da gaske ne an kashe su? Ina Anisah? Wallahi duk wanda ya kashe min iyaye sai na rama masu koma waye..."
"Alhamdulillah kunga ya farka ma ashe! Sannu ya jikin?"
Kallon likitan yakeyi kafin kuma ya fashe da kuka sosai. Da k'yar aka rarrashe shi, sannan likitan ya zauna kusa da gadon da yake kwance tare da dafa sa.
"Faruk, hak'uri zakayi iyayenka sun riga sun rasu, kukanka bazai ta6a maido su ba, yanzu addu'arka ita kad'ai suke buk'ata, kayi hak'uri kaganni nan na maka alk'awari k'wato maka 'yancika a gurin azzaluman da suka aikata maka wannan mummunan aikin, kar ka d'aga hankalinka kaji ko?"
Ya share hawayensa
"Nasani doctor, iyayena basa buk'atar kukana amma kuma ya zama dole nayi kuka, ba wanda zai gane abinda nakeji a zuciyata abin yana min ciwo, zuciyata tana min zafi, iyayena sune komai na, banida kowa a garinnan sai su, don haka dole nayi kuka saboda na rasa komai na rayuwa, na rasa iyayena, sannan na rasa gidanmu da dukiyar mahaifina..."
Kuka yaci k'arfinsa. Doctor ya numfasa
"Faruk kaganni sunana Dictor Ishaq Aliyu, ni d'an garinnan ne, daga yau na maka alk'awarin taimaka maka har sai ka samu ingantacciyar rayuwa da kai da k'anwarka, inada mata d'aya da yara hud'u, maza na guda biyu sai mata biyu, kar ka damu bazakayi maraici ba Indai kana tare dani don haka ka bar kuka ka share hawayenka."
Faruk ya kalleshi da mamaki yace
"Da gaske doctor? Zaka taimaka min duk da baka san koni waye ba?"
Likitan ya gyad'a kai
"Zan taimaka maka kuma zan taya ki fighting battle d'innan har sai kayi nasara, yanzu kaga kwananka hud'a a nan asibitin, kana buk'atar muje gida ka huta."
Faruk yace
"Nagode doctor! Nagode Allah ya saka da alkhairi! Ya k'ara budi."
Likitan yayi murmushin jin dad'i yace
"Amin Faruk mu tafi ko?"
Yace
"Eh, amma ina Anisah?"
Likita yayi murmushi.
"Gata can office d'ina tana bacci muje mu d'auke ta sai mu wuce."
Ba'a d'auki lokaci ba suka iso gidan Doctor Ishaq, gida ne tangameme na gani na fad'a da ke Maitama, lallai shima doctor Ishaq mahashuk'in mai kud'i ne.
Shi ya jagorance su har cikin gidan, suna shiga wata mata dattijuwa ta fito da murmushi a saman fuskanta.
"Sannu da zuwa Alhaji."
Ta fad'a tana k'ok'arin amsar jakarsa dake rataye a kafad'arsa.
"Yauwa sannu da gida Malama Rukayya."
Tayi murmushi. "Ahh bak'i mukayi kenan, sannunku da zuwa ku shigo mana."
Suka shiga suka zazzauna kan kujera.
Alhaji ya fara magana, ga yara nan, ki shiga dasu ciki suyi wanka ki basu abinci akwai maganar da zamuyi da ke bayan nan."
Tace
"To Alhaji."
Ta tashi sannan su Faruk suka bi bayanta. Wani d'aki suka nufa daga gani na yaranta ne mazan, tace ma Faruk ya shiga yayi wanka, sannan ta fiddo masa kayan da zai saka. Hannun Anisah taja, ta mata wanka ta saka mata kaya masu kyau.
Kan dinning taja su ta zuba masu abinci suka ci sosai sannan suka wuce parlor inda Alhajin ke zaune da alama abinci ya gama ci.
Bayan sun zauna Alhajin ya fara magana.
"Ina su Yazeed?"
Tace
"Suna can waje suna buga ball."
Yace
"Jeki kirawo man su gaba d'ayansu."
Da girmamawa ta amsa ta fice.
Can sai gata yaran na biye da ita a baya.
"Dada welcome." Suka fad'a gaba d'aya.
Yace
"Thanks, ku zauna." Duk suka zauna, nan kuma suka hau kallon su Faruk. Alhaji ya numfasa ya fara magana.
"Hajiya kinga wad'annan yaran guda biyu?"
Tace
"Eh nagansu."
Yace
"Yauwa, wannan shine Faruk sai ga k'anwarsa nan Anisah, shine yaron da nake kula dashi a asibiti bayan rasuwar iyayensa."
Tace
"Allah sarki sune yaran kenan? Allah ya jik'ansu da rahama."
Yace "Amin, so nake mu cigaba da rik'esu a matsayin iyayensu, na farko kinga marayu ne gasu yara k'anana, na biyu duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi. Yara ne kuma marayu, basuda kowa sai Allah, shine na ga dacewa in d'auko su in rik'e don samun lada, ko ya kika ce?"
Ta numfasa.
"Haka ne Alhaji, wallahi wannan ba wani abu bane, insha Allah zan rik'e su a matsayin uwa a garesu, Allah ya bamu ikon rik'e amana."
Yace
"Amin, Faruk wad'annan k'annenka ne gasu nan, kaga wannan shine babba mai suna Yazeed, shekarsa sha biyar sai mai bi masa Hauwa'u ana kiranta Jidda shekararta Sha hud'u, sai k'aninta Nabeel shi yakeda da sha biyu sai auta gata nan Yusra ita keda shidda, don haka kuna jina wannan 'yan uwanku ne ban yarda wani ya nuna musu wariya ba a cikinku, kuna jina?"
Suka ce
"To Dada."
Alhaji yayi murmushi
"Faruk ga kannenka nan sai kuje kuyi wasa ko?"
Faruk yayi murmushi inda gaba d'aya suka mik'e suka fice.
Alhaji ya ce
"Allah ya bamu ikon rik'e su amana, ya tona asirin azzaulumai."
Tace
"Amin ya Allah Alhaji, yaran sun bani tausayi wallahi, Allah ya bi musu hakk'insu."
Yace
"Amin amin, anjima zanje inyi magana da manyan lauyoyin da na sani, asan me za'ayi a kai."
Tace
"Hakan yayi daidai, yanzu makarantarsu fa?"
Yace
"Makarantarsu ba matsala bace na d'auki
nauyin karatunsu, yanzu ayi k'ok'ari a saka su makarantarsu Yazeed."
Tace
"Haka yayi daidai, Allah ya k'ara bud'i."
Yace
"Amin Amin, bari inje in d'an kwanta kafin anjima zan koma asibiti."
Tare suka mik'e ya fice tabi bayansa.
***
MSB💖
No comments:
Post a Comment