ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
maryamsbellowo.wordpress.com
*πTagwaye ne? π*
This page is for you maman dana (Maman Nabeel) Allah ya raya mun Nabeelπ
45
Jin motsi ya sa tayi saurin dagowa, ganin Adnan ya fita da sauri yasa ta qara fashewa da wani kukan.
Shi kuwa Adnan a bakin qofa ya tsaya yana maida numfashi idan akwai abinda ya tsana bai wuce wari ba, mutum ne shi mai qyengyemi, a qarshe ma wanka yayi ya fita daga gidan gaba daya don ji yake idan ba fitan yayi ba bazai samu sa'ida ba.
Har bayan magriba ba labarin Adnan, a rana daya duk Khadija ta fita hayyacinta, wuni tayi tana kuka ga kanta dake mata ciwo ko ruwa ta kasa sha, ita bataso taga yana toshe mata hanci hankalinta tashi yake.
Nan ta zauna kan sallaya tayi ta kai kukanta ga Allah, har akayi isha'i, tayi karatun qur'ani tana ta jero addu'oi. Bayan ta gama ta miqe ta linke abin sallar ta shiga bayi ta dauko ruwan turaren wanka da Mami ta hada mata tayo wanka da shi, kamar tayi 6arin turare, duk da haka bata gaza ba ta dauko cream mai matuqar qamshi ta shafa sannan tabi da turaren jiki ta fesa ko wane lungu na jikinta, bayan ta kammala ta dauko kayan baccinta cikin wanda Heenad ta siya mata ta sanya, ta kuma bi da turare masu qamshin dadi ta fesa.
Kicin ta nufa ta hado masa fura da nono mai sanyi, tana shirin sakawa cikin firij taji shigowarsa, gabanta sai da ya fadi, yadda ya shigo kadai ya tsorata ta, gaba daya babu walwala a fuskarsa, fuskar nan a murtuke haka ya shigo, ta daure ta karasa garesa ta kar6o jakarsa, shi dinma daurewa yakeyi amma sam baya qaunar ta matso kusa da shi. Ta qaqalo murmushi tace
"Sannu da dawowa"
Yauwa kawai yace ya wuce dakinsa yayi wanka ya shirya tsab cikin kayan baccinsa riga da wando.
Yana shirin maida towel din da yayi amfani da shi Khadija ta shigo dauke da bowl (kwano) din fura da ludayi a sama, ta jawo table ta dora masa sannan ta zuba masa a cup ta miqe masa, yaqe yayi ya kar6a, yasha sosai hakan ba karamin faranta ran Khadija yayi ba. Ta miqe jiki babu qwari ta fice daga dakin, yabi ta kallo kamar ya kamo ta ya rungume amma yana tsoro.
Kan gadonta ta fada tare da lumshe idanu a yayinda hawaye masu zafi suka gangaro mata, tunani ta shiga yi yadda suka gudanar da rayuwarsu mai dadi a satin daya gabata, amma rana daya wannan abu ya wargaje, wasu hawayen suka kuma zubowa, ta runtse idonta gam tana tuna yadda Adnan ya nuna tana wari me yafi wannan baqin ciki?
Fashewa tayi da kuka mai cin rai sai da tayi mai isarta tukunna tayi shiru.
Can cikin bacci taji motsin bude qofa ta miqe a razane cike da tsoro da fargaba, fitilar dakin aka kunna, Adnan ya shigo ya qaraso kan gadon ya zauna kusa da ita yana fuskantarta. Cikin wata irin murya taji ya kira sunanta.
"Khadija"
Bata amsa ba amma ta kalle shi.
Hakan ya bashi daman kamo hannunta duka biyun ya cigaba
"Kiyi haquri Khadija da abinda ya faru dazu, nima kaina bansan ya akayi ba kiyi haquri kinji?"
Tayi murmushi mai hade da hawaye.
Tausayinta yaji sosai ya rungumo ta yana lallashi, sai dai ko minti daya ba'ayi ba ya saketa yana toshe hanci, ta kalleshi tare da fashewa da kuka, itafa ta tsani toshe hancin nan da yakeyi, hakan yana nufin wari takeyi?
Wannan karon duk da yanajin warin qin fita yayi sai ma kamo ta yayi ya rumgume ta tsam a jikinsa, kukanta yafi komai daga masa hankali.
* * *
Badiya ce zaune kan gado tana waya da zee, zee tayi shewa tana fadin.
"Ai kawata kisha kuruminki nan ba da jimawa ba zai koro ta, shekaranjiya naji inda kika aike ni amma fa yace next zuwa da ke za'aje saboda akwai abinda dole sai kina nan"
Badiya tayi dariyar jin dadi.
"Ai wannan ba matsala bane zanje din nidai idan har buqatata zata biya babu matsala, yanzu anyi wancan aikin kenan?"
Zae tace "eh mana anyi kuma ya tabbatar mana da yanzu ta soma fuskantar tashin hankali a gidannan"
Badiya tayi shewa
"Allah ya bar min ke kawata muna jiran result"
Daga haka sukayi sallama, a yayinda Badiya ta soma hango ta cikin gidan Adnan a matsayin matarsa.
* * *
Goggo tayi danwake mai dadi ta tura Husna ta kai ma Heenad, koda ta shiga tana kan kujera tana chatting, gaishe ta kawai ta aje mata abincin ta fito, Heenad tayi tsaki ta bude kular, da sauri ta rufe tana tunanin ina ita ina hade wannan lumqa lumqan abin, saboda haka sai ta dauko kular ta kai kicin ta aje, falo ta dawo ta jona chargy sannan ta koma kicin ta soma hada shawarma.
A gajiye ya dawo gidan, tun daga bakin qofa ya soma jiyo qamshi na dukan hancinsa. Dama ga yunwa ya kwaso, da sauri ya watsa ruwa ya fito sanye da jar jallabiya marar tsawo sosai sai ya sa dogon wando ciki, kicin ya leqa ganin Heenad tana hada kayan dadi ya sa shi hade yawu, amma yasan da qyar idan zata bashi.
Yana kallonta ta fito ta koma dinning ta soma cin kayanta, ko a gyalenta bata damu da ta ce masa ko zaici ba.
Hakan ba qaramin qona masa rai yayi ba, ya miqe a fusace ya shige daki tare da rufe kofar. Heenad ta ta6e baki, ta kammala cin kayanta ta miqe ta kai kicin sannan ta koma don yin sallah jin an soma kiraye kiraye.
* * *
BAYAN KWANA BIYU
Maryam S belloπ
No comments:
Post a Comment