Sunday, 23 July 2017

AUREN FANSA 27

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹

Hip!!!hip!!!hipp!!!
Hurray!!!!!!!
Wishing u long life in Islam and prosperity Faridat Allah k'aro shekaru masu albarka ya kuma k'ara basira da hazak'a Amin💃🏻💃🏻💃🏻😍😍

          🌹27🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com


Gaba d'aya suka dube ta sadda take k'arasowa cikin parlon tare da zama gefen Dada sannan ta d'ora.
"A gaskiya Alhaji banga amfanin aurensa ba duka duka yaushe akayi aurennan da zai bijiro mana da zancen wani auren kuma? Haba me kake so duniya tace mana? Ko sati d'aya fa bakuyi ba da aure haba Faruk ka bani mamaki, me tayi maka? Me ta tsare maka? Yarinya salihar baiwar Allah zaka ce zakayi ma kishiya daga yin aure yanzu? To a gaskiya ban lamunta ba Alhaji, ya sake lala."
Dada bai ce uffan ba yana dai ta kallon Mama tana zuba har sai data gama sannan ya numfasa yace
"Wai da kike ta wad'annan maganganun kece zaki zauna masa dasu ne? Bashi yace yaji ya gani ba? Ba wanda ya masa dole ay, kuma ni bazan iya hanasa yin aure ba, amma abinda nakeso ka sani Faruk shine kasan shi aure ba abin wasa bane, sannan kuma kaji tsoron Allah idan har kayi aurennan tofa dole sai kayi adalci a tsakaninsu, idan kuwa bazakayi adalci ba gaskiya ban yarda ka sake aure ba kuma bada yawu na ba, sannan magana ta k'arshe   sai na tuntu6i ita Jiddar naji ta bakinta tukunna..."
"Ay Alhaji kar ma ka 6ata lokacin ka saboda Jidda ta dad'e da ciwon son Faruk a cikin ranta, don ma ina kwa6ar ta ay da tuni ta sanar maka tana sonsa, sai dai Alhaji dole fa sai mun tashi tsaye kasan halin Jidda bata jin magana ina gudun kar taje tasa d'iyar mutane a gaba kaga babu dad'i hakan."
Dada yace
"Haka ne, Faruk a gaskiya sai ka tsawatar ma Jidda sosai saboda duk wani abin tashin hankali ta guje shi, idan kuwa bazata iya kiyaya ba to a fasa auren. Hajiya kira min Jidda tazo ina nemanta."
"To Alhaji."
Bayan fitar Mama Dada yace
"Ina fatan ka sanar da ita Aminar batun k'ara aurenka? Kuma ta yarda ta amince da hakan?"
Yayi shiru, Dada ya ce
"Alamu sun nuna min cewa baka sanar da ita ba Faruk, to a gaskiya idan kaga ka auri Jidda sai da amincewar Amina, don haka kaje ka nemi shawarar matarka."
To kawai ya iya cewa ya mik'e, a daidai bakin k'ofa sukayi kaci6us dasu Jidda zasu shigo, bai tanka mata ba yasa kai ya fice, bayan sun shigo Dada ya soma magana.
"Jidda Faruk ne ya zo mana da wani zance wai yana son auren ki..."
Bai k'arasa ba ta mik'e cike da murna tace
"Dada? Da gaske kakeyi ko wasa? Da gaske Faruk zai aure ni? Mama da gaske kukeyi don Allah?"
"Ke meye haka wai!"?
Dada ya daka mata tsawa, zama tayi tana ta murna a yayinda Dada ya cigaba
"Kinga Jidda ki nutsu ki saurare ni da kunnen basira, kamar yadda na fad'a miki Faruk yazo man da zancen aurenki, amma inaso kisani kiji tsoron Allah Jidda, kar ki cutar da d'iyar mutane kinsan dai Allah na kallonki, sannan duk wani abin da zakiyi da bai kamata ba na samu labari to ki sani k'arshen zamanki gidan Faruk yazo kenan, don haka ki kama kanki. Hajiya kisa ido akanta sosai, tashi ki tafi."
Da gudu ta fice tana zuwa d'akinta ta fad'a kan gado cike da murna, har ma ta fara imagining wai gata can har sunyi aure da Faruk...



***


Da sallama ya shigo parlon tana zaune kan kujera tana kallo, tana ganinshi ta mik'e tana murmushi sosai ta k'arasa wurinsa tace
"Sannu da dawowa my soul." Ta fad'a tana amsar ledojin da ke hannunsa.
Ya kalle ta tana sanye da army green Indian  sari d'inkin riga da wando, kayan sun matuk'ar amsarta, fuskarta babu wata kwalliya don Meenah ba ma'abociyar yin kwalliya bace bata ma iya ba, hakan yasa kullum fuskanta take fresh gwanin kyau, d'ankwalin kayan kuwa yana d'aure akanta d'aurin ya zauna daram a kanta. Haka kawai kuma sai ta basa tausayi, ganin mummunna labarin da zai fad'a mata, yana tunanin yadda ma zata d'auki maganar.
"My soul inata magana kayi shiru."
Ya susa kai yana k'ak'alo murmushi yace
"Ohh sorry baby, banji ba me kika ce?"
Tace
"Nace muje na saka maka ruwan wanka kayi sai kaci abinci."
Yace
"Ok ok bismillah muje."

Tana gaba yana biye da ita, duk wani motsi nasa akan idonsa haka kazalika k'amshin turarenta duk ya cika masa hanci hakan ya haifar masa da kasala, jikinsa ya mutu.
Suna shiga d'akinsa yau a karo na farko data ta6a shiga, simple d'aki ne mai d'auke da black gado duka furnitures d'in dake d'akin black ne, hartta wasu 'yan kujerun hutawa guda biyu da table tsakiyarsu suma black ne, carpet black, sai paintin d'akin ne kawai yake fari k'al hakan ya haskaka d'akin. K'amshi gami da sanyin ac kuwa sun had'u sun mata sallama.
Kan gado ya zauna a yayinda da ta shige toilet nasa ta had'a masa ruwan wanka ta fito. Tana fitowa tace
"My soul ga ruwan can na had'a maka, idan ka fito ina parlor."
To kawai ya iya cewa shi duk jikinshi a mace yake ya rasa dalili.
Bayan ya fito ya kimtsa cikin kayan baccinsa kalar dark blue, ya fesa turare mai sanyin dad'i ya fito.

Tana zaune a parlor tana jiranshi, yana zuwa ta mik'e tana murmushi tace
"Har ka fito my soul? Ga abinci nan na girka maka."
Yayi yak'e yace
"Thanks my baby."
Tare suka zauna ta shiga zuba masa tuwon shinkafa miyar ku6ewa d'anya da k'ashin rago a ciki sai man shanu, bayan ta zuba masa da tsiyaya masa lemon kwakwar da tayi masa a glass cup, sai taja kujera tana fuskantarsa, a natse ya fara cin abincin sai dai gaba d'aya hankalinsa ba'a kwance yake ba. Ya kalle ta yaga hankalinta a kwance tana kallonsa, ya k'ak'alo murmushi yace
"Baby bangane ba ke bazakici abincin bane?"
Tayi murmushi tace
"Zanci amma ina so sai kaci ka k'oshi tukunna."
Ya kalleta cike da mamaki yace
"Sam ban yarda ba, idan bakici ba nima bazan ci ba."
Da sauri tace
"Haba dai? To zanci."
A tare suka ci abincin bayan sun kammala ta gyara wurin. Tana kitchen tana d'auraye plates ya kirata. Ta fito tana zuwa yace.
"Baby zauna ina son magana da ke."
Tace "to." Ta zauna. Ya had'iye wani miyau mai d'aci tukunna ya fara magana.
"Meenah kinsan dai ina sonki ko?"
Da mamaki tace
"Sosai ma my soul, nasan kana sona amma lafiya?"
Yace
"Kuma kinsan dai ina k'aunar ki ko?"
Tayi murmushi
"Nasani."
Yace
"Yawwa, kinsan kaddara mai kyau da marar kyau ko?"
Tayi dariya mai cike da mamaki tace
"Nasani mana."
Yace
"Kinsan kuma dai kowa da tasa kaddarar Meenah, maganar da zan fad'a maki tana da nauyi, amma ina so badan ni ba don Allah da kuma soyayyar da kike min ki fahimce ni."
Jiki a sanyaye tace
"Don Allah my soul ka fad'a min ko meye, sai kwana kwana kakeyi."
Yayi shiru cikin nazari, can yace
"Hakane zan fad'a maki amma ina so kiyi min alk'awari guda d'aya."
Tace
"Na me?"
Yace
"Bazaki d'aga hankalinki ba sannan bazakiga laifi na ba."
Gabanta yayi mummunan fad'uwa, tace
"Don Allah ka fad'a min my soul ka barni a duhu don Allah."
Tashi yayi tsaye yana mai juya baya don ya kasa ma had'a idanu da ita. Da k'yar ya iya tattaro kalamunsa wuri d'aya, yace
"Auren zan k'ara Meenah..."
A gigice take kallonsa, kanta yayi wani dum! Nuna sa takeyi da hannu tana fad'in
"Anya naji da kyau, sake maimaita mini."
Yace
"Kiyi hak'uri haka d'in dai nace, aure zan k'ara."
"Innalillahi wa inna ilahir raj'iun." Take kuma gumi ya dinga sassarfo mata ta ko ina, kafin kuma taji wani irin kuka ya taho mata cikin tashin hankalin ta fasa ihu sai dai yaji abu ya fad'i k'asa tim!


MSB💖

No comments: