Tuesday 27 June 2017

AUREN FANSA 02

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹

Dedicated to Ummi Aisha and Zeebee💘

          🌹02 🌹


"Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar, idan kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan kuma bakada shi babu damuwa."
Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole yace.
"Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan zan zo na sanar dake."
Murmushi tayi tace
"Allah ya nuna mana."
Yace "Amin."
Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare, gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito parlor.
Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani American series, jin alamun shigowa yasa ta kalleshi lokaci guda kuma tace
"Har ka dawo?"
Yace
"Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa tayi kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa. Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse shirun nasu
"Hamza, wai ya maganar mu ne?"
Yace
"Wace magana kenan?"
Ta zum6uro baki tace
"Ba dai har ka manta ba?"
Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce tana son kud'i.
Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da shagwa6a tace
"Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro kaya."
Shiru yayi gami da sauke nannauyan numfashi yace
"Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa basai ki bata ba ta kawo maki."
Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi don haka sai tace
"Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in nawa zaka bani?"
Yace
"Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai na k'ara maki."
Da sauri ta tashi zaune
"Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an."
A fusace ya tashi tsaye yace
"Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana, ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki."
Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan don ya fusata.

Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci.
K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman baya jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a hanzarce yake komai tashinta yayi daga bacci ya ce mata zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace masa "Toh" sannan ta ja bargo ta rufe har kanta. Girgiza kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi.
Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko yaji yunwa sai yaci kawai.
A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa kamar kullum. Haka ya wuni yana juya maganar Goggo a ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake sukuku dashi har lokacin sallah sannan ya tashi ya fice tare da sauran abokanan aikinsa musulmai.

Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin.
Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a hankali ya ture ta yace
"Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi."
Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige d'akinsa.
Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da kwarkwasa. Can kuma tace
"Alhaji."
Bai kalle ta ba yace
"Na'am."
Tace
"Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta shine nake so ka bani kud'i na bata guddumawa ta..."
Da sauri yace
"Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da zancen wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai ko?"
Murmushi tayi tace
"Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka huta sai muyi magana."
Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita don yaga lokacin sallar magriba ta gabato.


***


"Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata irin makekiyar kujera tana duba magazine da glass d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga ido ta kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya haye bisa cinyar ta yana mai hugging d'inta. Itama hugging d'insa tayi tana kallonsa cike da so tace.
"Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?"
Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum dogo fari ya shigo yana sanye da kayan hausawa harda babbar riga, sai da yazo daidai bakin k'ofar da zata sadasa da parlon yaja ya tsaya yana murmushi, sannan kuma yace.
"Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya lashe baki gaba d'aya wato overall as always."
Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana murmushi.
Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk sosai a jikinta tace
"That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara maka basira, toh saura na Islamiyya, idan har kayi k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar maka ta mussaman."
Cike da jin dad'i Faruk yace
"Allah Mummy?"
Tace
"Kayi ka gani I promise."
Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon, kusa da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana doguwar kujera, sai da ya cire babbar rigarsa sannan ya zauna yana shafa kan Faruk yace.
"My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai kazo muci abinci."
Faruk yace
"Ok Daddy."
Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa.
Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce fara mai yalwar gashi don kuwa har gaban goshinta ya fito. Bana tantama ta had'a iri da larabawa. Kamo hannun mutumin tayi mai suna Adam tace
"Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?"
Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara fizgarsa sannan yace
"Muje sahibata."
Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka nufi kan bene inda hannunsu na mak'ale da na juna...



MSB💖

No comments: