Thursday 16 March 2017

KHALEEL Page 55&56

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀


Wannna page d'in naku ne my dearies.
Hafsat Basheer, Maryam Sayaya, Fatima Bindawa, Asma'u Ammani, Hauwee Bash, Asmeen, Fatima Raiyana, Tafisuu, my dear CHUCHU, Miemiee bee,  Fakabir, Faty Ladan, Aisha Yakubu, Susu, Cutie, kawata Zee bee, 'Yar ficika, My besty Fatima Muhd Mansur.... And all members na PWF Hmmm banida bakin godiya akan yadda kuke nuna k'aunarku gareni da book dinnan nawa, nagode maku Allah ya bar zumunci❤️❤️❤️❤️❤️❤️ INA TARE DAKU💞



©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻55&56✍🏻✍🏻


K'ofar gidansu yayi parking a tare suka fito suka jera, Hanifah ta kalli gidansu wani irin dad'i na ratsa ta, hannunta Khaleel ya kamo suka kalli juna fuskokinsu d'auke da murmushi, Khaleel yace
"Shall we?"
Tace
"Yes" a haka suka soma tafiya zuwa ciki. Daga bakin k'ofar gidan suka soma knocking, ba'a juma ba aka bud'e, Halisa ce tsaye cike da mamaki da jin dad'i, da k'arfi tace
"Hanifah...!"
Mak'alk'ale ta tayi tana hawayen farin ciki, Halisa ta share hawayenta tace
"Alhamdulillah Amina! Allah shine abin godiya gaki kin dawo gida cikin k'oshin lafiya, Allah ubangiji ya k'ara tsare mu daga sharrin masu sharri ya tsarkake mana zuciyarmu"
Hanifah tace
"Amin Halisa, ina Ammi?"
"Tana ciki tana wanka tun d'azu dai ta shiga nasan yanzu ta..."
Kafin Halisa ta k'arasa magana har Hanifah tayi ciki da gudu tana kiran sunanta.
"Ammi! Ammi!! Ammi!!!"
Khaleel yayi murmushi suka soma gaisawa da Halisa tana masa barka.

Ammi tayi tsai tana jiyo muryar Hanifah na k'wala mata kira, da sauri ta doshi k'ofar fita daga d'akin, aikuwa a bakin k'ofa suka yi kaci6us Hanifah tayi tsaye tana kallon Ammi, itama Ammi tsayen tayi tana kallonta, da sauri Hanifah ta mak'alk'ale ta tana kukan farin ciki, sun jima a haka kafin Ammi ta fara janye jikinta da k'yar don Hanifah batada niyyan sakinta, Ammi tace
"Sannu Hanifah, ya jikin naki? Badai abinda ke miki ciwo ko?"
Hanifah tayi murmushi tana kallon Ammi tana share hawaye tace
"Babu Ammi, nayi kewarki da yawa"
Ammi tayi murmushi
"Dena kukan komai ya wuce, Allah ya kyauta gaba"
Hanifah tace "Amin"
Nan ta soma bata labarin abubuwan da suka faru sanda aka sace ta, bata k'arasa ba Saif ya shigo da sallama, da gudu Hanifah taje da mak'alak'ale shi wane za'a k'wace shi. Da k'yar ya 6an6are ta yace
"Y'ar autar Ammi ya jikin?"
Tayi murmushi
"Da sauk'i ya Saif, nayi kewarku"
Yayi murmushi
"Muma haka, Allah ya k'ara karewa ya tsare mu gaba d'aya"
Suka amsa da "Amin" a haka suka d'an ta6a fira ta yaushe gamo, Khaleel ya shigo Ammi tayi murnar ganinshi ba kad'an ba haka ma Saif, a d'akin suka baje suka soma fira, kowa yayi kewar kowa, Hanifah ce tace
"Ammi wanka nakeson yi"
Ammi tace
"Ay ya kamata kiyi wanka ko kya ji dad'in jikinki"
Ta kalli Khaleei tace
"Kai ma kaje kayi wanka sai kuzo muci abinci"
Duk suka mik'e, Hanifah d'akinta nada ta wuce ta shige toilet, ta d'auki lokaci mai tsawo tana tsaftace ko ina na jikinta sannan ta fito, a cikin d'akin ta iske Halisa tana aje wasu kaya set biyu ta kalli Hanifah.
"Wad'annan wasu kayanki ne da kika manta shine Hajiya ta aje miki su, nayi tunanin mancewa tayi dasu sai yanzu tace a kawo miki ki za6i d'aya kisa kizo ki ci abinci"
Hanifah tayi murmushi
"Nagode"
Halisa ta fice, su man shafawa da turare duk na Ammi tayi amfani da su, dark pink doguwar riga ta d'auko ta material bai matse ta ba sosai amma ya mata kyau, turare ta fesa kad'an sannan ta yafa d'an k'aramin pink veil.


Akan dinning ta iske kowa banda Khaleel, da alama bai gama kimtsawa ba, zama tayi ta zuba soyayyen dankali da k'wai da miyar hanta, ta soma ci, Khaleel ya fito, yayi k'al yayi fes da shi gwanin kyau, idonta akansa har ya k'araso ya zauna yana fuskantarta, shima ita d'in yake kallo a take kuma suka sakar ma juna da wani k'ayataccen murmushi mai tafiya da imanin masoya.
A natse suke cin abincin ko wane motsi nasu akan idon Saif, dad'i ne ya cika sa lallai k'anwarsa tayi hankali, addu'a yake Allah yasa su d'ore a haka ya karesu daga sharrin mak'iya. Ganin yadda suke kallon juna kamar zasu cinye junansu ya sanya Saif yayi gyaran murya, ita dama Ammi tuni ta gama ta koma d'aki don yin karatu. Shima Saif mik'ewa yayi yana dariya yace
"Bari na baku wuri naga kamar kun manta dani a nan"
Hanifah tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa a yayinda Saif ke ta murmushi yace
"Dama ya za'ayi mu tuna da kai mun sanka ne?"
Saif yace
"Yayi lover birds banga laifinku ba, amma dama ku lalla6a ku koma gida sai ku soye son ranku"
Khaleel yayi dariya
"Saif yaushe ka zama marar kunya ne bansani ba?" Saif yayi murmushi
"Ahh dama ni ina da kunyata ay"
Khaleel yace
"Kar ka damu bari Salma ta shigo zamu rama ne"
Sai a sannan Saif yayi murmushi bai k'ara magana ba.
Khaleel yace
"Tun yanzu har kayi sanyi kafin ma ta shigo?"
Da sauri Saif ya bar wurin yana fad'in
"Nidai fita zanyi idan kun gama ku tattara ku koma gidanku"
Khaleel ya d'aga murya
"Hala wurin Salma za'aje?"
Yana jiyo dariyarsa har ya fice daga gidan.


Bayan sun kammala k'wabta aka fara turarowa zuwa yin barka Hanifah ta dawo, gidan kamar ana biki ko suna, shiga kawai akeyi ana fita, dole Ammi tasa aka girka abincin rana da yawa saboda dole sai ka bada abinci, don wasu zaune sukeyi, kuma kar suce ba'a basu abinci ba, haka dai gidan ya koma kamar gidan biki. Y'an uwan su Hanifah ma sun kira sukayi mata barka sunce idan sun samu dama zasu zo.
Bayan sallar azahar Ammi ta tura Halisa ta gyare gidan ta share ta goge had'e da turaren wuta, don tace ana yin isha'i zasu tattara su koma gidansu.



MSB✍🏼

No comments: