Tuesday 27 June 2017

AUREN FANSA 03

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹


Dedicated to my darling Maman Ihsan  (SAFNA) much love darl💕💘❣️

          🌹03 🌹

***

Daddare sai da Bilki ta k'ara tada masa da maganar wasu kud'in inda a ranar sai da ya yi 6ata mata rai fiye da tunaninta sannan ya nuna mata ta cika son kud'i, duk dai abubuwan da ya dad'e  dasu a ransa shekara da shekaru sai da ya amayar mata dashi, sum sum ta tashi ta koma cikin d'aki tsabar borin kunya.
Jingina yayi da kujerar parlon tare da lumshe idanu don ya samu nutsuwa sai dai bai kai ga yin hakan ba wayarsa ta fara ruri, kallon screen d'in wayar yayi yaga sunan da ya bayyana wato My sister, murmushi ya saki na tsananin farin ciki a lokaci guda kuma damuwarsa ta 6ace 6at, d'auka yayi gami da yin sallama, d'ayan 6angaren aka amsa sannan tace.
"Ya Hamza! Da fatan an wuni lafiya?"
Sai da yayi murmushi sannan yace
"Lafiya lau Amina ya gida?"
"Alhamdulillah, ya Anty Bilki?"
"Tana nan lafiya ya zafi kuma?"
"Lafiya lau ya Hamza, da fatan komai lafiya?"
Yace
"Alhamdulillah ya jiki kuma?"
Ta d'an yi murmushi kad'an sannan tace
"Alhamdulillah gashi nan muna ta fama."
Dariya yayi yace
"To Allah ya raba lafiya."
Tace
"Amin."
Sannan ta kuma cewa
"Ya Hamza akan maganar mu dai ce yasa na kira ka, kaga yanzu cikina ya shiga watan haihuwa kuma nasha fad'a maka idan na haifi babyn nan na baka shi ka rik'a..."
"Amina! Insha Allah ke zaki rik'a babynki sai dai ki dinga kawo min shi hutu."
Tayi murmushi mai bayyana hak'ora sannan tace
"Ya Hamza na kenan, yaya na na kaina, nidai kayi min alk'awarin rik'a abinda zan haifa koda bayan raina ne, shine kad'ai burina a halin yanzu."
Haka kawai sai yaji gabansa ya fad'i cikin firgici yace
"Kinga Amina, nasha fad'a maki mutuwa lokaci ne kuma insha Allah zaki ga abinda zaki haifa har ma ki shayar da shi ki daina fad'in maganganu haka ba dad'in ji."
Tayi dariya
"Ya Hamza mutuwa fa na kan kowa sanin gaibu sai Allah nidai alk'awari na zaka rik'e min kaji?"
Nannauyan numfashi ya saki sannan ya d'ora
"Naji shikenan are you happy now?"
"Yeey! Allah ya bar mana kai ya Hamza, nagode!"
Dariya yakeyi sosai itama tana taya sa, sanann ya kawar da wancan zancen ta hanyar jefo mata tambaya
"Ya kingama rubuta list d'in abubuwan da kike buk'ata?"
Tace
"Eh na gama ya Hamza yana hannun Goggo na bata."
Yace
"Ok zan kar6a insha Allah sai na ga abinda za'a siya."
Tace
"Toh ya Hamza Allah ya k'ara bud'i."
Sai da suka d'an ta6a fira kad'an sannan sukayi sallama ko wane yana mai farin cikin ganawa da d'an uwanshi.

Amina k'anwar Hamza ce uwa d'aya uba d'aya, bayan nan kuma su kad'ai ne Goggo ta haifa bayan Amina sai haihuwar ta tsaya, tunda ta haifi Hamza sai bayan shekara kusan bakwai sannan ta haifi Amina, kasancewar su biyu ne kacal yasa suka shak'u da juna sosai Hamza na son Amina  kuma yanaji da ita, kullum suna mak'ale da juna tun suna yara har kawo yanzu da aure ya rarraba su kuma, amma kusan kullum sai sunyi waya.
Amina tasha ci ma Bilki mutunci akan halayanta da take nuna ma Hamza saboda bazata iya jure ganin d'an uwanta cikin bak'in ciki da k'unci ba. Mijinta ya rasu tun tana da ciki wata biyar Allah ya amshi ransa, ga bashi da uwa bashida uba haka ma shi kad'ai ne mahaifiayarsa ta haifa, bayan rasuwar tasa ta zauna nan gidanta da ke cikin garin Katsina a G.R.A.
Wannan kenan!


***

        BAYAN 'YAN KWANAKI

Yau weekend ne Hamza baya zuwa aiki don haka yana gida yana hutawa, bayan ya gama waya da Amina kamar kullum Bilki ta shigo cikin shirin fita unguwa ta sha ado sosai tana ta zuba k'amshi. A hankali yake binta da kallo kafin kuma ya sauke su kan shigar da tayi. Sanye take da wata silky doguwar riga mai dogon hannu kalar brown an mata aikin duwatsu ba laifi rigar ta kamata sai ta yafa gyalen kayan. Haka ma takalminta mai tsini ne kalar kayanta da jaka kalar kayan. Har tazo ta zauna bai bar kallonta ba cike da mamaki, Bilki tace.
"Hamza zan fita."
Ya kalleta da mamaki yace
"Ina zakije?"
Ta had'e rai
"Gidan Hajiya Laila."
Shima ya had'e rai
"Ba inda zakije."
Ta mik'e zumbur!
"Me kace?"
Yayi banza da ita, ta rik'e k'ugu tana sassarfa masifa
"Hamza! Gaskiya ka takura min haka kawai! Kuma ay dah ba haka kake ba wannan k'anwarta taka duk ta zuge ka."
Tashi yayi a fusace yana nuna ta da yatsa
"Kar ki k'ara saka Amina a cikin zancen mu saboda babu ruwanta, kina ji na?"
"Ahayye nanaye, an ta6o masa rabin rai, to an fad'a Amina ce ke zuge ka kayi abinda zakayi."
Bai san lokacin da ya d'auke ta da mari ba yace
"Kisani ni mijinki ne, kuma nafi k'arfin ki wulak'anta ni, sannan wallahi kika k'ara fad'in magana makamancin wannan a bakin aurenki!"
Ta zaro idanu waje
"Iyye! Kan mage ya waye, lallai Hamza yanzu kayi baki, amma tunda ka mare ni don na fad'i gaskiya shikenan kaje Allah zai saka min."
Yace
"Nidai na fad'a miki ki iya bakinki, kuma fita bazakiyi ba ay inace dai sai na bada izini ko? To mugani idan kin isa!"
Har ya tafi ya dawo yace yana mata mugun kallo.
"Magana ta k'arshe ina so ki sani aure zan k'ara na gaji da zama da mace irinki wadda batasan inda duniyar ta dosa ba, na aure ki don ina tsananin sonki amma kisani dole zan k'ara aure."
A fusace ta cakumo masa wuyan riga kamar kura taga nama.
"Aure Hamza! Baka isa kayi min kishiya ba, ni kad'ai ce babu k'ari!"
Yayi dariya gami da cire mata hannu daga rik'on da tayi masa sannan yace
"Kin isa ne ki hana? Ay baki isa ba aure kamar anyi ne an gama."
Yana gama fad'in haka yayi shigewarsa d'aki ko kallonta baiyi ba. Yana jin ihuta tana fad'in
"Wallahi babu wacce ta isa ta shigo min gida ta zauna lafiya, wallahi koma wacece sai na kashe ta!!!"



MSB💖

No comments: