Sunday, 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 16 to 20

TAGWAYE NE? Na Maryam s bello {16 to 20}
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

16

Yana kallonta, kallo na qurilla yace.

"Ita yarinyar zata kamo "kadangare ta cire kan, ta kawo mana, da wannan kan zamuyi amfani don gudanar da aikin.

Ke kuma, ya nunata da yatsa, ke zaki 'dauko jikin ki yar da shi a jeji kar ki bari wani mahalu'ki ya ganki.
Hajiya Abu ta zaro ido, ta kalli qawarta Hindatu tana kyarma tace.

"Kadangare kuma malam? Gaskiya bazan iya ba.

Hindatu ta make mata cinya tana mata nuni da ido tare da girgiza kai alamun kar tace a'a.

Sannan da sauri Hindatu tace.
"Z... Zasu iya malam"
Malmin wanda bayada maraba da boka ya kece da wata irin arniyar dariya yace.
"Ai yazama wajibi su aikata umarnina in kuwa ba haka ba zamu 'dauki mataki akanku don haka ku ajiye ku'dinku ku tashi ku tafi"
Da sauri Hindatu ta aje ku'din sannan suka bar wurin zuciyar Hajiya Abu cike da fargaba ta yaya zasu kashe 'kadangare.

Ko da suka shiga mota Hajiya Abu ta kalli Hindatu tace.
"Hindatu gaskiya bazan iya ba mu chanza wani wurin ta yaya Badiya zata kashe 'kadangare, ai bazata iya ba saboda tsoronshi da..."
Hindatu ta daka mata tsawa tace.

"Ke Zainab kar ki raina mani hankali tun farko nina saki kice in kawo ki nan kinsan bazakiyi ba kika ce kina so?

 To wallahi ki bu'de kunnenki da kyau kiji abinda zan gaya maki, aikin Zalza'u daban yake dana sauran malamai don kuwa kamar yankan wuqa yake aiki, sai dai ba'a tsallake sharu'dansa, muddin kina so ki zauna lafiya muje a aikata aikinnan a huta kawai, ai dama magnin bari to kar a fara"
Hajiya Abu da tuni jikinta yayi sanyi bayan sun hau titi ta kalli Hindatu tace

"Shikenan muje mu 'dauko badiyar"
Hindatu tayi shewa irin ta 'yan duniya tace.

"Yauwa tawan ko kefa."

* * *

Har kusan magriba Khadija na zaune qarqashin bishiyar nan, duk ta zama weak ga yunwa ga qishirwa na addabarta, bakinta ya bushe qamas, sai yanzu ta soma dana sanin tahowa da tayi, gari ya fara dubu mutane sai harama sukeyi kowa ka gani sauri yake zubawa don samun sallar magrib.
Ta miqe jiki a sanyaye ta soma tafiya ga wani irin jiri na kwasar ta, ga sanyi anayi sai ka'dawa yake sai makyarkyatar sanyi take yi.

Sai da tayi tafiya mai 'dan nisa daidai wata kwana ta hangi wata mata ta fito daga wani shago 'dauke da kwanonin wanke wanke.

Dabara ta fa'do mata tayi saurin 'karasawa wurin da sallama, ba yabo ba fallasa matar ta amsa mata sannan Khadija ta soma magana kanta na 'kasa.
''Don Allah ki taimaka ki bani ruwa inda hali''
Matar ta galla mata harara tace.
''Ruwa?'' Tana wani yamutsa fuska.



Da sauri Khadija ta girgiza kai alamun eh.
Matar ta kalleta a wulaqance tana ta6e baki tace.
"Zan baki ruwa amma sai kin min wanke wanke da shara"
Khadija tayi saurin cewa.

"Na yarda har aiki ma ko wane iri ne zanyi miki dama aikin nake nema"
Sai a sannan matar ta wani washe baki tace.

"To, to ba damuwa muje ki ci abinci ki sha ruwa, matar ta shige Khadija na biye da ita a baya.
'Dan restaurant ne madaidaici, wurin zagaye yake da tabeura da kujerun cin mutum hu'du, wata 'kofa matar tabi, 'dan tsakar gida ne sai can daga gefe 'katon kicin ne wasu mata akalla sun kai biyar keta faman aiki kowa da abinda yakeyi, ita dai Khadija sai bin matar takeyi.

Haka suka isa wasu 'yan 'dakuna guda hu'du jere, na biyun matar tasa mukulli ta bu'de su sauran duk a bu'de suke alamar akwai mutane aciki.
Bayan sun shiga Khadija ta qare ma 'dakin kallo ba laifi katifa ce madaidaiciya da filo sai abin rufa, tayi godiya ga Allah da ya rufa mata asiri da yau da tayi kwanan waje.
Matar ta kalli Khadija da gur6atacciyar hausar ta tace.
"Ga toilet can waje ki shiga in kin fito akwai tuwa a tap sai ki yi allola, kiyi sallah, za'a kawo miki abinci biko?"
Duk da ba duka ta fahimta ba amma ta gane abinda take nufi.
Bayan Khadija ta idar da sallar isha'i tana zaune tana lazumi aka shigo da sallama, wata budurwa ce da bata haura 25 years ba ta shigo da sallama 'dauke da plate da wani a rufe da cokali sama sai kofin ruwa.

Bayan ta aje ta kalli Khadija fuskarta 'dauke da murmushi tace.
"Idan kin gama kizo inji Anty tana son magana dake"

Bayan ta shafa tace "to" tare da mayar mata da murmushin

Sai da budurwar ta fita sannan Khadija ta jawo filet 'din ta bu'de shinkafa da miya ce da nama, Khadija tayi bismillah taci tayi nak tasha ruwa, tayi hamdallah ga Allah.

Bayan ta huta ta miqe don kiran Hajiya.

Maryam S belloπŸ’–
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

17

Wata qofa tabi bayan ta tambayi inda Hajiyar take, wani 'dan gida ne wanda ya sadata da qofar da ta fito, gidan kamar a ha'de yake sai dai zaka iya shiga ta qofa daga 'dayan sashen.

Daga bakin qofa ta shiga doka sallama, matar na zaune kan kujera cikin madaidaicin falon, 'yan mata guda biyu masu matuqar kama da matar daga gani yaranta ne 'daya zata kai shekara 15 'dayar kuma 18 years, dukansu suna kallon mbc max, matar na rubuce rubuce tana qirga ku'di ta juyo ta kalli Khadija tace.
"Come in"
Khadija tayi tsaye don bata gane abinda matar tace ba sai zare ido take.

Sai a karo na biyu matar ta sake kai dubanta ga Khadija tace.
"Sorry i mean ka shiga"
Sai a sannan Khadija ta shigo ta samu wuri daga qasa ta zauna ta gaishe da yaran suka amsa fuska a sake, sannan ta gaida matar ita ma ta amsa sannan ta fara magana da hausa don ta fahimci Khadija bata iya turanci ba.
"Yaro ko zaka iya fa'da min sunaka?"
Khadija tayi murmushi tace.

"Sunana Khadija"
Matar tace "nice name, to daga ina kake and ina iyayenki?"
Khadija tace.

"Kano kuma iyaye na sun mutu" saboda ita sam batasan me zatace mata ba.
Matar ta jinjina alamar tausayi tace

"Bakomai, ok ni sunana Taufiqat, a nan garin nake zaune mijina ya mutu ga yara na nan Guda biyu, ni ke running restaurant 'dinnan shekara kusan bakwai kenan bayan rasuwar mijina, so baki da kowa nan right?"
Khadija ta girgiza kai alamun eh tace

"Haka ne"
Taufiqat tace "ok ba damuwa zaki cigaba da zama a nan 'dakin da na kai 'dazu shine 'dakin ki, daga gobe zaki fara aiki, zaki zama waitress ma'ana mai serving abinci ma customers 'dina idan sun bu'kaci hakan, kinyi karatu?"
Khadija ta girgiza kai alamun a'a.
Taufiqat tace "ok zansa Lasina (babbar 'diyarta) tana koya miki karatu idan kin tashi daga aiki saboda aikin yana bu'katar iya ha'da baqi, atleast ki 'dan iya wani abin is something.

Sannan magana ta gaba shine kiyi a hankali saboda ba'a 6ata ma customers 'dina rai da lokaci da zarar sun bu'kaci abu kiyi gaggawar kai musu sannan banda raini, bana son raini ki zauna da kowa lafiya sai abinda nafi tsana a rayuwata shine sata kar ki yarda na kamaki kina min sata idan ba haka ba a bakin aikinki bana tolerating sata, i think that's it for now yanzu dare yayi kije ki kwanta sai gobe.

Au na manta ki dinga tashi da wuri duk wata zan dinga baki 5k dubu biyar ok?"
Khadija ta girgiza kai a sanyaye ta miqe tayi musu sai da safe ta koma 'dakinta.

Koda ta koma wanka tayi tazo shiga daidai 'dakinta ta jiyo wasu mata na gulma.
"Uhm su Hajiya kuma ina aka samo wata karuwar, ina amfani bakada aiki sai kwaso 'yaran mutane kana 6ata su? Wasu ma karuwai ne su ke kawo kansu"
"Bari kedai Binta ga yarinya kyakkyawa amma za'a 6ata mata rayuwa, har na tasauya mata wallahi"
"Kinsan wani abu Harira? Wannan sabuwar yarinyar data 'dauko wayo takeyi musu tace zata 'dauke su aiki a hankali take jan ra'ayinsu har ta lalata su, kin manta farkon zuwan Zuwaira? Yarinya saliha amma ji yanzu yadda ta koma kai Allah dai ya kyauta.
"Amin amma dai Hajiya anyi girman banza ita dai indai harkar ku'di ce zata iya komai, wallahi don dole nike zaune da ita don kuwa tayi girman kwabo"
"Ai Jamila dan ma baki kaini da'dewa ba da kinga manyan alhazawan nan na zarya ta nan kinsan da wani abu sheyasa nake ba yaran shawara sai sunyi takatsatsan da Hajiya amma zakiga idan dama halinsu ne baji suke ba, don ina tunanin inje in sanar ma sabuwar yarinyar nan sai tayi a hankali kar aje a kaita a baro yarinya 'karama a lalata mata rayuwa"
"Tabbas haka ne da kuwa kin kyauta kuma kinsamu lada gobe idan Allah ya kaimu muje mu garga'de ta in ma bataji ba ai dai mun fita haqinta"
Daga nan bata qarasa ji ba ta shigo 'daki da sauri gabanta na fa'duwa' a daddafe ta gama shirin bacci tunani kala kala ta shiga yi lallai Allah ya taimaketa da ta jiyo wannan labari ai da ta ka'de, ko sun fa'da mata goben zata nuna bataji ba,dole ta nemi mafita da wannan tunanin har ta kwanta tayi addu'ar bacci tare da yima Ummanta addu'a kamar kullum daga nan wani irin bacci mai nauyin gaske ya kwashe ta.

* * *

10:45 pm
Adnan ne yake saukowa daga bene sanye da dogon wando na bacci sai singilet fara, Ummi da Hajiya Abu na zaune falo suna tattaunawa.
"Hajiya ni sai nake gani kamar Badiya da Adnan san juna sukeyi, ko baki lura ba?"
Ummi tayi yaqe tace

"Ban lura ba gaskiya ke a ina kika ga hakan?"
Ta wani yi dariyar munafunci tace

"Kama suyi nayi suna soyayya". Ta fa'da tana sosa qeya.
Itadai Ummi bata ce komai ba saboda tasan halin Zainab munafuka ce ta qarshe, ga son abun duniya

Saboda takaici ma Adnan fasa shan ruwan yayi dama shi ya sauko sha ya koma yana Allah ya tsare shi da auren Badiya ai ko me zai faru sai dai ya faru amma bazai ta6a auren Badiya ba, zancen banza ma kenan ai sai ya koya mata hankali, yaji wata tsanarta ya mamaye shi ga haushin Hajiya Abu dukkansu munafukan banza daga Abun har Badiyar kuma sai ya 'dauki mataki akanta da garga'din kar ka ta qara shiga harkarsa.

* * *

Washe gari Hajiya Abu tayi wa maigidanta qarya wai zataje gaisuwa an mata rasuwa suka fita itada Badiya, Hindatu nacikin mota tana jiransu da sauri suka bar unguwar.
Bayan sun fito daga mota Hajiya Abu tayi wa Badiya bayanin aikin da zasuyi muddin tana son soyayyar Adnan to dole ta aikata hakan, duk da tanajin tsoro ta dake tare da 'kudurin aikata hakan indai har zata samu biyan bu'katarta.

Dukkansu sukayi shewa cike da jin da'di.
Suka 'dan shiga cikin daji inda bamai ganinsu wurin akwai 'kadangaru don haka dama da wuqarsu suka zo don haka Hindatu ta kamo 'daya dama ta saba irin aikin nan don haka ko a jikinta.
Badiyar ta kurma uban ihu qaton qadangare marar kyan gani, yayi quri yana kallonsu, sai kyarma take fitsari ne ka'dai ya rage tayi.
Hindatu ta daka mata tsawa ta ce dole fa sai anyi in ba haka mutuwa zasuyi ko su haukace, jin haka yasa Badiya tayi kukan kura ta saita kanshi ta fe'de kan.

Sai dai me? 'Kadangaren ta gani bisa hannunta ta kurma uban ihu tana neman agaji.
Su hajiya Abu suka tambayeta ko lafiya ta nuna musu hannunta tana ihu.

A tsorace suka duba amma basuga komai ba ita kama kuma Badiya sai ihu take tana neman taimako.

Ganin haka yasa Hindatu ta zame ta ja motarta ta bar su nan, ba abinda takeyi sai ihu wai yana cizonta, ita dai Hajiya Abu bataga komai duk ta ru'de ta rasa abinyi.

Maryam S belloπŸ’–
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

18

Badiya ba abinda take sai rusa ihu, ita bilhaqi 'kadangare take gani bisa hannunta yana gartsa mata cizo, Hajiya Abu ta ru'de ta rasa inda zata sa ranta, da qyar da ji'bin goshi ta samu tayi shiru amma ba abinda take sai kuka, Hajiya Abu ta duba gabas kudu da arewa ba Hindatu ba labarinta, abin ya matuqar qona mata rai, sai kace ba itace ta kai su wajen malamin nan ba lallai ma Hindatu a cewar Hajiya Abu, ta saki tsaki cikin baqin cikin abinda tayi masu, ta jawo Badiya tace kalle ni nan Badiya indai ina raye bake ba Adnan wallahi kin rabu dashi kenan har abada haba sai kace dole, to ya zama dole ki rabu dashi kalli wahalar da muka sha saboda shi, shi fa ba sanki yake ba.

Badiya ta razana ta ta fasa ihu jin ance zata rabu da masoyinta ita fa jin Hajiya Abu kawai amma ba wanda ya isa ya raba ta shi, tana kuka wiwi Hajiya Abu ta tari taxi, yanzu kukan ya lafa don ta bar ganin 'kadangaren sai ra'da'din azaba hannun ke mata, suna isa gida suka fito zuciyoyinsu a cunkushe.

A bakin gate sukayi kaci6us da Adnan da alama fita zaiyi sanye yake cikin blue 'din yadi mai 'dan karan kyau ya zauna das a jikinsa kasancewar yana da 'dan jiki ya sanya kayan suka kama shi kuma sukayi masa kyau matuqa.

A nan Badiya ta shagala da kallonsa ta ma manta abinda ya sameta yau ji take kamar ana rura mata wutar sonsa. Sarai ya lura da yadda take kallonsa kamar zata cinye sa, sai kuwa ya basar da ita ya cigaba da tafiya don wata irin muguwar tsanar ta yakeji daga ita har yayar tata dama can baya 'kaunar halinsu.

Da sauri Hajiya ta fizgo hannun Badiya suka shige ciki.
A falo suka tarar da Ummi tana shan fura ta kallesu tayi musu sannu da zuwa, ita kuwa Hajiya Abu wata irin kunya ta kamata ji take kamar ta gano abinda suka aikata, don haka kanta a qasa suka shige 'daki, suna zuwa ta 'dauki waya ta kira Hindatu da niyyar zazzaga mata bala'i amma bata 'daga ba sai da ta kirata ya fi a qirga amma fir taqi 'dauka kuma bawai don bata gani ba a'a hasalima wayar na hannunta, idan ta 'dauka bata san me zata ce da qawar tata ba.

Haka ta qarashe kiranta ta gaji ta qyale ta.
Da daddare haka Badiya ta hana su bacci qadangare ya dawo mata, duk gidan ya hargitse ba wanda ya rintse, Ummi ta kamo hannun nata ta tofa mata addu'oi sannan aka samu lafiya, koda ta kwanta bacci sai da tayi mafarki da qadangaren nan wai yana ta binta a daji sai gudu take tana ihu, sai da ta gaji ta tsaya sai qadangaren ya kalle ta yace.
"Baiwar Allah akwai dalilin da yasa nike binki, naga kina nema ki kauce hanya don ki samu biyan buqatarki, to kisani Allah baya bacci kuma baki ta6a samun abinda ba naki ba, har abada kuwa me zai hana kiyi addu'a da neman za6in Allah? Ya kamata ku zauna kuyi wa kanku fa'da keda 'yar uwar ki kusani idan kuka cuci wani Allah zai saka masa"
Kawai ya 6ace a gigice ta farka ba salati ba komai, koda ta farka sam kasa yarda tayi wai mafarki tayi tuna maganun qadangare ya sanya jikinta yin sanyi qalau tayi zaune jigum tana tunanin abinda maganganunsa suke nufi.

* * *

Khadija ta cigaba da aikinta ba laifi tana qoqari kuma Laseena na koya mata karatu tana ganewa, kullum tana serving ma customers abinci har ya zamana Taufiqat tana matuqar samun costumers ba kamar dabanda zakije ki iske mutane 'yan ka'dan, sai kuwa ta qara son Khadija saboda yarinyar akwai nutsuwa da sanin ya kamata tunda tasan aiki taje to kuwa bata wasa gashi har yanzu har ta iya ha'da sentence da turanci kuma idan akayi mata magana zata mayar, duk ma'akatan wurin su Binta suna sonta tunda sukace zasu je su fa'da mata halayen Taufiqat koda sukaje bata nuna ta sani ba sai ma godiya ta yayi musu tace zata kiyaye tun daga lokacin Khadija ke birgesu su har mamaki suke suna tambayar kansu wai Khadija anya jinsin Hausa ce ko kuwa fulani don sau da yawa su kance zasu kama mata kanta don suga kanta ta kanyi dariya tace ita bata kitso saboda tun tasowarta bata qaunar kitso tun tana qarama gashi Allah ya bata gashin masha Allah, har shigowa suke 'dakinta musamman idan ta fito wanka suyi ta kallon gashinta, don ma baya samun kulawa sosai yadda ya kamata ay da sai ya fi haka, komai nata burgesu yake gata 'yar fara lol.
Yau ta kasance Wednesday Khadija na aikinta kamar yanda ta saba wani mutum ya shigo babban mutum ne akalla zai haura saba'in zuwa sama, wata mata ta kawo wa Amala da miyar 'danyar ku'bewa mutumin ya kirata, bayan ta ajiye ta isa gareshi ta gaida shi da ladabi sannan ta tambaye shi abinda za'a kawo masa. Ya kalle ta tun daga sama har 'kasa doguwar rigar atamfa ce ta sanya ta 'dan ko'de ja da ruwan hoda sai ta sanya hijabinta bata kai qasa ba amma ta wuce gwiwa, ya kalli fuskarta sannan ya sauke ajiyar zuciya yace.
"Rice and stew with salad then a cold drink"
Ta amsa da ladabi sannan ta wuce don kawo masa, tunda ta tafi yake kallonta wata irin tsananin sha'awarta ya kama shi, yarinyar ta ha'du ya raya a ranshi sannan ya saki murmushi, daidai nan ta dawo 'dauke da faranti mai filet 'din shinkafa da miya sai salad 'din sai ta ajiya masa ta juya ta bu'de firij ta 'dauko fanta mai sanyi ta aje masa sannan ta juya, duk wani motsinta a idanunsa, haka ya dinga kallonta tana serving abinci, kallon sha'awa shikam yarinyar ta masa sai dai bata waye ba, koya zai wayar da ita har ta bashi kanta (Subhnalillah), ita kuwa bata lura da kallon ba saboda bata damu da kallon kowa ba, aikinta kawai tasa gaba, ya kasa daurewa ya sanya 'daya daga cikin ma'aikatan suka kira masa Taufiqat.

Maryam S belloπŸ’–
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

19

Zainabu ce ta kutsa kanta falon madam Taufiqat zaune ta taradda ita tana waya da alama wayar nada matuqar mahimmanci don haka sai ta ja ta zauna daga gefe ta kai duban ta ga tv inda yaran ke kallon Mbc 2 har sai data qare sannan ta sanar mata saqon Alhaji akan cewar lallai lallai yana son ganinta yanzu, farin cikinta sam ya kasa 6oyuwa har bayan fitar Zainabu tana ayyanawa a ranta zata samu wani abu daga Alhaji, don haka da hanzari ta fice tana gyara daurin zaninta.

A inda suka saba haduwa wato daga waje a can ta same shi tsaye jikin motarsa ya hade hannuwa, bayan ta qaraso ta dube shi cike da farin ciki tace.
"Alaji alaji! Alaji namu, ta samu kenan?"
Ya saki murmushi yana dubanta yace

"Kwarai ma kuwa to basai an tsaya wasa ba nidai naga daya daga cikin yaranki ina so yarinyar ta mani sai dai matsalar bata waye ba"
Madam ta dube shi tace

"Wace kenan kasan yaran nawa sunada yawa"
Oho yace "bansan sunanta ba tana nan dai zaki ganta fara doguwa marar jiki tana da kyau yarinyar amma cikin hijabi take"
Madam tayi shewa a lokacin data gano Khadija yake nufi ai tuni ta washe baki tana fadin

"Ah ai babu matsala Alaji kar ka damu ni nasan yadda zanyi mata har ku hadu kar ka damu yanzu dai inji dumus tukunna"

Ta fada tana miqa misa hannunta alamar ya zubo mata.
Ya kece da dariya yace

"Madam madam! Madam da kudi to ga 100k ki rike idan aikin ya kammala zan kara linka miki wasu"
Tayi shewa tana masa kirari tana shafa kudin kai kace wata mayyar, daga bisani sukayi sallama ya shige motarsa ita kuma ta wuce cike da farin ciki.
* * *

Tuqi take sharawa hankalinta kwance tana tafe tana jin sautin waqa tana taunar cingam, Abida na gefenta tana mitar ta rage gudu hakan bashida wani amfani, da ta gaji da magana sai ta rabu da ita ta cigaba da chatting dinta saboda Heenad bajin shawara take ba.

Wani bawan Allah ne tsoho akalla zai kai 70 zuwa sama ya taho dauke da galon din mai yana kokarin tsallaka titi, a daidai nan wayar Heenad ta fara ruri, tana neman daukar wayar ne ta ji ta bugi abu, tayi saurin tsayar da motar tana buga tsaki.
A rude Abida ta fito ganin tsoho kwance kansa na zubar da jini ya sanya ta qwala ihu ganin Heenad na cikin mota kamar ba itace ta kade mutumin ba ganin haka yasa ta qwala mata kira tana fadin
"Haba Heenad ya zaki kade mutum amma kiyi zaune a mota? Wallahi na tsani halinki kwata kwata baki san datajar dan Adam ba ki fito mana mu taimka masa!"
Tsohon ya miqe da qyar dafe da goshi inda jinin ke zuba yace

"Nagode yarinya qyale ta zan kai kaina asibiti bakomai"
"A'a ayi haka? Ai haqqinta ta kula da kai tunda ita ce ta ka'de ka, Heenad ki fito mana!"
Sai a sannan ta fito cike ta qasaita da yanga kamar batayi komai ba, bata ma damu da ganin halin da mutumin yake ciki ba kawai tana fitowa tayi tsaye qiqam kansu tana taunar cingam dinta hankali kwance.
"Mtsw laifi na ne? Ni nace kana ganin mota amma ka taho irinku ne ke jawo wa mutane accident"

Tana fadin haka yayinda take duba ko akwai abinda ya sami motarta.
A haka Abida ta cigaba da yarfa ma qawar tata masifa ita kuwa gogar ko a jikinta, ta juyo da niyyar ce ma tsohon ya tashi zata qara gaba ta hango shi yana fitowa daga motarsa da sauri yana qarasowa inda suke.
Cak ta tsaya har numfashinta na neman daukewa, tunda take bata ta6a ganin mutumin da ya burge ta ba a rayuwarta ba kamar wanann gayen, gabanta ya cigaba da harbawa kasa tsayuwa tayi ta jingina jikin mota, bata san me ya auku ba sai dai dai taga Abida da shi suna qoqarin sanya shi cikin motarsa sai faman sannu yake masa, ta dube shi fuskar nan tashi a hade kamar bai ta6a dariya, ta saki tsaki tare da maqe kafada irin oho dinnan ta shige mota. Amma still ta kasa dena kallonsa.
Abida ta qaraso cike da jin haushin qawarta tana fadin.

"Ke dai kinji haushi wallahi to kin ga wadanda suka fimu sanin darajar mutum can ya zo ya daukeshi zai kai shi asibiti, ke da bige shi amma wani ne zai kaishi asibiti? Kedai Allah ya shirye ki amma kam ki chanza halinki wannan ba yi bane, in kinsan yadda mutumin nan yaji haushinki ko? Sai mita yakeyi"
Bata ko kulata ba illa murza key da tayi bayan motar ta tashi tace.

"Kanki ake ji dai"
A haka suka qarasa gida Abida ko sallama batayi mata ba ta shige gidansu ita kuma Heenad ta juya kan motarta zuwa gidansu a lokacin qarfe biyar da rabi na yamma.

* * *
Washe gari misalin qarfe tara da minti hamsin na safe Khadija na yanka albasa Halima daya daga cikin ma'aikatan Madam ta ce ma Khadija.
"Khadija kizo inji Madam"

To tace bayan ta miqe ta dauraye hannuta ta zura hijabinta ta bi bayan Halima.
A waje ta iske ta tsaye Khadija ta gaishe ta da ladabi bayan ta amsa sa'adda ta miqa ma Khadija dubu biyar tace.
"Ungo kasuwa zakije ga list din kayan nan na rubuta miki ki hanzarta ki dawo fa"
To tace bayan ta kar6a kudin ta juya ta cigaba da tafiya da sauri, bayan tayi nisa Hajiyar tayi wata dariya wadda ita kadai tasan ma'anarta sannan tace.

"Zakiyi bayani yarinya"
A haka Khadija ta cigaba da tafiya har ta isa bakin titi ta tari mai taxi ta fada masa inda zai kaita.

Sunyi tafiya mai nisa Khadija ta kalle shi da mamaki tace

"Bawan Allah kasuwa fa zaka kaini"

Kasancewar ba yau ta fara zuwa ba taje akalla kusan sau uku sheyasa ta gane cewar ba kasuwa zai kaita ba
Bai ce komai ba illa fakin yayi gefen wani gida yace ina zuwa zan sayi wani abu ne, bayan shigarsa da kamar minti biyar ya fito shida wani babban mutum suka qaraso ta inda Khadija ke zaune, mutumin ya shafi gemunsa da ya cika da furfura yana murmushi yace.

"Kayi kokari Bala na goge sosai"

Balan yayi murmushi bayan Alhaji ya miqa masa kudi da Khadija bata san ko nawa bane, Ta kallesu da mamaki tana nazarin manufarsa can ta tuno da maganar su Binta da suka fada mata.

Gabanta yayi mummuma faduwa, ta soma salati a hankali tana duk addu'ar ta tazo bakinta.
"Fito yarinya ki amshi saqo inji Madam yi sauri ki fiti mu tafi"

Cewar Bala kamar gaske, tayi murmushi.

(Ni zakuyi wa wayo?) ta fada a hankali.

Ta fito kamar gaske harda cewa to, sun fara tafiya kenan ta kwashi qasa mai yawa ta watsa musu a ido, tana jiyo ihunsa a yayinda da ta fara gudu don neman tsare mutuncinta da martabarta a matsayinta na ya mace budurwa, gudu take ba tare da tasan ina take zuwa ba, gabanta sai faduwa yake ita kuwa sai haqi take yi tana cigaba da gudu.
* * *
"Ummi gida zan kaiki kenan ba inda zaki je?"

Cewar Adnan yayinda yake tuqi ita kuwa mahaifiyarsa na baya ta amsa da.

"Eh gida zaka kaini Adnan"
Ba tare da yasani ba sai ji yayi ya bugi mutum, tayi sama ta fado tim qasa. Ummi tasa salati a yayinda da take fitowa daga motar shima haka Adnan hankalinsa a tashe duk suka fito, a lokacin mutane har an fara taruwa kowa da abina yake fadi.
Duban yarinyar yayi jini na zuba daga kanta da kafarta, gabansa ya fadi, ras!  

Ya gane ta, amma me takeyi a nan kuma da wannan shigar yarinyar da ya san yar gayu ce ga kuma wulakanta mutum, to me takeyi haka da shigar talakawa?"
"Adnan kamo ta mu kaita asibiti don Allah mun shiga uku mun kashe yar mutane, kamo ta mu sa ta mota!"

Ummi ta fadi hankalinta a tashe, haka suka kinkimeta ta suka sanya ta mota, Adnan ne ya ja motar da sauri zuciyarsa cike da tambayoyi kala kala.

Maryam S belloπŸ’–

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

20

Hankalin Ummi ya tashi matuqa ganin yarinyar da batada maraba da gawa duk gaban rigar ta ya jiqe jagab da jini, ta riqe mata hannu tana kwararo addu'ar Allah yasa tana da ranta, ba'a dauki tsawon lokaci ba suka isa Federal Medical Center, Jabi Abuja, da sauri Adnan ya fito ya sanar ma Nurses suna da marar lafiya kuma emergency, haka suka fito da sauri dauke da gadon marasa lafiya, Ummi na tsaye gaban motar tana faman safa da marwa hankalinta tashe, ganin mahaifiyarsa cikin wannan hali ya sa zuciyarsa tsinkewa take qwalla ta cika mai idanu, da taimakon nurses da taimakon Ummi aka dora Khadija kan gadon nan ba tare da 6ata lokaci ba akayi ciki da ita, Ummi na qoqarin bin bayansu Adnan yayi saurin riqo mata hannu, ta kalle shi hawaye na neman zubo mata, yayi qoqarin kwantar mata da hankali akan cewar yarinyar na raye amma ina Ummi gani take kamar ta mutu, sanin Ummi da tausayi ita haka take tana da matuqar tausayi, da qyar ya samu ta dan kwantar da hankalinta nan tace ya kira gida ya sanar musu abinda ya faru, ya tabbatar mata zai kira Abba wato mahaifinsa da sauran yan gidan.
Dr. chimaobi Onwuzuruoha, shi ke kan duty kuma babban likita ne na ko wane fanni don haka ko wane case yana solving dinshi, take shi aka sanar mawa akwai patient an kawo tana bukatar taimakon gaggawa ba tare da 6ata lokaci ba ya kar6i case din, koda yaga yanayin jikinta ya tabbatar sai an mata aiki, take aka shiga da ita tiyata, bayan su Ummi sun biya duk kudin da ake bukata na aikin suna tsaye suna jira, Ummi addu'a kawai take duk da likitan ya tabbatar musu tana raye amma gani take kamar mutuwa zatayi.
An dauki kusan minti hamsin kafin likitan ya fito sanye da kaya kalar green na tiyata, baqi ne amma ba wulik ba, mai dan jiki sanye da farin glass a idanunsa, Adnan dake tsaye shima fuskarsa dauke da damuwa tuni Ummi ta taso da sauri ganin Dr. chimaobi, ya gaisa da Adnan ta hanyar miqo hannu saboda ya gane shi a matsayinshi na qawarraran likita, sannan cikin harshen turanci Dr. chimaobi yace musu.
"Ku same ni office yanzu, akwai maganar da zan fada muku"
Gaban Ummi ya fadi, shima kansa Adnan din sai da gaban nashi ya fadi zugui zugui suka bi bayan biyan likitan jiki a sanyaye.

Tare suka shiga office din nasa bayan ya zauna ne ya nuna masu kujera alamar su zauna, sannan wata nurse ta shigo ta miqa mishi wani file na patients, bayan ta fita ya Kalli su Ummi yana rubuce rubuce, yace cikin harshen turanci.
"Ya sunan patient din tamu?"
Ummi da Adnan suka kalli juna, Ummi tayi yaqe kawai tace sunanta Khadija. Adnan ya kalle ta cikin ransa yace meyasa Ummi bazata fadi gsky ba tace bamu santa ba?"

Likitan yayi murmushi bayan ya rubuta yace.
"Ya kuke da ita?"
Duk sukayi shiru, Dr chimaobi ya gyara zaman glass dinsa sannan yace.
"Kar ku damu dokarmu ce sanin dangantaka ko alaqar dake tsakanin wadanda suka kawo mana marar lafiya saboda kunsan duniya ta zama abin tsoro, idan muka fuskanci bayada alaqa da marar lafiyar muna iya yi masa tambayoyi akai, so kar ku damu amsa kawai zaku bani zan rubuta details na yarinyar.

Ummi tayi karfin halin cewar matar dana ce, take Adnan ya kuma kallonta sai dai gudun 6acin ranta da kuma bayanin da likitan yayi ya sanya shi yin shiru.

Bayan likitan ya gama tambayoyinsa da rubuce rubucensa ya dago da dubansa garesu yace.
"Mun duba yarinyar sosai na farko dai tana bukatar jini don bleeding tayi goshinta ya fashe sosai, sai kafanta shima ta mugun buguwa i think kamar ma gocewa tayi a kafan ga ciwuka a fuskanta da jikinta ba iyaka, so yanzu mun mata duk abinda ya kamata abinda ya rage jini ake bukata within 24 hours mun dibi jininta yana can lab ana testing da an gama zamu duba muga wane irin group ce ita but before then ko kunsan blood group nata?"
Suka girgiza kai alamar a'a.
Yayi murmushi yace

"Babu damuwa ai ana testing a lab da an kawo sai a duba idan kuma siyowa za'ayi duk daya ne, yanzu zamuyi moving nata zuwa daki ga room number na dakin, ya miqa musu file"
Ya miqa ma Adnan file din nata tare da miqewa tsaye suma sai suka tashi tsayen, ya sanar musu zai je ayi moving nata kuma yayi warning nasu banda hayaniya ba'a son mutane da yawa suzo.

Room 5 aka kaita, bayan ya kammala gyara ta ya nuna ma nurse din abinda ya kamata tayi ya fice,su Ummi na tsaye bakin qofa, ya kalli Ummi yace.
"Hajiya ga yarinyar nan please a kula da ita sosai saboda tana bukatar hakan, yanzu zata zama unconscious har sai nan da some hours maybe ma har sai an sa mata jini sheyasa nace ayi saurin samo jinin, yanzu zanje lab din nagani ko an kammala"
Sukayi masa godiya sosai bayan ya tafi nurse din ta fito dauke da tray na magunguna, ta sanar musu zasu iya shiga zata dawo nan da minti talatin ta mata allura"
A hankali suka tura qofar dakin, bayan sun shiga ko wanne jikinshi yayi mugun sanyi barinma Adnan da yake ganin sanadinsa hakan ta faru, a hankali ya kai dubansa gareta itama Ummi tsaye tayi tana qare mata kallo cike da tausayin yarinyar.

Kanta gaba daye an nade da bandage da hannunta, kafarta kuwa gaba daya an mata dauri alamun an kare an daura ta bisa katon filo, banbacinta da gawa kawai numfashinta dake fita a hankali, amma daga ganinta tana mugun jin jiki. Dukkansu suka sauke ajiyar zuciya, ko wane jikinsa yayi sanyi qalau, shi kuwa Adnan banda tambayoyi da saqe saqe ba abinda zuciyarsa keyi, ya qara dubanta tabbas itace amma amsoshin da yake nema yasan bazai same su yanzu ba. Suna nan har kusan sha biyun rana, kuma asibitin ta cika da yan uwa harda Abba, duba ta kawai sukayi suka tafi saboda likita ya hana zama su Ummi ne kawai da Adnan shima Adnan din bayan sallar la'asar zai tafi saboda yanada aikin da zaiyi a wannan lokacin, sai dai kafin su tafi Ummi ta sanar musu ana bukatar jinin da za'a sa ma yarinyar amma zata kirasu kome kenan, saboda tun dazu likita yace ze dubo ko result ya fito amma shiru kakaeji.
Sai kusan sha biyu har da rabi sai ga liktan ya dawo dauke da takardun result din, su Ummi duk sun qosa suji don a bawa yarinyar taimakon da ya dace.

Ba tare ba 6ata lokaci ba kuwa ya sanar musu blood group na yarinyar O negative ne, take Ummi tace Alhamdulillah koni zan iya bata kenan? Adnan yayi saurin cewa a'a Ummi keda bakida isassar lafiya ya zaki bada jini? Ki bari kawai ni zan bada, cikin farin ciki Ummi tasa ma Adnan albarka shi kansa ya san jihadi yayi kuma taimako ne, meye to don ya bata jini ai daga nan ma kadai duniya ta koya mata hankali da sanin darajar dan Adam, a nasa tunanin kenan.
"Ok Adnan muje ko don a gwada jininka aga koba bakada wata matsala ko"

Ummi tayi masa fatan dacewa sannan ta shige toilet don dauro alwalla kasancewar azahar na neman kunno kai.

Maryam S belloπŸ’–

No comments: