Sunday, 12 February 2017

KHALEEL 7&8

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀


 ®TALENTED WRITER'S GROUP(TWG)✍🏻

                 🎀🎀🎀🎀
                  *UNCLE*
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
                 🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


 February 2017💎

I dedicated this page to my beloved sister Faiza Moh'd Salami (Ammin SS) much love❤️😘

              PAGE


✍🏻✍🏻7&8✍🏻✍🏻


Kwanaki na rikedewa a hankali su koma watanni, watanni su koma shekaru, cikin hukuncin ubangiji yau Hanifah ta kammala nursery dinta ta fada primary.
A lokacin kuma Khaleel na aji uku a fannin secondary yayinda da Saif ke aji daya a fannin secondary.

Haka rayuwar ta cigaba da gudana har ta kammala primary dinta ta fada secondary, wanda a yanzu haka Saif na aji biyar yayinda da Khaleel ya gama zana jarabawarsa ta WAEC yana jiran result dinsa, sai dai bai zauna haka nan ba ya fada computer school don baya son zaman banza.
Abinda Khaleel yasani yana son Hanifah har cikin zuciyarsa, sai dai bai nuna ma kowa ba ya bar abin a cikin ransa, tunda a ganinsa Hanifah yarinya ce yanzu bai kamata ya bijiro mata da zancen soyayya ba, ya dai jinkirta har ta kara girma ta mallaki hankalin kanta ta san ciwon kanta. Amma a 6angaren Hanifah bata ta6a kawowa a ranta cewar Khaleel ba ciki daya suka fito ba, tana masa kallon da take yi wa yayanta Saif.
Ammi kuwa kowa yasan tafi son Khaleel kuma a gaban kowa ma bayyanawa take, tun abin na damun Saif da Hanifah har suka saba da hakan.

Khaleel nada saukin kai, kuma yanada kirki, sai dai shi baya daukar raini ko kadan, sheyasa ma wani lokacin Hanifah ke 6ata masa rai don ta fiye raini, duk da yana yayanta bata bashi girmansa, sai dai fa tana bala'in tsoronsa musamman idan tayi laifi tasan abinda zai biyo baya, sai dai ita sam duk da ta dauke shi a matsayin yaya bata sonsa, haushi yake ba ta kuma rasa dalili, wani lokaci yadda yake damuwa da ita misali, cin abinci, yin wanka, yin homework, ita kuma bata so. Duk wannan abubuwan suke kara bada gudummusa wajen kara tsanarsa, wani lokaci har addu'a take Allah yasa ya mutu ta huta. Wani lokaci idan yana mata wani mayen kallo taji kamar tasa ihu, har tambayar kanta take meyasa Saif bai mata irin kallon? Amma duk wulakanci da mugayen halayen Hanifah baisa ko sau daya yaji baya sonta ba, sai kaunar ta da take dada linkuwa a cikin zuciyarsa, ko laifi tayi masa sai ya kai zuciyarsa nesa yake hukuntata, ko kuma idan ta 6ata masa rai sai yaji duk haushinta ya kama sa, bayan mintina kadan kuma yaji sonta da yakeyi yana karuwa!


******


    *Cigaban labari*


Tana jiyo muryarsa ta hau kyarma tana cigaba da duba socks dinta, dakin ya fada yana kallonta yace.
"Ke! Kefa muke jira tun dazu kamar wasu sa'anninki"
Da sauri tace
"Kayi hakuri yaya, safa ta nake nema bangani ba"
Yace
"Dama kullum daga kice bakiga safa ba, sai kice bakiga rigarki ba, kinsan test gareni karfe takwas wallahi kika sa na makara zaki sani ne"
Har ya kai kofa ta juyo yana kallonta yace
"Na baki minti goma ki karasa shiryawa"
Yana fita ta saki wani irin dogon tsaki wane zata 6alla bakinta. Sannan ta 6alla ma inda ya tsaya harara tace
"Gaskiya Ya Khaleel ka takura min, nikam ka zo kayi aure ka tafi ka barni na wala haba"
Daga haka ta cigaba da neman socks nata har Allah yasa ta gani, da sauri ta karasa shiryawa ta fito, tsaitsaye suke suna jiranta, Khaleel ya kalli agogon hannunsa karfe bakwai da minti talatin da takwas, (7:38 am), kallonta yayi kamar ya make ta, Ammi ce ta sauko tana musu addu'ar sa'a har suka fice, zuciyar Khaleel fes! Saboda addu'ar da Amminsa tayi masa shi yasa shi nishadi, har yayi dropping nasu makaranta sannan ya wuce.

Bayan Khaleel ya fito daga test dinsa yana shirin fitowa daga makarantar ya siya kati wayarsa kirar iPhone ta fara ruri, dauka yayi gami da yin sallama, dayan 6angaren aka fara magana cikin harshe turanci.
"Kaine yayan Aminatu Abdul'aziz?"
Yace "ni ne lafiya dai ko?"
Tace "a'a Hanifah ba lafiya kazo ka dauke ta please"
Yace "ok gani nan yanzu"
Mota ya fada zuciyarsa na bugu da sauri, hankalinsa duk ya tashi, cikin mintina kadan ya isa makarantar, yana shiga office din principal ya iske Hanifah kwance tana kuka dafe da ciki, principal din tayi masa bayanin cewar al'ada ta fara shine kuma abin yazo mata da ciwon ciki. Kunya da haushin principal suka taran ma Hanifah, kamar ta shake ta takeji.
Tace masa zai iya tafiya da ita yanzu.
Kallonta yayi duk ta basa tausayi yace
"Muje ko?"
Ta 6alla masa harara ta mike da kyar suka fito daga office din, tama ki yarda su jera tare, don yadda take ji kamar ya tafi kar ta bisa, yanzu gashi nan wannan principal din ta tona mata asiri gaban wannan mugun. Tayi tsaki kadan yadda ita kadai zataji, da isarsu mota ta bude baya zata shiga ya dakatar da ita.
"Wallahi idan kika shiga baya, bazan kaiki gida ba dama ki dawo gaba"
Yanzu idan ta 6ata motar ya gani kuma fa, wayyo Allah na shiga uku, ta fada a hankali.
Har ya shiga motar yaganta tsaye, ya dan leko da tagar motar yace
"Kin fasa tafiya ne?"
Ta girgiza kanta da sauri, dabara ta fado mata, dankwalinta ta ciro ta shimfida sannan ta zauna tare da juya masa baya, ji take kamar ta shake sa ta huta!!!
Ya kalle ta yadda ta hada rai, yayi murmushi yace
"Kina tunanin idan kika 6ata min mota zan yi fada ne? Kar ki damu ai lalura ce"
Ta runtse idanunta tana mai kara jin haushinsa.
Daga nan bai kara cewa uffan ba har ya isa gida a lokacin da mai gadi ya bude masa get, yasa kan motar ciki.

Koda yayi parking, bata tsaya daukar jakarta ba tayi ciki da gudu kamar ta hade zuciya tsabar haushi, Khaleel yayi murmushinsa mai kyau hade da girgiza kansa, sannan ya dauko mata jakarta yabi bayanta.


MSB✍🏼

No comments: