Monday, 21 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 22

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 22}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Kamar wata marar lakka haka ta dauki madaidaicin akwati ta fara hada kayanta, tasan yadda yace zaiyi kwana goman nan ita sai ta wuce haka a agadez, zuwa yanzu ma hawayen sun daina zuba ta koma kukan zuci, bayan ta gama hada kayanta tsab, zuciyarta kamar ana zuba mata garwashi haka takeji, hijab ta saka maroon color ta dauko hand bag ta saka wayarta da sauran abubuwan da zata bukata kafin ta fita. Booth ta gani a hangame ta saka kayanta a ciki ta zagayo ta shiga driver ya jasu ya kaisu airport. A cikin jirgi ne ya juyo ya kalleta yaga tayi wani fayau ta rame kamar wacce babu jini a jikinta, sam jikinta babu karfi kamar wacce ta shekara tana jinya. 

Har suka kusa isa Agadez babu wanda ya ce uffan a cikinsu, sai can ta juyo ta kalle shi tace "Ka taimakeni ka sakeni Sultan, idan munje agadez ka bani takardata in yaso sai ka dawo kai." Wani irin juyowa yayi har yana neman sarkewa, "Me kikace? Saki? Ay tsakani na dake babu maganar saki." Ta fashe da kuka "Toh meyasa kake azabtar dani Sultan? Babu abinda nayi maka fa baka tunanin kana daukar alhakina?" Wani mugun kallo ya watso mata take ta kara karfin kukanta ta duke bisa cinyarta ta dinga sheshekar kuka wane ana zare mata rai, har suka isa Hoodah bata daina wannan kukan datake ba, ko kallonta baiyi ba yace "Idan kin gama kukan zaki iya fitowa." Uber yayi masu suna tsaye suna jiran motar ya dauko mata robar ruwa ya bata ta wanke fuskanta, har motar ta iso sannan suka shiga har kofar gidan su Hoodah aka tsaya, sai ganin Sultan tayi baida niyyar fita ya wani hade rai kai kace bai taba dariya a duniya ba, "Ki fita daga cikin motar nan, ko gidan naku ne baki gane ba? Ko akwai inda za'a ki?" Mamakin rashin tausayinsa takeyi sai kace ba Sultan din da tasani ba shagwa6a6e ba, yana fadin haka ya janyo wayarsa ya fara latsawa ba tare da ya sake koda kallon inda take ba, tafi minti biyar tana kallonshi kafin ta hadiye kukanta mai cike da bakin ciki da takaici, "Sakina kayi?" Dan ita bataga dalilin maido ta gida da yayi ba, ko kallonta baiyi ba yace "In sakinki nayi ay xan fada maki!" Share hawayenta tayi tace "Akwai ranar da zakayi dana sani Sultan, amma still kasani zan yafe maka kuma zan fahimce ka, sannan duk ina alkwarin I have you in my life? I will always be by your side? Ko dayake it's fine I totally understand Just know that zaka dawo da kanka kana rokona gafara good bye." Tana gama fadin haka ta fita daga motar ta bude booth ta kwashi kayanta ko kallon inda yake bata kara yi ba ta shige gida. Ya kusa kai minti goma yana kallon gate din gidansu kafin yace da driver din su tafi inda zai sauka. Hoodah ba karamin mamakin irin tarbar da Umma tayi mata tayi ba dan sosai ta tarbeta hannu biyu biyu harda taimaka mata ta sauke kayanta daki, Abbanta ma yaji dadin ganinta sosai yayi kewarta, kamar yadda Sultan ya fada mata cewar ten days zaiyi itama haka tace masu ay kwana goma zasuyi....

*******

Wani irin wahalallen amai takeyi kamar xata amayo yan cikinta, "Innalillahi Khairy me nake gani haka? Lahaula fi shi'atillah! Aman me kikeyi Khairy?" Mama ce ke rafka wannan salatin yadda kasan ance mata yau ka gawar Khairy nan a kwance, wani irin mugun numfashi taja ita kam yau ta shiga uku ta ga rayuwa, yau babu mai kwatarta hannun Mama "Ke dan ubanki kinaji ina maki magana kin man shiru, ana tambayarki abu amma kin zura ma mutane na mujiya!" Ta furta da karfi tana janyo hannun Khairy daga cikin bathroom din tana kare mata kallo, ita kuwa Khairy kuka ta fara yi a hankali cike da tsoro da kuma fargaba, yadda taga Mamar na janta har parlor yasa tace "Mama dan Allah ki tsaya sai jana kike kamar ance maki an kamani ina sata!" Ta fadi haka tana neman kwace hannunta daga hannun Mama, nan Mama ta kureta da idanu tana mata wani irin kallo "Nace ki fada man aman me kikeyi? Tun jiya na kula dake daga amai sai kwanciya uban me ke damunki? Wallahi ko kiyi magana ko inci ubanki cikin gidannan yanzun nan shegiya mai mugun hali!" Nufar inda Khairy ke tsaye bakin kofa tayi kamar wata zakanya don son tabbatar da zarginta Khairy ta kurma wani uban ihu, "Dan Allah ki tsaya Mama! Zan fada wallahi zan fada!" Mama ta kama kugu tana jijiiga "Toh ina jinki!" Nan ta fara karkarwa "Dama.... dama.... ya kamata ace na ga al'adata tun sati daya ya wuce ban gani ba, shine na sa6e naje akayi man test.... aka...aka...ga ciki...na wata daya...." ko karasa maganar bata yi  ba take Mama ta wanke da wani irin wawan mari! Ihu ta kurma nan Mama ta damko ta "Dama nasani yawan karuwanci kike zuwa! Dan ubanki wa yayi maki ciki? Iyye wani dan iskan ne yayi maki cikin shege!? Ciki? Na shiga uku na lalace Khairy kin cuceni kin gama dani! Dan ubanki abun naki har ya kai haka? Aikau zaki ga ciki don wallahi badai a nan gidan ba, na rantse da Allah na cikin kabari sai yafi ki jin dadi dan ubanki! Gara ma tun wuri kisan nayi cikin gidannan!" Ihu ta zabga ta fashe da kuka "Na shiga uku Mama ki hakuri ki rufa man asiri!" Ranar Khairy ta daku mutuwa kadai ya rage mata tayi, da kyar da sudin goshi Baba ya ceceta daga hannun Mama.

Tana kwance dakinta bisa gado tana kukan fitar rai, babu abinda takeji sai karar tsuntsaye cikin daren nan tayi mugun buguwa wurin Mama, amma abun mamaki duk da jikinta na ciwo amma zuciyarta tafi komai ciwo, gaba daya ta rasa meke mata dadi a duniya wai yau itace da cikin shege? Kukan ne yakeson yaci karfinta toshe bakinta tayi da hannunta ta dinga razgar kuka...

Da safe kamar daga sama taji saukar bulala, ko ba'a fada mata ba tasan Mama ce ta fara gana mata daya daga cikin azabobinta, wani kukan zuci tayi kafin idanunta su bude tabbas kuwa Mama ce tana ta faman huci, kallon window Khairy tayi nan taga rana fayau, ruwa Mama ta sharara mata mai sanyin bala'i ihu ta fasa ihu take ta fara karkarwa "Dan Allah Mama kiyi hakuri wallahi da kin magana zan tashi..." kukan ma ta kasa yinshi "Dan ubanki inzo inta faman tadaki kiyi sallar asuba amma kik'i tashi saboda ni kin maidani sakara shashasha ko? Wato sai kika kwanta kika cigaba da baccinki ko? Tou na rantse da Allah zaki gane kurenki, wannan kafircin ba'a nan gidan zakiyi man shi ba, ga karuwanci da rashin yin sallah ga cikin shege dan ubanki! Munafuka algunguma!" Mama ce keta faman masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba. Mikewa Khairy tayi da kyar ta nufi hanyar bathroom "Kuma wallahi na baki minti goma ki fito, sharar gidannan kaf hade da tsakar gida zakiyi shi ko inci ubanki yanzun nan, ga wanke wanke da wanke band'aki! Ina jiranki!" Hawayenta ta share "Bazan iya shara ba Mama bayana  ke ciwo kamar zai balle..." ta fada tana nufar hanyar bathroom "Toh dan ubanki sai kinyi! Wallahi gara ma kiyi cikin arziki, ki gama zagaye zagayenan sai kinyi shi! Kuma cikin gidannan sai na lahira yafi ki jin dadi badai ciki kika yo ba na shege? Tou zaki ci ubanki kuwa! Ke karewa ma daga yau awara zaki dinga toyawa kofar gidannan kuma inga uban da xai hanaki ko shi uban naki yayi kadan!" Share hawayenta tayi, tayi tsaye bakin bathroom din zuciyarta na tafarfasa, da sauri ta share hawayenta jin wani zagin da Mama ta kunduma mata daga parlor, da sauri ta shige bathroom din da sauri. Bayan ta kammala ta fito a hankali ta fara sharar tsakar gida tana yi tana jin kamar zuciyarta zata bar kirjinta, duk ta rasa sukuni ta rasa abinda yake mata dadi. Tun kafin ta gama sharar nan Mama ta fito tsakar gida ta dinga yarfa masifa da bala'i ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, dole ta dinga sauri ta karasa aikin gidannan tas ta gama wanke wanke, ita ko abinci bata tunanin xata iya ci, a nan inda ta gama wanke wanken ta zauna sai kuka ya kufce mata a daidai nan Baba ya fito daga daki don zuwa wurin aiki. Yana ganinta a haka yaji tausayinta matuka saidai kuma ko menene ita ta jawo ma kanta ko jiya baisan meke faruwa ba sai yau da safe Mama ke fada masa abinda tayi, yace ko kusa kar wanda ya sake ya zubda cikinnan don ita Mamar tace zubarwa za'ayi yace ahir laifi kan laifi kenan? Yace kar a sake a zubda shi. Tsugunnawa yayi daidai saitinta ya miko mata abinci yace "Kar6a kici Ummalkhairy, kiyi hakuri da duk wata rayuwa da zatazo maki, kuskure ne kin riga kin tafka, saidai fatan Allah ya yafe maki kurakurenki ya zamo wannan shine sanadin shiriyarki, zuciya a koda yaushe ko ta kasance cikin farin ciki ko kuma kunci, kuma na hana zubar da cikinnan don nace koda bayan idona kika zubda shi toh ki sani ban yafe maki ba, don ke kanki zaki aikata laifi akan laifi ga laifin aikata zina ga kuma na kisan kai!" Nan ya aje mata abinci ya tashi ya fita, ganin yadda Khairy ke kuka ya sanya Mama ta danji wani iri a ranta "yau xaki zakici ubanki wallahi, saboda ke ay ya fita bai bada ko sisi ba toh wallahi sai na fanshe ta a wurinki, maza tashi ki gama wanke wankenan kije ki tashi ki fara wanke wake suya, badani za'ayi wannan iskancin ba don wallahi in kika bata man rai ko haihuwa kika tashi yi kallon arziki ma bazanyi maki ba sai ki nemi wata uwar, shegiyar yarinya kawai haka nan kin kwaso mana abin kunya. Kai innalillahi wa inna ilahir rajioon." Sai kuma ta fashe da kuka harda fyace majina, cikin kuka Khairy tace "Mama suyar awara a kofar gida zanyi?" Wata uwar harara ta watsa mata wane zata cire idonta "Toh kinfi karfin kiyi ne dan ubanki shashasha yarinya! Zakici ki tashi ko sai na iso nan? Ubanwa yace kiyo cikin shegen?" Ta daka mata tsawa wadda batasan lokacin data hadiye kukan nata ba ta fara tura dumamen tuwo da miyar kuka tana hadewa da kyar.

Fad'in yadda rayuwa ta sauya ma Khairy ma bata baki ne gaba daya duniya ta juya mata baya, kawayenta sun guje ta yanzu iyayenta ko nan da kofar gida basu isa su leka ba yanzu za'a fara nunasu ana cewa yarsu tayi cikin shege. Zagin yau daban na gobe daban... Ranar tana xaune tsakar gida ta zabga tagumi abun duniya duk ya isheta ji take kamar ta kashe kanta ta huta "Dan ubanki taso kizo ki amsa ki sha bazaki kashe kanki ba tunda dai cikin ya riga ya shiga mazinaciya! Allah kadai yasan irin mugun abun da kika shuka Allah ya jarabe ki ta wannan sigar!" Yadda tayi tsaye kememe a bakin kofar ya tabbatar ma da Khairy jiranta take taxo ta amsa, a hankali kamar wacca kwai ya fashe mawa a jiki ta mike dab da kofar dakin Khairy tayi mika daidai da dagawar rigarta sama cikinta yadda ya bullo shi ya tsorata Mama wani wawan ihu ta kurma hade da dora hannu bisa kai, da sauri Khairy ta karasa wajenta tana tambayar lafiya? Ita tsoro ma ta bata. "ubanki lafiya lau Shegiya yar iska! Ashe dai maganar cikin nan da gaske ne wallahi Allah na dauka wasa ne, gashi nan ya bullo wallahi ya bullo!" Khairy don dole tayi baya cikin tashin hankali ta fara magana "Na shiga uku don Allah don annabi kiyi hakuri wallahi sharrin shaida ne!"  Finciko ta Mama tayi hade da shaketa "Kar kiyiwa shaidan karya dan ubanki!"

YAR AGADEZ PAGE 21

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 21}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Da kansu suka ja mata rigarta kasa sannan suka mikar da ita tsaye, kuka take harda shasheka daya ya kece da dariya "Ba dai ice cream kikeso ba? Gashi nan mun baki." Suka sake kecewa da dariya gaba dayansu, fizgo ta sukayi suka cillata cikin mota, haka suka tada motar motsin kirki Khairy ta kasa yi  in banda kukan fitar rai babu abinda takeyi, hayaniya sukeyi cike da nishadi cikin motar "Kai ay amma fa mutumina ka cika wayau wato wai ta bimu kwadayin shan ice cream sai gashi mun bata hot tea!" Wata irin makirar dariya suka sheke da ita, yace "Allah mutumina nake gaya maka na dade ina kwadayin yarinyar nan kasan dole saida wayau da dubara in kana son cinma burinka!" Suka kwashe da dariya gaba dayansu, wani irin bakin ciki ne ya lullu6eta, ji tayi sun tsayar da motar kafin ma ta ankare taji sun jefar da ita tana kallo suka tada motar suka tafi suka bar ta cikin kasa, ita yanzu ya zatayi? Ina zata saka ranta? Wannan wace irin kaddara ce haka ta afka mata? Ko a mafarki bata ta6a tunani ba! Dama haka duniyar take cike da marassa imani? Hawaye ta cigaba da zubarwa, tabbas tasan dare ya lula can tsakiya wani sanyi da taji yana ratsata, yanzu tasan in ta koma gida ubanta Mama zataci, babanta kuwa ay kasheta kawai ma zaiyi! Da kyar ta mike ganin wani rumfar shago tana tafiya da kyar ta lallaba ta isa wurin ta zauna, nan take kuka ya dawo mata sabo, zuciyarta kuwa kamar ana tafasa ruwan zafi takeji kuka take bil hakki har tana cijewa har ji take wani wahalallen zazzabi ya rufeta kamar yadda yayi ma ruhinta da baibayi, kwantawa tayi bisa dakalin shago don kuwa ko motsin kirki bata iya yi a nan bacci yayi awon gaba da ita baccin kuwa babu abinda ke cikinshi sai tarin bakin ciki da takaici.

Sanyin asuba ne yayi nasarar tada Khairy daga wahalallen baccin da takeyi, tana bude ido wani dafin bakin ciki ya daki zuciyarta nan take hawaye suka sake zubo mata, hakkun a wajen shago yau ta kwana shagon ma tana tunanin na saida kayan dinki ne. Bakin titi ta nufa tana tafiya da kyar ta samu machine ta hau gidan wata kawar ta mai suna Zaliha ta nufa, daidai bakin gate ya ajeta saukinta ma tana aje kudi cikin bra dinta nan ta zaro wasu yan chanji ta mika masa, kwankwasawa ta soma yi can mai gadi ya zo ya bude yana ganinta ya fara murmushi don yasanta sosai kawar Zaliha ce ta secondary school, bata ko jira ta gaishe shi ba tayi ciki da sauri ta kofar baya tabi don tasan basu kulle ta tana bude kofar taci karo da Zaliha tsaye da cup din ruwa wanda kallo daya zakayi mata ka hango baccin dake idanunta, a tsorace ta dago tana kallon Khairy "Innalillahi Khairy kece?" Ta fada dafe da kirji idanu a waje, sulalewa tayi a kasa tana wani irin gunjin kuka "Zaliha sun cuceni! Sun gama dani! Na shiga uku!" Kuka take kamar ranta zai bar jikinta, a hankali Zaliha tayi hugging dinta ta tadata tsaye ganin kukan Khairy bazai kare ba yasa taja hannunta suka tafi dakinta ta zaunar da ita kan gado tace "Khairy kiyi hakuri don Allah! Wallahi Bangane me kike nufi ba? Zazzabi kike ne? Naji jikinki da zafi. Bari naje dakin Mami na dauko maki magani in kika samu bacci anjima sai muyi magana."  Tana fadan haka ta mike ta fita daga dakin can sai gata ta dawo da cup din ruwa da magani a hannunta, bayan tasha maganin ne Khairy ta kwanta, har lokacin bata daina kuka ba ita kadai tasan bakin cikin da take ji, a haka har bacci ya sureta.

Sai can wajen 11am ta farka tana bude ido wani bakin ciki ya dabaibayeta, ashe bacci ma rahama ne? Saidai fa every second of her sleep bakin ciki ke cikinsa da tarin takaici. Da ta tuna yadda sukayi mata sai ta fara wani sabon kukan, dama haka duniyar take ba kowa ke son ganinka cikin farin ciki ba? Cusa kanta tayi cikin cinyarta tana gunjin kuka, a haka Mamin Zaliha ta shigo "Wai Khairy ce taxo da sassafe? Lafiya kukan me takeyi haka?" Zaliha tace "Wallahi bansani ba Mami, tun dare ta shigo gidannan tana wani irin kuka da kyar nasamu tayi shiru na bata magani shine tasha ta kwanta, Khairy don Allah ki fada mana meyafaru?" Cikin kuka Khairy ta soma magana "Mami ashe haka wasu mutanen suke? An wulakantani Mami, haka zan kare babu mai aurena ko? Nasan idan Mama ta gane korata zatayi Babana kuma ya tsine min." Dan rungume ta tayi Mamin alamun rarrashi "Khairy ki saurara kinji? Waya gaya maki babu wanda xai aure ki? Yanzu dai ki fada mana meyafaru? Komai yayi zafi maganinshi Allah." Ta tsaida kukan nata "Da misalin karfe sha daya na dare akwai wani guy da na taba haduwa dashi ya nuna man shi corper ne zuwa yayi ashe cutata zaiyi, kullum muka hadu sai yace man sai na bishi shan ice cream, jiya daya zo na bishi dashi wasu friends dinsa su uku suka taru suka yi min fyade, fyaden cin mutunci suka tullani cikin daji da suka gama suka wullani bakin wani shago suka gudu...." kuka ne yaci karfinta takasa ci gaba wani sabon zafi takeji da radadi a cikin ranta, rarrashinta Mamin ta cigaba dayi kafin Khairy ta cigaba "A bakin shagon nayi baccin wahala don wallahi ko hauka nake bazan fara komawa gida ba, Mama kuwa dama tsine min zatayi sai nasha shi ba iyaka hade da zagi, na gaji da rayuwa dama mutuwa nayi da wannan abun...." Mami tace "Kul na sakejin kin fadi haka..." Khairy ta cigaba "Inaga abinda na shuka ne na fara girba tun yanzu..." Mami ta dago tana kallonta tace "Me kika shuka?" Ta share hawayenta "Mami ay dai kinsan yadda nake da Sultan ko Yarima?" Mami ta gyada kai "Ba yayi aure ba kar dai har yanzu baki hakura dashi ba Ummalkhairy?"  Ta gyada kai "Ban hakura ba ina sonsa Mami, kuma bana jin zan iya hakura, toh shine na dinga kulla makirci kala kala babu abinda banyi ba don ya rabu da ita baiyi ba, wannan abun daya faru dani sak na aika a mata irinsa daren da aka kaita amma sai basuyi mata fyaden ba, sai suka yi recording bayan nan nayita kokarin tarnishing image dinta wai fa don dai ya tsane ta ya rabu da ita amma a banza karshe ma sai yaci man mutunci yace ya tsane ni bazai aureni ba..." ta karasa tana kuka Mami ta numfasa "Tabbas kinsan in har akace hakki toh an gama komai, tabbas hakinta ne yake bibiyarki kuma inaso kisani baki kyauta ba tou shi kishi hauka ne Khairy? Da haka zaki kwaci soyayya? Yanzu da kikayi haka kinyi nasara? Kinga dai tun ba'a je ko ina ba kin fara kwasar kashinki a hannu, kuma muddin baki nemi gafararta ba toh ina tabbatar maki da yanzu kika fara haduwa da bakin cikin duniya kafin ki hadu dana lahira! Dan haka tun wuri ki nemi gafarar wadanda kika cuta saboda basuda hakki a kanki sai kiyi tunani."

Sai bayan sallar azahar Mami ta kwashi Khairy a mota xata maida ita gida ana shiga layin gidan ta fara zufa ihu ne kadai ya rage ta kurma, suna tsayawa Mami ta juyo tana kallon Khairy duk yadda ta tsure sai ta bata tausayi matuka, itadai kawai zata taimaka mata ne "Kinaji Khairy? Ki kwantar da hankalinki, nan ba gidanku bane? A nan fa aka haifeki kika girma?" Nan Mami da Zaliha suka fito daga motar suka jawota da lallashi da ban baki suka samu da kyar tace zata shiga tana tafiya kamar wacce aka ma duka don har yanzu jikinta ko ina ciwo yake mata, suna shiga gidan suka iske Mama bakin kofa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba masifa ce take zazzaga ma Baba kamar wani dan cikinta wainan dole sai ya tashi ya tafi neman Khairy kamar zata cinye shi danye wai ya tashi ya shiga gari neman Khairy, ita kuwa Khairy najin an fadi sunanta take yan hanjinta suka hautsine, "Na rantse da Allah zama bai ganka cikin gidannan ba, namiji dakai sototo wai kai a dole kana cikin damuwa alhalin yarka bata kwana gidannan ba! Itama shegiya gantaliyar banza da wofi na rantse da Allah idona idon Ummalkhairy dan idan na damketa sai dai kila yan sanda ne zasu amshe ta a hannuna, dan ubanta ni zata jama abun kunya cikin unguwa? Ace wai wai katon banza ne ya dauketa cikin mota, gidan ubanwa taje? Na rantse maka da Allah....!" Mama bata karasa magana sai ga Khairy ta kutso kai ta shigo jikinta kamar mazari sai kyarma takeyi cike da tsoro "Ke! Zo nan dan ubanki! Gidan ubanwa kikeji? Gidan wane kato kika kwana? Wane dan iskan ne ya daukeki? An fada man anganki kinbi saurayi cikin dare! Na rantse da Allah yau cikin biyu za'ayi daya, kodai masu wankan gawa su amshe ki hannuna ko kuma yan sanda su kwace ki su mika ki can wurin malaman asibiti dan ubanki!" Kukan kura Mama tayi tayo kanta gadan gadan ta wani shako wuyan Khairy kamar zata kasheta, bata ma lura tare take da su Mami ba ita kuwa sai masifa take yarfa mata, a guje Mami tayo kanta ta shiga kokarin raba su....

Da kyar ta kwace ta tana ta faman bata hakuri da kyar da ji6in goshi ta yadda ta hakura suka kaisu parlor suka zazzauna, ta gefen Baba suka wuce bayan sun gaishe shi shidai kanshi a duke ya kasa dagowa alamun kunya, bayan an natsu "Kamar yadda kuka gani tare muke da Khairy, kiyi hakuri Khairy bawani wajen banza taje ba, tare suke da yar wajena gata nan Zaliha aikensu nayi shine suka tafi yayanta Zalihar mafarin kenan da aka ce anganta cikin motar saurayi, amma dan Allah dan annabi kiyi hakuri dalilin rashin dawowarta gida jiyan naga sunyi dare sheyasa nace su tsaya su kwana gidana da safe sai in maidota har gida kuyi hakuri dan Allah." Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Mama ta sauke "To to ay babu damuwa indai hakane mun gode Kwarai da gaske Allah ya bar zumunci." Baba ya gyara zama yace "Mungode Hajiya Sakina, amma nidai nayi fadan nayi fadan akan yawon yarinyar nan bataji, kullum ina mata fada amma kamar baya shiga Kunnenta zagayowa yakeyi ta bayan kunne, amma babu komai tunda jiya ma tana tare dake ay alhamdulillah mungode da kulawa Allah ya bar zumunci." Tace amin nan suka gama tattaunawa daga karshe Mamar ta mike itada Zaliha suka tafi, har bakin gate ta rakasu sannan ta juyo ciki.

*********

Cikin ikon Allah tunda aka fara ma Sultan magunguna da rubutu yana sha aka dage bil hakki sai gashi ya warke tas, saidai tunda ya dawo daidai yaji baya son ganin Hoodah tsanarta yakeji har baisan ganinta for no reason. 

Ranar wata Thursday sunyi fada sosai har tana tsoron fita parlor su hadu tana daki zaune har karfe goma da kusan minti hamsin, ga yunwa na addabarta ji take kamar ranta zai fita tsabar yunwa ita tsoronta bai wuce su hadu ba idan ta fita, saida da taga har 12 kuma batajin motsin kowa ba sai kawai tayi shahada ta fito kitchen, tea kawai ta hada tayi frying eggs ta zauna parlor tanaci haka nan takeci bawai don dadi ba, ita dai kullum addu'arta Allah ya saka mata cikin gaggawa duk wanda ke son ganinta cikin bakin ciki tana addua'r ya dawwamar dashi cikin kunci har abada. Da rana bai dawo ba sai kawai ta dafa indomie har dai wajen goman dare babu alamun shi, nan ta fara jin tsoro kodai shaye shayenshi ya koma? Tace no ay Kawu na prison ta ya zai cigaba? Nan parlorn bacci ya dauketa can sai wajen daya na dare taji alamun an shigo, zumbur ta mike ta nufi inda yake taga babu alamun maye a tattare dashi, "me kikeyi a nan? I told you several times ki fita harkata wai ke mayyar ina ce? Na tsane ki Hoodah! And for the last time ki fita harkata in ba haka ba sai na farfasa maki baki!" Cikin wani irin kuka take girgiza kai zuciyarta na tafarfasa "Toh wai dole ne zama dani? Nima na tsaneka na tsaneka in baka iyawa ka rabu dani mana!" Cikin wata irin razananniyar kara ya furta "Bazan rabu dake ba! Zama dake yanzu ma na fara!" 

Babu irin kukan da Hoodah batayi ba tasan yana daga cikin dakinsa yana jinta amma ko alamar zai bude kofa baiyi ba, karshe ma bubbuga kofar takeyi akan ya bude kofar ya sauwake mata don gaskiya ita ta gaji da wannan wahalallen auren yau dadi gobe babu, tun tana jin alamar motsinshi a cikin dakin har ta daina, nan ta silale bakin kofar tasa tun tana kukan har bacci yayi gaba da ita. Da asuba sai dai taji motsinshi ko kafin tace wani abu har ya tsallake ta ya fita daga gidan, tunda taga ya fita da wayarshi a hannu tasan bazai sake dawowa ba sai dare yau ma, haka ta wuni cikin gidannan tun tana kiran wayarshi bai dauka har ya koma yana rejecting, gashi bata taba tunanin soyayyar da take ma Sultan tayi zurfi haka ba abun har ya fi karfinta ma.

Wasa wasa har sunyi sati daya a haka tun yana kwana cikin gidan har ya daina a cewarsa baya so yana haduwa da ita baya son ganin koda fuskarta, tasan dai babu inda zaije ya kwana daya wuce sashensu Ummi, tun tana kuka har ta hakura ta fawwala ma Allah lamarin ta koma addu'a sosai ba dare ba rana, duk yar kibar da tayi ta zube ta koma kamar a hure.

Suna cikin sati biyu a haka ne ranar taji motsinsa a parlonta, da sauri ta fito ko dankwali bata sa ba, sai ta iske shi dauke da trolley din kayansa ga kayansa a saman kujera ya watsa, kallo daya ta masa take hawaye suka fara zarya, kana ganinshi kaga wanda yake cikin matsananciyar damuwa amma duk da haka baiyi lalacewar da Hoodah tayi ba. Ko kallon inda take baiyi ba, "Ki hada kayanki na kaiki Agadez...." wani irin duka da kirjinta yayi sai kayi tunanin ce mata akayi ya rasu a hankali ta kama bangon dake gefenta ta rike har wani jiri take gani, sai can taji ya furta "Zanje nayi 10 days a can." Ko jira yaga halin da take ciki baiyi ba kawai ya suri bag dinshi ya fita daga gidan gaba daya sai dai taji ya bude mota....

Sunday, 20 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 20

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 20}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Dedicated to members na YAR AGADEZ your comments are so mua 😘🥰I heart you all❤️❤️



********

Gaba daya ya rasa abinda ke masa dadi, sadness, helpless, confusion, lost sune abinda yakeji a cikin ransa, bai ma san abinda zaiyi da rayuwarsa ba yanzu, Allah ba yadda baya Ikonsa ko a mafaraki bai taba tunanin za'a zo masa maganar aurenshi da Zarah ba, jifa yadda kamar jiya ne yake tsara yadda rayuwarsu zata kasance shida Hoodah, bai taba tunanin al'amarin zai juya haka ba, juyi ya kuma yi a karo na bakwai, haka ya raba dare yana ta faman tunanin gashi yanzu babu abinda kansa keyi sai sarawa, tunda Yasir ya fada masa wannan news din sam bai musa ba especially da yace masa ay Hajiya ce take suggesting ta yaya ma zai soma cewa baya son yarta? Mutanen nan da suka karbe sa a lokacin da ya rasa mafita a lokacin da duiniya ta juya masa baya, saidai shi bai mata wani kallo ba daya na wuce na kanwarsa ta jini wanda ya tabbatar itama haka babu soyayya a tsakaninu. Farko da ya kawo masa shawarar har ji yayi kamar an caka masa mashi a cikin zuciya wai yana nufin ya auri Zarah? Ya salam rasa abinda zai ce yayi da farko sai daga baya ya amince ba tare da ya tsaya wani kwakkwaran tunani ba, Yasir yace masa "Kayi hakuri in har mun maka katsalandan cikin rayuwar ka Ashraf, wallahi we were just trying to help you out of this misery, ina maka addu'ar yasa wannan shine ya zamo sanadiyar samuwar farin cikinka, natsuwa da kuma kwanciyar hankali, na maka alkawari bazaka taba yin dana sanin wannan zabi da mukayi maka ba, amma fa kar ka kwari kanka in har kana da ja akan haka ina so kar kaji nauyin komai ka fito fili ka sanar dani,..." saurin girgiza kai Ashraf yayi "ko kusa banida haufi akan zabin naku, I know Zarah is a good and decent girl, she's well mannered and respectful, tanada nutsuwa da hankali nagode da wannan karamci da kauna da kuka nuna min saboda sai ana sonka za'ayi maka wannan, nagode nagode inaso ku bani dama naje gida na sanar ma da Abba..." Yasir cikin matukar farin ciki yace "Alhamdulillah nine da godiya tunda har ka amince da wannan kudurin namu kaga ko ba komai zumuncinu zai kara karfi, sannan kuma Hajiya zatayi farin ciki sosai da amincewa da kayi, mun gode abokina, amma ya kamata ku kara fahimtar junanku sosai, duk da dai naga Zarah na yawan zarya zuwa kawo maka abinci a nan..." ya fada cikin zolaya Ashraf yayi dariya "Hakane kawai tana tausaya man ne..." yace "Ay kai din abin a tausaya maka ne saidai banaso ina yawan tuna maka da batun don nidai burina bai wuce ka dawo normal ba and move on..."

Sultan yayi murmushi kurum, Yasir yace "So do you like my sister Zarah?" Ya fada yana taba masa kafada da tasa kafadar yana kashe masa ido, tashi yayi ya fita daga dakin "Yasir ni na fita na lura so kake kasa ni a gaba da safen nan!" Yasir ya bishi yana dariya "Sai ma ranar tukunna."

******

"Dama tsanar da Umma tayi man ta kai har haka? Har zata iya nema ta kashe mutum? Ko ta nemi ta tarwatsa ni because of a so called kishi! Kishin ma tanayi ne da wacce batada rai! Tayi enough I will not spare her!" Ta fada tana nufar Kawu a fusace "Kawu! Meyasa ka biye ma Umma? Bakasan ko wace irin mace bace? Zata kai ta baro ka a banza! Baka kyauta ba! Uncle your own flesh and blood? Kawu why?" Nan take ya fara dana sani jikinshi ya fara bari kafin kace me Sultan ya kira masa yan sanda, nan da nan suka iso suka ja shi yana ta faman bashi hakuri, amma ina Sultan ya zuciya yace "Mu hadu a kotu Kawu! Sai na dauku fansar abinda kayi wa iyayena! Macucu mugu azzalumi!" Da kyar Hoodah ta dinga dragging Sultan suka tafi sashensu suna zuwa ya jawo ta yayi hugging sai ya sakar mata kuka, itama take ta fashe da kukan sun dauki tsawon lokaci a haka, shi ya fara janyewa yayi scooping fuskarta "You dont have to worry, zan hukunta Umma duk abinda tayi kinji?" 

**********

2 DAYS LATER 

Wasa wasa daga magana Sultan ya fara kissing din Hoodah "Hoodah every girl you see pass this stage kafin ta zama cikakiyar mace, you're going to be okay kinji?" Hijab din ya yaye mata, ita kuwa gaba daya hankalinta ya fara tashi, zuciyarta kuwa kamar ta bar kirjinta, a hankali Sultan ya daina ganin fusakar Hoodah, ya fara ganin fuskarta duk gashi kamar dai ba mutum ba, ba zato taji ya turata da karfin bala'i yana nunata jikinshi har wani rawa yakeyi, "Who are you?! Karki matso inda nake kar ki kasheni!" Turus ta tsaya tana kallonsa tace "Ni? Sultan Hoodarka ce fa what's wrong with you?" Ta fada tana matsawa kusa dashi wata irin kara ya fasa wane zai fasa mata dodon kunne, take ya runtse ido ya takure wuri daya yana makyarkyatar sanyi, anan ne ta fahimci kamar hankali baya jikinshi, tashi tayi a sanyaye ta fada bathroom tayi wanka ta kimtsa jikinta, ta fito, haka daren nan bata rintsa ba dan a takaice ce Sultan kamar mai ta6in hankali ya koma ya dinga wasu misbehaving dai haka kamar bashi ba... Idan ta kalleshi saita ga ya takure jikinshi wuri daya ya kura mata ido, matsawa tayi kusa dashi a hankali ta ta6a shi sai ta ga baiyi wani yunkurin hanata ba amma dai da ka kalleshi kasan babu lafiya, a hankali ta dora kansa bisa cinyarta ta dinga dan shaffawa, idan bacci ya kwashe shi na kamar minti biyar sai ya farka a firgice yana neman guduwa, sai ta damko shi da kyar take samu ta tofa masa addu'oi sannan sai ya natsu, babu abinda takeyi sai innalillahi wa inna ilahir rajioon, wai meke shirin faruwa dasu haka? Sai bayan sallar asuba bacci yayi gaba da ita. 

Bata ma san yadda akayi tayi baccin ba saidai ta farka ta dakin babu kowa, a rude ta mike ta leka bathroom taga wayam, can ta ganshi a kitchen kasa dirshen yayi kuri da ido kamar mai tunani, yana ganinta sai ya fara kacaniyar mikewa a rude, nuna ta yakeyi da hannu "Kar ki matso inda nake tsoron ganinki nakeyi." Yana fadan haka ya fice da gudu daga dakin yana zuwa dakinta ya danna lock, da gudu ta bishi babu abinda takeji sai watsi da abubuwa nan ta rude ta dinga kwala mashi kira tana bubbuga kofar da karfin bala'i, da gudu ta fita waje neman taimako sai ga dogarawa sun biyota a guje nan suka bude kofar da kyar a razane suka ganshi yadda yake fasa kwalaben turare duk yaji ciwo dashi, dogarawan nan sukayi kansa suka fara kacaniyar rike shi kafin kace me sun damke shi nan ta sa aka nemo mata family doctor dinsu, kafin ya iso an kimtsa dakin ko ina sannan sun kwantar dashi kan gado suna rike da shi don kar ya gudu, hijab dinta ta sanya jin sallamar Doctor din nan taje ta shigo dashi ya soma duba shi, shidai a iya bincikensa yace mata babu abinda yagani yana damunshi don haka baya tunanin maganin nan na asibiti ne su nemi malami ya duba shi, iyaka dai allurar bacci yayi masa ya fita.

Bayan yayi bacci ta sulale kasa kawai sai ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, tana nan a haka har akayi azahar da kyar ta samu ta lallaba ta shiga ta dauro alwalla, wai meke faruwa dasu? Duk sadda suka samu farin ciki da kwanciyar hankali sai wata fitinar ta bullo? Tana sallah tana kuka tana fada ma Allah. Addu'a ta dukufa yi tana kai ma Allah kukanta.

*****

Banko kofar tayi tana shiga ta iske Hajara da huci ta shiga, "Kin cuce ni Hajara sam ba abinda nakeso ba kenan! Ya zaku maida sh kamar wani mai tabin hankali?" Hajara ta sheke da dariya "Toh kila dai bakiyi yadda aka saki ba kin kuskure!" Tace "Ni ban wani kuskure ba, nayi duk abinda aka sani nayi, kawai dai cutata akayi! Kuma wallahi sai an biyani duk abinda na kashe!" Tsaki Hajara tayi ta ta6e baki haka Khairy ta fita fuuu a fusace. 

Misalin karfe goma na dare Khairy ta dawo daga yawon gantalinta daidai wata kwana wata makekiyar mota tayi parking, sauke glass din motar akayi wanda ke mazaunin gaba ya washe baki "Su Khairy yan mata." Nan ta ganeshi wani guy ne da ta taba haduwa dashi har ya bata dubu 10 ranar yace mata ay service ya kawo shi garin, ta washe baki "Yan samari tunda har yanzu kaki bari nasan sunanka ba." Yayi dariya "Wannan ay ba matsala bane, gashi kuwa yau nazo daukarki muje shan ice cream kamar yadda nayi maki alkawari rannan. Ya zakije din ko kuwa?" Matsowa tayi daf da motar tana gyara daurin dankwalinta "Babu matsala amma dai ba zamu dade ba ko?" Yace "Ah no bazamu dade ba sharp sharp mun dawo." Ta bude motar tana shiga kenan sai ta ga ashe kusan su hudu ne cikin motar yace mata ay abokansa ne, sunyi nisa a tafiyar kenan taga sun sata a tsakiya sun mata wani irin mugun dauri, nan suka ma motar lock, a razane ta dago "Lafiya? Me zakuyi man?" Ay tuni jikinta ya fara karkarwa a take ta kara rudewa yadda ya kara gudun motar, wani irin kuka ta fashe dashi a motar, shure shure Khairy ta fara yi tunda daya ya zabga mata wani irin marin da tunda aka haifeta ba'a taba mata irinsa ba, take wuta ta dauke mata, bata kara sanin inda take ba saidai ta farka ta ganta bayan gari cikin dokar daji, sun kulle mata kafafu da hannuwa sun zagayeta suna kallonta cike da sha'awa, wata irin razananniyar kara ta saki mai rikitarwa ta fashe da kuka, kallonsu takeyi tana girgiza kai hawaye kuwa kamar an wanke mata su a fuska, kyarma ta farayi inda ta kasa koda kwakwaran motsi, wayyo Allahnta yanzu wadannan fyade suke shirin yi mata? Daya ne ya nufota gashi yana faman daga riga wani gunjin kuka ta saki zuciyarta ta harba kamar ranta zai fita, dama haka bakin ciki yake? Haka kunci da rashin sanin madafa yake? Duka rayuwarta ta taso tana abinda taga dama sai gashi ta zama hopeless a yau ba tada wani kata6us, "Ku taimaka man! Don Allah ku kyaleni kar ku cutar dani ba haka mukayi daku ba!" Kuka take har kasan ranta kyalle suka cire suka kulle mata baki dashi, sanann suka damke ta suka daga mata riga har zuwa cibiyarta haka samarin nan kusan su hudu sukayi nasaran raping din Khairy....

Saturday, 19 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 19

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 19}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Murda kofar tayi ta shiga tana wani cika tana batsewa, kallon gidan ta fara yi da wani expression na rainin wayau, nan tayi tsaye ita batayi sallama ba ita bata ida shiga ba, tafi minti biyar a nan tana kare ma gidan kallo tana wani tauna chewing gum, bayan minti kusan uku sai ga Hoodah ta fito daga daki da alama sallah ta gama dan ga carbi nan a hannunta tana azkhar, da mamaki ta tsaya tana kallonta tace "Ah bakuwa mukayi? Ya kika tsaya a nan ki shigo ki zauna mana, sorry banji sallamanki ba ina ciki ina sallah." Khairy ta wani yi mata kallon uku saura kwata ta shigo tana wani yauki ta samu wuri ta zauna ta dora kafa daya kan daya tace "Tooo bakiji ba? Alright ba matsala mai gidan na ciki?" Da mamaki Hoodah ke kallonta "A'a baya nan, lafiya kike nemansa? Sorry ban gane ki ba?" Khairy tayi wani murmushi "Of course bazaki ganeni ba! Tunda kin shigo inda baki chanchanta ki shigo ba..." Hoodah da lokacin ta fara gane wannan bada arziki ta zo mata ba tace "Excuse me? Anya kinsan da wa kike magana? Who are you da xakizo gidan mutane kina masu isa?" Khairy ta tabe baki "Gidan mutane? It's supposed to be my house not yours! But you snatched it away from me! Kin kwace mun masoyina and now you are calling this your house?" Hoodah tace "Ohh na fahimce ki if am not mistaken kina nufin kece wadda Sultan ya kamata ya aura bai aureta ba ya aure ni?" Khairy tace "Of course am the one! You are the reason am in pain now, I have done everything possible to separate you but to no avail! Wai wane irin asiri kika yi masa? Nace wane barbaden kikayi masa har ya kasa rabuwa dake? I was his first love! Mun tsara duk yadda rayuwarmu zata tafi amma rana daya kika rusa mana farin ciki! Why Hoodah!?" Hoodah tace "Na rusa maku farin ciki? You must be joking ni na auri kaina? Shida ya auro ni shi zakije kiyi ma haushin nan da kikeyi kamar wata karya amma ba ni ba! Bakida labarin shine yaje har garinmu ya auro ni? So please banida lokacinki I have things that are more important to do zaki iya tashi ki fitan man daga gida," Khairy ta kule ta mike tsaye "Toh bari kiji in gaya maki! I will not rest sai na fitar da ke daga gidannan, baki isa ba, duk wanda nayi a baya baiyi working out ba though dai na fara cin nasara, amma zaki sha mamaki yadda zanyi dake sai kin raina kanki!"

Hoodah ta mike tsaye har wani 6ari jikinta yakeyi, so itace ta dinga plotting against against her kenan? Itace ta nema tayi tarnishing image dinta a banza duk da sunan kishi? Toh wai kishi hauka ne? "And sai da kika gama bata ma kanki lokaci kikaga plan din naki yayi backfiring? Ke bakisan zuwa da kikayi nan ba kinyi downgrading kanki? Kin kaskantar da kanki! And let me tell you something I am glad  naji dadin makirci da kika kulla you know why?" Tafada tana nufar inda take tana kallon cikin idonta "Because duk Abinda kika shuka every single plan of yours has drawn us closer to each other, relationship dinmu ya gyaru, so ina fatan zakije ki sake shuka wani makircin? Kuma ko me xakiyi bazai tasiri ba cuz Sultan yayi trusting dina more than he had ever trusted anyone! And also da yake banida hakki a kanki sai gashi kin kawo kanki da kanki kin tonawa kanki asiri, dama I have been looking for you, cuz na fara ganowa is all a plot! Abbi ma yana ta fafutar bincike a kanki sai gashi yau kin kawo kanki wow Alhamdulillah! So wama kike da suna? Do you think I will let you go so easily? Kin yi karya sai na dauki fansar abinda kikayi man!" Wani damka Hoodah ta kai mata a fusace sai yanzu ma anger din tate ke sake haye mata, tana tuna what she went through all because of this witch! Wani irin duka Hoodah ta kai mata, take Hoodah karfi ya kara yazo mata ta dinga dukanta ta ko ina ta fuska ta ciki, ba abinda Khairy keyi sai ihu tana dana sanin kawo kanta da tayi,  "You witch! Har kin isa? Baki san ko ni wacece ba da har xaki neme ki shigo man gida! How could you do this to me?" Take bayi suka fara shigowa ba abinda suke sai rokon Hoodah akan ta kyaleta! "Gimbiya don Allah ki kyaleta have mercy on her!" Hoodah ta dago a fusace "Jeki kira wanda ke tsare da dungeon!" Da sauri ta fita nan Khairy ta tsorata ta fara bada hakuri "You have the audacity to ask for my forgiveness, kina tunanin da boka na dogara? Ke har kinyi tunanin kafin nayi wining Sultan har sai na hada da boka? Never! Sai dai idan kece zakibi bokaye da malamai don a karkato maki da hankalinsa, you are very stupid! Wallahi duk garinnan babu wanda zai tsaya maki idan na kulle ki! Ni dai kika nemi bata ma suna ko? Toh naki sai ya linka nawa sau dari! Ke har wani abu ma ya gani a jikinki da har zai ce yana sonki? Kalleki fa wata kucaka da ke! Kazama! Har kina tunanin zaki goga dani? Kinyi karya!" Hawaye ya fara shatata da idanun Khairy a matukar tsorace tace "Don Allah don annabi kiyi hakuri wallahi sharrin shaidan ne just spare me wallahi bazan sake koda kallon Sultan ba bare har in masa wani kallo da idon soyayya! Please believe me princess na tuba." Ta fada tana tsugunnawa bisa gwaiwarta alamun roko ta hade hannayenta wuri daya. Hoodah na rike da kwalar rigarta tayi murmushi "I will not fall for your trap you witch! Ke kika kawo kanki ina nemanki ma bare kuma yanzu da kika kawo kanki har taya kike tunanin zan barki ki tafi? Never! Allah ba azzalumin bawansa bane!" Khairy ta dinga gunjin kuka.... Sultan ne ya shigo turus ya tsaya yana kallon abinda yake faruwa "Hoodah! Lafiya?" Tana ganinshi ta saki Khairy wurinsa ta nufa idanunta cike da hawaye tace "Itace take neman tarwatsa farin cikinmu she's the one sultan, she has been plotting against me don ka tsaneni!" Ya juya yana kallonta take yabude idanunsa a waje yace "Khairy? You? Dama duk kece kike hadani da matata Hoodah!" Da sauri ta mike tana tangadi "Sultan ni ya kamata na zama matarka! Remember we used to love each other...? Kar ka gujeni kasan ina sonka kuma kaima nasan kana sona, kar ka bari wannan ta rabamu nice kakeso please Sultan..." hannu ya daga mata "Shut up! Haka ake so? Dama shi so zaka iya hurting wanda kakeso? You hurt me several times Khairy and now you're claiming you love me? You must be joking!" Ta nuna kanka "Ina sonka Sultan! Duk abinda nayi saboda kai nayi shi, don ka rabu da ita ka dawo muyi aure nasan nice wacce kakeso remember wannan kawai hada ku akayi?" Ya mata wannan irin mugun kallo "Let me tell you something no matter yadda kike kishi bazaki aikata abinda kika aikata ba, Khairy ba sona kike ba obsession ke damunki! And kinga matata Hoodah I trust her more than anything else in this world! Ina so kisa wannan aranki, your plots and tricks will not work on us again! And bari na fada maki magana ta karshe ki fita harkata nagane bakida hankali bakida wayau! Ni kuma bazan iya zama da mace irinki ba! I hate you Khairy I hate you! And now leave my house kuma ki fita harkata don idan nasake jin kinyi wani abun kuma you will regret ever being born! Guards! Zo ku fitar da mahaukaciyar nan daga gidana ko shadow dinta kar na kara gani a kofar gidannan! Kuyi mata bulala hamsin sannan ku bata kashi yadda ko tafiya bata iya yi, kafin ku barta ta tafi...." Wani irin ihu ta kurma "No Sultan kar kayi man haka! Kasan ina sonka!" Haka aka fiddata daga sashen kamar mahaukaciya!**

