Sunday, 12 February 2017

TAGWAYE NE? 21 to 25

TAGWAYE NE? Na Maryam s bello {21 to 25}
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

21

Sai da Adnan yayi sallah sannan aka fara gudunar da aikin dibar jininsa zuwa jikin Khadija, an dauki tsawon rabin awa sannan aka kammala, koda aka maida ta dakinta shi kuma likitan ya umurce sa da ya kwanta ya huta in ba haka ba zai iya faduwa idan yace zai tashi, haka nan ya hakura yayi kwance sai da aka tabbatar masa zai iya tashi tukunna ya miqe ya fice zuwa dakin da Khadija take.

Da sallama ya shiga hade da ture kofar dakin, lokacin wajajen uku da rabi, Ummi na kan sallaya tana lazumi yaje ya samu wuri kusa da ita ya zauna yana kallonta cike da tausayi, mahaifiyarsa yar gayu fara tas amma yini guda duk ta qode saboda tashin hankali, kafin ya kai ga magana aka turo dakin da sallama, Abbansu ne sai Abba da Isma'il suna biye dashi, da sauri Ummi ta miqe ta basu wuri suka zauna, tayi musu sannu da zuwa, Abba yayi mata sannu da qoqari sannan ya tambayi mai jiki suma su Isma'il duk suna gaishe da mahaifiyar tasu da kuma tambayar mai jiki, Suka tambayi Adnan jikin nasa kasancewar an sanar dasu ya bada jininsa, Abba ya yaba da qoqarin da yayi ya sa masa albarka, Ummi taji dadi sosai, sun yi kusan minti sha biyar sannan suka miqe zasu tafi, nan Abba ke sanar masa su Bilkisu da Asma'u zasu zo gobe sunyi waya ya sanar masu abinda ya faru (yaranta mata dake aure a kaduna) sai Rashidat ita ke aure a yola ita kam ta mata fatan samun lafiya don bazata iya zuwa ba, sai guda biyu Aisha da Farida suke aure a kano ita Aisha tsohon ciki ne da ita haihuwa yau ko gobe ita kuwa Farida tana exams don haka duk bazasu samu zuwa ba sai Bilkisu da Asma'u daman sune manyan yayanta mata, Asma'u ce babba sai Bilkisu na bi mata, ko wace tana da yara hudu, sai Rashidat ita keda guda uku, Farida ita kuwa daya gareta tal sai Karamar Aisha ita yanzu zatayi haihuwar farko.

Shima Adnan yana gama sallar la'asar ya fice zuwa wurin aiki, don haka Ummi ita kadai ce, sai yau tayi kewar yaranta mata da suna nan da yanzu su zasu taya ta zaman jinya.
Sai bayan isha'i sai ga Hajiya Abu da Badiya sun shigo dauke da basket din abinci, tunda abin ya faru ko sau daya bata kira ta mata jaje ba, babu abinda ya dame ta, yanzu ma ta tabbatar Alhaji ne ya sata gaba dole sai da tazo.

Dabas ta zauna qasa ita kuwa zaqaqar marar kunyar kan kujerar roba ta zauna, tana wani yatsina fuska tana kalle kalle ko zata ga masoyinta, motsi kadan sai ta kalla taga koshi ne amma sai taga wayam.

Ita kuwa Hajiya Abu sannu kawai tace tare da Allah ya qara lafiya amma in banda haka bata ce komai ba sai wannan cika take tana batsewa, Ummi ta jinjina kai, tace a ranta,"dan adam mai wuyar sha'ani" nan suka dauki tsawon minti ashirin sannan suka miqe zuciyar Badiya duk babu dadi rashin ganin Adnan, haka Hajiya Abu ta dinga aika mata da zaqon harara don ta gano ta, koda suka shiga mota tasha zagi wai ta rako mata batada zuciya, ita dai Badiya ko a jikinta wai an tsikari kakkausa don ita bihaqi sonsa take.
Sai wuraren goman dare Adnan ya shigo dakin dauke da leda, Ummi na zaune tana gyangyadin gajiya, ya tausaya mata matuqa, ya gaishe ta tare da zama gefenta sannan ya miqa mata ledar, naman kaza ne sai yoghurt mai sanyi sai kayan marmari su ayaba, lemon bawo, kankana da sauransu, sai kwalbar swan babban, dah da farko cewa tayi bata jin yunwa, sai da yayi da gaske sannan taci naman tasha yoghurt din shima ba wani da yawa ba, sai da ya tabbatar ya gyara komai yana shirin tafiya su Abba da Isma'il suka shigo, nan fa ya fasa tafiya, yan uwa rabin jiki, nan suka sha hira da yan mazanta guda uku da Allah ya bata taji dadi sosai, har ma ta sake sai dariya takeyi, tabbas yaya rahama ne Allah ya bamu masu albarka amin.

Basu tashi tafiya ba sai wuraren sha dayan dare da zasu tafi kamar kar ta rabu dasu takeji, haka nan ba don taso ba sukayi bankwana tare da tabbacin zasu dawo gobe da safe.

Haka nan Ummi tayi kwanan zaune saboda tayi tunanin Khadija zata farka kafin safiya amma ina shiru kakeji duk ta damu.

* * *

Heenad da aka sani yar gayu mai ji da gata da kudi hade da wulakanci duk tayi sanyi, saboda yadda take yaqi da zuciyarta kan lalle ba son Adnan take ba, tilas daga qarshe ta yardar ma kanta so ne take masa wanda bata san yadda zatayi ba, haqiqa Allah ne ya kamata, wurin wulakacinta ta hadu da wanda take mutuwar so, tayi kuka tayi baqin ciki a cewarta zuciyarta bata kyauta mata ba saboda Adnan ba irin kalar mazan da take burin aure bane, ko a mafarki batayi tunanin zata so kamar Adnan ba, a cewarta tafi qarfin ajinsa (kuji qarfin hali wai 6arawo da sallama), kullum cikin kuka take hankalin Daddynta duk ya tashi ganin tilon yarsa cikin wannan hali, duk ta rame bata fita ko ina a cewarta batason ta fita ta sake haduwa dashi sai dai hakan ya gagara saboda yanzu ba abinda take son gani sama da Adnan, ita ma Mami ta yi tambayar duniya amma kullum amsa daya take samu wato "bakomai" har dai ta gaji ta qyale ta, shi kuwa daddy har ya soma tunanin ko aljannu suka shafi yarsa yadda ta sukurkurce lokaci daya ko cikin bacci batada aiki sai sambatu, tun abin baya damun iyayenta har ya soma basu tsoro.

* * *
Washe gari misalin qarfe takwas da rabi na safe Adnan ya shigo dakin da sallama hannunsa dauke da basket din abinci, bayan sun gaisa ya tambayi lafiyar Khadija, ya samu wuri ya zauna suka dan ta6a hira sama sama nan Ummi tabasa kudi tace ya siyowa yarinyar kaya idan ta farka tasa kullum tana fama da yagalgalallun kaya kala daya.
A hankali ta fara motsa bakinta ba'a jin abinda take cewa kasancewar a hankali take fadi, sai da Ummi ta matsa dab da ita sannan taji ashe addu'a take karantowa tare da salatin annabi, hannunta ya soma motsi kafin kafarta ta motsa, Ummi na tsaye kanta riqe da hannunta Adnan na gefenta suna jiran ta bude idanunta, sai da ta kara akalla second goma kafin idanunta su bude tangaram, alhamdulillah! Shine abinda Ummi ke fadi, da sauri ta umarci Adnan ya kira likita don sanar masa ta farka. Da sauri ya fita don cika umarnin mahafiyarsa.

Tun tana ganin biji biji kafin a hankalin fararen idanunta su sauka kan Ummi, Khadija ta kalli Ummi dake ta faman yi mata sannu tana qoqarin gasgata shin a asibiti take? Ta tambayi kadan, nauyin da kanta yayi mata tare sarawa kamar zai tsage ya sanya ta saurin riqe kan tana kokarin miqewa zaune, da sauri Ummi ta hanata, ta koma ta kwanta tana jin jikinta gaba daya kamar ba nata ga kafarta da hannunta sun mata nauyi in banda ciwo babu abinda takeji, hakan yasa ta runtse idanunta, tana addu'ar samun sauqin radadin da takeji daga waje rabbil izzatu, ta kai dubanta ga qarin jinin da akayi mata.
"Harda qarin jini akayi min? Wanene ya bada jininsa aka sa min ni Khadijatu?" Ta tambayi kanta cikin rai.
Daidai nan aka bude qofa likita na gaba Adnan na biye dashi a baya.

Maryam S belloπŸ’–
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

22

Da sauri Ummi ta ba likitan da nurse din da suka shigo tare wuri don gudanar da aikinsu, dauke da murmushi yana duban Khadija yace sannu ko, bata iya magana ba illa kanta da take dagawa alamun yauwa, ya dudduba ta sosai sannan aka sake yi mata dressing din wuraren da ta ji ciwo, ranar kam Khadija tasha azaba da radadi, musamman da aka zo duba mata qafarta, sai sannu Ummi ke mata kamar ta yi kuka don tausayi, Adnan ma ya tausaya mata sai da likitan ya gama yi mata duk abinda ya dace sannan ya kalli Adnan yace.
"Weldon fa Adnan kayi qoqari daka bada jininka yanzu gashi ta samu sauki Allah ya saka maka da alkhairi"
Daga shi har Ummi suka amsa da amin, ita kuwa Khadija ji tayi gabanta ya fadi ganin wanda ya bata jini ba dangin iya bana baba, ashe har zata samu gatan da wani zai ciro jininsa ya bata, ta tambayi kanta.

Muryar likitan ta tsinkaya yana fadi ma nurse din yadda zata kula da ita sosai da magungunan da zata dinga bata da allurai.

Haka Ummi tayi ta jinyar Khadija har taji sauqi sosai wanda sanadin hakan yasa har zaune tana tashi da kanta ta jingina da pilo, kullum ta kalli Adnan sai ta ga yana qara qima a idanunta ko don ya bata jini?

Cikin kwana biyun nan likitan yace Khadija tana iya yin wanka don a wanke mata jinin da ya bushe mata a jiki ita kanta zataji dadin jikinta, nurse din da Ummi ta taimaka mata suka shige toilet, tuna Adnan bai siyo kayan da tace ba ya sanya ta kira shi, a lokacin yana tare yan uwansa da suka zo daga kano ana ta hira da raha wayarsa ta fara ruri. Bayan ya daga Ummi ta sanar masa cewa ya siyo ma Khadija kaya don yanzu haka ma wanka ake yi mata. Nan yace mata mancewa yayi amma yanzu zai biya ya siyo sai ya kawo mata.

Bubu ready made ya siya mata masu kyau babu laifi guda hudu.

Sadda suka iso an fito da ita kan wheelchair(keken guragu) Ummi ta taimaka aka dora ta kan gado sannan Asma'u ta shafa mata mai (mutane masu kirki) inji Khadija cikin rai, shi dama Adnan yana kawo su fita yayi waje, kafin Ummi da Asma'u su gama shiryata Bilkisu ta zubo mata abinci, farfesun hanta, da dankali sai kwai, sai maltina ta dora mata saman tire a lokacin an gama shirya ta tas! Duk da batada lafiya tayi ma su Ummi kyau matuqa, ita dai sai sunkuya kai take alamar kunya.

Ta kalli abincin yawanci na qara jini ne, amma ita ina zata kai duka wadannan?

Haka su Bilkisu suka sata gaba sai da taci da yawa sannan suka qyaleta, duk ta saba dasu a kwana biyun nan kamar sun dade da sanin juna, ba kamar Ummi da takejin kamar diyarta ce ta jini, sai dai tasan tana warkewa dole ta maida ma iyayenta duk da tasha tambayar Khadija ta fadi inda suke don a sanar masu halin da take ciki, amma taqi har Ummi takanyi tunanin tare da tuhummar kanta anya sunyi adalaci kuwa? Qin sanar da iyayenta babu dadi sam gashi Khadija ta kafe akan idan ta warke zata koma wai sunyi nisa kuma basuda waya iyayen nata, hakan nan Ummi ta qyaleta amma zuciyarta babu dadi a ganinta rashin kyautawa ne. Kwanan su Asma'u biyu suka koma gidajen mazajensu tayi kewarsu sosai don mutanen kirki ne ainun.
Satin Khadija daya ta murmure kafarta kadai ta rage ta warke amma ta fito fes da ita tayi gwanin kyau sosai soboda kulawar da take samu daga wurin Ummi, farinta da kyawunta sun bayyana, hakan yasa Adnan kullum ya kalle ta sai ya tuna marin da masa amma ya kan danne zuciyarsa saboda Ummi don ya lura yarinyar ta gama shiga ran mahaifiyarsa yadda take dawainiya da ita har abin ya soma yin yawa, ai dole ta kula da ita tunda mu muka jefa ta cikin wannan halin, yayi saurin kawar da wancan tunanin. Haka yayi zaune a office dinsa yana saqa da warwarewa, a haka babban abokinsa kuma abokin aikinsa Khalil ya same sa, sai da ya dafa sa sannan ya dawo hayyacinsa, Khalil ya zauna a kujerar gaban teburinsa yana fuskansa yace.
"Adnan wai meyake damunka kwana biyu ne? Yanzu bakaga miss call dina bane sau nawa na kiraka baka daga ba?"
Adnan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ba Khalil labarin abinda ya faru tun daga kan marin data masa har kade da yayi komai ya fada masa kaf.
Khalil yayi dariya har yana buga teburin sannan ya dago ya kalli Adnan wanda gaba daya annurin fuskarsa ya sauya haushi ya kama shi sosai ganin yanda Khalil ke dariya yama raina masa hankali hakan yasa ya qara daure fuska kamar bai ta6a dariya ba, sai a sannan Khalil ya bar dariya yace.
"Haba Adnan don me zaka damu da ita don ta mare ka, nikam inda zaka bi shawara ta ma ka manta da ita ka dena saka damuwa a ranka ai duniya ce, wata rana da kanta zata yi nadama, kai meye na damuwa kai da zakayi aure soon, ko har ka manta alqawarin auren da ke tsakaninka da Fatima ne? Ka kusa zama ango fa nan da yan watanni kadan ne"
Adnan ya qara tsuke fuska an soso masa inda ke masa qaiqayi annurin fuskansa ya qara 6acewa 6at!
"Alqawarin dake tsakanin iyayenmu dai! Kai bakasan biyayya ce tasa na yarda da aurennan ba? Banason 6acin ran iyayena, amma abin yana damuna musamman idan na tuna bamu ta6a ganin juna ba, yarinyar da tayi rayuwarta kaf a turai duka duka yaushe suka dawo, bakada labarin yadda Mahaifinta ke 6ata ta da gata? Kullum na tuna da irin matar da zanyi rayuwar aure sai naji baqin ciki, kuma banason sanar da Abba halayen yarinyar saboda kasan yana da matsalar ciwon zuciya sheyasa na bar abin a raina bana son abinda zai ta6a lafiyar Abba na"

Ya fada hakan da damuwa shinfide saman fuskarsa.
Khalil ya jinjina

"Tabbas hakane amma ka kyauta Adnan, biyayyar iyaye ba qaramin abu bane kuma ina tabbatar maka zaka ga haske a rayuwarka, kuma nayi imani da cewar ko bayan aurenku zata chanza halayenta da zarar ka cigaba da dora ta hanya madaidaiciya, Allah yasa mu dace"
A sanyaye ya amsa da amin.

Khalil ya cigaba da cewa
"Amma ya kamata ku gana ko da sau daya ne don ku samu ku fahimci juna koba haka ba? Kasan aure ba qaramin abu bane rayuwa ce za'a yi ta har abada"
Da sauri Adnan yace

"Bana buqatar hakan idan munyi auren ai zamu gaji da ganin juna ko?"
Khalil yayi murmushi

"Haka ne angon Fatima"
Harara ya jefa masa da wasa, daga haka kuma suka chanza chapta hira ta 6arke tsakanin abokanan biyu, sai da aka kira la'asar sannan suka katse hirar tasu tare da miqewa don sauke farali.
* * *
Kwanan Khadija tara daidai aka sallame ta ta murmure sosai kamar ba ita ba, sun kuma shaquwa da Ummi kamar mahaifiyarta ta dauke ta, haka suka dunguma gida wajajen karfe sha daya na safe, bayan sun isa Ummi ta kamo Khadija kasancewar tana dangyashi saboda qafar tata bata ida warkewa ba, daki na daban aka ware mata don hutawa sai da tayi wanka taci abinci sannan ta kwanta ta fara baccin gajiya rabon da tayi bacci irin wannan har ta manta.

Ba ita ta farka ba sai wajajen 2 saura, sallah tayi, tana cikin shafa addu'a aka turo dakin, nancy ce mai aikin Ummi dauke da tiren abincin, tayi mata ya jiki sannan ta ajiye, ta sanar mata idan ta gama ci Madam dinta zata zo tana son magana da ita, to tace tare da yin godiya.

Sai da taci abincin ta qara hutawa sannan Ummi ta shigo dakin, fuskarta dauke da murmushi, sai da ta zauna gefenta sannan ta qara tambayar jikinta, tukunna ta fara magana"
"Dama kinga tun a asibiti nake fama da ke ki fadi inda iyayenki suke a sanar musu halin da kike ciki kika qi, to kuma gashi har an sallame ki basuda labari, gaskiya anyi wauta hakan kuma bai dace ba yanzu da kin qara kwana biyu insha Allah kika qara warkewa zan dauke ki na maida ki gida"
Take hankalin Khadija ya tashi, tunanin irin kalar rayuwar da tayi, tuno da mahaifiyarta ya sanya zuciyarta tsinkewa nan da nan ta fashe da kuka, hankalin Ummi ya tashi sosai nan ta shiga tambayar abinda ya same ta ko kuma jikinta ya tashi, a'a tace sai data tsagaita da kukan sannan ta kawar da ko wace irin fargaba ta sanar ma Ummi da labarinta tun daga farko har qarshe.

Ummi ta tausaya mata sosai, ta kuma yi alqawarin nemo mata mahaifiyarta da danginta a duk inda suke sannan tace zata riqe ta har aga mahaifiyar tata, Khadija ta mata godiya sosai kuma taji dadin wannan karamcin da tayi mata, wannan duniyar bata santa ba amma ta ce zata zauna da ita, gaskiya Ummi ta chancanci dukkan yabo don dattijuwar akwai karamcin sosai.
* * *

Yau da daddare misalin qarfe goma da rabi na dare Mami na zaune saman gado tayi shirin bacci tana karanta wani littafin addu'oi, daddy ya fito daga wanka yana shafa mai Mami ta kalle shi tace.
"Alhaji"
Ya juyo da dubansa gareta sannan ya amsa yana tambayar ko wane abin take buqata.

Ce masa akwai maganar da takeso suyi don haka ya zo ya zauna don maganar nada muhimmanci.

Bai musa illa jallabiyarsa ta bacci ya zura sannan ya zauna yana fuskantarta, glass din karatunta ta cire tare da ajiye littafin a gefe sannan ta soma magana cike da damuwa.
"Alhaji dama dai kan maganar Fatima ce, gani nayi yanzu fa ba yarinya bace, kuma nasha fama da kai lokaci yayi da ya kamata a sanar mata alqawarin da ke tsakaninku da general Usman amininka na kusa, ya kamata ta fuskanci rayuwa"
"Uhm Safiyya kenan, nifa bana son abinda zai dami Heenad dina ki bari ta qare jarabawarta tukunna a sanar da ita"
"A'a Alhaji yanzu fa Heenad ta kai mizanin soyayya baka gudun kar ta fada soyayyar wani kuma ga babban alqawarin da kuka dauka tun suna qanana?"
"To meye sai a janye ai yanzu ma an daina auren dole, ni dama ba har cikin zuciyata mukayi alqawarin ba baki ganin yanzu ma zumuncin yayi rauni? Yaushe rabon da mu gana ai an dade"
Mami ta dube shi da kyau tace

"Alhaji kenan, ni sai nake ganin kai ne ka yada shi saboda kaine ka kwashi iyalinka ka bar qasar, duka duka yaushe muka dawo tunda muka dawo ka nemeshi koda ta waya ne? Ya kamata dai kasan muhimmancin alqawari ba yi bane ka fasa bashi auren yarka don kawai ta nuna bata so"
Kafin Daddy yayi magana sai gani sukayi an banko qofar dakin da suke, da sauri suka kalla ko waye, Heenad ce tsaye tana haqi idanunta sun kada sunyi ja tana duban mahaifannata tare da fashewa da wani irin kuka.

Maryam S belloπŸ’–

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

23

A razane Daddy ya miqe ya isa gareta a lokacin ta kai qasa tana sheshekar kuka, Mami kuwa batayi komai ba illa idanu data zuba masu, hannunsa yasa ya tada ta tsaye ya dube ta, idanunta sun kumbura sunyi jajir wane wuta, kai Daddy ya shiga girgiza mata alamun kar tayi kuka amma ina sai ma ta qara sautin kukan nata, kamo hannunta yayi ya zaunar da ita saman gado sannan shima ya zauna yana fuskantar ta tare da share mata hawaye yace.
"Fatima"
Sunan da bai ta6a furtawa ba kenan saboda sunan mahaifiyarsa ne, jin haka yasa Heenad ta dakatar da kukan da take amma hawayen na cigaba da zuba sannan ta dube sa tana so tayi magana amma tayi shiru saboda tafiso ta fara jin daga bakinsa tukunnan sai ta amayo abinda ke cikinta wata qila ma ta samu sa'ida.
"Fatima kalle ni da kyau, kiji abinda zan fada miki, bana so kiyi min mummunar fahimta akan zancen da zakiji daga gare ni, ga ki ga Mahaifiyarki nan"

Ya fada yana kallon Mami wadda itama ta samu gu ta zauna tana sauraronsa.

Ya cigaba da magana yana duban yar tasa da kyau.
"Na kasance ma'abocin son karatu kuma tun ina qarami gaba daya family dinmu sunsan ina mutuwar son soja, sai dai lokuta da dama mahaifiyata Allah ya jiqanta da rahama ita ke bani haquri kan cewa sai dai wani ikon Allah saboda a lokacin bamuda kudi, muna fama da babu, wallahi Fatima inda kinga yadda muke samu muci abinci sau biyu sai kin tausaya mana wani lokacin ma sau daya muke ci saboda talaucin da yayi mana katutu, a lokacin kuma ga qarfin mahaifina ya qare qarshe ma ciwo ya kama shi wanda muka rasa meke damunsa, har Allah ya dauki abinsa.

Wata rana ina wajen aikin wankin mashin da yake lokacin shine sana'ar mahaifina daya rasu sai na kar6a inayi, gani lokacin dan qarami duka duka shekarata goma lokacin amma saboda rashi dole na tashi tsaye don nema mana abinci, sai wani dattijo yazo goye da wani yaro wanda zan iya ce maki tsarana ne ko kuma ya girme ni da kadan, bayan sun kashe sun sauka sai mutumin ya qaraso inda nake a lokacin na gama wankin wani mashin ina daurewa, daga ganinsu bazakice musu talakawa ba saboda yanayin shigarsu ta nuna hakan, na gaidasa ya amsa sannan yayi min bayanin wankin mashin dinsa zanyi masa zuwa bayan magriba zai zo ya kar6a, na kalli yaron dan fari mai kyau, aiko sai muka hada ido ya sakar min murmushi, nima na mayar masa, wani abu yake sha wanda bansan ko menene ba aiko ya miqo min alamun zansha nace masa a'ah nagode.

Wannan dattijon ya duqo daidai saitin fuskata yace yaro amshi mana tunda ya baka, sai a sannan na kar6a nasha, abin dadi ga sanyi ga gardi, nace a raina garin dadi na nesa, har yaja hannun yaron zasu tafi ya juyo da dubansa gareni yace ya sunanka yaro, nayi murmushi nace sunana Ahmad, yace to Ahmad kaji Usman yace wai yana son ku zama abokai, na gyada kai kawai amma banyi magana ba.

Haka ta kasance kullum sai an kawo Usman a mota sai daga baya na gane mutumin nan ashe direbansa ne, cikin qanqanin lokaci mun shaqu da Usman nan yake wuni yana taya ni wankin mashin, da yamma ake zuwa daukarsa, yace man yana makaranta amma yanzu hutu sukeyi. Har dai wurin mahaifiyata na kai shi itama ta amininta da hakan, har direbansu ya san gidan mu.

Yasha tambayata wai aji nawa nake a makaranta amma abinka da yaro sai in saki baki ince ay bamuda kudi don haka ba'a sanya ni makaranta ba.

Haka dai ta kasance nida Usman mun zama aminnai sosai, duk ansan mu tare.

Wata rana ina zaune gida kasancewar banje aiki ba sai ga Usman yazo shida wata mata masu matuqar kama, Mahaifiyata ta tare su cikin sakin fuska ni kuma ina ta murna naga abokina, harda tsarabar alewa ya kawo mani.

Bayan sun gaggaisa sai matar ta shaida ma mahafiyata wai alfarma tazo nema zata tafi dani gidansu, wai ta dauki dawainiya ta zata sanya ni makarantar su Usman, kinji wani zancen kamar almara? Haka kawai daga abokai sai kawai ki dauki nauyin karatun yaro baki sanshi ba? Cewar mahaifiyata, Hajiyar tayi murmushinta mai kyau tace.

Wallahi Hajiya Usman yana son danki kullum zancensa Ahmad, wai yace masa baya makaranta basuda kudi.

Mahaifiyata ta riqe baki cike da mamaki tana kallona. Nasan na 6allo ruwa kenan amma sai na dake na ma juya kaina ina cigaba da maganata da Usman.

Nan dai da qyar ta shawo kan mahaifiyata ta amince a tafi dani makaranta amma tace a dinga kawo ni ina ganin gida, tayi na'am da hakan tare da alqawarin riqe ni amana. Haka na kwashi yan kayana muka tafi ina ta murna.

Wai! Zo kiga aljannar duniya, haka naga an kaini wani daki wanda yaji kayan more rayuwar duniya, nan aka ce dakina ne na saki baki ina kallon ikon Allah, gidan kam ya hadu ba kadan ba.

Haka nayi kwana 2, a gidan na saje na zama dan gida komai anayi mani, hatta kaya an chanza mani wasu, sannan an kaini makarantar su Usman anyi duk abinda ya dace, aka sanya ni ajin da yake primary 3, ajin da Usman yake, haka fa na dage nayi ta karatu tunda na shiga nake kwaso na 2, nasha yabo wurin iyayen Usman kuma sunji dadi hakan.

A kwana a tashi muka kammala secondary school gaba daya, mun zama samari yan gayu, mun kuma shaquwa da Usman, ko ina kikaga daya zakiga dayan, hatta kaya iri daya muke sawa, komai dai tare mukeyi, har akance wai kamar mu daya!

Mahaifinsa da kansa ya nemo mana makarantar sojoji aka sanya mu, kasancewar shima Usman burinsa kenan na zama sojan, wuu zo kiga murna wurina bakina har kunne nayi kukan farin ciki, ina gab da tafiya mahaifiyata ta rasu dama ita kadai ta rage man a duniya nayi kuka, naso ace idan nayi kudi mun more ku'din nan tare da ita, amma ya na iya? Haka Allah ya kaddara.

Haka muka kammala makaranta muka zama cikakun sojoji.

Alhamdulillah! buri na ya cika, kullum nayi sallah sai nayiwa mahaifin Usman addu'a, don a duniya banida uba kamar sa yayi man qoqari a ruyuwa.

Zumuncin mu kullum abin gaba yake duk duniya banida amini kamar Usman shima haka, shine abokin shawarata shima haka.

Haka cikin ikon Allah muka so wasu qawaye suma makarantar su daya, bayan an sanya rana muka fara shirye shiryen biki.

Wata daya aka sanya, aikuwa lokacin biki

Yayi aka sha shagalin biki aka qare.

Haka matar Usman ta haihu ta samu mace Asma'u, ni kuma ban samu haihuwa ba, abin mamaki Usman yace man aure zai qara nayi qoqarin hanasa nace ya bari koda zai qara sai nan gaba amma fir yaqi ji idanunsa sun riga sun rufe. Haka kuwa akayi ya auro Zainab yarinyar fitsararriya marar kunya, idanunta a bude suke, ga matarsa ta farko akwai haquri.

Wata tara uwar gidansa ta sake haihuwa da namiji, aka sa masa Aliyu ana kiransa Adnan amma fa ni har yau bamu samu haihuwa ba, haka zainab da Halima sukayi ta haihuwa daya bayan daya, amma ni ko 6ari matata bata ta6a yi ba. Sai muka fawwala wa Allah komai.

Akwana a tashi nima matata ta samu ciki wuu zokiga murna wurina ba'a cewa komai! tun cikin na wata daya nake ji dashi, kowa dai yasan da cikin, Alhaji Usman har cewa yakeyi ya kama ma Adnan idan ta haihu, duk a tunanina wasa ne, sai kuwa na amince a cewar wasa.

Da cikin yayi wata bakwai Saudia na kwashi matata muka tafi akayi scan aka tabbatar yan biyu ne zata haifa.
A razanae Heenad ta dago da rinannun idanunta tace yan biyu? Ina suke to?

Daddy yayi dariya, uwata kenan ki tsaya kiji mana. Ya cigaba da cewa.
"Bayan wata tara kuwa mamanki ta fara naquda sai dai tasha wahala ba kadan ba, hankalina ya tashi matuqa, qarshe ma aiki akayi mata ganin batasan inda kanta yake ba aka shiga emergency da ita.

Bayan kusan minti talatin aka haifo man santala santalan yayana mata guda biyu farare sol! Masu kama kamar an tsaga kara.

Saboda murna rasa inda zansa kaina nayi. Bayan awa biyu na fita siyo magani na dawo na iske mummunan labari wai daya ta koma, an ajiye su akaga bata motsi, na taho da sauri duk nabi na rude kafin nazo na iske babyn wadda ta mutu nayi ta kuka, har nace ta chanza kama ko dan ta mutu ne?oho.

Itama mahaifyar taku sai data dawo hayyancinta aka sanar mata tayi ta kuka amma ya zamuyi dole mu rungumi kaddara. Ranar suna aka sanya miki Fatima kasancewar sunan mahaifiyata ne sai ake kiranki da Heenad.

Heenad ta dago tana duban daddynta tace.

"Dama mu yan biyu Daddy kuma shine ba'a ta6a gaya min ba?"

Ba amfani Fatima saboda ta riga ta mutu, sheyasa nida mahaifiyarki muka yanke shawarar kar a sanar miki.

Sai da kikayi wata hudu muka koma gida Nigeria, gata, so da qauna kinsha shi, na nuna miki.

Haka kika cigaba da girma har kika shakara daya, a lokacin ne kuma aka maida ni london da aiki, koda naje ma Usman bankwana sai da ya tuna min batun alqawarinmu, na dube sa cikin rashin fahimta nace wane alqawari?

Yayi dariya yace Alhaji Ahmad har ka manta wai? Alqawain Heenad da Adnan mana!

Nayi yaqe nace oh eh..eh haka ne yana nan Allah ya nuna mana nace amin.

Daddy ya sauke ajiyar zuciya, ya kalli Heenad yace kinji abinda ya faru koba haka ba Safiyya? Ya kalli Mami.

Ta gyada kai almaun eh sannan tace.

"Heenad kinji an riga an miki alqawarin aure da Adnan, don haka yanzu kin sani kiyi takatsatsan kinsan dai girman alqawari.

Heenad ta fashe da kuka zuciyarta na quna, idanunta suka qanqance, hankalinta ya gushe, ta miqe tsaye tana huci tace.
"Wallahi Daddy a janye maganar auren nan inada wanda nake so Allah!"

Maryam S belloπŸ’–

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

24

Mami ta miqe a fusace tana fadin.

"Ke marar kunyar ina ce? A gabanmu kike cewa akwai wanda kike so ke Fatima?"
Haba Safiyya ki lalla6a ta mana baki ga halin da take ciki bane? Ai ya kamata a tausaya mata.

Ita kuwa Heenad kuka take kamar ranta zai fita ga zuciyarta na mata wani irin quna, kasa tsayuwa tayi ta zube qasa tana cigaba da rusa kuka kamar an aiko ta.
Daddy ya zaune kusa da ita cikin muryar lallashi ya soma magana.

"Mamana?

Ta juyo da rinnanun idanunta ta kalle shi hawayen na cigaba da kwarara wane famfo.

"Na'am Daddy" ta furta da muryarta da bata fita a dalilin kukan da taci.
Ya kamo hannuwanta ya hade wuri daya yace

"Heenad kar kiyi tunanin bana sonki kamar yadda zuciyarki ke raya miki ba, a'a ina sonki a matsayinki na diyata dana haifa a cikin cikina, wallahi yanzu idan kikace bakyason aurennan kika fadi min wanda kike so kinji na rantse an janye aurennan kenan, kuma kinsan a iya zamana da ke ban ta6a sanin kina da wanda kika so ba ko?
Ta gyada kai a sanyaye.

"Yanzu na baki dama ta qarshe kuma zan miki adalci ki fadi min wanda kike so da tarihinsa da iyayensa ni kuma na miki alqawarin zan je na samesu a daidaita"
"Haba Alhaji..."
"Ba ruwanki". Ya fadi yana daga mata hannu alamun ta dakata

Dole tayi shiru cike da takaici.
"Ina jinki mamana"
Tirqashi! nan fa akeyinta, ita ina ta sanshi kuma a ina zata san iyayensa, na shiga uku, nayi wauta, zuciyata ta cuce ni, ta furta hakan a cikin zuciyarta tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi ga mai sauraro.

Tausayinta ya kamasu harda Mami sai dai batason ta nuna hakan saboda tason muhimmancin alqawari.
"Ke nake sauraro" daddy ya furta hakan tare da tsare ta da ido.
Nan fa muryarta ta fara rawa.

"Da...ddy. Ban....sanshi ba, amma kayi man rai zan nemo sa, ka banj kwana 2 dan Allah daddy, ka cece ni kar ka min auren dole, dan Allah daddy" ta fadi tana qara cigaba da kukanta.
"Zancen banza ne ma wannan! Lallai Fatima bakida hankali, ai ca nake duk wannan abin ma soyayya kuke yana sonki kina sonsa ashe ba haka bane, son maso wani kike ko me?"

A cewar mama tana tsaye kansu.
"Wallahi a'a nima bansan ya akayi na fara sonsa fa"
"To aljani ne kenan? Ta ya ya za'ayi kice kina son wanda baki sani ba to aure babu fashi kamar anyi an gama ne"
"Ke ya isa da Allah, mamana kiyi haquri ayi aurennan ni na tabbatar miki nan gaba zakiyi alfahari da mu kinji yata?"
Ina ita Heenad batasan wannan ba, zuciyarta ta riga ta makance da soyayya bataji bata gani, haka ta dinga ihu tana cewa suyi haquri a janye maganar aurennan, sai haquri daddy ke bata, duk ta basa tausayi, da qyar Mami ta kaita dakinta, ta kwanta tayi ta kuka kamar ranta zai fita, da qyar tayi sallar isha'i kanta kamar ya fadi qasa takeji.

Ta lalla6a ta hawo gado ita kadai tasan me takeji a ranta, ko abincin dare bataci ba.
Daddy kam ya riga ya gama tausayawa yarsa ji yake kamar yace an fasa, sai dai yasan hakan bamai yiwuwa bane, ya riga ya tafka babban kuskure da ya aminta da hakan, mesa baice bazai bayar ba? Anya zai iya jure ganin Heenad cikin wannan hali kuwa?
* * *

Washe gari bayan Khadija ta idar da sallah wanka tayi, ta gyara dakin da take kwana sannan ta fito ta iske nancy na shara, taje kar6a da niyyar sharewa nancy ta hana ta tace madam tace kar a barki kiyi aiki kije ki kwanta ki huta, tayi ta magiya akan zata iya wai ta warke, haka nan Nancy ta bar mata ta koma kicin tana taya Blessing fere dankalin kalaci.

Aikuwa ta share tana cikin goge goge Badiya ta sauko sanye da kayan bacci doguwar rigar bacci fara tas iya gwiwa ko dankwali bata sa ba, sai wannan cika take tanan batsewa, Khadija na kallon sanda ta qaraso ta taka inda ta goge sannan ta wuce kicin, ba'a jima ba ta fito da kofi a hannunta ta sake takewa ta saki tsaki ta haye sama.

Duk akan idon nancy kuma taga kamar Khadija bata damu ba, ta dafa ta tace.

"Kiyi haquri haka take ta saba wulqanta mutane sai kin daure da irin wulaqancin da zata yi miki muma haka take mana, ta saba ce mana bamuda daraja wai mu masu aiki ne wulaqantattu ke bama mu kadai ba hartta baqi wulaqanci take musu"
Khadija tayi murmushi.

"Babu komai"

Daga haka ta cigaba da aikinta, sai da ta kammala sannan ta nufi kicin din ta kama musu a lokacin har sun fara soya dankalin, nan dai aka gama komai da ita, tama koyi wani abin, basu suka gama ba sai wurin qarfe goma da rabi. Suka jera komai saman table suka gyara wurin.
Basu dade da gamawa ba Adnan ya sauko da shirin fita aiki, Khadija na zaune bakin qofar kicin ta juyo qamshin turare na mata sallama, kan table din ya zauna ba tare daya lura akwai mutum a wurin ba ya soma cin abincinsa kasancewar wurin nada dan duhu a dalilin labulai dake rufe saboda sanyin da ake yi.

Da sauri Khadija ta miqe ta gaida shi, ba tare da ya kalle ta ba ya amsa yayi mata ya jiki, tace dasuki sannan ta koma dakinta.
Ya kusa kammalawa Badiya ta sauko sai wannan cika take tana batsewa, ta hau kan kujerar dake fuskantarsa ta zauna tare da qura masa ido.

Sanye yake cikin riga mai layi layi ratsin fari da baqi, tana da dogon hannunsai ya sanya baqin wando, da baqin tie, sumar kansa sai sul6i takeyi tana sheqi ta kwanta lub lub, baqar kwat dinsa na rataya kan kujerar da yake.

Muryarsa ta dawo da ita daga duniyar tunani, ta sauke ajiyar zuciyar ganin yana waya cikin muryarsa mai taushi da dadin sauraro.

"Dr Adeel?

Ohh ayya sorry banida numberka ya aiki?

Alhamdulillah

Ok shikenan ai zan shigo asibitin yanzu.

Ok bye

Ya katse kiran, ya kammala cin abincinsa ya miqe, ya dauki kwat dinsa ya rataya a kafada, ya haura saman cikin tafiyarsa mai daukar hankalin duk wata ya mace, ko ba'a fada mata ba tasan gun Ummi da Abba zaije yace musu ya fita, ta lumshe idanu, tare da qwalawa Khadija kira.
"Ke!"

Tana kwance saman gado tana hutawa taji ana ta faman kiran ke, ta fito ba tare data san da ita ake ba, da ladabi ta ce gani.

Ta watsa mata harara tace.

"Da kika kawo abinci kika aje baki iya zuwa kice min an gama har sai ya huce? Kuma kina nufin ni zan zuba da kaina?"

Ikon Allah, shine abinda Khadija ta fada a cikin ranta sannan a sanyaye tace "kiyi haquri bansan ina ne dakinki ba"

Tsaki ta mata sannan tace

"Baki tambaya, wawuya kawai"

Zagin ya ma Khadija ciwo amma sai ta dake ta bude kular ta fara zuba mata abincin sai kyarma take a dalilin kallon rainin da Badiya ke binta dashi.

Ta kammala zubawa ta kwashi wanda Adnan ya gama zata kai kicin shi kuma ya sauko kenan, ba tare data kula ba sai ji tayi ta bugi abu plates din hannunta suka watse katse, tana kyarma ta dago da fuskanta tana kallonsa yayi tsaye kamar an dasa shi a wurin yana kallon rigarsa.

A hankali ta kai dubanta ga inda yake kallo, rigar tayi faca faca da sauce har saman wandonsa, kyarma ta dinga yi tama kasa magana, hawaye ya cika a idanunta, hatta takalmasa baqaqe masu sheqi miya duk ta 6ata su, Badiya ta taso a fusace ta dauke Khadija ta mari a kuncinta na hago, sai data ga taurari suna mata yawo.

"Kina hauka ne kalli kayansa yanda kika 6ata masa da miya daqiqiya marar hankali, jaka"

Bata ankara ba sai jin saukar mari tayi ta dafe kuncinta, sai dai me? Ashe ba ita aka mara ba, Adnan ne ya dauke Badiya ta wani irin wawan mari, ta fasa ihu.

Adnan yace

"Kina hauka ne? Me tayi miki? Ina ce ni ta 6ata ba ke ba mesa bazaki bari na dauki hukuncin da kaina ba sai kece zaki daukar min?"
"Adnan ka mare ni? Akan wannan banzar zaka mare ni?"



"Ita banzar ba mutum bace kamar ki? Bana son shishigi ki barni ni na dauki matakin da ya dace da ita bake ba, wuce ki bani wuri!
Tsanar Khadija ta mamaye ta, haushi ya turniqe ta, tana shiga daki ta fashe da kuka tare da fadawa kan gado, sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru.

Cikin takaici tace

"Lallai yarinya saikin raina kanki a gidannan kisa masoyina ya mare ni akan ki? Impossible!!! Bazai yiwu ba, sai kin raina kanki na miki wannan alqawarin, sai kinyi dana sanin marina da akayi!

Maryam S belloπŸ’–
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

25

Ummi ce ta sauko da alama yanzu ta tashi daga bacci, ganin Adnan da Khadija ya sanya ta tsayawa inda take tare da cewa.
"Adnan baka tafi aiki ba meyafaru?"
Ta kalli Khadija dake ta faman kwashe plates din da suka fashe qasa, sannan ta kai dubanta ga jikin Adnan ta ya 6aci da miya, ta qaraso da sauri tana tambayar abinda ya faru.

Nan Adnan ya labarta mata abinda nan ta basa haquri sanan ya koma daki don sake wani sabon wanka hade da chanza kaya tare da kiran Dr Adeel don basa haqurin rashin zuwansa da wuri.
Jikin Khadija sai 6ari yake don tsoro, Ummi ta kira sunanta, ta amsa tare da dagowa don kallon Ummi a sanyaye tace na'am.

Ummi tace

"Tashi yata, ki kwantar da halinki ba dukanki zaiyi ba kinji ko? ya jikin naki kinsha magani?"

Ta gyada kai alamar eh.

Ummi tace

"Shikenan amma meyasa kike yawo keda baki ida jin sauqi ba? Bana ce ki samu wuri daya ki zauna ba har sai kin warke"

Khadija tayi shiru kanta na qasa.

Ummi tace je ki samu wuri ki zauna bana son ganinki kina yawo"

A sanyaye Khadija ta koma dakin sannan Ummi ta kira nancy don gyara wurin.

* * *

     *Bayan kwana biyu*

Jikin Khadija ya warware, ta dawo da rayuwarta cikin walwala, a gidan batada wata matsala, Ummi ta zama tamkar mahaifiayarta, haka Abba ya riqe ta kamar mahaifinta, Abba yana qoqartawa qwarai game da neman mahaifiyarta da aka rasa inda ta shiga kwana da kwanaki, an sanar ma yan sanda da duk inda ya dace kuma ba laifi duk suna iya bakin qoqarinsu.

A cikin kwana biyun nan a yammacin wata rana ne jikin Abba ya tashi, ya fito daga bandaki ya yanke jiki ya fadi, tashin hankalin da suka shiga gidan baya misaltuwa, take akayi asibiti dashi, su kansu sun yi iya qoqarinsu amma sauqi sai wajen Allah.

Kwanansa hudu asibti aka kwashe shi sai qasar Egpyt (Cairo), da Ummi da Abba, Hajiya Abu, Isma'il da Abba qarami, sune yan rakiya shi Adnan bazai samu zuwa ba saboda yanayin aikinsa, amma sam hankalinsa na can ya kasa kwanciya.

Gida ya rage daga Adnan, Badiya sai Khadija, a lokacin ne Badiya ta bude shafin iskanci kala kala, idan Adnan na wurin aiki ta tara qawayenta suyi ta chasu, ga karan tsana data ta dorawa Khadija, da sata aikin da ya fi qarfinta duk salon mugunta ta sani, da gangan take sata share mata daki sai ta gama gaba daya har da wankin bandaki sai tace baiyi mata ba sai ta sake haka Khadija zata sake, ko kuma ta tsiri cin indomie da daddare wajajen qarfe sha dayan dare, wani lokacin sai Khadija ta soma bacci take kiranta sai ta gama dafawa tace bazataci ba ita tea zata sha, haka zata koma ta hado mata shayin. Da yake Khadija nada tsananin haquri bata nuna 6acin ranta ko kadan tana dannewa.
Wata rana Khadija na kicin tana taya nancy girkin abincin rana Badiya ta shiga qwala mata kira, tana shiga ta iske su zaune saman gado ko wace tayi shigar kananan kaya da qarin gashi saman kansu sai hira sukeyi suna shewa irin ta qawaye, bayan tashiga kati ta bata ta siyo mata na MTN sarai tasan wurin akwai nisa ba kadan ba, bayan Khadija ta kawo mata katin ta kar6a sai ta daka ma Khadija tsawa, wai ita ba MTN tace ba Airtel tace, haka Khadija ta koma ta chanzo mata da Airtel din.

Bayan ta kawo mata zata koma kicin tayi kaci6us da Adnan zai nufi garden sanye yake cikin gajeren wando da rigar polo, ya kalle ta cikin sakin fuska, yace.

"Kawo min ruwa ina garden"

Kanta na qasa ta amsa ta to sannan ta wuce firij qirjinta na dukan tara tara, ita ta rasa meyasa take jin tsoronsa ko idanu bata bari su hada, koda sun hadan cikin rashin sani take saurin kauda tata fuskar, da zarar sun hada ido zata ji gabanta na faduwa, ta dauko ruwa da lemon kwali ta dora saman tire sannan ta dora kofin glass sama ta wuce garden gabanta na cigaba da faduwa tana addu'ar Allah yasa kar ya kuma sata wani aikin data kai masa juyowa zatayi.
Zaune ta iske sa saman kujerun shaqatawa mai zaman mutum biyu da table a tsakiya, a lokacin da ta isa waya yakeyi da su Ummi tanajin yana tambayar ya jikin Abban, da sallama ta isa ta aje tiren ta juyo da saurinta don kar ya kuma kiranta, batayi zato kawai sai ji tayi ya kira sunanta cikin wata irin muryar data ratsa mata har cikin kai, gabanta ya bada ras! Ta runtse idanunta tana mai karanto addu'ar Allah ya sauqaqa mata tsoron mutumin nan da takeji, a sanyaye ta juyo tana tafiya kamar wata marar lafiya, bayan ta isa kanta na qasa ta durqusa alamar girmamawa sannan tace

"Gani"

Kallonta yayi ya kauda kansa gefe sannan cikin muryarsa mai dadin sauraro yace

"Zuba min ruwan ki miqo min sannan ki zauna a nan akwai maganar da nakeso muyi dake"

Qirjinta ya buga, kanta na qasa dai, ta daure ta bude lemon ta tsiyaya masa a kofin sannan ta miqa masa hannunta har kyarma yake.

Wurin ya amshi kofin hannuwansu suka gogi juna, jikin Khadija yayi wani yar, tayi saurin janye hannunta, gabanta na ci gaba da faduwa, ya tsare ta idanu yana kur6ar lemon sannan ya sauke ajiyar zuciya yace

"Zauna mana"

Ta miqe jiki babu qwari ta zauna tare da takure jikinta wuri daya kamar mai jin sanyi.

Sanyin da taji ne ya sanya ta tuna cewa ashe fa bata sanya hijabi ba, kunya ta kama ta, doguwar rigar atamfa ce jikinta rigar ta kamata daga sama sai ta bude daga qasa, ta daura dankwalin atamfar.

"Khadija wai me kike nema a wurina ne? Idan har tuba kikayi daga halayenki ne ko kuwa kina da wata manufa ta daban da har kika yanke shawarar kawo kanki gareni, na roqe ki da ki daure ki fada min dalilinki na wulaqanta Dan Adam?"

Saukar kalaman Adnan wanda yayi sanadiyar jefa ta cikin rudu har sai da ta dago kanta babu shiri ta sauke su kan kyakkyawar fuskarsa, wanda shima ita din yake kallo yana jiran amsar ta, tayi saurin sadda kanta qasa sanadin kwarjinin da taga yayi mata a idanu.

"Ke nake sauroro"

Bakinta na rawa tace
"Ban...bangane b...a"

Yayi murmushi.

"Menene ke baki gane ba ca nake Hausa nayi miki ba yare ba?"

Idanunta suka kawo ruwa ta sadda kanta tana cigaba da wasa da yatsunta.

"Nasan dai kin gane inda na dosa Khadija, abinda yafi bani mamaki dangane da lamarinki shine gaki dai da kudi, da gata har ma da ilimi.

Meyasa kika za6i ki wulaqanta Dan Adam da ki kyautata masa? Bakisan darajarsa bane ko kuwa kin sani kika manta da hakan? Meyasa na ganki da wannan shigar alhalin ke diyar hamshaqin mai kudi ce wata qila ma diyar wani sanata ko minista" meyasa kika za6i zama nan gidan bayan da iyayenki da gatan ki meyasa? Khadija ina buqatar amsoshin nan daga gareki kar ki ce zaki 6oye min"

Kanta ya daure, to meyake nufi da wannan? Ita sam ta kasa fahimta.

Sunfi minti daya yana tsare ta da idanu, amma sam Khadija ta kasa magana asalima kanta na qasa tana wasa da yatsanta tana son gano inda magananganunsa suka dosa.

Daga qarshe miqewa tsaye yayi ya yana duba agogon hannunsa sannan ya dube ta ya ce

"Zan fita idan na dawo zamu qarasa maganar nan Khadija"

Daga haka ya wuce kansa tsaye cikin gida ta dago tana dubansa har ya 6ace zuciyarta cike da tambayoyi kala kala.

Maryam S belloπŸ’–

No comments: