Thursday 30 March 2017

KHALEEL Page 71&72

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻71&72✍🏻✍🏻


Washe gari Hanifah batada paper tana zaune palo ta baje guava tana ci ta jiyo sallama, da sauri ta tattara wurin ta mik'e ta nufi bakin k'ofa gami da bud'ewa, da mamaki tace
"Rufaida? Yau kece a gidannamu?".
Rufaida tana murmushi tace
"Wallahi kuwa".
Hanifah tace
"Bismillah shigo mana" ta shigo Hanifah ta bata izinin zama sannan ta wuce kitchen don nemo mata abin motsa baki, bayan Hanifah ta dawo ne suka soma gaisawa, Hanifah tace
"Ya exams?".
Rufaida tace
"Alhamdulillah, ya gida?".
Hanifah tace
"Lafiya k'alau, ashe zaki gane nan gidan?"
Rufaida tace
"Kin manta mun ta6a zuwa nida Humaira?"
Hanifah tace
"Haka ne fa na tuna".
Shiru ya biyo baya tsakani, Rufaida tunanin hanyar da zata fad'a mata wannan matsala takeyi, can tace
"Hanifah wata magana nazo muyi mai mahimmanci, amma kafin nan ina so ki kwantar da hankalinki ki saurare ni kuma ki fahimce ni, sannan kar kiyi saurin tada hankali".
Hanifah tayi shiru amma sai data samu kanta da fad'uwar gaba, ta dai daure tace
"Insha Allah komai zaki fad'a zan fahimce ki"
Rufaida tayi murmushi tace
"Yauwa, akwai wani al'amari mai rikitarwa dasa mutum shiga rud'ani, sannan mai matuk'ar mamaki. Abinda yasa kika ga zan fad'a miki wannan magana saboda nima mace ce y'ar uwarki, bazanso abinda yake faruwa dake nima ya faru dani ba"
Cikin rashin fahimta Hanifah tace
"Bangane abinda kike nufi ba, ki warware min yadda zan fahimta".
Rufaida ta dafa ta tana murmushi
"Kar ki damu yanzu zakiji komai insha Allah, wato akan maganar k'awarki ce Humaira"
Hanifah tace
"Humaira kuma? Meyafaru da ita?"
Rufaida tace
"Yadda kika d'auke ta ita ba haka ta d'auke ki ba, wato duk wata matsala ta gidanki tsakaninki da mijinki Humaira ce ke haddasawa, don da k'arfin tuwo so take ta k'wace miki miji...".
Hanifah gabanta yayi mummunan fad'uwa ta dafe k'irji tace
"Humairar?".
Rufaida tace
"Ita fa, kuma kinsan Allah dai ko? Wannan magananar da na fad'a idan har na mata sharri ko k'azafi Allah ya saka mata duniya  da lahira, amma dole ne fa sai kinyi takatsantsan da ita,  idan ba haka ba wata rana kina ji kina gani zata fi k'arfinki, sannan dole ki tashi tsaye da addu'a shine kad'ai mafita".
Hanifah hankali tashe tace
"Indai har maganganun da kika fad'a min gaskiya ne Rufaida, nagode miki kuma insha Allah zanyi a hankali, addu'a kam inayi zan dai k'ara. Sannan da sannu zanyi maganinta insha Allah, sai dai ga tambaya meyasa Humaira ke bibiyar mijina? Meye had'inta dashi?"
"A zahirin gaskiya ni tuntuni na fahimci Humaira muguwa ce, sannan wai ita nan sonsa take, amma kar ki damu zan binciko miki, komai kenan zan neme ki".
Hanifah tace
"Kai nagode sosai wallahi Allah ya bar zumunci"
Rufaida taji dad'in yadda Hanifah tayi reacting don haka sai tace
"Amin Hanifah, kuma Allah ubangiji ya shige mana gaba, duk lokacin da kike buk'atar k'arin bayani ko kuma wani abu ya shige miki duhu, don't hesitate to call me anytime".
Hanifah tace
"Insha Allah i will, nagode sosai"
Rufaida tace
"Bakomai ni zan wuce".
Hanifah tace
"Haba dai tun yanzu? Ki tsaya kici abinci mana"
Rufaida tace
"Wallahi na k'oshi next time dai"
Ba haka Hanifah taso ba, sai kawai tace
"Shikenan tunda kin k'oshi"
A tare suka mik'e inda Hanifah ta raka ta har bakin k'ofa ta juyo ciki zuciyarta na cigaba da sak'e sak'e.
Ko minti 15 batayi da shigowa ba wayarta ta fara ruri, ganin Humaira ce mai kiran taji wani bak'in ciki da haushinta sun mamaye ta, sai dai dole tabi komai a sannu bata so tayi saurin ganowa, sai kawai ta daure sosai tana murmushi tace
"Humaira yane?".
Humaira tace
"Lafiya lau kina gida ne?".
Hanifah tace
"A'a na d'an fita tun d'azu".
Humaira tace
"Da zan shigo, yaushe zaki dawo?"
Hanifah tace
"Sai dare gaskiya".
Humaira tace
"Ayya ba damuwa to".
Sukayi sallama inda Hanifah ta buga tsaki tace
"Munafuka no wonder kad'an kad'an zata ce zatazo ashe da abinda ta taka, ta Allah ba taki ba. Kuma insha Allah sai kin bar min mijina don yafi k'arfinki".


*****

Su Hanifah sun k'are exams d'insu lafiya na first semester inda yanzu sam ta daina bama Humaira fuska tana zuwa gidanta, da tace mata zatazo zata samu reason ta fad'a mata.  A school ko tare suke Hanifah bata cika zuba ba a gabanta, sama sama suke magana.
Sun samu hutu inda Hanifah suke zaune lafiya da Khaleel d'inta yanzu basuda matsala, zamansu har yafi nada dad'i.
Sam Khaleel bai san 6acin ran Hanifansa, musamman yanzu da cikinta ke dad'a girma, basu wasa da appointment d'insu.

Sun gama exams da kwana biyu Khaleel ya d'auke Hanifah suka tafi Abuja, a can d'inma sun sha dad'i da yawo, ga siyayya ba irin wacce ba'ayi ma babynsu ba, Khaleel ya kwaso kayan babies ba iyaka.
A hotel suka sauka inda da yamma bayan sun dawo daga shopping suka tafi gidan Saif. Sanda sukaje Saif na wurin aiki sai Salma suka tarar a gidan. Bayan sun gaisa Khaleel ya mik'e ya kalli Hanifah yace
"Bari na same shi office d'in".
Daga haka ya fice, nan su Hanifah suka baje suka dasa fira kamar ba gobe, cikin firarsu ne Hanifah ke bata labarin Humaira, da mamaki Salma tace
"Meyasa kike saurin yarda da mutum ba tare da kinsan ko waye ba?".
Hanifah tace
"Bari kedai tautsayi mana, ay yanzu na ja baya da friendship d'in babu dole, kuma a hankali zan fitar da ita daga rayuwarmu gaba d'aya, idan ma tak'i to zan buga mata warning ta tafi can ta nemi daidai da ita".
Salma tayi dariya
"Hakan dai ya kamata, kinga kinyi learning lesson sai kiyi a hankali saboda gaba"
Hanifah tace
"Ay dole".
Suna zaune Hanifah ta lura Salma sai faman tashi take tana zubar da yawu ta dawo, ta zubar a karo na uku ta dawo Hanifah ta kalleta tace
"Kodai mun samu k'aruwa ne?".
Salma tace
"K'aruwar me?".
Hanifah tace
"Kin fa sani zaki wani nuna baki sani ba"
Salma tayi murmushi kurum, Hanifah ta yi dariya tace
"Ah! Ni nasan da zance a k'asa kuma shine ko ki sanar dani, ni kuwa ranar dana gano nawa na fad'a miki".
Salma ta kamo hannun Hanifah
"I'm sorry kinji? Wallahi kunya naji na kasa fad'a miki".
Hanifah ta janye hannunta
"Ashema kunya, da yanzu sai dai mu ganki da ciki ko? Ke haka kikayi planning ba?"
Salma ta shiga ba Hanifah hak'uri inda ta k'yar ta hak'ura tace
"Naji yanzu wata nawa?".
Salma tace
"Wata d'aya kawai".
Hanifah tace
"Iyye! Ah lallai su Ya Saif za'a zama daddy"
Sukayi dariya gaba d'aya.
Salma ta kuma cewa
"La ni na manta fushi nake dake"
Hanifah ta zaro idanu waje tace
"Menayi miki?".
Salma tace
"Wai kuzo gari ku wani sauka a hotel"
Hanifah tayi dariya
"Kai ya za'ayi mu takurawa amare? Kedai barmu a hotel d'inmu".
Salma tayi murmushi kurum.
 Sai da suka gama firansu sannan suka tashi Hanifah ta taimaka mata suka d'ora girkin dare, jollof d'in shinkafa da soyayen kifi.
Bayan sun gama suka gyara kitchen d'in, sannan suka dawo palo suna kallon wani movie mai suna Raising Helen, su Saif sukayi sallama, bayan sun zauna ne kuma suka fara fira, da k'yar suka tashi lokacin an fara kiraye kirayen sallar magriba.
Bayan sun gama sallah ne suka d'unguma dinning suka ci abinci, suna ci suna fira. Hanifah ta mik'e taje daidai saitin kunnen Khaleel ta rad'a mishi wani abu, duk akan idon su Saif, suna kallo Khaleel ya ware idanu waje yace mata
"Ah haba don Allah".
Tana murmushi tace
"Wallahi kuwa da gaske".
Saif yace
"Kai mekuke cewa haka?".
Khaleel ya k'yalk'yale da dariya yace
"Abin arzik'i muke cewa, lallai Saif shine kuka 6oye mana wannan abin alkhairin?"
Cikin rashin fahimta Saif yace
"Wai mene?".
Khaleel yace
"Shikenan tunda baka sani ba, uhm mu bari mu tashi mu wuce hotel mu kwanta dare nayi"
Saif da sauri ya taresa yana fad'in
"Haba dai ya Khaleel, ya gs gidana zaku tafi hotel? Gaskiya banji dad'i ba".
Khaleel yace
"Wallahi bawai don bama son zuwa nan d'in bane, a'a bama son mu takura muku ne"
Saif yace
"Haba ya Khaleel! Wane irin takura kuma? You are my brother fa remember?".
Khaleel ya dafa sa
"Haba nasani Saif, but don't worry na maka alk'awarin gobe zamu dawo nan. Amma dai ka barmu muje hotel d'in yanzu mu kimtsa mu kwashe kayanmu sai mu dawo"
Saif yaji dad'i yace
"Yauwa ko kai fa, har naji dad'i yanzu".
Akayi dariya, har bakin mota suka rasa su. sannan suka koma ciki.


Haka kuwa akayi washe gari sai gasu sunzo, aikuwa Saif akayi ta murna, kullum da yamma sai sun fita yawo su dawo da daddare. A haka har sukayi sati d'aya sannan kuma suka soma shirin dawowa gida.


*****

Sun koma Kaduna da daddare inda Hanifah ke tattara kayan baby da suka siyo tana adanawa, Khaleel na gefenta yana taya ta. Wasu set na overall pink color Hanifah ta d'aga tana kallo cike da adoration Khaleel yace mata
"Wai meyasa kika kwaso na mata?".
Ta kalleshi tana murmushi tace
"Kai meyasa ka kwaso na maza?".
Yace
"Saboda nasan baby boy zaki haifa min insha Allah".
Hanifah tace
"Ni a'a mace ce ma insha Allah".
Yace
"Kece macen ay, Allah ya kawo namiji"
Tace
"Mace Allah ya kawo ta".
Kamar wasa gardama ta 6arke tsakaninsu, da k'yar Khaleel yace
"Shikenan idan macece nayi miki alk'awarin kiss hot one immediately bayan kin haihu, kuma ko gaban waye, and idan namiji ne zaki bani hot kiss koma a gaban waye"
Tace
"Na yarda Allah ya kaimu".
Cike da confidence
Jawo ta yayi ta fad'o bisa k'irjinsa yana zolayarta wai cikinta ya fara fitowa sosai, ita kuma sai shagwa6a take zuba masa, kafin ta ankara taji bakinsa cikin nata, inda kuma wasa ya chanza salo, da sauri na fito kar ka naga abinda yafi k'arfina.




MSB✍🏼

No comments: