Monday 5 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 34

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 34}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Da asuba Sultan yana tashi yaga babu Hoodah a kan gado wani irin yawu ya hadiye don a tunaninshi har ma tayi tafiyarta, yanzu duk magiyar da yake bazata hakura ba? Masallaci ya wuce yayi sallah hade da azkhar kafin yayi karatun qurani, sai wajen 7:30 ya dawo, yana shigowa yaga Hoodah a kitchen tana hada breakfast a hankali ya shiga kitchen din yana gyaran murya hakan yasa ta juyo, "Good morning habibty." Ya fada yana jingina da counter din kitchen din, kallo daya ta masa ta kauda fuska, can kasan makoshinta ta amsa "Morning." Sannan ta cigaba da abinda takeyi, kallonta yakeyi har ta kammala aikinta taimaka mata yayi suka fara jera abincin kan dining, Sultan debar abincin yayi ya tafi parlor ya zauna Hoodah ta bishi da kallo sannan ta tabe baki, bayan sun gama kawai sai yaje dining din ya jawo hannunta, "Meyafaru ka jawoni nan parlorn ina xaman xama?" Kallonta yakeyi kafin ya numfasa "Yanzu ke Hoodah tsabar rashin yarda da kaddara ta kai haka? Wai meke damunki? Tou ko Ammi tana raye babu abinda takeso face taga jikokinta ballantana mu da muke son ganin jininta, yanzu ke butulci zaki ma Allah bayan ya baki kyautar da ba kowa yake bamawa ba? Wasu fa da kudi suke zuwa kasashen waje nema basu samu, wasu kuma kullum cikin kuka suke don dai kawai Allah ya basu amma basu samu ba, wasu kuwa shekara da shekaru da aure babu haihuwa sai ke don ya baki kike neman ki butulce masa? Shin Hoodah hankalinki daya kuwa? Kuma da kike cewa zakibi Abba in kin haihu zaki maido man baby shin da wane ido xaki kalli babyn in ya girma? Kice kin rabu da mahaifinsa saboda baki yarda da kaddara ba ko kuwa akan wane dalili? Tsakani da Allah ki chanza tunani, na biki na roke ki na lallashe ki amma duk a banza haba Hoodah? Bai kamata kina bari shaidan yana cin galaba a kanki ba har ki dinga furta man irin wadannan munanan kalamai ina mijinki kice wai xaki zubar da ciki, yo ko dan shege ne ay babu kyau zubarwa bare kuma dan sunna," Hoodah har hawaye sun fara kawo mata a idanunta tace "Nidai tou ina so inje koda kwana biyu ne m wurin Abbana." Sai hawaye shar shar, Sultan ya gyada kai "Ay dama bawanda zai hana ki zuwa wurin Abba, amma yanzu fisbailillahi bakiiji wa'azin dana gama yi maki ba Hoodah? Kiyi hakuri mana babu kyau abubuwan da kikeyi." Kamo hannunsa tayi "Wallahi naji don Allah dan annabi kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da kuma fargaba, hakan bazata sake faruwa ba na yarda zan haihu wallahi kayi hakuri, please call Abba na bashi hakuri akan ya janye batun kishiyar nan." Murmushi yayi kafin ya miko mata waya ta ansa tana share hawaye kafin ta danna call, bayan ya dauka suka gaisa sai tace "Abba don Allah kayi hakuri wallahi na gane kuskure na, bazan sake zancen xubda ciki ba, na yarda zan haihu wallahi sharrin shaidan ne don Allah kayi hakuri, ka yafe man sannan ka janye batun karin aurennan." Abba matse speaker din yayi ya saki dariya sosai kafin ya maida ya daure fuska "Ke yanzu kina tunanin wannan dan rokon da kikayi man yasa zan chanza maganata? Abinda har nayi magana da shi abokin nawa akan batun yarsa, aiko aure babu fashi ba dai taurin kai ba tou na fiki iyawa." Sultan ya kalli Hoodah ganin tashin hankalin dake kan fuskarta, karbar wayar yayi yasa a speaker sannan yace "Abba don Allah tace kayi hakuri, ta gane kuskurenta har yanzu baka hakura ba? Kaifa kace mana hakuri shine ginshikin zaman duniya." Ya fada kamar zai fashe da kuka, ji yayi Hoodah ta kamo hannunsa alamun yayi shiru, "Kai Sultan kasan Allah? Ka kiyayeni ni, nafa riga na gama magana har abokina na masa maganar auren, duk waya jawo? Ashe haka kake malalaci wato kai har nema mata yafiya kakeyi ko? Aure dai nace babu fashi," yafada on a serious note, tuni jikinsu yayi sanyi, wani daci ne ya ziyarci zuciyarta, "Don Allah Abba kayi hakuri." Ta fada cikin sheshekar kuka, kuka take tamkar ranta zai bar jikinta har tsoro taba Sultan wanda don dole ya tashi ya tafi kitchen don kawo mata ruwa, babu musu ta karba ta sha, tana gama sha ta fada jikinshi hade da aje wayar gefe tana wani irin kuka, babu abinda yake mata dadi a zuciyarta wani daci takeji har kasan ranta. Rocking dinsu yake a hankali "Kiyi shiru don Allah Hoodah, ko kinaso wani abu ya samu babynmu?" Ya tambaya kamar zaiyi kuka yana kara riketa gam, cikin sheshekar kuka ta fara magana "Sultan wallahi nayi nadama bazan sake ba, kaba Abba hakuri yayi hakuri ya janye maganarshi, wallahi sharrin shaidan ne da kuma tsoro gudun abinda ya faru da Ammi ya faru a kaina, amma yanzu nayi nadama kuyi hakuri." Sultan da kyar ya iya saita kanshi "Hoodah kiyi shiru ki bar kuka, na tabbatar ya yafe maki, wannan kukan bashi bane zai maki magani..." kafin ya rufe baki sai jin muryar Abba sukayi ta cikin waya "Hoodah ki saurareni kina jina?" Har kyarma take ta dauko wayar ta rike suna saurarensa, yayi murmushi "Alhamdulillah ala kulli halin da kikayi realizing wannan babban kuskuren da kike neman ki tafka, amma tunda kin gano kuskurenki na yafe maki komai ya wuce indai har kin tabbatar da kinyi nadama ta gaskiya shikenan maganar ta wuce, na fasa maganar auren, abinda xan fada miki shine ki kula sannan ki kiyaye kinajina? Ita rayuwa da kike ganinta komai rubuce yake sannan kowa da kaddararsa, dan haka ki bi mijin ki Hoodah Allah yayi maku albarka," yana gama fadan haka ya kashe waye yana murmushi,  wani irin farin ciki ne marar misaltuwa ya ziyarce su, fadin ma farin cikinsu bata baki ne, haka sukayita ihun murna cike da jin dadi da annashuwa, Sultan ta kamo ma  hannu tace "Bansan da wane baki xan gode maka ba, hakika na zama butulu da ace na zubar da cikinnan, nayi rayuwar gata hade da kunci da bakin cikin rayuwa, rayuwa ce wadda babu digon farin ciki a cikinta, banason abinda zan haifa ya dandani koda rabin abinda na dandana, I can vividly still see my mother on the floor jikinta gewaye da jini, gaba daya floor wall duk jininta ne," zuwa yanzu ji take zuciyarta ta kafe da sauri Sultan ya debo mata wani ruwan tasha, bai ce mata kala ba don shima yayi experiencing kusan abinda tagani ta kuma taji, a hankali ya jawo ta yayi hugging "Say no more Hoodah say no more...." hugging dinsa tayi back kafin ta lumshe idanu tana murmushi "Thank you Sultan I love you." Wani kayataccen murmushi ya saki zuciyarsa cike da farin ciki yace "I love you more Habibty na, Allah ya sauke ki lafiya." 

*****

Kallonsa take gabanta na duka tara tara, a lokacin kuma taji zuciyarta tamkar wuta take ruruwa a ciki, kallonta yake a natse take ta sadda kanta kasa tari ne ta sarke ta da sauri ya mika mata cup din ruwa tasha, "Zarah menene?" Ya tambaya yana kallonta saida ta tabbatar natsuwarta ta dawo sannan ta fara magana "Ni ka daina kallona ko so kake na kara kwarewa?" A dan masife tayi maganar dan ita har ga Allah idan ya kalleta zuciyarta bugawa takeyi, yar dariya yayi yana nuna mata abincin dake gabanta, da kamar bazataci ba sai kuma ta fara gyara wurin, tasan jira yake ta zuba masa shiru tayi jin ya fara magana "Yau kuma bazaki zuba min ba?" Ay bata jira ya ida magana ba sai tace "Nan ma gidanku ne ko? Kai zakayi serving kanka ko a kira maka Khadija idan baka iyawa?" Da sauri ya mike yasan kishi ne ke dawainiya da ita yasa yace "Bai kai haka ba baiwar Allah." Tana kallonshi ya gama zuba masu abincin a hankali ta fara ci shima haka, kamar daga sama taji takun Khadija ta taho hannunta dauke da cup din dessert, fuskarta dauke da kyakkywan murmushi ta karaso cikin wani matsiyacin lace maroon color dinkin fitted gown, ba abinda ke tashi sai kamshi, ido suka zuba mata har ta karaso yadda kukasan zata tafi dinner wannan kwalliyar datayi, cream caramel din da yayi mugun kyau ta aje gaban Ashraf tana kallonsa sannan ta zauna gefensa tana ma Zarah wani irin kallo, tace "Ya zaki kawo masa abinci babu dessert? Haka ake kula da saurayi ke kuwa baiwar Allah? Yaya Ashraf idan ka gama cin abincin gashi na maka da kaina na hada maka please kasha." Ko kallonta baiyi ba ya kalli Zarah "Kamar naga akwai ice cream a freezer ko?" Ta gyada kai a sanyaye yace "Jeki kawo min zansha," ya kalli Khadija data zama speechless yace "Sorry am not interested in your dessert, zaki iya zuwa kisha kayanki, thank you."  Hawayen data rike ne sukayi nasarar saukowa nan take ta fashe da kuka kamar ranta zai fito, baki sake Ashraf yake kallonta "Khadija ya da kuka kuma? Lafiya dai ko?" Ya fada yana kokarin tashi tsaye, girgixa kai amma ta kasa magana karshe ma kukan nema yake yaci karfinta, tsaye yayi in shock yana mata kallon irin lafiya dinnan? "Abinda na fada ne ya bata maki rai?" Girgiza kai tayi tana kara fashewa da wani sabon kukan "Yaya Ashraf soyayyarka taci karfina, wannan rejecting na abinda na kawo maka ba karamin impact yayi ma zuciyata ba, yaya Ashraf ina sonka wallahi tallahi ina sonka, bansan ya zanyi da raina ba..." ta kifa kanta bisa table tana shesheka kamar zata shide, turus yayi yana kallonta, in baccin yaga hawaye da sai yace she's trying to get his attention, da kyar ya samu ya furta "Am sorry Khadija, hakuri zakiyi ki cireni daga ranki, Am in love with your sister Zarah, I love her with every part of my being, bazan iya maki karya ba Khadija karan kanki kinsan a addinin musulmi haramun ne! Dole zaki cire ni aranki I belong to somehow else...."  Girgiza mashi kai tayi tana kukan fitar hankali kafin tace "Nasani, amma ka duba girman Allah ka tausaya min, ko yanzu da kake fada man wannan kalaman ji nake kamar ruwan zafi ne ake yayaffa mun, ka taimaka man kar sonka ya kasheni..." Zarah ce ta karaso zuciyarta na tafasa gadan gadan tayo kan Khadija kamar zaki tana fadin "Ko zaki mutu saidai ki mutu! Amma wallahi Ashraf ya maki nisan da bazaki iya kamo sa ba, wannan wane irin abu ne haka? Tou wallahi baki isa ba Khadija! I told you times without number abinda kikeyi ba daidai bane, you're trying to come between two lovers that are madly in love with each other! Enough is enough na gaji! Na baki last warning ki fita harkarsa a gidannan in ba so kike nida ke a kwashi gawar daya tsakani da ke ba!" Tana gama fadan haka ta ruga da gudu tayi waje tana fita ta zube a nan ta fashe da wani irin kuka tamkar ranta zai fita, da sauri Ashraf yabi bayanta bayan yayi ma Khadija wani irin mugun kallo, har ya juya zai fita yaji Khadija ta wani damke masa hannu kallonta yake zuciyarsa na tafarfasa kafin ya fizge hannun nasa ya fita nan ya barta tsaye hawaye nabin kuncinta, yana fita ya iske Zarah zube kasa tana kukan fitar rai, wani irin tausayinta yakeji da sauri ya duka inda take tana ganinsa ta kara sa kuka sosai zuciyarta kamar zata bar kirjinta, "Yaya Ashraf ka aureni kona huta da wannan bakin cikin da Khadija ke kunsa man! Just let's get married da munyi aure shikenan zata hakura ta kyale mu..." gyada kai yayi ya fiddo hanky ya fara goge mata hawaye, "Zan aure ki Zarah, jira nake Mummy ta dawo in fada mata zan tafi gida daga nan zan turo da manyana, kinji? Ki kwantar da hankali ita Khadija ta isa ta aure ni ne? Ba ni ne namiji ba? Ke zan aura InshaAllah tashi muje ki wanke fuskarki a tap." Mikewa tayi bayan ta gyada kai kamar wata karamar yarinya sannan ya rakata ta wanko fuskarta ta, sadda suka koma ciki Khadija bata nan, dining suka nufa ya sake zuba masu wani abincin, bayan ya gama yace "Ki daure kici abinci." Murmushi tayi masa a haka suka cin abincin har suka kammala.

Can cikin dare da misalin karfe biyu na dare sai wayar Ashraf ta fara ruri, a firgice ya bude ido yana mai jawo wayar tasa daga kan bed side, kasa gane number din yayi ba tare da tunanin komai ba ya kara a kunne, "Hello yaya Ashraf! Da fatan ban tashe ka a bacci ba ko?" Da mamaki yake saurarenta har wani faduwa gabansa keyi wai wannan wace irin mayyar yarinya ce? "Da alama bacci kakeyi na tashe ka ko?" Daure fuska yayi tamau yace "Lafiya kike kirana Khadija da tsohon daren nan? What's wrong with you?" Wata makirar murmushi ta saki cike da salo na kwarewa gamida yaudara tace "La kayi hakuri yaya Ashraf naga miss call dinka ne da wannan layin nawa shine ma nake ta mamaki nasan ba kowa yake da layin ba sai special people kadai," ta karasa tana murmushi, "Ni na kiraki da wannan layin? You must be mistaken, ni ban taba kiranki da original layinki ba bare wani special line, look duk wani salo na yaudara da kike son ki tsiro dashi bazan taba fadawa ba no matter what you do, nasan irinku sarai mayaudara masu kwacen saurayi gorrit?" Maimakon ta bata rai sai ta saki murmushin yaudara "Ayya kayi hakuri idan na bata maka rai is not my intention, toum bari dai na barka kayi baccinka kar na cika ka da surutu, good night!" Kit ta kashe wayar ta bar Ashraf sagale da waya a kunne, wannan abun na Khadija sai anzo an fara taimaka mata da addu'a ta fara hauka ne, kwanciya yayi cike da tunani kala kala a haka bacci yayi awon gaba dashi. Da safe tun karfe bakwai na safe Khadija ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wani baggy trouser sai wata yar ficit din riga marar hannu sosai, hada hada takeyi a kitchen tana kokarin kammalawa da sauri, saida ta tabbatar ta hada komai saman tray kawai sai ta nufi bangaren nasu tana zuwa ko knocking batayi ba ta fada ciki, Allah ya rufa masa asiri ma ya kammala sanya kayansa yana balle ma6alli, a razane ya dago yana kare mata kallo zuciyarsa na tafasa, a fusace yace "Wai ke wace irin dabba ce? Ke a gidanku ba'a koya miki sallama bane da zaki fado min cikin daki sai kace ajiya kika bani?" Murmushi ta saki ta karaso ta aje abincin sannan tace "Kayi hakuri don Allah nayi sallama maybe baka ji bane, am so sorry please, Dama breakfast na kawo maka naga Zarah kullum ita ke faman dawainiya da kai shine nace bari na taimaka mata yau ta huta..." daga mata hannu yayi "Wallahi ko zan mutu da yunwa bazanci abincinnan ba, don haka maza maza zo ki dauka ki fita dashi."  Bata ce komai ta tsugunna ta fara masa serving abincin sai da ta gama ta taso dab da dashi ta mika masa plate din tana binsa da kallo daga sama har kasa, tace "Kayi hakuri kaci don Allah, I made it with love and care..." kafin ta karasa magana sai ji tayi ya kifar mata da plate din saman riga wanda a sanadin haka duk ta bace da sauce ga zafi dama, wani uban ihu ta kurma, hannunta ya damko ya shiga dragging dinta kamar zai tashi sama saida ya fita daga side din kwata kwata sannan ya cillata yana mata kallon tsana, "Bana sonki bana kaunarki! Kuma daga yau na sake ganin kin shiga harkata a gidannan wallahi sai kinsha mamaki ki fita hanyata for the last time! And kafin na dawo make sure you clean that mess up or else..." ya matso dab da ita fuska daure yace "I will deal you in this house!" Yana gama fadan haka yasa kai ya fita kamar zai tashi sama nan ta bishi da kallo zuciyarta na tafasa kamar ta bar kirjinta. 

Ciki ya koma nan ya tarar da Zarah har ta kammala breakfast tana faman hada masa a tray, sautin murmushinsa kawai taji shi ya tabbatar mata da isowarsa, "Basai kin kai min daki ba a kan dining kawai zanci." Juyowa tayi, tayi murmushi sannan ta nufi dining ta kai ta jera komai, zama sukayi Zarah tace "Ina kwana? Halan yanzu ka tashi daga bacci?" Yayi murmushi yana tsiyaya ruwan zafi cikin cup ya dan dakata yana kallonta cike da so da kauna "Waya fada maki yanzu na tashi?  Ay tun asuba yau ban koma bacci ba..." itama murmushin ta maida masa kafin tace "Okay, naga idanunka sunyi wani kala, me xan zuba maka? Akwai chips, plantain, pancakes akwai sauce me kakeso wane combination?" Ya gama hada tea dinsa sai ya dora hannunsa bisa table yace "Duk abinda kikaga ya dace zan ci, after all ke kika man serving dolena inci." Ya karasa yana mata wink,  sadda kanta kasa tayi murmushin fuskarta ya kasa boyuwa, a haka sukayi breakfast din bayan sun gama yaga ta fara kokarin tashi tsaye, ganin ya tsare ta da idanu yasa tace cikin muryar shagwaba "Banki zanje banaso in iske layi," ya kalleta "Tou gashi nikuma ban gaji da ganinki ba?" Har kasan ranta taji sanyin maganar. Dama akwai wanda akeso ayita kallo kamar wata tv? Saurin kawar da tunanin tayi kafin tace "Tou ay kasan bank yadda yake in mutum baije da wuri ba layi zai iske." Yayi murmushi "Tou kizo in rakaki bankin?" Tayi saurin girgixa kai alamun a'ah tana murmushi, Ashraf yace "Tou kafin ki tafi kice zakiyi missing dina." Shiru tayi tana auna kalamansa, tabbas kona second daya bata tare dashi ba karamin kewarsa take ba, a hankali tayi murmushi tace "Zanyi missing dinka sosai ba kadan ba, kafin na dawo zan maka tsaraba." Yar dariya yayi na alamun jin dadi yace "Na hutar dake yan mata, banason wata tsaraba, ke kadai nakeso ba abin hannunki ba." Murmushi tayi ta wuce ciki da sauri ya bita da kallo, can sai gata ta fito tana sanye da pink hijab da hand bag dinta, kallonta yakeyi yadda hijabs ke mata kyau shidai bai taba ganin ta fita koda da mayafi ba, hakan ba karamin kara masa sonta yake ba, kallon juna suka tsaya yi kafin tayi hanyar fita kanta kasa, kusan cin karo da Khadija tayi a bakin kofa nan suka tsaya suna kallon juna cikin ido kafin Khadija tayi murmushin mugunta, "I can see you're claiming what's going to be mine, kisani wannan na kankanin lokaci ne kukeyi kafin nayi taking over, sai kinyi kuka da idanunki amma a lokacin bakida mafita illa ki dau kaddara da hakuri..." Zarah itama irin murmushin da tayi mata irinshi ta maida kafin ta fara zagaye Khadija tana mata mugun kallo sai dai taxo daidai gabanta ta tsaya tana kallonta from head to toe, "Am sorry to say Khadija but Ashraf will never fall for someone like you, ko inuwarki bazai so ba ballantan kuma ke." Ta fada tana nuna ta da yatsa sannan ta cigaba "No matter what you do, you'll never succeed InshaAllah, shi Allah bai bari a cutar da innocent person no matter what happens, keep on dreaming zaki farka ne kiga na zama mallakin Ashraf halak malak, and then me xakiyi? Nothing right?" Ta fada tana mata wani kallo daga sama har kasa, daga haka ta sa kai ta fita tabar Khadija tsaye tana jin kamar zata kamu da ciwon zuciya, dafe bango tayi hawaye ya taran mata a idanu kafin tace "I will never let you take hime away from me, is either na aure shi ko kuma mu rasa shi gaba daya!"

No comments: