Sunday 12 March 2017

KHALEEL Page 47&48

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€


Na sadaukar da wannan page d'in ga dukkan masoya na, na gode da k'aunar ku a gareni INA TARE DA KU koda yausheπŸ’™πŸ’›❤️πŸ’šπŸ’œ


©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻47&48✍🏻✍🏻


Tunda ya hau titi yake sak'e sak'e a ransa, ga tunani da yaci k'arfinsa, ga Hanifah da yake kewa, har wani d'aci yakeji a cikin ransa, ya kudiri a ransa duk wanda ya sace masa Hanifah bazai k'yaleshi ba koma waye. Rabin hankalinsa sam bayaga titi, don ma Allah mai tsarewa ne da bana tunanin Khaleel zai iso lafiya. Daga gefen titi yaja ya tsaya, ya kalli wurin babu gida ko k'wara d'aya, yayi mamakin dalilin da yasa ya buk'aci lallai lallai sai a nan zasu had'u, ko wace irin magana ce haka oho? Koma dai menene zaiji idan har yayi hak'uri mutumin yazo. Ya d'auko wayarsa zai tura ma mutumin sak'on cewar fa gashi ya iso wurin kiran Saif ya shigo wayarsa. Murmushi yayi gami da karawa a kunne
"Hello ya Khaleel! Kana ina?"
Yayi murmushi
"Yanzu na iso wurin, ina jiran mutumin ne bai k'araso ba"
 "Ok please kayi a hankali tunda kasan bamusa wanene ba, just be careful please, and komai kenan don Allah ka kiramu, Ammi na gaishe ka tana maka fatan alkhairi ya Khaleel"
"Allah sarki d'an uwa! Kar ka damu zanbi a hankali insha Allah, ka gaida Ammi please"
Ya kashe wayar, ya tura ma mutumin sak'o
"Gani fa na iso five minutes ago ya kamata ka k'araso ina jiranka"
Yayi tunanin zai ji shigowar sak'on amma ga mamakinsa har wurin bayan minti uku shiru kakeji. Da har zai k'ara tura masa da wani sak'on sai kuma ya fasa, amma idan yaji shirun tayi yawa fa zai kira.


*****

Hanifah na kwance kan tabarmar d'akin taji an turo k'ofar, ko d'aga ido batayi ba don tasan bai wuce d'an iska Deen.
Zama yayi kan wata kujerar robar da ke d'akin ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya.
Runtse idonta tayi gam tana mai jin haushinsa, taba yake zuk'a kamar ba gobe, abinnan yana matuk'ar 6ata mata rai, ta tsani warin taba, amma ba yadda ta iya don ko magana batasan yi masa.
Ya kalleta yayi murmushi
"Ke...!"
Tayi banza da shi
"Lallai yarinyar nan bakisan Dboy ba, kar ki kuskura kice zaki kawo min raini a nan wallahi zan iya 6a6alla ki kina jina?"
Tayi shiru
Bindiga ya d'auko yace
"Zaki tashi ko kuwa?"
Ba musu ta tashi tana share hawaye, ya kalle ta yace
"Awwn crying baby, kukan ya miki kyau"
Ta 6alla masa harara wane zata zazzago idanunta.
Ya k'yalk'yale da dariya yace
"Kinsan Allah idan kika kwafsa min zan koya miki hankali, na kira mijinki yanzu yana nan  yana jirana, kinsan dai halina zan iya tarwatsa masa kai ni babu abinda ya dame ni..."
Gabanta yayi mummunan fad'uwa, idanunta suka kawo ruwa batasan lokacin da tace
"Idan ka kuskura ka ta6a masa lafiyarsa wallahi zakayi nadama"
Ya juyo ya kalleta
"Jibeki da Allah wata y'ar k'waila da ke, mts bakida hankali yarinyar nan"
Tana ji tana gani ya fice suka kulle ta da kwad'o, wani kukan tasa mai tsuma zuciyar duk wani sauraro, zuwa yanzu idanunta har wani rad'ad'i suke mata, gashi sun kad'a sunyi jajir, Hanifah ta zama abin tausayi tana missing Khaleel, sai yanzu take jin idan har aka rabasu to zata iya mutuwa kawai, tana nan tana razgar kuka taji an sake bud'e k'ofa, wannan matar ce ta shigo da kular abinci sai pure water guda d'aya, ta d'aga ido ta kalli matar mai k'irar samudawa, gata bak'ik'irin kai anya ma musulma ce wannan? Dan ba alama kayan jikinta sun nuna haka.
Abincin ta dire mata da karfi a gabanta tana wani hura hanci tace
"Kici yarinya kar yunwa ta kashe ki"
Hanifah ta kauda fuska don ko zata mutu bazata ci ba. Tace
"Ni ki bani ruwa inyi sallar asuba tunda kun kulle ni, sannan ina son in shiga toilet"
Matar tayi shiru tana tunani, gashi babu toilet ta ciki dole sai an fita ta baya, sai dai ta tsareta har ta gama"
Matar tace
"Ok ba matsala muje kiyi"
Hanifah ta mik'e matar ta fice tabi bayanta, ta baya suka zagaya ta nuna mata bayin, Hanifah ta shiga.
Tana nan tsaye mai gadin gidan ya zagayo, to dama saurayin matar ne, tana ganinshi ta isa inda yake hannunta ya kamo, dama shima kafiri ne irinta, yace
"Zo muje kiga wani abu"
Zatayi magana yace
"Shhh, idan bakizo ba zanyi fushi"
Ba yadda ta iya tabi bayansa, gashi tana tunanin ta bar Hanifah a bayi, sai dai ta k'udiri a ranta sauri zatayi kan ta fito.
Hanifah ta kammala ta fito, tana fitowa kuwa ta kalli gabas kudu da arewa ba matar nan
"Aiko guduwa zanyi kafin ta dawo"
Da sand'o ta dinga tafiya tana waige waige, gashi batasan kan gidan ba, dole tayi ta tafiya har sai ta gano gate d'in.
Sai da ta zagaye gidan kaf bataga alamar hanyar fita ba, hankalinta ya tashi duk ta rud'e, ta soma kuka tana tunanin mafita.
Kamar ance kalli can ta kuwa ango makeken gate kuma ba kowa wurin ga k'ofa a bud'e.
Da gudu ta doshi gate ta fito, ta fara waige waige ta ina zata fara? Ina zata dosa? Addu'a tayi tabi gabas da gudu, fatanta Allah yasa taga titi daga nan ko taxi sai ta shiga ta kaita gida.

Matar ta gama suka fito, tana ta sauri kuwa, saidai ga mamakinta Hanifah bata ciki, ta duba toilet d'in sosai amma bata nan, a rud'e ta fito ta fara dubawa ko ina amma wayam, ciki ta koma ta soma dubawa nan ma ba alamun Hanifah, hankalinta ya tashi sosai, oganta yau kashe ta kawai zaiyi, da gudu fa fito hannunta saman kai ta fara k'wala wa mai gadi kira
"David... David.... David!!!"
Ya fito yana cewa
"My love how far?"
"Don't my love me, banga yarinya ba yau na mutu" a rud'e take fad'in haka
David yace
"Ba'a ganshi ba ina yaje kenan?"
A fusace tace
"Ay duk laifinka ne meyasa ka kirani?"
Shima a fusace yace
"Dan na kiraka wayace ka biyo ni? Ji mata kai" aiko nan fad'a ya 6arke tsakaninsu, sukayi ta cacar baki, daga k'arshe suka watse ta fito neman Hanifah.


*****

Khaleel ya gaji da jira har zai tada mota ya hango shi yana k'arasowa, fitowa yayi daga motar ya tsaya yana jira ya k'araso duk da bai tabbatar da ko shi d'in bane amma yaga alamun nan d'in yake tahowa.
Aikuwa sai gashi ya k'araso, suka gaisa kamar na kirki Khaleel yace
"Tun d'azu fa nake zaman jiranka a nan"
Deen yace
"Sorry fa kasan mutum mai iyali sai a hankali"
Khaleel yace
"Hakane"
Deen ya fara magana
"Kasan dalilin kiranka da nayi?"
Khaleel yace
"Sai ka fad'a"
Deen yace
"Bazan tsaya wani 6oye 6oye ba, don ba halina na bane 6oye 6oye,  kasan Hanifah?"
Khaleel yace
"Hanifah fa kace? Wannan wace irin tambaya ce?"
Deen yace
"Just answer malam"
Khaleel yace
"Nasanta mana MATATA CE! Ina ka santa?"
Deen yayi murmushin mugunta
"Nice! Kar kayi mamaki idan nace maka tana hannuna"
A fusace Khaleel ya shak'o wuyansa
"Me kake nufi kenan? Kai ka sace ta komai? A wane dalili?"
Deen baiyi wani yunk'uri ba, sai yayi murmushi still Khaleel na girgiza sa yace
"Kar ka damu dama nasan hakan zata faru, kayi ka gama, you are free to continue"
Wuyansa ya shak'e gam gam, kishi ya rufe masa ido, sai da Deen ya fara hango lahira sannan ya fara k'ok'arin k'wace kansa amma ina ya kasa, Khaleel yace
"Kayi magana mana, meyasa ka d'auke ta? Bazaka fad'a ba?"
Ya k'ara k'arfi wurin shak'e sa da yayi.
Deen fa ya sha wuya, baiyi tunanin Khaleel yafi k'arfinsa haka ba, cikin wahallaliyar murya Deen yace
"Sake ni zan fad'a maka wallahi"
Khaleel yace
"Ka rantse"
Deen ba yadda ya iya don ya wahala yace
"Na rantse da Allah zan fad'i"
Sai a sannan Khaleel ya sakesa amma fa idanunsa sun yi ja!
Deen ya soma tarin wahala, yana numfashi sama sama, amma still Khaleel bai sake sa ba.
Sai da Deen ya d'an dawo daidai yace
"Na sace Hanifah ne saboda wasu dalilai nawa, mun ta6a soyayya a baya kafin aurenku, amma ni har ga Allah ba sonta nake ba sha'awarta nake"
Tasss! Khaleel ya d'auke Deen da wani irin gigitaccen marin da tunda uwarsa ta haife sa ba'a ta6a mai irinsa ba, sai da ya daina ji ya daina gani na wucen gadin! Lallai ashe haka Khaleel yake? Yayi tunanin zai same sa sa6anin haka.
Khaleel yace
"Tun muna mu biyu muje ka fiddo min matata na tafi da abata, tun kafin kayi dana sani, kar kayi tunanin zan k'yale ka kaci bulus"
Deen duk da yana d'an shakkarsa sai da yayi dariya yace
"Nifa nan na kiraka ne don ka sakar min ita, amma naga kamar sai mun d'an fafata da kai"
Khaleel yace
"Saki fa kace? Ai kai baka isa ka sani na saki Hanifah ba, kalleka fa kamar wani sandar snooker, banga ta inda zaka iya bani tsoro ba"
Ya kalli Khaleel, tabbas baiyi k'arya ba don jikinsu mu ba d'aya bane, anya zai iya da Khaleel bai fiye masa kawai ya bashi matarsa ba?
Khaleel yace
"Ka bani matata nace, tun kafin na had'a ka da hukuma, waya kawai zanyi yanzu azo a kama ka"
Deen ya kalle shi, shima Khaleel d'in shi yake kallo ido cikin ido, alamun baya jin tsoronsa ko sau d'aya. Sun jima a hakan Kafin idon Khaleel su sauka kan bindigar Deen dake yashe a k'asa, Khaleel yayi murmushi, zaiyi amfani da ita yasan dole Deen zai basa Hanifah.





MSB✍🏼

No comments: