Sunday, 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 52

๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ❤
    ๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ
        ๐Ÿ’š๐Ÿ’™
            ๐Ÿ’™


MSB๐Ÿ’–


maryamsbellowo.wordpress.com


®TALENTED WRITER'S GROUP (TWG)✍๐Ÿป


*๐Ÿ’•Tagwaye ne? ๐Ÿ’•*



52

Bata ankara ba sai jin bakinsa tayi a nata, tunda sukayi aure Khadija bata ta6a maida masa da martani ba, kullum shi ke rawarsa da kidinsa, amma yau dinnan sai ta tsinci kanta da maida masa, gaba daya ya gama gigitata ji takeyi qaunar da take masa ta linku a cikin zuciyarta, sannan yadda takejin gaba daya ta sallama masa zuciyarta da kuma ruhinta! Sakinta yayi da sauri a sanadiyyar motsin tafiyar mai gadi da sukaji, suka tsaya suna maida numfashi. Wucewa yayi wanda kamar ba'a abinda ya faru ya gaishe da Adnan ya qara gaba don dama bai gansu ba.
Ta dauki hoton motar ta nuna ma yar uwarta rabin ranta, murna a wajen Heenad ba'a magana, ta taya ta murna da kuma fatan akhairi.

Adnan da kansa ya dauki Khadija suka tafi koyon mota, tun tana jin tsoro har ta saki jiki ta fara koya.
Haka kullum suke fita da yamma kasancewar lectures din Khadija na safe ne.
Cikin kwana hudu kacal Khadija ta koyi mota wanda har tana kai kanta makaranta ta maido kanta.

Wata rana Khadija suna zaune a bakin department nasu, itada da wata kawarta mai suna Safinat itama matar aure ce, yaranta biyu, baifi minti goma ya rage malamin ya shigo ajinsu ba, hira ce sukeyi sosai a yayinda Safinat ta kalli Khadija tana dariya tace.
"Wato Khadija ashe mun kusa zama mama?"
Khadija ta kalle ta cikin rashin fahimta tace
"Bangane ba?"
Safinat dariya tayi sosai tace
"Uhm alamu nagani a jikinki Khadija, ina kyautata zaton haka"
Khadija tayi shiru tana nazarin maganganun Safinat, sai can ta kalle ta da mamaki tana zaro idanu waje
"kina nufin ni?"
Safinta tace
"To da wa nake? Mu biyu fa muke zaune a nan, amma idan baki yarda ba kije asibiti a gwada ki, ina tunanin ke ba mai laulayi bace ba"
Khadija tayi shiru maganganun Safinta sun dan girgiza ta wai ace ita da ciki, tace na shiga uku a hankali.
Safinta ta dafa ta
"To menene a ciki? Kike wani jin tsoro kefa matar aure ce, kin cika shirme Khadija kinga Malam Aminu can yana tafe tashi mu shiga kafin ya karaso"
Haka suka miqe jikin Khadija a sanyaye har suka shiga lectures tana tunani.
Bayan sun fito tana wannan tunanin, tana tafiya inda motarta take ta hadu da Heenad tana tafiya da wata kawarta. Nan suka gaisa take tambayar Heenad kota gama ne su tafi tare, Heenad tace a'a yanzu ma zasu shiga wata.


* * *

Badiya ce zaune kan keken guragu (wheelchair) a gaban madubin dakinta take, tayi tsai tana kallon fuskarta ta madubi, a yayinda ta zurfafa kwarai cikin tunani, kwarai tayi dana sanin abinda ta aikata a baya sai dai tafi ganin laifin yayarta da tun farko take biye mata suna aikata sa6on Allah, da ace yau iyayensu nada rai da ta tabbatar bazata ta6a aikata aiki makamancin wannan ba, don tasan halin iyayenta musamman Abbansu baya wasa da tarbiyarsu har ya rasu yana musu nasiha akan rayuwa.
Karar bude qofa ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, Hajiya Abu ce bakin qofar dakin tana kallon Badiya cike da tausayi.
Kofi ta miqo mata wanda yake cike da shayi mai kauri, maganinta ta 6allo mata da ke saman drawer ta miqa mata, bayan ta hadiye, Hajiya Abu ta juya zata bar dakin Badiya ta tsaida ta da sauri ta hanyar kiran sunanta.
"Anti"
Ta juyo bayan ta amsa, Badiya tana kallon qasa tace
"Dama... Dama wani tsohon saurayina ne yake ta matsa min wai yana son zuwa wurina dama ya dade yana bina ina wulakanta shi, shine kwatsam shekarajiya naga message nashi wai idan har yanzu ina da ra'ayi na bashi dama yazo"
Hajiya Abu tayi murmushi
"Ai babu komai nidama fatana ki samu mai sonki kiyi aurenki ki huta"
"To amma Anti na kasa fada masa lalura ta ina gudun kar ya guje ni..."
Ta karasa muryarta na rawa
Hajiya Abu tace
"Indai har tsakani da Allah yake sonki bazai guje ki ba kedai ki daure ki sanar dashi kafin ya zo"
To tace a sanyaye a yayinda da Hajiya Abu ta fice daga dakin.
((Kuyi hakuri da wannan banda charge))


Maryam S bello๐Ÿ’–

No comments: