Monday 6 March 2017

KHALEEL Page 41&42

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️


This page goes to my dearest sister Faty Axland, you are the best sister one could have ever ask for, thank you for everything, ina mik'a gaisuwata ga dukkan members na PWF U are d best Allah ya k'ara mana had'in kai ya k'ara muku basira ameen i heart you all one loveπŸ˜˜πŸ˜˜πŸ‘ŒπŸ»πŸ‘ŒπŸ»πŸ˜Ž


           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻41&42✍🏻✍🏻


2 weeks later!

Tana kitchen tana dafa abincin rana ya shigo yace
"Zanje airport, abincin mutum biyu zakiyi, muna da babban bak'o"
Shiru tayi ba amsa, Khaleel ya juyo da mamaki yana kallonta sai ya ga shi d'in take kallo tana murmushi, mamakin duniya ya kama shi, da k'arfi yace
"Hanifah...!!!"
Kunya ta kamata tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa cike da kunya. Khaleel yace
"Wai kin kuwa ji me nace?"
Tayi shiru, murmushi yayi yace
"Nace zanje airport muna da babban bak'o, shine nace abincin mutum biyu zakiyi"
Da k'yar tace "To" saboda kasala, haka ta gama girkin ta gyara dinning d'in gwanin kyau, abinci kuwa kala kusan hud'u ta had'a, banda drinks kala kala na kwali dana gargajiya, da snacks. Haka tayi ta tunanin ko waye zaizo kuma.

Tana gamawa ta k'ara gyara gidan, ta sanya turaren wuta gida ya gauraye da k'amshi.
Wanka tayi ta shirya cikin wani jan material dinkin doguwar riga, tana gyara fuskarta ya lek'o amma bai shigo ba yace.
"Ki fito ku gaisa da bak'on"
Yana gama fad'an haka yasa kai ya fice, haushi ya kama ta, "wato bazai ma iya shigowa ba ko?"
Ta kimtsa ta fito tana zuwa ta k'walalo idanu waje, wazata gani?
Saif ne ya had'e cikin suit, yayi jawur ga wata uwar k'iba yayi.
Batasan lokacin da ta ruga a guje ba ta rik'eshi tana tsallen murna. Cikin dariya yace
"Ke meye haka so kike na fad'i ne?"
Ko sauraronsa batayi ba, sai da tagaji amma tak'i sakin hannunsa. Khaleel na daga tsaye yana dariya, dinning suka d'unguma ya zauna yaci abinci, Khaleel ya mik'e yana dariya
"Bari na ba y'an uwan juna wuri su gana, naga har kun manta dani gara nayi gaba"
Hanifah ta murtuke fuska kamar zatayi kuka tace
"Ya Saif shine tunda ka tafi baka kirani ba ko?"
Yayi murmushi
"Ya za'ayi na kiraki kina cikin wani yanayi, sannan naga lokacin haushin kowa kikeji sheyasa kika ga ban kira ki ba"
Tace
"To amma ya akayi ka dawo bayan da sauran sati kusan hud'u ka gama?"
Yace
"Wallahi kuwa mun gama fa tun last week, dama su suka tsaida mu wai mu tsaya ko zasu iya d'aukar mu aiki, ni kuma naga so suke su rik'e mu and bana son yin aiki a wata k'asa nafison k'asarmu"
Tayi murmushi
"Hakane Allah ya bada sa'a"
Yace
"Amin"
Idonta ya kai kan screen d'in wayarshi, cikin mamaki ta d'auko wayar tace
"Ya wacece wannan?"
Ya d'anyi murmushi sunanta Salma, surukarku ce"
Murna ta cika Hanifah, tace
"Da gaske yaya?"
Yace
"Zan miki k'arya ne?"
Tace
"Wane gari take? wace makaranta take? A ina kuka had'u?"
Dariya ta kama Saif yace
"In banda abinki Hanifah ta yaya zan amsa duka wad'annan tambayoyin lokaci d'aya?"
Itama dariya tayi tace
"Yi hak'uri to ka fad'i min dalla dalla"
Yayi dariya yace
"Sunanta Umma Salma, kuma a nan garin take, iyayenta mutanen Katsina ne, amma zama ya kawo su nan, wata rana bayan bikinku na had'u da ita suna tafiya ita da k'aninta, tun lokacin naga ta kwanta min a rai, so mun d'an fahimci juna kafin na tafi, kuma gaskiya alhamdulillah na yaba da hankalin yarinyar, wato iyayenta sun rasu, tana zaune a hannun k'anin mahaifinta yanzu haka. Yanzu dai maganar da akeyi mun daidaita da kawun nata har sun fara cewa na turo.
Ta gama makaranta kusan tare dai kukayi graduating, kawai dai kin d'an girme ta amma ita ta gama da wuri ne"
Hanifah tayi dariya
"Wallahi ya tana da kyau, gata black beauty, Allah ta tabbatar da alkhairi"
Yace
"Amin"
Sai kuma ya d'an yi shiru kafin yace
"Naga alama kamar komai ya daidaita tsakanin ki da yaya ko, k'ila ma na kusa zama baba"
Ta k'ara shagwa6ewa tace
"Wallahi a'a ya"
Dariya yayi yace
"Ai naji dad'i sosai dama haka nake fatan naganku tare"
Ta basar da zancen ta hanyar jefo masa tambaya
"An mana tsaraba dai ko?"
Yayi murmushi
"Jakarki daban tana nan waje"
Tayi murmushin jin dad'i, tace
"Nagode yaya"
Yace
"O ke Hanifah, ya kikeji dan Allah, wai ya Khaleel ne mijinki?"
Tace
"Hmm wallahi kuwa ya..."
"Kai kai kai...."
Da sauri suka juya, Hanifah tace
"Wai har ya dawo?"
Ya sosa k'eya, yace
"Dama ba nisa nayi ba, y'an nema kuna nan kuna gulmata ko?"
Hanifah kunya ta sa ta mik'e tayi ciki da gudu.
Da ya tashi tafiya gida ya fiddo musu tsarabobinsu, jaka ce mak'il da kaya, su kayan bacci da english wears, sai jallabiya guda biyu, da kayan kwalliya, Khaleel shima harda su takalmi da kayan sawa.
Lallai agaida Saif yayi k'ok'ari, Khaleel ya maida shi gida saboda motarshi na can, a mota ma labarin Salma ake ba Khaleel, dama dai ya santa don har hoton an turo masa. Koda suka isa gida Ammi ma tayi mamakin ganinsa don batayi zaton zai dawo yanzu ba, Khaleel shi ya bata labarin Salma, aikuwa tayi murna sosai da fatan alkhairi.

*****

Daddare Khaleel palo ya kwana, wannan karon kuka taci har ta gode Allah, kafin safe idanunta sunyi luhu luhu sunyi ja, ta shiga wanka taji motsinshi aikuwa tak'i fitowa, ya gaji da jiranta ya aje mata dubu biyar kan drawer d'in side bed, sannan ya fice.

K'arfe goma da kusan rabi Saif ya shigo cikin shigar k'anan kaya, yana ganinta yace
"Ke kuma meyasami idanunki?"
Bata iya fad'a masa dalilin kukanta ay da kunya, da k'yar ta maida kwallan da ke neman zubo mata,  tace,
"Ciwo suke"
Yace
"Subhanalillah! Kin sa magani?"
Tace
"Eh nasa"
Yace
"Allah ya k'ara sauki"
Tace
"Amin"
Yace
"Ina yaya ne?"
Tace
"Har ya fita office fa"
Yace
"Da wuri haka?"
Tace
"Wallahi fa da wuri yake zuwa wani lokacin"
Yace
"Ok zan same shi office d'in kawai"
Tace
"Ok"
Daga haka yasa kai ya fice.

Da rana waina tayi da miyar kaji, tana gamawa ta shirya kan dinning ta koma d'aki tayi kwanciyarta, amma fa hankalinta naga sahibinta Khaleel! Tana son ganinshi sai dai dole ta dinga daurewa.
Shigowar motarsa taji, gabanta ya fad'i, tana jinshi ya shigo har ya wuce d'akinsa amma fa ta yanke shawarar bazata fito ba har sai ya neme ta da kansa!
Bayan kusan minti talatin taji shigowar text, amma ko dubawa batayi ba duk da tasan shi d'inne. Can kuma wayarta ta fara ruri, shima kamar bazata d'aga ba amma wace ita? Bata iyawa. Ta d'auka a fusace
"Hello!"
Ya kwantar da murya kamar wani k'aramin yaro da wani irin salo mai rikitar da duk wata mace mai lafiya yace.
"Rankiyadad'e azo a bani abinci yunwa nakeji"
Kafin ta bashi amsa har ya kashe wayar, ta kalli screen d'in tare da sakin murmushi tace
"Shu'umi Ya Khaleel"

Yau shigar bak'ak'en kaya akayi, riga bak'a haka ma wandon bak'i, ko kallonsa batayi ba ta shiga zuba masa, tana gamawa ta tura masa gabansa kawai sai ta juya zata bar palon.
Da sauri ya mik'e
"Idan har kika tafi to nima na k'oshi wallahi"
"Lallai ma ya Khaleel wai ni zaiyi wa wata barazana" ta fad'a cikin ranta, hakan yasa ta fasa tafiyar sai kawai ta dawo amma fa tayi tsaye kamar dogari, shima haka.
Sai data zauna shima ya zauna, ya duk'ar da kai yana cin abincinsa fuskarsa k'unshe da murmushi, daga gani yana cikin nishad'i.
Cikin ranta tace "sai wani murmushi yakeyi mugu kawai, idan har ya gano ni meyasa bazai basar ba mu cigaba da rayuwarmu, amma tsabar mugunta kullum daga dariya sai murmushi, gaskiya kana wahalar dani ya Khaleel, ka sassauta min haka..."
Ya d'ago suka had'a ido. Yayi murmushi
"Wannan kallo haka Hanifah? Ai sai kisa na k'ware"
Tayi murmushi
"Ni ba kai nake kallo ba, wancan hoton nake kallo"
Yayi dariya kurum yana cigaba da cin abincinsa.
Yana gamawa ya mik'e tsaye da cup d'in ruwa a hannunsa, bayan ya shanye yace
"Zan koma office sai dare zan dawo, kina buk'atar wani abu?"
Ko kallonshi batayi ba tace
"A'ah, a dawo lafiya"
Ta bishi da ido yanda yake wani tafiyar k'asaita kamar wani basarake...


K'arfe biyar na yamma Surayya tazo, Hanifah taji dad'i sosai, bayan ta kawo mata lemo da ruwa Surayya tace
"Naga sak'onki Hanifah, kuma na fahimci matsalarki"
Hanifah tace
"To ya kike ganin zan 6ullo wa lamarin Surayya?"
Surayya ta kur6i lemo bayan ta aje tace
"Abin nan ba k'arami bane Hanifah, saboda Khaleel ya fahimci kin kamu da sonsa shine yake garaki, bawai don ki wahala ba, a'a yana son ya dasa garkuwa mai amfani a cikin zuciyarki"
Hanifah kamar zatayi kuka tace
"Amma bai man adalci ba Surayya, kinsan abinda yafi damuna yawan kallon da nake masa kamar mayya, muddin muna tare daidai da minti d'aya ban iya d'auke idona daga kansa, shi kuma dizgi wallahi"
Surayya tace
"Haba Hanifah, sam Khaleel baya nufinki da shan wahala, kar ki manta shi ya gama shan tashi wahalar akanki, hak'uri ba irin wanda baiyi ba da ke, wulak'anci, cin fuska, amma still yace sai ke..."
Hanifah tace
"Uhm"
Surayya tace
"Ay nama ga k'ok'arinsa da wani ne da sai kin raina kanki wallahi, tace yanzu shawarar dazan baki kije ki same shi ki cire kunya kice kin kamu da sonshi"
Hanifah ta numfasa tace
"Kinsan Allah ko? To wallahi bazan iya ba"
Surayya tace
"Tsaya kiji Hanifah wannan ita kad'ai ce hanyar da zamu bi a shawo kan matsalar Allah"
Hanifah tace
"Bazan fa iya ba, bazaki gane halin Ya Khaleel ba Surayya, miskili ne na k'arshe, k'arshenta ma ina iya zuwa ya gwasale ni, ko ya kunyata ni, ke yana iya ma koro ni"
Surayya tace
"Kai anya, kedai ki jaraba"
Tace
"Bafa zan iya ba period"
Surayya tace
"To ya kike so ayi yanzu?"
Tace
"Mu chanza wata shawarar dai"
Surayya tace
"Kamar wace?"
Hanifah tace
"Nidai ko wace amma banda wannan"
Surayya tace
"Naji amma sai kin jira na nemi shawarar yayata kinsan sune matan aure, ni kinga ba matar aure bace, komai kenan zan kiraki"
Hanifah tace
"Toh shikenan ina dai jiranki dan Allah"
Surayya tace
"Insha Allah"
K'arfe shidda ta rakata ta tafi, ta dawo palo ta zauna.

Bayan sallar magriba Surayya ta turo mata sak'o
"Na tambayi yayata, tace dole sai naje zatayi min bayani amma ga sirri na farko, kinsan namiji na san k'anan kaya, dole ki dage da sakawa har kija ra'ayinshi..."
Murmushin mugunta tayi, sai kawai  tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin wani matsiyacin wando iya gwiwa dark pink, da bak'ar top matstsa. Gashinta ta taje ta bazo shi bisa gadon bayanta, k'amshi kuwa kamar shagon saida turare.
Ta dawo palo ta kame kan kujera 2sitter.
Can tajiyo k'arar shigowar mota, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya tare da tsare ta da wani asirtaccen kallo, mai cike da ma'ana daban daban....


MSB✍🏼

No comments: