Wednesday, 9 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 08

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 08}



Dariya suka bushe da ita dayan mai kirar samudawa ana kiransa da katako ne ya kunna camera ya saita ta yadda zasu aiwatar da komai yadda aka umarce su! Nan suka fara recording inda Damisa ne yayi pretending kamar yana kissing Gimbiya da yake ya ba cameran baya ita kuma Hoodah tana kwance unconscious ya sanya baza'a gane idanunta rufe yake, ya kai akalla minti sha biyar a haka sannan ya sauka suka kashe cameran suka kalli juna alamar sun kammala abinda ya kawo su sannan da sauri suka dinga fita suna tsallake bayin da ke kwance shame shame a kasa suna sharar bacci, a waje ma gaba daya bawanda ya gansu yawanci duk anyi bacci. Sai can wajen karfe 1am Hoodah ta farka, a hankali ta bude idanunta tana budewa take ta tuna incident din daya faru da sauri ta mike ta nufi bathroom ganin basuyi mata komai ba ya sa ta saki nannauyar ajiyar zuciya, sai kuma ta fara tunanin meya kawo su toh in ba fyade suka zo yi mata ba? Nan ta dinga tunani kala tana tsaye gaban mirror duk a tsorace take, kamar daga sama taji an dafata kirjinta yasake bugawa, ta fasa wani irin gigitaccen ihun da sai daya sa Yarima yayi baya a guje har yana neman faduwa, ita kuma runtse idanunta tayi gam gam tana makyarkyatar sanyi ko ina na jikinta yana kadawa, kaduwa mai ban mamaki! "Ka taimaka man, kar ka cutar dani! Karka tabani!" Yarima yayi kasake yana kallonta cike da mamaki, kuka takeyi sosai tana adduar Allah yasa suji tausayinta su kyaleta toh meyasa suka dawo? Still tsoro ya hanata bude idanunta taga ko wanene bata fatan ta sake hada idanun dasu. "Hoodah...! Lafiya? Mesame ki?" A hankali ta daina kyarmar da takeyi tayi kuri idanunta a rufe tana saurare kodai kunnenta ne baiji da kyau ba!!? Daf da ita ya isa tare da kamo hannunta ita kuma kamar tana jira tayi sauri ta makalkale shi jikinta na cigaba da kadawa wane mazari ko ina na jikinta ya dau zafi... Yarima yayi hugging dinta back yana fadin "Shhhh.... Kiyi shiru ni bangane me kike nufi ba Hoodah, ni ne zan cutar dake? Zazzabi kike ne naji jikinki akwai zafi, yama akayi na ganki ke kadai bayinki suna kwance suna bacci! Is that how to do their jobs?!" Ya fada da karfi! Ganin yanayin kukan da takeyi yasa Sultan yaja ta har cikin daki sannan ya kwantar da ita ya lullu6e mata jikinta da har yanzu bata bar rawar sanyi ba sannan ya shiga rarrashinta.... ya kai minti uku sannan ya mike yace "Bari na kawo maki koda juice ne sai na baki magani kisha kiyi bacci ko?" Tana jin haka ta wani mike da sauri tana rike hannunshi tana kalle kalle "Kar ka tafi ka barni ni kadai tsoro nakeji..." ta fada hawaye na surnano mata, kallonta yayi yace "Yanzu zan tada bayinki su zauna dake kafin in dawo kinji? Zauna a nan yanzu zan dawo babu abinda zai faru..." yana fadin haka ne yana zaunar da ita kan gado nan ta yarda ta zauna tana hade hannayenta wurin daya zuciyarta na harbawa. Yana fita parlor ya wani daka masu tsawa suka mike a gigice a kuma rude ko wace tana neman mikewa tsaye, "Yanzu ku ashe Gimbiya batada lafiya shine kuka kwanta a nan kuna sharar bacci bakusan halin da take ciki ba? Abinda aka dauko ku kuyi kenan?!" Ya daka masu wata watsar, a tsorace suka durkusa suka dinga bashi hakuri don su basu tabayin bacci haka mai nauyi ba, nan dai sukaita bada hakuri da kyar ya hakura sannan yace "Yanzu zan dawo ku shiga wurinta tana jin tsoro ne..." daga haka ya sa kai ya fita, yakai minti kusan ashirin sai gashi ya dawo da cup da magani a hannunsa, suna ganinshi duk sai suka fito daga dakin suka kulle kofar, nan ya iske ta ta shige cikin bargo tana jin alamun shi tayi sauri ta bude idanunta ta mike zauna, kan drawer ta gefen gadon ya zauna ya mika mata juice din ya balla mata maganin sannan ya bata ta sha, sai kuma yace "Kici kaza kafin ki koma ki kwanta nasan kina tare da yunwa..." ta girgiza kai da sauri tace "Na koshi..." ya wani daure fuska "Dama ay ba tambayarki nayi ba umarni ne na baki..." ya fada yana bude ledar kazar yago mata cinya yayi ya mika mata fuskar nan tasa tamau ta kalli fuskar shi sai ta karba da sauri tana ci a hankali, tare suke ci yana tirsasa mata da kyar ya samu ta danci sannan ya kyaleta yace ta kwanta, tana kwanciya nan da nan bacci barawo ya saceta, gyara mata bargon yayi shikuma ya fada bathroom yayi wanka ya fito ya shafa cream ya sanya kayan baccinsa ya haye can gefen gado ya kashe side lamp yayi addu'a ya rufe idonsa.

 A hankali Hoodah ta bude idanunta ta ga haske fayau ta mike da sauri tana duba lokaci, da hanzari ta mike ganin ko sallar asuba batayi ba, alwala tayi ta fito ta tada sallah bayan ta idar tayi wanka ta fito ta shirya, kayanta masu ado da kwalliya, tayi kyau sosai sai dai daka kalleta kasan ba'a cikin nutsuwa take ba, bayinta na ganinta parlor suka shiga gaisheta ta amsa fuska sake sannan suka take mata baya har bangaren sarki can ta iskeshi shi da matarsa Batul suna karyawa, nan ta gaishe su suka amsa fuska sake sannan Sarauniya tace "Ashe bakida lafiya? Dazu ay munzo bangaren naki muka tarar kina bacci, da fatan jikin naki da sauki?" Ta danyi murmushi "Allah sarki, eh da sauki sosai Alhamdulillah..." Sarki yayi murmushi "Toh madallah, ki koma bangaren naki ki huta yanzu zansa a kawo maki kalaci kuma ki tabbatar kinci..." ta gyada kai a hankali ta mike ta nufi sashen nata, tana komawa kuwa ba'a wani jima ba sai taga ana shigowa da abinci kala kala, bayan sun gama kawowa suna niyyar fita sai ga yarima ya shigo yasha kaftan sai kamshi ke tashi daga jikinsa, ta kalleshi a hankali sai tace a ranta "Wannan anya ba jinsin larbawa bane kuwa?" Ya karaso cikin dakin yana fadin "Kin tashi? Ya jikinki?" Ta danyii murmushi "Dasauki alhamdulillah nagode da kulawarka..." yayi murmushi "It's my duty..." nan ya zauna gefenta ya hada masu shayi ya mika mata cup daya ya zuba mata chips da kwai da sausage sai kidney sauce, ta kalli plate din a dan tsorace tace "Ko a rage Abincin?" Yace "Dalili?" Tace "Ya min yawa..." yace "Toh ba sai muci tare ba?" Tayi murmushi kurum, a haka suka ci abinci har suka kammala...

******

Safa da marwa takeyi a inda suka saba haduwa sai faman duba time takeyi she is restless, ajiyar zuciya ta sauke trying her best to calm down, takai kimanin minti arba'in can sai gasu sun iso inda take ta wani daka masu tsawa "Ya mukayi daku? Sai yanzu kuka ga damar zuwa? Tun yaushe nake jiranku a nan!?" Damisa ya wani huro hanci fuskar nan a yamitse ba kyan gani yace "Wa kike ma ihu a nan? Ni sa'anki? Hattara!" Shiru tayi tana kallonsu Katako yace "Mun kammala maki aikinki, sai ki cika sauran kudinki sannan mu baki video!" Ta wani daka masa hara tana mika masa envelope din, fizgewa yayi ya yageta ya zaro kudin, kirgawa yayi a natse sannan ya kalleta "Ya naga dubu 100?" Tace "Sata kakeso inyi? Kasan a yaya nasami kudinnan?" Yace "Ina ruwana? Ba dubu dari uku mukayi dake ba?" Tayi crossing hannayenta tace "Banida su!" Ya daka mata tsawa "Ke karki raina mana wayau mana! Na rantse da Allah zan tattake camera dinnan a gabanki kuma babu abunda zaki iya yi a kai!" Ya dakko ta zai wullata kasa kenan ta fasa ihu "Wait! Tsaya! Dan Allah tsaya! Karka fasa! Zan baku wallahi zan bada complete...!" Ta fada tana zuge zip din jakarta ta fiddo dayar envelope din har guda biyu ta mika masu, dariya ya kece da ita irin ta mugayen nan abokanansa na tayasa ya dauki second goma sannan ya daure fuska tamau ya fizge sauran kudin hannunta ya shiga kirgawa a natse ganin sun cika yasa ya kunna sigari ya hura mata a fuska yana mata kallon rainin wayau.... "Toh gashi..." ya mika mata cameran, da sauri ta karba tare da kunnawa tana kalla, dariyar jin dadi tayi "And nothing is going to save you from this humiliation am getting you into Hoodah! Tun farko ke kika shiga gonata da baki shiga ba da duk haka bata faru ba! Kece kika rabani da masoyina kika tarwatsa farin cikina dan haka welcome to hell Gimbiya Hoodah..." ta fada tana jujjuya cameran, Damisa yace "Dama ay ke ba mutunci gareki ba ba'a ta6oki bama ya aka kare ballantana kuma an taboki, jahilai ne kadai ke maki kallon mutuniyar kirki amma mu da muka san wacece ke....!!" Ta daga masa hannu "Rufe man baki a nan!" Ta fada tana nufar hanyar fita. Duk suka bushe dariya a take.

**********

ONE WEEK LATER.

Da yammancin ranar wata asabar Yarima da Gimbiya suka fita yawo, aka raka su cikin gari, idan ka gansu baka ta6a cewa cewa basu son junansu tsabar yadda suka dace da juna, amma kowa ta ciki na ciki kawai dannewa sukeyi, tunda akayi aurensu basu taba fada ba suna respecting juna, sunyi exploring garin an zagaya da Gimbiya har kusan yamma, haka suka dawo saidai tunda suka shigo fadar mai martaba suka iske dashi da Sarauniya tsai tsaye kowane cikin bacin rai, turus sukayi bakin kofa mai martaba yayi tafi da karfi duk bayin da dogarawan suka fita da sauri, Yarima yace "Abbi lafiya?? Ummi meyafaru?" Kauda kai yayi yana kallon wani gefe Ummi ce ta tako daf da Hoodah tana mata wani irin kallo sannan tace cikin bacin rai, "Ashe haka kike? Meyasa kika bata mana suna! Kinsan nan gidan wanene! Nan gidan fuskar mutane ce meyasa kika zabi ki tozarta mu ki ci mana mutunci sannan ki wulakanta mu....!?" Hoodah a razane tace "Ni kuma Ummi?Menayi?" Abbi yace "Bakisan me kikayi ba? Yanzu dan baki son dana shine kike nema ki tozarta kanki ki tozarta shi? Har kiyayyar da kike masa ta kai haka?" Cike da confusion Sultan yace "Wai meyake faruwa ne? Ku fahimtar damu...." Abbi ya mika masa wayar Ummi wanda aka turo da wata unknown number danna masa play yayi ya fara kallo, runtse idanunsa yayi yana girgiza kai "Anya Ummi? Wannan ba Hoodah bace bazata ta6a aikata wannan abun ba!" Ya kara kallon videon ashe anyi editing sosai ansa mata jikin wata wacce batada kaya jikinta sai aka bar fuskar wacca ake gani sosai, Ummi tace "Toh fuskar take ce?" Juyawa yayi yana kallon Hoodah wacce ke tsaye kamar an dasata a wurin, a hankali yake taku har ya isa dab da ita ya damko mata hannunta ya sa mata wayar ciki, hawaye ne suka fara zuba daga idanunta tana kyarma ta dago wayar tana kallon screen din hankali tashe tana girgiza kai, "Ban aikata ba wallahi ban aikata ba..." Sultan yace "Toh wannan wacece Hoodah? Ki fada man gaskiya kinga sai a wuce wurin wallahi idan kika fada man zan iya yafe maki..." ta dago tana kallonsa sannan ta kai dubanta ga Sarki da Sarauniya wadanda suka kauda fuskarsu daga kallonta da sukeyi. "innalillahi wa'inna ilahir rajioon!" Take ta fara recalling incident da ya faru da ita daren ranar da aka kawota, "Ya akayi sukayi controlling dina? Meyasa zasuyi man haka? Menayi masu? Su wanene suka aikata mun wannan abun?" Gaba daya ta jera ma kanta wadannan tambayoyin amma babu amsa, duniyar gaba daya taji ta fara juya mata, ji tayi an damko ta take ya dinga janta kamar wani zaki fuskar nan jawur alamun bacin rai, Sarki suka dinga kiranshi amma ina har sai da ya kai sashensu ya kulle kofar, ya turata ta jingina da bango, sannan ya matso dab da ita yasa hannunsa biyu ya dafa bango yana kallon cikin idonta! girgiza kai takeyi hawaye wani na kara wani, Sultan yace "Ashe tsanar da kikayi man zatasa ki aikata wannan mummunan abun?" Ya nuna kan gado "A bisa gadon mu na sunna kika aikata alfasha Hoodah, why!? Why did you do this to me? Why?!" Ya fada yana girgizata da karfi, "Ya za'ayi kayi tunanin zan aikata wannan abun? Never in my life ban taba aikata makamancin haka ba, why don't you believe me I was unconscious I don't know what happened...." tsoro da fargaba sune suka mamaye zuciyarta don yanzu burinta bai wuce ace ya fita ya bar mata dakin ba, a hankali ya zauna kan gado ya dafe kai "Innalillahi wa inna ilahir rajioon....!" A hankali ta zube kasa gabanshi tace "Ka kalli cikin idona idan har inada gaskiya zaka gane, amma kar ka zargeni akan abinda bakada tabbas a kanshi...." ya dago kai yana kallonta idanun nan jajir "Zargi kikace? Ba maganar zargi anan, nagani da idanuna me kuma zaki fada man?" Ta share hawayenta duk da ba tsayawa hawayen yake ba "A lokaci da dama abinda muke gani ba shine yake faruwa ba..." wata irin iska me zafi Sultan ya furzar ya runtse idonsa, "This is what you want right? Ayita jan zance? Da yanzu kin fada min gaskiya an wuce wurin amma na lura baki son zaman lafiya dani..." kuka ta fashe dashi jikinta har kyarma yakeyi "Allah yaga zuciyata, ban aikata abinda ake zargin na aikata ba, framing dina akayi bansan dalili ba, ban san menayi ba...." Tsaki yayi mai sauti kafin ya mike tsaye, "You should be ashamed of yourself, na tsaneki na tsani mai irin halinki, gashi kin man karya bazaki fada man gaskiya ba you lied to me, I saw everything and you still have the guts to lie!" Yana gama fadan haka ya bude kofar fita ji kake garam!Wani irin kuka ne ya kufce mata sulalewa tayi ta kwanta shame shame a kasa har sai da tayi mai isarta, takai awa daya a haka har sai data gaji don kanta tayi shiru idanunta sunyi luhu luhu sun kumbure, da kyar taja jikinta ta shige bathroom ta watsa ruwa ta dauro alwala fito ta shafa mai, wata riga ta sanya ta material doguwar riga ta tada sallar magrib.

A 6angaren Sultan kuwa bayan ya fita daga wurin Hoodah bai zama ko ina ba sai dakinshi na da, kan gadon ya fada ji yake kamar ya fashe da kukan bakin ciki, "Why would Hoodah do this to him? Why?" Ya tambayi kansa amma ba amsa....

Tuesday, 8 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 07

 YAR AGADEZ

 

         

              {Page 07}



Tunda suka kama hanya Hoodah bata bar shar6ar kuka ba, maganganun Kaka kadai ke mata yawo cikin kai kafin a taho da ita lokacin da take mata nasiha daga ita sai Hoodah a cikin daki. "Kiyi kokari wajen girmama mijinki Hoodah, a koda yaushe ki zama mai sauarensa a duk abinda zai ce maki, mun baki tarbiyya daidai gwargwadon ikonmu, in har kika zamo mai yawan kyautata masa na tabbatar a hankali soyayyarki zata dasu a cikin zuciyarsa, yi nayi bari na bari kar ki, ki cigaba da kwalliya kamar yadda kika saba yadda ko kallonki yayi zai ji dadin zabin iyayensa, ki zamo mai tsafta da gyara muhalli karki dubi daga inda kika fito, ki tabbatar kina masa kwalliya ki zama attractive, ki zamo mai kamshi a koda yaushe nasan kina son kamshi amma ki kara kan wanda kike dashi a nan, ki masa girki, kinsan way to man's heart is his stomach, ki zamo babbar aminiyar mijinki daga abota akan zamo masoya, ki fidda Ashraf daga cikin ranki tunda yanzu kinga ke matar wani ce, kece zakiyi grooming dinshi yadda kikeso ki tabbatar kece mace ta farko da zai nema wajen shawara. Mijinki public figure ne, yarima ne wanda zai iya zama sarki nan gaba ke kuma ki zama sarauniya, kingane me nake nufi, ki tsaya dashi duk dadi duk wahala rayuwa ba yadda bata kamawa yau gareka gobe ga waninka, don haka ki kaunace shi, ki rirrirace kamar sabon jariri, ki girmama iyayensa da yan uwansa da duk wani wanda zai ra6e shi, iyayensa suma naki ne ki saki jiki dasu wajen neman shawara duk sadda wani abu ya shige maki duhu...." kuka take a hankali Kaka ta numfasa "Ki zamo mai riko da addini, sallah da azkhar ki nemi tsari daga dukkan wani sharri, Allah yayi maki albarka ya baku zaman lafiya mai dorewa..." Wani hawaye masu dumi suka gangaro mata yanzu ita duk abubuwan nan da Kaka ta fada mata anya zata iya? Idan shi baiyi treating dinta yadda ya kamata bafa ita ya zatayi? Ta dinga kuka cikin jirginnan ta kasa controlling kanta, Aunty Rahanatu dake gefenta ta kamo hannunta cikin nata tayi squeezing, ta dago a hankali sai ta fada bisa ita ta dinga kuka kamar an aiko ta, Aunty Rahanatu batayi gigin hanata kuka ba haka ta barta tayita kukan kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa, d'an shafa kanta takeyi alamar rarrashi....

Bayan sun sauka dama an aiko da motoci sunfi kala biyar wanda zai daukesu daga airport, haka aka dinga sakin kirari a haka suka shiga mota aka wuce dasu gidan Sarkin Niamey. Da isarsu dama kowa su yake jira nan da nan aka tarbe su tarba ta musamman aka masu iso, amarya aka ja har bangarenta wanda yake bangare ne dake ke6e shi kadai na daban, kowa sai da yayi mamakin haduwar gidan don ba karamin kyau yayi ba, mahaifiyar Sultan tasa aka dinga shigo masu da abinci, su kaza, tsire balangu wannan tire dinsu daban daban banda salad, aka aka dunga jida ana shiga bangaren amarya dashi, nan da nan gidan ya sake kacamewa da baki shiga kawai ake ana fita kamar ana hankado su, nan suka cicci Abinci suka sha drinks sai kuma sukayi sallah, suna gamawa aka jawo amarya don taje gaido surukan nata.... har fadar Sarki aka kaita inda suka karbe ta hannu bibbiyu suka sa mata albarka, ana gamawa aka maida amarya ta sake yin wanka ta fito nan aka shirya ta Budan kai. Amarya tasha golden lace mai kyalkyali wanda akayi mata harda veil na bisa kai, bayan an gama shiri aka fito da ita inda aka gyara za'ayi event din yayi kyau sosai nan aka fara gudanar da Budan kai.

"Takawarki lafiya yar sarki jikar sarki kuma Gimbiyar mata, sarauniyar kyau, doguwar mace alkyabbar mata, shugabar mata kyakkyawa mai dimple Gimbiya mai siffan larabawa ko ba'a sanki ba sai an tambayi wacece ke..." Ba abinda Hoodah keyi sai murmushi kanta cikin veil, "Masha Allah...!"" Shine kawai abinda suke fadi, can sai ga cousins din Yarima ne sun kai su bari suka je inda Gimbiya take a hankali sukayi lifting mayafinta, take aka fara mata liki ana zubar da ruwan kudi, sannan sai ga aunties din Yarima suka fiddo turare suka dinga fesa mata, suka dinga welcoming dinta into the family, duka bayan an gama wannan aka damka wa dangin ango amarya inda sukace sun dauki amana... daga nan makada suka fara nasu aikin suna cigaba da praising Gimbiya Hoodah!

"Sarauniya Hoodah, yar gaban goshin mai martaba, farar mace alkyabbar mata, sun buga dake sun barki, takawarki lafiya yar sarki jikar sarki, Allah yaja zamanin uwar gida sarautar mata...." Nan da nan wurin ya rikice da guda da kide kide da raye raye na ban mamaki! Bayan an natsu na kamar minti sha uku haka sai kuma taji an fara cewa "Ga yarima nan isowa shida tagawarshi! Ga ango nan shigowa yanzu muna so kowa ya samu wuri ya zauna! Dan sarkin Niamey zai shigo...." Take ya shigo yasha wasu kaya masu kama dana indiyawa sunsha aiki sai kyalkyali yake, gefensa yana tare da abokansa sun kai biyar, bayansa dogarawa ne ke ta faman take masa baya... take suka fara da cewa "Yarima na Gimbiya, Sultan na Hoodah! Ango na amarya! Kun zauna an tashi, Gimbiya Hoodah matar Yarima Sultan, Dan sarki jikan sarki, mulki yafi kudi, Allah yaja zamanin masu sarauta...." cike da kasaita yake tafiyar har aka kaishi mazauninsa wato kusa da amaryarsa Hoodah. Bayan ya zauna. Nan Sarauniya Hajiya Batul itama akayi mata iso da kirari nan da nan ta fara gudanar da kyauta ta musamman da zasu bada itada sarki. Bayan an ci an sha sai aka cigaba da gudunar da shaglin biki ba karamin dukiya aka kashe ma wannan sabga ba, kaji kuwa sai da sukayi kamar zasuyi magana banda tsire da ragunan da aka gasa. Ba su suka gama bikin sai gab da magrib nan aka kare kowa ya kama gabansa, Hoodah dakinta aka maida ita nan mutane sukayita tururuwar zuwa ganin amarya da kuma dakin amarya....

Nan aka soma watsewa tashi akayi aka kara kimtsa ma amarya dakinta aka sanya turaren wuta. Hoodah ce zaune har kusan karfe sha daya babu ango babu dalilinsa, itama kanta ba son zuwansa take ba dan gaba daya kirjinta in banda bugawa babu abinda yakeyi, wani tsoro da fargaba ne ya darsu a ranta. Can cikin dare misalin sha biyu na dare taji alamun bude kofa dama ta kasha fitilun dakinta ta fara bacci sama sama...

********

Khairy ta kalli samudawan dake gabanta kusan su uku suna tsaye bayan wani kango ko wane fuskarshi kadai abun tsoro ne tace tana huci 

"Wannan aikin da zaku aiwatar bana son kuskure... ku tsaida hankalinku kuyi shii yadda ya dace yadda nikuma zanji dadin biyanku yadda ya kamata..." daya daga ciki mai suna damisa ya dakatar da ita yana busar sigari, yace "Toh malama sai ki fara bada rabi kinsan banida mutunci kan kudi, zan iya yin komai..." tace "Haba zan bayar yanzu ga wannan..." ta damka mishi abu cikin envelope, ogan ya karba yana tabawa saida yaji da dan kauri sannan ya bushe da dariyar mugunta "Kisa a ranki anyi a gama kawai..." Khairy tayi murmushi tana kada kai "Kuna iya tafiya, idan kun kammala ku neme ni a nan..." daga haka tayi gaba zuciyarta fes.

********

Jin motsin bude kofa tayi, tayi zaton ko Yarima ne ya shigo, a dan tsorace ta kalli kofar, ta mike a hankali tana fadin "Sultan?" Jin shiru ya sanya ta fara kokonto ji tayi an damke mata kafafu an matse an kunna fitilan daki, ganinsu ya gigitata ya kuma razanata matuka, take jikinta ya fara rawa ganin katti gabanta sun rufe fuskarsu da mask, "La....fiya? Me kukazo yi mun?" Ta fada tana tunanin inda bayinta suka tafi bataji alamun motsinsu ba, wani irin damka sukayi mata take Hoodah ta fara shure shure, amma tunda daya ya zabga mata wani irin gigitaccen mari taji gaba daya tunaninta ya dauke, take ta fara ganin biyu biyu ji tayi an wullata kan gado da mugun karfi, ta dafe kanta tana kokarin mikewa tsaye amma ina she's weak haka ta koma ta fada shakaf kan gado tun tana ganin biji biji har idanunta suka rufe ruf......


Kuyi hakuri da wannan๐Ÿ˜›๐Ÿ˜›

Monday, 7 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 06

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 06}



Kamar kullum tana zaune suna labari itada Kaka akayi sallama Jamila ce daya daga cikin bayi ce ta shigo ta durkusa kasa tana fadin

"Barka da hutawa Kaka, Barka da hutawa Gimbiya, Gimbiya wai kizo Yaya Ashraf yana son ganinki...." tayi shiru can tace "Kice masa ina zuwa." Tafi minti sha biyar batada niyyar tashi Kaka tace "Me kike jira Hoodah? Kije ki same shi mana." Tace "Zanje..." Kaka tace "Toh tashi mana yana can yana jiranki. Ko kina gudun kada Karima ta ganku tare ne?" Ta gyada kai a hankali, Kaka ta dafata "Babu matsala tashi kije don yanzu na tabbatar tana can daki tana zuga bacci." Tashi tayi a hankali ta fice daga dakin Kaka ta nufi inda tasan zata same shi, da isarta sai ya bita da kallo har ta karaso ita dai kanta na kasa, tana zuwa ta samu wuri ta zauna ta gaishe shi ya amsa fuska sake, yayi murmushi yace "Kwana biyu kina guduna ko? Meyasa?" Ta fara inda inda "Abinda.... ya... yasa... na....na...." ya numfasa "Meyasa Gimbiyata...?" gabanta ya dan buga tace "Babu komai fa." Yace "lafiya dai ko?? Kina jin tsoron Umma ne?" Ta girgiza kai da sauri tana kalle kalle yace "Shikenan tashi ki tafi...". Ta mike da sauri har tana hada hanya zata bar gurin kawai taji tayi karo da mutum, Saurayina tayi taga taga zata fadi Gimbiya tayi saurin tarota a tsorace, Da sauri Ashraf ya mike inda Sarauniya ta tsaya tana kare masu kallo, "Mey kukeyi a nan? Kuma a tare?" Duk sukayi shiru Karima tace "Ohh a gidannan ban isa na bada doka ba sai ku karya mun? Sau nawa zan maimaita maganar nan? Nace kar ku sake ke6ewa tare amma da yake kunnuwan qashi ne daku ko kuma kun raina ni ban isa daku ba?" A hankali Ashraf ya tako dab da ita sannan yace "Hoodah kanwata ce ta jini ko babu soyayya tsakanina da ita akwai alaka mai karfi tsakaninmu, ke baki isa ba kice zaki karya bond din dake tsakanina da ita, duk fiffiko nan naki da wani nuna isa da gadara da kike takama dashi bai isa yasa naji tsoronki ba, mun maki biyayya iya biyayya amma da yake bakida imani....." bai karasa ba Karima ta dauke shi da wani irin wawan mari ta daga hannu zata kara dauke shi da wani marin saidai taji an rike mata hannu gam bata karasa marin ba, ta dago a fusace sai ganin Hoodah tayi tana mata wani irin kallo idanunta jawur, "Duk abinda zakiyi kar ki sake daga hannu kice zaki mareshi no matter what..." wullar da hannun tayi taja hannun Ashraf da har yanzu shock din marin bai sake shi ba tayi hanyar fita, har ta kai kofa Karima tace cikin daga murya "Bari kuji na fada maku bazaku taba yin aure ba indai ina bisa doron kasa ina rayuwa, na haramta maku yin aure don haka kuje ku gama soyayyar taku a banza, sannan dani kuke zancen sai na nuna maku wacece ni a yau dinnan, tuggu da makircina zan nuna maku tasirinsa a yau, tana gama fadan ta juya itada bayinta tayi hanyar harabar mai martaba tana matsar kwalla... da isarta kawai sai ta zube gabansa ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, da sauri sarki ya taso yana tambayar lafiya? Ita kuwa sai ta kara sautin kukanta, dagata yayi ya zaunar da ita yana rarrashinta sai data tsaida kukan nata kadan sannan tana shesheka tace "Tunda nake a rayuwata ban taba cin karo da jarabawa ba irin ta yau, ka duba fa kagani mai martaba yaran nan ni ce nayi dawainiya dasu, da cinsu da shansu, sutura da sauransu duk ni nayi, amma yau sunyi girman da har ni zasu daga hannu su mara, daga ita har Ashraf daga wai nace masu su daina shige ma juna kaga yadda na iske su dazu? Kamar zasu shige cikin jikin juna wai da sunan soyayya yanzu shikenan daga nace basu kyauta ba yanzu nayi laifi kenan? Ashe ban isa dasu ba saboda ban haifi nawa ba ko?" Ta kara fashewa da sabon kuka, sarki ya mike a fusace yace "Ay wannan bake suka raina ba kadai har da ni suka raina, Kai Sadiqu jeka kira man su yanzu yanzu kace suzo su sameni a fada..." da sauri dogarin ya ruga ba'a dau lokaci ba sai gasu sun shigo a tare suna shigowa sarki ya shako ma Ashraf wuyan riga yana jijjiga sa "Yanzu kai wuyanka har yayi kwari haka? Ka daga hannu ka wanka ma matata mari? Ko baka dubi matsayinta gareni ba ay ka duba dawainiyar da tayi daku!" Cike da rashin fahimta yace "Abba wallahi ban mareta ba ta ya za'ayi in mareta? Ita ce fa ta....." Karima ta fashe da wani sabon kuka tace "Kagani ko Mai martaba? Wai karya zaiyi man Wallahi karya yakeyi tambayi jakadiya...." Hoodah ta kalli Karima cike da mamaki tace "Umma...?" Abba yace "Yi man shiru a nan marar kunyar wofi, tunda kukayi wa matata wannan dibar albarkar toh dole na dauki mataki a kanku!" Sadiqu kuje ku rufe man su a dungeon yanzu sai gobe yi war haka za'a bude su..." Ba abunda Hoodah keyi sai faman zubar da hawaye zuciyarta na tafasa wane garwashi  suna ji suna gani aka kulle su sai kace wadanda suka aikata kisan kai. Tunda Kaka taji labari ba irin magiyar da batayi ba da fada amma fir ya ki sauraronta... Aikuwa Kaka ta dauki fushi dashi can kasan ranshi yasan bai kyauta ba amma ya kasa ta6uka komai yana tsoron Karimah. 

Kafin safe duk sun zama wata kala ba kamar Hoodah duk ta kode, bai sake su ba sai wajen karfe 2 na rana da sauri Kaka ta nufi wajen Hoodah wacce ke tafiya da kyar da isar Kaka sai kawai Hoodah ta zube kasa da sauri aka sureta akayi dakin Kaka da ita inda aka kira Doctor ya shiga bata taimakon gaggawa da kyar aka samu ta farfado tana farfadowa sai ta fashe da kuka sosai, nan Kaka ta bata ruwa ta sha sosai sannan ta taimaka maka tayi wanka sai data tabbatar ta gashe mata jikinta sannan ta fito da ita, she's still in shock abinda Abbanta yayi mata ko a mafarki bata ta6a tunani ba, wai meye shiga kanshi ne haka? Wasu hawaye masu dumi suka gangaro mata, Kaka ta sa aka debo mata abinci taci kadan shima saida kaka ta tilasta mata, Kaka ta zauna gefenta tace "Kiyi hakuri Hoodah nice nace maki ki tafi wurinsa da bance kije ba da duk haka bata faru ba, ki yafe mun..." da sauri Hoodah tasa hannu ta rufe ma Kaka baki tana girgiza kai idanu sha6e sha6e da hawaye, "Ba laifinki bane Kaka, babu mai babban laifi irin Abba..." tafada tana share hawaye kaka tace "Hakika Jalal yayi nisa baya jin kira baban abun tashin hankalin shine ko maganata ma bayaji sai na wannan tsinanniyar matar tasa..." Hoodah tace "Itada Allah Kaka duk abinda ka shuka shi xaka girba..."

    LATER THAT SAME EVENING

Hoodah na dakin Kaka still tana bacci kamar daga sama Kaka taga Jalal bakin kofa da hanzari ta mike a fusace ta isa bakin kofar tace "Lafiya? Waye haka? Waye kai? Me kikayi mun a kofar daki macuci kawai..." yayi shiru shi kansa baisan kwakkwaran dalilin daya kawo shi ba kawai dai abunda yasani ya aikata ba daidai ba, dukar da kansa yayi kasa yace "Nazo in duba Hoodah ne..." da sauri tace "Wace Hoodar!?" Yace cikin kwantar da murya "Yata mana Kaka ki taimaka ki barni na duba ta..." Kaka tasa hannu ta tare bakin kofar tana fadin "Ya kuke da Hoodah? Ay bakada wata sauran alaka da ita maza ka juya ka koma wurin wacce kafi so tun muna biyu da kai..." yace "Don Allah kaka kawai halin da take ciki zan gani." Kaka tace "Ka damu ne? Mugu kawai kaje dai kayita biyewa waccan matar taka ta kaika ta baro, ni matsa bani wuri..." ta ture shi ta rufe kofarta da key, ya juma a nan yana knocking amma fir Kaka taki bari ya shigo, yafi minti talatin tsaye nan tun yana sa ran zata bude har ya gaji yajuya ya koma kamar wanda kwai ya fashewa a jiki, yana isa fadarsa ya hadu Karima tana fadin "Ranka ya dade lafiya?" Daga mata hannu kawai yayi ya juya yayi komawarsa daki, ta6e baki tayi ta kama gabanta. Haka sarki ya kwana yana juye juye bai ta6a feeling guilty ba irin na yau gaba daya ya rasa natsuwarsa, gashi saura sati biyu kacal a daura auren Hoodah da yarima amma gaba daya ji yake auren kamar a fasa saidai bazai iya tunkarar Karimah ba da maganar nan dole saidai ya hakura.

Washe gari da misalin karfe sha daya na safe daya daga dogarin sarki ne ya rugo a guje yana zuwa ya fadi kasa yana kwasar gaisuwa sannan yace "Ranka ya dade! Na nemi Ashraf sama ko kasa ban ganshi ba, sai wannan takardar na tsinta..." ya fada yana miko masa ita ya karba ya jujjuya ta ya mika masa "Karanta mana." Nan ya warware ya soma karanta masu: "Assalamu Alaikum Abba, da fatan idan kayi arba da wannan wasika tawa zaka fahimce ni, na tafi na barku bazan iya cigaba da zama tare da ku ba, kayi man komai na rayuwa ka kula dani na gode Allah saka da alkhairi saidai a bisa abubuwan da suke faruwa ana ganin a dalilina ne Gimbiya bataso tayi aure sheyasa na nisance ku gaba daya yadda zaka samu ka aurar da yarka cikin kwanciyar hankali. Inaso kuyi mun alkawari bazaka fadawa Hoodah ba don bana so ta tada hankalinta akan wannan, kuma ina nan lafiyata lau so karku damu, na barku Lafiya Ashraf..." squeezing takardar yayi yana kallon Sarauniya da take masa wani kallon banza tace "To shine me don ya gudu? Zakabi kawani tada hankalinka? Ka barshi yafi ruwa gudu mana ya dade..." ta fada tana wani jujjuya ido, nan Sarki yayi shiru ya kasa koda cewa uffan, tsoronsa idan Kaka ko Hoodah sukaji maganar nan yasan akwai kura, nan ya fara tunanin yadda zai bullowa al'amarin can yace da mutanen wurin "Maganar nan ya tsaya iya nan! Kar na kuskura najita a waje duk wanda ya tambayi Ashraf kuce nina aike shi wani waje shikenan..." kowa ya amsa da toh ya juya ga Sarauniya "This is a serious warning Karimah ki kiyaye..." yana gama fadin haka ya tashi ya fita. Haka kuwa akayi aka fadawa su Kaka can cikin ranta taji dadi "Gara ma ya bar garinnan ya huta ma rayuwarshi sarki ya kyauta daya tura shi wani wuri..." ita kuma Gimbiya fushi tayi cewar meyasa zai tafi bai fada mata ba? Tace lallai zai dawo ya sameta.

Tunda abinda ya faru da Abba yayiwa su Hoodah ta kasa sakin jikinta da Abbanta dari dari take dashi gaba daya ta tattaro kayanta ta dawo dakin Kaka da zama, duk wani shirye shiryen amarya Kaka ce ke fadi tashi, gaba daya yanzu Hoodah ta daina damuwa da maganar aurenta ta fawwala wa Allah komai ta saki ranta daidai misali hakan ba karamin dadi yayiwa Kaka ba. Tun ana saura sati daya daurin aure gidan ya fara daukar harami gaba daya an cika da yan uwa da abokan arziki dama wanda ba'a gayyata ba, ba wanda xai ga Hoodah yace wai auren dole ne za'ayi mata. 

Ana jibi daurin aure ne Hoodah taci kukanta a bandaki ta wanke fuskarta ta fito, ranar ne kuma aka kawo lafe akwati goma sha biyar ko ita kanta Sarauniya bata zaci haka zasu kawo kayan ba don ba karamin mamaki tayi ba. Gaba daya gidan ya kacame da hayaniya, angwaye har sun iso tun safiyar ranar daurin da dangin ango, sun samu tarba ta musamman inda akaita dawainiya dasu sunji dadin hakan. 

 Yadda Sarauniya Karimah ke hidima sai ka rantse zaman lafiya ake da ita sai wani nan nan take da Hoodah, ita abin mamaki ma yake bata, Kaka tace "Duk abinda zatayi ki rabu da ita taje tayi... wannan rawar jikin da takeyi ba don Allah bane." Duk cikin shagulgulan biki baxasuyi bidi'a ba daga daurin aure sai walima. 

Ranar daurin aure amarya tasha kyau cikin tsadaddun leshi hadade sai kamshi na musamman ke tashi daga jikinta. Makeup dinta light akayi mata wanda yayi mata very simple. Safiyar ranar da misalin karfe biyu aka daura auren Hoodah da Sultan akan sadaki dubu dari biyu, ana gama daurin aure aka dinga daukar hotuna in banda yake babu abinda Hoodah keyi don ita har ta gaji da daukar hotuna. Dakin kaka yawanci duk yan uwan Hoodah ne a ciki sai kawayenta yawanci wadanda sukayi makaranta tare dasu ne suka zo mata biki.  

Washe gari aka fara shirin daukar amarya ta jirgi za'a dauka saboda nisan wurin anyi selecting wadanda zasu tafi kai amarya, saida Kaka tayi mata nasiha sosai sannan shima Abba ya dora da nashi ya dade yana mata nasiha kafin daga karshe tayi hugging dinshi tana gunjin kuka.

Haka suka tafi zuwa Niamey wanda ta jirgi ne zai kaisu awa biyu kacal..... 

Tafiya take yi tsakanin dakin, daga wannan corner zuwa wata, kawar tace mai suna Abidah ta riko ta tace "Wai lafiya kike tafiya ke kadai kamar wacce keyin safa da marwa? Me akayi miki?" A mugun fusace ta juyo tana huci, "Meye ma ba'ayi man ba? Yaudara! Cin amana! Da kuma Butulci..." Abidah tace "Wai har yanzu maganar nan baki manta da ita ba ki dauki kaddara ba...?" Tace still a fusace "Kaddara kuma? Tou bari kiiji in fada maki ina nan ina jiran wacce zai auro zatazo ta sameni wallahi sai ta gwammace dama bata shigo ba, sai na dasa mata tabon da bazata taba mantawa dashi ba sannan kuma sai na addabeta yadda zai zamana ko kwadayin zama da yarima batayi zansa ya tsane ta, ya kuma kyamaceta ta yadda na rasa shi haka itama zata rasa shi bazan taba bari su zauna lafiya ba! Wallahi...! Sai illata rayuwarta! Saina muzunta mata! Sai kuma na rabata da yarima ki rubuta ki aje....!" A tsorace Abidah tace "Innalillahi wa inna ilahir rajioon, da hankalinki kuwa Ummalkhairy? Wai kishi hauka ne? Na shiga uku!" Khairy tace "Eh hauka ne kuma sai na nuna mata ni mahaukaciyar ce wacce ta fara sabon hauka a titi....!"

Sunday, 6 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 05

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 05}



Kwance take kan cinyar Kaka a hankali Kaka tana shafa dogon gashinta wanda ya baje bisa bayanta, tanada gashi asalin na buzaye mai tsawo da sheki, lumshe idanu tayi kafin Kaka ta soma magana "Kiyi hakuri da duk abunda yake faruwa na tabbatar maki dukkanmu nan ba wanda ya tsara hakan sai Allah (SWA), ba Jalal ba, ba Sultan ba balle kuma Ashraf... Akwai dai sila amma Allah shine ya kaddara hakan a gareki..." Hannun kaka ta kamo tace "Kiyi man wata alfarma guda daya Kaka..." tace tana gyara rikon da tayi ma Kaka "ki daina ambaton sunansa a gabana na tsane shi..." tace feeling hurt already, Kaka ta daga ta zaune suna fuskantar juna sannan tace "A'a Hoodah karki sake fadin haka, kalmar tsana bata kamace ki ba hakika kalmar tayi miki tsauri da yawa...." Ta girgiza kai "Toh me kikeso ince Kaka? Nace ina sonsa?" Kaka tayi murmushi tana shafar fuskarta a hankali "Ko me mekika ga ya faru yana dalilin faruwa InshaAllah..." Hoodah tace "Ko kusa Kaka tunda nake ban ta6a dandana heartbreak ba sai wannan karon, Abba ya dasa man wani ciwon zuciya wanda warkewarsa ba nan kusa ba, Kaka ba'ayi man adalci ba...." tace wasu sabbin hawaye na neman zubo mata, da sauri Kaka tasa hannu tana share mata hawayen, zuciyarta babu dadi sam. "Zuciyar mace tanada matuqar rauni, takan kamu da soyayyar mai kyautata mata da bata kulawa, ba daya bane da zuciyar namiji idan har ita mace tana son abu, abu ne mai sauki ta hakura dashi, amma namiji ba hakan bace shi a nashi bangaren ba lallai bane yaso wacca bayaso amma wasu sukan sauya a hankali su so wacce basu so din...  Hakika namiji zai iya auren mace hudu kuma ya basu kulawar data dace amma can karkashin zuciyarsa akwai wacce yafiso a cikinsu, kamar yadda na fadi maki a baya Allah ne kadai yasan dalilin dayasa yayi hakan, kedai naki hakuri Allah yana tare da masu hakuri, na tabbatar idan kika auri Sultan zaki samu farin ciki koba yanzu ba. Tabbas yanzu baya sonki amma akwai yuwuwar ya soki wata rana, ba namijin da zai ganki yace bakiyi masa ba, gaki kyakkyawa, ga gashi tubarkallah ga kyan hali da sanin ya kamata, ga hakuri da addini, gaki yar babban gida babu abinda kika rasa don haka ki kwantar da hankalinki Gimbiya da izinin Allah zakiyi alfahari da zabin mahaifinki koba yanzu ba kinji yar albarka?" First time ever Hoodah ta danji sanyi a ranta sannan ta saki murmushi a hankali kanta na kasa. Kaka tayi murmushin itama, ban taba fada maki ba amma auren mahaifiyarki da Abbanki yarjejeniya ce da wani makudan kudi da ya kamata Jalal ya biya don kare masauratarsa daga kawo hari. Can garin su mahaifiyarki wanda mahaifinta shine mai garin garin, garin yana daya daga cikin gari mai matukar girmama sarautarsu basu dauki abun wasa ba, masauratu da yawa sun so su dawo karkashinsu amma basu amince ba. Yin yaqi ba shiine mafita ba don lokacin army dinmu na nan basu da wani karfi. Gashi lokacin masarautar tana cikin mummunan hadari, lokacin ne Mahaifinki ya dinga neman shawarwari har daga karshe suka yi yarjejeniya aka bashi Safinah a matsayin wannan deal din, yayi alkwarin zai kare masarautar da kuma Safinah na nuna jin dadinsa don dama ansan mahaifin Safinah mutum ne mai matukar saukin kai da sanin ya kamata, bazan taba mantawa ba ranar da za'a daura masu aure Abinda Abbanta yace da Safinah. (Zaki zama safe tare dasu yata na maki wanann alkawarin kiyi man wannan saboda masarautata, ni mahaifinki ne kuma I want the best for you) ya kamo hannunta cikin nashi, tana zubda ruwan kwalla tace dashi "Zan aure shi Abbu, zanyi duk abinda kakeso indai bai sa6awa addininmu ba InshaAllah na maka alkawari..." Cikin jin dadi yace "Allah yayi maki albarka Safinah, na tabbata bazaki bani kunya ba..." abinda yasa na baki wannan labarin shine Inaso kiyi koyi da mahaifiyarki kinga dai yadda ta amsa kudirin mahaifinta kuma batayi nadama ba sun gudunar da rayuwarsu cikin jin dadi da soyayya kafin waccan matar tazo ta ruguza komai..." ta numfasa "kinga dai ta yadda akayi auren amma a hankali soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu...." Hoodah ta numfasa sannan tace da Kaka "Toh ita Umma ta yaya akayi ta hadu da Abba har ya aureta?" Kaka tayi murmushin karfin hali sannan ta dora "Hakika Karima itace ta kamu da soyayyar Jalal, lokacin da farko baya kaunarta har ta kai ta dinga kawo masa ziyara, karshe ta shiga ta fita har ya amince zai aureta tofah tunda ta shigo gidannan ta tarwatsa farin cikin gidannan, gashi dai Allah bai bata haihuwa ba duk kuwa dabararta, don a cewarta tana so ta haifi namiji don ya gaji ubansa, amma dai shiru ba labari, koda Safinah ta samu cikinki Jalal ba karamin murna yayi ba don ya dade Allah bai bashi ba, a lokacin ne ita kuma Karimah bakin cikin duniya yabi ya haye mata ta dinga neman yadda zata kashe dan cikin Safinah Allah bai bata iko ba, har dai aka haifeki bata daina bin hanyoyin da zata rabaki da duniya ba, amma da yake shi Allah ba'ayi masa dubara sai gashi kin rayu har ma kin girma cikin hukuncin ubangiji, saidai fa ba karamin tsanar Safinah tayi ba gata muguwa ce bama Safinah ba gidannan ta addabi kowa kuma abin takaicin ma Jalal baya ganin laifinta duk abinda zatayi bai ta6a daukar mataki ba, duk abinda tace ayi shi za'ayi abinda ta hana toh ya hanu kenan, harta dai abinda za'a girka saida izinita don dai fa ta kuntata wa Safinah, amma da yake Allah ya zuba mata hakuri bata ta6a complain ba."  Kuka sosai Hoodah takeyi na tsananin tausayin mahaifiyarta "Ki daina kuka Hoodah, abinda kawai nakeso ki gane shine ki kar6i kaddara mai kyau ko marar kyau Allah shi yasan daidai shine ya kaddara hakan...." cigaba da kuka tayi Kaka na faman share mata hawayenta, can dai ta tsaida kukan nata tace "Allah sarki Ammina taga ukubar rayuwa, tabbas ranar da Allah zai tashi kama matar nan toh ta kiyayi karshenta, na gode ma Allah da bangani ba da bazan taba mantawa ba da halin da Ammina ta shiga ba..." Kaka tayi murmushin karfin hali "Hakane, kuma na tabbatar Sultan mutumin kirki ne kuma nan gaba zaki bani labari da kanki lokacin kin kamu da soyayyarsa...." Kaka ta fada cikin yar dariya....

*******

Ashraf yana tsaye bakin kofar dakinsa ya zurfafa cikin tunanin abubuwan da suke faruwa da rayuwanshi cikin yan kwanakin nan... A kullum burinshi ya zama yana yawan kyautata wa Abba wanda na kasanshi zasuyi alfahari dashi... ajiyar zuciya ya sauke, amma meyafaru idan har wannan yayan yayi hurting kanwarshi daya kamata yayi protecting. Take ya fara recalling abinda ya faru shekarun baya da suka shud'e. 

"Ammi!" Yaro dan kimanin shekara goma shabiyu ne ya shigo dakin yana sanye da farar kaftan da hular data shiga da kayan a guje ya shigo ya dawo daga Islamiyya hannunsa dauke da jakkar littatafansa, Ammi na rocking Hoodah wadda ke lumshe idanu a hankali alamun bacci ya fara surarta, da yake islamiyyar boarding ce tunda aka haifeta bai ganta ba sai yau don haka da mamaki shimfide saman fuskarsa ya shigo idonsa na kan kyakkyawar jaririyar dake kwance, Ammi ta juyo tana kallonshi fuskarta dauke da murmushi tace "Na'am Ashraf." Yana isowa daidai inda babyn ke kwance yace "Ina kika samu baby?" Ya kuma lekawa yana kara kallonta har yanzu bai bar mamaki ba, Ammi tayi dariya sosai bata ce dashi komai tana dai kallonshi yadda yake ma babyn kallon mamaki can ya kuma cewa "She's beautiful Ammi, kanwata ce?" Ammi tace "Eh kanwarka ce Ashraf she will call you yaya Ashraf...." wata kayataciyar dariya yayi jin an ce kanwar shi ce sai yaji kaunarta ya shige shi yana jinta har cikin ransa, yana murmushi ya kuma kallon Ammi yace "I like her already, Ammi ki bata kulawa sosai yadda zata girma muyi wasa tare..." Ammi ta shafa kansa tana murmushi "Karka damu Ashraf amma kaima inaso kayi man alkawari guda daya tak..." yace "Anything for my Ammi." Tace "Inaso ka kula da kanwarka ko bayan bana nan..." da sauri yace "Ina zakije Ammi?" Tayi murmushi tana shafa fuskar shi "Babu ko ina kawai dai ina so ka kula da ita sosai..." yayi murmushi shima yace "Na maki alkawari Ammi, amma Ammi zaki sake siya man wani babyn amma namiji nakeso wanda xamu dinga fita wasa tare...". Dariya ya ba Ammi tace "Ay ba siyan baby ake ba Ashraf, Allah ne yake badawa zan dai tayaka addu'a ya sake bamu wani namijin next time..." yace "Promise?" Ya bata dan karamin yatsansa sai ta sakala nata ciki tace "InshaAllah." Haka ya cigaba da kallon babyn yana taya Ammi raino. Dawowa yayi daga duniyar tunani yana share kwallan dake zuba daga idonshi yace "Kiyi hakuri Ammi da alama dai ban cika kadan daga cikin alkawarin dana daukar miki ba."

YAR AGADEZ PAGE 04

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 04}



Tashinsa kenan daga bacci aka kwankwasar kofarsa yayi bismillah ya mike tsaye ya zura bedroom slippers dinsa ya nufi kofar yana budewa daya daga dogarinsa mai suna Sani ne tsaye da wata envelope a hannunsa ya zube kasa yana fadin "Rankaya dade barka da kwana! Ga wannan sakon aka ce na kawo maka." Yasa hannu ya karba yana jujjuya takardar sannan yace da Sani "Wannan fa?" Sani yace "Banida masaniya rankaya dade." Sultan yace "Kana iya tafiya..." daga haka Sani ya mike ya tafi inda Sultan ya juya ciki da tunani kala kala... Zama yayi a daya daga kujerun dakin sannan ya warware takardar a hankali ya soma karantawa kamar haka: 

"Assalamu Alaikum mai girma yariman Niamey! Da fatan kana lafiya? Allah yasa haka ameen. Bazan tsaya wani dogon bayani ba saboda banida bakin zan maka wata magana, amma inaso kasani ban taba tsammanin zan rubuta wannan takardar a gareka ba saidai banida za6i don kai kajawo! A tunanina soyayyarmu ta ginu acikin zukatanmu sannan ina ikirarin da kakeyi na cewar bazaka ta6a iya rabuwa dani ba? Ashe duk karyar banza ce! Naji labari a gari na cewar zakayi aure, nayi mamaki matuka kuma na karyata hakan! Saidai yanzu banida damar kara saka doubt cikin raina don na tabbatar da zancen nan haka dinne! Shekara kusan shidda muka dauka muna soyayya amma rana daya ka rusa mana farin ciki ban taba tunanin haka daga gareka ba, ya zama tilas nayi hakan amma kasani bazan ta6a yafe maka ba! Ka cuceni ka yaudareni! Bazan ta6a kar6ar uzurinka ba! Zanyi kokarin ganin nayi moving on amma kasani kamar yadda ka rusa farin cikina haka kaima kayi bankwana da zaman lafiya da ma ko wacece zaka auro! I don't care who the fuck she is I must destroy her mark my words! Though it will be slowly but painful amma daga karshe sai nayi winning! Kar kayi gigin zuwa inda nake don zan iya halakaka! Nagode da abinda kayi man na barka lafiya! Daga wacce ta tsaneka Khairy Yusuf!" Squeezing gashin kansa yayi yana huci idanunsa sunyi jajir wane garwashi, bai ta6a tsintar kalaman da sukayi masa zafi ba irin kalaman Khairy ba, ya tabbatar Khairy duk abinda ta fada bil haqi iyakar gaskiyarta ta fada ya fahimce ta amma meyasa ba zatayi masa uzuri ba? Meyasa ta zabi ta ci mutuncinsa sannan ta wulakanta sa? A hassale ya mike kamar mai shirin zuwa dambe ya fice daga dakinsa da isarsa fadar mai martaba sai yayi kansa gadan gadan yana huci "Kayi nasara!" Abinda kawai ya furta kenan, da hanzari Sarki ya mike yana fadin "Kai lafiya? Are you okay?" Yace cikin damuwa, a zuciye yace "Ka daina mani wannan tambayar! Na bayar da zuciyata da ruhina ga wacce nakeso amma saida kasan yadda kayi ka rabamu! Wow bravo! Clap for yourself you deserve an award for that!" Hannunshi ya kamo ya damke da karfi yana huci shima yace "Ka manta dawa kake magana ne? Kana magana da sarkin garinnan kuma mahaifinka! Don haka kar ka sake bude baki ka fada man maganar da bata dace ba! Am your father don't you dare disrespect me!" Hannunshi yake kokarin fizgewa yana fadin "Let go of my hand! Ka sakar mun hannu! Baka cancanci ka zama mahaifina ba saboda abinda kayi man don haka ka sakeni!" Ya fizge hannunsa ya fita daga fadar kamar zai tashi sama!

******

Sallama tayi harabar mai martaba yana ganinta ya mike da sauri yana fadin "Kaka meyasa kika taso da kanki? Ay da kin kirani nazo....." zama tayi gefensa tace "Kar ka damu magana nazo muyi dakai...." ya sallami guards dinsa sannan yace "Lafiya ko?" Tace "Lafiyar kenan....Abban Hoodah..." yace "Na'am..." tace "Meyasa kakeso kayiwa yarka auren dole? Ka tuna fa ita kadai Allah ya baka, bayan haka marainiya ce, baka ganin akwai daukar alhaki a cikin lamarin nan kuwa?" Yace "Bangane me kike nufi da akwai daukar alhaki ba? Banida right din da zan zaba mata miji sai ya zama daukar alhaki?" Tace "Ba haka bane kana da iko amma kuma ka dubi girman Allah da ma'aiki ka janye batun auren nan da yarima, kuma ka tuna fa Ashraf jininka ne meyasa kake gudunsa? Har ka gwammace ka aura mata bare akan jininka?" Yace "Ban taba tunanin rana mai kama da yau zatazo ba, ranar da zakiyi questioning right dina! A matsayina na mahaifin yarinya na zaba mata miji and that's final...." ta dakatar dashi "Hoodah ta maka biyayya taji maganarka kai meyasa baza kaji maganata ba? Sai na matarka?" Yace "Karki sako matata cikin maganar nan Kaka ba ruwanta..." tace "Dama ay haka zakace amma bana maka fatan kayi dana sanin matakin daka dauka akan yarka!" Yace "Kuma maganar Ashraf kin manta dana ne? Ina son sa kamar yadda nakesona nawa...." ta dakatar dashi da hannu "Karya kake! Baka sonshi, da kana sonshi da bakayi masa haka ba ka nuna baka so ya auri yarka!" Yace "Shikenan bazan musa maki ba, amma nidai am doing this for Hoodah's happiness and maganar Ashraf am not selfish Allah yasani a cikin raina ban taba daukar Ashraf a matsayin bare ba..." tace "Amma kuma ka nuna ba kai ka haife shi ba ko kana so ko ba kaso ko ka yarda ko kar ka yarda ka nuna masa banbanci don haka kaje kayi abinda kaga dama kawai addu'a zan biku dashi Allah ya yaye maka abinda ke damunka... a matsayinka na sarki kana nufin you are always right and not wrong, ina nufin baka iya making wrong decisions kai kullum you are always right, bazai yuwu ba kuma baka fi karfin ka nemi shawara ba ko ka karbi kuskurenka ba, kaima haifanka akayi hakan baya nufin you are weak a'a yana nufin kaima mutum ne kuma dan Adam yana kuskure. Kasani nina haifeka kuma bazan fasa fada maka gaskiya ba duk wanda aka ce bayada magaya gaskiya toh ya shiga uku, don haka na fita hakkinka a matsayina nan uwa, rokona daya kawai ka duba abubuwan dana fada maka nagode...." daga haka ta mike ta gyara daurin zaninta sannan ta fice daga harabar ta barshi ya kasa koda kwakwaren motsi.

********

Tunda take bata taba tsammanin akwai ranar da zatazo ace an fasa aurenta da yarima ba, inda haka bata faru ba da yanzu saura wata hudu kacal bikinsu amma wai an wayi gari anyi canceling bikinsu... zaune suke itada Sultan hawaye na shatata daga idanunta, "Meya kawo ka wurina? Ba na ce karka kuskura kazo inda nake ba mayaudari kawai... Gaskiya ne zancen da nakeji cewar aure zakayi zaka aura wacce tafini matsayi zaka aura yar sarkin agadez!" Ya numfasa "kiyi hakuri gaskiya ne zancen da kikeji saidai wallahi...." daka masa tsawa tayi "Dama abinda nake so naji kenan kuma ka riga ka fada da bakinka! Bana son sake jin komai kuma!" Mikewa tayi da kin son kara kallon fuskarsa ta ruga da gudu tana gunjin kuka taso ace akwai wuka a hannunta da ta caka masa kowa ma ya rasa, "Na tsaneka na tsaneka Sultan kuma bazan ta6a yafe maka ba!" Ta tsaya bakin kofa ta fada masa haka sannan ta shige ciki ta barshi nan baki sake yana kallon kofar. Tafe take tana maganar zuci. Yanzu a dalilin wata wai Hoodah shine dalilin daya sa nake cikin wannan pain din, tunda take bata taba fada ba a rayuwarta amma yanzu ta kudiri she will fight wacce zai auro kuma bawai dambe ba a'a zata kwato yancinta... dakinta ta fada kan gado tana ihu hade da zage zage, can mahaifiyarta ta shigo a guje jin ana fasa abubuwa tana shigowa taga dakin kaca kaca tayi watsi da komai na dakin. "Ke Khairy meye haka!?" Nan ta fara kokarin kwace wani vase dake hannunta tana neman ta buga shi ga bango, da kyar tayi nasarar kwacewa nan suka hau kokawa tana so ta zille daga hannunta ta cigaba da aikata aika aika, nan maman ta dage ta wanke ta da mari sai a sannan ta tsaya cak daga kokowar da takeyi tana kallon wuri daya, zamewa tayi kasa ta dukar da kanta tare da rufe fuskarta ta fashe da wani irin kuka... "Mama an yaudare ni, yarima ya yaudare ni aure zaiyi Mama, shikenan yanzu aure na dashi anyi canceling baza'ayi ba, macuci! Mugu! Azzalumi...." Mama ta daka mata tsawa "Wai ke meye haka? A kan namiji kike wannan abun? Wallahi dama ki daina wahalar da kanki ki dauki kaddara, kiyi hakuri komai kika ga ya faru haka Allah ya hukunta ki kaddara yarima ba alkhairinki bane...." ta dago da jajayen idanunta tana kallon Mama tace "Indai har bazan same shi ba shi toh itama bazata same shi ba dukkanmu sai dai mu rasa ko ta aure shi bazan barta ta zauna lafiya ba sai na tarwatsa farin cikinta na rama abinda tayi mun...." Maman ce ta make mata baki "Kul na kuma jin kin sake fadin haka Khairy babu kyau kinji ko, nasan ba'a kyauta maki ba amma dai kiyi hakuri komai mai wucewa ne kuma Allah yana tare da masu hakuri...." Shiru tayi amma can kasan ranta tasan cewar sai ta rama ko ta wane hali ne....



Kuyi hakuri da wannan jiya na fita ne๐Ÿ˜…๐Ÿ˜†

Saturday, 5 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 03

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 03}



"An koya mana a kullum mu girmama hukuncin iyayenmu, tun zuwana duniya tunda nake ban ta6a sa6a umarnin iyayena ba I always respect their decisions and honors, zan iya cigaba da rayuwa ba tare da Khairy ba? Abbi yana so ya jefa rayuwata cikin bakin ciki na hana ni abinda nake so..." yana tunanin nan yake tafiya cikin dakinsa daga wannan corner din zuwa wata... t-shirt dinsa ya dauko ya saka ya fito harabar mahaifinsa ya nufa nan ya iske sa shida mutanensa, Abbi na ganinsa ya umarci da mutanen su basu waje nan suka fita Abbi yace "Da fatan kanada labari nan da wata daya za'a daura maku aure kaida Hoodah...? Ya kalleshi da sauri yace "Why are you doing this Abbi? Kasan meke tsakani na da Khairy ta yaya kawai rana daya ace na rabu da ita haka kawai?" Abbi yace "Look, na riga na yanke hukunci am not going back on my word! Who's Khairy? Sai kace idan ka rabu da ita rayuwarka ta kare?! Maganar nan na riga na gamata jibi zakaje kaga yarinya ku tattauna a tsakaninku I mean ku daidaita kanku!" Sultan ya girgiza kansa yace "No! Bazan iya ba! Banda auren dolen da kace zakayi mun har sai an tursasa ni naje wurin wacce nakejin tsanarta cikin raina!kun rusa mun farin ciki Abbi!" Abbi ya hassala yace "Nine mahaifinka! A gidana kake kuma a karkashin ikona kake, kuma dole ayi mun biyayya don haka I said you're going to meet Hoodah whether you like it or not!" Shiru yayi ya kasa cewa komai wannan wane irin turn ne yayi taking a rayuwanshi lokaci daya? Zaiso ace wannan abun da yake faruwa mafarki ne ya tashi yaga komai bai faru ba. "Do you have anything else to say? If not u may leave..." Shiru yayi still ya kasa furta koda kalma daya "Haba mai martaba! Meya faru da kai lokaci daya kabi ka chanza akan wata wadda bamuda alaka da ita? Kodai sun asirce ka ne har kake neman jefa dan da ka haife a cikinka cikin kunci da bakin ciki? Kasani fa shi aure ba abun wasa bane, abu ne da ake fata ayi na har abada! Taya zaka aura masa wacce baya so sannan kace su zauna a inuwa daya a matsayin ma'aurata....!" Ummi ta karaso tana huci Abbi yace "Ke lokacin da za'a aura mun ke sonki nakeyi? Bama gwanda shi ba na bashi izini yaje yaga yarinya su daidaita ba? Kefa? Sai ranar da aka daura mana aure kika shigo cikin gidana a lokacin na fara ganin fuskarki...." tace "Toh naji amma ay a wancan zamanin akayi haka bare yanzu zamani ya riga ya chanza yaron nan yana maka biyaya daidai gwargwadon ikonsa toh don me kawai yanzu zaka ce zaka masa wannan danyan hukuncin?" Abbi yace "Wai meyasa kuke nema ku bijire ma umarni na ne? Toh ko me zakuce auren nan kamar anyi an gama ne babu fashi sai idan na mutu ne sai kuyi yadda kukaga dama!" Daga haka yasa kai ya fice Ummi da Sultan sunyi cirko cirko suna mamaki yadda tashi daya ya rikice haka!

*********

Ta idar da sallar magriba kenan aka shigo babu ko sallama, dagowa tayi taga Sarauniya Karima ce tsaye saida Hoodah ta dan razana da farko kafin a hankali ta mike tsaye tace "Barka da dare Umma?"  Karima tace "Barka bakiji sakona bane nace ki sameni harabata shine kikayi watsi dashi saboda kin raina ni ko don ban isa da ke ba?" Tace "Ko kusa ba hakane Umma, inaso na idar da sallah ne sannan saboda lokacin da sakonki ya iso gareni ana kiraye kirayen sallah...." ta daga mata hannu "Toh sannu uwar musulunci sai akace ke kadai kikeyin sallah a fadin duniya!? Well anyway bari dai kar na bata lokacina a nan na fada maki kai tsaye abinda ya kawo ni...." Hoodah tace "Ok..." hannunta ta harde wuri daya sannan tace "Jibi Yarima zaizo ku fuskanci juna kuma kinsan Allah na samu labarin kin masa wulakanci sai naci ubanki cikin gidannan no matter what ki karbesa hannu biyu kar ki wulakanta sa...." Hoodah ta dago da sauri gabanta ya bada wani ras ras, tace "Na'am?" Karima ta daka mata wata uwar tsawa "Kinga kar ki nemi ki raina man hankali meye kuma wani na'am? Sarai kinji abinda nace don haka sai ki fara shiri daga yanzu na barki lafiya....!" Har ta tafi sai kuma tadawo tana wani murmushin mugunta "Aww na manta abu daya ban fada maki ba, nan da wata daya za'a daura maku aure da Yarima, daga yau ki fita harkar Ashraf in ba haka ba ke kinsan wacece ni sarai zan iya saba maku daga ke har shi a bi umarni na a zauna lafiya..." daga haka ta fice daga dakin tana wani yanga da cika da batsewa, zubewa Hoodah tayi kasa wannan karon kukan ma yaki zuwa a halin da take ciki gwara ace kukan takeyi da abinda takeji a yanzu. Tafi minti talatin zaune a nan har aka fara kiran isha da kyar ta yunkura ta tada sallah tana gamawa ta fashe dawani irin kukan bakin ciki.

Saida ta gaji don kanta tayi shiru sannan kuma ta fara jero addu'oi na neman za6in Allah akan wannan al'amari. Tana nan har bacci barawo yayi awon gaba da ita...

2days later ******

Tun safe haka ta tashi batada walwala ko kadan, taga Karima sai  wani shirye shirye takeyi. Ita kuwa duk fushin da takeyi bai sa Abbanta ya chanza mind dinshi ba, Sarauniya Karima tace "Sai ki tafi ki shirya don suna hanya yanzu haka nasan neman Ashraf kikeyi toh kar ki damu bazaki ganshi ba har sai bakinmu sun tafi!"

Ba da dadin rai ake kimtsa ta ba bayinta guda biyu ne keta faman shirya ta bayan sun kammala suka yafa maka gyalenta mai kama dana indiyawa suka daura mata har bisa kai ba karamin kyau yayi mata ba, daya daga bayin Umma ce tayi sallama ta durkusa kasa tana fadin "Ranki shi dade kizo bakinki sun iso sunce ayi maki iso..." gabanta ya buga, kallon yarinyan Hoodah ta tsaya yi can ta numfasa tace "Ina zuwa..." a hankali take tafe kamar mai tsoron taka kasa ta nufi harabar saukar baki inda ta tabbatar can suka sauka, tsaye tayi bakin kofa ta kasa shiga har sai da Karima ta fito ta watsa mata wani irin kallo sannan ta shiga ciki da sallama, Abbanta ta gani zaune suna tattaunawa saida suka kammala sannan Abba yace "Shigo mana...." a hankali ta karaso kanta kasa sannan ta samu wuri ta zauna can Abba ya mike "Bari na baku waje ku tattauna ko?" Daga haka ya mike dogarawansa suka rufa masa baya... Su Biyu ne tagani zaune saidai bata tantance wanene yariman ba a cikinsu, ganin an cika masu gabansu da kayan alatu yasa tace "Bazaku sha koda ruwa ba?" Daya daga cikinsu ne yace "No we're ok." Ta kakalo murmushin dole tace "Hospitality dina zai zama abin tambaya idan har baku amsa tayina ba..." tana gaman fadan haka ta fara tsiyaya masu juice cikin cups din da aka ajiye masu, ba masu suka karba daga hannunta ita kuma ta mike ta koma kan kujera yadda suka tsareta da idanu yasa gaba daya ta zama uncomfortable, amma duk da haka sai ta daure tasan dai ba dadewa zasuyi ba. Daya daga cikinsu ne yace "Sultan kace ma future wife dinka wani abu mana tunda mukazo bakayi magana ba ko da sau daya ba..."  wanda yayi maganar ne kasa kasa amma duk da haka taji me yake cewa, ta dago a hankali tana kallon wanda akayi ma magana, "Me zance mata? Ay kai ya kamata kayi magana bani ba Usman..." Hoodah ta kalleshi a kule tace a ranta "As if ina son magana dakai kaima..." ta hadiye abu da kyar wanda aka kira da Sultan mai kama da larabawa shine ya dago yana kare mata kallo sannan yace "Kina son auren nan ko bakiso?" Tayi shiru na yan dakikai sannan tace a hankali "Aure abu ne mai kyau amma idan har ma'auratan suna son junansu..." ya karkata kansa kadan sannan ya yace "Bakiso kenan? I mean wannan auren da ake shirin yi tsakani na da ke?" Ta ciji lips dinta kadan na wannan tambayar daya jefo mata sannan tace "Hakane, amma kuma bazan iya bijire wa iyayena ba..." yace "Kin riga kinyi, kamar yadda bakison auren nan haka nima bana son auren nan dukkanmu muna bin umarnin iyayenmu..." tayi murmushi kadan "Toh kai me kake ganin mafita a nan tunda dukanmu bamu son auren nan?" Ya dora kafa daya kan daya "Sai ki bani lokaci nayi tunani a kai..."  tace "Amma kuma idan baka ce wani abu ba kenan haduwarmu ta xama in complete kenan if you don't decide..." yayi sipping juice cikin nuna isa yace "As I said before ki bani lokacin in har kikaji shiru toh kisa aranki auren zai tabbata kenan, sai dai kuma kinsan me zaki tarar kika bari aka daura auren nan don bana sonki dole akayi mun..." ta hadiye kululun bakin cikin ganin irin kalar mutumin da xa'a hada ta rayuwa dashi wanda bai iya adana kalamansa da kyau ba don haka sai tace a kule "Kamar yadda na tsane ka ba? Ay inajin an fi yin mun dole akanka don haka anyi equal dukkanmu bama son juna....!" Yayi wata yar dariya "Very well then Hoodah, is your saying not mine..." yana gama fadan haka ya mike da niyyar tafiya. Nan sukayi bankwana dasu Abba sukayi gaba. 

"Nasan me kikayi..." Hoodah ta fada tana shiga cikin harabar Karima. Sarauniya Karima ta mike tace "Kamar yaya?" Hoodah tace "Da girmanki kike mana labe don kiji abinda zamu ce?" Sarauniya tace "Eh...ehh, nayi laben is a good thing Abbanki xai maki aure whether you like ot not, duk magaganun da kuka fada na cewar bakusan juna duk a banza ne, kuma naji ko wace kalma da kuka fada..." tayi wani shu'umin murmushi tace "So it doesn't matter aure babu fashi..." tana gama fadan haka tace "Zaki iya tafiya..." tace tana nuna mata kofa. Tunda suka tafi ta shiga tunani kala kala ita kam mutumin bai mata ba ko kadan kyan dan maciji kenan zuciyarsa bakikirin kamar hadarin kaji, "Ya Allah! Meyasa za'a zabi a aura mun wannan mutumin duk mazan dake duniya? I deserve the best meyasa mahaifina ya zaba man rayuwar bakin ciki meyakon farin ciki? Anya Abba shine ya haife ni kuwa? Duk wani uba zaiso yaga yarsa cikin farin ciki a kullum amma banda nawa mahaifin, Abba meyasa why? Why?" Ta fada tana buga karfen gadonta da karfi hawaye na shatata daga idanunta duk tayi squeezing gashinta kamar wata sabuwar mahaukaciya data fara hauka a titi. Bayinta ne suka shigo da sauri jin ihu suka ce "Ranki shi dade lafiya?" Ihu ta daka masu "Ku fita ku bani wuri!" Da sauri suka fita ita kuma ta cigaba da kuka....

*******

Tunda suka zauna yanzu za'a kai kimanin minti sha biyar amma bai ce da ita komai ba idanunsa na kan table din dake tsakiiyarsu, kafafunsa kuwa yana dan bubbuga kasa dasu duk Hoodah taji ba dadi amma karshe daya dago yana dubanta sai ta gwammace dama cigaba da kallon kasan yayi, idanunsa sun koma abun tsoro kamar ba Abban data sani ba yadda yake tsareta da mugun kallo sai ka rantse da makiyarsa yake bada yar cikinsa yake ba, wani ajiyar zuciya ta sauke tasan cewar Sarauniya Karima ce ta kawo masa wata magana wanda ta tabbatar ba abinda ya faru kadai ta fada ba ta kara karya da gaskiya ta zuge shi don ya bata mata rai. An jima rabon data ga fushinsa har haka koba komai duk abinsa da fadansa idan ya tashi ya iya controlling kansa amma duk ranar daya kasa controlling kansa toh sai mutum ya rantse tashin duniya ne yazo.

"Cin mutunci!" Abinda ya furta kawai kenan tunda ya kirata harabarsa ita dai kanta na kasa batace komai ba, "Kinci mutuncina da kimata kin kuma ci mutuncin masarautata.....!" Ta runtse idanunta gam cikin jin zafin kalamansa da duk abinda zai fito bakinsa, ya juya yana kallon tagar harabar. Can sai kuma ya mike ya fara zagaye harabar hannuwansa sarke ta baya "Na hadaki da mutumin kirki, mutumin arziki mai kirki da sanin ya kamata......" ya bata baya sai ya dan karkato kadan yana kallonta "Amma kin bata hakan! Kamar yadda kike bata komai na rayuwarki gaba daya!" Ya cigaba da tafiya yana huci "Duk kinyi wannan abun ne saboda bakisan darajata ba da kuma kimata a matsayina na mahaifinki! Toh kisani basu kika ci mutuncinsu ba nine kika ci ma mutunci!" Ta dago idanunta cike da kwalla tace "Kayi hakuri Abba banci mutuncinsu ba....!" Wani irin mugun kallo ya watso mata kamar zai fashe yadda ya cika yayi fam "Toh kina nufin matata karya tayi maki kenan?" Ta girgiza kanta da sauri hawaye na zuba daga idanunta, iska ya furzar na haushi sannan ya dora "Kina sane maganar auren nan ba inda bata zaga ba cikin garin Agadez amma kina nema ki watsa man kasa a ido! Duk kinyi wannan abun ne saboda ki nuna man cewa kin iya soyayya ko? Toh kanki aka fara ne ko kuwa akanki za'a kare?" Ta dago tana dubanshi tana share hawayenta "Na dauka na isa dake ashe ban isa ba, kinyi rejecting wanda na kawo koba komai bazakiyi considering nina kawo shi ba kiyi man biyayya a'a sai kika je kika ci mutunci na ko? Me za'a daukeni? So kike a fara man kallon mutumin banza ko?" Hoodah ta kai kololuwa wurin gajiya da abinda makirar matar nan keyi mata! Ita kullum burinta ta hadata da Abbanta, wai shin kishi haukane? Ita wadda take kishin akan ta riga ta tafi! Haba! Kuka ta fashe dashi mai kara harda shesheka ya juyo yana kallonta "Dama ki bar kuka ke kika jawo ma kanki!" Sai kuma ya dawo dab da ita yana nuna ta "Zan sake gayyatarsu ki basu hakuri sannan ki gyara barnar da kikayi!" Cikin kuka tace "Toh!" Ya nuna mata kofa "Tashi ki fita!" Ta sauri ta mike   gudu gudu ta fita tana wani irin kuka bata xame ko ina ba sai dakin Kaka, tana azkhar taji an shigo da kuka Hoodah na zuwa ta fada bisa Kaka ta kara fashewa da wani irin matsananci kuka! Kaka tayi hugging dinta tana dan bubbuga bayanta tace "Menene? Jalal ko Karima?" Cikin kuka tace "Su duka! Ni meye laifina? Kaka matar nan anya tanaso ta gama da duniya lafiya? Taje ta hadani da Abbana yayi mun wulakanci da magaganu marassa dadi sai kace ba yarsa ba? Ko makiyarsa bazaiyi mata abinda yayi man ba Kaka..." ta kara sa kuka sosai Kaka tace "Kiyi hakuri Hoodah! Komai na duniya mai wucewa ne wata rana sai labari, duk abinda ka shuka shi zaka girba don haka kiyi hakuri ki kai kukanki ga Allah shi zai share maki hawayenki...". A hankali tayi shiru tana share hawaye tace "Kaka ina Ashraf?" Kaka tace "Ya bar gari yau da safe Karima ta koreshi wai ya dawo gobe, shima ay nasan bazai so ya ganki tare da wani ba gwanda da akayi haka idan ya dawo kinga bai gani ba yafiye masa a'ala..." tace "Uhm..." kaka tace "Ki tafi ki huta sannan koda Karima ta fada maki maganar banza kar ki tsaya ki saurare ta kar ki bari maganganunta suyi maki tasiri a cikin rai." 

Washe gari Abba ya sake inviting dinsu a gabanshi da Karima yasa ta durkusa ta basu hakuri ta kuma assuring dinsu bazata sake ba...  Sultan ne yace "Babu abinda tayi mana meyasa xakace ta bamu hakuri?" Abba yace "Karka damu kaidai tunda nace haka kawai ka amsa, ba yadda ya iya haka yace ya hakura shidai bai san wani laifi tayi ba, kodan dan maganganun da sukayi amma ay bai kai ace har sai an sake taso suba saboda a basu hakuri!  Yayi ajiyar zuciya ya saki murmushi yace "Karki damu komai ya wuce bakiyi mun komai ba...." Abba yace "Toh MashaAllah, ya kamata kuci abinci kafin ku juya ko?" Suka amsa ta toh nan aka kaisu inda ake sauke baki aka shiga kawo masu abinci kala kala, Hoodah ta fara tunanin he didn't seem like a bad person saidai babu abinda zai chanza daga kiyayyar da take masa.....

Bayan sun tafi Sarauniya Karima ta kirata harabarta da isarta sai ta kyalkyale da wata irin muguwar dariya tace "Da fatan zaki kiyayeni Gimbiya, kinga dai kadan daga cikin sharrrina, ba'a ja da sarauniya! Dama sai dana ja maki kunne nace kar ki sake ki wulakanta su amma kika ji, ay ga irinta nan..." ta sake kyalkyalewa da dariya sannan ta daure fuska tamau kamar wata aljana. Hoodah tace "Bakomai duk abinda kikeyi Allah nagani kuma ki saurari sakamonki tun a nan duniya kafin ki iske na lahira, kinyi mun abubuwa na shanye saboda ina baki girma a matsayinki na matar mahaifina amma kibi a hankali kada wata rana na zubar da girman nan naki da nake gani...." Sarauniya Karima ta ce "Har kin isa? Na riga nayi maki zarra babu wanda ya isa ya ja da Sarauniya shi kanshi ubanki shakkata yake ballantana kuma ke....." tace "Naji amma ay ba'aja da ubangiji ko? Duk takamarka shine kadai zai iya dakai kije zan hada ki dashi..." ta daga mata hannu "Tafi ki bani wuri kuma kar ki manta dokata na cewar kar na sake ganin kin tsaya da Ashraf!" Hoodah tace "Ko babu soyyaya kar ki manta Ashraf dan uwa na ne bazaki iya karya bond din dake tsakaninmu mu ba!" Tana gama fadan haka tayi wucewarta zuciyarta na harbawa.

Friday, 4 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 02

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 02}




Kallon Abba tayi tana cigaba da kuka tare da dukewa kasa, Ashraf ne ya tako daf da Abba yace still in shock of the slap, "Abba ka mareni akan wannan? Abba ka tuna cewa fa ni danka ne koba komai kai kanin mahaifina ne wanda ya rasu shekarun baya da suka wuce, banida kowa sai ku sai Allah mahaifiyata ta rasu bayan mahaifina ya rasu, kuma kafin ya rasu shine ya fara taka wannan matsayin da kake takama dashi a yanzu, Abba ka zauna kayi tunani kar ka cutar da yarka kwara daya tak da Allah ya baka ka bari ta zabi wanda takeso kar kuyi mata auren dole tana da wanda takeso..." Abba ya daga masa hannu "Meyasa kake tunatar dani abinda na riga da nasani tun tuni? Nasan matsayinka a gareni saidai tunda Umma ta riga tayi maganar nan babu yadda zamuyi...  kuma da kake maganar tana son wani waye shi? A iya zamana da Hoodah ban taba ganin tana soyayya dawani ba..." Ashraf yayi murmushi mai ciwo "Hakane Abba bakasani ba saboda baka damu da yarka ba ko? Bakasan me take ciki ba baka bata kyakkyawar kulawar da mahaifi ya kamata ya baiwa yarsa..." Umma ta daka masa tsawa "kaga Ashraf ka rufewa mutane baki a nan idan manya na magana yara basa saka masu baki wannan wace irin rashin tarbiyya ce da rashin sanin ya kamata?" Ashraf ya kalleta da idanunsa suka sauya kala sannan ya kalli Abba ya kamo hannunsa yace "Abba mun kasance mun shaku da juna nida kanwata Hoodah, a sanadiyar haka zukatanmu suka kamu da soyayyar junansu Abba a yanzu haka dama mun yanke shawarar sanar dakai halin da ake ciki....." Umma tace "A gidan ubanwa zaka auri Hoodah? Toh bari kaji in gaya maka ko kaine Romeo na duniya bazaka auri Hoodah ba..." abba yace "Kaga Ashraf tunda kaga Umma bata amince ba kawai a bar maganar nan banason tashin hankali..." Umma tayi shewa "Kadai ji da bakinka yanzu? Don haka tun wuri ka fitar da ita daga ranka tun kafin wanki hula ya kaika dare." A hankali ta kewaye jan idonta daya kumbura ta yunkura ta mike da kyar tana duban Abbanta daya dukar da kansa zuwa kasa yana kallon carpet tace "Kana jinta Abba? Auren dole fa Abba. Abba please kasa baki Abba kar ka bari a mun auren dole yaya Ashraf nake so please help me Abba." Aunty Rahanatu ta soma janta da karfi tana tirjewa amma rikon da ta mata   ji take kamar zata balla mata hannu nan ta hakura da tirjiyar sannan tabi bayan Aunty Rahanatu dake janta da hannu. "Ku bamu waje..." aunty Rahanatu ta fadawa bayin dake binsu har daki take suka fita suka kulle kofa, suna zuwa Hoodah ta zube kasa ta kara fashewa da matsananci kuka mai ban tausayi jikinta har wani rawa yakeyi, hugging dinta Aunty Rahanatu tayi tana fadin "Shhh... everything is going to be okay InshaAllah." Cikin sheshekar kuka tace "No it's not! It's not going to be okay, kina ganin abinda ake shirin aikata mun? Za'a cuci rayuwata a mun auren dole abunda aka daina yi tun zamanin iyaye da kakkani shine ni za'ayi mun why me? Ta dasawa mahaifiyata bakin ciki kala kala kafin ta bar duniya bata gamsu ba shine ni zata dawo kaina? Ita ba Allah bace ba zata zo tayi deciding abinda zai faru da mutum ba she can't! Kaddarata ba'a hannunta take ba bazata zo kawai ta aurar da ni da dan sarkin Niamey ba, banma sansa ba, bansan halinsa ba, ba'ayi min adalci ba..." ta fada muryarta na kakakarwa hawayenta na tabo lips nata. "Hoodah..." ta fada cikin sigar rarrashi, "Akwai abubuwa da yawa da zasu iya faruwa da rayuwarmu Allah zaki ba zabi ba zabin ranki ba, idan wannan auren alkhairi ne ki karba hannu bibbiyu sai kiga wanda kikeso din ba alkhairi bane a gareki na tabbatar maki Allah zai sa maki albarka a ciki..." ta dago da jajayen idanunta tana kallon Aunty Rahanatu "Kema side din su Umma kike?" Aunty Rahanatu tace "Ko kusa ba side kowa nake ba, kawai ina tunatar dake zabin Allah ba naki ba, bakisani ba ko Ashraf ne alkhairi ko kuwa yariman Niamey, just have faith in Allah ki bar komai a hannunsa InshaAllah komai zaizo cikin sauki InshaAllah..." girgiza kanta ta shiga yi, "Bazan iya bari hakan ya faru ba, ya kamata kuyi wani abu a kai bazata iya making decisions ba anyhow akan mutum ba..." ta tura kanta cikin cinyarta tana cigaba da kuka "Babu abinda zamu iya yi a kai ke kinsan halin matar nan sarai yayah Jalal ma bai iyawa da ita balle kuma mu a suwa? Kedai kawai ki mika lamarinki ga Allah shine zai share maki hawayenki InshaAllah khairan ne..." Hoodah tace "Idan ba shi bane bafa?" Ta sakar ma Hoodah da murmushi "Bazai faru ba trust me, idan har kikasa Allah a ranki InshaAllah komai zaizo da sauki..." shiru dukansu sukayi still tayi hugging din Hoodah na cigaba da kuka a hankali, bayan ta gaji da kukan nata tayi shiru. "kina bukatar hutu Gimbiya, ya kamata kije ki kwanta kada kanki ya fara ciwo..." Hoodah tace "Naji amma shi yaya Ashraf waye zai rarrashe shi kamar yadda kika rarrashe ni?" Aunty Rahanatu tayi murmushi tace "Karki damu zanje na same shi kedai ki tafi kiyi wanka ki huta kinji?" Ta gyada kai ta yunkura da kyar tana hade hanya ta fita daga dakin, Har yanzu Umma na nan parlor tana magana kasa kasa da jakadiya, Abba da kaka basu nan yanzu, ko kallon inda suke batayi ba ta wuce dakinta da sauri tasa ma kofar lock, bathroom ta fada tayi wanka ta dade ciki ta dauro alwala ta fito ta gama shafe shafenta ta saka loose gown ta lace tayi kyau, sallaya ta shimfida ta saka hijab dinta ta fara sallarta a natse har yanzu zuciyarta bata mata dadi, cikin sojood takai kukanta ga Allah mai kowa mai komai har saida taji idanunta suna neman kafewa, zuciyanta wani irin zafi take mata da radadi, bayan ta idar ta mike a hankali nan taga wayarta na haske Ashraf tagani yana kiranta gefen gadonta ta zauna ta saita kanta ta dauka "Yaya Ashraf..." ya saki ajiyar zuciya "Ina fatan Gimbiyar tawa ta bar kuka?" Duk da tana cikin yanayi saida ta saki murmushi tace "Na daina...." yace "Yawwa, kinga yadda al'amarin ya juye ko? Abinda nakeso dake karki sa damuwa a ranki mu bar wa Allah kar mu tursasa, zabin Allah shine zabin mu..." tace "Nasani nagode da kaunarka gareni yaya Ashraf bazan taba daina sonka ba har karshen ruyuwata ba..." kwalla suka cika masa idanu ya hadiye abu da kyar yace "Nima haka Gimbiyata kece zabina idan har inada iko, saidai dole muyi biyayya ga Abba sannan kuma mu barwa Allah zabi..." ta lumshe idanu, shiru ya biyo baya Ashraf yace "Kizo na kaiki favorite place dinki..." tayi murmushi mai sauti "Gani nan zuwa...." 

Ta gaban Jakadiya suka gifta itada Ashraf wadanda suke hira a natse daga gani kasan suna tafe cikin nishadi sai kace wani abu bai taba faruwa ba dazu, rike baki tayi cike da mamaki tuna maganar da sukayi da sarauniya cewar tasa ido idan har taga Gimbiya tare da Ashraf toh tayi gaggawar sanar da ita, cikin hanzari tayi cikin harabar Sarauniya tana zaune bayi biyu ko wace tana mata tausa a kafa daya daya, jakadiya ta shigo kamar an aiko ta, Sarauniya ta daka mata tsawa "Lafiya zaki fado man a kai haka?" Jakadiya ta zube kasa gwiwwa biyu biyu tana bada gaisuwar ban girma "Ranki shi dade ayi man aikin gafara amma yanzun nan naga Gimbiya da Ashraf suna tafe zasu fita tare..." hankade bayin nata tayi dake ta faman yi mata tausa har saida suka fadi tim sannan ta mike tsaye tace "Kika ce mey? Maimaita naji!" Tace "Ranki shi dade nace yanzu naga Gimbiya da Ashraf suna tafe zasu fita ta..." bata karasa magana ba kawai Sarauniya ta fita da sauri hakan bai hana Jakadiya da bayinta binta ba da hanzari, mai martaba yana tattauna da waziri da sauran mutanensa kawai ta fado masu babu ko sallama, hakan yasa kowa na wurin ya dago yana dubanta, ba tare data kallesu ba tace "Privacy! Zanyi magana da mijina..." a take kowa ya fita sannan ta kalli mai martaba tace "Idan har na isa ga Hoodah kuma idan har ana daukata da mahimmanci toh inaso kazo muje ka tsaida Gimbiya da Ashraf kayi masu kashedi kar na sake ganinsu tare tunda yanzu tasan cewa bada ita za'ayi!" Ya mike da hanzari har yana neman tuntube yace "Ina suka tafi?" Tace "Kaima kasan inda zasuje...." yace "Muje...." tare da bayi biyu suka tafi sai sauri take zubawa kamar zata tashi sama. Zaune suke bakin ruwa sun zuba kafafuwansu cikin ruwan itada Ashraf suna hirar soyayya, Ashraf ne yace "Yawwa Gimbiyata wallahi naji dadin yadda kika yi saurin sakin jikinki baki ji yadda nakejin dadi ba..." tayi murmushi "Toh ay idan ina tare da kai bana jin wani bacin rai a tare dani." Yace "Nasani Gimbiyata nima ay hakane a wuri na." Tayi dariya ba zato taji an fizgo ta da karfi cikin tsoro ta juyo kawai suka hada ido da Sarauniya sai suka mike da sauri Ashraf yace "Lafiya?" Wani wawan mari Abba ya dauke Gimbiya dashi har sai data daina ji na minti biyu, zai kara kai na biyu Ashraf yayi sauri yasha gabanta hakan ya dakatar da Abba sannan yana huci yace yana nuna su da yatsa "Daga yau na sake ganinku tare sai na dauki mataki akan haka, kinsan aure za'ayi maki meyasa zaki tsaya dawani?" Ta dago tana kallon Abba tace "Abba meyasa kake bari matar nan tana cin galaba a kanka? Tana so ta watsa maka family dinka kai baka gane ba Abba please ka zauna kayi tunanin abinda kake shirin aikatawa...." ya daga mata hannu "Ba abinda zan zauna nayi tunani a kai nadai fada maku daga yau kar na sake ganinku tare!" Sarauniya tayi dariya "Toh kun dai, wai shin soyayyar dole ce? Ku hakura da junanku mana, idan kunne yaji?" Abba yace "Jiki ya tsira." Sarauniya ta jawo Gimbiya da karfi wadda ta kafe da kyar take janta tana tirjewa, Abba ya kalli Ashraf kaima muje..." 


      BAYAN KWANA BIYU.


Tana dakin Kaka da yamma, Kaka ta kalli Hoodah tace "Abincin ya maki dadi?" Hoodah ta kalli plate din ko ci batayi ba tayi yake tace "Eh." Kaka tace "Nasani, ba'ayi maki adalci ba ko kadan, amma kar ki sake kiyi wasa da cikinki Gimbiya kar ciwon yunwa ya kamaki..." ta kakalo murmushi "Abba ya daina sona kaka laifi na yake gani saboda nace bazan yarda ayi mun auren dole ba kuma kinsan ba laifi na bane sai na waccan evil matar, tunda ta shigo gidannan rayuwarmu ta juya daga farin ciki zuwa bakin ciki, na tabbatar da Abbana bai aure ta ba da yanzu ba haka rayuwarmu take ba, Amma Allah ya kadarta hakan sai ta faru babu yadda muka iya...". Kaka ta numfasa cike da alhini "Nasani Gimbiya, saidai duk da haka mahaifinki ne, ki daina fadin haka ba'a ja da hukuncin ubangiji..."

Hoodah tace "Kaka kinfi kowa sanin yadda ya koma yanzu, da Abbana mutum ne shi wanda ko wace y'a take burin samu a matsayin mahaifinta, saidai kash banda yanzu bond din da mukayi sharing da Abbana yanzu babu shi he only care about that monster of a wife..." Kaka ta dafata "Addu'a kadai itace mafita, ki daina tuna baya..." Hoodah tace "Ta ya zan daina tuna baya karki manta a sanadiyarta Ammina ta rasa ranta saboda mugun halinta, wani tabo ne da bazai taba gogewa ba a cikin raina ya riga ya zama permanent scar, lokacin ban wuce shekara shiga naga kisan mahaifiyata da idona cikin dare da misalin karfe sha daya na dare, muna kwance daki sai mahaifiyata ta tashi da niyyar shiga bayi, toh naji motsinta nima sai na farka sai na tashi na daga labule me zan gani? Kawai naga Umma da katon dutse ta bayan katanga saida ta saita daidai inda Ammina take kawai ta jefa mata shi gaban idona Ammi ta zube jini yana fita ta hanci ta baki ta kai, hannunta da kafarta duk ya kurje, kaka girman dutsen nan zai kai katon block na fasa ihu ashe ita kuma ta gudu ba wanda ya ganta nan nayi kan Ammi ashe ta tafi... kamar ta rufewa kowa baki ba wanda yayi yunkurin daukar wani mataki akai...." Kaka tace "Kwarai kuwa duk nasan da haka abinda ta aikata zata jira sakamonta tun a nan duniya, ay matar nan saidai mu bita da addu'a don ta riga ta gama da Jalal..." Hoodah tace "Yanzu yana ji yana gani zai bi umarninta? A aurar dani?" Kaka tace "InshaAllah komai zaizo da sauki maganar auren nan idan har ba alkhairi saikiga baza'ayi shi ba, Allah yayi maki albarka, ya kareki daga dukkan sharri..." tace "Ameen." A hankali ta kwanta bisa cinyar kaka ta lumshe idanu...



*****



 "Assalam Alailkum..." ya fada yana sa kansa cikin harabar gidan nasu, "Wa'alaikumusalam." Abbi ya mike yana fadin "Sultan...!" Yace yana murmushi sosai "Nine Abbi..." Abbi ya jawo shi yayi huggin dinshi yana faadin "MashaAllah ka samu sako na kenan? Na cewar ka dawo ina nemanka...." Sultan yace cikin hausarsa mai kama da larabci yace "Na samu Abbi sheyasa na dawo da gaggawa." "MashaAllah toh ya hanya?" Yace "Alhamdulillah Abbi na same ku lafiya?" Abbi yace "Alhamdullah ya Madinah? Wato kafi son zama can daga tafiya karatu kuma shikenan tunda ka gama sai kaki dawowa? Bakaso kazo ka tayani mulki ko?" Ya saki murmushi da ya bayyanar da ainahin kyawunsa "Ba haka bane Abbi wani abu ne ya rike ni acan din..." Abbi yace "That's alright mu tafi wurin Umminka ka gaishe ta..." Tare suka shiga harabar mahafiyar tasa Hajiya Batula wacce ke zaune tare da bayinta suna gadinta tana ganin Sultan ta mike da sauri cike da murnar ganinsa sukayi huggin juna "Barka da dawowa Yariman Niamey, ka chanza ka kara kyau, tsawo ka kara girma my son..." ta fada tana taba masa sajensa da ya kwanta luff yana kyalli, "Kai Ummi ban wani chanza ba shekaru biyu ne kawai rabona da gida." Ta dan make shi da wasa "Shekara biyu ba kwana biyu bane..." kowa ya kyalkyale da dariya, dukawa sosai yayi ya gaishe da mahaifan nasa suka amsa da fara'a, daga nan dakinsa ya tafi yayi wanka ya watsa ruwa ya fito ya ci Abinci. Kwanansa biyu da dawowa ya huta sosai kullum yana hawan doki, farauta ko fishing. 

Yau kwanansa uku ya shirya tafi gidan abin. kaunarsa Khairi tunda ya dawo bai nemeta ba don haka yaga rashin kyautawarsa kwarai. Bayan ya isa gidansu Khairy yasa aka kirata tana fitowa ta gansa sai ta hade rai ta juya masa keya, dogarawansa yayi ma alamar da su bashi waje take suka tafi, yayi murmushi "Khairy naga kamar bakiyi murnar gani na ba ko?" Ta zumburo baki tace "Eh ay kwananka nawa sai yau zakazo??" Yace "Afuwan wani abu ne ya rike ni amma kiyi hakuri..." tace "Babu komai toh na yafe maka, ka shigo daga ciki Mama ta aje maka abinci da fura..."l gyada kai yayi ya bita ciki yana murmushi. 


  

   WASHE GARI



Yana dakinsa aka aiko masa da kiran mai martaba yanzu, mikewa yayi ya fito ya nufi harabar mahaifinsa nan ya iske Ummi itama a nan, ya zube ya gaishe su suka amsa da fara'a Abba ne ya soma magana "Dama dalilin daya sa nace ka baro madina kazo ina nemanka shine... munyi magana mun tattauna da sarkin Agadez shine muka yanke shawarar hada ka aure da yarsa Gimbiya Hoodah....!" A razane ya dago bashi ba harta Ummi saida ta razana jin abinda Abbi yace da sauri tace "Aure kuma mai martaba? Dalili da mey zakayi mashi aure da rivals dinmu? Meye dalili?" Abbi yayi shiru na yan dakikai can yace "Rivals nada ba? Ay yanzu komai ya rigada ya wuce? Nidai sun aiko man da sako cewar ga bukatarsu kuma na amince da hakan!" Ummi tace "Toh da ka amince ita Khairy yayi yaya da ita? Duk garin nan waye baisan yarima da Khairy ba? Anya kayiwa danka adalci kuwa mai martaba?" Ya numfasa "A matsayina na mahaifin Sultan bazan yarda na cutar da dana ba don haka kuyi addu'a idan akwai alkhairi a ciki...." Sultan ya dago da kansa ke duke ya kalli Abbinsa da shock cikin idonsa ya girgiza kai "Abbi why? Meyasa zakayi man haka? Khairy nakeso kowa yasani meyasa za'ayi mun auren dole?" Abbi yace "My decision is final!" Daga haka ya mike ya bar harabar ya nufi waje inda Ummi tace a zuciye "Shikenan tunda haka ya xaba mu zuba nida shi ko wacece ta shigo wallahi sai ta gudu da kafarta don haka ka kwantar da hankalinka indai ina raye bawanda ya isa yasa ka zauna da wacce bakaso....."

Thursday, 3 June 2021

YAR AGADEZ PAGE O1

 YAR AGADEZ

 

Na MSB 

              {Page 01}



Bismillahi Rahmannir Raheem! Am back y'all!๐Ÿ˜†๐Ÿฅฐ



Lumshe idanuwanta tayi tare da shakan dadad'an kamshin iskan dake kadawa, bayinta guda biyu dake gefenta ta kalla bayan ta bude idanunta a hankali ta kalli daya ta saki murmushi, daka kalli wurin yadda ya kawatu kadai abin kallo ne ga ruwa malale yayi blue sharr gwanin ban kyau, banda itacen da suka kewayen wurin ga grasses hade da kasa data kara ma wurin kyau duk fadin garin agadez babu inda takeso tazo fiye da nan ko damuwa ta shiga data tazo wurin nan take samun sauki. A hankali ta juya ta fara tafiya a hankali kafafuwanta na nitsewa cikin kasa tana tafe suna binta a baya duk inda tasa kafa kamar rakumi da akala. Daga nesa take hango shi yana nufarta fuskarsa dauke da annashuwa da murmushi itama haka, saida sukazo dab da juna sannan suka tsaya inci biyu zuwa uku tsakaninsu, da murmushi a fuskarsa yace "Gimbiya yar sarki jikar sarki, da ay wurinki zanje don nasan a ina zan same ki, saidai kuma na hango ki kina dawowa da alama zaki koma gida ko?" Cikin muryarta mai dadin sauraro tace "Na jira zuwanka Yaya Ashraf amma baka zo ba kamar yadda ka saba, toh nikuma na gaji da jira sheyasa na dawo..." yace "Kema kinsan duk rintsi zanzo mai martaba ne ya tsaida ni sheyasa kika jini shiru..." tace "Toh tunda mun a hadu a nan sai mu koma gida ko?" Yayi murmushi "Har kin gaji da ganina ne da kike cewa mu koma gida?" Tayi yar siririyar dariya "Ko kadan ba haka bane yaya Ashraf kaima kasan bana gajiya tare da kai, ko ba komai kai dan uwa na ne na jini sannan mun shaku tun muna yara kaine abokin shawarata kaine abokin wasa ne, kai kadai ne na tashi na gani a kusa dani banda iyayena..." yace "Hakane Gimbiyata..." tayi murmushi tace "To muje ko..." yace "Your wish is my command your highness." Tayi dariya suka soma takawa cikin masauratar agadez kasancewarsu jinin sarauta, tun daga nesa dogarawan dake baje a waje suka hango su take suka fara kirari "Yar sarki jikar sarki, Gimbiya jinin sarauta, muna maku barka da dawowa Ashraf da Gimbiya Hoodah...  Allah ya karawa sarki lafiya ya kara maki lafiya...." murmushi kawai sukayi suka shige ciki kanta tsaye bata zame ko ina ba sai harabar mahaifinta wato Sarki Jalal. Tana shiga dogawaran sarki suka mike suka fara mata sannu da zuwa hade da kirarin da suka saba yi mata, tana shiga ta isa inda Abbanta ke zaune yana ganinta ya fadada murmushinsa ya gyara zamansa tace "Barka da hutawa Abba..." yace "Yawwa Gimbiya Hoodah da fatan kina lafiya?" Tace "Lafiya lau Abba." Ashraf ya gaishe da sarki ya amsa da sakin fuska sannan yace "Duk inda kaga zara zakaga wata..." sukayi murmushi a take Abba ya kuma cewa "Dazu naji kaka tana ta nemanki kina da labari ko baki dashi?" Tayi Murmushi "A'a Abba banida labari yanzu na dawo gidan..." yace "Toh maza kije wurin ta kiji kiran me take miki..." ta mike tare da bayinta suka taka mata baya har dakin kaka wanda yake bangarensa na daban, da sallama ta shiga kaka na kishingide saman katon carpet din da ke baje a harabar parlon ta kishingida bisa tuntunaye ana yanka mata Apple, tana ganin Hoodah ta dan gyara zamanta kadan tana mai murmushi, zubewa tayi har kasa tana gaida kaka, kaka ta amsa da fara'a itama tace "Halan kina wajen da kike so duk fadin garin nan ko?" Hoodah tace "Kwarai kuwa kaka tun dazu nake a can, saboda can ya fiye man zama cikin gidannan sau million..." take fuskarta ta sauya hawaye suka taru cikin idanunta zucuyarta na tafasa, kaka ta dafata itama fuskarta ta sauya tace "Sai hakuri Hoodah kina ganin dai kowa hakuri yakeyi ba yadda muka iya" Hoodah tace "Toh wai meyasa Abba bazai iya daukar mataki ba a kanta? Taya zatazo ta takura mana ta hana mu sakat sannan ta gagari kowa ba wanda zai iya daukar mataki a kanta..." Kaka ta gyara zama tace "Toh wai kina tunanin haka nan ta barshi ne? Kina ganin ko ni dana haife shi ban isa nayi magana ba, gaba daya ta shanye shi sai yadda tayi dashi bai tankwaruwa...." Hoodah tace "Tunda na rasa mahaifiyata a gidannan nayi bankwana da farin ciki gaba daya rayuwata ta sauya..." Kaka tace "Ay bake kadai ba tunda Safinah ta rasu shekaru kusan goma kenan kowa yayi bankwana da zaman lafiya, gaskiya munyi rashin Safinah gidannan mutuniyar kirki mai halin dattako Allah jadadda rahama a gareta." Hoodah tace "Ameen kaka ke kadai ce nake zuwa wurinta naji dadi yanzu haka ma Abba ne yace nazo kina nemana..." kaka tace "Eh babu komai dama naga baki shigo ba nan da safe shine nake cigiyarki..." Hoodah tace "Ina nan lfylau kaka... bari na shiga ciki." Kaka tace "Sai kin fito." Daga haka ta mike ta fito bayinta na binta har bangarensu tana shiga tayi sallama hakimar na kan kujerar mulkinta ga bayinta nan sun kai bakwai suna mata fifita, Hoodah ta isa gareta ta zauna kan sauran kujarun da suka zagaye makeken parlon tace "Barka da hutawa Umma..." wani mugun kallo ta watsa mata sannan tace "Lafiya... daga ina kike?" Tace "Daga Darwish Mahal nake..." Ta karkada kafa "Da izinin wa kika fita?" Hoodah is beginning to lose her patience, wani ajiyar zuciya ta sauke tace "Da izinin Abbana..."  Sarauniya Karima tace "Daga yau na sake ganin kin fita baki sanar dani ba zanga uban da zai tsaya maki a gidannan, tashi ki bani wuri..." ta mike zuciyarta na kuna tayi dakinta, bayinta ta kalla idanu duk kwalla tace "Privacy..." take suka fita daga waje ita kuma ta kulle kofarta ta jingina tana mai lumshe idanu. Tafi minti sha biyar a haka ita batason wannan rayuwar tanaso tayi rayuwa as normal mutum she hates being royal, tanaso tayi rayuwar privacy ba tare da an takura mata ba, tanaso taganta tana rayuwa normal ba irin wannan rayuwar ba... gathering courage nata tayi ta wuce bathroom tayi wanka ta fito bayan ta kimtsa aka kirasu cin abinci gaba dayansu wato dinner. Bayan kowa ya hallara aka masu serving abincinsa Ashraf ne da Hoodah suka kalli juna sannan sukayi murmushi a haka suka kare cin abinci. Can wurin karfe takwas daya daga bayi ce ta shigo da sallama bayan Hoodah ta amsa tace "Ranki shi dade kizo Ashraf na son ganinki acan harabar shan iska..." dan murmushi tayi tace "Ki ce masa ina zuwa." Daga haka ta dan russuna kadan sannan ta dau mayafinta ta fita inda yace mata yana nan, bayinta basuyin gigin binta ba saboda dama inda Ashraf yayi mata kiran nan na musamman basu cika binta ba. Zaune yake bisa daya daga kujerun shakatawa da center table mai dauke da Apple da aka yayyanka sai glass cup guda biyu wanda aka cika da madara yana cin Apple din a hankali yaga ta shigo da sallama, ya karkato kansa yana dubanta duba na musamman sannan ya amsa da fara'a yace "Ya zaki tsaya a nan? Ki karaso mana..." tayi murmushi ta karaso ta zauna tana fuskantarsa sannan yace "Da fatan gimbiyar tawa tana nan lafiya lau? Ko dayake banga alamun haka a tattare da ita ba... meyake damunki?" Tayi yake tace "Babu komai Yaya Ashraf meyasa kake zaune a nan kai kadai?" Yayi murmushi "Ba ni kadai nake zaune a nan ba daman ke nake jira sheyasa kika ganni a nan... amma still ina so ki fada man me Umma tayi miki nasan dai itace..." ta hadiye abu da kyar tace "A gaskiya yaya Ashraf abinda Umma takeyi bata kyautawa gaba daya tabi ta tsaneni bansan menayi mata ba, abu kadan zata hauni da fada da zagi na cin mutunci nida gidan mahaifina amma bana tare da farin ciki..." yace "Haba Gimbiya ay kema kinsan bake kadai takeyi wa haka ba in kin kula haka halinta yake batada imani ko kadan sannan batada kirki, don Allah daga yau kar ki sake bari maganganunta suyi tasiri a cikin zuciyarki..." ya numfasa ya cigaba "wato akwai wata mahimmiyyar maganar da nake so muyi dake Gimbiya in har bazaki damu ba..." tayi murmushi "Nagode yaya Ashraf kai kadai ne kake sanyaya raina kaida kaka idan an bata mun rai, sannan kwarai zaka iya yin magana dani ina jinka..." ya sauke ajiyar zuciya yace "Mun dauki tsawon lokaci muna soyayya a boye baki ganin lokaci yayi da ya kamata mu fito fili asan irin kaunar dake tsakanina dake? Ya kamata manya su shiga cikin maganar nan...." ta dago da sauri tana dubansa tace "Nasani yaya Ashraf kamar yadda kake sona nima haka nake sonka saidai kana ganin hakan mai yuwuwa ne kuwa?  Ina tsoron Umma karta hanani aurenka idan na rasaka bansan a wane hali zan shiga ba..." yace "Haba Gimbiya meyasa kike irin wannan maganar? Ita Umma keda iko da ke da zata hanamu aure? Ay indai Abba ya bada goyon ay sai inga ba wata matsala..." tayi ajiyar zuciya tace "Shikenan..." nan suka cigaba da fira cikin so da kaunar junansu...



      Washe gari


Gimbiya Hoodah tanason zane like real drawings tana dakinta karfe kusan 9 na safe tana making outline na gown da black pencil, tana cikin sanya colors din akayi knocking kofa daya daga cikin bayin Umma ce tsaye ta gaida Hoodah, Hoodah tace "Yadai?" Ruqayyah tace "Afuwan ranki shi dade Umma tana son ganinki yanzu yanzu..." Hoodah ta dan zaro ido kadan tace "lafiya?" Ruqayyah tace "Banida masaniya ranki shi dade ta dai ce ki sameta harabar mai martaba yanzu..." tayi tsaye kamar gunki sannan ta gyara zaman gyalenta tace "Ina zuwa..." 

tafe take tana maganar zuci "Wai meye matsalar matar nan ne? Me take bukata daga gareni tunda uwar safiyar nan, tausa takeso nayi mata ko wanka?" Tana tafe tana kara zama frustrated. Sallama tayi mahaifinta ne zaune cikin kujerarsa ta musamman yar mulkin na gefensa, saiga kaka da yayar shi Aunty Rahanatu. Duk suka amsa sallamanta ta samu gu ta zauna yadda ta tabbatar Umma zata sha wahalar ganin fuskarta. 

"Ke Hoodah!" Ta daka mata tsawa mai razanarwa tace "Dawo gabana ki zauna..." ta nuna wurin da yatsanta, zama tayi kanta kasa sannan Umma ta fara magana cikin nuna isa "Kamar yadda kuka sani nice na hada wannan taron don mu tattauna gameda auren Gimbiya da Yarima...." a razane kowa na parlorn ya dago yana kallo Umma cike da firgici da rudu, Abba ne yace "A'a Umma maganar nan mun riga munyi ta dake ba wata maganar aure da za'ayi wa Gimbiya ina tunanin mun gama maganar nan tuni?" Nuna shi tayi da yatsa cikin daga murya "Jalal wannan maganar ba wanda ya isa ya chanza ta a gidannan a matsayina na uwar yarinya ay ko ban haifeta ba ni ce na rike ta don haka inada hakki a kanta kuma yanzu nace zan hada aurenta da yarima ba wanda ya isa ya chanza ta." Shima nuna ta yayi da yatsa "Amma nine ubanta! Inada hakki a kanta nima kuma na fada bazata auri yarima ba, ke sanin kanki ne bamu shiri da masauratarsu don me zaki so ki hada yata aure dasu? Baki isa ki yanke hukunci ina raye ba saidai bayan na mutu!" 

 Umma ta mike tsaye tace "kaga Jalal bana son wani dogon bayani ko surutu a nan ko uwarta daka aura ay kaima hadaku akayi inace ba ganinka kayi kace kanaso ba? Don haka kamar yadda akayi wa uwarta itama haka za'ayi mata!" 

Hawaye suka fara wanke ma Hoodah fuska zuciyarta kamar ta bar kirjinta, kallon Ashraf da yayi tsaye bakin kofa kamar an dasa shi a wurin, Kaka cikin rawar murya ta mike tace "Saboda kece uwarta? Toh ko mahaifiyarta bazan yarda tayi mata dole ba bare kuma ke..." Jalal ya kalli kaka yace "Kiyi shiru kaka ki barni inyi magana kar ki bata mata rai..." kaka tasa salati tana tafe hannu "Wato kafi gudun bacin ranta akan ka na yarka? Kai kadai ne zaka iya mata fada amma mu bamu isa ba kenan? Wannan ay zancen banza ne zancen wofi ba itace uwar yarinya ba don haka bata isa ba!" Cikin nuna halin ko in kula tace "Well, mun riga mun gama yanke hukunce shima kanshi mai martaba ranar da mukayi maganar bai musa man ba dan haka za'a daura auren ko kuna so ko baku so..." kowa yayi shiru parlon an rasa me bakin magana 

"Excuse me!" Hoodah tayi magana karon farko tun zuwanta "Meyasa kike treating dina kamar wata dutsi? Ina da damar yin abinda nakeso da abinda naga dama dan haka bazan auri wani yarima ba..." ta fada muryarta na sama  "Zancen banza kikeyi!" Umma ta fada tana buga sandarta a kasa  "Dama wayace sai kin yarda sannan mu cigaba da shiri ? Duk nan manyanki ne kar ki sake saka man baki ba tare da an baki izinin magana ba!" Hawaye wasu suka sake wanke mata fuska, kakkausar muryarsa sukaji yana fada "Kinyi tunanin feelings dinta ko bakiyi ba?  Da abinda takeso da wanda bataso? Kinyi tunani? Ko ke uwarta ce da zaki zo ki nuna isa a nan?" Tasss! Abba ya dauke shi da wani irin wawan mari yace yana nuna shi da yatsa "Dayake bakada kunya  agabana kake fadawa matata magana!?" Wata irin razananiyar kara Hoodah ta fasa tace "Nace baxan aure shi ba! Stop!" Ta fada cikin razana ihu! Aunty Rahanatu ta taso ta kamata take Hoodah ta tura ta gefe "Ba inda zanje inada damar da zanyi magana na fada bazan auri yarima ba, baza'ayi manipulating dina ba a cuce ni da wani auren dole!" Ta fada cikin daga murya hawaye na wanke mata fuska.....

Monday, 4 January 2021

AKAN YATAH 01

♠️♠️♠️AKAN Y'ATAH♠️♠️♠️


                         1


Tafiya take a hankali da ka ganta kasan ta gaji amma duk da haka bai boye farin cikin da take ciki ba, saboda yalwantatcan murmushin dake a fuskar ta, tafiya kadan tayi ta isa parking lot din Court din, daidai wata mota kirar BMW naga ta tsaya ta fiddo key a jakanta tayi unlocking motan sannan ta bude ta shige, ta dade zaune idon ta a lumshe tana murmushi, a hankali cikin muryan ta mai sanyi naji tace "Alhamdulillah" sannan ta tada motar cike da kuzari ta bar federal court of Appeal din. Daidai gate din wani tamfatsetsen gida naga ta tsaya a cikin G.R.A Malali,  horn ta danna ba'a dau lokaci ba naga an wangame gate din, a hankali ta danna kan motar ciki daidai parking lot ta tsaya, saida ta d'an duba lokaci sannan ta fito cike da gajiyar da ta d'ebo, "Sannu da zuwa Hajiya..." Wanda ya bude mata gate d'in ya fada cikin girmamawa. Ta kalleshi tana murmushi tace "Yawwa Malam Iro, an d'auko Sanah daga makaranta?" Kafin ya kai ga bata amsa taji an rungume kafafun ta, cikin jin dad'i ta duka daidai tsawon yarinyar data rungume ta d'in, kyakkyawar gaske ce, k'arancin shekarunta basu '6oye kyawun yarinyar ba, kumatunta ta kama cikin jin dad'i tace "Sanah habibty yau kin riga ni dawowa ko?" washe white teeth dinta tayi cikin jin dadin ganin Momyn  tata, tace 'Yes Mummy today I came back before you, but why did you come back late? Remember you promise to take me out" Ta idar da maganar tana wani b'ata fuska irin na idan yara basuji dadi ba. Kamo yan kananun hannunta tayi cikin sanyin murya tace "oh am sorry my love aiki ne ya rike ni yau amma I promise to take you out tomorrow, since am not going to work tomorrow ok?" Kyalkyalewa tayi da dariya ta fada jikin mom dinta alamar taji dadin zance, haka ta kama hannunta suka nufi cikin gidan.

 Iya tsaruwa gidan ya tsaru da ka gani ba sai an fada maka ba zaka san masu gidan sun kama k'asa, a hankali ta tura kofar palon dake dauke da royal chairs masu shegen kyau kalar ash da gold, palon ya hadu iya haduwa kai tsaye ta hau stairs din, saman ma palo ne dan madaidaice da study room daga gefe sai wasu dakuna guda ukku. A hankali ta murd'a handle din dakin ta shiga, fantsamemen d'aki ne na gaske, tsayawa ma fad'in girmansa da tsaruwarsa ma bata baki ne, sanyin ac ne hade da kamshin freshner da turaren wuta ne sukayi mata sallama, a gajiye ta zauna gefen gado tana mai balle buttons din hannun rigarta, kai tsaye toilet ta fada don yin wanka tana gamawa ta shafa creams masu kamshi ta nufi closet dinta, rasa kayan da zata sa tayi don kaya marassa nauyi tafi bukata a yanzu. Wani material ta hango Wanda akayi ma dinkin doguwar riga ash and black yasha stones, tayi murmushi ta daukota ta kimtsa tsaf da ita, tana gaban mirror tana taje dogon gashinta akayi knocking kofa, dan juyawa tayi gami da cewa "Yes? Come in" mai aikinta ce ta shigo gami da gaisheta "Welcome ma" ta danyi murmushi "Thanks Blessing, what is it?" Blessing cikin girmamawa tace "Ma I came to ask you if you're ready to eat, I wanna warm the food" tayi murmushi "Of course you can, set the table as well" Blessing ta dan russuna "Ok ma" sannan ta fita. 


Cikin 5 minutes ta kammala ta fito downstairs, hango Sanah tayi gaban tv zaune 'kasa tana kallon favorite cartoon d'inta wato Masha and the bear ta du'kufa tana kallo tsakaninta da Allah, murmushi tayi sosai tana kallon yar tata cike da kauna tace "Sanah?" Hankalinta naga tv tace "Yes mummy?" 

"Come here" tasowa tayi ta iso inda maman tata take tace "Mummy gani" dan shafa kanta tayi "have you eaten?" Sanah tayi murmushi "yes mummy" Maman tace "toh homework fa?" Ta dan turo baki "Mummy nayi" ta danyi dariya "I mean both na islamiyya and school?" Ta gyada kai alamun eh a k'agare take ta koma ta cigaba da kallonta. UMMU SULAIM tace "Alright love you can go" da gudu ta koma cike da murna.


Blessing ta gama had'a komai a dinning nan ta zauna taci abinci, bayan ta kammala ta mi'ke a gajiye don d'auro alwallan sallan magrib, kallon Sanah tayi tace "Oya a tashi aje ayi sallah, zo muje kiyi alwalla"


Bayan sallar isha'i suna zaune palon kasa itada Sanah, kan Sanah yana kan cinyarta tana tsefe mata kai. "Mummy na gaji" Mummy tace "Wai Sanah meyasa bakya son kitso ne? So kike kanki duk yabi ya lalace ya zube ne?" Dan turo karaminta pink lips dinta tayi, idan akwai abinda Sanah ta tsana shine kitso bata son abinda zai taba kanta, lallabata tayi har ta kammala, gobe takeso a kitse kan saboda weekend ne ba school. Bayan sun gama ta gyara mata gashin, indomie tasa Blessing ta dafa mata tare da soyayen sausage, bayan ta gama cin abincin taja hannunta suka hau sama, wani daki daban naga ta bude ta shiga opposite wanda ta shiga dazu, ko ba'a fada ba kasan wannan ne dakin Sanah, pink and purple, kanshi bed sheet din dake shimfide saman gadon pink ne mai matukar kyau tare da curtains pink, dakin kamar shagon saida toys, ba abinda babu na kayan wasan yara, d'akin kashi kashi ne akwai study room wanda yake kama da library, story books ne both English and arabic. Sai closet dinta wanda akwai kofar toilet ciki, inda toys nata suke kamar toy room yake, dakin dai ya tsaru iya tsaruwa ba abinda kake ji sai sanyin ac. 

 Wanka tayi mata ta shirya ta cikin pajamas dinta pink and yellow masu zanen teddy na bacci an rubuta goodnight a jiki, bayan ta kwantar da ita kan gado kujera taja ta zauna gefenta tana shafa mata fuskanta a hankali, addu'an bacci tasa ta, tayi ta shafe mata jikinta gaba daya, sannan ta dauko daya daga cikin story book din ta fara karanta mata tai tayi har bacci ya dauke ta, koda baccin ya kwashe Sanah kasa tashi Ummu Sulaim tayi, k'ura ma yar tata ido tayi cike da 'kauna ga wani irin tausayinta da ke fizgarta lokaci daya taji hawaye na neman zubo mata, take zuciyanta ya mata nauyi kokarin gani take hawaye bai zubo mata ba, amma ina saida stubborn one ya zuba, gogewa tayi tare da manna mata kiss a goshi sannan ta mik'e a sanyaye ta kashe mata wutan dakin ta fita.


Dakinta ta shiga tayi wanka ta fito daure da towel, kanta ta kalla ta mirror idanunta sunyi jawur, murmushi tayi da yafi kuka ciwo ta zauna a sanyaye ta shafa mai, kayan baccinta ta zura ta hau gado lamo ta kwanta, tana kwanciya da minti kusan biyar wayarta ta fara ringing. D'auka tayi ganin mai kiran yasa ta mik'e tana murmushi, jingina tayi da gado ta dauka. D'ayan bangaren akayi sallama Ummu Sulaim ta amsa sallaman tace "Mama bakiyi bacci ba har yanzu?" Mama tayi murmushi tace "Wallahi banyi ba Ummu Sulaim ina dai shirin yi" Ummu Sulaim tace "Ayya Allah sarki, to ya sanyi sanyi?" Mama tace "Alhamdulillahi, akwai sanyin garinnan ba kadan ba" Ummu Sulaim tace "Ayya to yaushe zaki dawo ne mama?" Mama tace "Ranar Monday inshaa Allah, hope kuna lafiya? Ina Sanayah?" Ummu Sulaim tayi murmushi "Tayi bacci wallahi, Allah kaimu ya dawo mana dake lafiya" mama tayi yar dariya "Amin, a shafa man kanta idan ta tashi' Ummu Sulaim tana murmushi tace "Inshaa Allah Mama, ay tayi missing naki sosai" Mama tace "Nima haka ay nayi missing dinta sosai" Ummu tayi murmushi, shiru sukayi dukkansu can Mama tace "Goodnight dear" Ummu Sulaim tace " Toh Mama Allah kaimu goodnight" katse wayar Ummu tayi ta kwanta da tunani iri iri a ranta. 


Washe gari bayan Sanah ta dawo daga islamiyya, kitso akayi mata bayan an gama ta shiryata kamar yadda tayi mata alkawarin zata fita da ita, palo suka fito tana rike da hannun Sanah duk sun sha kyau sai kamshi suke zubawa. "Uwani!" Uwani dake kitchen tana goge cooker ta fito da sauri tace "Hajiya gani?" ta furtan hakan tana mai russunawa. "Zamu fita nida Sanah, Idan kin gama aikinki kice ma Blessing ta bude freezer ta fiddo kaji guda 3 ta gasa man su, sannan ki fada mata na chanza kitchen time table ta duba sai a d'ora girkin rana" Uwani tace "Toh Hajiya Allah ya tsare" cikin murmushi tace "Ameen" 

Ramat shopping mall naga sun tsaya. Fitowa sukayi tana rik'e da hannun Sanah suka shiga ciki. Duk abinda Sanah takeso take dauka, sai da suka cika shopping trolley din dam sannan suka hak'ura, bayan sun fito direct Havillah ta tsaya, a nan suka tsaya suka sha, suna gamawa suka wuce City Central Amusement Park, Sanah was over the moon, she was so happy she had fun, nan ma sun shak'ata sosai, sai da Sanah tace ta gaji sannan ta kamo hannunta suka fito daga park din....


A gajiye suka shigo palon misalin karfe 5 saura, Sanah na gaba Ummu Sulaim na biye da ita a baya, Malam Iro ne ke ta shigo da ledoji daga mota, sai daya gama sannan ta kwashi kayan ta hau sama dasu, sallan Asr sukayi itada Sanah sannan suka sauko downstairs, da Blessing suka ci karo tana d'auke da plates zata sauke su bisa dinning, da fara'a ta gaishe da Ummu Sulaim  "Good afternoon ma, you are welcome ma" itama cikin fara'a ta amsa mata tana fad'in "Thank you Blessing, kin gama komai?" Blessing tace "Yes ma" Ummu Sulaim tace "Alright weldon, you can go" Blessing tace "OK ma" bude kulolin tayi taga Lafiyayen jollof rice ce, sai tray din coleslaw, gefe kular kajin da tace a gasa mata ne, sai drinks kala kala. Zaunar da Sanah tayi sannan ta zuba mata abincin, wani plate ta samu ta d'ibar ma su Blessing kazar sannan ta kirata ta bata, itama ta zuba nata ta tsiyaya masu drink din a cups. Zaunawa tayi ta fara cin abincin, amma kana kallon fuskanta kasan ba walwala kawai dai daurewa take in banda juya abincin ba abinda takeyi, ajiyar zuciyar data saki shi ya janyo hankalin Sanah ta dago tana kallonta, abincin ta kalla ganin bata ci ba tace

"Mummy why didn't you eat your food?" K'ak'alo murmushi tayi da sauri tana shafa kan Sanah tare da kai spoon daya baki tace

"N...nothing habibty...the food...is...ho...ho...ot..." Sanah ta kalli maman duk da karancin shekarunta hakan bai hanata gane mummynta na cikin damuwa ba, dama jefi jefi mood din Ummu Sulaim ya kan chanza, za'a ga kamar dai tana cin damuwa.

"No mummy the food is warm not hot, please Mummy tell me why do you look so worried? Did I offend you?" Da sauri Ummu ta rik'e mata hannu tana girgiza kai tace

"No darling it's nothing don't worry, is just stress you know the nature of my work, am really tired" Sanah ta kalli maman tata

"Am sorry mummy, I wish I can do anything to ease your stress" Ummu Sulaim tayi murmushi "Of course you can sweetheart" cike da jin dadi Sanah tace "Tell me mummy" Murmushi tayi tana shafa gefen fuskanta

"I want you to study hard in school, be a good girl, that's the only way you'll ease my stress" G'yada kai Sanah tayi tana murmushi

"InshaAllah Mummy I promise" Ummu Sulaim tayi murmushi "That's my baby"

Haka tayi weekend dinta tana ba Sanah kulawa kamar ko wace weekend saboda yanayin aikinta, kuma harga Allah tana son ganin y'arta cikin walwala da annashuwa,  haka takeyi ko wace weekend suna fita yawo just to spend some time together, har bataso ace Sunday tazo. 


Ranar monday tunda ta tashi sallar asuba bata koma bacci ba, tana kan sallaya tana azkar aka turo kofar aka shigo, Zainab mai aiki ce ta shigo, budurwa ce bazata wuce 23 years ba, sallama tayi Ummu Sulaim tana addu'a bayan ta shafa ta amsa sallamarta tana mai bata izinin shigowa ciki, har k'asa ta zauna ta gaisheta ta amsa da fara'a kamar kullum  sannan Zainab din tace "Anty me Sanah zatayi breakfast dashi yau?" Shiru tayi tana tunani can tace "Toh Zainab nakega ki mata French toast amma kiyi amfani da butter wurin frying dinsa, sai ki dama custard" Zainab tace "Toh Anty" sannan ta mik'e ta fita. 

Saida Ummu Sulaim ta gama azkar d'inta sannan ta mike ta ninke sallayar ta fito daga d'akinta, d'akin Sanah naga ta shiga, tana shiga ta kunna fitila su Sanah anata bacci daga gani baccinta take mai dadin gaske, Ummu Sulaim ta dan taba ta tare da kiran sunanta, juyi tayi tana kokarin bude idonta, take kuma ta koma baccinta, dariya taba Ummu Sulaim don haka kawai sai ta jawota gaba daya ta direta k'asa ba shiri ta tashi tana murza ido. Hannunta ta kama har toilet tasa ta wanke fuskanta tare da yin brush, ruwan wanka ta hada mata ta cire mata kaya, Ummu Sulaim tana k'ok'arin fitowa daga toilet din ta juya tana kallon Sanah dake shirin fara wanka, tace "Sanayah hurry up kinji ko? Kar kiyi late and kiyi alwalla daga nan" Sanah tace "Ok mummy"  Kafin Sanah ta gama har maman ta gama hada mata uniform d'inta da komai ta aje mata kan gado. Bata d'auki lokaci sosai ba ta fito d'aure da pink towel. Ummu Sulaim ta gama shirya ta tsab fes da ita tasa tayi sallah sannan ta kamo hannunta har downstairs, kan dinning ta zaunar da ita ta zuba mata breakfast d'inta, Ummu Sulaim ta kira Zainab dake kitchen tana tattara ma Uwani kayan wanke wanke ta amsa tare da fitowa daga kitchen d'in tace "Anty gani" Ummu Sulaim tace "Zainab kin hada ma Sanah abinci a lunch box dinta?" Zainab tace "Eh Anty na hada" Ummu Sulaim tace "Yauwa jeki d'auko" da toh ta amsa sannan ta wuce kitchen. Bayan Sanah ta gama breakfast Malam Iro ya leko bakin k'ofa da sallama sannan yace "Hajiya, Bala driver yazo yana jiran Sanah" Ummu Sulaim tace "Ok Malam Iro kace masa gata nan" wucewa yayi yana fadin "Toh Hajiya" Har bakin mota ta rakata kamar kullum, Ummu Sulaim na gaisawa da  Bala ta mik'a masa lunch box din Sanah, da sauri ya bude back seat Sanah ta shiga tana daga ma mamanta hannu, Ummu Sulaim ta shafi fuskanta tana fadin "Be good, ayi karatu da kyau, Allah ya bada sa'a" Sanah tace "ameen Mummy" Ummu Sulaim ta mata peck tace "Love you" Sanah ta mata peck itama tace "love you too Mummy" 


Ummu Sulaim na shiga ciki tayi wanka tare da brush, sauri sauri ta shirya ta fito downstairs tana rufe briefcase dinta, da Blessing taci karo ta gama had'a mata lafiyayyen breakfast tasa mata a warmers "Good morning ma" Ummu Sulaim na murmushi tace "Morning Blessing" hanyar kofa tayi da sauri tana duba time a wayanta 9:20am ta gani, har ta kai bakin kofa ta juyo tare da cewa "Blessing where is Zainab and Uwani?" Blessing tace "They are inside ma" Ummu Sulaim ta nufo dinning tana fad'in "Please call them for me Blessing" ciki tayi tana fadin "Ok ma" gaba daya suka fito daga kitchen din bayan sun iso Ummu Sulaim tace "Yau zan dawo gida da wuri, inason ayi general cleaning yau Mama tana hanya, a girka abinci da dan yawa, kuyi shinkafa da miyar kaji, ku hada salad, sai ayi zo6o, Uwani don Allah kuyi aikin nan yadda ya kamata" suka amsa da toh sannan ta cigaba "Zainab ki d'auko sabon bed sheet a shimfida wa Mama, a wanke toilet din a share mata dakinta sosai kafin na dawo" Zainab tace "Toh Anty" Ta kalli Blessing tace "Blessing I told them mama is coming back today, I want you to cook rice and stew use the chicken to make the stew then salad, including zobo too, please I want everything to be perfect before I come back" cikin girmamawa Blessing tace "Ok ma" 

Sauri sauri ta isa motanta Blessing na biye da ita a baya rike da warmers a hannu. Bude motanta tayi ta shiga inda Blessing ta zaga ta gaba da saka mata warmers din tana mata a dawo lafiya. Tana murmushi ta tada motar gate aka wangame tana danna kan motanta waje, Malam Iro na d'aga mata hannu har ta bar anguwar.....


♠️♠️♠️AKAN Y'ATAH♠️♠️♠️


Littafi ne da ya kunshi alamura Akan fyad'e da ya zama ruwan dare yanzu, mun rubuta wannan littafin ne saboda  karfafa masu guiwa Akan su tashi su nemi hakkin su, sannan su san cewa they can fight for their right akan cuta masu da akayi.

Sannan Kuma susan cewa suna iya rayuwar su kamar kowa ba tare da sun tsangwami kansu ba, saboda babu wanda yafi karfin kaddara.


Littafin yana kunshe da cin amana, tsangwaba da jajircewar *UWA AKAN YARTA*


Muna fatan zaku bamu goyan baya Akan abunda muke so mu isar, mun gode.


AKAN Y'ATAH NA KUDI GA MAI BUKATAR LITTAFIN, 


NAIRA 300 ne


DUK WANDA KESON BIYA YA TINTIBI WA'INNAN NUMBERS DIN.


0802 874 8204 ko 07035642883


   "Karku Bari a Baku labari"


♠️♠️litattafan  marubutan♠️♠️


KOMIN NISAN DARE

TAGWAYE NE?

KHALEEL

BA'KUWA

AUREN FANSA

RAYUWAR HOSTEL

FAWZAN KO ADEEL?


THANKS FOR PATRONIZING US