Sunday, 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 51

๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ❤
    ๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ
        ๐Ÿ’š๐Ÿ’™
            ๐Ÿ’™


MSB๐Ÿ’–


maryamsbellowo.wordpress.com


®TALENTED WRITER'S GROUP (TWG)✍๐Ÿป


*๐Ÿ’•Tagwaye ne? ๐Ÿ’•*



51

Washe gari ta kama monday saboda yanayin aikinsa ya sanya bazai iya raka ta registration ba duk da ya so hakan kwarai, sai dai ya kokarta yaje banki ya biya kudin first semester sannan ya bata takardun bayan ya aje ta ya juya wurin aiki da niyyar idan ta gama ta kira shi ya dauke ta.
Ta kalli gabas, kudu da arewa taga batasan ko ina ba haka kuma bata san kowa ba, tayi tsaye tana nazari wayarta ta fara ruri, Heenad ce, ta dauka gami da yin sallama. Heenad tace
"Wai kina ina?"
Khadija tace
"ina cikin makaranta amma bansan ko ina ba"
Heenad tayi dariya
"Kema dai Khadija basai ki tambaya ba?"
Tayi murmushi kawai, Heenad tace
"Shikenan ki jira ni gani nan ina hango ki daga nan"
Ta karaso tana murmushi tace
"Mu je na nuna miki yadda zakiyi sai naje na yi nawa idan kin gama ki kirani"
To kawai tace suka jera har department dinsu Khadija.
Da sallama suka shiga office din, mutumin zai kai kimanin shekara hamsin zuwa sama, bayan sun gaishe shi ya amsa Heenad tayi masa bayanin su sabbin zuwa ne sunzo registration. Wata paper ya miqa musu Khadija ta sa sunanta sannan ya bata reg. number, ya miqo mata wasu forms yace ta cika, suka fita daga waje Heenad duk ita ta taimake ta da rabin aikin, karshe ma gaba daya sai da Khadija ta kammala registration din sannan ta raka Heenad tayi nata.
Bayan sun gama ko wacce ta kira mijinta ya zo ya dauke ta.


* * *

Da daddare Heenad na zaune a daki tana gyara handout dinta tana nazari Khalil ya shigo dauke da leda yana mata murmushi.
Da sauri ta miqe ta masa sannu da zuwa gami da kar6ar ledar hannunsa. Hannunta ya kama suka zauna, tray ta da wuqa dauko don tasan bai wuce nama ko kaza ba dama Khalil maye ne wurin cin nama baya wasa, da kansa ya bude ledar gami da fiddo gasassun kifi guda biyu, da  ya debo ya sanya mata a baki, sai dai tun kafin ya wuce ta moqoshinta ta ruga da gudu bayi ta shiga kwarara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta. A rude Khalil ya bita yana tambayar lafiya, bayan ta gama ya taimaka mata ta gyara jikinta suka fito, ya zaunar da ita kan gado yana mata sannu duk ya rude. Aikuwa tana zama wani aman ya taso mata ta qara rugawa da gudu ta shiga karar da yan cikinta. A ranar Khalil yaga tashin hankali, haka suka kwana Heenad na amai ga matsanancin ciwon ciki da ya addabe ta, kafin wani lokaci zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta, haka tayi ta karkarwa, ya rungume ta ji yake kamar ciwon ya dawo jikinsa. A dare daya duk ta rame ta zama kalar tausayi.
Tun yana sa ran zata ji sauqi amma abu sai dada gaba yake, don haka da sanyin asuba Goggo ya sanar mawa zai kai Heenad asibiti batajin dadi, tayi mata fatan samun sauki.
Asibiti mafi kusa ya kaita saboda yanayin jikinta, koda suka isa basu samu likita ko daya ba sai nurses, takaici ya ishi Khalil, da qyar ya samu aka nuna masa gidan wani likita dake kusa da asibitin ya fita da sauri.
Ba'a jima qwarai ba suka dawo da likitan, shi yayi mata gwajin jini da duk wani gwajin da ya kamata.
Bayan minti goma an kammala likitan na ofis dinsa suka shiga, ya basu izinin zama, bayan sun zauna Khalil ya miqa masa gwajin da akayi, bayan ya warware yana nazari can kuma ya dago da kansa yana murmushi yace.
"Congratulations matarka tana dauke da juna biyu"
Cikin rashin fahimta yace
"Bangane ba likita"
Likitan yace "haba dai bakasan juna biyu ba to ina nufin matarka tana dauke da ciki na kimanin sati biyu"
Baisan lokacin da ya saki dariya ba! Fuskarsa na nuni da matsanancin farin cikin daya kasa 6oyewa.
Likita ya rubuta mata maganin da zata rika sha sannan ya ce
"Ki nemi Sister Bilkisu tana cikin asibitin nan itace zata taimaka miki da shawarwarin da ya dace da ke don na lura kamar wannan ne na farko?"
Sukayi shiru, Likitan yayi murmushi
"Shikenan kuje, please madam kar kiyi wasa da magungunan nan fa suna da matukar amfani a gare ki"
Sister Bilkisu suka nema ta kuwa basu shawarwari ba iyaka daga haka sukayi mata godiya, suka tafi gida.

Haka Heenad ta kwana biyu tana zazzabi marar sauka ga amai da take fama dashi banda yawan  kasala da take samu, ga uwa uba sabon tsanar mijinta Khalil da takeji ko kusa da ita bata qaunar ya matso musamman idan ya fasa wani turarensa da bata qauna, duk ya ya rude ya sussuce, ranar da sukaya waya da Khadija take sanar da ita, ta tayata murna sosai, ita kuma Khadija data je gida wuni ranar wata lahadi ta sanar ma Mami, Mamin sai da ta kira Heenad ta bata shawarwari masu matuqar amfani ga mace mai qaramin ciki.
 Laulayin cikin nata sai a hankali rigima yau daban ta gobe daban, kuma duk yadda tace haka yake bi da ita.
Goggo ma tana iya qoqarinta wajen kula da ita, duk da taji sauki sosai amma duk da haka basu gaza ba wajen ganin bata nemi wani abin ba.


* * *


     BAYAN KWANA SHIDDA


Yau kimanin kwana shidda da Khadija ta soma karatu yau lecture din safe tayi wurin karfe sha biyu ta dawo gida ta ci karo da baquwar  mota a waje cike da mamaki take tunanin ko baqi sukayi, tana wannan tunanin ta shigo gida kasancewar yau Adnan aiki ya masa yawa sheyasa bai kaita ba sai dai ta hau adaidaita duk da sai da qyar ya barta ta shiga.
Tana shigowa ta ci karo da shi zaune kan doguwar kujera yana chanza tasha, hannunsa daya riqe da kofin tea yana sha. Sallamar Khadija ce ta katse masa kallon ya kalle ta gami da yin murmushi, kusa dashi yayi mata nuni da alamar ta zauna, bata musa ba illa zaman da tayi sa'ilin da take gaishe shi, fuska sake ya amsa yana bata tea din a baki tana sha.
Kallonta yayi sannan ya juyar da kansa gefe ya dauko mukulli yana karkada mata. Tayi tsai tana kallonsa, can kuma ya numfasa yace.
"Menene wannan?"
Tayi dariya
"Mukulli mana"
Yayi murmushi yace
"Mukullin daki?"
wannan karon dariya tayi sosai tace
"Na mota dai ko"
Hannunta ya jawo ya miqar da ita tsaye yana fadin
"Zo kigani"
Har inda motar take sukaje ya kalli motar yace
"Tayi miki?"
Da mamaki take fadin
"Ni kuma?"
Ya girgiza kansa yana kashe mata ido daya
"kwarai ma kuwa taki ce agogo a leda dazu da zan dawo na biya na siya miki ita"
Bazata iya misalta irin farin cikin da taji ba, nan ta hau masa godiya marar adadi tana hawayen farin ciki.
Jawo ta yayi yana shafa bayanta
"Meye na kukan kuma? Wallahi kinfi haka a wurina Khadija nidai burina na faranta miki rai"
Batasan sadda ta dago ta kalle shi ba, kallo mai cike da saqonnin qaunarta a gareshi!



Maryam S bello๐Ÿ’–

1 comment:

isha spa said...

Hi am Isha here from mumbai , 23 year old staying bangalore we provide body to body massage services in bangalore, All My Dear Customers Ishaspa is your perfect haven for a day of stress and tension-free relaxation. People often say that only journey matters as you have to experience everything thoroughly. But, at Ishaspa, we ensure that both your journey as well as your final point are both filled with satisfaction beyond your expectations A spa is a simple, calming, parlor-like destination where you enter for a day of rejuvenation. If you want to removeing all the stresses, tensions and woes of your daily life, a spa is the place for you to be. Every spa treatment is a form of water treatment which involves using hot baths, saunas, steam rooms and even whirlpools. These treatments soothe your skin, and simmers you down to relax and enjoy the time at the moment.
massage bangalore
massage in bangalore
body massage bangalore
body massage in bangalore
body to body massage in bangalore
body to body massage bangalore
massage parlour bangalore
massage parlour in bangalore
body massage parlour in bangalore
body massage centers in bangalore
body to body massage bangalore
body to body massage in bangalore
erotic body massage bangalore
female body massage bangalore
full body massage bangalore
female massage in bangalore
girls body massage in bangalore
b to b massage in bangalore
b to b massage bangalore