Saturday 24 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 36

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 36}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




A ranar Zarah kasa rintsawa tayi gaba daya abubuwan da suke faruwa ba karamin girgiza ta sukayi ba, wai mey ya shiga kan Khadija ne? Anya kuwa yar uwarta ce ta jini? Bata tunanin wanda suke fito ciki daya zaiyi mata haka, maganganun da Ashraf ya fada mata kafin ta kwanta ba karamin amfani sukayi mata ba, dan kuwa data samu tayi bacci da kyar tana farkawa da misalin karfe uku saura sai taji ranta ya saki sannan tana jin natsuwa cikin kirjinta, kasa komawa tayi sai kawai ta sauka daga kan gadon ta nufi bathroom ta dauro alwalla ta fito ta dinga jera nafilfili sai da data ji kiran sallar asuba sannan ta tashi tayi sallah bayan ta idar, tana nan har gari ya washe tangaram mikewa tayi ta kwanta nan da nan bacci yayi awon gaba da ita. Karfe goma da kusan rabi da farka, daga bisa bene ta tsaya cike da mamakin ganin gidan fes an share an goge sai kyalli yakeyi, galala take bin parlon da kallo, a sanyaye ta sauko kasa ta nufi kitchen mai aikinsu ce wacce ta tafi gida hutu ce ke tsaye tana goge cooker, da mamaki Zarah tace "Mama Hauwa!" Mama Hauwa ta juyo ta saki murmushi, da sauri Zarah ta nufeta ta makalkaleta cike da murna, Mama Hauwa mai aikinsu wacce kakarsu kafin ta rasu taba Mummy ita tun tana yar yarinya har ta girma ta mata aure, bayan an mata auren shekara da shekaru mijinta ya rasu ba tare da sun samu haihuwa ko daya ba, aikuwa bayan ta kare takaba shine Mummy ta sake daukarta tunda bawani shekaru gareta masu yawa ba, auren wuri akayi mata Mama Hauwa batada matsala ko kadan tana xaune dasu tsakani da Allah, ba karamin shakuwa Zarah tayi da ita ba, duk wata matsalarta tana fada ma Mama Hauwa da kuma shawarwari in ta kama, tunda Mummy bata cika zama ba tana harkar kasuwancinta bata ba yaranta enough attention yadda ya kamata, "Yaushe kika dawo Mama Hauwa?" Zarah ta tambayeta still tana rike da ita, Mama Hauwa tayi murmushi tace "Tun karfe takwas na iso, ina ta bubbugawa naji shiru har baba mai gadi ban gani ba? Ina yaje? Sai can naga wani bako ya fito daga bangaren Yasir ya zo ya bude man gate, tou shine ma yasa makulli ya bude man ta kitchen bayan na fada masa ko ni wacece, ina shigowa na hau aikace aikace, gida ba kowa babu Hajiya in ba Khadija data fito hada shayi da safe ba ashe tazo hutu? Na tambayeta kina ina tace bata sani ba." Zarah ta girgiza kai "Allah sarki Mama Hauwa ay bamuson zaki dawo yau ba, eh baki gane shi ba yaya Ashraf ne abokin Ya Yasir kin manta shi? Wai daga zuwa sai ki hau aiki Mama Hauwa bazaki ma ko huta ba keda kika sha hanya? Hmm wallahi baba mai gadi fa baya nan shima yayi wata tafiya gidan mu kadai ne Mummy ma basu nan sunyi tafiya amma gobe zasu dawo InshaAllah, aiko Khadija tazo hutun semester amma ta kusa komawa itama." Mama Hauwa tace "Ayyo tou babu damuwa, bari in karasa aikina." Daga haka ta cigaba da aikinta har ta kammala ta kwashi buckets da tsummanan ta fita zata wanke, karatun Qurani Zarah ta kunna tana bi tana girki, koda Mama Hauwa ta dawo zata kama mata ce mata tayi ta barshi kawai zata karasa taje ta huta, Zarah aikinta ta cigaba dayi a natse tana gamawa ta jera komai kan dining sannan ta shiga wanka. Tana fitowa daga wankan aka hau kwankwasa kofa gyara towel dinta tayi ta zumbula hijab har kasa sannan tace "Wanene?" Muryar Khadija taji tana fadin "Nice Zarah ki bude min kofa." Wani irin yawu ta hadiye mai daci kafin ta karasa bakin kofar ta bude mata, "Kin tashi kenan?" Abinda Khadija ta furta kenan tana yamitsa fuska kamar wacce ke tauna Panadol, sai  can kuma ta saki fuskarta tana murmushi, ita dai Zarah tsayawa tayi tana binta da kallo yadda take wani tauna chewing gum, kasa boye mamakinta tayi can tace "Na tashi, lafiya kike man knocking kofa kamar kin bani aiiya a ciki?"  Khadija tayi murmushi "Haba sis me yayi zafi haka? Nifa bada tashin hankali nazo maki ba, in fact nayi nadamar abinda na aikata maki nazo na baki hakuri, don Allah kiyi hakuri wallahi sharrin shaidan ne..."  Kasa magana Zarah tayi don ta kasa yadda da maganganun da tazo mata dasu, "Ya kikayi shiru? Baki yadda dani ba ko?" Zarah ta saki baki tana binta da kallon mamaki kafin ta ankare Khadija ta zube kasa tana zubda kwalla, abinka da mai taushin zuciya tuni Khadija ta bata tausayi hannunta ta kamo tana share mata hawaye, "Indai har kin tabbatar kinyi nadama ba ha'inci tou na yafe maki, Allah ya yafe mana gaba daya," Murmushi Khadija tayi sannan tayi hugging Zarah tana fadin "Alhamdulillah, nagode Zarah InshaAllah bazaki sake samun matsalar komai ba daga gareni," Zarah tayi murmushi "Bari na sa kaya sai muje ki ba Ashraf hakuri sannan sai muje muyi breakfast ko?" Tou tace kafin Zarah ta shiga daki ta kimtsa cikin wata material purple mai manyan flower irin mai madaurin nan a ciki, sai tasa hula hannunta Zarah ta kamo har side din Ashraf yana danne danne a laptop suka shigo, da da farko murmushi yayi ma Zarah sai da yaga Khadija tuni ya hade rai kamar bai taba dariya ba, karasawa sukayi ciki ya mike yana binsu da kallo kafin yace "Zarah me wannan take min cikin daki? Don't you know how much I hate her? Bana son ganin bakar fuskarta kamar yadda zuciyarta take baka!" Durkusawa Zarah tayi cikin taushin murya tace "Nasan abinda Khadija tayi bata kyauta ba tabbas, she hurt both of us kuma nasan ba lallai bane mu duka mu manta da abin farat daya, amma kuma Khadija tayi nadama ta bani hakuri ka dubi girman Allah ka yafe mata koba komai yar uwata ce kayi hakuri ni na riga na yafe mata, please mi amor." Ajiyar zuciya ya sauke a raunane yace "Zarah ko kare kika nemi alfarmarsa kisani zan saurare shi bare kuma kanwarki ta jini, na yafe mata kuma ina fatan tayi nadama har can kasan ranta." Khadija ta durkusa "Nagode sosai yaya Ashraf, Allah ya yafe mana gaba daya." Yace "Amin." Zarah tace "Kazo muje muyi breakfast." Yayi murmushi "Azumi nakeyi yau." Tace "Oh yau monday right?" Ya gyada kai "Kuje kuci abincinku dear." Murmushi tayi kafin su mike itada Khadija su fita daga dakin. 

Kan dining suka zauna Zarah ta bude kulolin abincin tana murmushi tace "Yaushe rabon dana girka wannan abincin ci kiji idan har yanzu na iya?" Ta fadi tana mika Khadija plate dinta tana murmushi wani dadi na ratsata yadda yar uwarta ta shiryu haka tashi daya "Ay bazaki manta yadda ake girkin nan ba Zarah, ni zanzo ma in fara daukar lesson very soon." Sukayi dariya gaba daya a haka suka cigaba da cin abincinsu cikin nishadi da annashuwa. ---

Washe gari babu abinda sukeyi sai gyaren gida saboda dawowar su Mummy, Zarah da Khadija gyara suke bil hakki kafin sha daya na safe sun tsabtaccen gidan sai kamshi ke tashi, Mama Hauwa tuni ta gyare kaji tas Zarah ta dora peppered chicken ita kuwa Khadija na hada Chinese fried rice. Ashraf kuwa yana gefe yana dura zobo da kunun aya cikin jugs da kwalabe, suna aikin suna fira. Mama Hauwa ta gyara kayan salad Zarah ta hada hadadden rich salad wurin sha biyu sun kammala komai sun jera bisa dining gida sai kamshi yake, wanka duk suka tafi sukayi suka shirya cikin atamfa wata sallah aka dinka masu ita iri daya kawai color ne ya bambanta, basu karasa shiri ba suka ji karar gate aikuwa da sauri suka fita a guje suka nufi waje ashe shi Ashraf ma har ya rigasu fita nan ya tarosu, suna fitowa daga motan sukayi hugging dinsu Mummy, Mama Hauwa ce ta fito itama tana "Lale lale dasu Hajiya, sannunku da zuwa sannunku da zuwa." Wani irin farin ciki Mummy taji na ganin Mama Hauwa, nan ta tarbesu cike da murna bayan an gama gaggaisawar yaushe gamo kafin kuma Mummy tasa a shigo da kaya ciki, wasu irin manya manya kwalaye ne aka dinga jida ana kaiwa ciki, akwati kam yafi kala hudu wanda aka shiga dasu, nan Khadija ta fahimci ay kayan kitchen ne Mummy ta siyo ma Zarah, a parlor suka baje ana fira Ashraf yace da Yasir "Gaskiya nayi fushi dakai Yasir, gaba daya ka tafi ka manta dani a nan ko?" Yasir yayi dariya "Ah haba wallahi Mummy ce ta tsaida ni ay ni da tuni na dawo ma," Ashraf yace "Tou ya hanya?" Yace "Alhamdulillah, tashi muje ka rakani na watsa ruwa." Daga haka suka mike suka fice Yasir yana dafe da shoulders din Ashraf. Mummy ta kalli yan matanta tace "Am sorry girls, wallahi wata hidima ta tsaida ni sheyasa ma ban dawo ba, wasu kaya na tsaya clearing da fatan dai babu wani matsala?" Zarah tace "Wallahi Mummy komai lafiya, wai wadannan uban kayan fa?" Mummy tace "Wallahi kayanki ne Fatimah, kinsan gara in rarrage wasu abubuwan don Yasir ya fada man Ashraf yace masa so yake da mun dawo yaje gida maganarku dashi, tou nasan dai bazai dau lokaci mai tsawo ba, tou sheyasa na rage kayan kitchen don gaskiya na siyo abubuwa da dama so nake mu zauna dake sai ki fadi man abubuwan da kikeso na kitchen sai a kara maki." Tunda Mummy ta fara magana gaban Khadija ke faduwa daurewa tayi ta kalalo murmushin dole, "Gaskiya kam Mummy haka yafi, tou ya kamata kuyi sallah ga abinci nan kuci." Mummy ta mike "Hakane har watsa ruwa zanyi, please ku kwaso kayannan ku kai man shi sama box room a jera su a ciki." Da toh suka amsa kafin su mike su fara tattara kayan suna kaiwa sama, ko kadan Khadija bata bari ta nuna wani abu ba ta danne. 

Suna kan dining suna cin abinci ne Mummy tace da Ashraf "Kayi hakuri Ashraf nasan kana so kaje gida na tsaida ka ko?" Yayi murmushi "Ba damuwa Mummy." Tace "Tou yaushe kakeso ka tafi?" Yace "Nan da kwana hudu haka zuwa biyar." Tace "Allah kaimu, da fatan dai yaran nan basu baka wata matsala ba ko?" Ya kalli Khadija wacce kanta ke kasa tana juya spoon, idanunsa na kanta yace "Ko kadan babu wata matsala, everything was okay." Mummy tace "Tou MashaAllah, ke kuma Khadija yaushe zaki koma school har yanzu hutun naku bai kare bane?" Ta dago kanta tace a sanyaye "Ya kusa karewa Mummy nan da 3 weeks." Mummy ta kalleta "Wai wannan hutun dai ya dade kin tabbatar baki kara kwanaki ba?" Ta girgiza kai da sauri "Ban kara ba Mummy." Mummy tace "Tou shikenan, Yasir ma sun daidaita da Hafsat InshaAllah ina sa ran hada bikinsa dana Ashraf gaba daya." Kowa na wurin yayi murmushi yana fadin MashaAllah, Allah ya tababtar da alkhairi mummy tace Ameen, da haka suka karasa cin abincinsu suna cigaba da fira. 

*________

"Idan har kinaso Ashraf ya soki sai kin kwantar da hankalinki kin daina tashin hankali kin jawo hankalinsa gareki cikin siyasa, dole fa ya fara sonki muna nan dake aure shida Zarah baza'ayi ba, da fatan kin fahimta?" Wannan shine shawarar da wata kawar Khadija ta bata a yayin data kai mata kukanta wata rana, tou shine fa taje ta bada hakuri ta nuna tayi nadama. Zaune take a restaurant tana jiran order din abinci, tuno da magaganun kawarta tayi tana tunanin hanyar da zata bi don jawo hankalin Ashraf gareta wani dan guntun murmushi ya subuce mata, wayarta ta dauko ta kirashi bai dauka ba, ta kuma kira a karo na biyu bai dauka ba fidda rai tayi nan ta zauna jugum, message ta tura masa kafin ta aje wayar aka kawo mata abincinta. Godiya tayi mata kafin ta gyara zama yadda zata ci abincinta, kamar daga sama taji muryarsa yana fadin "Khadija yane?" Ya fada tare da janyo kujerar dake gabanta ya zauna harda kiran mai abinci, Khadija bata san lokacin data sauke wata boyayyar ajiyar zuciya ba, kallonta yakeyi tana cin abincinta a natse  kafin yace "Naga sakonki na kina son ganina a lokacin da kika kirani ina masallaci sheyasa kikaga ban daga kiranki ba, tou yanzu ya akayi meyafaru? Meyasa kike son ganina a nan ba a gida ba?" Tayi murmushi "Hakane, dama ba wani abu bane kawai inaso ka bani shawara me zanba Zarah as a wedding gift? Sheyasa na kiraka a nan bana son tasani surprise zan mata sai ranar bikin she will be shocked!" Ya kalleta da sauri "What do you mean she will be shocked?" Ta gyara murya da sauri tana fadin "I mean wane irin gift zan bata da zataji dadi sosai?" Yace "Komai kikaga ya dace ki bata ki bata mana, gasu nan kala kala, ki siya mata ko mota, ko ki bata jirgi...." a daidai lokacin ne mai kawo mashi abinci ya kawo masa, bayan ya aje abinci ya tafi Khadija ta kalli Ashraf tace "Jirgi da mota? Ina naga kudin siyan wadannan abubuwan? Ka rufa man asiri yar karama dani." Yar dariya yayi ya fara cin abincinsa, "Wai yar karama dake kiji tsoron Allah Khadija, masu shekarunki a kauye suna can sun fara tara jikoki bama yaya ba." Hararar wasa ta mashi, yayi dariya yace "Zan fadawa Mummy gaskiya ya kamata a aurar dake a huta haka nan." Dariya tayi "Sai inga da abinda za'a aurar dani ay, badai siyen gida da kayan dake ciki ba in zauna, sai a jira na samu saurayi tukunna." Dariya ya kuma yi "Saurayin ma ay zaki samu very soon, yanzu dai maganar gift ki bata something special wanda zatayi appreciating ta kuma ji dadi sosai." Ta gyada kai "I will think about it InshaAllah, nagode da amsa kirana da kayi thank you very much." Koda suka gama cin abinci har titi ya rakata ya tsaida mata adadaita don shi yace mata ba gida zai je ba yanzu sai anjima zai dawo zaije yayi renewing passport nashi, yayi booking flight dinsa. Saida ya samu mai napep din ya kalleta yana fadin "Wannan murmushin dai sai ki adana ma wanda zaki aura don zai ji dadi sosai." Dariya tayi "Dole kam yaga murmushin nan mai tsada don shi kadai ya cancanta ya gani," daga haka ta shige shi kuma ya juya, da murmushi ta karasa gida zuciyarta fes, "A hankali a hankali dai." Ta furta cike da jin dadi. Wani irin farin ciki takeji yana ratsa ta kamar ta kira Sumayya ta fada mata sai kuma ta tuno da labarin zaifi dadi da ido bata waya ba sai ta hakura. A da tana ganin kamar bazatayi nasara ba amma sai daga baya ta fahimci yafi komai sauki, daga karshe ma da yamma garden ta koma da dan lemunta da snacks tanaci tana latsa waya, batasan da zuwan mutum ba saidai taga an daukar mata cookies guda daya, gabanta saida ya fadi tana dagowa taga Ashraf ne yana zaune gefenta da laptop a gabansa yana duba wasu boxes da zai siya na lefe yana so yayi order, bai kalleta ba idonsa na kan laptop ita kuwa kallonsa tayi na seconds kafin ta dauke idonta da sauri, sunfi minti sha biyar a haka karshe ma cup din da take shan juice din ya dauke ya maida gabansa, "Wai dan Allah meye haka? Idan kanason sha kasa a kawo maka naka mana ni ba bakuwar zafi bace kasan kawo maka zanyi ay." Da mamaki yake kallonta kafin yace "Maida wukar malama juice bazai hadani fada dake ba," cup din ya turo gefenta kafin ya dauko wayarsa yayi dialing yakai a kunne, yace "Dearie please kawo mun juice ina garden." Dayan bangaren tace "Wane iri?"  Ya karkato ya kalli wanda takesha kafin yace "Pineapple and coconut." Kallonsa take bako kyaftawa tace "Wai kana nufin baka san wasa ba?" Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da abinda yakeyi ya hade fuska kamar bai taba dariya ba, "Wai kyamata kike da baki iya hada cup daya dani Khadija?" Cup din ta aje tana kallonsa "Yaushe mukayi haka dakai? Nifa wallahi ba haka nake nufi ba wallahi wasa nake maka." Kara hade rai yayi "Wasa ko? Nan gaba kuma ay zagina zakiyi Khadija." Juyowa tayi suna facing juna "Nifa ba kyamarka nake ba me kake nufi wai daga wasa don Allah?" Shiru yayi ya daga kai tare da hango Zarah tafe dauke da tray,  ya kalli Khadija "It's okay gashi nan an kawo mun nawa." Karasowa tayi tana murmushi ta aje tray din gefensa ta zauna, ta kalli Khadija "Halan rowa kikayi masa? Kedai kinji haushi wallahi." Ta karasa tana tsiyaya masa a cup sannan ta mika masa, "Kayi hakuri don Allah Khadija sai a hankali," Ashraf yace "Wai fada take dani akan ordinary juice." Zarah tayi murmushi "Ah Khadija Ashraf din yau ake fada dashi he's your friend now remember?" Khadija ta kakalo murmushi "Fada kuma? Wasa fa nake masa shine ya dau abin da zafi..." Wata irin dariya Ashraf yayi yana fadin "Rabu da ita mutum sai rowar tsiya." Khadija ta mike ta murguda baki ta yi gaba tana fadin "Kaidai kasani kaji dashi dai, ni karma ka kara nuna kasanni daga yanzu." Zarah ta fashe da dariya tace "Ah Khadija sai nazo biko gaskiya ayi hakuri!" Take itada Ashraf suka kyalkale da dariya, xama sukayi suna fira cike da nishadi yana nuna mata akwatinan da yakeso yayi order, runtse idonta tayi gam gam wai don kar ta kalla shi kuwa Ashraf yace "In baki kalla ba zakiga ana jide ghana must go a kofar parlor." Wata irin dariya ta kyalkyale dashi kafin ta mike tayi ciki da gudu, me Ashraf zaiyi in ba dariya ba?

Washe gari cousins dinsu Zarah su biyu kusan tsararraki ne sukazo daga Yemen, wani irin ihun murna sukayi cike da murnar ganinsu, daya ke sunfi shiri da Zarah a dakinta suka sauka haka suka baje suna firar yaushe rabo. Daren ranar bayan sunyi dinner suna dakin Zarah, gyara zama Raihan tayi tana kallon Zarah da guntun murmushi a fuskarta, "Wai ni Raihan bangane wannan murmushin da kikeyi tayi ba tun dazu wai meyafaru haka?" Dariya Raihan ta fashe dashi tana gyada mata kai, Ammah da kamar an kunna radio ta fara bata labarin su itada Ashraf ita kuwa Raihan dariya kawai takeyi, "Dan darajar Allah? Kai amma naji dadi wallahi bansan waye angon ba saida kika fadi man yanzu." Ammah tace "Dama na fada maki kiris ya rage bikin nasu wannan irin kauna haka?" Dukan wasa Zarah ta kai mata "Nifa wallahi banki ba a daura auren ba yau, keni wallahi..." kukan shagwaba tafara harda bubbuga kafa, Raihan da Amma suka kyalkyale da wata irin dariya, "Wayyo Allah diyar mutane ta afka kogi bari inje in fadawa Mummy karki lalace mana cikin gida." Wata irin janyowa tayi mata har saida ta fada kan gado "Ke dalla banza sharri zakiyi mani? Ni ba aure nakeso ba shi din dai nakeso." Dariya sukeyi ba kakkautawa harda tafawa "Yanzu dai tsaya aurenshi kikeso kiyi ko da gaske?" Amma ta tambaya tana murmushi, Gyaran murya Raihan tayi harda gyara zama, Zarah tace "Gaskiya kunga ko? Wallahi ina sonsa ni banma san ya akayi ba na fara sonsa haka ba, I think love at first sight." Ganin yadda tayi maganar da mahimmanci yasa suka girgiza kai suna kara bata attention, "Lokacin da ya Yasir yace zaizo da bako gidannan har haushi naji irin kawai sai yazo yayi mana zaune a gida, daga baya kuma naga yanada tausayi yanada kirki, da mutunci sosai tou nidai I don't know how it happened na fara sonsa, kuma alhamdulillah he loved me back and now we are getting married soon InshaAllah," fira suka cigaba dayi cike da nishadi kafin wayar Zarah ta fara ringing mikewa tayi tana murmushi ta nufi parlor tana rungume da throw pillow, "Ina wuniiii!" Kalmar taja cike da kwanciyar hankali, "Fadimatu na ya kike?" A shagwabe ta tabe baki yau ce ranar da farko daya kirata da fadimatu na, "Yau kuma Fadimatu na koma? Kuma baza'a amsa gaisuwata ba?" Yayi murmushi "A'a na isa? Lafiya Zarah ya kike ya yau?" Tace "Lafiya wai yanzu ka kusa tafiya ka barni ko? Gaskiya zanyi missing dinka sosai." Yace "I will miss you more dearie... kuma ay ba dadewa zanyi ba zan dawo, kinga dana dawo sai ayi maganar aurenmu ko?" Khadija ce taga ta fito daga kitchen kamar daga sama, wani irin tsoro Zarah taji da taga mutum batayi zaton akwai kowa kitchen ba don bataji alamu ba, batasan lokacin data latse wayar ba ta mike jikinta na bari, "Zarah nice fa, wai tsoro na baki?" Zarah ta wani saki ajiyar zuciya tana sauke numfashi "Wallahi naji tsoro dama kina ciki shine banji motsinki ba? Kina tafiya sai sahun taku kawai akeji kuma dare yayi sosai." Dariya tayi tana sosa kai "Tou kiyi hakuri kina waya na baki tsoro, ku cigaba da soyewa amma fa karku kone." Tana gama fadan haka ta wuce sama kamar zata fashe da kuka.




Da fatan kowa yayi sallah lafiya? Tou Allah ya maimaita mana amin.🥰🥰i

No comments: