TAGWAYE NE? Na Maryam s bello {26 to 30}
ππππ❤ ππππ
ππ
π
MSBπ
Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM
*(zeebee)*
*(Xarah)*
Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.
*πTagwaye ne? π*
26
Khadija tayi zaune sukuku kanta a matuqar daure, minti biyu tsakani ta hango shi ya fito cikin shigar qananan kaya wando baqi da riga baqa, fuskar nan tasa babu walwala, tana kallon sanda ya bude motarsa ya fice daga gidan, ta kasa dena kallon hanyar da ya bi har sai da nancy ta sanar mata zata fita siyan kati tazo ta duba miyar kafin ta dawo, ta amsa da to kafin ta miqe jiki babu qwari ta kwashe kayan sannan tayi cikin gida.
A falo ta iske Badiya da qawar ta wadda batasan sunanta ba, gaishe su tayi ta wuce kicin abinta.
Tana cikin motsa miyar data kusa tsanewa ta jiyo hirar tasu sai faman daga murya suke sai kace ba mata ba.
Zee ta kalli Badiya da mamaki shimfide saman fuskarta tace.
"Wai nikam Badiya ina kuka sami wannan cute yarinyar?"
Badiya ta ta6e baki tace
"kwashekwashen Ummi mana, taje ta jaji6o mana ita wai a matsayin taimako"
Zee ta ta6e baki
"Amma fa yarinyar nada kyau shekararta nawa?"
"Oho ina zan sani ne ki kirata ki tambaye ta mana ke ni na fa tsane ta, tunda ta shigo gidannan naji batayi min ba, kinsan ma ni fargaba ta daya kar ta yi min kwacen Adnan dina wanda na ci buri akansa"
Zee ta kyalkyale da dariya har tana duqewa qasa.
Badiya ta qule tana tambayar Zee dariyar me takeyi. Sai da ta tsagaita da dariyar da takeyi sannan ta dago tana duban Badiya da ta hade rai tana kallon tv.
"Haba qawata maida wuqar, kinsan dariyar da kika bani wai kinci buri akan Adnan, har kin manta akwai alqawarin wata akansa ne? Kefa idan ma zaki aure shi to a matsayin ta biyu za'a kai ki"
Ran Badiya ya 6aci an sosa mata inda ke mata qaiqayi, ta tsani jin ance Adnan zaiyi aure sheyasa ma ko kusa bata so ana tuna mata, ta tashi da gudu tayi dakinta Zee ta bi bayanta tana bata haquri.
Khadija ta leqo tana kallon ikon Allah, ko me suke yi ma gudu kuma oho, ta koma kicin don kwashe miyar don ta yi, daidai nan nancy ta dawo ta kamata suka qarasa.
* * *
Heenad na kwance saman gado duk ta qode ta rame dama can ita ba me jikin qiba bace, taci kuka har ta gode Allah, Daddynta yayi tafiya, yanzu ita akayi ma alqawarin aure da wanda bata sani ba, ita yanzu an mata adalci kenan? Ta qara fashewa da kuka mai cin rai har yau tana da na sanin jefa kanta cikin soyayya da mutumin da baisan tanayi ba, a wannan halin Abida ta iske ta.
Da mamaki ta qaraso tana kiran sunan qawar tata, Heenad ta dago da jajayen idanunta ta rungume Abida tare da qara fashewa da wani kukan, Abida ta rude kanta ya daure, da niyyar masifa ta shigo saboda tun jiya take kiran layin Heenad bata daga ba, ga messages ta aika mata ba iyaka don haka ta taho taga ko lafiya.
Sai da ta gaji don kanta tayi shiru sannan ta kwashe labarin komai ta fada ma Abida, itama Abida abin ya bata mamaki, ko dayake ta fahimci cewar shi Daddy bayada laifi kuma ita bataga aibun hakan ba, nan dai tayi wa Heenad nasiha mai ratsa zuciya tare da qara jajdadda mata muhimmancin alqawari, ita dai Heenad jinta take amma ita zuciyarta na can ga soyayya wanda bata sani ba, kuma gani take bata iya auren wani mahaluqi a duniya idan bashi ba, ta dan saki jikinta babu laifi sun dan ta6a hira da Abida sai wajajen biyar na yamma ta miqe zata tafi gida har waje ta raka ta sannan ta juyo ciki.
* * *
Yau ta kasance Saturday satinsu Ummi uku cif da tafiya kuma a yau dinne zasu dawo don sunyi waya da Adnan sun shaida masa Abban ya samu sauqi, sunce za'ayi masa aiki amma ba yanzu ba ita ma Khadija an bata waya ta gaishe su ta masa ya jiki, a sati biyun nan tun da Adnan ya kira Khadija sukayi wannan maganar basu qara yi ba saboda sam Khadija bata bari su hadu, bata fitowa sai ya fita aiki kuma kafin ya dawo ta kwanta, sai dai ta kasa gane meyasa a duk lokacin da ta juyo muryarsa take kasa sukuni, gabanta yayi ta harbawa kamar zai hudo qirjinta ya fado, ita taji haka sai tayita addu'ar Allah ya sauqaqa mata wannan tsoro da takeji na Adnan.
Tun safe gidan ya kacame da aiki, aikin ya mata yawa kasancewar nancy bata nan an aiko mahaifiayarta batada lafiya can Uyo state dole ta tafi babu shiri kwana biyu kenan da tafiyarta, Khadija na kicin tana yanka karas din fried rice din za'ayi musu Mudi mai wankin mota ya shigo da leda niqi niqi ya dire su yana maida numfashi, Khadija ta kalle shi tana dariya tace.
"Malam Mudi wannan kayan fa?"
Ya hadiye yawu sanadiyyar qamshin da miyar data bugi hancinsa, Khadija ta iya girki saboda nancy da ke koya mata indai girki ne nancy ta iya a nan fannin sannan yace.
"Kai yau zamuci dadi, miyar taki duk cika min ciki wallahi, don Allah idan kin gama ki dan zuba min da yawa harda naman shima"
Tayi murmushi tana gyada kai alamun to sannan tace
"Ina tambayar ka menene a cikin nan ledar?"
"Ahaf na manta kaji ne manya guda takwas inji yalla6ai sai kifi gashi inji Badiya wai farfesu zakiyi mata"
Ta kalli kifin taga girmansa sai da taji tsoro, ita ina zata iya da wannan kifin?"
Mudi ya dan rage sautin muryarsa yana waige waige sannan yace.
"Wannan munafukar ce Badiya zakiyi ma farfesu wai kinji Adnan zata ba tace ita tayi, tsabar iya yi wai ita dole sai ta burgesa"
Ita dai Khadija bata ce uffan ba aikinta kawai takeyi, :da taga yana neman wuce gona da iri sai tayi maza tace.
"Nagode malam Mudi kaje idan na gama zan kawo maka"
Yayi dariya mai sauti sannan ya fice, second biyu sai gashi ya leqo.
"Af na manta kajin biyar zaki gasa uku kuma ayi fefe cikin ake cewa kome?"
Tayi dariya tace "papered chicken ne jeka na gode"
Ta bada himma da aikin sai gashi kuma qarfe biyar da rabi na yamma ta kammala, ta jera komai saman table ta gyara ko ina na gida tsaf tayi turaren wuta sannan tayi wanka, gaba daya jikinta ciwo yakeyi saboda ta jiqatu da aiki.
8:50 PM
Qarar bude gate ta juyo tana kan sallaya tana lazumi, kafin kace me gidan ya kacame da hayaniya, ashe su Asma'u duk sunzo ganin jikin mahaifinnasu, suka shigo falo ana ta gaishe gaishe da ban gajiya, Khadija ta shafa addu'a ta linke abin sallar ta fito babban falo inda takejin hayaniya, kunya ta kamata yadda falon ya cika da mutane anya zata iya shiga? Tana cikin saqe saqe ta hango akwatina jere guda takwas harda dan kit dinsu, bata kawo komai a ranta ba ta sa kai cikin falon tana tafiya kamar marar lakka. Kafin ta qarasa shiga ta tsinkaya muryar Isma'il yana fadin.
"Su babban yaya an kusa zama ango" duk suka kyalkyale da dariya.
"Wazaiyi aure ta tambayi kanta?"
Kafin ta lalubo amsa ta juyo muryar Bilkisu tana fadin.
"Wai Ummi daga zuwa asibiti sai ku kama hado lefe?"
Ummi tace "to ai yafi sauqi kin manta bikin saura sati hudu ai gara mu fara ragewa ko ba haka ba Adnan? Kuma Alhajin satins daya ya warke.
Gaban Khadija ya bada wani ras! Taja baya ta 6uya bayan qofa tana raba idanu.
Bilkisu tace take fadin tana dariyar zokaya "ai Adnan kamar ba ango ba sam baya wani shiri"
Gaban Khadija ya qara bugawa, ta rasa a wace duniyar take, ta fara taku baya baya sannan ta juya tayi daki da gudu tana haqi.
Saman gado ta fada dafe da qirji har yanzu bata gama gaskgata zancen ba, sannan ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, tana mamakin jin ance Adnan zaiyi aure, ba shiri taji kuka na neman qwace mata, sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru, ita kanta ta rasa dalilin kukanta. Ta share hawayenta
ta miqe a sanyaye ta koma falon don gaishe dasu Abba.
Maryam S belloπ
ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM
*(zeebee)*
*(Xarah)*
Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.
*πTagwaye ne? π*
27
A sanyaye ta shiga falon da sallama, falon daga Ummi sai Abba sai Adnan suna hira, Abba na saman kujera yana shan furar da taji nono jefi jefi yayin da Adnan ke zaune qasa kusa da kafafuwansa, suna dan ta6a hira.
Gaba daya suka maida dubansu gareta bayan sun amsa sallamar, kanta na qasa ta russuna ta gaishe su, ta masa ya jiki ya amsa yana murmushi irin na manya, jefi jefi take duban Adnan da gefen ido a yayin da yake latse latse a wayarsa qirar Iphone 6s, gabanta ya harba a lokacin da sukayi ido biyu sakamakon dago fuskarsa da yayi da zummar magana, kallonta yake kamar yana karanta wani abu saman fuskarta a yayin da ita kuma tsoro da fargaba suka far mata, take kuma gabanta ya haundukan tara tara.
Da sauri ta miqe har tana hada hanya ta bar falon ta koma dakinta ta sauya kayan baccin da Ummi ta bata sannan ta kwanta. Sam ta kasa bacci sai mutsu mutsu takeyi, idonta biyu har wajen uku saura, sam ba alamun bacci a tare dasu, daga qarshe miqewa tayi ta shige bayi ta dauro alwalla tayi ta nafilfili tana nan har aka kira sallar asuba.
Washe gari bata tashi ba sai qarfe goma saura a dalilin baccin da yayi awon gaba da ita.
Bandaki ta shiga ta wanke bakinta sannan tayi wanka ta fito ta zura wata doguwar riga dinkin bubu marar nauyi cikin kayan da Ummi ta siyo mata sannan ta dora hijabi qarama ta fito, kicin ta iske su Asma'u da Bilkisu suna ta hada kalacin safe, ta gaishe su suka amsa da fara'a, sannan ta kama masu suna hira gwanin sha'awa har suka kammala.
Bayan sun gama karyawa nancy ta dauko wata yarinya da taji ana kira da Ihsan yar kimanin wata bakwai tana rigima aka miqa ma Bilkisu ita, nan ta fahimci cewar diyar Bilkisu ce sai dai bata ga anzo da ita ba kwanaki da suka zo tana asibiti.
Bilkisun na ta mitar rigimar Ihsan Adnan ya sauko cikin jallabiya fara, da alama yanzu ya tashi daga bacci, nan ya zauna cikin yan uwansa ana ta hira har ya amshi Ihsan da take kuka tana miqa hannu almaun ya dauketa, Khadija na kicin tana wanke wanken kwananukan da akayi amfani dasu taji ana qwala mata kira.
Ta daurewa hannunta ta fito, Bilkisu ce tace mata ta goya mata Ihsan zata shiga wanka, to ta amsa da to, ta miqa hannu da zummar amsarta daga hannun Adnan yarinya ta maqe taqi zuwa, akayi juyin duniya Ihsan taqi zuwa, sai da Adnan din yayi mata wayo tukunna Khadija ta amshe ta hannuwansu na gogar juna, jikin Adnan yayi wani yar, ita kuwa Khadija har kyarma takeyi tare da shiga wani irin yanayi da ta kasa tantance irin shi, da ta samu ta amshi Ihsan tayi daki da sauri ta goyete radam a baya ta fito ta koma don qarasa aikinta.
Bayan kwana 2 da dawowar su Abba Rashidat tazo daga Yola, tazo yau washe gari Aisha ta haihu namiji, bayan kwana biyu da haihuwar kuma aka hau shirin zuwa barka gaba dayansu yaran ciki kuwa harda Khadija, Ummi kadai da Abba aka bari.
Ranar suna ba'ayi wani tarion suna ba, baby yaci sunan Abba ana kiransa da daddy.
Washe garin suna, duk sukayi shirin dawowa gida, su Bilkisu kuwa sun dawo washe gari kowacce ta koma gidan mijinta.
Maryam S belloπ
ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM
*(zeebee)*
*(Xarah)*
Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.
*πTagwaye ne? π*
28
Badiya na zaune dakinta tana kukan fitar rai wane an aiko ta, tun jiya take kuka bata rintsa ba sakamakon akwatinan lefen Adnan da taci karo dasu jiya da daddaren, tunda ta fahimci cewar na auren Adnan ne ta rude ta dinga kuka kamar ana cire mata rai, bayan taci kukanta ta qoshi ta daukar ma kanta alqawarin auren Adnan ko ta wane irin hali sannan kuma bayan ta aure shi ta kori matar tashi don bazata iya jure ganin tana hada Adnan da wata ya mace ba.
* * *
Ita kuwa Heenad a nata 6angaren batada aiki sai kuka, har abin nata ya soma 6ata ma iyayenta rai! Hankalinta bai qara tashi ba sai da taji ana maganar lefenta za'a kawo next week, nan ta rude ta dinga rusa kuka wai wallahi batason auren, ita tana da wanda take so, da qyar suka lalla6a ta suka samu tayi shiru.
Ko dan shirin da akeyi wa amare Heenad taqi yarda ayi mata komai, wai ita ko event daya bazata ba, kawai ita a daura auren a kaita in yaso ta mutu ta huta!
Sai da Mami tayi da gske aka yi mata dilka, gyran kai kuwa ta hana tace ba mai ta6a mata kai. Ta kuwa qara kyau da haske,
Haka dai suke lalla6a ta don su kansu iyayennnata sun san ba'ayi wa yar tasu adalci ba. Sai dai sukan danne basu so su nuna hakan a gaban Heenad din, dama burin su ta amince ayi auren komeye zai biyo bayan auren mai sauqi ne, can itada mijin.
* * *
Adnan na zaune a garden ya dan kwanto jikin kujerun shaqawa kansa na kallon sama ya lumshe idanunsa kamar mai bacci, nan kuwa damuwa ce ta taru ta cunkushe masa, kallo daya zakayi masa ka tabatar da hakan.
Bangare daya ciwon Abba ke damunsa, dayan 6angaren kuwa auren da ake so a kakka6a masa da yarinyar da bai sani ba, ya dai santa a bakin Abbansu don yana yawon amtatonta. Yayi zurfi cikin wannan tunanin ya jiyo siririyar muryarta daya ratsa masa har cikin kai, ya bude idanunsa ya sauke su kan kyakkyawar fuskarta da ke sunkuye a qasa, ya qura mata idanu sannan yayi saurin kawar dasu gefe, Khadija ta dake duk da kuwa jin zuciyarta take kamar zata hudo qirjintan ta fado qasa, da qyar dai ta tattaro dukkan nutsuwarta sannan ta sanar masa saqon Abba akan yana son ganinsa a falonsa na zama, daga haka ta koma ciki sauri ba tare da ta qara cewa komai ba.
Ya dade yana kallon hanyar da ta bi kafin ya miqe a sanayaye ya bi bayanta.
Zaune Abba yake saman kujera yana kallon tashar Aljazeera sallamar Adnan ce ta katse masa kallon da yake, ya dauki remote din ya rage qarar magana tukunna ya amsa masa sallmarsa, Adnan ya shiga ya zauna gefen qafuwan Abbansa kansa na qasa yace.
"Barka da hutawa Abba, Ya qarfin jiki?"
"Yauwa barka Adnanu, jiki Alhamdulillah"
Abba ya dan gyara zamansa yana duban dannasa yace.
"Adnan kasan cewar aurenka bai wuce sati uku masu zuwa ba ko?"
Ya gyada kai
"Yauwa, kuma naga har yanzu bakaje kun gana da yarinyar ko sau daya sannan banga ko sau daya ka kirata a waya ba, ai ca nake sai da na neman za6inka kace kai duk za6in da nayi maka shine naka, amma sai nake fahimtar cewa kamar bakayi na'am da zancen aurennan ba domin kuwa duk ina lura da kai kwana biyun nan yadda ka shiga damuwa, Adnan ina so ka fada man gaskiyar magana kuma abinda ke cikin zuciyarka, shin ka yarda ka amince da maganar aurenka da Fatima ko baka amince ba?',
Cikin maganar Abban nasa ya fahimci ya shiga damuwa sosai, shi kuma duk abinda zai 6ata ran Abbansa ba so yake ba, ya dan muskuta kadan ya gyara zamansa, kansa na qasa ya girgiza kai alamun a'a sannan yace.
"A'a Abba ko kusa ba haka bane ba, na amince da aurennan, sannan damuwar da kaga na shiga na ciwonka ne yake damuna, amma in banda wannan babu komai"
Abba yayi murmushi irin nasu na manya sannan yace.
"Shikenan Adnan, Allah yayi maka albarka, ai ciwo ba mutuwa, kuma idan ma mutuwar ce ka isa ka hana ta zuwa ne? Duk damuwa ba naka bane addu'a dai zaka cigaba da yi min,
sannan magana ta biyu kan maganar yarinyar nan ne Khadija"
Gaban Adnan ya fadi.
"Kaga dai muna iya bakin qoqarinmu na ganin an ga mahaifiyarta amma har yanzu shiru kakeji, inaso ka dage akan qoqarin da kake don Allah, sai kuma Mahaifiyar ka ke sanar dani kan cewa ta fahimci yarinayar kamar batayi karatu ba, shine muka tattauna da ita kan cewa zata shiga lesson school na wata daya, tunda ance saura ko wata daya da sati biyu ne makaratun zasu fara zana jarabawarsu ta qarshe, idan ta gama lesson school din na wata daya sai taje ta zana jarabawarta hakan yayi ai ko?"
Adnan ya girgiza kai a sanyaye sannan yace
"Hakan ma yayi"
Abba yace "shikenan sai ka qoqarta ka binciko makarantar da za'a sanya ta daukar darasin ko? Allah yayi maka albarka"
Amin yace sannan ya miqe a sanyaye ya hau sama, yayi wanka ya shirya cikin yadi mai taushi fari tas, dinkin ya zauna das a jikinsa, a qofar dakinsa yayi kaci6us da Ummi zata je dakinta, nan ya sanar mata zaije gidansu Khalil sai anjima zai dawo, tayi masa addu'ar a dawo lafiya sannn ta wuce dakinta don hutawa.
Washe gari Adnan ya fita don nema ma Khadija makaranta, kuma yayi sa'a ya samu suna koyar da duka subjects din science da kuma arts, form ya anso mata ya biya kudin wata dayan, bayan ya gama duk abinda ya dace ya juyo gida.
Maryam S belloπ
ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM
*(zeebee)*
*(Xarah)*
Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.
*πTagwaye ne? π*
29
Zaune ya hango ta a garden tana yan waqe waqenta bai ganin fuskarta kasancewar ta bashi baya, da takunnan nasa na qasaita ya iso inda take tare da kiran sunanta daidai nan kuwa qamshin turarensa ya doki hancinta, ta lumshe idanu kafin ta bude, sannan ta juyo gami da amsawa da yar siririyar muryarta bayan ta miqe tsaye kanta a sunkuye gabanta na dukan tara tara, Ya subhanalillahi! Abinda Adnan ya furta a ransa a lokacin da yayi tozali da kyakyawar surar da Allah ya zuba mata, yayi tsai da idanu yana kare mata kallo, sanye take cikin wani material dinkin riga da siket, mai kaloli da yawa a jikinsa, ba hijabi a jikinta amma ta yane karamin gyale har saman kanta, shirun da taji daga garesa ya sanya ta dago fuskarta a hankali, itama kanta batasan lokacin da ta qura masa idanu ba, shima ita din yake kallo ba tare da ya ankare ba, ita ta fara saurin kauda tata fuskar cikin jin kunyar abinda tayi, shima kuwa da sauri ya kauda tasa fuskar, cikin raunanniyar murya ya soma magana.
"Ga forms dinnan naki na amso, sai kiyi kokarin cikawa gobe da safe idan Allah ya kaimu zamuje ayi maki interview"
Ya karasa magana yana mai miqa mata forms din, a sanyaye ta karba.
Har ya juya ko wane tunani yayi kuma ya dawo yana fadin.
"Kinga kawo nan na taimaka miki ki cika"
Tayi dan murmushi tukunna ta miqa masa, a yan kujerun zaman mutum biyu suka zauna, yana tambayarta tana bashi amsa yana rubutawa daga haka suka kammala, akazo inda za'a lika passport (dan karamin hoto) nan tace bata dashi, aiko ya dauke ta sukaje aka dauko sannan suka dawo gida ya sanar ma su Abba an gama komai gobe zai kaita interview, yasha albarka kam, kuma shima yaji dadi har cikin ransa.
Washe gari ya kaita akayi mata duk abinda ya dace, aka bata uniform kan cewa gobe zata fara zuwa, ya siya mata littatafan amfaninta, daga nan shopping suka je, ita dai Khadija sai binsa take kamar raqumi da akala, wani shopping mall suka je, ya daukar mata takalmi da safa, sai yace ta dauki duk abinda takeso, kunya ta kamata ta kasa daukar komai sai ma kanta da ta sunkuyar, murmushi yayi ya girgiza kansa sannan ya dauki, su body spray, turare, kayan kwalliya, man shafawa, ya siya mata kaya kala biyar na zaman gida, sai sweater(rigar sanyi) Saboda ya kula batada ita sai wadda Ummi ta bata kuma ta mugun yi mata yawa, suka gama yaje ya biya shi kansa mamakin kansa yake meyasa ya yi mata siyayya haka?
Sun kammala zasu tafi kenan mutumin ya kalle su cike da sha'awa yace.
"Matar ka nada kyau, kun dace fa kaga yadda ake kallonku nikam kayi hakuri kasa daurewa nayi sheyasa na fada maka"
Gaban Khadija ya fadi, ta kalle shi ta kalli kanta meye hadin kifi da kaska? Ina ita ina Adnan? Ay Adnan yafi karfinta.
"Mun gode" shine abinda Adnan yace sannan yayi gaba abinsa, Khadija ta sauke ajiyar zuciya sannan ta bi bayansa.
Basu suka iso gida ba sai yamma, bayan sun fito shi yayi cikin gida ita ma ta wuce dakinta.
Tana tsakar fiffido kayan da ya siyo mata aka banko qofar babu ko sallama.
Badiya ce tsaye ta rike qugu kai kace tana shirin dambe, idanunta jawur da alama taci kukanta ta qoshi, gefen Khadija ta zaune saman gado tana mata wani irin mugun kallo tana kare ma jikinta kallo, irin kallon baki isa ba.
Sai da ta kwashi tsawon minti biyu tana mata wannan kallo tukunna ta fara magana mai nuni da alamar cikin fushi take matuqa.
"Ke talaka! Kalle ni da kyau ki kalli kanki ki kalleni kigani idan irinmu daya"
Sai a sannan Khadija ta dago tana dubanta.
Eh to ba fara bace amma kuma baza'a kirata da baqa ba, tana da manyan idanu farare, sai hancinta madaidaici, bakinta nada dan fadi,sanye take cikin wando baqi matsatse da riga matsatsiya kalar ja, tana da tsawo kuma tanada yar qiba kannan yasha qarin gashi, Khadija ta sauke ajiyar zuciya ba tare data ce komai ba. Sannan Badiya ta cigaba da magana cikin isa.
"Kin kyauta da kika kalle ni da kyau, ko nan kadai kinga bambacin da ke tsakanina da ke, to ki bude kunnenki da kyau ki saurare ni da kunnen basira! Ba tun yau na kula da ke ba, kuma sai dana tabbatar da zargina sannan kika ganni nan"
"Zargi kuma....?"
"Khadija ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara kin kamu da son Adnan!
Ta dago a razane gabanta yayi mummunar faduwa...
"kar ki musa man domin na tabbatar da hakan, abu na farko ki sani Adnan yafi karfinki ko kusa kar ki kai kanki inda Allah bai kai ba! Ki tsaya matsayinki. Na biyu ina kaunar Adnan ba tun yau ba, saboda haka ki kiyayi kanki kar ki yarda kice zakiyi kishi dani, don kece zaki wahala. Abu na uku kinga aure zaiyi kuma ina sa ran zai aure ni daga baya amma ita din wadda ya zai aura wallahi billahi sai ta gwammace kida da karatu! Abu na karshe ki fita harkarsa, wallahi tallahi idan kikayi wasa zan dauki munnunan mataki a kanki, saboda shi kansa Adnan ba inda zai kai mace kamar aljana irinki ba, gaki dai jahila bakiyi boko ba, don haka ki kiyayi kanki ni dinnan, ta nuna kanta, zan iya yin komai ga mutumin da yayi katanga tsakanina da Adnan da fatan kin fahimce ni"
Daga haka ta miqe ta fice tana mai jin dadin abinda ta aikata da kuma fatan zata rabu dashi.
Bayan fitarta Khadija teyi zaune tana nazari, soyayya kuma? Ta tambayi kanta, bana fatan zuciyata ta kamu da son Adnan, Ya Allah kar ka bari zuciyata ta kamu da son mutumin nan, ta fada a yayin da wasu hawaye suka ziyarci kumatunta, sai kuma ta tuno da Ummanta, take kuma ta fashe da kuka, sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru. Shin Khadija kukan mey takeyi? Kukan tuno da mahaifiyarta ko kuwa maganganun da Badiya ta fada mata ne? Allah masanin gaibu!
Maryam S belloπ
ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM
*(zeebee)*
*(Xarah)*
Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.
*πTagwaye ne? π*
30
Khadija ta fara karatunta cikin kwanciyar hankali, kuma Alhamdulillah tana ganewa sosai, tunda sukayi maganar nan da Badiya bata kuma kallon inda Adnan yake ba asalima ko zama a garden ta denayi ta koma zaman daki bataso ta hadu dashi, bawai don gargadin da Badiya tayi mata ba, a'a ita bata son tashin hankali ko kadan ina ita ina fada da masu gida, ita da aka kawo da sunan taimako, don me zata so yin tashin hankali dasu?
BAYAN SATI BIYU
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah yau sati biyu da Khadija ta soma karatu, ta bada himma sosai tana karatunta, wanda idan har ta dage batada wani gatan da ya wuce tayi karatun, haka zalika kuma yau saura sati biyu da fara bikin Adnan da Hennad, saboda haka an fara hada hadar bikin, Abba da kansa ya bashi mukullin gidansa da ke cikin Hotoro, upstairs ne madaidaici mai dakuna uku, a sama sai falo biyu a kasa sai kicin babba, yayi ma Abba godiya ba kadan ba.
* * *
A 6angaren Heenad kuwa, hankalinta qara tashi yake, gasu Mami sai shiri sukeyi hankali kwance, ita kam in banda haushi ba abinda takeji, Mamin ma ta dena kula ta saboda tayi ta gaji da halinta, sam bata so ana shirya ta kamar yadda ake shirya ko wace amarya, kullum tana daki bata ko fitowa.
Ana sauran sati daya bikin, aka je jere, an yi komai nagani na fada gidan yar gatan baba, yaji kayan more rayuwa, Abba da kansa ya kira mai dilka, makeup, kullum sai sun sha drama don Heenad sam bata yarda a ta6a mata jiki.
Gidan Mami ya dauki harama yan uwansu na nesa an fara zuwa, ga yan uwan Heenad na yola suma sun zazzo, da yake tsararrakin Heenad dinne kusan su biyar.
* * *
Daka kalli Adnan zaka fahimci matsananciyar damuwar dake shimfide a saman kyakkyawar fuskarsa, amma tilas yake 6oyewa gudun kar Abba ya gano halin da yake ciki.
Ummi kam gida ya cika da yan uwa da abokan arziki, ga maqota dake ta zarya don taya murnar Ummi za'a aurar da da namiji.
Ummi tayi ma su Khadija dinki kala uku uku wanda duk Abba ne ya bada kudi aka siya mata gyale da kusan ko wane ya shiga da kayanta sai dai sam bata cikin walwala kallo daya zakayi mata ka tabbatar da hakan.
* * *
Heenad ce zaune saman gadonta ga abokananta nan da yan uwanta suna ta mata magiyar ta tashi a shirya ta za'ayi kamu amma sam taqi tace ita ba inda zata.
Wata daga cikin yan uwanta kusan tsarar Heenad din ce kusan yan watanni ne tsakani kuma abokiyar wasanta mai suna Ikhram tace cike da zolaya.
"Wai ita wannan amaryar ana ta fama da ita ta tashi a shirya taqi sai wani jan aji takeyi to ko sai mun kira ango yazo ya dauke ki ya shigar da ke sannan zaki yarda a shirya ki?"
Duka dakin aka kyalkyale da dariya wasu harda kashewa.
Haushi ya qara turniqe Heenad ji take kamar ta qwala ihu, ta goge qwallar dake neman zubo mata tare da hadiye wani qululun baqin cikin da ya tokare mata a maqoshi, ta kauda fuskarta gefen taga.
Asiya ta kara kyalkyalewa da dariya tana fadin.
"Ina ji sai Sumayya ta danne ki zaki tashi tukunna"
Dayake Sumayyar nada jikin qiba ba kadan ba 6akutu ce. Aiko dama kamar jira take ta miqe zata danne ta din tana dariyar mugunta, Heenad tayi wuf! Ta miqe da sauri ta shige dakin cike da jin haushin qawayenta. Tana jiyo dariyarsu suna cigaba da zolayarta.
Sai da aka shiga da ita sannan Abida ta iso, nan fa aka tashi aka hau shiri duk sun shan anko sunyi kyau.
Da yake kamun babu maza mata ne zalla sai a lokacin Heenad ta dan saki ranta, don dama bata qaunar haduwarta da angon.
Anyi kamu lafiya an gama da wuri wuraren goman dare aka tashi kowa ya tafi makwancinsa, zuwa yanzu Heenad ta dena bacci, duk tayi wani iri da ita ta rame, ga bata cin abinci.
Washe gari ta kama juma'a a ranar ne kuma za'a daura auren Adnan Usman Buhari da Heenad (Fatima) Ahmad. tunda Heenad ta tashi kanta ke matsanancin ciwo ko tsayuwa bata iya yi, Mami ce ta fahimci halin da take ciki ta shigo dakin, gefen gadon da Heenad din take kwance ta zauna tana kallon yar tata cike da tausayi, Heenad ta rungume tana kuka kamar ana cire mata rai, Mami ma sai da tayi qwalla, tayi saurin gogewa sannan tayi qarfin halin janye jikinta daga na Heenad, ta tallabo fuskarta da hannunta guda biyu tana share mata hawaye. Nan tayi ta mata nasiha mai ratsa zuciya, da wa'azi, sai da ta tabbatar Heenad din ta saki ranta har ma ta sha ruwan tea tukunna ta rabu da ita a dalilin aikin abinci da ake ta yi, Mamin zata je ta rika dubawa don komai yayi yadda ya kamata.
Misalin sha dayan safe Heenad ta fito daga wanka a daidai bakin qofa ta fara ganin biji biji daga nan bata qara sanin inda kanta yake ba.
2:30 PM
A can 6angaren su Adnan kuwa bayan an gama sallah shiru ba waliyyan amarya ga jama'a an hallara, tun Abba na 6oye damuwarsa har ya fito fili ya kalli Adnan yace suje waje suyi magana.
Suka dan ke6e inda ba hayaniya sannan Abba ya soma magana cike da damuwa.
"Adnan wai lafiya naga ba waliyyan amarya gashi har 2:30 tana neman wucewa tun qarfe 2 aka sa amma an ajiye mutane ai hakan babu dadi"
Kafin Adnan yayi magana wayar Abba ta soma qara, ya duba ya ga sunan amininsa a kan screen din wayar wato Alhaji Ahmad.
Cikin sanyin jiki ya miqa ma Adnan wayar yace yayi magana, shima Adnan din a sanyaye ya dauka gami da yin sallama.
Ko sallamar Alhaji Ahmad bai tsaya amsawa ya soma magana cikin fushi.
"Adnan dama da kai nakeson magana, ina son sanar da kai na fasa hada auren Diyata Fatima aure da kai, saboda haka kuyi hakuri bazan kashe diyata ba saboda AUREN ALKAWARI, ka sanar da mahaifinka abinda nace maka yanzu sai anjima"
Gaban Adnan yayi mummunan faduwa, ya kalli mahaifinsa yaga yadda yayi tsai yana kallonsa, ya maida dubansa ga mutanen da suka taru su kawai ake jira, yanzu me zasu ce masu an fasa aure? Wannan wane irin tozarci ne?"
"Kar kace zaka 6oye komai Adnan saboda na riga naji zancen naku, saboda haka ka zo muje nasan me zanyi"
Abba ya miqe a sanyaye Adnan yabi bayansa.
Sun shiga sun zauna a sanyaye Abba ya soma magana.
"Ga dubu hamsin nan a maida auren da Khadija!"
Adnan ya dago a razane yace.
"Khadija....?"
Baiso yayi wata magana saboda ya fahimci ran Abba a matuqar 6ace yake, ya kalli yan uwansa dake zaune gefensa suma suka kalleshi.
Bai qara jin me ke faruwa ba sai ji sukayi ana fadin.
"AN DAURA AUREN ADNAN DA KHADIJA A BISA SADAKI DUBU HAMSIN, ALLAH YA SANYA ALKHAIRI YA BADA ZAMAN LAFIYA"
Su Khadija suna baya suna wanke kaji suka jiyo guda, wani abu ya tokare mata wuya, wato an daura kenan? Ba abinda gabanta keyi sai dukan tara tara.
Ta cigaba da abinda takeyi sai dai abinda tajiyo ya daki dodon kunnenta shi yayi sanadiyar sakin kajin da tayi wato wasu mata tsofaffi keta guda suna fadin.
"Amarya Khadija an daura kin zama ta Adnan shima ya zama naki"
Tayi tsai tana nazarin wace Khadija kuma bayan tana jin ana cewa sunan wadda zai aura Fatima, kafin ta ankare wata daga yan uwan Ummi tazo har inda take tare da jawo hannunta tana fadin.
"Ga amarya nan nata faman wankin kaji, muje a gyare ki tas in yaso an kaiki jibi"
Gaban Khadija ya yanke ya fadi, kanta ya dinga juya mata, da qyar ta daidaita nutsuwarta tana tambayar kanta yadda al'amarin ya juye, a falo ta tsinkaye mutane kowa na tofa albarkacin bakinsa. Wasu na murna wasu kuma akasin haka.
Ita kam ji da take al'amarin sabo, anya ba 6atan kai sukayi ba? Kafin ta lalubo amsa ta hango shi tsaye shiga dasu Isma'il, kallo daya zakayi masa ka tabbatar da ba lafiya ba.
Washe gari wata mata daga maiduguri Ummi ta kira aka soma gyara Khadija.
Maryam S belloπ
No comments:
Post a Comment