✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น23 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Baba yayi murmushi yana dubansa yace.
"Faruk ka saki jikinka dani mana, ka d'auke ni a matsayin mahaifinka, ka bani amsar tambayar da nayi maka."
Ya daure yace
"Da...dama Baba, dama... dama... ina so mu lokaci ne, sannan na gabatar maka da kaina a cikin manaiman auren Meenah, duk da dai tace min batada wanda ta tsada, to amma... amma mun daidaita kanmu."
Baba yayi murmushi gami da lumshe idanu na 'yan mintina, sannan ya bud'e su a hankali kan Faruk.
"Haka ne, Meenah batada wanda ta tsaida, hasali ma kai ne mutum na farko da ta ta6a yin soyayya da shi, sai dai wani hanzari ba gudu ba, kafin na amince maka da auren Meenah, ina so kayi min alk'awarin rik'e ta bisa amana da gaskiya, kar ka ci amanarta kar ka yaudare ta, shine kawai abinda nake buk'ata daga gare ka. Duk da nasan dai mahaifinka mutumin kirki ne kuma ina da tabbacin tarbiyarsa gareku, kuma ina masa addu'a Allah ya jik'ansu da gafara."
Yace
"Amin Baba, indai wannan ne kar kayi haufi a kaina insha Allah babu matsala."
Baba yayi murmushin jin dad'i yace
"Alhamdulillah, amma kuma ina so ka bari in tuntu6i yarinyar tukunna inji ta bakinta, nafiso na tabbatar sai a sanar da kai don ka turo magabatan naka." Faruk yayi murmushi.
Yace
"To Baba babu damuwa insha Allah."
Baba yayi murmushi gami da mik'ewa tsaye.
Yace
"Kana iya tafiya Allah yayi muku albarka. Ya amsa da "Amin."
Baba ya yi gaba, Faruk yabi bayansa yana jinjina al'amarin.
***
Abu k'arami na neman zama babba, tun tana ganin abin kamar wasa ta fara ganinshi babba. Cikin k'ank'anin lokaci Jidda ta fahimci Faruk soyayya yake, kuma wacce yake so d'in ta kame masa zuciya farat d'aya, duk wani observation nata akan Faruk ta gama gane komai, tausayin kanta ya kama ta. Anisah ce ta shigo d'akin tana tsaye a bakin k'ofa ta k'ura ma Jidda idanu, hannunta d'aya d'auke da cup d'in tea d'ayan kuma yana rik'e da wayarta k'irar Samsung galaxy S6, a hankali ta k'araso ciki tana murmushi. Zama tayi kan gadon da Jiddar ke zaune a kai ta dafa ta.
"Yaya Jidda..."
Firgit! Ta dawo daga duniyar tunani tana kallon Anisah, sai kawai ta k'ak'alo murmushin dole. Anisah tayi murmushi.
Meyake damunki?"
Tayi tsai kamar mai tunani kafin tace
"Babu komai."
Anisah ta girgiza kanta.
"Sam ban yarda ba yaya Jidda, na dad'e da ganin chanzawarki, gaba d'aya kin bi kin sussuce kin zama wata iri? Har Mama ta soma tambayarmu abinda akayi miki,a gaskiya yaya Jidda koma meyake damunki ki fito fili ki fad'a mana, k'ila da akwai taimakon da zamuyi miki..."
Har yanzu bata d'ago ba kanta na k'asa dai tana kallon wayarta. Yusra ce ta lek'o tace
"Anisah ya Najeeb na kira, kuma yace kiyi sauri kiran nada mahimmanci."
Sai a sannan Jidda ta d'ago tana dariya tace.
"Kice dai za'a je a soye, wai yanzu Anisah har ta girma ta iya soyayya ko?"
Anisah ta sunkuyar da kanta k'asa tana murmushi kafin kuma ta fice da gudu ganin zasu sakata gaba da zolaya.
Yana zaune a garden bisa kujera yana sanye da jar riga da ash wando (jeans). Kayan sun haska fatarsa da take kalar fatarsa chocolate mai haske, ta k'araso tana murmushi, tun daga nesa yake kallonta har ta iso inda yake. Yayi nisa a kallonta har bai san lokacin data zauna ba, sai data kira sunansa yayi firgit ya dawo duniyar tunani.
"Ya Najeeb."
Yayi sassanyar murmushi yace.
"Anisah kina lafiya?"
Tace
"Lafiya lau, ya naganka nan kai kad'ai?"
Yace
"Ke nake jira ki taya ni fira, ko baza'a ta ya ni ba?"
Tace
"Uhm, daman Yusra tace kana nema na, sheyasa na fito."
Yayi murmushi yace
"Hakane, ni nace ta kira ki, daman inji batun karatunku ina kukayi applying?"
Tace
"Nayi applying first choice d'ina a Base nida Yusra, sai second choice mukasa Turkish Nile. Sai last mukasa BUK."
Yace
"Ok yayi Allah ya taimaka."
Tace
"Amin."
Yace
"To ya batun maganarmu ina aka tsaya? Har yanzu fa baki bani amsa na ba, kullum dana miki maganar baki bani gamsashiyar amsa, amma yau ba inda zaki sai kin fad'a min."
Cike da kunya tace
"Wace magana ya Najeeb?"
Yace
"Kin fini sani."
Ta sunkuyar da kanta tana kallon k'asa, yace
"Ke nake saurare fa."
Tace
"Ya Najeeb, wai yanzu kake nufi za'ayi auren?"
Yayi dariya
"Eh mana idan har kin amince me ake jira? Bakiji me Baba yace ba? Yace mu dukkanmu zai had'a ya aura damu, yace mazan su fad'i matan da suke so, matan kuma su gabatar masa da wanda suke so, yace so yake yayi gaba d'aya ya huta. Kinga ni da ke sai ayi 'yar gida tuwo na maina. Ko ba haka ba?"
Tayi shiru bugun zuciyarta ya k'aru, tabbas tana son Najeeb kuma shima d'in yana sonta sosai. Tace
"To ya Najeeb Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Yaji dad'in kalamantanta sosai yace
"To Amin ya Rabbi, daman haka nake so naji daga bakinki."
Tayi murmushi.
Sai da suka kammala firar tasu ne kafin kuma su tashi su shige ciki.
MSB๐
Friday, 21 July 2017
Wednesday, 12 July 2017
AUREN FANSA 22
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to Mrs Fawwaz, Sadnaf, Momyn Sultan, my sakwara, Maman Khady, Jannatuwa, Faridat Musa, Rufaida Yusuf. One luv guys❤️๐
๐น22 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bilki ta soma magana cikin fushi.
"Kin bani mamaki Meenah, yanzu har yaushe idonki ya bud'e da kike neman k'wace ma 'yar uwarki saurayi? Ke ko kunya bakiji ace 'yar uwarki tana son wani kema kina sonsa? Fatima fa k'anwarki ce Amina, ay na d'auka ke mai d'auka ce ki sadaukar mata da wani idan ta kama, amma wai ke! Kece mai k'wacewa Meenah."!
Ta share hawayenta cikin tsantsan mamakin Mamin tasu, muryarta na rawa ta soma magana.
"Mami Faruk bai ta6a cewa yana son Zarah ba, ni yake so tun asali, ko ita Fatiman ba sonsa take ba, ni bansan ina kika ji cewar saurayin Fatima ne ba, idan ma kina tunanin cewar saurayin Fatima ne to ki daina tun wuri." Sai kuma ta juya mata baya gami da had'e hannayenta wuri d'aya tace
"A baya kinsha k'wace min kyauta a makaranta, amma gaskiya yanzu bazan yarda a k'wace min Faruk ba, hak'uri zakiyi ki sa mana albarka!"
Sai kawai Bilki tasa salati, yau tana fad'a Meenah na fad'a.
"Lallai wuyanki yayi k'wari ya isa yanka, akan nace kin k'wace wa 'yar uwarki saurayi kike neman ki fad'a min magana Meenah."
Ta fad'a tana nuna kanta.
"Bafa saurayi na bane Mami."
Duk suka d'aga ido tana tsaye bakin k'ofa idanunta sun kad'a daga fari zuwa ja! A hankali ta k'araso cikin d'akin tana share hawaye tace
"Akan me zaki mare ta akan maganar da bakida tabbas a kanta? Mami! Ki sani Meenah 'yar uwata ce ta jini, ta yaya kike tunanin zata k'wace min saurayi? To bari kiji abinda baki sani ba, Faruk saurayin Meenah ne bani ba, ko don kinga ina zuwa muna fira dashi kikayi tunanin saurayina ne?" Tayi murmushi tace
"To ba haka bane, ni kawai mun saba ne sheyasa kikaga ina fita amma lokuta da dama ay tare da Meenah muke zuwa, duk randa kika ga naje ni kad'ai to Meenah ta tura ni akan in je kafin tazo." Ta kalli Meenah dake hawaye wani na bin wani, tasa hannu ta share mata tace
"Daina kuka 'yar uwata, kiyi hak'uri da abinda Mami tayi miki, sannan kisa a ranki Faruk naki ne ke kad'ai kinji?"
Suka rungume juna suna kuka.
Haushi ya kashe Bilku kafin kuma sum sum ta fice daga d'akin cike da kunya!
A wannan daren Bilki batayi bacci ba, yadda taga rana haka taga dare.
Washe gari Meenah taga fushin Bilki fiye da yadda ta saba gani, da Zarah take sabgoginta, itama sai ta kama kanta a d'aki tak'i fitowa tana karance-karancenta. Sai dai zuciyarta cike take da tsoron Mamin, data tuna marin da tasha jiya sai gabanta ya fad'i.
*
K'arfe goma na safe Faruk yazo, Bilki na zaune parlor tana chanza channel, tun daga jin sallamarsa tabi ta d'aure fuska yadda bata ta6a yi masa ba. Yana zuwa ya zube k'asa yana gaishe ta, sai kawai ta kafa masa ido bata amsa ba, k'arshe ma sai ta mik'e ta haye bene zuwa d'akinta ba tare da tace komai ba. Meenah na daga bak'in k'ofar kitchen tana ganin komai, ita kunya ma ta kamata ta kuma kasa k'arasowa ciki. Sai da ta d'auki akalla minti biyu sannan tayi ta maza ta shigo parlon kanta a k'asa. Dukkansu sunyi shiru aka rasa mai fara yin magana a cikinsu.
Da k'yar Faruk ya daure yayi murmushi cikin basarwa yace
"Munyi ma Mami laifi ko?"
Ta d'an d'ago suka had'a ido, ta lumshe idanu tace.
"Tun jiya take haka, mun rasa gane mata."
Yayi shiru cikin tunani, can kuma yace
"K'ila bata amince dani ba..."
Tayi saurin cewa
"Bakomai zata huce ne."
Baba ne ya ke saukowa daga mattakalar bene Bilkin na biye da shi tana rik'e da briefcase d'insa, ya hango shi a parlor zaune, da sauri ya mik'e cikin girmamawa yabi bayansa don yaga kamar parlonsa ya nufa daga can 6angarensa.
Baba nakan kujera Faruk na gefensa daga k'asa. Bayan sun gaisa kamar kullum cikin mutunci da girmama juna, can Baba yace
"Umar Faruk."
Ya d'ago da fararen idanunsa ya dube shi yace
"Na'am Baba."
"Meke tsakaninka da Amina?"
Faruk ya rud'e ya shiga inda inda saboda yadda yaga Baban ya masa kwarjini, take kuma ya sadda kansa k'asa.

Monday, 10 July 2017
AUREN FANSA 21
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น21 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bayan kwana biyu da safe sai ga Baba ya diro garin wai da niyyar d'aukar su Meenah, hanakalin Meenah ya tashi don tasan da k'yar idan Mami zata barta tayi soyayya ba, tasan dai Baba baida matsala, amma Mami take ji. Aikuwa tana sanar da Faruk cewar gobe zasu koma Abuja yace shima zai tattara ya koma daman ya gama abinda ya kawo shi, sai ya koma zai cigaba da kawo mata ziyara.
Washe gari kuwa suka tattaro suka dawo gida.
Duk da hankalinta a tashe yake hakan baisa taji ko d'ar a zuciyarta game da son da takeyi wa Faruk Adam ba. A ganinta shi d'in yasan menene so, yasan darajar abinda yakeson, ya kuma iya tafiyar da shi ta hanyoyi daban daban, ya iya tarairaiyar mace da bata kulawa yadda ya kamata. Sheyasa son da take masa shi yake k'ara bata k'warin gwiwar fuskantar Mami.
Suna dawowa kuwa kusan kullum sai yazo, har dai ya zama d'an gida, yadda taga Baba ya amshi Faruk hannu bibbiyu ya sanya dole taja bakinta tayi tsit, kuma kullum yazo Zarah ke raka Meenah fira, hakan yasa ita kanta Mamin ta rasa gane wurin wa yake zuwa, amma tana fatan wurin Zarah yake zuwa, don a yadda take gani mutum ne mai kud'i sosai.
*
K'arfe takwas na dare kamar kullum Faruk ya isa gidansu Meenah, kasancewar ya zama d'an gida tsakanin Baba da Mami.
Bayan sun gaisa da Baba, a lokacin Baba yana da niyyar fita, haka ma Mami tana sama tana fama da lissafin kud'in kasuwancinta.
Yana nan zaune yana jiran Meenah. Aikuwa sai gata ta fito tayi kyau kamar kullum cikin material mai taushi silver da ratsin bak'i a jikinshi, d'inkin doguwar riga, d'inkin bai kama jikinta ba. Tun daga nesa suke sakarma da junansu murmushi mai sanyi. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa, centre table ne mai bak'in glass a tsakiya wanda aka d'aura kayan marmari cikin tray kala kala a cikinsa, irinsu Apple, grapes, banana, orange, pear da sauransu. Zamewa yayi ya zauna k'asa gami da rausayar da kai yace.
"Barka da hutu!".
Dariya ya bata sosai saboda yadda yayi maganar, tace
"Alhamdulillah, muna ta sha kam."
Yayi shiru zuwa wani lokaci sannan yace.
"Zuwa yaushe kike ganin za'a aurar da ke?"
Ita dariya ma ya bata tace
"Aure ay lokaci ne... sai lokaci yayi sannan."
Ya langa6ar da kai yace
"Haka ne, amma ni ko yanzu aka bani ke zan kar6a hannu bibbiyu, zan nuna maki k'auna ta ban mamaki, sai dai bansani ba ko ke zaki so ni kamar yadda nake son ki... sannan ina so idan Allah ya kaimu zan sanar da iyayenki cewar aurenki zanyi..."
Ta lumshe idanu cikin wata sabuwar k'auna dake k'ara mamayarta, ta kuma k'ara lallu6e mata zuciyarta, tace
"Kar kayi tantama a kaina ya Faruk, soyayyarmu had'in Allah ce, i respect you and your values.. Faruk d'in da nake so bana ganin kowa sai shi, bana jin k'aunar kowa sai shi... haka ma banida buri a yanzu sama da mallakarka a matsayin mijin aurena na har abada..."
Sai bayan ta furta hakan kuma kunya ta kamata had'e da mamaki, yadda ta zauna tayi ta zuba kamar pampo, amma daga baya sai take ganin kamar su6utar baki tayi. Sai tayi saurin cewa
"Nidai fatana ka rik'e soyayya ta, kada kaci amanata, ka yarda dani, idan kayi min wannan to ni kuma nayi maka alk'awarin baka dukkan kulawa."
Sai ya rasa abin cewa kuma, murmushi tayi ta sauko k'asa ta shiga yanka masa kayan marmarin yana sha.
***
Bilki ta soma tsarguwa da yawan zuwan Faruk cikin gidansu, da yawan ke6ewa da sukeyi shida Meenah akan Zarah suna fira. Ga wata sabuwar al'ada da Meenah ta 6ullo da ita na yawan kwalliya wadda ta gama lura don Faruk take yinta. Ta gigice ta shiga damuwa sosai, neman k'arin bayani takeyi tasan Zarah bazata ta6a fad'a mata ba saboda an ta6o 'yar uwarta haka bata ganin aibunta, su koda wani abin ne ba'ajin ta cikinsu kashewa sukeyi su rufe babu mai ji. Ko fad'a sukayi baya wuce yini d'aya idan kuwa sun dad'e to kwana d'aya ne sun shirya sun kuma manta komai. Don haka taga babu mafita illa ta tunkari Meenah tayi mata bayanin abinda take zargi.
K'arfe tara na dare ta raka Faruk ya tafi, tana dawowa ta taradda Mami tsaye gefen gadonta ta hard'e hanyayyenta wuri d'aya tana huci.
"Mami....?"
Ta dube ta sosai daga sama har k'asa tace
"Amina....!"
Bata amsa ba illa ta dube ta a yadda take kiranta cikin wata irin murya. Sai kawai ta jeho mata tambaya
"Meke tsakaninki da Faruk?"
Ta sunkuyar da kanta k'asa, batayi magana ba, sai da Bilkin ta daka mata uwar tsawa mai gigita k'wala.
"Bada ke nake magana ba?!"
Cikin sark'ewar murya tace
"Da...ma yace yana...so...na tun muna Katsina, kuma daman gobe ne Faruk d'in yake niyyar sanar daku muna son junanmu... mun yanke shawarar yin au..."
Ji kake tassa!!! Mami ta d'auke ta da wani irin wawan marin da har sai data ga giftawar wuta, ta nemi ji da ganinta ta rasa!

Sunday, 9 July 2017
AUREN FANSA 20
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to each and every reader, you always support me, and i am grateful for that! Thanks alot!❤️
๐น20 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Awa biyu tsakani ya diro cikin garin katsina, yana isa airport ya ciro wayarsa ya buga ma Meenah waya ya sanar da ita isowar tasa. Zarah bata gama shan mamaki ba sai da Meenah ta shiga kitchen don girka masa lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Coconut rice da miyar kaji, gefe kuma Russian salad ne, sai drinks kala kala. Banda su snacks da aka tanada. Goggo da k'amshi ya cika mata hanci ta fito daga d'aki ta lek'o tana fad'in.
"Kai lafiya me kuke dafawa?"
Zarah tayi dariya tace
"Ay Goggo surukinki ne zaizo, shine fa su Meenah ake ta shiri haka."
Meenah ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Goggo tayi dariya tace
"Ahh lallai kice munada babban bak'o, ay gara dai yayi yazo ko zamu huta hakan nan."
Bata gama komai ba sai da k'arfe bakwai harda rabi. Kasacewar yace mata da anyi sallar isha'i zaizo.
Tana gama wannan aikin ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin wani lace ruwan zuma (coffee brown) da light pink a jikinshi, d'inkin riga da skirt. Da taimakon Zarah ta d'aure d'ankwalin kayan irin na zamin da ake kira mai steps. Ga d'ankunne an sa kalar kayan. Tana gama fesa turare wayarta ta hau ruri da alama Faruk ya iso. A karo na farko taji ta gigice, kasancewar a yau zata ta6a fuskantar wani d'a namiji a rayuwarta da idanun soyayya. Bayan ta d'auka ya sanar da ita isowar tasa cewar yana bakin k'ofa. Ba yadda batayi da Zarah ba akan ta shigo dashi tak'i, harda zolayarta wai ay ba saurayinta bane ita. Hakan yasa ta d'auki waya ta tura masa da message akan yasa a shigo da shi bakin k'ofa (main entrance).
Tana bud'e mishi k'ofa suka bi juna da kallo mai kwantar da zuciya, kafin kuma dukkansu su saki murmushi mai d'auke da wani 6oyayyen sirri. Mamaki takeyi akan yadda yafi kyau a fili akan a hoto...
Ta kauce ta bashi hanya ya shigo, yanan sanye da shadda marar nauyi kalar sky blue sun kama jikinshi, idonshi mak'ale cikin farin glass wanda ya k'ara fito da cikar kamalarshi na cikakken namiji, wanda boko ya zauna masa sannan kud'i ma suka zauna masa had'e da hutu, ga kuma uwa uba kyau, ba abinda ke tashi a wurin kamar k'amshin turarensa mai sanyaya zuciya.
Meenah fa tayi nisa a kallonsa yayi murmushi ya soma karkad'a mata key d'in motarsa, taji kunya sosai ta wuce ciki kanta k'asa, yabi bayanta. Suka zauna kan kujeru parlon Goggo, da k'yar ta ce
"Ya hanya? Ya kuma gajiya?"
Yayi k'awataccen murmushin dake fizge zuciya yace
"Alhamdulillah, ya gida ya hutu?"
Tayi murmushi still bata d'ago kanta ba tace
"Komai alhmdulillah, yasu Anisah?"
Yace
"Suna can lafiya lau, ina Goggo da Zarah?"
Kafin tayi magana Zarah ta fito da k'aton tray mai d'auke da lemo kala kala da cups d'in glass guda biyu. Sai data dire bisa center table d'in dake parlor sannan ta zauna suka gaisa a mutunce, yace
"Ga Zarah nan kenan? Itace sweet sister d'inki. Sannu Zarah ya kike? I've heard so much about you, gaskiya sister nan taki tana ji take."
Zarah tayi dariya
"Haka ne, nima ina ji da ita ay."
Tana gama fad'an haka ta mik'e tsaye ta fice. Ba'a juma ba kuma ta dawo d'auke da wani tray d'in mai d'auke da kuloli guda biyu, plate biyu sai kuma bowl na snacks da salad. Bayan ta dire sum sum ta fice saboda yadda taga sun kasa 6oye soyayyar da ke zuciyoyinsu a gabanta.
Ta lek'o don zuwa kitchen had'o tea, daman ita Zarah al'adarta ce duk dare sai tasha ruwan lipton (green tea) kafin ta kwanta, nan ta hango su suna cin abinci a plate d'aya, sai kuma sukayi mata kyau, kuma sun mugun dacewa da juna, abinda Faruk zai nuna ma Meenah shine haske fata don shi fari ne nesa ba kusa ba, Meenah kuwa bak'a ce (chocolate color). Suna cin abincin suna kallon juna, fatar bakinsu kuwa kad'an take motsi daga lokaci zuwa lokaci. Ta koma d'aki tana mamaki sai kace ba Meenah ba, gaba d'aya ta fad'a tarkon so.
Kafin ya tafi ya d'auko kyauta gift d'in turare da agogo ya bata, amma sam tak'i kar6a, sai da yayi da gaske har yana neman yin fushi sannan ta kar6a tana godiya sosai.
Soyayya tsakanin Meenah da Faruk kullum abin dad'a gaba yake cike da salo na ban mamaki, basu iya yini d'aya basuyi waya ba, haka ma kullum yana kan hanyar zuwa wurinta.
Tabbas zuwa yanzu soyayyar da Meenah ke ma Faruk bata misaltuwa, abin mamaki Faruk ya iya tafiyar da soyayya yadda ya kamata ya kuma son hanyoyi daban daban na yadda zai jawo hankalinta gare shi, ga yaci sa'a wannan shine karo na farko data fara sanin yadda ake soyayya, sheyasa a halin yanzu duk wanda zata so zata soshi ne da dukkan zuciya da kuma ruhinta. Faruk ya riga da ya saye zuciyarta farat d'aya, ko irin kalaman da yake furta mata kad'ai ya isa ya saye zuciyar Meenah, don haka sheysa bai sha wahalar yiwa zuciyar Meenah kamun kazar kuku ba!
Batada wani tunani sai na Faruk, batada wani ra'ayi sai nasa, sannan batada wani buri sai na mallakarsa a matsayin mijinta na abokin rayuwa na har k'arshen rayuwarta ba.

Thursday, 6 July 2017
AUREN FANSA 19
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น19 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Tun kafin ta kai ga d'auka haka kawai ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, ta kira sunan Allah don neman nutsuwa cikin zuciyarta. Cikin ikon Rabbi kuwa ta samu nutsuwa sai dai kafin ta d'auka tuni wayar ta katse. Ajiyar zuciya tayi, sai dai tana katsewa wani kiran na shigowa.
"AssalamuAlaiki yake ma'abociyar kyau, kwarjini da kuma nutsuwa."
Abinka da rashin sabon waya da maza, tuni ta rasa nutsuwarta, da k'yar ta amsa masa
"Wa'alakumsalam."
"Yau dai na taki sa'a tunda har aka d'auki wayata sannan aka d'aga lokacki d'aya, lallai ni mai babban sa'a ne. Ko ba haka ba 'yan mata?"
Ta k'ara kiran sunan Allah a karo na biyu, saboda rashin sabo da kuma muryar mutumin da bata san ko waye ba, sai dai me? Jin muryar takeyi kamar ana busa sarewa, bata ta6a jin murya mai dad'i ba irin ta wannan mutumin ba...
"Ya kikayi shiru Princess?"
Gabanta ya yanke ya fad'i, wai wannan mutumin kamar aljani? Da yayi mata magana sai gabanta ya fad'i.
"Nidai muryar nan taki ko dai zan biya ne don na lura tana tsada..."
"Ina wuni?"
Yayi murmushi, har tana jiyo sautin yana bugun dodon kunnenta, sannan a take tsikar jikinsa ta tashi tayi wani yarr!
"Kina lafiya?"
"Lafiya lau."
"To masha Allah, zan d'an baki dan gajeren labarina, bana so ki zo kina ce min bakisan ko da wa kike waya ba... ko ba haka ba?"
Tace
"Uhm."
Yace
"Yauwa, da farko sunana Faruk Adam, shekarata 26 kacal a duniya, iyayena sun rasu gaba d'aya tun ina k'arami, yanzu daga ni sai k'anwata muka rage, ina zaune gidan wani uncle d'ina a garin Abuja. Mahafiyata shuwa ce while babana fulani ne. Yanzu dai na kammala karatuna ina aiki. To kinji kad'an daga cikin tarihin rayuwata, ko zan iya jin naki?"
Tace "uhm, Allah ya jik'ansu."
Yace
"Amin, ina jinki fa."
Da k'yar ta iya tattaro nutsuwarta wuri d'aya ta soma magana mai cike da nutsuwa.
"Sunana Amina Hamza, mahaifina d'an garin Katsina ne amma yanzu aiki ya kai shi Abuja, na kammala karatuna na fita daga secondary ina jiran admission zan tafi university. Mu biyu ne kad'ai a gidanmu daga ni sai k'anwata mai suna Fatima."
Yayi murmushi
"Allah sarki Allah ya taimaka, to baki fad'a min shekarunki ba?"
Tace
"16."
Yace
"Wow, lallai ashe dai da sauranki yarinya."
Tayi murmushi mai cike da kunya.
Haka suka 6ata wannan daren Faruk na janta da fira, tun tana d'ari d'ari har ta d'an saki jikinta tana bashi amsa, idan akayi labarin dariya suyi dariya, daga k'arshe ganin har uku na dare ya sashi yayi mata sallama akan zai kirata da safe.
Koda ta kwanta kasa bacci tayi, muryarsa kawai takeji cikin dodon kunnenta kamar yanzu yake mata magana.
Daman bata sallah sheyasa ma bata tashi da asuba ba. Bacci takeyi har kusan goma da rabi na safe.
Juyi d'aya tayi akan gado tayi tozali da wayarta kamar had'in baki sai kuma ta fara ruri. Ganin number d'in jiya ya sata sakin murmushi ba shiri.
A kasalance ta d'auka gami da yin sallama.
"Good morning! Rise and shine, raina ya bani yanzun nan kika farka daga bacci, ko da yake laifi nane dana hana ki bacci da wuri tun jiya ko? To ayi min afuwa. Bazan sake ba."
Cikin ranta tace
"Wannan sai kace aku ko gajiya baiyi da magana?"
"Ina kwana?"
Yayi murmushi
"Lafiya lau da fatan princess d'in tawa ta tashi lafiya?"
Ta langa6ar da kanta gami da lumshe idanu tace.
"Alhamdulillah, thanks."
Yace
"Yauwa, to yanzu abinda ya kamata kije kiyi wanka sai kici abinci."
"To." Kawai tace gami da yi masa sallama ta kashe wayar. Ganin Zarah tsaye bakin k'ofa ya sa gaban Meenah ya yanke ya fad'i. Zarah ta k'araso tana dariya
"Love in the air, yanzu don Allah bakiji dad'i ba? Amma ace mutum ya takura ma kansa da rayuwar kad'aici haba!"
Murmushi tayi ta sauka daga kan gadon tace
"Bari nayi wanka."
Tana jin Zarah na d'aga murya tana fad'in
"Wai don dai kar ayi maganar zaki wani shige wanka."
Murmushi kawai tayi.
Wunin ranar zungur a d'aki tayi shi, har dare bata fito ba, ba abinda ke tashinta daga gado sai shiga toilet.
Washe gari kuma haka ta tashi sukuku. Zarah ta rasa gane kan yayar tata.
Haka dai komai ya cigaba da gudana a tsakanin Meenah ta Faruk, wuni sukeyi mak'ale a waya, zuciyarta ta aminta da shi lokaci guda, ta yarda ta amince shi d'in takeso. Tun da ya turo mata hotunan sa taji yayi mata, lokaci guda ya sace zuciyarta ya kuma tafi da imaninta gaba d'aya, har ta soma cewa cikin ranta
"Anya ba surk'ullensu na fulani yayi mani ba?"
Wata rana da daddare yana ta kiranta ya sanar mata gobe zaizo wurinta, daman sunyi zaizo Katsina, idan yazo zai shigo su gaisa. A lokacin da yake ta kiranta tana bacci kuma wayar a silent take.
Washe gari da safe sai ta iske message d'insa ya turo mata.
"Just to say good night! With you in my mind... ?"
Sai tayi murmushi ta tura
"In both the soul and mind...."
A lokacin da ta tura masa sak'on bai gani ba saboda yana cikin jirgi don tahowa Katsina!

AUREN FANSA 18
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น18 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
***
Kwanci tashi babu wuya wurin Allah har su Meenah sun gama zana exams d'in k'arshe. Ranar da suka gama Baba yayi musu kyauta mai tsoka sannan ya musu alk'awarin tafiya Katsina hutu. Murna a wurin Meenah ba'a magana, daman tafison can saboda can tafi sakewa tayi abinda takeso, babu mai takura mata.
Haushi Bilki kamar zata fashe, daman duk sadda zasu je Katsina hutu sai hankalin Bilki ya tashi a cewar ta mai mata ayyukan gidan bata nan.
Akan dole takeyi har sai sun dawo.
A tsarin hutun sati biyu zasuyi inji Baba, don haka tun ranar Meenah ta fara shirin tafiya. Ta wanke kayanta ta goge.
Ranar da zasu tafi tunda asuba ta tashi, bayan tayi wanka ta d'auko cikin sabbin kayanta na wata sallah ta saka, blue atamfa d'inkin riga da skirt, tayi kyau sosai.
A lokacin data sakko k'asa ta iske Baba da Zarah suna karyawa, yana ganinta yace.
"Maza zo kici abinci mu kama hanya."
Da saurinta kuwa ta taho tana murmushi.
Bayan sun kammala, Hassan mai gadinsu ya shigo ya fara fitar musu da kayansu yana sakawa boot.
Bilki ce ta sauko tana yak'e, tace
"Badai tafiyar bace?"
Baba yayi dariya yace
"Itace yanzu zamu kama hanya ma."
Ta had'iye 6acin ranta tace
"Wai tun yanzu Alhaji?"
Sai da yayi murmushi yace
"To idan bamu tafi yanzu ba sai yaushe zamu tafi? Katsina fa ba nan ba."
Tace
"Hakane kam, to Allah ya tsare ya kaiku lafiya."
Yayi murmushin jin dad'i yace
"Amin."
Bayan gama ban kwana, Alhaji ya d'auki hanya zuwa Katsinan Dikko.
Sai can yamma suka isa, da gudu su Meenah sukayi ciki suna zuwa suka haye 'yar tsohuwar dake zaune tana hutawa a parlor.
"Kai kai zaku 6alla ni ne?"
Sai kuma tayi murmushin jin dad'i
"Ahh Aminatu da Fatsima ne? Saukar yaushe?"
Meenah tace
"Yanzun nan muka iso, ina wuni Goggo?"
Tace
"Lafiya lau, ina Baban naku."
Meenah tace
"Yana waje yanzu zai shigo."
Bata rufe baki ba ya shigo.
"Lale maraba da Hamza."
Yayi dariya tare da zama k'asa yana kai gaisuwa zuwa ga mahaifiyar tasa.
"Mun same ku lafiya?
Tace
"Alhamdulillahi, ya aiki?"
Yace
"Alhamdulillah, ya k'arfin jiki?"
Tace
"Sai godiyar Allah."
Yace
"Allah k'ara lafiya, daman yaran suka kammala makaranta shine na kawo suyi maki sati biyu, naga sun kwana biyu basu zo ba, ni kuma gobe in Allah ya yarda zan juya."
Tace
"Kai masha Allah! Allah ya bada sa'a."
Suka amsa da "Amin."
BAYAN KWANA BIYAR.
Kamar kullum bayan Meenah ta sanya kayan baccinta riga da wando kalar dark pink, tana shirin kwanciya Zarah dake kwance tana latse latse a wayarta ta ajiyewa wayar gami da kiran sunanta.
"Meenah..."
Ta kalle ta gami da yin murmushi tace
"Na'am Zarah."
Jingina Zarah tayi jikin bangon gadon da take kwance tace
"Meenah wai meyasa kika k'i sauraron wannan mutumin? Nafa lura kamar sonki yake da gaske."
Take annurin fuskarta ya 6ace 6at! Ta d'aure fuska tamau gami da gyara zamanta kusa da Zarah.
"Wane mutumi kenan?"
A iya sanin Zarah babu wanda ke takura mata kamar wani wanda ke yawon matsa mata wai ya had'u da ita a Instagram!
"Haba mana Meenah, kinfa san wa nake nufi."
"Ay ni bai furta man cewar yana sona ba..."
Ta fad'a gami da jawo wani novel na turanci mai suna Behind the clouds ta soma bud'ewa tana k'ok'arin karantawa.
Zarah tayi ajiyar zuciya tace
"Bafa kyau wulak'anci, ki daure ko yaya ne ki sauarare shi."
Meenah ta ajiye littafin tana mai kallon Zarah tace
"Zarah duk duniya banida aminiya sama da ke, ke kanki kinsan cewa soyayya bata cikin ra'ayina a yanzu, ban iya bama bansan ya take ba, ban kuma san ta ina zan fara ba, nifa tun farko sheyasa nace miki kar ki bud'e min irin wad'annan abubuwan kika k'i ji Zarah, yanzu ga irin ta nan, daman abinda nake gudu kenan."
Zarah ta kalle ta da mamaki tace
"Me kike gudu?"
Meenah tace
"Samarin zamani mana, 'yan k'arya mayaudara, ina tsoron ayi min wasa da feelings d'ina, sheyasa ma kikaga ina tsoron yin soyayya..."
"Ay ba duka aka taru aka zama d'aya ba, idan kikayi sa'a sai kiga kin samu mai sonki da gaske..."
"Zarah da kinyi hak'uri kin k'yale ni bazan iya yin soyayya yanzu ba..."
Ta fad'a tana k'ok'arin cigaba da karatunta ranta idan yayi dubu to ya 6ace.
"Bazan tilasta miki ba, amma ina rok'onki ki bashi chance idan kikaga alamar mayaudari ne basai ki rabu dashi ba? Menene a ciki? Ni wallahi haka nan kawai yake bani tausayi kullum cikin damuwa yake da ke, ina laifin me sonka? Koda bai furta miki kalmar so yanzu ba, to na tabbata zai furta maki nan bada jimawa ba! Haba Meenah bansanki da wulak'anci ba..."
Ta d'aga mata hannu
"Ya isa Zarah, naji na amince zan bashi chance, shikenan?"
Zarah tayi murmushi
"Shikenan, kiyi karatunki sai da safe."
Tayi murmushi
"Allah ya kaimu lafiya."
Gajiya tayi da karatun ta d'auko wayarta gami da duba lokaci. K'arfe 12:53am, ajiye littafin tayi tana k'ok'arin kwanciya message ya shigo ta wayarta.
Tasan bai wuce d'an k'wak'war nan, ta fad'a a cikin ranta gami da sakin d'an guntun tsaki.
Dubawa tayi.
"Hello."
"Hey."
"No answer?"
"How are you dear?"
"Hmm."
"Are you sleeping?"
"Please talk to me mana."
Da k'yar tace
"Hi."
Yana kwance yana latse latse a laptop nasa message nata ya shigo, ya ware manyan idanunsa cike da mamaki, murmushi yayi ya rubuta mata.
"Thank God! Naji dad'i da kika man reply, i thought na maki wani laifi ne?"
"A'a bakomai..."
"So ya kike? Kin dai hanani number ki ko?"
"Hmm."
"Bakomai kina min rowan jin muryarki mai dad'i ko?"
"A'ah..."
"To ki bani mana, idan ba rowa ba."
Yau yaci albarkin Zarah, don haka sai kawai ta tura masa number d'in.
Minti biyu tsakani...
Kwance take lamo, zuciyarta na mata sak'e sak'e. Bata ankara ba wayarta ta fara ruri, bak'uwar number ta gani. Da k'yar tasa hannu ta d'auka....

Wednesday, 5 July 2017
AUREN FANSA 17
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to Kiddies friends 4ever, thanks for the support you are special to me! Love you guys❤️
๐น17 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
D'aya bayan d'aya yake duba hotunan dake baje a gabansa, sai daya d'auki lokaci kad'an yana analyzing ko wanensu duk Usman yana kallonsa. Sai da ya gama sannan ya d'ago yana kallon Usman yace.
"Nagode, sai kayi min bayaninsu."
Usman ya gyara zama yace
"Yalla6ai ka duba wannan takardar na rubuta komai amma duk da haka zan maka bayani da baki.
"Da farko hotunan nan sai da nayi k'wak'waran bincike akansu kafin nazo nan."
Hoto d'aya ya d'auko ya mik'a masa.
"Wannan sunansa Alhaji Hamza Umar, haifaffan d'an garin Katsina ne kafin ayi masa transfer zuwa nan Abuja. Wannan kuma matarsa ce Hajiya Bilkisu, yaransu biyu kacal duka mata. Babbar itace Amina wadda suke kira da Meenah ga hotonta nan, sai k'aramar wadda babu wani tazara a tsakaninsu mai suna Fatima Zarah. Duk wad'annan hotunan sai da nayi bincike na gano account name d'in d'iyarsa mai suna Zarah duk a nan na kwaso hotunansu, ita Meenah a nata account d'in babu hoto ko k'wara d'aya, hartta handle d'insu yana nan a rubuce a jikin takardar.
Sai ita d'ayar mai suna Hajiya Layla ita tana Kaduna da zama da mijinta mai suna Alhaji Sambo, sai d'iyarta k'wara d'aya mai suna Yasmeen."
Gwauron numfashi Faruk ya sauke a lokaci guda kuma ya d'auko hotunan yaran nasu da akayi masa nuni dasu yana ta kallonsu yana juya hotunan. Aje hotunan kuma yayi yana kallon Usman tare da d'ora hannayensa saman table d'in yace.
"Good job, so anything else?"
Usman ya cigaba
"Yes, makaranta d'aya suke zuwa mai suna Turkish, ita babbar tana k'ok'arin kammala karatun nata ne while ita k'aramar wato Zarah tana SS2 a yanzu. Duk weekend suna zuwa Katsina wurin mahaifiyar Hamzan mai suna Hajiya Fatima.
Idan suka je kamar misali ranar Juma'a zasu dawo ranar Lahadi, amma yanzu bincike ya nuna mani cewar sunyi akalla sati biyu basuje ba, sakamakon jarabawa da d'iyar Alhaji Hamza take shirin zanawa ta fita daga secondary.
Alhaji Hamza yakan d'auki yaranshi su fita yawon shak'awatawa duk ranar Alhamis da daddare."
Ajiyar zuciyar ya sauke yana kallon Usman ya kuma cewa
"Anything else?
"Yawwa, ka tambaya ina da ina suke zuwa, to a zahirin gaskiya yaran Alhaji Hamza basa fita yawo, daga makaranta sai islamiyya, amma daga nan basu cika zuwa ko ina ba. Amma kayi hak'uri a 6angaren Hajiya Layla sai na k'ara bincike don bansamu wani information sosai ba, na dai gano cewar tana yawan fita Dubai saro kaya."
Faruk yace
"Nagode, ka manta ka sanar dani aikin da sukeyi fa."
Usman yace
"Sorry sir, Alhaji Hamza ma'aikacin banki ne, amma matarsa bata aiki tana harkar kasuwanci, wanda naji ance tana da gidajen mai, shaguna, mall, tana da k'aton shagon saida saide, da sauransu.
Haka zalika Alhaji Sambo shi d'an kasuwa ne kuma yana aikin gwamnati."
Ya saki ajiyar zuciya yace
"Nagode da taimakon da kayi min duk da akan aikinka ne amma ni ka taimake ni ba kad'an ba, so nagode Allah saka da alkhairi."
Usman yayi dariya
"Haba yalla6ai menene na godiya? Ni keda godiya ay."
Faruk yace
"Bakomai Usman zaka iya tafiya."
Daga haka ya amsa da "To." Sannan yayi masa sallama ya fita.
Yana fita ya saki murmushin da shi kad'ai yasan mana'arsa.
Murd'a k'ofar akayi aka shigo, Najeeb ne, da murmushi Faruk yace
"Ka shigo mana."
Bayan ya zauna ne Najeeb ya soma magana
"Ka bani mamaki Faruk, ban ta6a tunanin haka daga gareka ba..."
Gaban Faruk yayi mummunan fad'uwa, yace
"Me akayi?"
Najeeb yace
"Yanzu daman abinda kake shiryawa kenan baka sanar dani ba? Inda banji me kuke cewa ba da bazaka ta6a fad'a min ba ko?"
Faruk yace
"Ko kad'an ba haka bane, naso ace sai na gama duk abinda ya kamata sai na sanar maka..."
Najeeb yace
"To tunda yanzu naji sai ka fad'a min komai."
Faruk yayi dariya yace
"Akan dai maganar nan ce ta kwanakin baya."
Najeeb yace
"Maganar iyayenka ko?"
Faruk yace
"Eh ita, so wani d'an bincike nasa aka yo mani akan mutanen kuma an kawo."
Ya k'arasa yana mik'a masa hotunan.
Najeeb ya duba bayan ya gama yace.
"Ok to menene next move naka?"
Faruk yayi murmushin nasa da ya saba yi masu ma'ana daban daban yace
"Zan sanar da kai komai, yanzu muje muyi sallah mu dawo."
Najeeb yace
"Ok muje."
A tare suka mik'e suka fice daga office d'in.
***
Yana shiga d'akin nasa ya jiyo k'amshin turaren wuta mai dad'i, ga sanyin ac gaurewa da d'akin. Yasan baya wuce aikin Jidda, don ya lura tunda suka dawo take faman d'wainiya dashi, bakin gado ya zauna ya shiga cire takalminsa da safa, bai kai ga gamawa ba ta shigo d'akin nasa, hannunta d'auke da tray d'in ruwa da lemon kwali 5alive, a d'an k'aramin table ta ajiye ta d'ago tana kallonsa cike da kunya, tace
"Sannu da zuwa yaya."
Yace
"Yawwa sannu da aiki."
Tace
"Yawwa, kana buk'atar wani abu?"
Ya d'an karkato gami da kallonta yace
"A'a nagode."
Daga haka ta fice daga d'akin a yayinda shi kuma ya fad'a toilet don watsa ruwa.

AUREN FANSA 16
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น16 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
***
Tsaye take a gaban wardrobe tana gyara zaman skirt d'inta, duk da kayan dake jikinta sun mata kad'an hakan bai hana ta yin kyau ba, ji tayi an rungume ta ta baya, tasan baya wuce aikin Zarah.
"Auch! Haba mana Zarah so kike ki k'arasa ni ne?"
Zarah tasa dariya, tace
"To sarkin fad'a, yanzu dai maida wuk'ar albishir nazo miki dashi." Meenah ta juyo da murmushi saman fuskarta tace
"Ina jinki."
Zarah tace
"Fari ko ja?"
Meenah tace
"Fari k'al ma kuwa."
"Baba yace nayi WAEC d'ina yanzu idan naci mu tafi university tare!"
Zarah tace cike da murna. Meenah farin ciki ta rasa ina zata sa ranta, dama ta dad'e tana addu'ar su tafi university tare da Zarah, sai dai tasan Baba ne ya hana yace bazatayi ba sai ta kai SS3, amma yanzu ko ya akayi ya yarda? Meenah tace
"Amma ya akayi ya yarda?"
Zarah tace
"Wallahi ikon Allah, kuma fa ba tambayar sa nayi ba, shi da kansa ya kirani yace na shirya yin exam tare da ke."
Meenah cike da murna tace
"Lallai ikon Allah, Allah yasa kici."
Zarah ta rungume Meenah tana murna tace
"Amin sisi."
"Kai meye kun cika ma mutane kunne da hayaniya?"
Cewar Bilki daga bakin k'ofar d'akin tana tsaye, fuskarta ba yabo ba fallasa.
Sukayi tsit, ta kuma daka musu tsawa
"Ba da ku nake ba?"
Zarah tace
"Da... dama, Baba ne yace za... zan iya tafiya university tare da Meenah..."
Take ta washe baki kamar ba ita ba, tace
"Allah d'iyar Baba? Yaushe ya yarda?"
Tace
"D'azu kafin ya tafi wurin aiki."
Bilki tace
"Alhamdulillah, yayi daidai Allah ya bada sa'a sai ki dage, tun kafin ace bakida k'ok'ari, ko kuma ace wasu sun fiki."
Ta k'arasa tana ma Meenah wani irin mugun kallo. Duk sun san abinda take nufi kuma hakan ya sosa ransu.
"Ke! Meenah zo ki matsa man k'afa ta."
"Mami zan taya ta."
Wani kallo ta watso mata na irin kika k'ara magana sai na kakkarya ki sannan ta fice. Meenah ta dafa ta tana fad'in.
"Don Allah Zarah daga yau ki daina cewa zaki taya ni idan tasa ni aiki, wallahi fad'a kike ja man duk sadda kika fad'i haka."
"Uhm." Kawai Zarah tace, daga haka Meenah ta juya da sauri zuwa sashen Mami.
Da sallama ta shiga, zaune take kan wata
kujerar hutawa ta baje k'afafuwanta ma'ana ta mik'ar dasu saman kujerar, tana faman danne danne a wayarta k'irar iPhone 7plus, tana zuwa ta durk'usa har k'asa tace
"Gani Mami."
Sai data samu tsarabar harara sannan tace
"Meya tsaida ki tun d'azu nake zaman jiranki?"
Bata ce komai ba kanta na k'asa dai.
"Sai anyi magana kiyi sum sum da kai kamar mutuniyar arzik'i..."
"Kiyi hak'uri Mami, wallahi ban tsaya yin komai ba nan na taho."
Tayi tsaki gami da mik'o mata k'afa.
"Ni matsa man k'afata, kuma saura kiyi mani mugunta irin na rannan wllh sai na yi maganinki, don yau sai dai a kaiki asibiti don sai nayi miki lis!"
A hankali take matsa mata cikin lalla6awa, sai kuma ta sakar mata k'wanya a kai.
"Ke bakida hankali ne? Ya zaki dinga mani abu kamar susar k'adangare?"
Sai ta hau yi da d'an k'arfi, nan ma ta kai mata wanda yafi na d'azu zafi.
"Yau ga muguwa! Zaki 6alla min k'afa ne?"
Ta rasa yadda zatayi, mistake kad'an sai taji k'wanya mai shegen zafi a kanta.
Da daddare tana kwance ita dai abin duniya yabi ya dame ta, zuwa yanzu ta yarda ta amince ba Mami ta haife ta ba, ta yarda Baba ne babanta amma sam ta kasa yarda Mami ce ta haifeta. To ina mahaiyarta? Ta rasu ne ko tana raye? Ko kishiyar Mami ce? Kullum ire-iren wad'annan tambayoyin sune suke mata yawo a cikin kai, kuma har yanzu ta rasa amsa. Daga k'arshe ta yarda ta amice mahaifiyarta ta rasu kuma kishiyar Mami ce kawai. Wasu zafafan k'walla suka zubo mata, ita kam batasan dad'in uwa ba, bata san ya ake ji ba idan mutum na tare da mahaifiyarsa.
Sama sama tayi bacci gudun makara saboda ga aikin gida ga kuma shirin makaranta.
Da asuba ta mik'e bayan ta gabatar da sallar asuba tayi wanka, ta yi aikin gidan kamar kullum, ta had'a kalaci, d'aki ta wuce ta sanya uniform d'inta da basu samu guga ba, bayan ta gama shirinta tsab ta fito don ta karya, tana bud'e kular abinci sai ta ganta wayam! Nan ta hau dube dube amma kaf ba komai a ciki.
Mami ce ta sauko cikin kayan bacci da d'aurin gaba tana zuwa tabi Meenah da mugun kallo, ta wuce kitchen. A ranar haka nan ta hak'ura da kalacin daman sun makara, sauk'inta ma Baba ya basu kud'in makaranta da batasan ya zatayi ba.
***
BAYAN KWANA BIYU
Da sallama ya shigo office d'in, yana zaune yana fama da aiki kamar kullum, d'ago da fuskarsa yayi yace
"Shigo mana Usman."
Sai da ya kammala abinda yakeyi sannan ya maida dubansa ga Usman dake zaune d'auke da wata babbar brown envelope.
"Yalla6ai daman akan aikin da kasani ne, to Alhamdulillah na kammala maka komai shine na kawo maka ka gani."
Da sauri ya d'ago yana duban Usman yace
"Da gaske ka kawo duk abinda nake buk'ata?"
Usman yana murmushi sosai yace
"K'warai kuwa gasu."
Ya sa hannu ya zazzaro wasu hotuna guda biyar ya dire a gabansa, sannan ya fiddo wani dogon paper mai rubuce rubuce a samanta....

Monday, 3 July 2017
AUREN FANSA 15
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น15 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Ba'a fi minti biyar ba suka kunno kai, ko wanensu yana tura trolley nasa, tunda suka fito Jidda ke kallonsa ya za'ayi ta mance da wannan fuskar?
Ya chanza gaba d'aya ya zama wani babba, k'irar jikinsa kansa abin kallo ce irin giant
d'innan, abinka ga fari sai ya k'ara murjewa ya zama bature sak! Ta kalleshi yana murmushi.
"Sannu da zuwa yaya!" Anisah ta ruga tare da mak'alk'ale shi, a yayinda Yusra ke mak'ale da nata ya'yyen, sai a lokacin Jidda ta dawo duniyar tunani.
Da k'yar ta daidai nutsuwarta tace
"Sannunku da zuwa!" Ko alama bai gane ta ba.
"Yauwa sannu... Jidda ko?"
"Wow haka muryarsa take?" Ta fad'a tana k'ara kallonsa cike da mamaki. Tace
"Eh nice yaya."
"Wow duk kun girma..."
Suka taya su jan kayan nasu har bakin mota. Tafiya suke amma idonta na kansa. Abu d'aya take maimaitawa a zuci...
"What kind of change is this?"
Haka aka loda kattunan jakunansu a boot.
Koda suka shiga mota shi ya zauna gaba, daga baya babu abinda Jidda keyi sai aikin kallonsa.
"Ya Faruk? Ya Faruk? Ya Faruk?" Wannan abu shi take ta fad'i a ranta. Ta d'an k'ara kallonsa ta baya, gashin kansa kad'ai abin kallo ne, ya k'ara kyau akan wanda yake dashi da, sai shinning yake kamar taurari a sama...
"Anya bayada iri da larabawa?"
"Wa kenan?"
Ta kai dubanta tana kallon Najeeb daya tsareta da kallon tuhuma, tace
"Uhm uhm bangane ba."
Nabeel yace
"Rabu da ita tun d'azu na lura da yadda ta chanza."
Tace
"Na chanza kamar ya?"
Najeeb yasa dariya.
"Kamar yadda kika fahimta."
Daga nan ba wanda ya tanka har suka iso gida.
Mama harda d'an gudunta tana fad'in
"Welcome home."
Suka shiga parlor Najeeb ya kalli matan yace
"Ku kai mana kayanmu d'aki."
Sannan ya maida kallonsa da Mama.
"Bari mu d'an watsa ruwa muyi sallah."
Mama tayi murmushi
"Eh hakane lokacin sallar azahar yayi ya kamata ayi sallah sai aci abinci, sannunku da hanya."
Nabeel yace
"Yauwa Mama, ina Dada?"
Tace
"Yana Ireland yau satinsa d'aya da tafiya, amma insha Allah ya kusa dawowa."
Najeeb yace
"Ok... hakane munyi waya yake fad'a min batun tafiyar tasa Allah ya dawo dashi lafiya."
Aka amsa da "Amin"
Daga haka kowa yayi hanyar d'akinsa.
Faruk d'akinsa ya burgeshi yadda yayi tsab sai k'amshi da sanyin ac ke ratsa dukkanin illahirin jikinsa, bai tsaya wata wata ba ya fad'a toilet.
Yana gamawa ya saka k'aramar riga da dogon wando.
A dinning aka hallara kowa yayi serving kansa jollof d'in shinkafa, da pepper soup, sai kaza gasassa sai salad.
Sun fara cin abincin ne Mama tace.
"Alhamdulillah, Allah na gode maka daka nuna man wannan ranar, ranar da 'ya'yana suka kammala karatunsu lafiya, fatana Allah ya albarkaci karatunku, Allah ubangiji ya baku sa'a."
Gaba d'aya sukace "Amin amin."
Ta cigaba
"Yanzu dai ga Likita Najeeb, ga Detective Faruk, ga kuma Banker Nabeel, kai masha Allah! Allah yayi albarka."
Suka ce "Amin Mama mun gode Allah ya saka da alkhairi."
Tace
"Amin, yanzu dai ya kamata kuyi settling kowane ya nemi mata yayi aure, shine kad'ai abinda ya rage."
Duk kansu k'asa basu ce komai ba, itama Mama murmushi tayi a haka suka cigaba da cin abinsu.
***
Bayan Wata D'aya...!
Zaune yake kan kujerar office d'insa yana faman dube dube a computer d'insa, aka shigo da sallama, a hankali ya d'aga ido ya kalli k'ofa yayi murmushi.
"Ah Usman! Shigo mana ya zaka tsaya a bakin k'ofa?"
Ya k'araso yana gaishe shi
"Ina wuni sir?"
"Lafiya lau zauna magana zamuyi."
Bayan ya zauna, Faruk ya soma magana.
"Wani aiki zan saka, don Allah ina so duk abinda nake nema ka yi k'ok'ari wajen ganin ka samo min duk wani abu zan buk'ata."
Usman yace
"Insha Allah, ay ba yau ka fara sani aiki ba, kuma duk lokacin da kake sani abu ina k'ok'ari waje ganin na gano maka koma me kake nema."
Faruk yace
"Haka ne, to yau ma ina tafe da wani aikin mai matuk'ar mahimmanci a wurina."
Ya fad'a yana fiddo wani abu a cikin drawer d'in table d'insa.
"Karanta kaga."
Da ladabi ya kar6a ya soma karantawa. Bayan ya gama yace
"Yalla6ai amma suna ne kawai nake gani."
Faruk yayi wani d'an guntun murmushi yana juya kujerar da yake zaune akai. Sai da ya d'auki tsawon mintina biyu zuwa uku sannan ya soma magana.
"Eh sunaye ne na mutum biyu, bincike nake buk'ata akansu."
"Toh yalla6ai."
"Yawwa, i want every bit of information regarding them. Ina buk'atar komai idan nace komai i mean everything. Wane gari suke? Wace unguwa? Sunada 'ya'ya? Guda nawa ne? Suna da miji? Meye sunansa? Wane aiki yake? Ina da ina suka fi zuwa? Wace makaranta yaransu suke? Don't left out anything, including their photos."
Usman ya gyara zamansa yana fuskantarsa.
"Angama amma yalla6ai meyasa kake neman information d'innan haka? Sannan ta ina zan samo hotunan su?"
Faruk ya mik'e tsaye tare da dawowa gaban Usman gami da zama saman table a kusa da shi yace
"Usman bana son shishigi, aiki na saka shi zakayi min, kawai kaje ka kawo min abinda na saka please banda wasa, sannan hotunansu wannan kai zaka nemo."
Usman yace
"Hakane insha Allah zanyi k'ok'ari."
"Yauwa kana iya tafiya."
Daga haka ya fice, inda Faruk yayi murmushi yace.
"This is my first step towards my goal, waiting for the next step."
Yayi murmushi yana kad'a kai.

AUREN FANSA 14
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to Susu, thank you for everything!❤️
๐น14 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bakajin komai a d'akin sai k'yalk'yatar dariya, da k'yar suka dakata, Laila ce ta soma magana.
"Shegiyar gari, wato kina nan kina facaka cikin dukiya, kina nan kina taka matsayin da kika d'ad'e kina burin takawa, kina nan kina hawa kud'i ki taka kud'i ki yadda kikeso a cikinsu, lallai shawara d'aukar d'aki yau gashi mun da'auka tayi mana amfani!"
Suka sake sa dariya, Bilki tace
"A da na bijirewa shawararki, kuma da farko na tsorata amma yanzu abin sai wanda ya gani."
Suka sake sa dariya gami da tafa hannu. Laila ta kuma cewa tana dariya
"Yayi daidai kin birgeni! Yanzu keda talauci sai dai ko a lahira..."
Bilki tace
"Kada Allah ya had'ani da shi koda a lahirar ne ma. Yanzu tsoro na kada wata rana a gano mu ya zamuyi kenan?"
Laila tace
"Daman ay ke bugun Abuja ce, daman ke kalarki bata k'auye bace ba..."
Bilki tayi dariya
"To kin dai gani, rabona da k'auye har na manta, tunda muka dawo Abuja idan kin ganni k'auye sai dole..."
"Assalamu Alaikum..."
Ta shigo d'auke da tray d'in lemo da glass cups guda biyu sai plate d'in cincin da dambun nama. Ta ajiye tray d'in sannan ta gaishe su, sai da suka watsa mata harara sannan suka ce "Lafiya."
Bilki tace
"Kin d'ora abincin rana?"
Tace
"A'a yanzu zan d'ora."
Bilki tace
"Aikin me kike da tun d'azu baki d'ora ba har kusan k'arfe sha biyu?"
Tace
"Wanke wanke ya taru da yawa shine na..."
"Yi min shiru a nan!" Ta daka mata tsawa.
"Duka duka wanke wanken guda nawa ne da har zaki ce yayi yawa? Sai anyi magana ki dinga rissina kai kamar wata yarinyar kirki, zaki wuce ki d'ora ko sai na san me zan miki!"
"Uhm... me za'a dafa?"
Tayi tsaki
"Ki dafa mana fried rice da peppered chicken, sai ki had'a coleslaw, akwai kaji a freezer ki d'auki guda biyu kiyi amfani dashi. Sai kinsan halin babanku yafison tuwo, kiyi masa tuwo miyar busassar ku6ewa."
Da k'yar tace "To." Ta fice idanunta cike da hawaye!
"Anya bataji mu ba d'azu?" Cewar Laila cike da damuwa.
"Ko taji me za'ayi? Ah babu ay."
Sukayi dariya Laila tace
"Haka ne fa."
Tana kitchen tana yanka kaji Zarah ta shigo tana sanye da wando jeans sky blue sai light pink shirt marar hannu.
"Meenah zo ki ga..."
Da mamaki take kallonta tana d'aga mata fuska don taga idan idanunta ba k'arya suke nuna mata ba.
"Meenah kukan me kike? Hala Mami ce? Me tayi miki?"
Ta k'ak'alo murmushin dole tace
"Babu komai, wani abu ya fad'a min ido ne."
Zarah tayi murmushi
"Uhm baki iya k'arya ba Meenah, ni nasan wani abu Mami tayi miki."
Meenah tace
"Bakomai amma don Allah Zarah zan miki tambaya inaso ki fad'i man gaskiyar abinda kika sani."
Zarah tace
"Ina jinki."
Meenah tace
"Don Allah a iya zamanki a gidannan kin ta6a ji koda a wurin wani ne cewar tsintso ni akayi?"
Zarah ta k'yalk'yale da dariya harda duk'ewa, Meenah ta kalleta galala cike da mamaki tace
"Meye haka wai Zarah? Ya ina tambayarki kin tsaya kina min dariya?"
Har yanzu dariya takeyi, da k'yar ta tsagaita tana duban Meenah tace
"Anya baki buk'atar ganin likita Meenah? Kanki d'aya kuwa?"
Meenah ta k'ule tace
"Shikenan sai kije kiyi ta dariyar, gani kike kamar wasa nakeyi ko?"
Zarah tace
"Daman ay wasan kikeyi, ta yaya ma zaki fara irin wannan tunanin?"
Meenah tayi murmushi mai ciwo tace
"Dole nayi tunanin haka Zarah, na rasa meyasa Mami bata sona..."
Da sauri Zarah ta rufe mata baki
"Kar kice haka, ay indai zaki kula halinta ne haka, koni tana min."
Meenah tace
"Eh amma ba kamar yadda take min ba, dole ne na fara tunanin duk yadda akayi ko tsinto ni akayi ba'a san asali na ba, ko kuma ni 'yar rik'o ce."
Zarah ta 6ata rai
"To yayi miki kyau, ki cigaba da fad'in haka ni kuma daga yau na daina miki magana a gidannan."
Meenah ta juyo da sauri
"Haba dai?"
Zarah tace
"Ki cigaba ki gani."
Da sauri Meenah tace
"La na bari, ya za'ayi na bari mu 6ata?"
Zarah tayi murmushi
"Yawwa sweet sis bara na taya ki aikin don ayi sauri, kuma idan kika hanani yi sai na daina miki magana a gidannan."
Ta fad'a cike da shagwa6a, Meenah tasa dariya ta kwaikwaiye ta
"To bazakiyi ba wuce ki tafi ki kwanta."
Zarah tace
"Nak'i"
Haka suka k'arasa aikin suna zolayar juna, wasu abubuwan sai da Meenah ta dinga koya mata, kuma ba laifi tana fahimta.
***
"Wai bazakuyi sauri ku fito ba Jidda? Kodai a tura driver ya d'auko su ne?"
Da sauri Anisah ta fito cikin shigar atamfa d'inkin doguwar riga kalar blue and purple sa ta d'ora purple mayafi.
"A'a Mama mu zamu d'auko su, nifa na gama shiri su ya Jidda ne tun d'azu basu gama ba."
Mama tayi dariya.
"Au kin k'agu kiga yayan naki hala? Wannan irin zakwad'i haka?"
Anisah dariya, daidai nan sauran 'yan matan suka fito sun sha ado sunyi kyau inda dukansu suke cikin shiga iri d'aya.
Yusra tayi dariya
"Kai Mama duk kin k'osa a dauko miki yaranki ne haka?"
Mama tayi dariya
"Ke ni ba kakarki bace, ku wuce ku tafi haka nan."
Da sauri suka tafi suna dariya...
Jidda ta dubi agogon dake mak'ale a hannunta, k'arfe sha biyu harda rabi ta wuce.
"La Ibrahim kayi sauri sun kusa sauka."
Ibrahim yayi murmushi
"To ranki ya dad'e."
Tunda suka dira a airport hankalinsu ya kwanta ganin har yanzu basu sauka ba, amma daga inda suke suna hango jirgin yana niyyar sauka k'asa. Duk sukayi ajiyar zuciya.
A hankali jama'a suka fara fitowa daga jirgin, haka ma duk wanda ya hango d'an uwansa sai ya ruga ya taro sa.
Tsaye suke kusa da kujerar zama wato (waiting chair) idonsu k'yam saitin k'ofar jira kawai suke suga ta inda zasu 6ullo.

Subscribe to:
Posts (Atom)