Da kyar take jan kafa tana tafiya hawaye na wanke mata fuska, a duniya zata iya daukar komai amma banda wulakanci, wulakancin ma daga masoyinta a gaban matarsa matar da tafi tsana duk fadin duniya itama meya kaita? Ay saida kawarta tace mata kar taje amma ta kafe ay ga irinta nan yanzu da wane ido zata kalli kawar tata ji yadda aka farfasa mata fuska da baki duk ya kumbure, ido duk yayi baki, she was heartbroken and miserable, meyasa zai mata haka she thought he loved her ashe ba haka bane? Is he dumb or something? Ta ya zai ma fara rejecting dinta yama san kuwa yadda take? me waccan tsinanniyar zata gwada mata in banda sarauta? She cannot tolerate this bullshit, kwankwasa kofar gidansu Hajara kawarta tayi, tana budewa sai tayi tsaye sakaka tana kallonta "Ke lafiya? Meyafaru dake?" Ta gefenta tabi ta wuce ta tafi parlor ta zauna tana huci, bin bayanta tayi da hanzari tana zuwa sai Khairy ta fashe da kuka "Yau bakiga dizgin da akayi man ba Hajara! Yau ni Sultan zaici mutuncina?" Hajara ta kyalkyale da dariya "Maganinki kenan! Ay saida nace kar kije kika kafe ay ga irinta nan!" Tana fadan haka ta nufi kitchen ta dora ruwan zafi ta dauko karamin towel, tana fara danna mata towel din data zunduma wani irin ihu kamar ana cire mata rai ita kuwa Hajara babu abunda takeyi sai dariya, "Gobe ma ay kya kara sannu mai masoyi, da kinbi shawarata ay da ba'a kai haka ba nace maki shi irin wannan bakayin haka ay, yanzu gashi nan banda ma haka kinje sun gane abinda kika shuka kuma ke a tunaninki a iya dukan nan abin xai tsaya? You are wrong ay kin kai kanki yarinya!" Tsawa ta daka ma Hajara "Da Allah ya isa haka! Wallahi bawai na daina bane ni wannan karon ma abinda xan mata sai yafi wanda nakeyi a da! Sai na dauki fansa sai ta raina kanta wallahi!" Hajara tace "Nadai fada maki you should be careful in kunne yaji?" Da haka ta cigaba gasa mata jikinta in banda ihu babu abinda takeyi.... ita kuwa ta kuduri sai tayi destroying life din Hoodah ko ta wane hali ne.

********

Bayan sallar isha'i Sultan ya shigo gidan fuskarsa cike da annuri da murmushi, direct dakin Hoodah ya shiga yaga ta zauna jugum alamun tana cikin damuwa, saboda a fuskarta ma ya nuna hakan, a hankali ya zauna kusa da ita saida ya rike hannunta ma tasan ya shigo dakin. Share hawayenta tayi ta juyo tana kallonsa "Habibty meya faru? Ko abinda ya faru dazu ne kike ma kuka?" Tambayar da yayi mata kenan hade da rungumota ta gefe fuskarta cike da damuwa, duk sadda yaga Hoodah cikin damuwa sai yaji zuciyarsa bata masa dadi ko kadan, balle ma yanzu daya fara fuskantar feelings dinsa akanta duk da yasha karyatawa ya kasa yarda, ba karamin tausayinta yakeji ba, "Sultan am scared..." sai kuma ta fashe da kuka, hugging dinta yayi "Haba Hoodah, why would you be scared when I am always here with you? You have me in your life kuma I will be there for you, you have Abbi and Ummi, you have your Abba, kuma kisani babu wanda ya isa yayi maki komai sai abinda Allah yayi maki, as I told you before I trust you Hoodah no matter what babu wanda zai sake shiga tsakaninmu again, then meyasa zaki ji tsoro? Dont be scared you have me to protect you always." Da kyar tayi shiru jawo hannunta yayi suka parlor nan taga ya siyo masu kaza da yoghurt sai ice cream, bayan sun kammala ya ja hannunta suka nufi daki yana ta faman tarairayarta lallabata.

*********

Buga kasa yayi yana shekewa da dariya "Meke tafe dake?" Ta gyara zama "Wannan da kake gani kawata ce malam, akayi mata kwacen saurayi toh duk tayi iya abinda xata iya na ganin ya dawo hannunta abun ya ci tura, shine nake bata labarinka aikinka kamar yanka wuka yake, nace da kayi anyi angama shine mukeso ka taimaka malam a dawo mata da saurayinta hannunta...."  malamin wanda baya da maraba da boka ya sheke da dariya "Za'a iya haka, saidai ina fatan kin mata bayanin yadda nake aikina?" Tace "Na mata bayani tace zata iya..." yace "Toh yanzu me kukeso ayi mata? A kasheta? A haukatar da ita? Ku fada da kanku!" Khairy tace "Nidai malam so nake asan yadda akayi ta rabu da shi, kawai nidai burina su rabu ko ta wace hanya ce" mikewa yayi ya juma can sai gashi ya fito da wasu kwalabe da kullin magani "Wannan kwalbar zaki amfani da ita ki sha kafin ki sha zaki ambata sunan shi saurayin naki sau uku..." zaki ga result mai kyau, Wanann kuma zakiyi wanka dashi kwana uku, dayan kuma sha ne da madara kwana 7..." tace "Malam mungode..." nan ya umarce ta data tashi ta bishi cikin dakin haka ta bada ajiyar jakanta ta mike ta bi bayansa, wa'iyazubillah Allah kasa mufi karfin zuciyarmu.... sun dauki lokaci sai gasu sun fito nan suka bashi kudinsa sannan suka tashi suka tafi....

*******

Sultan ne ya fito daga sashensu, a hankali ya tsaya ta window jin kawu yana wasu yan maganganu

"Wallahi Hajiya Karimah bana tunanin duk abinda muka tsara fa yana aiki, ni gani nake ma kamar kara tsunduma wa suke kogin son juna, the more muke son tarwatsa su the more suke son kara kusantar juna...." yayi kwafa "Tou  bazamu ce da sauki ba amma gaskiya suna can jikin dai gashi nan sai a hankali...... wallahi nayi duk abinda kika sani kawai dai akasi aka samu..... yanzu meye mataki na gaba da xamu dauka?...... ina jinki..... Toh shikenan zan kiraki zuwa gobe...... ok.... sai anjima...." wani irin tafasa zuciyasa keyi baisan lokacin da ya kutsa kai cikin harabar ba idanun nan jajir Kawu na ganinshi kawai sai ya saki wayar ta silale kasa ya mike, Sultan tsaye yayi yana kallonshi da hawaye a idanu "Kawu? So is all you all along? You of all people? Dama haka kake?" Ya fada yana nufarsa tare da damko masa wuyan riga ya hada shi da bango sai da kansa ya kume yabada wani kummm! Girgiza shi ya shiga "Dama kaine kaso kashe Abbi da Ummi! Kawu kai? Your very own blood? Kai da waye kuka hada baki kuke aiwatar da aikinku?" Ya sake kai masa kai a bango shi kuwa Kawu harda wata yar kara, "Step mother din Gimbiya  ce, Umma...." karar wani abu sukaji suna juyawa sukaga Hoodah ce rike da tray da cup na glass ta sake su baki bude tana kallon Kawu, tace "Umma?"

Friday, 18 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 18

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 18}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



This page is for you Aunty Sadiya aka Sadnas😍❤️



Tsaye yayi yana kallonta tayi hanzarin tashi tsaye takamo hannunsa gam gam yayi ta kokarin fizgewa amma ina ya kasa, janshi ta dinga yi har daki tana wani irin gunjin kuka, kwantar dashi tayi kan gado ta tsugunna ta soma cire masa takalmi da socks ta kaisu mazauninsu socks din ta sanya masa a basket din wanki, zama tayi dirshen kasan gadon ta dinga rizgar kuka, irin kukan nan mai cin rai ga mai sauraro, tun yana wasu surutai da bata gane mai yake fada har bacci yayi awon gaba dashi, a nan inda take ta dora kanta bisa gadon tayita kuka, daren ranar ba irin kukan da Hoodah batayi ba a haka itama tayi bacci tana faman ajiyar zuciya.

Sai can angama sallah Sultan ya bude ido, wani irin sarawa kanshi yayi ya dafe shi ya mike da kyar yana dafe da kai, mikewa yayi yazo yi sai yaji Hoodah bisa kafarsa wani irin mummunan faduwar gaba yaji, nan ya fara mamakin ganinta a nan meya kawota nan har ta kwanta? A hankali ya daura hannunsa bisa bayanta ya ta6ata Hoodah ta bude idonta, kallonta ya tsaya yi take ta kauda fuskarta gefe sannan ta mike ta fita daga dakin, tou meya faru haka? Ya tambayi kansa, wanka yayi yayi sallah, har ya gama kimtsawa yaga Hoodah bata dawo ba, fitowa yayi ya zauna kan dining har kusan awa daya shiru babu Hoodah babu alamunta, a cikin kitchen ma baiji wani alamu ba tana ciki ba abun ya bashi mamaki ya tashi ya leka kitchen don ya tabbatar yasan bata wasa da girki ko cikin wane hali take duk da ba wani ci yake ba amma still tana yi masa. A hankali ya taka zuwa dakinta yana bude kofa ya ganta ta rakube kan gado kamar mai jin sanyi tanata kuka kamar ranta zai bar jikinta. Daga farko gabanshi yayi wani mummunan faduwa don yayi tunani kodai su Abbi sun rasu? Sai dayaga kukan nata yanada wata manufa don tana kuka tana magana ne ita kadai, "Sultan why? Meyasa zaka maido man da wasu abubuwa da suka faru a baya? Idan naga Umma na aje kwalbar nasan definitely sha takeyi don ko Abba baya gari tana sha na sha kamata ji nake kamar na dauki wuka na caka ma kaina kowa ma ya huta, tun tana yi a boye har Abba ya ya gano ta saidai kuma ba abinda ya iya yi a kai, a hankali mutane suka fara fuskantar halin da ake ciki surutu kam ba irin wanda bamu sha ba, gashi Abba bai wani damu ba sai yace ay rayuwarta ce babu ruwan kowa, sai yanzu danake tunani na wuce wannan matakin zaka maida ni ruwa tsundum? Ya zakayi man haka? Indai muna tare wata rana zamu haihu! Me kake so na fada wa yayanmu a kanka? Ince mahaifinsu bai daukar kaddara ko kuwa dai raunin imani ne akan duk abinda ya same shi? Idan bakayi tunanin feelings dina ba ay kayi tunanin na Abbi da Ummi, Abbi Ummi i have failed you ko ba ku fada ba nasan kun bar amanarsa a hannuna, your Sultan is into drugs innalillahi wa inna ilahir rajioon...." bata karasa magana ba taji an rufe mata bakinta da hannu gabanta ya bada wai ras, fargaba da nadama da tsoro ne kan fuskanshi, yanzu me zai fadawa Hoodah? Yasan bai isa ya karyata ba kuma, take ya tsaya wani tunani da karfi ya furta "Kawu!" Ta dago a hankali tana kallonsa tace "Kawu?" Ya girgiza kai wane karamin yaro, tace "Me yayi maka?" Yace "Shine yake bani drink din." Tayi shiru tana kallonsa what the hell? "Kamar yaya shi yake baka drink? Kai karamin yaro ne zai baka drink ka karba? How?" Yayi shiru "Wallahi nima bansani ba, I don't know why duk sadda ya bani ban iya masa musu, kuma na kasa fada maki har kagara nake naje ya yabani I don't know what's happening to me," shiru tayi kafin tace "Innalillah wa inna ilahir rajioon kawu Murtala fa? Your uncle? What's happening?" Shiru ta kuma yi "Definitely something is fishy, Kawu Murtala? I don't think dan Allah yazo akwai abinda yake shukawa cikin ransa, in ba haka ba how on earth zai maida kai mashayin karfi da yaji? Innalillahi." Sultan yayi shiru shi dama can bawani bonding yayi da shi ba cuz shi ba'a nan yake rabin rayuwarsa ba, so bai wani san halinsa ba "Bansan me yake nufi damu ba, but I found myself wanting to drink more idan yabani, but now I am glad da na fada maki." Tace "Ya zama dole mu gane motive dinsa, we have to keep a close eye on him, Sultan ya xama dole ka dinga lura da shi koda yaushe, he must be up to something bad, we don't know but the sooner we find out the better for us all, ina ji a jikina so yake yaga bayanmu, karka sake ka nuna masa wani abu har sai mun gano what he's up to." Gyada kai yayi wane karamin yaro mikewa tayi tana share hawaye "Bari naje nayi breakfast." Tana fadin haka ta fita daga dakin, zuciyarta na mata wani irin zafi tana kuna, what's going on here? How can his own uncle harm his own son? Wai me duniya ta zama yanzu? Ace dan uwanka na jini shine yake so yaga bayanka? Kai innalillahi wa inna ilahir rajioon, gaba daya illahirin jikinta baya mata dadi a daddafe ta gama hada masa simple breakfast tana share hawaye tana aikinta har ta kammala, bayan ta gama jera komai bisa dining ta gyara gidan tas ko ina sai kamshi ke tashi, dakinta tanufa to her surprise sai ganin Sultan tayi kwance sai baccinsa yake, murmushi tayi ta ja masa bargo tarage masa sanyin ac, daga nan ta shiga bathroom tayi wanka, har saida ta gama shiryawa tana zaune gaban mirror gaba daya ta fada duniyar tunani, kamar daga sama taji anyi hugging dinta ta baya, firgit ta dawo a hayyancinta, ta cikin mirror suke kallon juna sai can ya fara magana

"Hoodah, nasan tunda kika sa kafa kika shigo gidannan babu abunda nake kunsa maki sai tarin bakin ciki da damuwa... don Allah kiyi hakuri forgive me..." hannu tasa ta rufe masa baki "Karka ce haka..." abinda ta fada kenan sannan ta mike tsaye baki daya, juyowa tayi tana kallonsa, tana jin different feeling yana kara ratsa kirjinta, wasu hawaye ne suka gangaro mata, can sai ta goge hawayenta ta nufi bakin gado zata zauna, saurin riko mata hannu yayi "Hoodah ki bari na bada hakuri once and for all, ki bari na baki hakuri, nasan nayi hurting dinki beyond major, na kunsa maki bakin ciki kala kala da kunci nasan kin tsaneni amma ni kuma Hoodah na tsani hawayenki, your precious face is not for tears, kiyi hakuri Hoodah na maki alkawari bazan kara ba, no matter what zaiyi man bazan karba ba, kiyi hakuri ki yafe mun..." ganin jikinta yayi sanyi ya sa ya jawota kan gado ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyarsa ya juyo da fuskarta tana fuskantarsa ga hawayenta da ta kasa controlling ta fara magana "Nasan da ciwo dole yadda ka saba da iyayenka kasan dadin mahaifiyarka ka soma tagayyara, duk da bawai rasa su kayi gaba daya ba, kawu yayi using weakness dinka ya cimma wata manufa tasa, abinda kawai zan fada maka nasan is not your fault amma Sultan ka zama mai tawwakali... toh amma fa wanda ya rasa nasa daya daga cikin mahaifansa fa? Wasu ranar da aka haifesu, wasu sai sun fara girma sun fara sanin dadin mahaifansu kuma su sai su kashe kansu? Ni da kake gani ban taba sanin dadin uwa ba, lokacin da Abbana ya kara aure nayi zaton zan samu wacca zata zama tamkar uwa a gareni ashe ba haka bane, she is the most wicked step mother ever, idan naga yadda Ummi ke tarairaiyarka sai inji dama nice kai, nasan your parents are the best amma wannan ba excuse bane da zaka biye ma kawunka har ya jefa ka hanyar banza, yanzu idan yace ka shiga wuta sai ka shiga? It's not healthy, bai chanchanta ba aga yadda ka fito daga gidan girman kaifa dan sarki ne baka tunanin it will tarnished your image and reputation? You are a respectable man wallahi gara ace ma hawan jini ne ya haye maka kana zarya asibiti akan sunanka dana iyayenka dana danginka gaba daya ya lalace har abada ko ka daina yi, wannan tabon na nan bazai ta6a gushewa ba, Sultan da haka nake rokonka kayi man alkawari bazaka sake yarda ba koda wasa ka karba kasha no matter what?" Hugging dinta yayi sosai kamar za'a kwace masa ita yana jin wani sanyi yana bin sako da lungu na jikinsa, shidai yana son yadda take masa magana cikin kwanciyar hankali da fahimta, so cool and calm ba hargagi babu masifa, yace "I promise you Hoodah." Wani kiss yayi mata a kumatunta a hankali ta janye jikinta ta mike tsaye ta fita daga dakin tana murmushi, a hankali shima ya mike ya bi bayanta da murmushi shimfide saman fuskarsa.

Sun gama breakfast suna zaune kan dining yayi gyaren murya yana kallonta ta dago ido irin lafiya dinnan? "habibty dazu najii kince yaranmu zaki bani ne?" Yadda yayi kamar on a serious note, take wani irin tari ya sarketa saida tasha ruwa ta natsu kafin ta dago tana kallonsa "Ya da chanza man suna? Sultan yau kuma Hoodah dince bazaka iya kira ba? Kodai yan shagwabar ne suka hau kai?"  Ita dai burinta bai wuce ya manta da maganar nan ba, "Ohh that, I find it cute to call you with it ya mugun dacewa dake, back to babies kin shirya bani su ne? Ko twins ma ko?" Idanu ta zaro waje ta mike da sauri ta fara tattara plates din da suka yi amfani dasu tana kaiwa kitchen, saida ta gama kaiwa kitchen kafin ta fara wanke wanken dole harda abunda bai kamata ta wanke ba, wata ajiyar zuciya ta sauke ganin bai dining "Ikon Allah Sultan yayi tunanin bashi amsar nan?" Kamar daga sama taji anyi hugging dinta ta baya ana sauke mata kisses bisa kanta, kyarma ta farayi "Eh mana so nake ki bani amsa, kodai don bakisona sheyasa bazaki haifa man baby ba? Kinga idan su Abbi suka warke saidai su dawo su ganki da jikansu a hannu." Da sauri ta fara kwace kanta "Sultan baka gani aiki nake? Kuma fa ya kamata ka tafi ka duba babu wani aikin daya kamata ka fara yi a can haraba? Kaje ka duba kagani." Sai neman zillewa takeyi daga jikinsa amma yaki sakinta harda nade hannunsa a kungunta. "oh my God Hoodah! Bakyasona kenan?" Yayi kamar tayi hurting dinsa cikin hanzari ta fara girgiza kanta "A'a ina sonka... ahh bana sonka, ya ilahi Sultan!" Sai kuma ta fara dukan chest nasa ganin sai dariya yake mata yadda duk ta rude ta rasa ansar da zata bashi... "Toh shikenan a barshi a kinasona, ni gaskiya babies nakeso at least 20." Ya kama hannayenta duka biyun yadda ta rufe idanunta alamun wai taji kunya, dariya yakeyi kasa kasa "20? Haba Sultan so kake in mutu?" Yayi dariya "Idan kin mutu sai na auro wata tazo ta haifa man." Tace "La la toh jeka aurota tun yanzu ni bazan haihu ba." Yar dariya yayi "Yi hakuri matata Hoodah, tou yanzu dai ya za'ayi da babies din? Sannan ashe ana kishina haka? Haha maida wukar daga ke ba kari kece amarya kuma uwar gida." Yafada yana mata kiss gefen bakinta "Nifa ka kyaleni am too young for all of this, kai you're even lucky daka sameni ka samu carbi sai ka gode ma Allah gaskiya..." ta fada tana jefa masa hararar wasan ta juya da niyyar komawa don cigaba da wanke wankenta. "iyye! You're too young ko? Yarinya xakiyi bayani wallahi, yanzu dai tunda na daina abu saboda ke what's my gift?" Tace "Aww dama ba dan Allah ka daina ba?" Ta fada tana watsa mashi wani kallo "A'a dan Allah na daina amma ay kace sila...." sai kuma ya rasa me xai ce "Tou kasa Allah a ranka..." ta na fadan haka ta juya "Habibty..." juyowa tayi ta kalleshi dawani dawani kayattacen murmushi tayi wrapping hannunta a chest dinsa "Wasa nake maka Sultan, Hoodah is yours zata haifa maka babies ko nawa kakeso...." ta fada tare da bashi wani side kiss tana gamawa ta sake shi ta ruga aguje ta bar kitchen din, dariya yayi ya bita da kallo har ta fice gaba daya zuciyarsa fes yana jin nishadin da bai ta6a ji ba, "I think am falling for you Hoodah...."

Thursday, 17 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 17

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 17}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



"Kayi hakuri Sultan attackers ne da alama dai makiya ne suka diro, kafin muyi wani yunkurin kama su har sun gudu, kayi hakuri amma duk sunada rai babu wanda ya rasa ransa a cikinsu, munyi making duk wani arrangement a fita dasu waje yanzu nan da awa uku za'a tafi, sannan likitoci sun tabbatar mana cewar indai aka barsu a nan zasu iya rasa ransu..." A hankali ya dago kansa yace "Kawu? Yaushe kazo?" Kawu Murtala yace cikin damuwa "Saukar dare nayi jiya sanda na iso kayi bacci, da niyyar in kawo ziyara na taho ashe abinda zan tarar kenan?" Ya fada yana fashewa da kuka. Wata ajiyar zuciya suka sauke shida Hoodah jin ance ay basu rasu ba, kafin Hoodah ta rike Sultan tana sheshekar kuka, tabbas tayi bonding dasu sun zama tamkar iyayenta. Kafin nan da minti 30 sai ga ambulance din asibiti ta iso nan da nan aka fara basu taimakon gaggawa, Sai da aka jojjonasu da machines sannan sukayi masu bankwana nan aka samu kannen Ummi su biyu mace da namiji zasu tafi dasu, kamar ransu xai fita haka suka dinga yi masu Abbi sallama kamar suna jinsu, bayan sun tafi nan Sultan yayi tsaye yana bin motar da kallo har ta bace bat bai daina kallon wurin ba, ji yayi an riko hannunsa ya juyo da kyar yaga Hoodah ce tsaye idanu sun kumbure, janshi ta shiga yi da kyar yake daga kafarsa kafin ya iya takowa zuwa babban parlor, memories suka dinga dawo masa kala kala idan ya yakalli parlorn, zama yayi dirshen a kasa hannunsa cikin na Hoodah itama a hankali ta silale a gun ji yake kamar wanda aka zare ma lakka, kuka yake so yayi amma jin yadda Hoodah tayi squeezing hannunsa ya sanya ya fasa kukan, yafi minti sha biyar a haka kafin a hankali ya fara magana "Ummi da Abbi nasan ko bakuji abinda kowa yake fada ba nasan zakuji nawa, ko ban fada ba nasan kunji Sultan, your one and only son, sai cewa sukeyi ba lallai bane ku dawo da rai daga can zaku iya tafiya ku barni shikenan bazan sake ganinku ba? Sai dai nasan ba gaskiya bane, how can they leave their life and go elsewhere? Am their life bazaku iya tafiya ku barni ba ko Abbi? Ko Ummi? Kuma ko su waye suke da sa hannu a wannan muguntar na gano su wallahi sai na dau fansa!" Sai ya fashe da kuka dama Sultan ya lafiyar kura bare kuma tayi hauka? Ay indai kuka na baya masa wahala. Hugging dinshi Hoodah tayi tana share hawaye, breaking hug din yayi "Mamata tafi ta kowa she can sacrifice the world for you just to be happy, nasha fada mata  I love her so much, kar tayi losing hope and keep fighting, fight for me and for us, Ummi batada makiyi ko daya toh waye yake son ganin bayanta? Also Abbi, you are everything a son would have ask for, you will make it inshaAllahu I know you will I have faith in Allah, InshaAllah zai dawo daku lafiya..." Hoodah ta share hawayenta ta fara magana "Tunda nazoo nan sun nuna man kauna, sun yarda dani they also trust me, i look up to them as my biological parents, banida mahaifiya bansan dadinta ba, amma danazo ta fara maye man gurbin Ammina, dan Allah Ummi be strong for us, I need you more than i have ever needed anyone in my life, idan babu ke our lives will have no meaning, dan Allah for our sake be well again." Ta girgiza hawaye na cigaba da shatata "Abbi, he was like a father to me, ya kaunace ni, dan Allah ka warke ka samu lafiya..." ta karasa muryarta na rawa, kan cinyarta Sultan ya kwanta "Nayi missing su Abbi kina ganin zasu dawo?" Sai yanzu hawayen nashi suka samu damar zuwa yadda ya kamata fiye da da, wani irin tausayinsa ke ratsa ko wane lungu da sako na jikinta, tasan zafin rashin mahaifi ko mahaifiya ta rasa daya bataji da dadi ba inaga Sultan da yake neman rasa duka nashi a take? Wa yasani ko zasu dawo ko bazasu dawo ba? Hannu tasa cikin sumar kanshi a hankali tana murzawa "I can't say zasu dawo ko bazasu dawo ba Allah kadai yasan gaibu, Sultan abinda zamu sa ma ranmu shine Abbi da Ummi suna sonmu bazasu yarda su tafi su barmu ba zasu dawo InshaAllah, nasan kana sansu more than anything else amma ka yarda dani they're part of me too, I lost my mother at a very tender age, Ummi is now the only mother figure I have in my life..." sai kuma tayi shiru ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, a hankali Sultan ya dago yadda take kukan tamkar za'a zare mata rai, take tausayinta ya kama shi, a hankali ya mike zaune ya matso daf da ita ya rungume ta a kirjinsa yana shafa kanta, "Duk yadda rayuwa ta kasance maki zaki iya zuwa ki sameni Hoodah, don naga alamar banda abinda ya faru akwai wani abu dake damunki, ban dade da saninki ba amma ki yarda dani nasan kina cikin damuwa, bansan meke damunki ba amma zan iya baki hakuri idan zaki iya hakura, kiyi murmushi kinada wadanda suke sonki a rayuwa wadanda ko duniya zata juya maki baya suna tare da ke Hoodah, nasan Abbi da Ummi suna ciki sannan nima ina so ki sani cikin jerin mutanen nan a cikin rayuwarki." Shidai yasan bazai iya cewa yana sonta ba dan yasan babu digon sonta a cikin ransa, amma kuma he respect her, cares for her and also adores her, yana jin dadin zama da ita yasan shi dai ba soyayya bace tou menene? Shiru Hoodah tayi kafin a hankali ta dago da idonta tana kallonsa, ido cikin ido suke kallon juna "Are you sure duk sadda nake cikin damuwa zan iya fada maka? I am safe with you right?" Gyada mata kai yayi ba tare da yace uffan ba, ajiyar zuciya ta sauke, a nan suka cigaba da zama kowane na addua'ar samun lafiyar su Abbi. Murtala ne ya shigo da tun dazu yake tsaye bakin kofa ya karaso ciki zama yayi kan kujera ya dafa shi "Ka dangana addua'ar ka ita kadai suke bukata ba kuka ba, bacin haka ma kai ne zaka jagoranci mahaifinka har Allah ya basu lafiya, kai zaka karbi mulkinsa kai zaka cigaba da yi har ya dawo cikin koshin lafiya." Girgiza kai yayi "Bazan iya ba kawu, mulki dawani sarauta ni ba damuna sukayi ba sheyasa ma kaga ban fiya xama nan ba saboda bana son wani abu daya shafi hakkin mutane a kaina, dan haka wallahi bazan iya ba kawu." Murtala yace "Hakuri zakayi wa yake dashi da zai iya karba in ba kai ba? Dolenka zakayi ay ba wai don kana so ba..." yace "Kaifa? Ba dole sai ni ba, badai rikon kwarya bane don Allah ka karbar masa kafin Allah ya basu lafiya..." yar razana yayi "A'a Sultan kabar ma wannan maganar ma hakan bazai taba yuwuwa ba, kaine ya cancanta ka karba bani ba kaima kasani..." Sultan yace "Bakomai kawu, ni da bakina nace na bar maka tou meye a ciki? Kaima fa yayan Abbi ne uwa daya kuma uba daya Menene don ka karbar masa mulki?" Kawu Murtala yace "Jayayya bashida wani amfani Sultan, amma tunda ka kafe ka nace zan karba din nagode." Sultan yayi murmushi "Bakomai." D'aga Hoodah yayi data fara bacci bisa kafafarsa yace "Tashi mu tafi bangarenmu, an kusa kiran asuba..." mikewa tayi ya kama hannunta suka tafi sashensu. Saida da suka yi nisa kawu ya saki murmushi da shi kadai yasan ma'anarsa sannan ya dauki wayarsa ya kara a kunne....

****

Da daddare Sadiya d'aya daya cikin bayi ce ta kawo masu dinner wurin karfe taran dare, gaishe su tayi ta aje masu kan dining kawai ta juya ta fita, tuwon shinkafa ne da miyar gyada, shi kuma Sultan ko miyar miye bazai ci ba yadda ya tsani tuwo, indai kaga yana cin tuwo toh Ummi ca ta girka duk bala'in mutum bazai ci indai ba ita tayi ba.

Hoodah ta mike ta zuba masu a plate daya dan tasan baci zaiyi ba sosai, hannunsa ta kamo har sai ya zauna k'asa kusa da ita, "Kaci abinci please." Abinda tace kenan da disashiyar muryarta, girgiza kai yayi a shagwa6e ya tabe baki, nan taga zallar shagwa6a a fuskarshi tayi murmushi, koda Ummi ce tasan bazai ci tuwon nan ba yau saidai in ma zaici saidai ta bashi a baki. "Ko na baka a baki nima?" Ya girgiza kai alamun a'a "Dan Allah haba Sultan ka daure kaci please." Tayi rai rai da idanu kamar zatayi kuka, duk yinin yau ba wanda yaci wani abun arziki, "Kici kema toh." Ya fada wane karamin yaron daya yi kuka, "A'a sai kaci sannan zanci nima." Abinda tace kenan tare da kai hannunta wurin bakinsa amma ya juyar fa fuska "A'a kinga Hoodah kici abincin nan yanzu idan su Abbi suka dawo sukaga kin rame zasu ce mugunta nake maki, bana baki abinci ko bazasu ce haka ba?"  Ya fada idanunsa na ciccikowa da kwalla, dan murmushi yayi yace "Abbi will be like "Sultan bana son muguntarka fa yanzu dan kaga bana nan shine ko abinci baka bata? So kinga please kici." Girgiza kai tayi tana sharbar hawaye "Zasu dawo, kuma Abbi bazai ce maka haka ba, zanci abincin amma kaima sai kaci." Ta fada tana tallabo fuskarshi kafin a hankali ta dinga feeding dinsu tare. 

Washe gari Sultan yayi shawara take kuma waziri da sauran manyan manyan mutane bayan jayayya na wani lokaci daga karshe aka yanke baza'a nada shi ba amma zai zamana shine zai dinga tafiyar da harkokin garin, da kuma duk wasu ayyuka da ya kamata yayi. 

Wayarsa ce ta fara ringing sai da ya ke6e ya dauka "Da fatan kayi completing abinda na saka?" Yayi kasa kasa da murya "Nayi saidai duk basu mutu ba kamar yadda muka tsara amma dai rai a hannun Allah, saidai fa ina jin tsoro don garin gaba daya an baza yan sanda ana gudnar da bincike..." ta sheke da dariya "Kai da Allah! Nace maka babu ubanda ya isa ya gane mu dan haka kar ka damu kaidai ka cigaba da yin duk abinda na saka..." yace "Toh shikenan ranki ya dade angama," tace "Bissalam." Kit ta kashe wayarta tana wani dariya.

*****

Satika sun tafi tun su Hoodah nasa ran dawowar su Abbi har suka hakura, ya zama busy tare suke gudanar da harkokin gari shida kawu Murtala, kawu murtalan shine yake jawo shi a jiki yana nuna masa aiyyukan tun baya yarda har ya hakura yana binsa..... 

2 days duk Sultan ya zama wani iri dashi kullum cikin damuwa zaka ganshi gaba daya ya chanza, gashi baya bacci sosai cikin dare wani lokaci sai Hoodah ta farka taga hawaye na sauka bisa kuncinsa, haka zatayi ta lallashinsa wani lokacin sai ta fara kuka sannan yake shiru gaba daya Sultan yazama wani sabon Sultan ba wanda tasani ba a da. Wannan Sultan din baya son magana, ya wani da  rashin son mutane Sultan din yanzu sai tayi magana yafi sau biyar bai bata amsa ba. Gashi kullum yayi video call da yan asibiti basu yarda su bashi yayita roko a nuna masa fuskokinsa, kullum idan yace zaije India sai a hana shi ace ya zauna ya kula da harkokin Abbi. Kwana biyu da suka wuce Hoodah ta fara lura da yanayinsa ya fara canzawa, ga wani irin mugun bacci daya koya Idan ya shigo gida sometimes a parlor zai zube. Toh yau kam abin yafi na kullum har sha biyun dare bai dawo ba ta kalli window yafi a kirga shiru kakeji, bataso tasa ma ranta tunanin da takeyi a kansa ya zama Gaskiya, tasan alamu tasan signs tasan how they act, babu abinda bata gani ba tana yarinya Umma babu abinda batayi, salo salo na iskanci kala kala, don har mamaki takeyi wai mace da wannan dabi'un? "Ya Allah ya Allah kasa ba haka bane!" Abinda ta fada kenan tana faman zagaye parlornsu, ta zauna ta tashi, ta shiga daki ta fito har daya ta gota bai dawo ba, zama tayi kan kujera ta dafe kai kamar daga sama taji an banko kofa, tangadi yakeyi kamar zai fadi ga robar coke yana rike da ita a hannu daya, a razane ta mike ta karasa inda yake tsaye kafin ma yayi wani yunkure har ta fizge robar ta bude ta da sauri takai hanci kawai saita saki robar duk abin ya malale a kasa, tana furta "Innalillah wa inna ilahir rajioon! No not you Sultan not you!" Kafin kace me hawaye ya wanke mata idanu, wani irin kuka ta saki tana girgiza kai, baya baya takeyi tana faman girgiza kai, tasan kamshin abin don tun batada wayau take ganin kwalbar a dakin Umma tasha boyewa, har dauka take tana sinsina don haka tasan wannan ko menene har ta mutu bazata taba manta warinsa ba. "Sultan me ka jefa kanki a ciki? What have you gotten yourself into? Meka rasa Sultan? Dama baka dauki kaddara ba? Wannan wace irin rayuwa ce ka jefa kanka a ciki?"  Kuka takeyi bil hakki kamar ta fiddo Zuciyarta ko zataji sanyi, yanzu Sultan mijinta shine ya koma dan shaye shaye? Tangal tangal yazo inda take sai tayi sauri taja baya "Waya jefa ka wannan harkar Sultan? Innalillahi wa inna ilahir rajioon! Nasan dai ko kayi magana yanzu duk karya ce." Ta ma rasa abinda ya kamata tayi, tasan dai da kyar idan ba wani bane ya jefa shi wannan hanyan.... toh who? Umma? But how? Umma dake can Agadez ina taga Sultan? Haka ta jera ma kanta tambaya amma ba amsa. Zai fada kan kujera tayi saurin damko masa riga "Let's go to bed...." kallonta yakeyi kamar wani sakarai, toh wai kukan me takeyi? Shi ya ya kamata yayi kuka ta zubda mashi drink, drink din da kawunsa ya basa yace idan yasha zai rage damuwa, yasha kwalba tafi uku a yau, sanda ya fara bashi da da farko ya nuna bazai sha ba sai yace masa ay coke ne kuma mai sanyi, nan ya kafa kai ya shanye, toh tun daga wannan ranar kullum sai yaje ta bashi yasha, Hannunshi ta kamo ga hawaye gawani tukar bakin ciki dake cizon ranta, fizge hannunsa yayi yawani tunkudeta ta fadi tim bisa kujera!

Wednesday, 16 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 16

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 16}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



A hankali yake rocking dinsu yana dan jijjigasu kafin yaji chanji daga yanayin saukar numfashinta wanda hakan yana nuni da cewar tayi bacci. Daukarta yayi ya kaita kan gadonsa har ya juya zai tafi sai yaga alamun hijab dinta kamar ta takura mata, cire mata hijab din yayi sannan ya sunkuyo yayi mata dan karamin peck a goshinta karasa kashe fitilun yayi zuciyarsa cike da tausayinta.

A hankali ta bude idanunta nan ta fara juye juye, tana ganinshi ya taho gunta sai ta dan tsorata ita tabata yayi jya dafa hannunta "Calm down a Hoodah, babu abinda zan maki kinji?" A hankali ta sauke ajiyar zuciya ya xauna kusa da ita yana sanye da towel yana kallon face dinta da hawaye har ya taru "Hoodah kukan me kikeyi?"  Ya fada cikin sauti mai taushi mai kuma kwantar da hankali, ji yake kamar ya bude kirjinsa ya sata a ciki yakeji, shiru tayi ta kasa magana, matsowa yayi dab da ita ya zauna yana goge mata hawayen fuskarta "Do you still trust me? Komai zai faru a gaba zaka yi trusting dina?" Bai bari ta karasa ba yayi hugging dinta hade da shafa gashinta, "Look at me Hoodah..." ya fada yana scooping fuskarta da hannuwansa biyu a hankali ta sauke idanuwanta cikin nashi "I trust you dear, I will never let anything happen to our relationship again, and I promise you Hoodah zan gano ko wacece take neman tarwatsa farin cikinmu, it's fine kinji?" Kuka ta fashe dashi "Thank you Sultan, nagode I feel relieved now..." dan Murmushi yayi mata "Tou kukan na menene kuma? Sai kace ance maki na mutu?" Ya fada yana hugging dinta, shi kanshi mamaki yake ya kasa tsaida kansa daga faruwar hakan, "How can I not trust my wife? Na maki alkawari daga yanzu I will always be by your side, kuma bazan sake bari a hada mu ba." Ta yi murmushi ita tama kasa magana mamaki kawai yake bata yadda Sultan ya chanza gaba daya kamar bashi ba, "Tashi ki shiga bathroom kije kiyi wanka, zan dauko maki duk abinda kike bata a dakinki, and forget about cooking na mana breakfast..." ba zato ba tsammani kawai sai jin hannunsa tayi ya daga ta cak har suka sauka kasa, tsaye tayi kamar an dasata ita gaba daya ji yake jiyoyin jikinta basu aiki tayi tsaye kamar wata dogari sai kawai ta tsaya tana kallonshi, "Hoodah kafin nayi counting 3 ki tafi ki wuce bathroom kiyi wankan nan, 1,2..." bai ida rufe baki ba ta zunduma da gudu bata tsaya ko ina ba sai bathroom dinsa, saida tasa key ta rufe ta tsaya tana maida numfashi, amma meyakon ta fara wankan sai kawai ta durkusa ta rizgi kukanta a nan bata taba tunani ba ko a mafarki Sultan zai zama caring haka ba, ashe dama haka yake bata sani ba? Abinda ya mata yau ya ta6a mata zuciya. Tana shiga shi kuma ya gama gyara dakin tsab baka taba cewa namiji ne ya gyara shi haka tas, yana gamawa ya sa kaya sai ya wuce dakinta ya dauko mata duk abinda yayi tunanin zata bukata da kayan da zata sanya. Koda Hoodah ta fito ta gama shirinta tsab bata ganshi ba, tana fitowa ta ganshi yana jera plates bisa dining yana ganinta ya saki murmushi itama ta mayar masa, hannunta yazo yaja ya zaunar da ita ya shiga serving dinta abinda ya girka masu wato doya da minced meat sauce sai hot coffee, ba karamin enjoying abincin nan tayi ba, ya mata dadi sosai, suna gamawa ta sauko hijab dinta yaja hannunta suka tafi gaida  su Abbi. Bata taba tsintar kanta cikin farin ciki ba irin yau ba, he's a blessing to her.

Throughout ranar yau data yi spending da Sultan he's the sweetest man ever, riritata yake kamar kwai, dan wani lokaci saidai ta tsaya tayita kallonshi har sai ya mata snapping hannu sannan ta daina kallon nashi, idan ya tambayeta kallon me take mashi saidai tayi dariya tace "So nake na tabbatar idan da kai nake zaune anya Sultan kaine kuwa?" Bai iya yace mata komai saidai yayi dariya don shima kansa mamaki yakeyi. Tun daga ranar suke zaune lafiya kalau cikin kulawa da juna saidai fa ba wanda ya fahimci me zuciyoyinsu ke ciki. Shi da mai martaba gaba daya babu abinda sukeyi sai bincike sosai don gano waye ke haddasa masu fitina a tsakaninsu waye ke masu wadannan abubuwan.

******

An shude watanni, cikin watannin nan Ashraf yanata healing a hankali duk da dai ba gaba daya ba amma ya ragu sosai all thanks to Yasir, saidai fa ko fita baya yi sai Yasir yayi da gaske kafin ya fita. 

Yana kwance cikin dakinsa kullum saidai kawai yaje ya gaida Hajiya mahafiiyar Yasir da safe shikenan, kannen Yasir kuwa su biyu suke kawo masa abinci kulllum, suna matukar tausaya masa gidan gaba daya dan haka suna kokarin ganin sun tsamo shi daga dilemma da ya afka ciki, ya danyi adjusting to environment din, wani lokaci haka zai kura ma bango ido abubuwa da yawa suna rushing back cikin kwalwarsa yana tunanin abubuwa da yawa da suka faru a baya, baya tunanin zaya gushe daga cikin ransa har abada har bayan ransa, wani lokaci haka zaka tsince shi yanata murmushi ko kuma yana goge hawaye, yasan dai tunda ya rasa Hoodah toh bazai taba samun wata rayuwar da yayi ta farin ciki a baya ba, saidai kunci da bakin ciki, a hankali yaji knocking kafin ma yayi magana yaji an murda kofar an shigo a hankali, Zarah ce tsaye bakin kofa rike da tray din abinci, stool ta jawo ta aje mashi kusa dashi, sannan ta tsugunna tana kallonshi cike da tausayawa "Yaya Ashraf barka da dare? Ga abincinka nan inji Hajiyah tace don Allah ka daure kaci abinda kake so ne tayi maka da kanta, don Allah kaci tace na dawo anjima na kwashe na kai mata taga ko kaci..." tunda ta fara magana yake kallonta bai ce uffan ba ya kai akalla second kamar ashirin sannan ya kalleta "Nagode Zarah." Yayi murmushi har cikin ransa, "Basai kayi godiya ba yaya Ashraf, ka riga ka zama dan gida yanzu." Ta fada tana murmushi, ta kuma ce masa "Try and be strong duk da is not going to be easy, nasan da ciwo kuma duk naji labari daga gurin yaya Yasir yadda kuke da Hoodah da duk abubuwan da suka faru abu baiyi ba dadi ba, amma kasani kowa da tasa kaddarar wannan itace taku kaddarar yaya Ashraf..." shiru yayi na yan dakikai "It's not going to be easy amma kasani kaifa namiji ne, ita kanta Hoodah baza taso ta ga yayanta cikin wannan halin ba, wata kila ita ta dauki kaddara ta cigaba da rayuwarta, kai me zai hana ka yin hakan?" Wani kwalla ya goge "I will be fine, it will surely take time, but gradually ko?" Tasaki murmushi "Yes sure, kadai ci abincin nan please ko in zuba maka?" Ya girgiza kai "A'a Zarah karki damu, thank you." Ta mike tana murmushi "You are welcome kaci fa zan dawo na duba." Yayi murmushin shima "Zanci." Daga haka ta sa kai ta fita daga dakin. 

Yasir ya shigo parlon Hajiya tana zaune kan kujera ya zauna kasa kusa da ita "Ina wuni Hajiya?" Tace "Lafiya lau Yasir." Yace "Gani Hajiya naji ance kina nemana?" Tace "Eh hakane, abinda yasa na kiraka shine inason muyi shawara da kai." Yace "Toh Hajiya." Ta gyara zama "Wannan yaro Ashraf wato abokinka dinnan, a gaskiya ina matukar jin tausayinsa, kuma ni gani nake wannan zaman kadaicin da yake yana kara contributing to kara damuwa a gareshi, sheyasa na zauna nayi tunani naga me zai hana mu hada shi aure da Zarah?" Yasir yayi murmushi "Hakika Hajiya ba ke kadai ba nima abin ya dameni sosai da sosai, nayi iya yina na ganin na tsamo shi daga cikin wannan halin da yake ciki amma abun yaci tura, gaskiya naji dadin shawarar nan taki Hajiya, kuma bana tunanin za'a samu matsala daga ko wane bangare, Allah ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi, hakan ma karamin rage masa damuwa zaiyi ba." Tace "Sosai ma dan haka kaje kayi shawara dashi." Yace "InshaAllah zanyi." Tace "Shikenan tashi kaje." Daga haka ya mike ya shige ciki.

*********

2 days later....

A gigice ya bude idanu, ba inda jikinshi baya kadawa zufa kuwa gaba daya ta wanke masa jiki, ya saba mummunan mafarkai amma na yau yasha bam bam, bazai iya cewa ya kalar mafarkin yake ba amma dai ya tsorata matuka, Hoodah ta bude idanu itama a tsorace ta kunna bed side lamp tace "Sultan lafiya? Meyafaru? Ko mafarki ka sakeyi marar kyau?" Ta tambaya tana dan taba fuskarsa data jike jagab da zufa, duba time Hoodah tayi taga karfe biyun dare, addu'a ya shiga jerawa jikinshi na cigaba da kadawa Hoodah na tayasa addu'ar duk da tazo bakinta. itama zuwa yanzu ta fara tsorata, "Sultan menene?" Ta sake tambaya a tsorace, saida ya dan dawo daidai ya furta yana maida numfashi "Wani mummunan mafarki nayi marar kyau." Tace "Wane iri?" Yace "I can't say, bansan ya zan fassara sa ba," ta dora kanta bisa kirjinsa "It's okay InshaAllah, everything will be ok." Yayi mata murmushi, nan ta tashi taje ta debo masa ruwa ta kawo masa ya fara sha, yana cikin sha dinne sukaji kururuwar mutane da hayaniya, da sauri Hoodah ta kalleshi jin ana jijjiga kofarsu kamar za'a ballata, Hoodah batasan lokacin data bude ba, dogawara sun kai bakwai tsaitsaye sai zufa ke keto masu, "Ranki yadade, Sarki da Sarauniya...!" Cup din Sultan ya saki take ya tarwatse kasa, Hoodah ta juyo sai yanzu ma kwalwarta tayi registering abinda suka fada masu, kallo daya tayi masa ta lura kamar hankali baya jikinsa, "Meyafaru dasu?" Ta tambayesu, "Sai dai kuzo ku gane ma idonku." Suna fadan haka suka juya da sauri suka bar wurin, a hankali ta taka kusa da shi wani irin bala'in shock ne kwance kan fuskarshi, kofar ya kura ma ido bako kyaftawa gaba daya kwalwarsa ta chunkushe, Hoodah itama kanta batasan yadda zata misalta abinda takeji ba, glass din da ya tarwatse kasa Hoodah ta tattara gudun kar a ji ciwo don dukkansu bamai takalmi a kafa, dispenser taje ta debo masa ruwa ta sa masa a baki gaba daya ya zuke ruwan nan kafin ya saki wata ajiyar zuciya, sulalewa yayi kasa gani yake kamar abinda suka fada mashi karya ne gani yane wasa ake masa, dan marin kansa yayi yaji ko shin har yanzu mafarki yakeyi bai farka ba? Hoodah itama sulalewa tayi bisa gwiwoyinta kusa dashi ta kura mashi ido, tunda ya sulale a gurin da kyar ko numfashin kirki bai iya yi, sai da yaji muryar Hoodah tana fadin "Sultan kazo mu tafi..." ta fada tana dragging dinshi wai ya tashi, sai yanzu Sultan ya dawo hayyacinsa tunani yake meyafaru? Meyafaru da iyayensa? Mutuwa sukayi? How? When? Where? Ya za'ayi su tafi su barshi a take? Shin basu san rayuwarshi is incomplete bane without his parents? The people he love beyond everything and everyone, they're his entire life, saukar hawaye daidai kumatunsa yayi daidai da furtawarsa "I need to go and see... nasan ko me nake tunanin ya faru dasu ba haka bane, they're ok, they can't do this to me ko Hoodah?" Take yaji wani tausayin kanshi ya dirar masa, wani gunjin kuka ya saki wanda ya razana Hoodah itama take ta fashe da kuka, sun kai minti hudu a haka kafin Hoodah tayi karfin halin mikewa tsaye kamar yar maye tana tangadi, cikin karfin hali ta soma jan hannun Sultan "Tashi muje Sultan, let's go and see for ourselves." Gyada kansa yayi ya mike tsaye da kyar kafin ta kamo hannunsa suka fita daga gidan. Tun daga wajen sashen zuciyarsu na wani irin harbawa ba kamar Sultan da yake jin kamar zata huda kirjinsa ta fito, hannunsu rike cikin na juna suka kutsa kai ciki, wani irin sakin hannun Hoodah yayi ya karasa cikin parlon da sauri hawayenshi suka tsaya cak, Abbi da Ummi suka gani kwance kasa tsakiyar parlor dogarawa sun zagaye su da wasu wanda baya gane ko su waye, steps uku ya kara baya baya ganin jini na fita ta goshinsu da cikinsu, Hoodah na karasowa kusada su a gigice ta rufe bakinta da hannuwanta biyu, wata irin kara ta saki ta zube nan jikinta na kyarma....!

Tuesday, 15 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 15

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 15}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Haka ta kwanta tana ta faman tunanin little Affan, yayi karami ace yana experiencing wannan abubuwan, subhnallah kuma mahaifinsa wanda shi ya cancanta ya zamana yana gefensa yana share masa hawaye wannan wane irin uba ne? Anya shine ma ya haife shi kuwa? Abinda matar nan ta fada mata gakiya ne ko kuwa? Kodai wani 6oyayyen al'amari ne tattare da abin? Indai har gaskiya ne bai dace ma ace ya ta6a haihuwa ba, astagfirullah ita wacece da zatayi judging abinda Allah ya hukunta? Da kyar bacci 6arawo ya sace ta.  Washe gari ta kai kimanin minti 30 tana wanka, gaba daya ta rasa mafita ta rasa meye abinda ya kamata tayi, tana son ta taimaka mata amma wani bangare na zuciyarta baya so. Kamar kullum sai ta fada ma Sultan zataje yawan shakatawa, har fa fita sai ya kirata "Wai bakya gajiya da zuwa wurin nan ne? Kullum sai kinje?" Dariya ta kakalo "I promise wannan ne zuwan da zanyi na karshe zan dauki time banje ba..." yace "It's fine, but do you need someone to take you?" Tace "No, I will be ok thank you." Gyada mata kai yayi "Alright be safe..." daga haka tasa kai ta fita zuciyarta na harbawa, inda suka saba haduwa yau ma a nan ta iske matar na zaune tana zaman jiran Hoodah ta karaso, idanunta jawur alamun taci kuka murmushi ta kakalo ganin Hoodah, sallama Hoodah tayi mata ta amsa "Ya jikin Affan? Wurin wa kika barshi?" Tace "He's better Alhamdulillah, na barshi da nannynshi." Hoodah tace "zamu iya tafiya? Amma gaskiya bazan shiga hotel ba, sai dai ki masa magana ya fito waje..." matar tayi yak'e ta tashi suka fito parking lot, mota suka shiga ta jasu, tafe suke babu wanda ya tanka cikin motar amma ji take kamar abinda take ba daidai bane, tana ji kamar bata kyauta ba, gani take wannan shine worst mistake da zata aikata,  parking sukayi gaban makekiyar hotel din matar tace "Muje?" Hoodah tayi shiru gabanta na faduwa, "Muje ina? I thought I said am meeting him outside? No kije ki kirashi I can't go inside..." matar ta numfasa sai ga hawaye shar shar tace cikin shesheka "Taya xan fara ce masa ya fito? Bakisan halin Aliyu bane wallahi bazai fito ba, amma indai har kina ganin kamar cutar dake xanyi kawai mu hakura mu koma, am seriously telling you and ke da kanki kikayi niyyar taimaka man I want my baby to survive..." Hoodah tayi shiru gabanta na harbawa tana sauraren sheshekar matar "Don Allah ki daina kuka, bawai ban yarda dake ban, kawai dai zuciyata ce bata amince man da in shiga ciki ba I don't know why!" Matar sai ta kifa kanta a steering wheel ta dinga sheshekar kuka "Babu komai, a haka ma nagode da niyyar taimaka man da kikayi, I don't mean to make you feel uncomfortable, bari naje na gwada kiran nasa nagani... amma alfarma daya xakiyi mun, muje bakin receptionist sai na masa magana a nan ya sauko..." tace toh ta fito daga motar suka cigaba da tafiya a natse duk Hoodah is uncomfortable sai kalle kalle take, can tace "Kar kice na cika complain amma gani nake kamar ana kallonmu..." matar ta juyo ta dafata "Toh ko dai ki tsaya a waje? Idan baki iya shiga." Hoodah tayi smiling back "A'a it's fine muje kawai." Nan ta shiga ciki ta bar Hoodah tsaye. Tun Hoodah nasa rai zata fito har ta fara gajiya da jira, toh dama akwai steps a wurin sauka nan tana cikin tafiya kawai sai tayi taga taga zata fadi, wani dake gefenta yayi saurin tarota.....

Shi kuma a bangaren Sultan tunda Hoodah ta bar gida ya kasa samun nutsuwa, a hankali ya fito ya dinga binsu ga mamakinsa sai yaga sun tsaya a hotel, nan ya fara tunanin meya kawo Hoodah hotel wacece wanann da suka zo tare? Kawai yana fitowa daga mota sai ga Khairy kamar an korota, "Sultan!" Cak ya tsaya ya juyo yana ganin Khairy yace "Khairy me kikayi a nan?" Ta matso daf dashi "Mama ce ta aikeni nan kawai ina fitowa sai naga matarka da wata mata sun shiga cikin hotel, toh a hankali na dinga binta ina zuwa sai naga asha da wani ne suka hadu..." yace "Mey? Me kikace? Yoh must be joking." Tace "I am sorry Sultan but that's the truth, believe it or not gaskiya matarka tana bin maza... karka ce kishi nake ko wani abun, ni da idona na ganta..." ya runtse idonsa gam gam yana girgiza kai "No! Karya kike Khairy kishi ke damunki amma Hoodah bata bin maza..." Khairy tace "Oh really, why don't you go inside and see it for yourself!" Kasa tsayuwa yayi nan yaji kamar zai fadi, rigarshi Khairy ta damko ta dinga jansa kamar wani gunki haka suka shiga cikin reception din, yana fara hawa steps daidai lokacin da Hoodah ta kusa faduwa wani ya tarota, tsayawa yayi yana kallonta take ya fara wani girgiza kai ya fasa kara "Hoodah!!!!" Yayi gigitaccen kara kamar wani zaki, ita kuma lokacin ta kusan fadowa tana kokarin rike stairs kar ta fada masa amma ina ta kasa controlling hakan, wata irin zabura tayi ta jiyo a gigice, kafin ta ankare sai ganin Sultan tayi ya nufo ta gadan gadan wane kura ta ga nama, wata irin damka ya kai ma kugunta ya dinga janta suka fita hotel din don mutane nata kallonsu, cikin motarsa ta tullata har sai da kanta ya bige da karfen motar ta rike kan hawaye na taruwa cikin idonta, gefe ya shigo ya kunna motar ya tada ta da karfin balai yaja su wane zai kifar dasu, "Na yarda da maganar da ake fada a kanki yau na tabbatar!" Muryarta na rawa tace "Me kake nufi?" Ko amsata baiyi ba ya kara wutar motar kamar zaiyi accident, a tsorace take kallon shi jikinta babu inda baya rawa, yana isa gida ya finciko ta ko tsayawa baiyi ba sauraron kowa ya nufi sashensu, yana zuwa ya wullata kasa yasa ma kofar key, "Sultan wai lafiyanka?" Ta fada tana kokarin mikewa tsaye tuni hawaye sun wanke mata idanu, finciko hannunta yayi ya matse gam gam yana kallon cikin idanunta "Tambayata ma kikeyi?" Ya fada kamar zai fasa mata dodon kunne Hoodah tace itama a tsawace "Dole na tambayeka! Naga alamar kamar kwalwarka ta samu matsala!" Kara matse karfin rikon da yayi ma hannunta yayi "Naganki dawani kato a cikin hotel sannan kizo kina tambayata meye faru da kwalwata?" Hannu tasa tana kokarin cire rikon da yayi mata cikin kuka tace "This is the second time Sultan zargina kake? Baka yi trusting dina ba? Sultan what the hell is wrong with you? Subhnallah don kawai kaganni da wani bai ci ace ka zargeni da aikata abinda ba daidai ba, trust me da wata naje taje ciki ta dawo kawai nazo faduwa...." daga mata hannu yayi "Bana son jin komai daga bakinki Hoodah! Akace maki ni wawa ne bansan me nakeyi ba?" Hoodah tace "Oh haba? Now I get it! Dama dai kiris kake jira ka fara mun abinda ba daidai ba! In banda haka meyasa bazaka tsaya kayi bincike ba? Ka gano idan na aikata hakan?" Idanunshi jajir jijiyoyinsa a waje yace "Ni mamakin da kike bani sai wani cewa kike bakiyi komai ba, bayan sau biyu ina kama ki dumu dumu amma still you're denying the fact!" Hannu tasa take karfi yazo mata ta fincike masa hannu daga jikinta tace "Toh bari kaji Sultan! Nagaji! You know what? I don't care anymore am tired of all this!" Ta fada tana nufar hanyar dakinta "And where do you think you are going?!" Saida ta kai dakinta ta juyo tace "My room, kuma babu abinda ka isa kayi!" Tana fadan haka ta shige daki nan yaji anata knocking "Sultan ka bude mana kofar nan!" Da sauri yaje ya bude nan sarki suka tsaya suna kallonsa "Lafiya? Me kuma ya faru? Ina Hoodar?" Ummi ta fada tana sa kai ciki, knocking dakin Hoodah tayi ta kai minti biyu sannan tazo ta bude, Hoodah na ganin Ummi kawai taje ta rungumeta gam ta saki kuka mai ban tausayi "Ummi I think someone else is setting me up! Inaga akwai wanda baya son zamana cikin gidannan ..." Ummi ta dago ta tana share mata hawaye "Meya faru?" Ta fada tana kamo hannunta ta zaunar kan kujera mai martaba ma ya shigo ya zauna shima yace "Meya hadaku fada tun farko?" Sultan yace "A hotel na kamata dawani kato..." daga masa hannu yayi "Ba kai na tambaya ba yata na tambaya ita nakeso tayi man bayani dalla dalla..." kwafa yayi ya fice daga gidan wane zai tashi sama, share hawayenta tayi ta dago daga kan cinyar Ummi sannan ta basu labari daga farko har karshe, mai martaba ya numfasa "Tabbas wannan set up ne daga ji ma, amma kema Hoodah kinyi ganganci meyasa kika bita kuma meya hana ki fada ma Sultan gaskiya tun farko?" Tace "Wallahi nima bansani ba! Kawai na tsinci kaina da son taimaka mata shine fa, amma bayan nan babu wani abu wallahi." Ummi tace "Toh wai wacece wannan da take son hanaku zaman lafiya? Sau biyu fa kenan! Amma karki damu zamu gano ko waye kuma wallahi idan na gano I won't spare her! Share hawayenki inshaAllah Allah zai bayyana mana gaskiya." Ta share hawayenta sai yanzu ta soma fahimtar komai dalla dalla. 

Bayan mai martaba sun fita nan Hoodah ta dinga safa da marwa a dakinta tana tunani "Waye wannan yake nemana da sharri? Meye hadina da shi? Me na masu? Waye?" Nan ta dinga tafiya tana tunani zama tayi gefen gado "Tunda yanzu na fahimci komai, I won't rest sai na gano ko waye wanann yake tarnishing image dina yake kuma hadani da Sultan, mark my word sai na gano ko ke wacece no matter what it takes I won't spare you!"

Tana nan zaune a haka har aka kira sallar magrib jiki a sa6ule ta tashi ta shiga bathroom ta watsa ruwa hade da alwala tana fitowa ta saka loose gown. Can bayan isha'i taji shigowar Sultan garam haka aka buga kofar dakin aka shige kamar zata balle, a hankali ta fara tunanin yadda rayuwarsu ta sauya cikin kankanin lokaci da irin kulawar da suka ba junansu amma yanzu lokaci daya ansamu wata shegiya ta tarwatsa masu farin ciki, tafi minti talatin sannan ta mike a sanyaye ta nufi dakin nasa, jikinta babu inda baya rawa, tana shiga ta tsaya kofar dakinsa tana kalle ganin babu kowa, nan tayi tsaye lost in her thoughts kamar daga sama taji takun tafiyarsa kusa da ita, wani irin mugun firgita tayi da tilas tari ya sarketa, bai ce komai ya juya ya fita ashe ruwa ya debo mata ya mika mata ta sha da sauri amma fa fuskar nan kamar an aiko mashi da sakon mutuwa, ta kula yayi wanka ya chanza kaya "Meya kawo ki dakina?!" Ya fada cikin daga murya, muryar nan babu taushi ko kadan. Ta dago da rinannun idanunta tana kallonshi, kafin ya ankara sai hawaye ya runtse idanunsa ya zauna kan kujera, ganin haka yasa Hoodah ta zame ta zauna kusa dashi tana tunanin maybe zata samu sassauci, kallonta yake babu ko kyaftawa ita kuwa kuka take tamkar ranta zai fita, kasa ta sauko don tayi alkawarin bazata taba barin gurin ba sai ya daina fushin nan da yakeyi, tayi missing kulawar da yake bata kwana biyu da suka wuce, ya dandana mata zuma mai saurin kama zuciya. Dan kwanciya tayi bisa cinyarsa ta lumshe idanu "Sultan ya kamata ka fahimceni kai kasan wannan ba halina bane is a set up don a rabamu, nasan bamu zaman lafiya bama son junanmu da farko, amma wallahi ban taba aikata abinda kake tunani ba please..." tausayi ta bashi matuka kamar ya durkusa ya rungume ta amma ego bazai barshi ba "Tashi ki fitan man daga daki!" Rufe idanunsa yayi da san ya manta abubuwan da suka faru 2days ago, it's a beautiful moment a happy one, "No bazan tafi ba har sai kace kayi trusting dina, sannan sai kayi hakuri nasan nima inada laifi da na tafi ban fada maka ba, kayi hakuri wallahi ba laifina bane matukar tausayina ne yaja mun amma nayi learning lesson, I was just trying to help her she told me to talk to her husband, yaronta yanada cancer batasamun kulawa daga garesa, I even offer to help her nace ta fada mun nawa ne kudin aikin yaronta tace indai inaso na taimaka kuma nayi niyya sai dai nayi magana da mijinta da ke zaune a hotel, kayi hakuri don Allah, nidai kawai so nake kace kayi trusting dina that's all that matters to me, ko da zaka dakeni ko kace ka tsaneni as long as zaka yi trusting dina I don't care, please Sultan don Allah..." ganin ko kallonta baiyi ba yasa ta zagayo da hannayenta duka biyun a waist dinsa ta makalkale wani irin shock sukaji su duka, juyowa yayi ya kalleta kafin yabi hannunta da kallo dake zagaye dashi!" Shiru yayi kafin yace "I hate you! Nace ki tashi ki fitar man daga daki! Abinci ma karki sake bani zan dinga fita inaci! And lastly koda wasa karki kara taba jikina!" Ya fada yana ture hannunta daga jikinshi ko second daya bai kara a dakin ba ya tashi ya fita ya buga kofar da karfin bala'i. Wani abu Hoodah taji kamar madaci ya tsaya mata a makoshi, sai yanzu ta tabbatar da duk kukan da take a baya ba kuka bane takaicin data kunsa dazu ba komai bane ba compared to na yanzu, duk wata kafa dake zuciyarta saida ta toshe sannan ya bude mata kofofin bakin ciki da damuwa mai tarin yawa. Kuka ta saki mai cin rai a nan, nan ta kwanta a kasa tayita kuka kamar ranta zai fita, tun tanayin kukan har bacci ya fara fizgarta, sannu a hankali bacci ya sureta a nan inda take.

Ashe Sultan yana parlor kwance shima a nan bisa kujera bacci yayi awon gaba dashi, can cikin dare fitsari ya ishe shi, ko lura da ita baiyi ba kasa sai da yafito daga bathroom ya hango ta can kamar xata shige cikin kujera ta kudundune da hijab dinta sai faman ajiyar zuciya takeyi, samun kansa yayi da rage mata sanyin ac sannan ya rage mata fitila, karasowa yayi a hankali inda take ya dafata a firgece ta farka "Kayi hakuri kace ka yar...."  sai a yanzu ya lura da kuka takeyi cikin bacci, tana bude idonta ta ganshi kawai sai tayi hugging dinshi ta fashe da wani irin kuka, "Kace kayi trusting Sultan, azzalumai ne suke so su rabamu, zaka nemo su? Ka hukunta su?" Kuka take har can kasan ranta, wani irin tausayinta yaji yana shigarsa, a hankali yayi hugging dinta back yace "Kiyi shiru ki daina kuka kinji? Zan sa a nemo su bazan bari su kara hadamu fada ba ki koma baccinki yi shiru."

Monday, 14 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 14

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 14}


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



******

"Malama Khairy lafiya kika kirani tunda sassafe haka?" Ya fada yana son jin dalilin kiran nata, ta numfasa "Naji dadin aikin da kayi man kwanaki but I have another plan, this is going to be my second success, na farko mun aiwatar dashi nayi bincike komai ya tafi yadda na zata! Am really happy about what I heard!" Yayi wata arniyar dariya "Ay ni kinsanni sarai indai da yayan banki babu abinda zai gagara!" Tace "Good! our second full proof plan is going to be a little different amma dai duk tafiyar tasu daya ce!" Yace "Ba matsala kawai ki man bayani me zan aikata maki amma fa kinsanni sarai you have to pay, in ba haka ba bazan amsa aikinki ba..." tace "Karka damu ay zan biyaka! Nidai bukatata ta biya, kagane...." nan ta zayyana masa aikin da takeso yayi mata, ya gyada kai can ya kece da dariya "Babu matsala ko kadan, zan maki amma ki tabbatar kin biya da tsoka don wannan aikin ba irin wancan bane...." tace "Babu matsala."

********

A hankali ya zare jikinshi daga nata yaje yayi sallah yana dawowa ya isketa yadda ya barta haka ya dawo ya sameta, yana kwanciya kamar tana jira ta makale shi ta kwanta bisa kirjinsa a haka ya kura mata ido ganin yadda take bacci so innocently kamar idan aka sa mata yatsa bazata ciza ba, haka ya samu kansa da cigaba da kallonta cike da sha'awa baima san yana smiling ba, gashi dan kwalinta ya zame ya cire gashi duk wani ya dawo gaban fuskarta ya dan rufe mata goshi, lips dinta ya kalla ashe haka lips dinta suke da kyau? Gasu wasu light pink sai sukaje da skin color dinta, daga gani bacci take mai nauyi, samun kansa yayi da sa hannu yana cire mata gashin fuskarta a hankali take ya kura ma lashes dinta idanu sunyi zara zara gasu masu cika wasu bakiirin dasu, gashinta yake shafawa wani irin santsi yaji da taushi marar misali, a hankali ya fara ta6a bayanta yana bubbugawa, bude idanunta tayi a hankali sai ta sauke su bisa fuskar Sultan, ta saki wani kayattacen murmushi ta danyi mika kadan "Good morning." Har yanzu bata daina murmushi ba, babu wanda ya dauka nan da minti biyar Hoodah zata iya yin fada amma dai let's wait and see no one trust her. "Morning to you too, yunwa..." sai kawai ya tsinci kansa da mata magana haka cikin kwanciyar hankali, dan tashi tayi zaune take Sultan ya fara kallonta da wata kayatacciyar night gown mai matukar kyau shi sai yanzu ma ya lura, kamar an kwance mashi noti haka yakeji, Sultan har dawani alamun shagwaba ita kuma yadda yayi haka sai kawai taga ya mata kyau, yau gaba daya sai taji yau ta tashi bata jin haushin shi, "Toh yanzu meye abinyi? Nidai kasan banida lafiya ko ya jiki ma bakace man ba..." ta fada cike da shagwa6a ba karamin burge Sultan tayi ba, "Am so sorry ya kike? Hope you slept well in my room? Ya ciwon cikin ya daina?" Idanunsu a makale cikin na juna yake mata maganar nan gaba dayansu yau mamakin kansu sukeyi, "Alhamdulillah, dasauki and yes I slept like a queen in your room thank you.. well Abincinka ko muje muyi tare?" Murmurshi Sultan yayi ya gyada kai wane karamin yaro a haka ya mike ita kuma ta tafi dakinta don yin wanka shima bathroom dinshi ya shiga don yin wanka. Haka tayi wanka har ta gama bata bar murmushi ba tana gama sa kaya taji ana knocking a hankali, kafin ma tayi magana har an shigo tana kokarin sanya sarka, galala yayi bakin kofa yana kallonta tana sanye da wata gown red color dinkin material mai taushi red and brown ne color dinta, karasowa yayi ta gaban mirror yana kallonta ta ciki, face dinta ba makeup dama ita ba makeup takeyi ba iyakarta da makeup powder da kawalli idan an kure lipstick shima bata sawa da yawa kadan kadan take shafawa, idanunta ya kalla ta mirror farare kal dasu gashi sunsha kwalli dama gasu dara dara  manya dasu MashaAllah, "Should I help ma'am?" Ya tambaya yana kallon sarkar tata golden color da ganinta kasan ta gold ce marar hayaniya, fuskarshi dauke da murmushi, dukkansu sunsan cewar abinnan da suke da kyar zai kai daren yau amma kawai duk sun tsinci kansu haka yau, a hankali ya kama sarkar dake hannunta bisa neck dinta ta lumshe idanu yana kallon fuskarta yasa mata a hankali yana jin wani bakon al'amari cikin zuciyarsa, "You look stunning." Ya furta a lokacin ne ita kuma ta bude idanunta ta taji wani yanayi na daban, wani tari ne ya dan sarke ta tayi saurin fita daga dakin "Muje rana tanayi..." yana shiga cikin Kitchen to make it less boring sai Hoodah tace "Ka taba girki kuwa? Sultan karfa muzo ka kona mana abinci.." dariya tayi ya tayata. "Wai ke bakyajin dan kunyar fadin sunana? Ko Yaushe Sultan wannan Sultan wancan..." dariya ta kyalkyale dashi "Toh idan ban kira sunanka ba Sultan sunan wa zan kira? Wa nake gani a cikin gidannan kullum in ba kai ba? Ni sunan ne ma yake burgeni gashi sunan yayi kama da sunan sarauta ne wai sultan, gashi na yan gayu, sunan ajebo kuma dan mamanshi, sunan fa ya dace da kai..." tahowa yayi gadan gadan zai damkota ta fita da gudu dan tasan babu abinda ya tsana ace mashi ajebo.. ta bayan kitchen ta nufa ashe suna da wani babban lambu bata taba sani ba nan ta tsaya galala tana kallon wurin cike da sha'awa, fruits dai ba irin wanda babu ga wurin gwanin kyau MashaAllah..." tana jin tafiyarshi ya karaso tace "Sultan dama kunada lambu a nan bansani ba? Gaskiya wurin yayi bala'in kyau kasan me za'ayi mu manta da wani breakfast kaga mango din can da basu nuna ba zamu sha... katso mana guda biyu ya isa kaga manya ne sosai." Baki bude yake kallonta "Hoodah ta ina kika ta6a ganin anyi breakfast da danyan mango? Ga wadanda suka nuna nan birjit sai ki rasa wanda zamu sha sai danye?" Ta kyalkyale da dariya "A'a da dadi fa bakasani ba? Kaidai katso mana kagani." Har wani dukawa tayi wai ita nan tana rokonshi. "Wallahi baki isa ba don bazan hau iccen nan ba, saidai na kira maki gardener yazo ya katso miki..." Wani shiru tayi tana kallonshi can yace "Umar wai mangwaro take so guda biyu danyu ka katso mana idan ka katsa ka sameni backyard kitchen," yana gama fadan haka yaja hannunta suka koma ciki, a hankali ya saki hannunta babu wanda yace komai acikinsu har Umar ya kawo masu mangoes luka luka guda biyu "Yanzu kazo ka tayani mu yanka su duk abinda kaga nayi haka zakayi, kabi a hankali fa kar kaje ka yanke hannu kaja na amsa query wurin Ummi." Dan harararta yayi kafin ya wanke mangoes din sannan suka yanka shi kanana. "Bari nazo." Tafada tana nufar cabinet, wani bowl taje ta dauko mai kyau fari kal, tana kawowa ta koma fridge ta dauko kwalin milk tasan idan Sultan yaci abinnan sai yayi karamin hauka, shi dai kallonta yakeyi ta gama kwad'on mangoes dinnan ta tuttula masu madara cikin glass cup, ta dauko ma kowa spoon daya daya sannan ta debo tayi loma daya nan da nan ta lumshe idanu tana hmmm hmmm kamar wacca take cin shawarma ko kuma pizza "Kasan Allah Sultan ka dandana kaji dadi kuwa? Just give it a try....Wallahi dadi sosai." Yayi kuri yana kallonta baki bude ganin yadda take ci kamar ta samu nama, da kyar ya dauko spoon ya debo shima ya kai baki, ji yayi tsami, maggi, albasa, yaji kai komai ma, runtse ido yayi yana taunawa da kyar har ya samu ya hade, aje spoon din yayi yana girgiza kai, danne dariyarta tayi ta kara dauko spoon ta tura mashi a baki haka nan ya daure ya dinga ci gudun kar ya bata mata rai suyi fada. Idan yaji azabar yajin yayi masa yawa sai yasha madara, ruwa taje ta dauko masu tana dawowa ta lura da yanayinshi "Ya salam Sultan yaji kakeji?" Ta tambaya innocently tare da dora hannu bisa kafadarshi cike da damuwa, daga kai yayi yama kasa magana, zuba mashi madara tayi a cup ta mika masa yasha amma a banza "Ko na dauko maka yoghurt? Maybe zai daina..." Girgiza mata kai yayi, ta kara cewa "Toh me kakeso?" Ya dinga nuna ta da hannu "Nikuma? Me zan maka ko wani abin zan dauko maka?" Kafin ta kare maganar ya hade lips dinsu wuri daya take ya fara kissing dinta itama kamar tana tsoronshi ta fara responding, sai can ta farga take jikinta ya fara rawa ta fara kacaniyar kwace kanta ina ya mata wata irin damka ta kasa ture shi, take ta tuna da irin zaman da sukeyi tasan Sultan tsab xai iya juyewa ya rikice ya koma mugu ba karamin aikinsa bane, da kyar ta kwace kanta sai ta tsinci kanta da sa kanta bisa kafadarsa ta fashe da wani irin kuka, bai hanata kukan ba sai ma hugging dinta da yayi yana rarrashinta, sai can tayi shiru dan kanta kafin ya zare jikinshi ya fita daga gidan. 

********

      2 days later

A kwana biyun da suka gabata ya kasance Hoodah na yawan fita yawan shakatawa da yamma, a hankali sai ta fara enjoying kanta takanje park ta zauna a gurin tana ta kallon yara suna wasansu, a hankali sai ta dinga lura da wata mata sai ta rakube gefe tayi shiru, an kwana biyu ana haka ita dai Hoodah tace bari taje ta sameta taji ko lafiya? dan ta6ata Hoodah tayi hawayen da take rikewa suka gangaro mata tayi sauri ta goge, Hoodah tace "Can I sit please?" Matar ta gyada mata kai tana cigaba da share hawayenta a hankali, Hoodah ta zauna "Thank you, karki ce na maki shishigi amma na lura a yan kwanakin nan kullum nazo sai na ganki a same position, same spot, always crying, nasan ba hurumina bane but please can you tell me what's bothering you?" Matar tayi shiru na yan dakikai can tace "Ni matar aure ce na kasance ina da yaro dan shekara biyar, and that boy yanada matsalan zuciya my husband doesn't have my time he's always busy, gashi Affan ya saba da baban nan nasa toh yanzu sai ya zama baya bashi enough time, ko dawowa yayi gida baya kula shi baya ko kalllonsa...." ta karasa muryarta na rawa "Nayi iya kokarina na ganin na jawo hankalinsa especially for my sick baby, amma abu yaci tura shine boss kuma shi ya ke kula da gida gashi sisinsa bana ci baya bani, so ba lallai bane ko nayi complain ya saurareni...." Hoodah ta numfasa "Baki taba samun aiki ba? Ko bakida ra'ayi?" Ta share hawaye "Na samu aiki mai kyau amma ba'a  dade ba kwarai aka koreni daga aiki..." Hoodah ta numfasa tana matukar jin tausayin matar yana ratsa ruhinta "Yanzu haka sai an masa aiki wanda muna bukatar kudi masu yawa banida halin da zan biya amma wallahi kinji rantsuwar musulmi ko? Toh Aliyu yana da kudin aikin nan, kawai dai bazai bayar ba." Hoodah cikin jin tausayin matar tace "Wannan wane irin uba ne haka? Nawa ne kudin aikin yanzu?" Matar tace "Ki yarda danii bazaki so jin kudin ba don gaskiya sunada yawa." Hoodah tace "No karki damu, zan iya taimaka maki inada halin da zan taimaka..." matar tace "Nasani ke matar dan sarkin garinnan ce, amma wannan ba huruminki bane it's not your place to help me..." Hoodah tace "Nace karki damu meye amfanina toh in bazan iya taimaka maki ba? Trust me zan taimaka maki just tell me the amount." Matar tace "Naji amma ki man alfarma daya kafin nan." Hoodah tace "Ok Menene?" Matar tace "Inaso ki taimaka man ki magana da mijina?" Dan zabura tayi tace "Na'am? Me kikace? Meyasa?" Matar tace "Bai cika zama gari ba, hotel ya cika zama meyakon gidanmu..." wani irin kuka matar ta fashe dashi "Don Allah ki cece baby na, indai kinyi niyyar taimaka man wannan nakeso kiyi man, don Allah ki taimakeni zan iya rasa dana..." Shiru Hoodah tayi tana kallonta na rashin sanin abin cewa....

Daga can nesa bakin wata bishiya wata mata ce cikin niqab kawai daga niqab din tayi tana murmushi tana juya wayarta, "Kawai kiyi accepting wannan kudirin namu, and surely you will meet your doom, just say yess Hoodah.!"