Tuesday 27 June 2017

AUREN FANSA 01

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
_AUREN FANSA_!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM!
Wannan shafin tukuci ne gareku members na pure moment...!

FATY AXLAND SUHANA JANNART,  AUNTY KHADY, HUSNAH, DEEJA WAZIRI, ZEE YABOUR, UMMUHANEEF, MOMYN SULTAN, UMMYN YUSRAH, ZARAH SURBAJO, MOMYN KHADIJA, UMMA YAHYA MUSA (SISIN MAMA), BIEBIE DEE, NANA FA'AD,
 FAtY MANSUR (XARAH), FATY KHALID NA SHUKA, SHAFA ABDUL, SUMYNBASH, SALMA ALI WADA, ROOKY KAZ, AISHA ALI GARKUWA, UMMI HAMBALI, UMMEE GARKUWA, RUFAIDA YUSUF, HAFSAT MUSA, SADNAF, FHARIEEDAT, RAFEE'AT, SAMRAH, BIBA WADATA, SEEMALUV, NEERATU LUV, AYSHA HANWA, AYSHA GANA, UMMU SAFWAN, DELU CHOGAL, MRS FAWWAZ
(YESMEN TAFEESU), RAFI'AT DIKKO, MAMAN IHISAN.❤️💖🌹

          🌹01 🌹


Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi,  wanda zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka, don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka fuskarta ta kanyi ja.
A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma  matar tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye 6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali har yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke kwance tana kukan fitar rai.
A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin wata irin sigar rarrashi.
"Hajiya Bilki."
Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata.
A hankali ya soma magana.
"Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki wallahi."
Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma zuciyarsa ta raunana!
Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana cikin 6acin rai.
"Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata mujiya haba!"
Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa, tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana.
"Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka zaiyi dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole sai kin samu haihuwa
zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya baki kyau, arzik'i ya wadata ki
da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?"
Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya cigaba da magana.
"Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa sannan ki rok'e sa gafara da rahama.
Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi. Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o, kina jina?"
Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na manya yace.
"Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa nakeji."
Ta6e baki tayi tace
"Kayi hak'uri na manta ban girka ba."
Yayi murmushi yace
"Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare shi?"
Tace
"Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya kamata ka barni na huta mana."
Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi murmushi yace
"Haka ne Allah ya baki lafiya."
"Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki.

D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana fitowa ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi kitchen, fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo parlor ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon tashar Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas sannan ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu a lokaci guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka har bacci ya sace sa.

Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm, zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah, bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya, kiranta  yayi a hankali.
"Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace
"Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana fusakarsa ba annuri ko kad'an.
"Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi sallah?"
Tace
"Kayi hak'uri na manta ne."
Girgiza kansa yayi yace
"Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo."
Ko kallonsa batayi ba tace
"To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama mana."
Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar nauyi ya fice daga gidan.

Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce gidan Goggo dake cikin Layout a garin Katsina, yana shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya saba bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar kullum sannan ta soko masa zancen da kullum baya son shi.
"Ya maganar aure Hamza?"
Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa dai na k'asa.


MSB💖

No comments: