Monday, 24 July 2017

AUREN FANSA 28

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹


Wannan page d'in nakune members na MARZAH HAUSA NOVELS, nagode da k'aunar da kuke nuna min, Allah ya bar zumunci amin❤️

          🌹28 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com

Da sauri ya juya abin mamaki wai Meenah ce kwance kamar ba rai, a gigice yayi kanta ya shiga jijjiga ta, abin mamaki ko alamar motsi babu a tattare da ita. Tunda yake a rayuwarsa bayan mutuwar iyayensa bai ta6a tsintar kansa cikin matsanancin tashin hankalin irin wannan ba, ya rud'e ya shiga tashin hankali mai wuyar fassara.
Da gudu kuma yayi dinning ya d'auko robar ruwan sanyi ya shiga bud'ewa har wani kyarma yakeyi.
Yayyafa mata ya dinga yi amma ba alamar zata farka, hakan yasa ya juye mata shi gaba d'aya a fuska, aikuwa take ta saki ajiyar zuciya sannan ta bud'e idanunta wanda suka kad'a sukayi ja kamar garwashi, tarr take kallonsa kamar sabuwar halitta, shi d'in ma ita yake kallo babu ko k'yaftawa, a hankali ya sure ta in banda sannu babu abinda ke fita a bakinsa.
D'akinsa ya wuce ya shimfid'ar da ita kan gado sannan ya nemi wuri ya zauna gefen ta har yanzu ita yake kallo.
"Sannu Meenah... ya kike ji yanzu?"
Kauda fuskarta tayi daga kallon da take masa zuwa d'ayan 6angaren sannan kuma hawaye suka shiga kwarara daga idanunta masu zafin gaske.
"Meenah..."
Ko motsi batayi ba bare yasa ran zata amsa.
Hannunta ya kamo duka biyun yana murzawa, runtse idanunta tayi a take kuma wasu hawayen sukayi nasarar saukowa, tana cikin mawuyacin hali mai wuyar fassara, ita kad'ai tasan me takeji a halin yanzu.
"Tabbas nasan dole kiji ba dad'i, nasan kin fara tunanin bana sonki ko? Sheyasa nace zan k'ara aure ko Meenah? Ina so ki fahimce ni Meenah har yanzu ina sonki kuma ina k'aunarki babu abinda ya chanza, auren da kika ga zanyi yana d'aya daga cikin kaddara ta, ina so a matsayinki na musulma ki d'auki kaddara Meenah, kawo wata mace cikin gidannan bazai chanza son da nake maki ba, nidai fatana ki yarda kuma ki amince don bazan iya k'ara aureba ba tare da kin amince ba."
Fuskarta ya shafa ya cigaba
"Wallahi ko yanzu kika ce kar nayi aurennan na fasa kenan ko da kuwa yanzu za'a d'aura shi, kuma ko wacece zata shigo cikin gidannan zan zamo mijin da zai kare miki martaba da kuma mutunci, har abada bazan wulak'anta ki ba, nidai fatana inji ta bakinki a halin yanzu Meenah..."
Wani gumi ya ziyarce ta, wato dai da gaske kishiya zai mata kenan? Ita kam batada sa'a a rayuwa, ta taso tun tana k'arama tana d'and'ana bak'in ciki a koda yaushe ba kwanciyar hankali, tana tunanin auren da zatayi hutu ne a gareta ashe tayi kuskure. Sai dai kuma dole zatayi hak'uri tunda haka Allah ya kaddara mata ita kam.
Ta yunk'ura ta tashi zaune tana mai share hawaye duk da kuwa wani na bin wani amma dole ta share, kanta kuwa kamar ana sara mata guduma haka takeji. Cikin wata irin muryar data dishe tace
"Haba my soul, meyasa sai ka nemi izini a wurina sannan ka k'ara aure? Ka manta Allah ya halasta maka daga mace d'aya zuwa hud'u? Bana cikin irin matan da idanunsu ke rufewa da kishi har su fad'a halaka, Allah ya halasta maka aure ni wacece da zan hana? Ay ban isa ba ma."
Tayi murmushi mai ciwo ta cigaba.
"Ba k'arin aurenka ya fi d'aga min hankali ba, kasan me ya tada man hankali?"
Yace
"A'ah."
Tayi murmushi
"Wai ace aurenmu da ko sati ba'ayi ba amma ace zakayi aure, sannan kuma ina tsoron ka daina sona ne sheyasa ko kuma ka gaji dani."
Yace
"Haba my baby, kima daina irin wannan tunanin har yanzu ina sonki, kuma insha Allah zan cigaba har in mutu."
Tayi murmushi
"Na yarda da kai my soul, kuma ina alfahari da kai a matsayin mijina, a koda yaushe ina gode ma Allah da ya bani mai sona mai kuma k'aunata, idan aurennan alkhairi ne Allah ya tabbatar, idan ba alkhairi bane ba Allah ya za6a maka mafi alkhairi."
Gabansa yayi mummunan fad'uwa, ya lumshe idanunsa kafin ya bud'e, ya kalle ta cike da sha'awa!
Tunda yake a rayuwarsa bai ta6a cin karo da mace makamanciyar wannan ba. Matsowa yayi dab da ita yace
"A gaskiya kafin a samu mace irinki a wannan zamanin sai an tona Meenah. Nima ina so ki sani ina sonki ina k'aunarki sannan ina alfahari da ke a matsayin matata."
Duk da tana cikin wani hali hakan bai hanata yin murmushi ba, ta yunk'ura zata tashi jiri ya kwashe ta, da sauri Faruk ya taro ta sai kuma ta fad'a jikinsa haka ya rungume ta kamar wata jaririya. Wani shock ya kama ko wanensu, sannan kuma suka dubi juna cikin ido. Sun kai minti kusan d'aya a haka kafin Meenah ta fara kauda tata fuskar tana k'ok'arin tashi daga jikinshi.
Duk ya dabarbarce, kwanciya tayi sakamakon wani bacci da taji yana neman kwasar ta.
Duka duka batafi second goma ba bacci yayi awon gaba da ita.
Jikin Faruk yayi matuk'ar sanyi, sannan kuma take ya fara tsintar kansa cikin wani irin yanayin da bai ta6a tsintar kansa a ciki ba. Wani abu yaji yana bin dukkanin illahirin jikinsa tun daga kansa har zuwa tafin k'afarsa, take tsikar jikinsa ta tashi tayi wani yarr!
"Hasbunallahu wani'imal wakil." Shine abinda yake fad'i, sannan ya mik'e jiki a sanyaye ya fad'a toilet, a gaban sink ya tsaya tare da bud'e pampo ya shiga wanke fuskarsa, bayan ya gama sai ya tsaya yana kallon kansa kuma ta mirror, ba abinda idanunsa ke gani kamar fuskar Meenah, wani gurin tana murmushi wani gurin kuma dariya, tsintar kansa yayi yana mai murmushin shima. Da sauri kuma ya girgiza kansa ya fice daga toilet d'in yana ta faman maimaita "No."
Kwanciya yayi gefenta tare da rufe idanu yana jin wani bak'on al'amarin da bai ta6a ji ba a tsawon rayuwarsa ba....


Sassanyar iskar asuba mai k'unshe da ni'ima tare da tarin albarka shi ya daki fuskar Meenah kasaancewar tagogin d'akin a bud'e suke. Hakan yasa taja dogon numfashi tare da motsawa, tayi tsawon minti biyu a haka kafin a hankali ta fara k'ok'arin tashi zaune.
A natse ta juya tana maida kallonta kan Faruk da baisan inda duniyar take ba. Tuni abinda ya faru jiya ya fara dawo mata, nan ta yunk'ura cikin k'arfin hali ta mik'e duk da batajin k'arfin jikinta, kasancewar tana fashin sallah sai ta taka a hankali zuwa jikin window. Hadari ta gani sosai, iskar damina  had'e da yayyafi ya daki fuskarta, hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba, tayi ta shak'ar iskan gami da ware hannayenta don ya ratsa ta sosai, take taji ta samu k'arfin jikinta fiye da dah.
Ruwan saman ne ya sauko mai k'arfi, ta mik'a hannayenta duka ta tari ruwan.
K'arar ruwan saman ne ya farkar da Faruk, idanunsa k'yam a kanta, sai yau ya ta6a ganinta ba d'ankwali, gashin kanta ya zubo har bayanta hakan ya faru ne saboda cirewar ribbon d'inta jiya da daddare. Kanta a nannad'e yake kamar na jarirai gashj bak'i wuik!
Yayi zumbur ya mik'e tare da duba time ganin lokacin sallar asuba yasa ya mik'e da sauri ya nufi toilet.
Har ya gama sallarsa a d'aki Meenah batasan yanayi ba. Tana can tsaye tana kallon ruwa na sauka k'asa, abin burgeta yake tun tana k'arama, ita dai rayuwarta tana son ruwan sama yanzu haka ji take kamar ta shiga ciki tayi wanka.
A hakan ya cigaba da kallonta wanda baison yana yi ba.
"Ina kwana."
Ta fad'a gami da zama gefen gado. Yayi murmushi
"An tashi lafiya? Ya k'arfin jiki?"
Tace
"Alhamdulillah."
Har yanzu kallonta yake ganin ba wani yanayi na damuwa a tattare da ita dangane da maganar jiya ba.
"Lokacin dana suma jiya kasan me ya kamata kayi min amma ka kasa sai rud'ewa, ashe dai kana sona haka?"
Take gabansa ya fad'i, ya rasa dalili da ta ambaci yana sonta sai ya tsinci kansa da fad'uwar gaba?
Yana jiyo dariyarta har cikin kansa.
"Yanzu dai ina so ka fad'a min kai da ka ganni cikin wani irin yanayi ka rasa abinyi saboda kana tunanin ko mutuwa nayi? Ashe kana tsoron rasa ni?"
Ta k'arasa maganar tana dariya.
Yayi dum, sannan ya mik'e ya zauna gefenta tare da rik'o hannunta yace.
"Ay dole na tsorata tunda ina ganin zan rasa masoyiyata ta hak'ik'a."
A zahirin gaskiya baisan ya furta wad'annan kalaman ba...
Don haka sai yayi saurin tashi tsaye yana fad'in
"Bari nayi wanka yau zan fita office da wuri."
Da mamaki ta kalleshi
"Yanzu fa k'arfe shidda."
Yace
"Eh wurin bakwai nakeson barin gidannan."
Tace
"Ok bari na had'a maka breakfast kafin ka fito."
Da sauri ya tsaida ta
"A'a kar ki wahalar da kanki tunda bakyajin dad'i."
Tayi dariya
"Haba ba wani wahala bari yanzu zan gama."
Bata jira amsar sa ba ta fice da sauri. Ya dad'e tsaye a wurin kafin yayi saurin shigewa toilet.


MSB💖

No comments: