Wednesday 1 March 2017

KHALELL Page 35&36

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017πŸ’Ž


              PAGE

✍🏻✍🏻35&36✍🏻✍🏻


Alhamdulillah! Naga sakonnin gaisuwarku yan uwa, Allah ya bar zumunci 😍😘


Ta k'ara karanta sak'on sau wajen uku tana ayyanawa a ranta da gaske dai Deen ne, a hankali ta soma tunanin ranar da Saif yayi masa dukan tsiya ya farfasa masa fuska, hannunta na kyarma ta tura masa reply.

"Deen kaine? Ina ka samu number ta?"

Ya gyara kwanciyarsa tare da yin wani
shu'umin murmushi, ya tura mata reply.

"Nine Hanifah, meyasa kika yaudare ni bayan kinsan irin son da nake miki?"

Kwalla ta cika mata ido ta tura masa reply

"Wallahi ba laifina bane Deen, wannan auren da kaga nayi ba da son raina aka yi shi ba, bana sonsa i hate him so much, ni kai nake so kuma  KAINE ZAB'INA..!"

Dariya yayi mai cike fa jin dad'i yace a fili.
"Lallai yarinya kin sauwak'a min aikina kenan, indai haka ne bazan sha wahala ba"
Ya k'ara tura mata reply

"It's ok dear, na yarda da ke, tunda kince kina sona ki kashe aurenki kizo muyi aure mana"

Tayi masa reply tana kuka sosai

"I can't Deen! Kayi hak'uri ka nemi wata kawai"

Ya mik'e zumbur yayi mata reply

"Me kike nufi kenan? Ina son da kikace kina man? Kenan k'arya kikeyi?"

Ta k'ara fashewa da kuka ta masa reply

"Ba haka bane Deen, har yanzu ina sonka, amma hak'uri zamuyi, ka hak'ura ka nemi Wata na rok'e ka"

Yana huci yace
"Ina bazai yiwu ba, is either ki dawo min ko kuma na d'auki mataki, ina! Bazan iya hak'ura  da ita ba, na riga nasa rai!"

Hanifah kuwa wayar tayi wurgi da ita k'asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai. Haka tayi ta kuka har sai da kanta ya fara sara mata, a wannan yanayin Deen ya dawo daga jogging, palo ya shigo yaga ba Hanifah, ya k'arasa d'aki, kwance ya iske ta tana kuka, a rud'e ya shigo ya zauna kusa da ita yace.
"My baby lafiya meyasame ki haka?"
Tace
"Babu"
Yace
"Ban yarda ba meyasa kike 6oye min damuwarki ne? Nifa mijinki ne"
Tace
"Kaine ke ciwo"
Tashi yayi ya fita, can sai gashi ya dawo hannunsa d'auke da glass cup da panadol, ya 6alla mata yace
"Tashi kisha magani, kinci abinci kuwa?"
Ta girgiza kanta alamun a'a, yace
"A'a ki fara cin wani abu sai kisha maganin, me kikeso?"
Cikin gadara tace
"Fura da nono"
Tasani sarai ba'a cika samun fura da nono ba sai da yoghurt sai dai idan zaka siyo dawo daban nono daban. Yace
"Ok amma wadda ba'a dama ba ko?"
Tace
"A'a damamma nakeso"
Yace
"Ok anything for my baby" daga haka ya fice yana fad'in
"Bari naje yanzu zan dawo"
Yana fita taja tsaki tana dariyar mugunta
Sannan ta tashi tayi kitchen, indomie ta dafa taci ta k'oshi ta kwanta sai bacci.

Bai dawo ba sai bayan kusan awa d'aya, tana jin shigowar mota ta rufe idonta kamar mai bacci.
Yana shigowa yayi tapping d'inta a k'afa yace
"Hanifah! Tashi ga furar"
Tayi mik'a kamar mai baccin gaske tace
"Uhmm bana son fura kuma, k'wai zanci da tea"
Yace
"Ok bari na had'a miki sannu ko"
Ba hak taso ba! Taso ya 6ata rai amma bari ya dawo.
Ya fice da sauri, yana fita tayi ta dariyar mugunta.
Minti sha biyar ya kammala ya dawo, ya tashe ta, ta tashi zaune kamar marar lafiyar gaske.
Da kanshi ya bata a baki, amma loma d'aya  kacal tayi tace ta k'oshi, fuskarsa mai nuni da alamun damuwa yace
"To sha tea d'in"
Shima sai da tayi ta sha a hankali sannan ta shanye, ya bata maganin, yace ta kwanta ta huta a haka ya fice daga d'akin, duk bayan some minutes sai ya dawo yaga ya jikin nata.


Haka Hanifah tayi kwana biyu tana ciwon k'arya, aiko yasha wahala, don bata komai daga bacci sai kwanciya, har k'iba ta k'ara, Khaleel ya kula da ita sosai.
Haka kuma Deen ya matsa mata da kira, amma ta riga ta fad'a masa yayi hak'uri don ita sam bata hango ta yadda Ammi zata yarda ayi auren ba, bama wannan ba bataga ranar da wannan mai nacin zai rabu da ita ba, sai kawai tayi blocking nasa daga wayanta.
Ganin tayi blocking nasa, hakan ba k'aramin 6ata masa rai yayi ba, kuma yaga da gaske dai take bazata dawo masa ba, hakan yasa ya yanke shawarar me zaiyi a kai.

Haka dai rayuwan ke gudana, nothing special a zaman auren su Hanifah, kullum ana abu d'aya, Khaleel ya d'auki alk'awarin daidaita tsakaninsu, meanwhile kuma Deen na can na neman hanyar da zaiyi revenging akan abunda Hanifah ta masa.


*******

Time went by, wata ranar Friday Hanifah ta fito a garden tana shan iska, Khaleel ta hango ya fito cikin maroon gajeren wando da bak'ar shirt marar hannu, tun daga inda take zaune take k'are masa kallo, ta sha ganinshi cikin singileti ma amma bai ta6a burge ta ba sai yau, wani bau taji yana mata yawo tun daga tsakiyar kanta har tafin k'afarta, da gaske shi d'in take kallo tsakaninta da Allah, sai da ta kusan one minute a nan bata san tana nan ba, sai da k'arar wayarta ya dawo da ita daga duniyar tunani, firgit ta tashi ta duba taga ba Khaleel a wurin, gabanta yayi mummunan fad'uwa, da gudu ta shige gida, yana zaune a palo cikin farar riga da ash wando, ta murza idanunta tana k'ara kallonsa sosai. Tana kyarma tace
"Amma... Amma.... Yaushe ka shigo nan?"
Yayi murmushi yace
"Tun dazu ay ban fito ba ina nan"
Tayi tsai kamar mai tunani can kuma tayi d'akinta da gudu tana sassarfa.
Zama tayi gefen gado image d'in da ta gani na Khaleel a tsaye ya kasa 6ace mata, ga mamaki fal zuciyarta, to ya akayi ta ga Khaleel a waje bayan yace bai fito ba, bama haka ba kayan da ke jikinsa daban da wanda ta gani dasu a waje. Amma fa Khaleel ne tabbas na ga face d'insa.
Haka ta 6ata one whole hour tana sak'e sak'e, daga k'arshe ta yarda cewar ba Khaleel bane ba kawai tayi imagining ne.


Wasa wasa tunanin Khaleel ya ishe Hanifah, abin mamaki yake bata, to meyasa take yawan tunaninsa? Tambayar datake ma kanta kenan ta kasa samu amsarta. Ga kwana biyu sam Khaleel ya rage zama gida, idan ya fita aiki tun safe sai yamma or bayan magrib zai dawo.
Haka zatayi zaune jugum tana tunane tunane, abinda ma yafi damunta sam bai cika sakar mata fuska ba kamar da, ko magana daga uhm sai uhm uhm yake had'a su.
Wasa wasa fa Hanifah ta fara developing a very strong and scary feelings for Khaleel, tun bata d'auki abin serious ba har ta fara jin tsoro, don idan yana wurin haka zata k'ura masa ido kamar zata cinye sa, duk da ko sau d'aya Khaleel bai ta6a lura da hakan ba.
Idan abin ya ishe ta haka zata kulle kanta a d'aki tayi ta kuka ita kad'ai.
"Yanzu da wane ido zan kalli ya Khaleel nace sonsa nake? Ina! Haba ay da kunya bazan iya ba, na gwammace na mutu da nace ina sonsa, ina zan kai wannan abin kunyar haka?"


MSB✍🏼

No comments: